You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dadinta akan hakan har dai ta gaza yin shiru tana gaya mata ita me yasa idan ta je mata take wata da watanni ina lefin ma mu yi sati daya sai mu tafi.

Jin abinda ta ce ya sanya mini fargaba don gaskiya bana so ko kwana daya mu kara a garin bayan wanda Hajjan ta

yanke.

Yanayin yadda inna Uwani ta nuna b'acin ranta ya sanya hajjan ta ce idan an yi addu'ar gobe jibi sai mu tafi lokacin dai duk wanda ya kamata a gaisa dashi an gaisa.

Dukda hakan dai inna uwani ba ta ji dad'i ba ta so a ce mun zauna mun yi sati guda kamar yadda ta buk'ata.

Jin shawarar da suka yanke ya sanya na fara tunanin nemawa kaina mafita dole gobe ma mu shiga cikin mutane kuma ba zai yiwu na sake komawa da kayan jikina ba ba don komai ba sai don na siyawa kaina mutunci.

Na gayawa hajiya Saratu abinda yake da akwai da buk'atar son ta yi mini jagora mu fita a daran tunda da sauran lokaci dare bai yi ba.

"Hajja ta kama fad'a sosai irin wanda bata taba yi mini ba gabad'aya taki kar'bar uzurina tana fad'in ai nasan ba yadda za a yi mu yi tafiya irin wannan mu je mu dawo a ranar na ce mata mantawa na yi sai da muka fito daga gidan tukkuna Allah ya tunasar da ni. Ina jin inna Uwani da tunda muke maganar ba ta ce komai sai da ta ji hajjan tana yi mini fada tukkuna ta sanyo bakinta wai ko dai ba na son zuwa aka tursasani. Takaici da b'acin rai bai barni na sake wata magana ba, na yi shiru kawai da bakina Ina mamakin yadda yanzu gabad'aya Hajja ta daina fahimtata ta kuma daina tausaya mini."

Haka dai muka fita ni da Hajiya Saratu ran mu duka a b'ace domin ita kad'ai ce ta dubi uzurina ta kuma fahimce ni ita Hauwa ma bata iya cewa komai ba har aka yi maganar aka gama kuma tana kwance a wajan amma uffan ba ta ce ba.

Direban da muka zo dashi ne ya fita da mu. Garin ba bak'on Hajiya Saratu ba ne ta san wurare da yawa don haka ma ba mu yi nisa da hawa titi ba muka ci karo da wani shop a d'aya hannun na cewa magaji direba ya shiga damu ciki.

Dogwayen riguna na sayo mana ni da Yusura na had'o da hijabai biyu da takalmi flat ko rabin awa ba mu yi ba muka koma gidan Hajiya Saratu tana kara ta tausata don gaskiya yanayinta gabad'aya ya nuna takaicin abinda aka yi mini tana gaya mini ita kanta ta rasa abinda yake damun Hajja a tsukin nan don ta fahimci kamar tana shakkar Inna Uwani dalilin ma da ya sanya ta fara dora zarginta akanta

"Na nuna mata babu komai kawai amma can kasan zuciyata abin yayi mini ciwo kawai da gaske, zan yi kokarin ganin na taushi zuciyata har mu tafi wani abu bai faru ta b'angarena ba."

Mussaman aka kunna genareto saboda mu. Gidansu Hauwa sai na ce da kadan ya dara namu gidan kwaryar sama ce take dukan ta kasa. Gidan kuma na had'aka ne mutum uku ne amma kowa da nasa bangaran wanda ya rasu ne kawai gidansa a waje. Mahaifinsu ya rasu kuma shine babbansu sai dai gabad'ayansu 'yan boko ne babu wani dan kasuwa a ciki suna ci da biro da takarda rufin asiri na abinci ne kawai kuma a cikin sa'aninta dai Ina ganin ita kad'ai ce take auran mawadaci sauran duk sai a hankali suna kula da kansu ne dalilin aikin gwamnati da suke yi sai dai yadda na lura suna da hadin kai da k'aunar junansu ba kamar na mu gidan ba.

"Wajan goma da rabi har mun kwanta ni da Hajiya Saratu da Yusura muna d'aki daya ita Hajja da 'yar uwarta suna tare Hauwa kuwa ba na ce ga inda take ba tunda ko lokacin da muka dawo ban ganta a falon ba. Muna d'an ta'ba hira kad'an kad'an Hauwa ta shigo da wayarta a hannunta tana fad'in."" Har kun kwanta ne?"""

"A tsanake na dubeta na ce."" E wallahi."""

"Sai ta miko mini waya tana cewa."" Maigidanki ne yake so ya yi magana."""

"Na yi sakare Ina kallonta yana so ya yi magana da ni bashi da lambata ne?"" Abinda zuciyata take tambayata kenan. Ta sake maimaita maganarta tana cewa'' Wata'kila ya kira layinki bata shiga ba kin san matsalar network, ni dai yanzu ya kira ni ya ce na hada shi dake."""

Ban ce komai ba na amshi wayar sai ta juya ta fita ni da Hajiya Saratu muka bi ta da kallo. Ita dai girgiza kanta ta yi a hankali ta koma ta kwanta ni kuwa na tashi zaune da wayar a hannuna ina tsammanin kiran nasa.

"Minti biyar da fitarta ya kira. Na daga a nutse na ji yana cewa."" Kin kai mata wayar?"" ""Eh ta kawo mini barka da dare?"""

"Na fad'a tare da ko'karin danne damuwata."""

"Ya d'an diririce ban san dalili ba can kuma na ji ya amsa yana cewa."" Dazu na kira Hauwa a waya ta ce mini kun fita ke da Hajiya Saratu ina kuka je?"""

"Babu mamaki a tare da ni saboda nasan zai iya yin abinda yafi haka na furta."" Ta yi mini rakiya ne na sayo abu a shop saboda ban yi guzurin kaya ba don ban yi zaton zamu kwana ba."""

"Ajiyar zuciyarsa na ji kafin ya ce."" Kada ki kara shiga wani shago da zummar sayan kaya Amina hakan yana nufin abubuwa da yawa, kin san dai ba zai yiwu ace ku je bauchi ko dawo a ranar daya ba, me yasa ba ki bawa maganata muhimmanci ba a lokacin dana kira ki na gaya miki ki shirya ki bi su."""

"Na hasala da jin yadda yake ko'karin d'ora mini lefi shekkenan ni ba zan yi kuskure ba, kuma ai da ya gaya mini bai ce mini na hada kayana kwana za mu yi ba."""

"Na ce."" Shine me? ai lefin ba na kowa ba ne naka ne ko ka gaya mini na hada kaya zamu kwana? da ka kira ni ka"

"sanar da ni na bijire maka ne, na ce to shikkenan ban yi maka jayayya ba saboda kuskure karami sai kuma a gaza fahimtata."""

"""Ban kira ki don ki gaya mini magana ba Amina, na ce kada ki sake shiga shago ki ce za ki sayi abu ina da dalilina."" Shiru na yi ban ce masa komai ba sakamakon yadda na ga Hajiya Saratu ta tashi zaune tana kallona da yanayi na damuwa."

"Sai kawai na datse kiran ban tsaya na saurari sauran maganarsa ba, wane irin dalili ne dashi wanda ya wuce na tozarci shikkenan don ina a matsayin na matarsa ba zan shiga shago na sayi abu ba ni din wacece. Itama Hauwa ta so faruwar hakan hakan ne amma menene na gaya masa ga inda muka tafi bai kira ni a waya don ya nuna ya ji dadin karar da na yi musu ba ya kira ni yana tuhumata akan wane dalili."

Ban iya daure kukan da yake ta yun'kuro mini ba na fara share hawayen da yake gudana a kumatuna Yusura ta yi lamo akan katifa tana kallona kamar ta taya ni kuka.

Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Hajiya Saratu ta dafa kafadata tana rarrashina a yanzu ita kadai ce take nuna damuwarta a kaina Hajja kam sai a

hankali 'yar uwarta ta samu galaba akanta.

"Hauwa ta shigo domin ta kar'bi wayarta ta same ni Ina kuka muna tattauna abinda yake faruwa da Hajiya Saratu sai ta yi kasa'ke tana kallonmu a lokacin Hajiya Saratu ta rufe ta da fad'a tana cewa."" Ki ji tsoron Allah Hauwa yadda ki ke ko'karin gyara auranki to na hore ki ki gyara na 'yar uwarki wadda ki ka zo ki ka sameta da mijinta, bayan abinda ku ke yi na karkashin kasa har sai kin yi mata bita da kulli kin san fa duk abinda ya faru me zai sanya don ya kira ki a waya sai ki gaya masa shikkenan mutum baya kuskure.."

"Babu wata damuwa a tare da ita ta ce."" Sai na yi karya kenan ko anti Saratu na ce masa gata nan a kusa da ni ko me? Ya tambayeni ina take na ce masa kun fita tare zata sayo kaya ko ba haka na ji kuna maganar ba. A lokacin da na yi masa karya ya ce na bashi ita kuma na yi yaya kenan, kuma na ji kina cewa muna yin abu ta k'arkashin kasa, ita din da kike shedarta kina da tabbacin ba ta yi ne? ai alhaki koikoyone wata'kila abinda ta yi ne ya waiwaiyo mata, ni wannan ai sai dai na kalleta kawai 'kiri-'kiri tana nuna mini 'kyama ta kuma fito da hassada da kishinta muraran a kaina ciki dai da izinin Allah sai na haifehe ko ana so ko ba a so gwara ma mutum ya ha'kura ya barwa Allah ikonsa"

Maganganun Hauwa sun yi mini nuni da cewa tabbas ta ji ciwon abinda na yi wanda har hakan ya sanya suka hade

"mini kai ita da mijinta. Amma kuma sun yi tsauri ga hajiya Saratu wata'kila ko ta manta da cewa ita din yayar mijinta ce fa ba kanwarsa ba, a tunanina ko kanwarsa girma da shekarunta bai kai ace ta tsaya a kanta da fitsara."

Ni idan ta yi mini kishiyarta ce ba abin damuwa ba ne tunda da kishi a tsakaninmu amma ni da ban had'a jini dasu ba ba zan ta'ba yi wa mai shekaru irin na Hajiya Saratu rashin kunya ba.

Abinda ya haddasa musu rikici kenan a tsakaninsu sai ya zamana ni na shiga tsakiya kuma a ta dalilina komai ya faru

"Hajiya Saratu fadi take yi ""Ba za ta je ta zauna miki ba din, ko ita ce ta yi miki cikin, ai ni Amina ta yi mini daidai duk abinda za ku ce akanta kun dade baku fad'a shegiya mara kunya ki dubi tsabar idona ki dinga nema ki zage ni saboda kin samu kanki ko, idan kin manta bari na tuna miki ni Yaya nake ga Tajo ba k'anwa ba balle ki ce za ki gaya mini magana son ranki Ubanki zan ci domin ba na ciki da iskancinki shashasha mara wayo kawai, ai iliminki bai amfana miki komai ba sai rashin dubara. "

*GARKUWAR MATA.*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar"

Opey bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*55*

Sai zamanta ya rage mini kad'aici mussaman idan Yusura ta tafi islamiyyar dana sanyata anan bakin titi domin ta cigaba da dora haddarta kasancewar dama ta yi saukar al'kur'ani wattanin shida da suka wuce wanda ya yi daidai da

lokacin da ta zana jarrabawar fita daga secondary da kaina na yi tunanin sanyata a makarantar saboda zaman a haka

bashi da amfani zata sake d'aukar darrusa masu muhimmanci kafin lokacin auranta tunda makarantar ba wai al'kur'ani kawai suke koyarwa ba har da sauran littafain na addini za ta kara sanin tsarki da hukunce-hukuncensu.

Ranar da Sahura ta zo yini muka yi muna magana daya har dai na gaji na yi mata shiru domin kuwa ba zan ta'ba yin

abinda take so ba don ban ga abinda na yi ba ai na d'auka sai mutum ya yi lefi tukkuna zai ta bibiyar wanda ya yi wa domin ya yafe masa.

"Ita kanta tasan maganata akan daidai take ba zai yiwu ace sun mori juna sun jiyar da kansu dadi ciki ya samu ace ni kuma dake gefe na je na yi musu wahala ba, ai ba yarinya ba ce balle ace kuma ita din menene bata sani ba tunda malamar asibiti ce duk wanda zai zage ni ya dad'e bai yi ba abu ne mai mutukar wahala wata mace ta aminta da hakan."

"Ita Sahura wai kada mutane su yi mini wata fassara ko a juya maganar ace ina yi mata b'akinciki don ta samu cikin haihuwa wanda ni kuma wallahi babu wannan a cikin raina komawa ne kawai ba zan yi ba, ni ma a lokacin da na samu nawa haka nayi ta fama dalilin ma da ya sanya kenan nake d'agawa Hadiza kafa saboda wahalar da ta yi mini."

Wai lallai sai na kira shi na bashi ha'kuri na gaya mata ha'kuri kuma na nawa lamarin da ba yau akayi shi ba an kusa

wata biyu to me zai sanya na damu kaina. Ina nan dai da kudirina wata uku na cika idan bai zo ba to kuwa zan san inda dare ya yi mini ai ko addini wannan abin da yayi ba daidai ba ne kuma daf yake da ya lalata auransa.

Duk hujjar da ta kawo mini zan soke ta dole sai ta ha'kura ta kyaleni ta tafi da b'acin rai dalilin da na ki na yi abinda take so.

"Babanmu da Baba Sule suka zo ranar wata jumaa bayan an sakko daga massalaci na ji dadin zuwansu sosai na shirya musu abinci mai kyau suka ci suka koshi suna ta yaba gidan da fatan alheri na dinga nazarin Baba Sule gabad'aya duk ya susuce tufafin ma dake jikinsa kamar ba wankakke ba takalmi irin soso shine a kafarsa. Babanmu ne kawai cikin sutturar arziki tsaf dashi, sai na ji kunyar hakan a cikin zuciyata ko babu komai Baba Sule uba ne duk lalacewsa kuwa, duk ranar da babu ran Babanmu dole shi din zamu k'alla a matsayin Ubanmu kuma idan da kara duk wata taguwa da zan dinkawa Babanmu shima ya kai ace na had'a dashi ganin da na yi masa babu kintsi ya sanya jikina yin sanyi domin yanayinsa ya nuna yana buk'atar agaji ilai kuwa ashe damuwa ce mai yawa a tattare dashi dalili ubangidan nasa Alhaji Muntari ya karye jinya ta cinye masa kudi ga tarin bashin mutane dake kansa komai ya karye masa wasu sun ha'kura wasu kuma sun ce sai an biya su, wannan dalilin ya sanya gidan da yake ciki aka sanya shi a kasuwa domin biyan bashin da yake kansa. Yadda Baba Sule yake mini bayani lamarin ya bani tsoro mutuka da gaske yanzu uwargidansa anti Maimuna ita kadai ce ke jinyarsa anti Jamila ta gudu garinsu Bichi bayan ta turasashi ya saketa wai ba zata iya zama ta lalata kuruciyarta a banza ba. Yana gaya mini baban yaronsa namiji wato Turmuzi yana nan yawo cikin tashar Kano line yana bin 'yan kamasho da samarwa da matafiya mota a sallameshi ya lalace da shaye-shaye tunda wasu lukutan a tashar yake kwana sai yayi sati bai je gida ba."

"Kuka sosai na dinga yi ina kiran sunan Allah amma anti Jamila ba ta yi wa kanta adalci ba, ni a tsarina duk wahala ba zan iya watsar da yarana akan jin dadin duniya ba, babu ma yadda za a yi na tafi na bar yarana a wurin da nasan ba zasu samu kulawa ba hankalina ma ba zai ta'ba kwanciya ba. Anti Maimuna ta ba ni tausayi sosai ita kuma tata jarabawar kenan rayuwa kenan. Ba ni da halin da zan iya biyawa Alhaji Muntari bashi har na kusan miliyan talatin gabad'aya ma abinda nake juyawa bai kai hamsin ba ribar da take fita yau da gobe da ita muke buk'ata ni da Hamusu da kuma biyan yaran shago hakkinsu. Alhaji Tajo shi yake da iko koda miliyan dari ne don ya fitar ya bayar ba na tsammanin dukiyarsa zata girgiza amma da nauyi sosai a ce na tunkare shi da wannan maganar har cikin raina nake jin wani iri dangane da ibtila'in rayuwar da ya faru da Alhaji Muntari domin ko banza ya taimaka mini ni ma a can baya a wannan ga'bar ya kamata ace na tagaza wani abu kafin akai ga kar'bar kudin gidan da yake ciki wannan duniyar ta zama abar tsoro."

Haka na kwana na yini da tunanin hanyar da zan bi wurin ganin na nemi taimako daga wajan wannan wannan d'an tahalikin ba tare da ya fassara ni ba.

Na kira anti Yagana na gaya mata domin ta ba ni shawara itama dai abinda Sahura ta ce shi ta fad'a na sauke abinda nake ji kawai na neme shi domin yin hakan babban taimako ne da zai sanya ni dashi mu tsinta a ranar lahira. Na yi na'am da shawararsu domin a raina na ji zan iya jure cin kashi da bakaken maganganunsa muddin zai taimaka ai me nema baya fushi ni ko bashin ne ma ya biya masa su dai zauna a gidan ni kuma zan yi kokarin ganin na d'auki nauyin kaishi babban asibiti domin a duba lafiyarsa sosai.

Na samu lokaci ranar lahadi da la'asar domin a irin wannan lokacin ne yake free sosai na kira shi a waya daf da zata katse ya daga yana sallama.

Na amsa a nutse kafin na gaishe ya amsa can kasa kamar wanda yake cikin mayen bacci.

"A sanyaye na ce."" Dama na kira ka ne kawai na gaisheka na ji ya kuke ina Yusi."""

"Ya ce."" Ina nan lafiya muna nan Abuja tare dashi gidan babban abokina Alhaji Amadu na taba baki labarinsa ko?"" Na ce."" Eh kun dai ta'ba yin waya sau daya a gabana ina yawan jin sunansa a bakinka."""

"A dan sanyaye ya furta."" Yana nan rai a hannun Allah Amina yana jin jiki muna kan shirye shiryen tafiya asibitin jiddah nan da kwana uku"""

"Jikina a mace na ce.""inna lillahi me yake damunsa haka?"""

"""Kin san yana da ciwon zuciya dama to wannan karon da ciwon ya motsa masa abin ba kyau ni har na fara fitar da raina a kansa Amina."""

"A sanyaye na ce."" In sha Allahu zai tashi zai samu lafiya."""

"Ya ce."" To Allah Ya sa, ina fatan dai lafiya kuke na yi mamakin kiran da ki ka yi mini a wannan lokacin da ban yi tsammani ba, ni da kika kullace ni kina gaba da mijinki ko Amina baki damuwa da halin da nake ciki ba, ai ina kallon yadda ake soyayya a wurin Hajiya Maryam mai d'akin abokina Alhaji Amadu amma ni da nake da mata biyu kun yi watsi da ni ko, ita waccan din idan an yi mata uzuri ke fa? son ranki kike bi, ba ki damu da abinda zai same mu ni da Yusuf ko ba haka ba ne?"""

"Jiki babu kuzari na ce."" Ban kyauta ba ka yi hakuri amma me yasa ka gaza fahimtata ya kamata ku yi mini adalci a wannan lamari sai ka tsiri gaba da ni, ban kullaceka ba kaine ma kake jin haushina dalilin da ya sanya ma kenan na ga rashin dacewar haka na kira ka yanzu domin mu sasanta gabar ta isheni haka."

"""To tunda kin nemi sulhu zuwa za ki yi inda nake ai ki lallaba ni domin ni ma ba ni da wata lafiya rashin lafiyar"

"abokina ta dame ni a kwanakin nan Ina buk'atar mai kula da ni ta ba ni magani ta kuma kwantar mini da hankali da kalamai masu dad'i zuciyata ta daina yi mini tunanin kamar ban yi sa'ar iyali ba."""

"Cike da mamaki na furta."" Yallabai duk me ya kawo wannan maganganun don Allah."""

"Ya nisa kafin ya sake cewa."" Kulawar da abokina yake samun wurin iyalinsa shine ya sanya nake jina kamar maraya gashi dai babu abinda Allah ya rage ni na jin dadin duniya amma matata ta na yi mini wulakanci."""

"Dariya maganarsa ta ba ni wai wulakanci wato shi baya duba abinda yake yi mini a matsayin wulakanci saboda namiji ne duk abinda ya yi daidai ne."""

"Na yi dariya 'yar kad'an kafin na ce."" To shi ba ka ganin bashi da lafiya ai dole a ninka bashi kulawa ko ka manta lokacin da ka yi mura a gidana yadda na dinga lalla'baka ina rarrashinka kamar jariri."""

"Ya ce."" Ni dai na gaya miki zan sanya a kawo miki ticket da za ki same ni anan abuja gobe kafin mu wuce saudiya ki ba ni magani kada na tafi da lalura."

A dukunkune yake maganar amma na gama fahimtar inda ya dosa wannan ya nuna mini cewa a mutukar bukace yake dauriya ce kawai da son dole sai an nuna iko ba zai neme ni ba muddin ba ni na neme shi ba yanzu kuwa dana tsaga billena na kira shi kai tsaye yake neman abu a wurina.

Ni ma saboda tawa biyan buk'atar yasa babu ja'inja na amshi gayyatarsa nasan ta wannan hanyar zan iya samun abinda nake so kai tsaye tunda Allah Ya riga ya ga zuciyata da munufaar da zanyi hakan.

Daya daga cikin masu yi masa jigila

ya turo da mota ya d'auke ni sunan shi Ade wani bayerabe mai gaggausan jiki da rashin fara'a

bayan saukata a garin abuja kai tsaye gidanshi da yake maitama ya nufa da ni kamar yadda ya bada umarni sai dai da yake ya san matsayina duk cud'ewar fuskarsa bai hana shi risina mini ba.

Gidan kwatankwacin na Legos me d'auke da bangarori da dama kuma cike da ma'aikata da masu tsaro da iyayen motacin da na tabbatar da cewa wasu ma sai a yi shekara ba a hau su ba.

Wurin ajiye motoci ya nufa domin gyara parking yayin da nake hangen maigidan da Yusi can daga nesa bakin wata bukka irin ta hutawa.

Yana kashe motar ya fito da sauri ya bude mini kofa har yana dan risinawa na fito a hankali Yusi ya taho a guje ya rukunkume ni yana dariya mamaki mai yawa ya lullubeni ganin yadda yaron ya yi wata iriyar ki'ba kamar wanda aka hura ya zama kato Na dinga binsa da kallo irin na mamaki da al'ajabi wannan wace irin ki'ba ce. Maigidan ya k'araso wurin yana sanye da jallabiya fara mai karamin hannu kansa da fara hula irin ta larabawa as'usul idonsa da farin gilashinsa. Na dube shi na 'yan dakika na fahimci zurmawarsa ya kara tsukewa dama abinka da mai karamin jiki ko dai da gaske yake shima din bashi da lafiya.

*GARKUWAR MATA*

*BINTA UMAR ABBALE*

"[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram. Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262. Binta Umar Opey"

bank. 'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton. A tura da sheda ta wannan

lambobin iya What'sapp kawai.*

*07084653262*

*08089965176*

*V-VIP AREWA PEN *

*56*

"Ade ya fito da k'aramar akwatina da na zubo kayana kala uku a ciki ya tsaya suna magana ni da Yusi muna gefa ya rike hannuna gam a cikin nasa yana cike da tsananin farinciki ni kam kallonsa kawai nake yi har na gaza ha'kuri na ce."" Kai me ka samu ka ke ci ka zama d'an lukuti kana duba mudubi kuwa?"""

"Dariya ya kama yi yana cewa."" Abinci kawai nake ci ai an yi hutu makaranta Mama amma ina hawa gym na tsinka jina na."""

"Na dube shi a lokacin da ya zo ya tsaya gabanmu Yana cewa."" Ke kuma daga zuwa sai tuhuma."""

"Yar dariya na yi a hankali na ce."" Abin ne ai da mamaki wallahi kibar ta yi yawa."" Ya wuce ciki yana cewa."" Ke ki ka gada masa ai ba kowa ba.''"

Yusi ya kamo hannuna muka bi bayansa yana ta yi mini labari yaran Alhaji Amadu wanda suka zama abokansa jinsa kawai nake yi amma ban

Please Login or Register in order to submit comment