You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a daidai lokacin zai koma bakin aiki can Legos

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar Opey"

bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*58*

"Zaune na tashi ina goge hawayen idonta na dube shi sosai kafin na ce."" Ba ni da ajandar komawa gidan Alhaji Muntari domin kuwa da da niyyar hakan a cikin raina wallahi tallahi da kaddarar aure ba ta ratsa tsakanina da kai ba."""

Na numfasa Ina kallonsa yayin da shi kuma ya sake hade fuska tare da zubo mini ido da yanayi na neman rikici a tare da shi.

"""Abu daya zuwa biyu ya sanya ni kokawa da rasuwar bawan Allan nan ko ka yarda ko kada ka yarda bai dame ni ba na farko shine hallacin da ya yi mini a lokacin da nake buk'atar agaji ya yi mini da kudi da karfinsa daidai gwargwado. Na biyu yadda gidansa ya tarwatse tun yana raye yaranshi suke walagigi ina ga kuma bayan rasu. Maganar nan da muke yi da kai a yanzu hankalina nakan babban yaronshi Turmuzi wanda tun asali nasan da cewa fitinanne ne an ce mini yanzu lamarinsa ya sake ta'barbarewa, ba zan manta ba mahaifinsa ba ya sha kokawa akan sha'aninsa. Wad'annan abubuwa biyu dana lissafa maka sune suka fi tsaye mini a rai domin kuwa na riga nasan sha'anin zumunci a yanzu ya zama abinda ya zama tunda can ma danginsu ba masu zumunci ba ne balle yanzu da baya raye"

kuma dama shi kadai ne mai dan rufin asiri a cikinsu. Ni uwa ce kuma na yi gwagwarmayar rayuwa da yarana

nasan zafin da ake ji idan aka rasa wani 'bangare dalilin da ya sanya kenan nake tausayawa Anti Maimuna uwargidanshi domin ita amaryar ta gudu ta watsar da yaran yanzu gabad'aya suna hannunta kusan su tara ka gaya mini ya za ta yi dasu wane hali za ta shiga domin ciyar dasu da basu tarbiya.

"Shiru ya yi bayan na kammala maganata ya gyada kansa a d'an kausashe ya furta."" Wannan shagube ne kawai Amina, ni kike so ki yi wa guri a matsayinki na uwa ko?"""

Na yi kasa'ke ina kallonsa tare da auna maganarsa domin na gaza fahimtar inda ya dosa.

"Ya d'ora da cewa."" Af ai ni na uba ba ne, tunda ban haihu ba ban san zafinta ke da ki ka haihu ke ce ki ka san ciwon haihuwa."""

Jikina ya d'an yi sanyi jin yana nema ya canza magana nasan hakan baya rasa nasaba da masifar kishin da yake kasa sarrafa shi shine dalilin da ya sanya yake jujjuya maganar dole sai ya fusata ni.

Sai kawai na share shi ban sake cewa masa komai ba na koma na kwanta hawayen na sake bin gefan fuskata. Ni har ga Allah mutuwar Alhaji Muntari ta dake ni sosai na kuma kara tabbatar da cewa duniyar nan aikin banza ce. Wannan ya sanya ni rushewa da kuka da karfin gaske ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ya kuwa zabura! da ganin yadda nake kuka haikan! Sai jikinsa ya yi tubis ya matso kusa da ni sosai yana d'an jijjiga kafafuna da hannunsa. Na sake tsananta kukan da nake yi had'e da jan hanci.

"Ya nisa sosai kafin ya furta Yi shiru, yanzu dai Allah Ya jikansa abinda zan ce kenan, sai abu na gaba ina so ki gaya mini yadda kike so ayi tunda ai ni na zama rumfa sha shirgi muddin wannan hawayen zai tsaya ki fad'i yadda ki ke so a yi miki zan yi in sha Allahu."""

"A hankali na dube shi ina nazartarsa akwai sasaauci a fuskarsa da kuma alamun tausayi da nadama kuma tunda ya ce zai yi to babu shakka kuwa zai yi din."""

Na tashi zaune. Ya sanya tafin hannunsa na dama yana taya ni goge fuskata. Na ja hanci a karon da ba zai lissafi ba.

"Na ce."" Ni abinda nake so kawai wannan yaron nasa Turmizi a d'auke shi a kai makarantarsu Kamalu bayan haka kuma ka shirya mana zuwa gaisuwa ni kuma zan zauna da anti Maimuna mu tattauna idan ya kama sai a bata jarin da zata kama sana'a ko?"""

"Idonsa a kaina ya ce."" Hakan ya yi miki?"" Kaina na daga. Sai ya ce."" Ai ni mai aiwatarsa ne tunda haka ki ka tsara shikkenan za mu je amma sai bayan an yi addu'ar arba'in din Alhaji Amadu idan na yi musu ta'aziyya daga nan sai na wuce Legos abinda na manta ban gaya miki ba kuwa hajiya Maryam ta bukaci akan na bar mata Yusi dalilin sha'kuwar da take tsakaninsa da yaranta akaran kaina ban so hakan ba sai dai ba yadda zan yi ne a yanzu tana buk'atar rarrashi da kuma biye mata akan dukkanin abinda take so domin dakushe mata kewar maigidanta, na san macace mai kokari sosai za ta kula da yaron kamar nata sannan ta yi alkawarin mayar dashi makarantar da Adam yake zuwa sai ya cigaba da dora karatunsa ina fatan babu matsala ta b'angaranki ko?"""

Haka kawai na ji ban ji dadin saurin yanke hukuncin da ya yi ba. To amma ba yadda zan yi koda kuwa raina bai so ba haka zan kar'bi hukuncin da ya yanke na tabbatar da matar tana da wata matsala mai muni ba zai bar mata yaron ba.

Washe garin ranar da aka yi addu'ar cikar kwanakin arba'in na rasuwar abokinsa kamar dai yadda ya fad'a muka nufi kano bayan ya jima a gidan abokin nashi wanda na tabbatar da cewa ya shiga ne domin yi masu sallama da kuma kara tausarta yadda yake nuna kulawa da iyalin marigayin nake ji kamar kafin rasuwar tasa ya bar masa wasiyayyar hakan ne

Gidan Hajja muka sauke ta ce itama sai a yi tafiyar da ita don haka muna idar da sallar la'asar muka nufi gidan Alhaji Muntarin dake kawo jirga inda na zauna yau kwanaki hud'u kenan da rasuwar an tashi daga zaman makokin sai kad'an daga cikin 'yan uwanshi sai kuma Babanmu tare da Baba Sule da suke zaman jiran isowar isowarmu tunda mun yi waya dama.

Kai tsaye cikin gidan muka nufa ni da Hajja Yallabai din ya tsaya daga waje tare da Babanmu da jama'ar da suka ankara dashi.

Kasa juriya na yi ganin yadda anti Maimuna ta zabge ta zama kamar mashiriciya ba komai ne ya janyo hakan ba kuwa sai jinyya da fargaba da zullumi na rayuwa. Tana tare da kakarta wadda itace ke zaune tare da ita don ta d'eba mata kewar takaba sai kuma yaran gasunan sun kara girma Salimat ta zama cikakkiyar budurwa sai dai dukaninsu babu wata sutturar arziki. Sun gane ni gabad'ayansu suka dinga gaisheni na yi musu ta'aziyya na tambayi anti Maimuna Turmuzi ta ce mini tun washe garin ranar rasuwar uban ba su kara ganinshi ba.

Nan ta shiga warware mini halin da suke ciki da yadda wasu daga cikin ma'kotan da akayi zaman arziki suke dan taimaka musu ta ce mini ai tun kafin rashin lafiyar maigidan nasu ta yi tsanani Jamila ta gudu ta ce ba zata iya ba kuma duka yaranta ta bari ko bata fadi mini ba na gansu da idona. Muka ci kukanmu muka ko shi ni da ita don kasa

ha'kuri na yi a lokacin da take ba ni labarin tana kuka ina yi ina kallon Hajja ma tana share hawaye domin kuwa

kowanene dole ya tausaya rayuwar kuncin da suke ciki. Shigowarsu ita ta sanya muka yi shiru Yallabai din tare da Babanmu Baba Sule da 'yan uwan Alhaji Muntarin suka yi musu jagora.

Sosai ya yi wa anti Maimuna ta'aziyya ya kuma jajanta mata kwarai tare da yi mata nasiha mai ratsa zuciya da kawo misalai mabambamta daga karshe kuma ya kare maganarsa da jadadda mata cewa zai taimaka mata iyakacin bakin kokarinsa.

Godiya kakarta ta dinga yi har da kuka Hajja ta dinga bata baki akan ta daina kuka hakan ba komai ba ne face taimakon kai da kai idan har bai yi hakan da dukiyar da Allah Ya hore masa ba sai ta zame masa masifa.

Mun tattauna sosai da anti Maimuna inda muka tsaya a matsaya guda daya cewa bayan ta fita daga takaba zata fara gudanar da kasuwancinta a cikin gida za ta duba abinda ya fi saurin tafiya a unguwar sai ta kafa kowa rabonsa zai samu.

Muka nufi gidan Hajiya Dogara domin yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya. Matar da kyar take iya kallona saboda nauyi da kunyar abinda ta yi mini akan Kamalu ta dinga godiya kamar ta yi kuka domin alherin da Yallabai din ya yi musu na saukewa mamacin tarin bashin da ake binsa tun kafin ya yi bankwana da duniyar.

A ranar da daddare ya aiki Sukairaju da kayan abinci da masarufi masu yawa gidan Alhaji Muntari.

A gidana muka sauka gabad'aya har Hajja domin ya fi kusa da Dambatta ga dare ya yi Hajja ta ce da safe ta tafi ba ta son tafiyar dare.

Baba Tabawa da Yusura sunan lafiyar Allah kamar ina tare dasu domin abinci da kayan masarufin dake store dina ina tsammanin za su iya hauraa shekara basu kare ba. Bayan haka kuma akwai masu tsaro a gidan kuma mun yi waya da Sahura sati daya da tafiyata na ce ta dinga zuwa gidan tana duba su duk sa'i da lokaci.

Baba Tabawa kuwa aka ci sa'a ta yi favorite dinsa towon dawa amma miyar ku'bewa bushashshiya sai dai ta wadatu da daddawa da nama sai k'amshi take yi. Aikuwa ya ci sosai har yana tsokanarta wai ta fi ni iya abinci dama idan na yi towo ha'kuri kawai yake yi yana ci. Hajja itama ta yaba mata sosai ta ce mini a ajiye mata d'umame da safe kafin ta tafi sai a d'umama mata shi. Baba Tabawa tace ai kamar ta sani ta yi shi da yawa.

Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biyani hakkina ba

Had'uwarmu ta daran yau sai ta zama ta daban domin kuwa lamarin da ya bijiro dashi bai samu kar'buwa ba a

wajena yayin da shi kuma ya kafe kai da fata sai ka ce wanda aka yi wa wahayi lallai ta haka yake so ya biya bukatarsa to sai bijirewata ta wanzar mana musayar yawu domin kuwa ni dai ban ta'ba jin inda aka yi wata kwanciyar aure a tsaye ba. A ganina ma ta wannan sigar ta yaya mutum zai fahimci wani abu ya za a yi lamarin ya yi armashin da kowa zai gamsu. Ya dage shi fa ga ta yadda zai yi domin sai ya fi gamsuwa a cewarsa ko ya koma zai jima sha'awarsa ba ta motsa ba ni kuma na ce ba zan iya jurar tsayuwa ba na amince a yi akwance duk yadda yake so zan yi amma a tsaye ba zan fahimta ba. Ai lamarin na mutum biyu ne ba na mutum d'aya ba. Sai ya fara fad'in ai Ubangiji ya ce ku shiga gonakinku ta kowace siga amma ban da ta waje daya don haka shi yau zai gwada yi a tsaye. Tun abun yana ba ni dariya da mamaki har ya dawo ba ni haushi da ganin kamar yana so ya sauka daga koyarwa addinin musulunci ya bi turbar nasara domin kuwa sune shaidanu masu kirkiro abun da zai cutar da mutane.

Ya ce idan ba zan amince ya yi ta haka ba kuwa sai da na yi sucking dinshi har ya biya bukatarsa. To dama dama wannan da sauki tunda wani sa'in ina yi masa amma ba sosai ba don baya ganewa muddin ba wajan nan ya shiga ba. Ya za a yi sucking ya iya gamsar dashi a yadda yake sai mu kwana ba mu rintsa ba. Amma dai na fi aminta da yin hakan akan ya yi a tsaye k'afafuna ma ba zasu iya jurewa ba.

Sarewa na yi da sha'aninsa domin kuwa duk tsayin lokacin da na d'auka ina yi masa abinda ya buk'ata din ko gezau bai yi ba wai da sunan samun satisfying yana dai nishad'antuwa k'warai da gaske tabbacin yadda nake yi masa yana jin armashi ammafa babu wani shau'ki na kawowa.

Gajiya na yi kawai na matsa gefe daya domin kuwa kafad'una sun k'age dalilin sunkuyo jikina ma gabad'aya ya yi tubis bacci ne yake mamayata. Ganin haka ya sanya ya janyo ni a ki'dime ya fara sarrafa ni akwancen dai ya biya bukatarsa amma ta siga daban daban. Ni kam duk wanda ya bashi shawarar yin amfani da maganin k'arfin maza ya cutar dashi domin kuwa abin nasa yana nema ya yi yawa. Da sassafe ya shirya yana ta zoyalata zai tafi amma zai dinga zuwa ta mafarki. Na.dinga zumbura baki ina fad'in duk wanda ya baka shawarar yin amfani da maganin karfin maza ya d'ora ka a hanya mara b'ullewa ai ba a ce kada a yi jima'i ba amma daidai misali yanzu baba don Allah wane hali zaka shiga a can babu mace a kusa.

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma"

#700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*59*

"To sai a lokacin ya ke gaya mini shi babu wani maganin karfin maza da yasha hana karya dai ya yi amfani da maganin sanyi watanni uku da suka wuce lokacin da Falalu mai yi masa abinci ya je garinsu mahafiyarshi ta bashi ya kawo masa a matsayin tsaraba. Falalun ne ma da kanshi ya dafa masa maganin da yake sassa'ke ne da saiwowi ya had'a da citta kaninfari tafarnuwa ya dafa shi sosai ya zuba masa a babbar gora ya yi amfani dashi.....08089965176 Wallahi maganin sanyi ne sadidan har basir ma yana lalata tasirinsa a jikin dan adam. Kaikayin gaba zafin fitsari fitar iska rashin ni'ima zubar fitsari karancin sha'awa ciwon mara ciwon kafafu rashin haihuwa. Ciwon ga'bo'bi rashin gamsuwa maganin kuma maza da mata ne duk wani dattin da yake mara za a fitsarar dashi, ga masu buk'ata a yi mana magana kai tsaye ta lambarmu da muka d'ora za a yi wa Allah godiya kuma za a yi mana godiya."

Na yi mamaki sosai da na ji ya fadi haka. Dama ai duk lalacewar namiji wajan saurin kawowa ko rashin dogon zango

"ko kuma daukewar sha'awar da kankancewar gaba gabad'aya sai dai idan bai yi katari da sahihin magani ba. Haka zalika ma duk lalacewar mace wurin rashin ni'ima bushewa da fitar iska, d'aukewar sha'awa da matsalar rashin gamsuwa daga maigidanta sai dai idan ba a yi katari da ingantaccen magani ba. Haka zalika ma 'yan mata da zawarawan da suke da niyyar shiga d'akin mazajensu yana da kyau su ma su magance sanyin da yake tattare dasu domin gujewa matsala...08089965176 a tuntub'e mu kai tsaye muna tura kayanmu kowane gari."

Bayan kwanaki uku da tafiyarsa yanayin jikina ya fara canzawa lamarin ba sabon abu ba ne a wajena amma ban

tabbatar ba dai tukkuna har sai da lokacin yin la'adata ya yi ya wuce ban yi ba yayin da ciwo-ciwon da nake ji yake 'kara tsananta. Kakarin amai da safe taruwar yawu kasala saurin bacci da k'yankyami. Ciki ne da ni ba shakka lamarin bai yi mini wani armashi ba domin kuwa ban shirya d'aukarsa ba kuma ba na tsammanin zan gaya masa har sai na yanke shawarar da nake ganin itace mafita ga rayuwata.

Ko anti Yagana ba zan gayawa ba balle ta dakusar da ni domin kuwa yana da kyau komai mutum zai yi ya kiyaye faruwar abinda zai sanya shi shiga rud'ani a gaba.

A takarda na rubutawa Yusura abin gwaji ta fita bakin titi akwai chamis ta je ta sayo mini da sassafe na yi sakamako mai kyau ya fito positive. Shiru na yi da bakina kuma na dinga kokarin ganin na karfafi jikina don kada Baba Tabawa ta fahimci halin da nake ciki. Ba Allah zan yi wa butulci ba amma ya fi ni sanin dalilina na yin hakan zan nemi maganin da cikin zai fita tun kafin ya kai matakin da za a busa masa rai a yanzu dai bai wuce kwanaki a arba'in ba na tabbatar da samuwarsa ne had'uwarmu ta farko dashi zuwana Abuja tunda lokacin da na je ban fi sati daya da yin wankan tsarki ba kuma ni ba ban yi amfani da wata kariya domin gujewa faruwar hakan ba. Mun had'u sosai tun kafin ma na tafi maiduguri mun yi kwanciyar aure amma rabon bai rantse ba sai yanzu.

Da kaina na fita da daddare bayan Isha'i cikin hijab har kasa da nikabi har da safar kafa domin yin b'adda kama na nemi maganina na dawo gida.

Zuciyata tana dokawa a daran ina ta shawarwari nasha ko kada nasha domin sai nake ganin kamar Allah zai tuhume ni kuma ba zai kar'bi uzurina ba tunda tun farko ai ba a san da menene silar dake haifar da ciwon ba iyaye da kakanni haka suka yi auransu ba tare da sanin matsayin jini ba. Domin kuwa da yawa As da As suna yin aure ba su san alakar jininsu ba kuma su yi haihuwa fiye da goma ba tare da samun wani mai lalura ba. Da yawa kuma akwai masu S A da S A din da suke aurensu lami lafiya su gama haife haifensu ba su ci karo da komai ba kuma yaransu duk yawansu suna rayuwa. Kamar yadda anti Yagana tasha gaya mini turawa ne suka kawo wannan rikitarwar har aka kafa doka mai k'arfi akanta. Akwai ciwon ba wai babu ba to amma babu hujja mai karfi wadda za a guji auratayya domin raya sunnar Annabi Muhammadu S.A.W.

Cike da cajin kai da zullumi tare da fargaba na sha maganin amma daya nasha sabida yana da k'arfi dayan kuma na yi flushing dinsa.

"Wajan karfe uku na tashi da matsanancin ciwon mara da baya, tare da cijewar kafafu. na dinga murkususu ni kadai don sallar asubahi ma sai da safe na yi ta. Abin karin kummalo d'akin Yusura ta kawo mini domin ban Kai ga fita falon ba ina kwance a gado murfin gwiwata sai ciwo yake yi mini da kafafuna kasan marata amma babu d'igon jini a pant dina sai da uban ciwon dai."

Na dinga zurga zurgar zuwa bandaki ina dubawa babu wata alamar zubar wani abu. Jikina ya mutu murus na yi

kwance a gado ina istigifari ga Allah lallai duk yadda na kai ga so cikin ya fita idan fa Allah bai kaddara ba sai dai na ci wahalar kuma na haife shi babu yadda zan yi

Idan kuwa aka yi rashin sa'a na shiga hadari gagarimi sakamakon shan maganin da na yi cikin bai fita ba kuma ba ni da tabbacin cewa yana cikin 'koshin lafiya sakamakon yun'kurin zubar dashi da aka yi da ganganci.

Hawaye ya shiga silalowa daga idona tausayin kaina ya kama ni. Na ha'kura kawai na barwa Allah lamarinsa muddin cikin nan bai fita ba kafin yamma to ba zan yi yun'kurin sake zubar dashi ba. Duk abinda Allah Ya yi daidai ne.

Da k'yar na iya kur'bar shayi na ci dankali da 'kwai kad'an na sake kwanciya da wayata a hannuna zuciyata na tashi yayin da nake dan jin sasaauci daga kasan marata na rintse idona a hankali ina tasbihi ga Allah tare da sake jaddada istgifari domin neman afuwata.

Bayan azahar sai ga Sahura da ma mun yi waya da ita ta ce mini za ta zo a cikin satin da muka shiga. Dole ta sanya ni k'arfafa jikina domin kada ta fahimci wani abu amma duk ko'karin da na yi gurin kwarara gwiwata sai da ta gane ba na jin dadi ta fara zolayata wai ko nayi tsaraba daga abuja ne domin wallahi alamun mai yaron ciki ya bayyana a tattare da ni. Bagarar da maganarta na dinga yi na ki ba bata muhimmanci har ta yi ta gama ta fara gaya mini an zo tambayar auran Yusura kuma za a kawo kudin auran ranar juma'a wannan din nan ne dai dan gidan Yayar babanta wanda na tambayeta ta ce mini shi take so kwanakin baya sosai na yi farinciki da jin haka domin duk wani bincike sun yi tana kuma jadadda mini cewa yaron mane mi ne mai zuciyar neman na kansa kuma yana can yana gini a sabuwar unguwar nan ta rimin auzinawa. Yadda ta dinga zolayata ni ma haka na dinga zolayata ina dariya ta tsufa don ana yi wa Yusura aure shekara daya za ta haihu dole ta dau'ki jika. Fad'i take ai tare muka tsufa domin kuwa 'yar ki ce ba tawa ba.

Sai da ta yi sallar magriba tukkuna ta yi shirin tafiya na sanya sabon direban da aka ajiye mini ya dauketa a mota ya kai ta har gida.

To mukan d'an yi waya da maigidan sa'i da lokaci amma mafi akasari shi yake kirana idan ya samu sukuni ba sosai ya

fiye amsa waya ba sai mai mutukar muhimmancin gaske Amma fa shi yana kirana a duk lokacin da yake da isheshhen lokaci sai mu fi karfin awa daya muna hira ta waya sosai. Amma fa ko da wasa ban ta'ba kuskuran gaya masa wani abu ba tunda cikin bai fita ba na bar shi kawai duk lokacin da ya zo garin sai ya gani da idonsa.

Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta shi ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Bayan wata biyu da dawowo ta ina lissafin watannin cikin dake jikina wata uku da kwanaki kenan wannan karon

laulayi nake yi sosai domin kuwa ba komai nake iya ci ba na fi kauri dai

Please Login or Register in order to submit comment