You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

team Winta sun yi ™o™arin ganin maganar bata fito ba idan Jalal ya ji labari zai iya amfani da hakan wajen samun hujjar gabatarwa a kotu dan a raba aurensu.

"Bayan maganar tabbatar da auren Jalal da ta zo yi Nigeria, babban dalilinta na zuwa Nigeria saboda case"

Win da aka yi da ita ya lafa ne kafin ta dawo.

Ta san abinda za ta yi. Šauke Junior za ta yi. Idan ta tafi da shi Jalal zai dawo hayyacinsa ya dena

maganar zai saketa.

***

CHAPTER FIFTY TWO

ZEEY

Fiskata na kalla a madubi. Fiskata ne shaidar abinda na gani jiya da dare ba mafarki bane. Ba zan iya tuna

"yaushe bacci ya Waukeni ba. A daren na haWa kayana a cikin akwati. Daga nan kuma sai na yi sallah na kaiwa Allah kukana. Tabbas na tafka kuskure, na yi wasa da sunnar Ma'aiki (SAW). Tun a wajen neman aure na tafka kuskure. Ta ya zan amince na ™ulla yarjejeniyar aure saboda wata manufa daban ta neman duniya. Wata™ila wannan dalili yasa abubuwa suka yita kwaSe mini daga sadda aka saka auren har zuwa yanzu."

Na fita daga sharrin Alhaji Nafi'u da ™yar yanzu kuma na shiga wata jarrabawar ta yaudara dana gani

™arara a gurin Jalal.

"Shi ga shi mai wayo, yana son Baturiyarsa, amma yana mini ™aryar zai rabu da ita. A halin dana ke ciki"

"yanzu Aurena ba shi da Guarantee a wajen Jalal. Idan kuwa haka ne gara na koma wajen Allah na nefi yafiyarsa sannan na ri™e sana'ata da mahimmanci, wannan shine mafita a gareni koda Jalal ya nemi rabuwa da ni."

"Na jima ina yiwa Gidan Girki Restaurant addu'a, dan business sai da ro™on Allah."

Šan baccin dana samu yi kaWan ne kafin alarm Wina na ™arfe huWu da rabi ya tasheni. Daga nan kuma na

sake shiga banWaki na iho wata alwalar na yi sallah raka'a biyu na kama salati.

Yanzu da nake kallon kaina a madubi sai na ke ganin anya idan na je gidan Hajiya a haka ba zan Waga

mata hankali ba?.

Na kalli akwatuna biyu manya dana cika da kaya sannan na sake kallon kaina ta madubi. Tabbas da an

kalli fiskata an san babu lafiya.

Ban gama tsaida shawarar in tafi ko kar in tafi ba aka fara buga mini ™ofa da ™arfi. Bugun matar gidan ne

bana YallaSai Jalal ba.

Har zan share sai kuma na ce gara dai na fuskanceta na ji da wata tsiyar ta sake zuwa mini. Miji dai na

bar mata ta je ta ji da shi.

"Ina buWe ™ofar na ganta sanye da wani shegen guntu riga iya gwiwa, rigar babu hannu, gashinta ya yi"

"buju-buju, make-up Win fiskarta duk ya zazzago. Warin giya ne ya bugo ni."

Ta nuna ni da yatsa tana gyara tsayuwarta da alama giyan da ta sha bai saketa ba.

"""HE'S MINE"" ta faWa da ™arfi."

"""Jalol is MINE"""

Ta fara karanto mini tarihin soyayyarta da Jalal. Yadda Jalal yake matu™ar sonta har ya bijirewa

"mahaifiyarsa ya aureta. Ta kira ni da kalmar Karuwa, ta ce ban isa na rabata da mijinta Jalol ba."

Daga ™arshe ta fara yi mini kashedin wai na tattara kayana na bar gidan sannan na fita daga rayuwar

"Jalal idan ba haka ba zan yi sanadiyyar da Jalal zai rasa Wansa, kuma na san yadda Jalal ya ke son yaronsa."

Ban ce mata uffan ba. Babu amfanin tanka ma 'yar giyar da giya bai gama sakinta ba.

Rufe ™ofar na yi tana cikin magana. Ta cigaba da buga ™ofar da ™arfi tana kirana da 'Bitch'. ˜arshe sai na ji

ta koma kiran sunan Jalal da ™arfi.

"Bayan abinda na gani jiya, babu wani sabon abu da za a yi da zai sake Sata mini rai, dan haka haukar"

Cassandra ko kaWan bai Waga mini hankali ba. Gida ne dai ko bata faWa ba zan bar musu gidan su je can

su ™arata tsakaninsu.

Lokacin dana fito da Akwatunana sai na ga ba zan iya jansu zuwa ™asa ta daWi ba wannan ya sa na Waga

Waya na fara saukowa da shi ina tafiya a hankali saboda takalmin dana saka yana da tudu sosai.

Ban kai ™asa ba na ganshi yana kawowa saman. Yana zuwa ya karSi Akwatin daga hannuna. Maimakon

ya yi ™asa sai na ga ya koma sama.

"""Gidan Hajiya zan wuce"" na faWa ina bin bayansa. Da gaske fa ba zan cigaba da zama da shi a gidan nan"

ba.

A ™ofar Wakina ya ajiye Akwatin. Ya sa hannu zai buWe Wakin ya jita a rufe.

"""Na faWa maka gidan Hajiya zan koma"""

Sai a lokacin ya Wago ya kalleni. Jajayen idanunwansa da suka ™an™ance kamar na 'yan China ne suka

nuna shaidar rashin bacci a fiskarsa.

"""Ki buWe"" ya faWa yana kallona da wani sanyin da yake ro™on in tausaya masa. Na kawar da kaina gefe."

Na gama jin tausayinsa. Fiska biyu gareshi.

"""Key"" ya faWa yana mi™a min faffaWan hannunsa."

"""Please"" ya marairaice ganin na ™i bashi key Win. Sai a lokacin na fito da key Win daga purse Wina na buWe"

Wakin muka shiga.

"""Ba zan hanaki tafiya ba"" ya faWa bayan ya kai min Akwatunan wajen closet."

"""Hajiya tana da ba™i a gidanta. Idan kika je a haka hankalinta zai tashi"" ya faWa yana kallona."

Jallabiyar jiya ne a jikinsa sai dai yanzu ya sakata da kyau ba kamar jiya da ya saka a juye ba. Sai dai

yadda take a cakuWe ma ya nuna tun jiyan bai cireta ba. Na Wauke idanuna daga fiskarsa dan haushinsa nake ji.

Ban ankara ba ya kamo hannuna. Wani shock na ji amma sai na danne tasirin hakan na kafe shi da

idanuna.

"""Ina so ki sani Gidan Girki Restaurant naki ne"""

Ya sa hannunsa Waya ya tallafo fiskata.

"""I'm wishing you best of luck, Sunshine"""

"Ya shafa kumatuna da babbar yatsarsa ya ce ""Allah ya sa miki Albarka a wajen"""

Amin Win dana faWa ya yi dai dai da cire hannunsa da na yi daga fiskata. Idanunsa suka wani marairaice

alamar in tausaya masa.

"""Zan wuce"" na faWa bayan na matsa daga gefensa"

Ya buWe baki kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru.

Muka tsaya kallon juna.

"Can sai ya ce ""Idan kin shirya, Abdullahi zai kai ki"""

"Daga haka sai ya fita, na bi bayansa da kallo ina jin zuciyata na min wani zafi..."

***

"˜arfe tara na safe aka buWe JK Plaza, muma a lokacin ne muka buWewa Wimbin Jama'ar da suke shigowa"

Plazar ™ofar Gidan Girki. Duk da halin da na ke ciki cikowar da Restaurant Win ya yi da yadda ake shige da fice a wajen sai ya Wauke min damuwar dake zuciyata. Na mayar da hankalina kan kula da yadda staff Wina suke tafiyar da komai.

Kafin ™arfe shaWaya ma breakfast menu Winmu ya ™are. Har an kusa fara serving lunch.

Wajen ™arfe shabiyun ne kuma Hajiya ta shigo Restaurant Win. Office Wina Janan da ke ta up-and-down

"tun safe ta kawota. Ta yi mini Addu'ar Allah ya sawa wajen Albarka. Ita da wasu ™awayenta guda biyu da wata da ta ce matar ™aninta ne suka kama table suka bada order abinci. Abinka da uwar miji ni da kaina na karSi order na zo na serving Winsu. Hajiya tana faWin ya haka na ce mata babu komai, Special Customer Service nake bata. Mutanen dake tare da ita suka sa dariya."

Lokacin dana koma office Wina ne wasu 'yanmata guda biyu suka shigo. Šayar kaman na taSa ganinta a

"lokacin bikina, ina ga 'yar uwarsu Janan ce"

"""Madam Chef Chef"" ta faWa tana wani kwashewa da dariya. Itama yarinyar da suka shigo taren dariyar ta"

saka.

Kallo Waya na musu na Wauke kaina na cigaba da danna Laptop dake ™aramin desk Wina. Na Wan iya

Computer tun a hutun JSCE da muka yi da nake karSan Laptop Win yaya Aminu nake kallo. Lokacin dana ke ta fafutukar karatun JAMB kuma yaya Aminu ya sake koya min saboda CBT ne Jamb Win.

Jiya dana shigo Jide ya nuna min yadda zan yi amfani da Software Win da aka saka dan na ri™a tracking

"duk abinda yake faruwa a restaurant Win, tun daga shigowar kuWi da fitarsa. Yanzun ma ina ™ara bibiyar Software Winne saboda ban gama ganewa ba waWannan ™ananan yaran suka shigo. Duk su biyun babu wacce za ta yi shekara ishirin a cikinsu. Shi yasa wani falli da suke bai dameni ba."

"""Idan babu abinda ya kawoku please ku fita min daga office aiki nake yi"""

Yarinyar dana ke tunanin 'yar uwarsu Janan ce ta kwashe da dariya har da tafawa.

"""Ku jita fa. Har ke za ki ce mu fita daga office. Kin san ala™ar dake tsakanina da yaya Jalal?"""

"""To barin gaya miki ni ™anwarsa ce. Kuma na san ya aureki ne dan ki kula masa da wannan Restaurant"

"Win, baki da wani matsayi a wajensa"""

"Ta kalli ™awarta ta ce ""In faWa miki a gaban Matarsa Cassandra ya kirata da JUST a Chef"" suka ™yal™yale"

da dariya.

"""Sharifa!"" Janan ta shigo office Win ranta a Sace."

"""Sharifa, dama ke kika faWawa Cassy yaya Jalal ya yi aure?"""

Rarraba idanu ta fara yi ganin babu wasa a fiskar Janan.

"""Answer me!"" Janan ta daka mata tsawa."

"""Sai me dan na faWa. Ai dama na san Soye mata aka yi saboda munafurci"""

"""Saudah ce ta saki?"""

"""Babu ruwan Anty Saudah da wannan"""

Na baza ido kawai ina ganin dramar su. ˜arshe dai Sharifa da ™awarta suka fita suna SaSSata fuska bayan

Janan ta ce za ta kai ™aranta wajen Uncle Idris.

"A yadda na fahimta, Sharifar ™anwar Saudah ce."

"""Don't mind them please"" Janan ta faWa bayan fitarsu. ""Sharifa bata da hankali Wallahi, ™anwar Saudah"

"ce. Kin san Cousin Wina Saudah ai?"""

Na gyaWa mata kai.

A wajen Hassana mai aikin Hajiya na samu gulmar Saudah. Ita ce ™anin Jalal zai aura Allah ya masa

rasuwa sati biyu kafin auren. Daga baya kuma Hajiya ta ce Jalal ya aureta amma sai ya ™i.

I guess saboda baya son auren Saudah shi yasa ya zo mini da maganar auren deal. Ni sai yanzu ma nake

"ganin wautata, tun farko ni Win ban dace da Jalal ba. Ya zaSe ni ne saboda ya samu damar cimma burinsa ba tareda ya sha wahala ba. Ai da 'yar uwarsa Saudah ya aura da ba zai mata wala™ancin da yake mini ba. Ai ba za ma ta yarda ya wala™antata a gaban Baturiyarsa ba. Ni Win ce dai ya renawa hankali, saboda bani da gata."

Na yi mamakin yadda Janan ta ke ta bani ha™uri duba da cewa baki da baki ta ce min bata sona. Koda

"yake ta faWa mini dalilin da ya sa ta ce bata sona Win. Da gaskiyarta, ni Win Local ce. Wata™ila hakan na daga cikin dalilin da ya sa Jalal yake rena mini hankali. Yana tunanin idan ya shirya mini zance ya mini daWin baki zan yarda da shi har ya samu kaina."

Wata™ila ma nufinsa idan ya samu kaina ya gama marmarina ya ga na gundureshi mayar da ni Ghetton

da ya Waukoni zai yi.

"""Wata Aunt Win Khalifah ce ta zo siyayya a plaza shine na ce ta shigo Gidan Girki ta ci abinci"" Janan ta"

katse ni.

"""Please ki sa a kawo musu best abincin dake Menu Winku, ita da yaranta suka zo"""

Tashi na yi ta bi bayana. Na lura dai ba ™aramin so take yiwa Mi Amor Winta Khalifa ba.

Kitchen na wuce na yiwa Bisola magana na ce a serving Winsu White rice da Classic Jajjage Sauce.

"Lokacin dana le™a hall Win Restaurant Win sai na ji wani daWi ya mamayeni, ta ko'ina mutane ne. Addu'ata"

shine kamar yadda mutane suka mana tururuwa a ranan farko Allah ya sa kasuwa ta cigaba da Worewa a haka.

Wajen ™arfe shida saura na yamma Jide ya shigo office Wina.

Maganar cinikin da muka yi a yau ya mini. Ya ce idan muka cigaba da samun irin numbers Winnan kafin

"shekara zai tara kuWin aure. Na yi dariya na ce shi burinsa kuWin aure, ni kuma burina idan Gidan Girki ya haSaka za mu buWe branch ne a Abuja da Kano, har Lagos."

Jide ya ce very soon kuwa za mu kai haka.

For now dai aiki za mu cigaba da yi muna haWawa da addu'a saboda wannan sabon waje da ya tara

Wimbin Jama'a yau ya cigaba da cika kullum. Hakan shi zai sa mu cimma dogon burinmu na buWe rassan Gidan Girki a wasu garuruwan.

Bayan mun gama reviewing cinikin yau sai na tattara kayana na yi musu sallama. Na shiga Kitchen na

musu jinjinar ban gajiya saboda da ni da su Win duka mun sha aiki.

"Lokacin dana fito mutane sun ragu a Plazar, ba kaman cikowar da aka yi daga safe zuwa ™arfe huWu na"

yamma ba.

"Lokacin dana iso gida ko'ina shiru. Da ™yar nake taka stairs saboda gajiya, dukkan jikina ke mini ciwo, ga"

uwa uba kaina dake sarawa kamar zai rabe biyu. Wanka na yi da ruwa mai zafi na yi Alwala na fito. Ina idar da Sallar Magariba na kwanta akan Sallaya jikina na Sari. A daddafe na mi™e lokacin da Isha ta yi na tada Sallah. Da ™yar na dragging jikina na hau gado na lulluSu da bargo saboda wani sanyi dana ke ji. Ina kwanciya zazzaSi ya rufeni ni kaWai sai rawar sanyi nake a cikin bargo.

Akwai First Aid Box a banWakin Jalal amma ba zan iya tashi bama balle na je Wakin na dubo magani. Ba

"ma zan sake shiga Wakinsa ba, kar na ci karo da abinda zai Waga mini hankali."

JAYKAY

A gajiye Jalal ya shigo gidansa ™arfe tara na dare. Da safe yana shirin fita wajen buWe Plaza Cassandra ta

tsare shi da maganar ba ta yarda da maganar saki ba. Ba za ta bashi saki ba saboda har yanzu tana sonsa. Har da cewa za ta yafe mishi cin amanarta da ya yi amma dole ne ya kori Ziyada daga gidan ya kuma cireta daga rayuwarsa.

Sake jaddada mata rushewar aurensu ya yi tareda faWa mata hukuncin da ya yanke shine dai-dai. Idan ta

bashi haWin kai divorce proceeding Winsu zai tafi da sau™i.

Ai kuwa Cassandra ta haukace masa akan bata san zance ba. Ta cigaba da i™irarin ba za ta taSa rabuwa

da shi ba. A haka ya fita daga gidan ya barta tana ta hauka ita kaWai.

Šakin Ziyada ya buWe a hankali ya hangota lulluSe cikin bargo tana bacci. ˜arisawa ya yi bakin gadon ya

"™ura mata idanu. Šan gyara mata bargo ya yi saboda ya ga kamar tana zufa. Ta kashe AC Win Wakin, sai ya yi tunanin ko sanyi take ji ya sa ta kashe. Manna mata kiss ya yi a kumatu da goshi sannan ya fita daga Wakin. Yana son kwanciya kusa da ita, amma ya san idan ta buWe ido ta ganshi ranta zai iya Saci tunda fushi take da shi."

Zai bata space ne zuwa lokacin da za ta sassauta fushinta.

Spare room dake sama da ya ajiye wasu daga cikin kayansa yau da safe ya shiga. Wanka ya shiga ya

sakewa kansa ruwan zafi. Lokacin da ya fito sai ya ga missed call Win Hajiya har guda biyu. Zama ya yi a bakin gado Waure da towel a ™ugunsa ya dannawa Hajiya kira.

"""Muhammad zai kwana a wajenku ne?"" Ta tambaya bayan ya amsa sallamarta."

"""Muhammad ya zo nan ne?"" Ya tambaya cikin rashin fahimta"

"""Kai zan tambaya ai. Tunda muka dawo daga Plaza da ya ce zai je gidanka ban sake saka shi a idona ba."

"Na ce ko wajen Mamansa zai je shi yasa ban hana shi ba"""

Mi™ewa Jalal ya yi bugun ™irjinsa na ™aruwa ya nufi hanyar Wakinsa.

"""Hello, kana jina?. Hello, Hello"""

Kasa motsawa ya yi daga inda yake tsaye ganin babu Akwatunan Cassandra a Wakin. Da ™yar ya ™arisa

wajen da ya ke ajiye mahimman takardunsa da passport Winsa ya buWe ya ga wayam babu Passport Win Wansa Muhammad.

Subhanallahi! Cassandra ta gudu masa da yaro...

CHAPTER FIFTY THREE

***

Nambar Cassandra Jalal ya shiga kira amma numbar bata tafiya. A haukace ya fito daga gidan bayan ya

saka Jallabiyarsa.

Wajen Maigadi ya nufa yana tambayarsa yaushe Cassandra ta fita daga gidan?.

Maigadi ya ce masa wajen ™arfe uku na rana ne.

"""Ita da Muhammad suka fita?"" Ya tambaya da ™arfi."

"""Eh, YallaSai"" Maigadi ya amsa a tsorace."

"""Shit!"""

"""YallaSai, lafiya?"""

"""Ina Abdullahi?"""

"""Ya tafi gida, YallaSai"""

Jalal ya koma ciki a rikice.

Key Win mota ya Wauko ya fita daga gidan da gudu.

Yana tu™i yana sake gwada numbar Cassandra. Sai da ya yi nisa ne ma ya fara tunanin ai bai san

takamaimai inda zai nemeta ba tunda numbarta ba shiga yake ba.

Kiran Hajiya ne ya shigo wayarsa.

Hankalinta ya tashi.

Jiki a sanyaye ya Wau kiran.

"""Jalal ina ta magana ka kashe wayar. Ina Muhammad yake?"""

"Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce ""Cassandra bata nan. Na duba babu Passport Winsa"""

"""Subhanallahi!. Garin yaya ka bari ta Wauke Passport Winsa?"""

Ya yi shiru bai yi magana ba.

"""Tunda ta Wau Passport Winsa kam kaima ka san London za ta kai shi. Ai shikenan... Mu kwana lafiya"""

Yadda ta kashe wayar cikin fushi ba ™aramin Waga masa hankali hakan ya yi ba.

Ganin babu amfanin fitarsa sai ya dawo gida. A falon ™asa ya zauna ya kira wani IT Staff Win office Winsa

"ya ce ya bincika masa ko Jirgi ya tashi daga Abuja zuwa London a daren yau, sannan ya duba masa"

sunayen Passengers ko akwai sunan Cassandra da kuma yaronsa. Cikakken sunansu ya tura masa ya

zauna yana jiran bayani daga wajensa.

Bayan kusan minti arba'in sannan aka kira shi aka tabbatar masa da cewa Cassandra da Wansa suna

"hanyar London a yanzu haka, dan Jirgin ™arfe bakwai na yamma suka shiga daga Abuja..."

Bai iya bacci a daren ba. Tunani ne kala-kala suka cika masa kai.

Washegari da sassafe ya wuce gidan Hajiya bayan ya le™a Wakin Ziyada ya ga tana bacci.

A Waki ya sameta tana Azkar. Ya gaisheta jikinsa a sanyaye.

"""Hajiya, a yi mana addu'a zan wuce Abuja, na booking flight zuwa London ™arfe uku"""

"Hajiya ta tsaida carbin da take ja ta ce ""yanzu idan ka je can Win kana ga za ta yarda ka dawo da yaron"

"cikin sau™i ne?. Tun yaushe ya kamata a ce ka nemi sole custody Win Muhammad. Da yanzu kai ne da Custody Winsa ai da ba za ta samu damar kidnapping Winsa haka ba""."

"""Dama abinda nake jiye maka kenan ga shi an zo wajen. Kai komai naka babu tsari. Da tuni ka rabu da"

"shegiyar yarinyar nan da an riga an wuce wajen. Ni dai ka saurareni da kyau. Ba zan sa baki a aurenka da Cassandra ba, amma zaman Muhammad a wajenta ba zai yiwu ba. Ka dawo min da jikana gidan nan"""

Zuciyarsa ne ya karye da maganganun Hajiya. Tabbas ta ji zafin abinda ya faru. Ita ce ke kula da

Muhammad tunda ya kawo shi Nigeria. Zaman yaron kaWai a gidan ya cirewa Hajiya yawan tunani.

"""Is bad enough ka aurota"" Hajiya ta cigaba da faWa. ""Yanzu yaron da nake Alfahari da ™o™arinsa a"

"Islamiyya shine za a mayar da shi London inda ko Sallah ba kwa bari ya yi"""

"""Sanda ka kawo yaron nan ko Alwala bai iya ba balle ya san menene Sallah. Idan ba dan Jamal bama da"

"ina ga..."" sai ta yi shiru."

Once again ta sake nuna gazawarsa.

Wani lokaci idan ta nuna masa hakan sai ya yi tunanin da za a bata zaSi a ce mata wa za a Wauke wa za a

bar mata a cikin shi da Jamal. Babu makawa ya san da yanzu shine a cikin ™asa ba Jamal ba.

"""Insha Allahu zan karSo Muhammad"" ya faWa a raunace."

"""Ba maganan karSo shi bane. Idan ka ce ba zaka raba ala™arka da Cassandra ba to ko ka karSo"

"Muhammad ka ri™e shi a wajenka"""

Mi™ewa ya yi jiki a sanyaye ya fito daga Wakin Hajiya bayan ya mata sallama.

Ji ya yi ya tsani kansa.

Ji yayi tarin shekaru kawai gareshi amma ba shi da basirar yadda zai tafiyar da rayuwarsa bisa tsarin da

zai farantawa mutanen da ke kusa da shi rai.

Ga Ziyada tana fushi da shi.

Ga Hajiya da ta sake tabbatar masa da abinda ya jima da sani. Tun ranan da ya auri Cassandra ta ke jin

haushin aurensa har yanzu abin na damunta.

Ga shi saboda sakacinsa Cassandra ta samu damar tafiya da Junior.

Tambayar kansa ya fara yi. Me ya sa tun farko da ya ajiye aikinsa ya dawo Nigeria bai nemi rabuwa da

Cassandra ba sai yanzu da abubuwa suka kwaSe masa?.

Dalilin hakan kuwa TSORO ne. Shi Win MATSORACI ne.

TSORO ne ya banbanta shi da Jamal.

A yayinda ya bari tsoro ya saka shi auren Cassandra. Tsoron ne kuma ya hana shi rabuwa da ita har

yanzu. Yana tsoron mai zai faru idan ya rabu da ita ba tareda ya shirya komai na rabuwar ba.

"Ya sani da Jamal ne da tuni ya jima da rabuwa da Cassandra, kuma ya cigaba da ri™on Wansa ba tareda"

tsoron komai ba.

"A halin yanzu ba zai iya rasa mutane uku da suke da mahimmanci a rayuwarsa ba. Ziyada, Junior da"

kuma Hajiya. Zai fara da Ziyada. Zai sake ro™onta ta bashi dama ko zai samu sassaucin ™uncin da

zuciyarsa ke ciki.

***

Tea take sha tana duba wayarta lokacin da ya shigo Wakin.

Tsayawa ya yi bai yi magana ba. Ta Wago ta kalleshi. Da alama tafiya zai yi dan har da Wan jakarsa a hannu.

Idanunsa ta kalla ta ga yadda suka yi rami. Cikin Wan sakannin da ta yi tana kallon fiskarsa kafin ta kauda

kai har wani tsufa ta ga ya mata. Yanayin Idanunsa kaWai manuni ne na irin damuwar da ke cinsa.

"""Zan wuce Abuja"" ya furta mata a hankali. Yadda ta yi halin ko in kula da shi ya nuna masa bata san"

abinda yake faruwa ba.

"""Cassandra ta tafi da Muhammad"" ya mata ™arin bayani."

Sai a lokacin ta Waga ido ta kalleshi. Tiririn shayin da ta gama kurSa ya saka mata zufa a saman bakinta.

"""Allah ya kiyaye hanya"" ta faWa a hankali sannan ta sake kurSan tea Win."

"""Idan na je zan iya jimawa saboda zan shigar da ™ara a bani full custody Winsa"""

"""Allah ya bada sa'a"""

Yadda take masa magana WaWWaya-WaWWaya cikin halin ko in kula ne ya breaking Winsa. Already

maganganun Hajiya sun riga sun karya masa zuciya.

"Ba zai iya tafiya a haka tana Waure masa fiska ba. Koda ba zata yafe masa a yanzu ba, gara ya warware"

mata iya gaskiyarsa

Ajiye jakarsa ya yi ya ™araso inda ta ke. Ta yi saurin juyawa tana kurSan shayin da sauri har yana ™ona

mata harshe.

"Kamo hannunta Waya ya yi ya Waura akan ™irjinsa ya ce ""ban san yaushe kika shiga nan ba""."

Ta ™ura masa idanunta yayinda bugun ™irjinta yake ™aruwa.

"""Kin jima da samun masauki a zuciyata, Zeeyadah. Barin faWa miki wani abu yau, da baki amince da deal"

"Wina ba, da zan sake nemo wata hanyar da zan samu damar aurenki...kin san saboda me???"""

Shiru ta yi masa hawaye na taruwa a idanunta.

"""Saboda INA SON KI, Zeeyadah. I Love You so much, Sunshine"""

Šago fiskarta ya yi yana so ta kalli ™wayar idanunsa ta ga gaskiyar da yake faWa mata.

"Hawaye ne suka fara zubo mata, ta kai hannu za ta share ya rigata yin hakan."

"""Zan baki lokaci. Nima kuma zan yi abinda ya dace. Wannan karan ba al™awarin ™arya zan miki ba."

"Wannan karan na shirya rabuwa da Cassandra..."""

"""Sai da ta gudu maka da Wanka shine zaka Wau mataki?... ai baka burgeni ba tunda ba komawa zaka yi"

"London Win da zama ku tare a

Please Login or Register in order to submit comment