You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka kaya.

Yaya Aminu ne ya kirani. Wai matarsa ta sauka jiya da dare. Na yiwa uwa da yaron addu'a. Dana ajiye

wayar sai na taso na zo wajen Jalal.

"""YallaSai ya da tashi?"""

"""Matarsa ce ta haihu ita ba za ta kira ba sai shi"""

Hmm! Kishi.

"""A yi ha™uri Captain, sa™on haihuwar kawai ya bayar"""

"""Ke kuma kika dinga jero masa addu'o'i saboda ya ji daWin muryanki ko"""

Na shiga uku.

"""A yi ha™uri, YallaSai"" ya juya ya fita bai ce komai ba. Yana fita na sauke ajiyar zuciya. Dana sani da ban"

"bashi labarin soyayyata da yaya Aminu ba. Ga shi dai yaya Aminun ya yi aure last year, ya auri wata farar Bafulatana a Yola amma duk sadda wani abu ya sa muka yi waya sai ransa ya Saci. Gaskiya kishin maza babu kyau."

"Bai dawo gidan ba sai dare. Allah ya taimakeni da ya shigo sai na ga ya Wan sauko, dan haka sai na buge"

"da yi masa taWin Zahra, ai kuwa sai gashi har da dariya. Yana son Zahra so bana wasa ba. Bana jin yana yiwa Junior son da yake mata. Itama yarinyar 'yar gaban goshin Daddy ce, komai Daddynta."

Da muka kwanta ban ta™alo shi bama shi ya ta™aloni na kuwa saki jiki na fara karSan sunnar Aure.

***

Captain yana tsaye jikin madubi yana saka links Win rigarsa na zuba masa idanu ina kallon yadda yake

"komai cikin nitsuwa. Wani murmushi ne ya ™wace mini ba tareda na shirya ba. Mijina kenan fa, farincikina, uban 'ya'yana, Abokina, Business Partner Wina. Saboda ina tare da shi babu wata matsala da zata tunkaroni a rayuwata ko business Wina da ba zan iya warwarewa ba."

"""Ka yi kyau"" na furta lokacin dana mi™e na tako inda ya ke. Juyowa ya yi yana kallona hannunsa Wauke da"

hula.

"""Na yi kyau ko?"" Ya faWa zai saka hular na karSe hular daga hannunsa na Wan yi Wagel na saka masa na ce"

"""ka yi kyau sosai"""

"Ya zagayeni da hannunsa ya ce ""wannan dana ke samun Compliment da safen nan so ake a hanani"

"tafiyar nan ko"""

"""Kaima ka san idan son raina ne ba za ka yi tafiyar nan ba"""

Hutu aka yi Jalal zai raka Muhammad London wajen Mamanshi. Yaron ba son zuwa yake ba amma

saboda yana cikin tsarin da Kotu ta saka musu dole ne Jalal ya tura shi hutu wajen ta. Tsarin zai ™are ne

idan Muhammad Win ya kai shekara shatakwas. A lokacin ne zai zaSi ya je ko kar ya je wajen Mamansa.

Idan ya je London Win ya ce akwai abinda zai tsaya yi dan haka sai ya yi sati guda kafin ya dawo. Sati

gudan nan yawa ne garesu a wajena. Idan son samu ne duk tafiyar da zai yi kada ya tsallake kwana biyu ya dawo gareni.

Kissing goshina ya yi sannan ya kwantar dani a ™irjinsa. Wani sanyi ne ya ratsa ni. Bani da wani waje da

ya fi mini daWi a duniya sama da kwanciya a jikin Mijina. Ina fata na Wau shekaru masu yawa nan gaba ina kwanciya a jikinsa irin haka.

"""Ka san me?"""

"""Sai kin faWa"""

"""Ina sonka, Mr Jalal Maiya™i"""

"Murmushi ya yi sannan ya ce""Nima ina sonki, MY SUNSHINE"" manna mini kiss ya sake yi a goshi."

"""Dad na shirya"" muka jiyo muryar Muhammad a bakin ™ofa."

"""Gani saukowa"""

Ina jin ™aran gudun yaron a stairs na Wauko wayata na ce barin mana Selfie.

A yadda nake kwance a ™irjinsa na yi mana hoton. Bayan na yi guda uku sannan na ajiye wayar na raka

shi waje.

"""Šan duba mana Hajiya Kaka idan bata yi bacci ba sai na mata sallama"" na shiga Wakin Kaka na sameta"

tana sharSan bacci. Na fito na ce masa tana bacci. A bakin ™ofa na tsaya ina gani ya wuce ya je ya shiga motar wanda tuni Muhammad ya shiga. Bayan motar ta fita daga gidan sai na koma ciki. Kayan wasan Zahra dana gani a falon na tattare na yi sama da su na kai Wakinta na mayar da su cikin sauran kayan wasanta. Tana can wajen Hajiya tana rigimarta.

Komawa na yi Wakina na kalli kaina a madubi. Wata Madam na gani tana kallona. Gaskiya ban ga ta zama

"ba, idan na haihu dole na mayar da hankali kan diet Wina da exercise Gym Winnan dai dana watsar shi zan koma."

Na shafa cikin ina addu'ar Allah ya sa na saukeshi lafiya.

Haka kawai dana zauna sai na ji ina son posting hoton dana Wauka. Hoton ya fito sosai mun yi bala'in

kyau ga shi dukkanmu murmushi muke yi.

"Tunda na auri Jalal da aka ri™a cecekuce akan aurena ana zagina wai ya fini kyau, a'a ba auren soyayya"

"muka yi ba, a'a dan kuWinsa na aureshi bayan na wala™anta Alhaji Nafi'u, ban taSa Waura wani abu gameda mijina a social media ba."

Ko lokacin bikin Janan da muka yi Reception ban Waura hoto ko Waya a shafukana ba. Janan ce ma ta

"Waura hotonmu a Instagram page Winta amma ni ban Waura ba. Na yi hakan ne saboda in Wan kiyaye Aurena daga bakin 'yan social media saboda bakinsu guba ne a gareni. Ina yin food content, ina saka business Wina a social media, amma aurena kam sai dai su yi ta hasashe."

Ban sani ba ko daWi ne ya min yawa ko kuma dai hormones Win ciki ne suke ingizani ban sani ba. Na dai

Waura hotonmu a duka social media pages Wina bayan na rufe fiskar Jalal da emoji Win zuciyad'. Na

rubuta MY HOME a ™asan hoton.

"Daga 2 likes Win dana fara gani a Instagram daga Waurawa haka likes Win suka fara ™aruwa. 10 likes, 74"

"likes, 1050 likes, 3k likes sai ™ara yawa suke, kan kace me cikin ™asa da awa Waya har hoton ya kai 17k likes, ga comments Win mutane rututu. Da gangan na ™i karanta comments Win saboda na san raina zai iya Saci. Ban damu da comments Winsu ba, ko su faWi alkhairi ko su faWi sharri."

Abinda na ke so su shaida shine MIJINA shine GIDANA.

JALAL is my HOME

Ba a babin makwanci ko ciyarwa ko shayarwa ba.

Ina nufin idan za a yi ya™in duniya na uku.

Idan za mu tashi bamu da komai gobe.

"Idan wata rigima ko matsala za ta tunkaromu, ina da tabbacin idan ina tare da shi, to ina GIDA!"

Jalal is HOME.

NOW and FOREVER.

Alhamdulillahi bisa wannan ni'imar...

THE END

Thank you for loving Jay and Zeey

Thank you for buying CHEF ZEEY.

"Allah Ubangiji ya saka muku Albarka a naku kasuwancin, Amin."

Whatsapp: 08137311900

AudioBooks on YouTube @ Marubuciya Azizat Hamza Channel

©AzizatHamza2025


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment