You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ˙ūCHEF ZEEY

Love in the Kitchen

Azizat Hamza

Ga duk wata mace mai sana'a. Allah Ubangiji ya dafa miki...AMIN



HAKKIN MALLAKA

ŠAzizatHamza2025

"Wannan littafi hakkin mallakar AZIZAT HAMZA ne. Ba a yarda wani ko wata su Waura shi a YouTube, ko a"

"Waura shi a shafukan facebook ko website na novels, ko kuma a maida shi Film, ko a kwafi labarin ba tareda izinin marubuciyar ba. Yin hakan zai sa a Wau mataki na shari'a."

ŽChefZeey2025

Za ku iya bibiyata ta waWannan Manhajojin:

ArewaBooks: Azizat Hamza

Wattpad: Azizat Hamza

TikTok: Marubuciya Azizat

YouTube: Marubuciya Azizat Hamza

WhatsApp: 08137311900



Marubuciya Azizat Hamza



Azizat Hamza



Azizat Hamza

CHAPTER ONE

ZEEY

"Sunana ZIYADA SADIQ HARUNA a.k.a CHEF ZEEY. Ofcourse na je culinary school, dan haka, I am a"

certified Chef. Certificate Wina ma yana cikin folder a ™asan gadon Kaka.

"A hankali nake duba littafin da ke gabana, a lissafin dana gama yi kuWin buWe restaurant Wina saura Naira"

"Miliyan huWu da dubu Wari takwas da saba'in (#4,870,000) kacal."

"Kenan na tara Naira dubu Wari da talatin (#130,000) a cikin Miliyan biyar da nake nema. Classy"

"Restaurant da za a ri™a siyar da abincin gargajiya zalla a garin Zaria na ke son buWewa, at least daga"

yanzu zuwa ™arshen shekarar nan na ke fatan haWa kuWin. Wannan shine babban burina.

"Watanni shida da suka wuce account Wina na Instagram ya tafi viral, wannan ya sa na fara samun 'yan"

chanji daga tallace-tallace da nake yiwa ™ananun 'yan kasuwa irin masu siyar da spices da kayan kitchen

haka.

Duk wanda ya ga numbers Win social media accounts Wina zai Wauka na fara samun wasu ma™udan

"kuWaWe, irin na BLOW Winnan. Amma gaskiyar shine, ZIYADA SADIQ HARUNA a.k.a CHEF ZEEY bata blow ba. Followers Wina dai sun ™aru, amma kuWin fa sai a hankali, musamman saboda masu kawo tallace- tallacen sun mugun rena ni. Dan kawai sun ga abincin gargajiya kaWai na ke yi, kuma bani da fancy kitchen irin na manyan Food bloggers da suka yi fice sai suke ganin ko nawa suka bani kawai in karSa in yi godiya."

"Ba laifinsu bane, Instagram gidan aesthetic ne, gidan kwalliya, gidan gayu, gidan ™arya, so babu wanda"

"zai Wauki ma™udan kuWi ya bawa wata ™aramar Chef da ke girki da murhun itace ta yi mata tallen kayanta. Sun fi son masu fancy kitchen. Chef Zeey bata da fancy kitchen. Ni da nake zaune da 'yar tsohuwata muna fama da kanmu ina na ga ta fancy kitchen. Amma Alhamdulillahi, Wan abinda na ke samu yana rufa mana asiri, ba ga ni kaWai ba, har da mutanen gidanmu."

"""Adda Ziya, wai inji Mamana wai ki bata aron dubu Waya idan kina da shi"""

A fusace na Waga idanuna na kalli yarinyar da ta shigo min Waki hanci duk majina tana sanye da wani

babban zani babu ko riga a jikinta.

"""Yanzu dan iskanci Atika kike ko waye..."""

"""Assima'u..."" ta gyara min tana wani zazzare idanu. Hannuna na kai na kwaWa mata biron da nake"

rubutu da shi

"""Ban hanaku shigo mana Waki babu sallama ba. Ana koya muku tarbiyan da zai gyara muku rayuwa"

"amma sai shegen taurin kai"""

Yarinyar ta wani zuba mini idanu ko a jikinta.

"""Koma ki je ki yi sallama!"" Na daka mata tsawa. ""Jibeta fiska duk majina, za a tashi da safe iyayenku ko"

"fiska ba za su wanke muku ba"""

"""Salaama Aleekumm"" ta faWa da ™arfi sannan ta shigo Wakin"

"""Bakinki ne Salama Alekum Win ai. Wai waya aikoki nema? Eh?"""

"""Mamana"""

Na kalli yarinyar da kyau ko zan gane daga wani balbali ta fito. Yaran da ke gidanmu sun yi yawan da ba

"iya ganesu nake ba, musamman ma ™ananan."

"""Mamanki ita ce, Amaryar Baffa Zakari?"""

Sai da ta ja hancinta ina ganin green Win majina da ya ma™ale mata a ™ofar hancin ya koma sannan ta ce

"""eh"""

"""Zo zo zo ki wuce ni bana son ™azanta"" na jawo purse Wina na cire gudan dubu Waya na mi™a mata. Na"

"san idan dubu Wayan nan ta fita ta fita kenan. Kaf matan gidan wacce ta ke da Wan ™o™arin biyan bashi idan ta karSi aron kuWi a wajena Anty Hafsah ce, amma duk sauran idan zan fara lissafin Wari biyu yau, Wari biyar gobe, dubu Waya jibi da suke karSa aro ba sa biya, ina ga sai ya cika littafi."

A yanzu haka a FaceBook page Wina ina da followers dubu saba'in (70k followers) FaceBook shi nafi

"samun followers saboda a nan na fara food content Wina. Sai kuma Instagram da nake da followers dubu talatin da takwas (38k Followers). Kar ku sha mamaki idan na ce muku a cikin wata shida na tara followers dubu talatin Winnan. Na yi shekara biyu ina posting a Instagram, ina samun followers kaWan- kaWan da ™yar na haWa 8k followers. Then, Boom!, wani video dana posting ni da Kaka muna yin kwaWon rama da zogale sai ya tafi viral. Ban san mutane na son abincin gargajiya ba sai a wannan videon. Shikenan Instagram Wina daga 8k followers sai ga shi wai video guda Waya tak ya kawo min mutane dubu talatin, har yau ina mamakin abin nan."

Shi kuma YouTube na buWe shi last year ne lokacin dana lura duk manyan food bloggers dana ke bibiya

"sun koma can kuma kowa na faWin YouTube suna bada kuWi sosai. Kai! YouTube ya bani wahala, sai na"

Waura video ya yi wata ban samu 1k views ba. A haka dai na yita gurgurawa har na samu 2k subscribers a

shekarar amma kuma ban zama monetized ba saboda haka bana samun kuWi. A YouTube dai videon

"dana yi na Alalen gwangwani shi ya jawo na samu 6k subscribers a wata shida, ya zamana ina da 8k subscribers kenan kuma na shiga YouTube Partner program amma har yanzu saboda bana samun views ban samu adadin kuWin da za su fara biyana ba."

"TikTok kuma gidan rikici ne, har kirana suke da 'yar Talakawa a comment section, ko su kirani da 'yar"

"gargajiya. A can followers Wina yanzu haka sun kai 52k followers. Tare na buWe da YouTube amma shi gudu yake kamar me. Ya ma fi Instagram saurin samun followers. Amma taron yu-yu-yu ne a can, dan wani lokaci har rufe comment nake saboda jarrabarsu. A TikTok har hashtag Win #ChefWinTalakawa aka bani, da ka saka Chef Win Talakawa a TikTok videos Wina zaka fara gani. Ban damu ba, dan ni Win Talaka ce, ni Win marainiya ce dana taso a hannun Kakata..."

*

Ina cikin buga lissafi Kaka ta kwala min kira daga tsakar gida

"""Ziyadatu, ba za ki fito ki wuce makaranta ba?"""

"""Kaks, Ina zuwa"" na faWa ina rufe littafin dana ke lissafin kuWi a ciki. Can ™asan akwati na saka saboda"

"'yan gulma da Sarayin cikin gida. Idan kana zama a babban gida komai za ka yi sai kana taka-tsantsan. Idan aka san ina tara kuWin restaurant ai labarina sai ya shiga kowani balbali a gidan nan, sannan masu karSan aron kuWi duk za su bi baya su zo su karSe Wan abin dana tara. Dama tunda aka ga na fara samun alkhairi a social media shikenan kowa ya saka mini ido."

Black handbag Wina da ke rataye jikin ™usar da ke kusa da window na Wauko sannan na ciro handouts

"Wina a ™ar™ashin pillow na sa a jakar. Jiya ina cikin karatu na yi bacci. Allah na gani ba zan iya tuno komai cikin abinda na karanta ba, komai ya gudu. ˜arfe goma muke da test Win so na san dai ko a cikin Keke ne kafin na isa school zan Wan yi bitar wasu abubuwan. Tunda na samu carryover biyu a shekarar farko na yi al™awarin ba zan sake wasa da karatuna ba."

"Jarrabawar soyayyar dana faWa a lokacin ya sa na samu Carryover biyu a Level One, ban ma Wauka zan"

"cigaba da karatun ba saboda yadda na lalace a lokacin. Amma dana farfaWo daga ciwon so sai na yiwa kaina karatun ta nitsu, babu ni babu soyayya har sai na cimma burina. Babban burina a rayuwa a yanzu shine: 1- na gyara shashin Kaka. 2- na buWe restaurant. 3- na kammala Degree lafiya."

"Sai dai at this point komai ma is proving to be difficult. Karatuna na shirin ™wace mini, kuWin restaurant"

"ya ™i haWuwa, gyaran gida kuma... na gyara mana banWaki daga pit zuwa water system, at least na Wan yi wani abu ai..."

Lokacin dana fito daga Waki sai na tarar Kaka tana tankaWe garin Masara a tsakar gida.

"""Kaks, Tuwo za ki mana ne yau?"""

"""Garin da Ladidi ta aiko tun kwanaki ne na ce barin yi tuwo da shi kar ya lalace"""

"""Kaks, lallai a gaishe ki, kusan wata huWu fa kenan da Umma ta aiko miki garin nan"""

"""Lah! na manta inda na ajiye ne. Sai jiya da yamma na gani a cikin jan Fantekan da ke ™asan gado"""

Wani tsumma da ke saman igiyar shanya na jawo na Wisa ruwa daga butan Kaka da ke bakin ™ofar Waki

na fara goge ba™in flat shoe dana saka dan ya yi ™ura sosai.

"Ina gama gogewa na yar da tsumman dan sai wani mai™o-mai™on datti ya ke min a hannu, ko uban me"

ma aka gobe da shi sai Allah. Na wanke hannuna da sauran ruwan da ke butan na yiwa Kaka sallama.

"""Kaks na tafi"" na faWa ina Waga mata hannu."

"""A dawo lafiya, Allah ya bada nasara ya kuma kaWe fitina"""

"""Amin, Kaka"" na amsa ina ficewa daga sashenmu..."

***

JAYKAY

A hankali ya ke saukowa daga matakalar da zai sadaka da babban falo. Meeting ya ke da shi da wasu

investors ™arfe tara na safe.

Hajiyarsu ce a falon ita kaWai tana shan green tea.

"""An fito"" ta faWa lokacin da ya gaisheta"

"""Yes"""

"Zama ya yi a kujera yana saka agogo yace ""Ina Janan?"""

"""Ai ina ga bata tashi ba"" Hajiya ta faWa tana kurSan tea Winta."

"""Bata tashi ba?"" ya duba agogon hannunsa, ™arfe takwas ne na safe har da minti bakwai"

"""Kaima ka san halinta ai"" Hajiya ta faWa tana ajiye mug akan saucer."

"Mi™ewa yai zai tafi ta kira shi ""Jamal"""

Tsayawa yai cak ya kasa motsi yayinda ™irjinsa ya fara cunkushewa yana masa wani suka.

"""Afuwan! Jalal, maganar Plaza Winnan ne, na ce har yanzu ba a yi komai akai ba"""

"Sai da ya Wau kusan sakan talatin yana ™o™arin saita nitsuwarsa kafin ya juyo ya kalleta ya ce ""idan na"

"dawo za mu yi maganar, ban manta da Plazar ba"""

"Hajiya ta sake Waukan mug Win da ta ajiye ta ce ""to sai ka dawo Win"""

Wucewa ya yi ba tareda ya sake cewa komai ba. Yana fita ya shiga mota Direba ya ja mota suka bar cikin

gidan. Sai da suka yi nisa da gidan sannan ya saka hannunsa a ™irji yana furzar da iska. A duk lokacin da Hajiya ta yi suSutan baki ta kira shi da Jamal sai hakan ya tuno masa da wannan mummunan rana da komai na rayuwarsa ya chanja. Shekaru uku kenan amma kullum ya tuna da wannan mummunan rana sai zafin abun ya dawo masa sabo.

Duk sadda Hajiya ta kira shi da Jamal ji ya ke yi kamar gazawarsa ya sa ta ke auna shi da sunan

Wan'uwansa. Wata™ila hakan shi ya ke sanyaya mata zuciya.

Wata™ila idan ta kira shi da Jamal zai rikiWa ya koma Jamal Win na gaskiya.

He was never her favourite.

Jamal shine perfect son. Šan Albarka. Wanda kowa ya ke alfahari da shi a family.

Ba zai taSa mantawa da abinda ta faWa masa ba ranan da ya ce mata zai auri Cassy.

"""Jamal ba zai taSa kawo min suruka wacce bata Sallah ba"" abinda ta faWa kenan, and it breaks him."

Lokacin da aka saka bikin Jamal ta fi kowa farin ciki. As if a lokacin ne Wanta zai fara aure. She was all

"over the place tana ta shirye-shirye, yau Dubai, gobe India, jibi China, tana ta siyayyan biki."

Lokacin aurensa da Cassandra saboda ma kar a yi auren tana kusa barin London ta yi ta wuce Nigeria.

Jamal da Daddy ne suka zo kotun da aka Waura aurensu.

Bayan auren Hajiya bata sake saka baki a maganar auren ba sai lokacin da Cassy ta haihu da ta zo ganin

yaro. A lokacin ne ta maimaita masa abinda ta faWa ranan da ya zo mata da maganan Cassy.

"""Kai da baka zama ka san dai kwacokam tarbiyyansa yana hannun uwarsa ko"" ta ™are da faWin ""Allah ya"

"bashi hasken musulunci"" tsabar sanyin jiki bai iya amsa addu'ar ba. Jamal ne ya amsa yana yiwa yaron"

"wasa yana faWin ""Hajiya kar ki damu, Ni da hannuna zan ri™a tafiya da yaron nan Masallaci"" yai maganar"

yana dariya.

"Jamal kenan, Sarkin dariya. Har yanzu yana iya tuno sautin dariyar Jamal na ™arshe a duniya."

"""YallaSai mun iso"" Direbansa ya faWa ganin Ogan nasa bai fito daga motar ba minti biyu bayan ya yi"

parking a parking space na Kamfanin.

"""Thank you, Abdullahi"" Jalal ya faWa bayan ya farfaWo daga duniyar tunani da ya tafi."

Yana shiga Kamfanin mutane suka fara gaishe shi yana Waga musu hannu har ya shiga elevator ya wuce

7th Floor inda office Winsa ya ke.

Yana zuwa Sakatariyarsa ta gaishe shi ta ce masa ba™in da za su zo sun iso. KarSan file Win hannunta ya yi

ya shige cikin office Winsa.

˜aton Hoton da ya yi tozali da shi a office Winne ya sake tuno masa da rashin dacewarsa da wannan

office Win. Kowa ya sani ba shi ya dace ya mallaki wannan office Win ba. Mamallakin Office Win Jamal ne. Shi yasa ya kasa cire hoton tun shekaru biyu da ya amshi ragamar tafiyar da kamfanin. Ji ya ke kamar idan ya cire hoton Jamal zai gani. Sannan Hajiya ba za ta ji daWi ba. Shi ya sa ya kasa cirewa. Amma a kullum ya shigo office Win ya kalli hoton sai gabansa ya yi ras!

Zama ya yi a kujera ya gyara tie Winsa sannan ya buWe file Win da Sakatariyarsa ta bashi dan ya duba

takardun kafin ya wuce Wakin da zai gana da ba™i.

Haka ya gama duba takardun har ya kai wajen da aka rubuta sunansa JALAL KABEER MAIYA˜I.

A baya sunan Jamal ne a wajen ba nasa ba. A baya Jamal ne zai yi signing a wajen ba shi ba.

"""JayKay"" aka kira shi."

Ya Wago idanunsa ya kalli ™ofar. Mr Munir ne abokin Jamal kuma CFO na kamfanin.

"""Time"" ya faWa yana nuna masa agogon hannunsa."

"""Oh, yes"" yai saurin saka biro a wajen sunansa ya yi signing. Sannan ya mi™e hannunsa ri™e da file Win ya"

bi bayan Mr Munir suka fita.

Za ku iya bibiyata ta waWannan Manhajojin:

ArewaBooks: Azizat Hamza

Wattpad: Azizat Hamza

TikTok: Marubuciya Azizat

YouTube: Marubuciya Azizat Hamza

WhatsApp: 08137311900

CHAPTER TWO

ZEEY

Ina jin Lecturer Winmu yana cewa kowa ya dena rubutu na ja wata siririyar tsaki a zuciyata. Haba Jama'a!

Ta ya mutum zai iya amsa Questions uku masu 'ya'ya a minti shabiyar. Shima dai wannan Malamin ba so

ya ke mu ci course Winsa ba. Allah na gani Question Waya na amsa da ™yar. Kwata-kwata ba inda na

karanta mutumin nan ya fitar ba.

"""Zeey, me kika rubuta? Ni fa babu abinda na sani, Ban rubuta komai ba"" Bestie na Faty ta faWa gaba Waya"

"ta rikice. Course Win da muka gama rubuta test Winsa 3 credit unit ne, kuma mutumin ba shi da mutunci."

"""Nima an gaya miki na rubuta wani abun kirki ne. Ke dai kawai Allah ya taimakemu ya bamu Assignment"

"mu Wan samu wani abu a nan in ba haka ba CA Win Dr Farouq zero za mu samu"""

"""Ni kinga gaba Waya wannan bikin da aka yanka mini ya bi ya hana ni karatu. Sai da na cewa Baby ya bar"

"bikin nan sai na gama Makaranta"""

"""TabWi! Abeg! Gara da aka sa mana shi nan kusa, kinga next year idan za mu yi graduation kina nan da"

"cute Baby girl ko Baby boy"" Faty ta kai min duka na sa mata dariya."

"Fatima Jibril, ita ce Bestie na a gaba Waya duniya nan. Idan aka ce in kira sunan ™awa guda Waya da zan so"

"mu yi ™awance har tsufa, to Faty zan fara kira. Faty mutum ce, Faty na da mutunci overrrr. Ba a iya shaidar mutum 100% saboda Wan Adam ajizi ne, but gaskiya zan bawa Faty 99.9% cewa mutuniyar kirki ce."

Za ku Wauka mun jima tare da ita but a wajen registration muka haWu lokacin muna Level One. Right

"from day one muka clicking and tun daga lokacin Faty ta zame mun ™awar arzi™i. Ko lokacin da matsalar soyayya ta sakani a gaba Faty was there for me. Lokacin da abubuwa suka mana zafi ni da Kaka Faty ta bani taimakon da ba zan taSa iya biyanta ba. Lokacin dana fara Wan posting video a FaceBook sama-sama haka, Faty ce ta bani ™arfin gwiwa ta ce na cigaba watarana page Wina zai yi girma har na fara samun kuWi. Ita ta sa na fara posting a Instagram saboda ni lokacin ina ma na samu kuWin datar da zan shiga IG. Faty za ta mini sub Win data ta ce Zeey ki dinga Posting a Instagram Winnan watarana za ki blow. Faty ce ta bani shawarar na je culinary school a Kaduna na koyi girki Professionally."

"Kada kuce na cika ku da labarin Faty, gaskiyar shine, without Faty wata™ila da babu Chef Zeey."

˜arfe uku muka baro cikin school. Kasuwa muka wuce saboda Faty ta ce za ta duba wasu kaya. Bikinta

saura sati shida yanzu. Mun jima a kasuwa. Bamu muka dawo ba sai ana kiran Magariba. Na riga na kira Kaka na faWa mata ina gidan su Faty dan haka bani da matsala.

Ba wani kayan arzi™i muka siya ba duk yawace-yawacen da muka sha a cikin kasuwa. Sai da muka ci

abincin dare kafin ta rakani har titi na hau Keke na taho gida.

Ina zuwa ™ofar gidanmu na samu su Baffa Lawalli da Baffa Zakari da wasu ma™otanmu akan tabarma

suna cin tuwo. Na haWe fiska zan shige ba tareda na gaishe su ba Baffa Lawalli ya kira sunana. Na waske na Wan risina na gaishe su.

"""Daga ina haka?"""

"""Gidan su ™awata Faty, na rakata kasuwa ne siyayyan biki"""

"""To a kula, banda yawon dare"""

"Har na shiga zaure ban dena jin haushin maganarsa ba, wai ""banda yawon dare"". ˜arfe takwas ne fa"

yanzun. Kumama in ba neman magana ba ai ya san su waye masu yawon dare a gidan. 'Ya'yansa ne ba na kowa ba.

A ™ofar Waki na tarar da Kaka tana zaune akan tabarma ta kunna radio tana ji. Wasu jikokinta kusan su

"biyar suna gefe ta zuba musu tuwo a tray suna ci. Kullum abin kenan. Babu mai bawa Kaka naira biyar a gidan nan, amma da zaran ta yi girku sai su sako zugan 'ya'yansu su zo su cinye mata abinci."

"""Kin dawo?"""

"""Kaks, Na dawo"" na faWa ina rataye gyalena a kan igiyar shanya. Wata ™aramar kujerar katako na jawo na"

"zauna na ce ""Kaks, kin ci abinci kuwa?"""

"""Dama na ce in jiraki ko za ki ci tuwon idan kin dawo mu ci tare"""

"""Kai Kaka! Kin san dai dole zan ci abinci a gidansu Faty"""

"""Garin na da kyau kuwa, Tuwon yayi dan™o sosai, barin zubo mana kema ki taSa"""

"""Ki zubo to, amma kaWan zan ci"""

"""Kaka Altine a ™ara mana miya"" wata daga cikin yaran da suke cin abinci ta faWa tana turo tray Win gaban"

Kaka da ta tashi za ta zubo mana tuwo.

"""Wallahi sai kun cinye gayan tuwon nan tas! Babu miyan da za a zuba muku. Oya Wauki tuwon nan ki"

"ajiye muku ku cinye"" na daka mata tsawa"

"""Adda Ziiyaa, dan Allahhhh"""

"""Barin saka musu kaWan"""

"""Kaks ba za a ™ara musu komai ba. Nan gaba za su koyi yadda ake managing miya, ko kuma suje balbalin"

"iyayensu a basu miyar a can"""

Wayata ce ta fara ringing a jaka na ciro sai na ga sunan Alhaji Nafi'u. Na ja tsaki ina mayar da wayar

jakata.

Lokacin da Kaka ta zubo mana tuwo na wanke hannuna na fara ci. As usual tuwon ya yi daWi. Girkin

Altine mai tuwo ne fa. Kakata ta kaina.

"Altine mai Tuwo ake kiranta, sama da shekara hamsin tana sana'ar sai da Tuwo. Tun kan ta yi aure ta ke"

"taya mahaifiyarta sana'ar sai da Tuwo a Kano. Da ta yi aure a nan Zaria kuma, tun tana Amarya da ta fara sana'ar bata dena ba har sai da iftila'in jinya da tsufa ya hanata. Da sana'ar Tuwo ta gina kanta, da shi ta aurar da 'ya'yanta, da shi ta siyawa kanta daraja a wajen kishiyarta. Na ta so na ga Kaka tana siyar da Tuwo dan haka da kuWin Tuwo Kaka ta reneni ta sakani a Makaranta."

"So, idan na ce muku tuwon Kaka daWinsa daban ne, to ku yarda kawai."

"Ni dana ce kaWan zan ci tuwon, sai ga shi da ni aka cinye shi tas. Dana gama ci na tattare wajen sai na je"

na Waura ruwan wanka a 3kg gas dana siya mana kwanaki. Da ruwan ya Wan yi lum-lum sai na juye na kai banWaki na yi wanka.

Lokacin dana fito daga wanka sai Kaka ta ce min wai Baffa Lawalli yana nemana. Tsaki na ja dan na san

maganar ba zai wuce aron kuWi ba.

Kayan baccina riga da gajeren wando na saka sannan na Wau ™aton hijabi na sa a kai sannan na wuce

Sangarensu.

"Mutum shi ba wata sana'ar kirki ba ya je ya zauna ya tara mata uku shi kaWai, ga yara kullum haihuwarsu"

ake.

Allah dai kawai ya shirya.

"Šakinsa na shiga bayan na gaishe da Uwargidansa Maman Suwaiba da ta ke tatar kamu a ™ofar Wakinta,"

wajen duk ya yi caSal-caSal da ruwa babu kyan gani.

"""Baba, Barka da dare"" na gaishe shi bayan na tsugunna."

"""Barka da dare Ziyadatu, ya Makaranta?"""

"""Lafiya, Baba"""

"""Kin kusa gamawa ko?"""

"""Eh, daga mun gama wannan semestern za mu shiga ajin ™arshe"""

"""Allah ya taimaka"""

Na amsa da Amin.

"""Šan ™ara mini gudun fankan nan"""

Ina tashi zan je na ™ara gudun fankar Nepa 'yan tsiya suka Wauke wuta.

""" 'yan iska, Yaushe ma suka kawo wutan har sun Wauke"" Baffa Lawalli ya faWa da ™arfi kamar a ofishin"

NEPA na ke aiki.

Na dawo na zauna ina Allah-Allah ya yi ya sallameni.

Ina gani ya fara neme-nemen mafifici bai samu ba.

"""Jummai, Jummai, ina mafificinkun nan ne?"" Ya ™walawa matarsa kira. Itace matarsa ta biyu. Ina ga yau"

"girkinta ne. Matansa duka uku gatan Waki WaWWaya suka samu da su da 'ya'yansu, duk wacce ta ke da girki ita ce za ta shigo Wakinsa ta kwana. Manyan yaransu Maza kuma na kwana a Wakin Zaure."

Har yau idan rikicin gidan ya tashi aka fara faWan gado za ka ji matar Baffa Zakari tana mitar ai Baffa

"Lawalli shi kaWai ya cinye gidan, Wakuna huWu ya take shi kaWai."

Ni bana tunanin an shatawa Babana fili a gidan da sunan gado. Ina ga tun da ya rasu suka haWu suka

"la™ume filinsa da ke gidan. Shi ya sa fa nake son na samu kuWin kaina. Bana so ko kaWan na shiga maganar gado. Wanda ya ga zai ci ya ci, ai Allah ne ya ce a bayar idan suka cinye za su je su haWu da Ubangijin da ya ce a raba gado."

Ina tsugunne duk ™afafuwana sun yi tsami Anty Jummai ta shigo ta duba masa mafificin a saman ™aramin

tsohon TV da ke Wakin. Ta mi™a masa mafificin ta fita.

Ina nan sai haWa gumi nake cikin hijabi shi kuma ya dage sai fiffita ya

Please Login or Register in order to submit comment