You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shirin yi da kuma"

abinda ta ke tunanin yi.

"Yanzu ta ina za a fara serving tuwo, da Wanwake da Fate a babban waje irin wannan?."

Target audience Winsa ba mutanen ghetto bane. Fahimtar hakan da Hajiya bata yi bane ya sa take

™o™arin haWa shi da local Chef Winnan.

˜o™arin cigaba da aiki ya yi a Laptop Winsa amma maganganun Ziyada sai ringing suke masa a kunne. Ga

kuma fiskarta da ya ke masa gizau yadda ta ke masifa. Yadda movement Win lips Winta suke bala'in

Waukan hankali.

"Lips Winta an yi su dan kiss ne, ba dan masifa ba. Yai saurin girgiza kai da wannan banzan tunanin da ya"

zo masa.

Gaskiya daWewar da ya yi babu mace ya fara taSa shi. Ta ya masifar wannan yarinya zai zama masa so

attractive.

Thank God ma ba zai sake ganinta ba. Babu wata ala™a da za ta sake haWa su dan haka wani banzan

tunani ma akanta ba zai sake shigo masa ba.

Bai jima a wajen ba ya fara tattare Laptop Winsa zai tafi gida dan aikin da ya ke son yi a wajen ma ya fara

gagararsa. Zai koma inda fiskarta ba zai ri™a yi masa gizau ba. Yana cikin tattare wajen sai ya ga takarda a ™asa gefen inda Ziyada ta tashi. Ya tsugunna ya sa hannu ya Wau takardar ya fara karantawa. CV Winta ne da ke Wauke da wajajen da ta yi aiki da kuma experience Winta a harkar girki.

Bayan ya gama karanta takardar sai ya sa a jaka kusa da Laptop Winsa.

"Duk da dai Local Chef ce, experience Win da ta ke da shi yana da matu™ar amfani. Idan har ta buWe"

restaurant kamar yadda ta ke i™irari to tana da experience da za ta iya running wajen.

Har ya wuce gida tunanin Ziyada ne fal a ransa.

***

ZEEY

"Tun dana fito daga JK Plaza nake tafiya raina a Sace, na kama tafiya cikin sauri fuuuu kamar zan tashi"

"sama. Sai da na yi tafiya mai nisa ban tsare Keke ba, masu Keke na mini horn amma ban tsai da su ba. Wani zafi nake ji a zuciyata, duk dana amayar da abinda ke raina sai nake ganin kamar akwai abinda na manta ban faWa ba. Inata sake playing abun dana faWa masa a raina amma zuciyata bata huce ba."

Ina ta sauri har sai da na kusa faWawa kwalbet ban sani ba saboda hankalina ya yi gaba. Wannan ya sa

dana kai junction sai na tsaya na tari Keke na wuce gida.

"Šan iska, mai keken ma wai in zai shiga dani har cikin layi sai na ™ara masa kuWi. Da a hayyacina nake sai"

mun yi rikici amma na ce masa mu je kawai.

Muna isa ™ofar gidanmu tun ma kafin na fito daga keke na hango motar Alhaji Nafi'u.

Na fito na mi™awa mai keke kuWi ina mamakin me ya kawo wannan Wan iskan gidanmu da rana tsaka.

Yana zaune akan tabarma ya baza rumbun jikinsa yana shan lemo da Ayaba a cikin ba™in leda. Ga Baffa

"Lawalli a gefe yana ta zuba masa dariya. Na ja tsaki ina faWin ""Šan Maula kawai"""

Ga shi dai Alhaji Nafi'u ™anin bayansa ne amma sai wani ladabin ™arya yake ta masa saboda kwaWayi.

"Na yi kaman ban gan su ba zan wuce na ji ya ce ""Sayyada, kin dawo?, Dama kuwa yanzu Baffanki yake"

"cewa zai kiraki"""

Na juyo da sauri na watsa masa harara. Tun dana blocking numbarsa bayan na tura masa kuWinsa na

manta da shi. Ya taSa kirana da wata sabuwar number amma ina jin muryarsa na yi blocking numbar.

"""Ziyada ba ki ganmu zaune bane. Ba magana ake miki ba"" Baffa Lawalli ya faWa da masifa."

"""Ina wuninku"" na gaishe su ina danne Sacin ran da ya taso mini. As if ban kwaso haushi daga wajen Jalal"

"ba, wannan ™aton banzan shima zai Sata mini rai. Ni kam ana soyayyar dole ne?."

"""Ki shiga gida ki ajiye jaka ki fito ku gaisa da Alhaji Nafi'u, dama ke yake jira"""

Ni yake jira kamar yaya?. Miye haWina da shi?. Na riga na sallameshi ba sau Waya ba ba sau biyu ba. Yo ko

ni 'yar iska ce ai ba zan zaSi yin iskanci da tujejen ba™in mutum kamar Alhaji Nafi'u ba. Allah na tuba yadda ya ke da uban jiki da tumbin nan ™aramin aba gareshi.

Ni Winma ba™a ce amma gaskiya ba™in Alhaji Nafi'u har da datti. Gashi da kuWi dai-dai gwargwado amma

"turare wannan ba zai saka ba kullum sai ka ji warin gumi a jikinsa. Lokacin da muke Wan mutunci irin wai dan na ankarar da shi Winnan har da kyautan turare na yi masa wani lokaci amma still kamar an masa farra™u da saka turare, baya sakawa. Maganar turare ya sa na tuno da ™anshin turaren Jalal. Kamar ma dai ™anshinsa biyoni ya yi har gida, dan har yanzu ina jin ™anshin."

Har na shiga gida zuciyata kamar za ta yi bindiga saboda haushin ganin Alhaji Nafi'u da Baffa Lawalli. Da

gani ba abin alheri suke kitsawa ba. Wato dan na rufe masa duk wata dama da zai sameni shine ya biyo ta wajen Baffana.

Ganin ™ofar Wakinmu da kwaWo ya sa na doka ™atuwar tsaki na fita. Ashe ma Kaka bata dawo ba. Na fita

na je na karSo key na dawo na buWe Wakin. Ina shiga Waki na cillar da file Wina saman gado na cire Jilbab

Wina na yar a ™asa. Zama na yi na jingina bayana da gado ina huci.

Yau dai ina ga akwai wanda ya jefeni da Sacin rai ne. In ba haka ba ta ya zan fita daga gida na kwaso

Sacin rai a inda na je sannan na dawo gida na sake tarar da wani ba™in cikin.

Zamana na yi a Waki na manta da batun Alhaji Nafi'u har sai da Baffa Lawalli da kansa ya shigo yana

kirana sai masifa yake wai na barsu zaune.

"""Ki wuce ki samu Alhaji Nafi'u yana jiranki a waje"""

"""Ni fa Baba gaskiya, gaskiya, ka fita harkarsa dan ni babu wata ala™a tsakaninmu yanzu. Na sallameshi"

"tun da daWewa"""

"""Ki ji min Ja'ira. Yanzu mutum mai arzi™i da kamala yana binki kina cewa ba kya so"""

"""Gaskiya Baba wannan ne na ™arshe da zan fita saboda Alhaji Nafi'u ya zo gidan nan, bana son irin"

"wannan abin"""

Na yi maganar kaman zan yi kuka ina wawuran Jilbab Wina da ke ™asa.

""" iskancin banza, mu muka kawo shi gidan nan ne. Ba ta dalilinki muka san shi ba. Za ki ce yanzu ba kya"

"son shi bayan ya jima yana kashe miki kuWi"""

Na ja na tsaya idanuna suka ciko da hawaye. Ban taSa tambayar Alhaji Nafi'u kuWi ba. Duk abinda ya yi

mini ban saka shi ba. Lokacin dana fahimci shi mutum ne da zai yi maka alkhairi kuma ya zo yana maka gori sai na dena karSan komai a wajensa gaba Waya. Tun da abubuwa suka fara dai-daita mini shima karan kansa ya fahimci bana bu™atar Wan chanji daya ke turo mini.

"""Baba amma..."" na buWe baki zan yi magana sai na kasa."

Da ce masa zan yi da ya san sau nawa Alhaji Nafi'u mai kamalan ke cewa na taSa masa gabansa ko kuma

na bari yai wasa dani na rage zafi a cikin mota da ba zai ce na wuce na je na same shi yanzu ba. Da ya san cewa Alhaji Nafi'u ya taSa yun™urin kaini hotel dan na bashi kaina da ba zai zauna da shi yana wage masa ha™ora ba.

"Sai dai, da wani bakin zan fara faWa masa wannan maganar?. Ina da zafi, bana juran wala™anci, amma"

Wan kunyar dana ke da shi ba zai bari na bayyana wa yayan Babana wannan maganar ba.

"A zaure na goge hawayen da ya zubo min, na Wan goggoge fiskata da hannun hijabina sannan na fita."

Babu kowa akan tabarma dan haka sai na yi wajen da ya parking motarsa.

Ina buWe ™ofar gaba na shiga na zauna na bar ™ofar a buWe na Wan saka ™afa dan kar ma ta rufu da kanta.

"""Sayyada kenan"" Alhaji Nafi'u ya faWa yana wani munafukin murmushi."

Allah Sarki ni. Wai mutumin da ke ir™irarin yana sona shine ba zai iya furta sunana ba. To ko sunan

Chinese gareni ai dole ya koyi faWansa. Lokacin da muke tare tun ina gyara masa har na lura iskancinsa ne kawai ba zai faWa Winba wai Sayyada ya fi masa sau™in faWa.

"""To ya kike?"""

"""Alhaji Nafi'u me ka zo yi gidanmu?"" Na tambaya ina kallon ™wayar idanunsa."

"""A'a. Da wuri haka, ai kya tsaya mu gaisa tukunna ko"""

"""Mu gaisa fa kace. Ka san babu wannan a tsakaninmu yanzu. Na riga na sallameka. Na tura maka kuWin"

"da Baffa Lawalli ya karSa, ka rabu dani Dan Allah"""

Dariya ya saka na yi saurin kau da fiskata gefe dan kar ya feza min yawu.

"""Kina tunanin dubu hamsin kawai nake bin Baffanki?. Idan ma baki sani ba to ki sani, yanzu haka abinda"

"nake bin Malam Lawal da Wayan Baffanki siririn nan zai fi dubu Wari biyar"""

Baffana siriri shine Baffa Zakari. Ya Subhanallhi! Naira Dubu Wari biyar ta yaya? Na zaro ido.

"""Wannan ina nufin kuWaWen da suka karSa a bashi fa kenan ba wai wanda na basu kyauta ba. Idan za a"

"haWa da lissafin kuWin dana basu sadaka zai iya haura Miliyan guda"" yai maganar yana kallona"

Na yi shiru ina Salati a zuciyata. A yaushe Win mutanen nan suka karSi ma™udan kuWi a wajensa haka?.

"Tabbas ba zai yi ™arya ba dan shi mutum ne da duk abinda zai maka sai ya saka a lissafi. Ba zan manta ba,"

"lokacin da ya fara kawo min kyauta, kayan Sallah ne Abaya da wata Atamfa."

"""Kin ga Abayar nan dubu talatin da biyu ake siyar da ita. Wannan Atamfar kuma ko ina kika shiga ba za a"

"siyar miki ™asa da dubu shatakwas ba. Ke kaWai Sayyada na kashe miki dubu hamsin. Kar ki damu ko nawa ne zan iya kashewa dominki"""

Dai dai da tsire idan ya siya sai ya faWi na nawa ya kawo min. Irin wannan lissafin da gorin ya sa na

™yamaci kyautarsa tun a baya.

"Dan haka idan ya ce su biyun sun karSi kuWin da ya kai Naira dubu Wari biyar, to ba ™arya bane."

"""Kin san na jima ina sonki. Ni har yanzu ban ha™ura da ke ba. Ina son ki kuma aurenki zan yi. Mutum"

"yana da mace irinki a gida ai ba zai sake duba wata mace a waje ba."""

Šan iska dai baya ™oshi. Ko irina goma zai samu ni na sani ba zai taSa ha™ura ba.

"Ya wani lan™wasa murya ya ce ""kin ga halittar ™irjinkin nan, sai na kwana ina tsotsansu ban gaji ba."

"Sayyada ke fa ba ki san baiwar halitta da Allah ya miki ba. Kullum na ganki sai na tafi gida da ji™a™™en wando. Na jima ina marmarin taSasu na ji laushinsu amma kin ™i bani dama. Ke gaki 'yar Jami'a babbar yarinya amma sam kamar baki waye ba"""

Dama na san kwanan zancen. Sha'awata ke cinsa ba wai sona yake ba. And duk tsawon lokacin nan

"alkhairinsa gareni trap ne ya Wana dan na dogara da shi har ya samu kaina. Sai Allah ya sa ban dogara da shi Win ba, nima ina da abin yi kuma ina samun rufin asiri."

"Šaure fiskata na yi ban bari ya gane na firgita da abinda ya faWa ba na ce ""Look Alhaji Nafi'u, ni ba ni na"

"karSi aron kuWi a wajenka ba. Lokacin da kake basu kuWin bana wajen dan haka sai ka je ka wanye da su,"

"can ku ™arata. Idan ma Police station za ka kaisu dan su fito maka da kuWi to Bismillah. Ni bai shafeni ba"""

Wani dariyan ya sake yi wannan karan na Wan tsorata da dariyarsa amma na dake ina addu'ar neman

tsari daga sharrinsa a zuciyata.

"Duk macen da matsin rayuwa ya sa ta faWa hannun mutum irin Alhaji Nafi'u, to ta shiga uku. Ni ga shi"

"daga taimako Waya, sai ga shi ya shigo rayuwata ya zame min jaraba."

"""Ki kwantar da hankalinki Sayyada, Baffanki ya yi mini al™awarin a satin nan idan suka yi magana da"

"sauran iyayenki za su bani aurenki"""

"""Aurena kuma? Kana Hauka ne?"" Na daka masa tsawa ko girmansa ban tuna ba. Yo dama girmansa ya"

jima da zubewa tun lokacin da ya nuna mini shi Wan iskan gari ne.

"""Ba hauka bane, gaskiyar magana kenan. Dan haka ki kwantar da kai mu fahimci juna tun yanzu. Ni dama"

"Sayyada kin sani na jima ina son ki, ke ce dai kike nuna min ™iyayya"""

A take a lokacin na yiwa kaina al™awarin zan auri kowaye amma banda Alhaji Nafi'u. Ko sama da ™asa za

su haWu ba zan taSa aurensa ba.

"Kallonsa na yi cike da ™yamarsa na ce ""sunana ZIYADA ba Sayyada ba, Waya kenan. Ka sa a ranka ba zan"

"taSa aurenka ba, biyu kenan. Na ™arshe shine ka sake sawa a ranka ZIYADA ba za ta taSa aurenka ba"""

Daga haka na fito daga motar na bugo masa ™ofar bauuuu...

CHAPTER FOURTEEN

ZEEY

Ina cikin kuka Kaka ta shigo Waki. Tana ganina a haka ta ajiye jakar Islamiyyarta ta rungumeni tana

tambayata me ya faru.

"""Wa ya taSa min ke Ziyadatu? Me ya same ki?"""

˜an™ameta na yi na cigaba da sheshshe™ar kuka.

"""To yi shiru, ya isa. FaWa mini wa ya taSa ki? Wa ya Sata miki rai?"""

Sai dana sha kuka mai isata kafin da kaina na yi shiru ina ajiyar zuciya. A irin waWannan moments Win

nake jin zafin maraicina. Da Babana na da rai na tabbata Alhaji Nafi'u bai isa ya ce zai aureni ba. Kai ba lallai na haWu da Alhaji Nafi'un bama balle na bashi dama ya shiga rayuwata.

Babana Direba ne. Amma duk da haka shi mutum ne mai wadatar zuci. Ai duk wanda ya Wauko halin

"Kaka kam, dole ma ya zama mai wadatar zuci."

"Kaka ta ce, Babana ya yiwa 'yan'uwansa hidima ba kaWan ba lokacin da ya ke raye. Su kansu 'yan'uwan"

"nasa idan suna faWin halayensa, za ka ji suna ambatarsa da shi mutum ne mai yawan kyauta da tausayi."

"Memories dana ke da shi na mahaifina ba su da yawa. Ya rasu a lokacin da ban yi wayo sosai ba, I think"

"ina shekara bakwai ya rasu, kai! kamar takwas ne. Allah Sarki! Har na fara mantawa da lissafin. Da, na kan tuna abubuwa dayawa akansa. Yadda ya ke kawo mini tsaraba duk lokacin da ya dawo daga tafiya. Yadda ya ke Waukana a wuyansa yai ta jujjuyani har Kaka ta dinga faWa wai ya dena irin wasan nan dani ni mace ce. But, a hankali ina girma, memories Win suna Sacewa. Na san fiskarsa kam, saboda har yanzu akwai hoton aurensu da Ummana da kuma wani hoto da aka yi a bikin autarsu Binta. A kamanni na Wauko yanayin fiskarsa, da ba™insa. Amma a jiki, Ummana na biyo, dan Ummana tana da ™iba gaskiya. Ko a hotunan bikinsu da ™ibanta balle kuma yanzu da girma ya sake buWeta. Daga wajen Ummana na samu"

dirin da mutane ke yabawa. Da na Wauko Sangaren Babana da abin ba zai yi kyau ba. Dan ga su nan

"matansu duka shafel, babu shape."

"Lokacin dana faWawa Kaka abinda Alhaji Nafi'u ya faWa ai tuni ta fara masifa, ta ce Baffa Lawalli bai isa ya"

min auren dole ba. Ta ce min za ta kira shi ta masa magana. Wannan ya sa na Wan ji sanyi kaWan a raina.

Da dare kuwa Baffa Lawalli ya shigo sashenmu sai huhhura hanci yake har da cewa na kawo masa abinci

"kamar ya bamu kuWin gari. Idan ba kwaWayi bama ko bai yi magana ba Kaka za ta ce na kawo masa, dan Kaka da bawa mutane abinci 5&6 ne."

Na wuce Kitchen na Webo masa tuwon Shinkafa da miyan busashshen kuSewa dana mana. Da ke ina jin

"haushinsa nama yanka Waya na saka masa a miyar, kuma sai dana zaSo ™arami sannan na jefa masa, duk"

da kuwa akwai nama sosai a miyar dan har yanzu bamu cinye naman da aka kawo mini ba.

"""Šan bamu waje"" ya faWa da wani gadara lokacin dana zauna can gefe ina son jin maganar da za su yi."

Na ja tsaki a raina na Wau hijabi na fita. Sashen Baffa Mamman na wuce dan ba laifi muna Wan Wasawa

"da matarsa Anty Hafsah. Shi kaWai ne yai gini a cikin gidan, duk sauran ginin gado ne suke zaune a ciki."

Šakuna uku Baffa Mamman ya gina da falo da kitchen a filin da aka bashi.

Da sallama na shiga falon na samu Anty Hafsah da yaranta biyu suna cin abinci suna kallo.

"""A'ah! Yau Chef tamu ta gargajiya ne a gidana"""

"""Anty Hafsah, Barka da dare"""

"""Barka da dare, Ziyada. Ya aka ji da hidimar biki kuma"""

"""Lafiya, Anty"""

"""Mun gode fa. Šazu da rana na ga sa™o"""

Da rana bayan na gama kuka ne na zauna na rabawa 'yan gidan chinchin Win biki na aika musu.

"""Ki yi ha™uri ba yawa ma. Kin san jama'ar gidan namu yawa garesu. Idan ban bayar ba kuma zan shiga"

"magana"""

"""Ashe kin sani. Na zubo miki abinci ne?"""

Na girgiza mata kai na ce a ™oshe nake. Zama na yi a kujerar one sitter na kanainaye jikina na kunna data

"na shiga Instagram ina son Wauke hankalina daga abubuwan da suka faru yau. Amma dik yadda na ke ™o™arin basar da maganar Alhaji Nafi'u, sai ™ara ringing yake mini a kunne. Ni yanzu abinda ya faru tsakanina da Jalal ma na ajiye shi gefe, bata shi nake ba. In Allah ya yarda ma babu abinda zai sake haWani da shi. Tunda ya ce baya son idea Wina, shikenan ya je ya yi duk abinda ya ke so. kuWinsa ne, restaurant Winsa ne ba nawa ba. Nima idan Allah ya buWa min zan buWe nawa restaurant Win, na Wabbakar da abinda na ke so a wajen."

Za ku ga na damu da maganar buWe restaurant. Ni kaWai na san inda ke mini ciwo. Na farko dama ina da

"sha'awar buWe wajen cin abinci tun lokacin da Kaka ta dena sana'ar Tuwo. Na biyu kuma, ba zan taSa dogara da food content ba, yanzu ina tashe a harkar ban san yaushe taurarona zai dishe ba, musamman saboda content Wina na gargajiya ne ba kowa ke so ba."

Na uku kuma ina son sana'ar ne saboda na san idan ta karSi mutum akwai samu a harkar. Na yi aiki a

restaurant kuma na san ya harkar ta ke idan mutum na samun ciniki. Da wannan sana'ar na ke so na cigaba da gina kaina na kuma inganta rayuwar Kakata. Ta bautu wa sana'ar siyar da abinci amma daga ™arshe bata mori sana'ar ba. Kishiya da 'ya'yan Kishiya su suka hanata moran sana'ar.

"Lokacin da Baaba Tabawa kishiyar Kaka ke raye, tun ma kafin mijinsu ya rasu. Kaka bata isa ta tara kuWi"

ta ce za ta yiwa kanta wani abun kirki da kuWin ba. Akwai lokacin da ta tara kuWin Hajji da sana'ar Tuwo Winnan amma da Baaba Tabawa ta tada fitina ™arshe sai mijinsu ya ce Kaka ba za ta je ba. Kun san a da yardar miji shine sama da komai. ˜arshe kuWin da ta tara na tafiya Hajjin salwancewa ya yi.

"Lokacin da Kakanmu ya fara jinya, duk da kuWin Kaka aka yi jinyar. Bayan rasuwarsa, Baaba Tabawa da"

'ya'yanta suka kwashe kusan komai na gado. Gidan Kakana babban gidane da kuma fili amma da aka tashi sai aka bawa Kaka wani Wan gefe inda muke yanzu kenan wai nan ne rabonta. Bata yi ™orafi ba ta dawo wajen da zama bayan ™urar rabon gado ya lafa.

�angaren Babana ma Baffa Lawalli ne ya cinye bayan rasuwarsa. Yanzu haka Amaryarsa ya saka a wajen.

"Saboda wannan rikicin ya sa nake so na inganta rayuwar Kakata. Kai, barin faWa muku. Yadda na ke ji da"

"Kakata ko, ko Ummana data haifeni bana jinta kamar haka. Kafin na yiwa Ummana abu Waya, sai na yiwa Kaka biyunsa. Na san matsayin Uwa ya fi na Kaka, amma gaskiya saboda sha™uwar da muka yi na fi ji da Kaka Altine sama da Ummana."

Bayan rasuwar Baaba Tabawa. Kaka ta cigaba da yiwa 'yan gidan hidima kamar ita ta haifesu. Amma

"jarabar aron kuWi, da 'ya'yansu da suke mata sata, sai da suka kassara mata sana'ar."

"A hakan bata dena ba, har sai da jinya ya kada ita. Lokaci guda daga faWuwa tana tu™a tuwo da aka kaita"

"Asibiti sai ga result kala-kala na ciwukan da ta ke fama da shi. Ga matsalar ido, har yanzu ido Waya baya gani sosai, Wayan ma dai gashi nan-gashi nan ne. Ga hawan jini, ga ciwon baya da ciwon ™afa. A lokacin fa har cewa suka yi akwai Chronic typhoid da kuma ulcer a jikinta. Abin mamaki, tana sana'ar sayar da abinci amma wai tana fama da matsalar ulcer."

Jinyar farko sai da Kaka ta yi wata biyu a Asibiti kafin aka sallameta. A wannan jinyar Wan kuWin da ta ke

"tarawa ya ™are. Nima a lokacin duk abinda na ke samu jinyar Kaka yake tafiya. Na san za ku ce ina su Baffa Lawalli suke a lokacin. Hmm! Yadda Baaba Tabawa ta nuna musu Kaka ba uwarsu bace haka suka Wauketa har a lokacin da take cikin tsananin bu™atar tallafawarsu. Umma Hadiza dai tana zuwa duba Kaka kusan kullum har na sati biyu, kafin daga baya ta rage zuwa. Ban ji haushin Wage ™afarta ba saboda na san mijinta bahagon mutum ne mai ba™ar a™ida, ba mamaki shi ya hanata zuwa."

"Umman Fada ba komai ta ke da shi ba, itama na fama da nata Talaucin a gidanta."

Baffa Mamman na bada abinda bai taka kara ya karya ba. Shima Baffan Katsina idan ya bushi iska yana

turo kuWi.

Daga ™arshe babu wani mai halin da zai iya Waukan nauyin jinyar Kaka. KuWin da ta tara shekara da

shekaru da su aka ci ™arfin jinyar har Allah ya tashi kafaWarta.

˜anwar Kaka da muke kira Baaba Murja ita ce ta zauna da Kaka throughout jinyar. Ni kuma kullum ina

"jigilar Makaranta, ina jigilar Asibiti, ina jigilar aikace-aikace."

A irin wannan yanayi na haWu da Alhaji Nafi'u a wajen ATM har ya taimaka min lokacin da ATM ya haWiyi

"katina. Ga shi yanzu ya bijiro da wata maganar da ba zai taSa yiwuwa ba. Alhaji Nafi'u ba mijin aure bane. Ba dan shekarunsa za su iya kaiwa hamsin ba, ba dan yana da mata ba, ba dan yana da ™iba ba (duk da ni bana son ™aton namiji). Ba dan kuma halinsa na gori ba. Ba zan aure shi bane saboda sha'awata yake, ba sona ba. Idan har ya aureni ya samu abinda ya ke so, to shikenan idonsa zai kauce a kaina ya fara neman wata. Wannan, ba irin auren dana ke son yi bane..."

***

JAYKAY

˜arfe tara na dare yana Waki yana zaune akan gado ya saka Laptop a gaba yana rubuta wani email sai

wayarsa ta fara ringing. Šan le™a wayar ya yi ya ga sunan C. Maria. Tsaki ya ja a fili. Sai yau ta ga daman

kiransa kenan. Kusan sati guda kenan ko waya ba su yi ba.

Šazu da yamma Junior ke masa ™orafin ya kamata Mom Winsa ta zo birthday Winsa da za a yi ranan

"Alhamis mai zuwa. Ha™uri ya bashi dan ya san ko ya faWawa Cassy ta zo, ba zuwa za ta yi ba. Aikinta ya fi mata komai mahimmanci."

"""J. Lovvvvve!"" Ta faWa da muryan maye."

"""Fuckkk Nigeria, I've being trying to call you for hourrrrrs"""

"""Cassandra

Please Login or Register in order to submit comment