You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya taSa aiki a

wajen tun farko-farkon buWewa. Na saki jiki dan na ga kamar ba za mu samu matsala da Jide ba. Yana da

sau™in kai.

JAYKAY

Dariyarta da ya ji dai dai ya karyo zai shiga hall Win ya saka shi banko ™ofar da ™arfi.

Dariyar kuwa ya gani a fiskarta lokacin data Wago ta kalleshi.

Me suke faWa haka har take dariya?

"Ya kirata nan ta zo ta yi hira da Jide ne, ko kuma ya kirata ta zo su haWa kai su yi aiki tare?."

Shiyasa ya ce Direba ya kawota Kamfani saboda baya so ita da Jide su keSe a restaurant Win suna

magana.

And the nerve tana yiwa Jide dariya. Dariyar da bata taSa yi masa ba.

"""Jide, aikin dana saka kenan?. Labari na ce ka zo ka bata?"""

"""Sorry, Sir"" Jide ya faWa yana mi™ewa."

"""Kun finalizing Menu?"" Ya tambaya yana kallon Ziyada"

"Jide ya ce "" erm, yanzu muke maganar..."""

"""Tun Wazu me kuke yi da baku gama ba?. Jide yaushe ka fara wasa da aiki haka"" Jalal yana maganar"

kaman zai daki Jide.

"""Sorry, Sir. Yanzu za mu gama. Infact dama za mu wuce Plaza Win kenan saboda mu ™arisa maganar a"

"can."""

"""Then me ka tsaya yi?"""

"Jide ya rufe Laptop Winsa ya kalli Ziyada ya ce ""Zeey, let's go"""

"Ziyada ta Wau jakarta itama za ta bi bayan Jiden yace mata ""tsaya"""

Cak! Ta tsaya ta juyo tana kallonsa.

"Sai da Jide ya fita daga hall Win sannan ya fara magana babu wasa ko kaWan a fiskarsa ""Jide is NOT your"

"friend. Aiki na ce kiyi ba hira ba"""

"""Hira kuma. Kawai fa muna taWin aiki a Zik..."""

"""Follow me"" ya katseta."

Yana gani tana motsi da bakinta amma bai ji me take faWa ba.

"Akwai aikin daya kamata ya yi a office Winsa, amma ba zai iya barinta ita kaWai da Jide ba. Gara su je a yi"

maganar komai a gabansa.

"Yana gani ta rungume jakarta tsam a ™irji ta tamke idanunta, bakinta na motsi lokacin da suka shiga cikin"

lifter. Wannan karan bata tsaya kusa da shi ba. Amma duk da haka sai ya tsinci kansa da kallon fiskarta. A

can ™asan ransa ya furta 'Matsoraciya'...

CHAPTER TWENTY SIX

ZEEY

Idanuna a rufe a cikin lifter da muke ina addu'ar Allahumma La Sahla... dan har cikina ya fara juyawa sai

"na ji mutum kusa dani. Na Wan buWe ido dan na san dai nesa da shi na tsaya lokacin da muka shiga lift Win. Ashe tsayawa muka yi wani mutum ya shigo shine ya matso kusa dani. Ina jin mutumin yana gaisheshi. Na Wan kalleshi sai kuma na sake rufe idanuna. Haushi ya bani Wazu, haka kawai muna cikin magana da Jide sai ya shigo ya fara mana masifa. Wallahi sai dana ji tausayin Wan Bayaraben nan. Daga ™arshe kuma ina ™o™arin yi masa bayani ya wani katseni wai na biyo shi."

Lokacin da lift Win ya tsaya har na yi yun™urin fita sai na ga mutumin Wazu ne zai fita shi gogan bai ko

motsa daga inda yake ba. Sai na juyar da kaina gefe nima na waske.

Ko sakan 40 ina ga bamu ™ara ba lifter Win ta sake tsayawa. Ina ganin ya fita nima na yi wuff na bi

bayansa tun kafin abun ya rufe dani na shiga uku.

Ina bin bayansa ina hararansa ta ciki-ciki. Ni ban san masifaffe bane sai yau. Wai mun tsaya hira ni da

"Jide. A'a ba hira ba, soyayya muke. Mtsww."

Da muka fito mutane sai wani gaisheshi suke yana wani amsawa irin Boss Winnan. Boss my foot.

Muna fitowa daga cikin building Win muka tsaya. Ban san tsayawar na me bane na dai tsaya a gefensa

ina kallon harabar wajen.

Jide ne ya fito daga building Win Wauke da jakar laptop Winsa. Ashe mun riga shi fitowa.

Šaga min babbar yatsarsa yayi ya min thumbs up nima sai na Waga masa ya wuce yana murmushi. A dai-

"dai lokacin wannan Šan Hajiyar ya juyo yana kallona. Na sauke yatsata, na haWe rai na juya gefe."

Direbansa ne ya kawo masa mota bakin building Win. Ya fito yana rawar jiki ya mi™a masa key Win motar

yana faWin a dawo lafiya YallaSai. Duk sai na ji haushin hakan. Na san dai ko babu yawa Direban zai girmi Jalal amma saboda matsayinsu ba Waya ba sai wani rawar jiki yake masa.

A rayuwata bana so na ga mutum yana haka. Shiyasa na tsani Baffa Lawalli. Idan ya ga mai kuWi haka

"yake jefar da shekarunsa ya fara ladabin ™arya yana rusunawa yana rawar ™afa. Allah watarana dana ga yana wani sussunne kai wa Alhaji Nafi'u ko, sai dana ji kamar na je na kifa masa mari. Mutumin nan fa ya haura sittin amma haka zaka ga yana abu kamar wani ™aramin yaro. Shi yasa Baffa Adamu ya fi shi daraja a idon mutane. Baffa Zakari ma akwai irin wannan amma nasa da sau™i compared to na Baffa Lawalli. Ko da yake shi dama ya saba yiwa kwastomomin Banki 'Yes Sir, Thank you, Sir'."

"Sai dana ji ya cewa Direban ""Thank you, Abdullahi"" kafin na Wan sassauta zafin dana ji a raina. Ashe dai"

yana da Wan hankali tunda ya masa godiya.

Ya karSi key Win motan ya je ya buWe ya shiga. Nima na bi shi na buWe gidan gaba na shiga. Ya ja motar

muka bar cikin kamfanin.

Bai min magana ba nima na tsuke fiska na manta da shi.

"Sai da muka kusa kaiwa Plazar na ji ya ce ""Agnes za ta joining Winku daga gobe. She's part of the team"""

"Ni ina ruwana. Koma mutane nawa ne za su joining Winmu su zo, Allah ya kawosu lafiya."

Har muka ™arisa wajen ban ce masa komai ba. Tunda masifa yake ji sai ya je can ya ™arata.

Na fito daga motar da sauri ko jiransa ban yi ba.

Šaya daga cikin masu gadin ya taso ya zo ya buWe mana restaurant Win. Na shiga na barsu suna magana.

Na samu waje na zauna. Can sai gashi ya shigo shima yana wani shan ™amshi. Da gaske fa ba zai ce na yi ha™uri ba.

Na jawo wayata na fara le™a duniyar social media. Bamu kai minti takwas da zama ba sai ga Jide ya shigo.

Jide ya jawo kujera kusa dani zai zauna ina ganin wani kallo da Jalal ya masa sai na ga Jiden ya ja kujerar

baya ya bada space tsakaninmu.

Kai wannan Bayaraben matsoraci ne. Allah idan nine ba zan matsa ba. To ina ruwansa da inda zai zauna.

Koda yake fa Ogansa ne.

Mtssw! masifaffen mutum kawai.

Kusan minti talatin muka Wauka Jide yana mini bayanin abubuwan dake ™asa da kuma yadda za mu

cigaba. An riga an yi rajistar JK Foods a matsayin sunan da restaurant Win zai Wauka tunda ™ar™ashin JK Group yake. Amma dama already wai Jalal ya ce za a sabunta rajistar JK Foods zai koma parent company mai zaman kansa. Shi kuma restaurant Win dama wasu brands Win da za a buWe a gaba ™ar™ashin kamfanin JK Foods za su Wauki sunaye daban. Wato a yadda na fahimta. Ba wai JK Foods Jalal zai bani ba. Zai bani restaurant Waya da zan gina ne ™ar™ashin JK Foods. Kenan a gaba JK Foods zai iya buWe wasu restaurants Win ko wasu business Win amma wannan da za mu buWe yanzu shine zai zama nawa idan muka yi aure.

Iya shege! Ashe ya san me yake yi. Wato dama ya bar mini wannan Winne na yi abincin gargajiya da duk

wata tsiyata. Idan ta failing ma nawa ne. Amma JK Foods za su cigaba da buWe restaurants a wasu wajajen ko kuma su yi any food related business a gaba.

To kuwa tunda na gano hakan ba zan bari wannan wajen ya yi failing ba. Wannan dama ce da zan

nunawa kaina ba ma Jalal kaWai ba cewa zan iya mallakar restaurant kuma na running Winsa successfully.

Ni da Jide muka fara brainstorming sunan da za mu sakawa restaurant. Ni da can da nake ta lissafin zan

buWe restaurant sunaye biyu ne nake tunanin sakawa wajen. Ko CHEF ZEEY RESTAURANT ko kuma na yiwa Kakata kara in saka sunanta wato FATIMA ALTINE FOODS. Na fi jin zan saka sunan Kaka. To amma wannan wajen temporarily ne. Ba zan samu mallakarsa gabaWaya ba har sai aurenmu da Jalal ya shekara kuma na gina wajen ya zauna da ™afafunsa. So saka sunan Kaka a wajen ba zai yiwu ba. Balle ma yadda Jide ke ta nanata min mutanen da suke so su attracting masu kuWi da middle class mutane ne. Dan haka na san ba za su yarda a sakawa wajen suna Fatima Altine ba. Amma Insha Allahu watarana zan buWe ™aramin restaurant da sunan Kaka.

Jide yace tunda local cuisine za a ri™a serving mu nemi sunan da zai tafi da hakan. Shi gogan aiki da calls

"kawai yake ta yi tun Wazu. Ni ban ma san me yasa ya biyo mu ba, dan duk bayanin da muke bai sa mana baki ba. Occasionally dai za ka ga ya Wago ya kallemu."

"Sunan GIDAN ABINCI ne ya zo mini. Ina faWa Jide yace perfect, sunan ya yi. Sai kuma ya ce ba ri ya duba"

ko akwai restaurant mai irin sunan saboda kar a samu matsala.

"""Shit!"" Ya Wan daki table"

"""Akwai irin sunan ko?"""

"""Wasu sun rigamu"" ya faWa yana girgiza kai dan sunan ya masa daWi."

"""What of GIDAN GIRKI?"""

"""Zeey, your brain is sharp ooo"" ya Waga min thumbs up. Na yi dariya."

Dariyar dana yi ya jawo hankalin Jalal ya bar wayar da ya ke a can gefe ya taho inda muke zaune.

Ya wani tambayi Jide cike da authority wai a ina muka tsaya?. Jide yace masa mun samo sunan

restaurant.

"""So, what did you come up with?"""

"""GIDAN GIRKI"" na faWa da Wan ™arfi dan ya san nina zaSi sunan."

"""And sunan is available, Sir"" Jide ya jaddada masa."

"Ya kalleni sannan ya kalli Jide ya ce ""Ku chanja"""

Mu chanja?. Mu chanja a wani dalili?.

"""Sir, I think the name is unique, and it's suits the restaurant's core idea"" Jide ya fara masa bayani."

"""Gidan Girki yayi fa. Ko Jide?"" Na kalli Jide da ya fara rarraba ido tsakanin ni da Jalal."

Da gangan na yi hakan. Akan me muna ta lissafi tun Wazu bai sa mana baki ba yanzu kuma ya wani shigo

wai a chanja sunan.

"Jide ya ce ""I think za mu iya tsayawa zuwa Agnes ta zo gobe before we decide, hope it's okay by you"

"Sir?"" Ya faWa yana kallon Jalal."

Jalal ya Waga masa hannu. Raina sai ya sake Saci. Ni fa ban gane deal Winnan ba.

"Ta ya zai dinga yi mana katsalandan a duk abinda muke yi. Idan bai yarda da ni ba, kuma bai yarda da"

"staff Winsa Jide ba, ai shikenan sai ya zauna yayi kayansa."

Haushinsa ya sa na mi™e na cewa Jide ni zan tafi. Ma haWu goben idan Agnes Win ta zo.

Jide yace ba matsala.

Har na fita bai yi kaman ya ji me nace ba.

Ni anya ma za mu wanye lafiya da shi kuwa???.

JAYKAY

Jalal yana gani Ziyada ta Wau jakarta ta fita.

Me yasa take da taurin kai ne.

"Why the fuck is she so comfortable with Jide, daga haWuwar kwana Waya."

First ta sake da shi suna taWi a office. Then yanzu kuma sun haWe masa kai. Shifa gani yake kaman sunan

yayi local dayawa. So yake ta tsaya ta masa bayani kaman yadda ta za™e tana yi da Jide but sai ta Wau jakarta ta fita.

To wai mi yasa yake jin haushin sakewarta da Jide ne?. Jide dama ko a office haka yake faran-faran da

mutane. Ita kuma she's just doing her job. But aiki yace ta yi ba murmushi ko dariya ba.

Aiki kaWai.

Bin bayanta yayi dan ba zai bari ta tafi gida ita kaWai ba.

Da sauri ya fito ya shiga mota ya bar Plazar ya hangota tana tsaye tana jiran Keke.

Dai-dai inda take ya tsaya. Yana gani tanata wani tsuke fuska irin ba zata shiga Winnan ba.

"He waited. Patiently, ya jirata."

Tun da ya haWu da yarinyar nan take saka shi jira.

Minti Waya ta yi tana masa jan aji kafin ta buWe ™ofar ta shigo.

Tana shiga ta fara magana.

"""Na shiga motan kane ne dan kawai kar mu tara jama'a, amma da ba zan shiga ba. Ehe"""

Bai ce mata komai ba ta gama surutu har ta yi shiru ta juyar da fiskarta tana kallon window.

So yake ta cigaba da magana dan hakan yana saka shi nishaWi.

"""Gidan Girki sounds nice"" ya faWa yana Wan kallon gefenta."

"""Kan buhu. Sai yanzu ne ka san sunan is nice. Ba cewa ka yi mu chanja ba. Tun da safe sai wani masifa"

"kake ta mana sai ka ce wani 'ya'yanka. Ai Wallahi Šan Yarabawa nan ma na ga ha™urinsa. Sai faWa kake masa kaman wani ™aramin yaro. Har da cewa sai wata Agnes ta zo kafin a tsayar da magana. Ba Agnes ba Agatha""."

Ta yi shiru ta sake juyar da fiskarta.

"Cikin ™asan ransa murmushi yake. He loves to see her talk, koda kuwa masifa take."

Those cute lips. Watarana sai ya yi maganinsu...

CHAPTER TWENTY SEVEN

ZEEY

"Finally mai girma YallaSai Jalal Maiya™i Šan Hajiya Layla ya amince mu yi amfani da sunan dana zaSa,"

"wato GIDAN GIRKI. Yau kwana uku kenan ni da team Wina muna ta aiki. Agnes ta zo, kuma itama tana jin sunan da muka zaSa ta ce ya yi."

Ai dama na san son nuna mulki da iko yasa Jalal yace wai a chanja sunan.

"Jide, shine aka barshi da bin procedure na registering sunan da CAC, da kuma trade marking Winsa. Ita"

kuma Agnes ita ce take handling designing logo na restaurant Win da kuma setting social media pages da

"sunan, saboda a nan zamu ri™a tallata restaurant Win idan aka buWe."

Ni kuma aka barni da creating Menu. Dukkanmu mun yarda akan Menu Winmu na breakfast da lunch

"dama dinner ba zai yi yawa ba. Za mu fara da kaWan, sai a gaba idan wajen ya karSu sai mu ™ara wasu"

abincin a Menu Win.

Tunda Agnes ta fara zuwa Jalal ya dena biyo mu restaurant. Da safe dai zai aiko min Direbansa ™arfe tara

ya Waukeni ya kaini Plaza. A nan za mu haWu da Jide da Agnes mu yi aiki. Kwana biyun nan ma har yamma muke kaiwa saboda aiki. Keke na ke hawa in koma gida duk da kuwa Jalal yace min idan na gama in kira shi zai saka Direbansa ya zo ya mayar dani gida. Amma ban taSa kiransa ba.

"Jide, Agnes kawai yake Wauka a motarsa. Wai ba zai Waukeni a motarsa ba kar Oga Jalal ya koreshi a aiki."

"Na ce masa akan me zai koreshi a aiki dan ya rage min hanya. Ya ce babu ruwansa, ai nima na san dalili."

Ni kam ban san dalili ba.

Har Agnes ta shiga maganar tana tambayata miye tsakanina da Jalal? Na ce mata babu.

Nima ban matsawa Jiden ba wani lokaci ma ni nake rigasu tafiya. Ba yau na fara hawa Keke ba. Mu

mutanen Ghetto dama ai Keke shine Jeep Winmu.

Yau na kawo draft Win Menu da za mu yi amfani da shi a restaurant Win. Muka haWu dukkanmu uku aka

tattauna yadda komai zai kasance.

"˜arshe aka cire wasu daga ciki, wasu kuma aka pairing Winsu da wasu side dishes Win saboda zai fi kawo"

kuWi.

Next abinda za a yi shine Food testing. Zan girka duka abincin da muka selecting a Menu Winmu saboda

su Jide da kuma anonymous tasters Win da aka zaSa su yi rating abincin.

"Za su rating komai, tun daga taste Win abincin, har zuwa plating da presentation Winsa. A wannan wajen"

"ake so na nuna bajintata. Dan idan aka buWe restaurant Win, abinci mai daWi shi zai tafiyar da wajen."

Ina da confidence akan na iya girki. Amma duk da haka sai da na ji wani War da aka ce za a yi Food tasting

Winnan.

Muka rabu akan gobe za a kawo ingriedients zan dafa first batch na Menu Win sai na serving mutanen da

za a gayyato su ci abincin.

Food tasting Win zai Wauki kwana uku. Dan haka kafin na tafi sai dana rubuta musu list Win abubuwan da

nake bu™ata da zai covering girkin da zan yi na kwana uku.

Ina fitowa daga Plazar wayar Faty na shigowa. Ta fara ™orafin wai gashi har an kusa resuming school

amma ban kawo mata ziyara ba kuma ta ce na zo na mata Wanwake a gidanta na ™i zuwa.

Ha™uri na bata na buge da tsokalarta Babynmu dai ke son cin Wanwake ba ita ba. Yadda ta fara dariya

tana wallewa ita bata da komai na fahimci da gasken ciki ne da ita. Na mata fatan alkhairi na ce ta yi ha™uri wani aiki ne ya ri™eni ba zan samu zuwa ba. Amma zan sa Kaka ta mata Šanwaken sai na sa yaro ya kai mata har gida. Ta ce ba matsala.

Idan ba haka na yi ba kam bani da lokacin zuwa gidanta a yanzu da muke shirin kafa GIDAN GIRKI.

"Da dare ina kwance akan gado amma bacci ya ™aurace mini. Kaka kam ita har ta fara bacci, amma ni"

gaba Waya tension ya sakani gaba. Sai lissafi nake. What if aka samu matsala suka ce ban iya girki ba.

Tabbas idan waWanda aka gayyato suka ci abincina suka ce bai yi ba na san Jalal sai ya yi min dariya.

Cewa zai yi dama alfarma zai min amma ba zan iya running wajen ba.

"""Kaka"" na kira a hankali."

"""Kaka"" na Wan Waga muryata ina taSata"

"""Kaka dai"""

"""Na'amm"" ta faWa da muryan bacci."

"Matsowa na yi jikinta sosai na ce ""Kaka, miye sirrin sana'ar abinci?""."

"Na yi tambayar ne saboda for the first time a rayuwata da nake dab da jagorantar restaurant, ina jin"

tsoro.

What if experience Wina har yanzu bai kai na karSi wannan aikin ba?.

Tun farkon amincewata da deal Win Jalal na yiwa Kaka bayanin zan fara aiki. Ban faWa mata deal Win dake

"tsakanina da Jalal ba. Iya abinda ta sani shine, Wan Hajiya Layla da nake zuwa gidanta na mata girki, ya bani aiki a restaurant Winsa a matsayin Head Chef. Wato kwacokam aikin abincin wajen yana ™ar™ashina."

"""Abinci hannu-hannu ne Ziyadatu. Ina da ya™inin hannunki akwai albarka, duk abinda kika girka mutane"

"za su ci su ji daWinsa"""

"""Kaka, hannuna ba irin naki bane. Har yanzu fa idan na yi Tuwo baya daWin naki"""

"""Ke kike ganin haka. Amma duk wanda ya taSa cin Tuwon da kika yi ya san Altine Mai Tuwo ta samu"

"Magajiyarta"""

Na saka dariya. Yanzu data faWi hakan sai na ji confidence Wina ya fara dawowa. Ba zan iya tuna yaushe

"na fara koyon girki ba. Idan ka taso a gidan da ake abinci tun kafin ka fara wayo zaka zama apprentice. Daga mi™o kaza, wanke kaza, daka kaza, juya kaza zaka fara, har a zo lokacin da za a fara sake maka kana yin wasu abubuwan da kanka."

Ba zan taSa manta shirme na farko dana tafkawa Kaka ba lokacin da nake tasowa. Ina JSS one lokacin.

Kaka ta yi miya ta bari a wuta yana dahuwa sai ta ce na duba ko yayi lokacin zata shiga banWaki. Dana taSa miyar sai na ji kamar gishiri bai ji ba. Maimakon na faWa mata sai kawai na je na Wauko gishiri a leda na zo na kambaza a cikin miyar. Ai kuwa Kaka data zo bata taSa ba ta sauke miya aka fara siyar da abinci. Sai gashi ba a jima ba mutane suka fara dawowa suna cewa gishiri yayi yawa a miyar.

Kaka ta WanWani miyar sai ta kalleni. Tun kafin ta yi magana na fara hawaye ina Wallahi Tallahi gishiri

kaWan na saka.

"Kaka ta ce Allah ya kyauta. Har yau ban san me Kaka ta yiwa miyar ba, dan kuwa bayan ta gyara miyan"

aka cigaba da siyar da abincin babu matsala har Tuwon nan ya ™are tas ba a sake ™orafin gishiri yayi

yawa ba.

Tabbas girki yana da sirri. Kuma sai yanzu nake ganin kamar har yanzu da saurana akwai abubuwan da

ban sani ba.

"""Kin iya girki Ziyadatu"" Kaka ta jaddada mini."

"""Yau da gobe ai ba wasa ba. Gashi nan kin iya abincin zamani, har da su wannan pirayid rayis (fried rice)"

"Winnan da kike mana""."

Na fara dariya ina faWin ai duk da haka ban kai ta iya girki ba.

"Kaka ta ce ""babu wani sirri da zan baki Ziyadatu, sai abubuwa guda uku da uwata ta bani lokacin dana yi"

"aure zan fara sana'ar Tuwo"""

Ina jin batun sirri na buWe kunnena da kyau.

Na yi Islamiyya. Hadda ne kawai ban ™are ba amma na yi saukan tartil kuma ba laifi kafin Boko da neman

kuWi su sakani na yaye Islamiyyar na yi nisa a karatun litattafai da dama. Haddar ma dai ba dan na dena zuwa ba da zan gamata dan na bawa izub arba'in baya. Dan haka sirrin addu'a nake tunanin zan samu a wajen Kaka ba wani abun da zai zama tsubbu ko shirka ba.

Ban taSa ganin Kaka da laya ko wani abu ba. Lokacin da nake ™arama mutane babu abinda basa faWa

"akan Tuwon Kaka. Musamman Baaba Tabawa, Allah dai ya ji™an rai. Har faWawa mutane take wai Kaka ta busine layayoyi a gindin murhun da take sana'arta, shiyasa take samun sa'a."

"""Sirri na farko shine, ki tsaftace zuciyarki. Kada ki ce za ki dafawa mutane abinci da mummunan zuciya."

"Manufarki akan mutane shine ki dafa musu abincin da za su ci, su ji daWi. Ke kuma alkhairin da za a baki ya zamo halal Winki kuma silar samun rufin asirinki a duniya. Idan kika yi girki da mummunan zuciya za ki samu matsala, saboda muguntar da ke zuciyarki zai bayyana a abincinki"""

Na yi shiru ina jinta.

"""Na biyu kuma ki tabbatar kin tsabtace muhallinki kuma ki ri™a amfani da abubuwa masu inganci. Idan"

"nama zaki siya ki sayi mai kyau. Idan kayan miya ne ki tabbatar mai kyau kika siya. Amfani da kayan haWi mai kyau da inganci wajen girki shine sirri na biyu da zan baki"""

"Ta Wan yi shiru bata sake cewa komai ba. Na Wan le™a fiskarta nace ""Kaka kin yi shiru baki faWa min sirri"

"na ukun ba?"""

"Ta Wan yi murmushi ta ce ""Na tuna Uwata ne. Murjanatu ikon Allah"""

"Allah Sarki!. Kaka ma fa 'ya ce. Kafin ta haihu ta zama uwa. Kafin a haifeni na zama jika a gareta. Ita,"

Fatima Altine 'ya ce. Šiya ce ga Murjanatu mai Tuwo.

Rayuwa kenan.

"""Sirri na ™arshe shine sirrin BISMILLAH. Duk abinda aka fara shi da BISMILLAH to zai yi albarka. Dan haka,"

"a koda yaushe kika isa bakin murhunki za ki fara girki, to ki fara da BISMILLAH. An kawo miki kayan miya za ki gyara a kai markaWe ne, to fara gyarawa da BISMILLAH. Abincin ne ya samu matsala kika Wan yi dabarunki dan ki gyara shi, to ki haWa da BISMILLAH. Wannan sirrin Uwata ta bani. Kuma shi na ri™e ake ta cewa Altine ta bisine layoyi a bakin murhunta. Ziyadatu ban san mecece laya ba. Ban gani a gidanmu ba, shima Malam dana aureshi ban ga laya a jikinsa ko a kusa da shi ba. Ban yarda da Boka ko Malamin Tsubbu ba. Sirrin BISMILLAH da kuma karatun FATIHA da aka bani shi na ri™e sama da shekara hamsin da na yi sana'ar Tuwo a gidan nan"""

Na rungume Kaka da kyau ina mata godiya.

"Daren ranan bamu yi bacci ba sai kusan ™arfe biyu, dan bugewa muka yi da labari. Kaka ta yi ta bani"

"labarin ™uruciyarta, dama farkon aurensu da Kakana Malam Haruna. Har da irin matsalolin da ta rin™a"

"fiskanta a sana'arta musamman daga wajen kishiyarta, dama mahassada dake gefe."

Wannan sai ya ™ara fahimtar dani duk sana'ar da za ka fara to ka ri™e Allah. Dan kuwa kana gefe kana

neman kuWinka wani can yana ta faWi-tashi dan ganin ya Sata maka sana'arka ko kuma ya ri™a yi maka

mugunta har sai komai ya lalace.

Tabbas sirrin kowanni sana'a shine yin ri™o da ADDU'A.

Da safe da muka tashi sai

Please Login or Register in order to submit comment