You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke bai ce da ni komai ba.

"Sai can ya ce mini ""Yawwa! Ziyada ban sani ba ko akwai kuWi a wajenki ki bani aron dubu hamsin"""

Na zaro ido cike da mamakin yadda ya kira dubu hamsin Win kaman ya taSa bani ajiya.

"""Baba, gaskiya babu kuWi a wajena. Kwanaki na biya kuWin Makaranta da su"""

"""To, to, ko dubu ishirin ba za a samu ba?"""

"Na haWe fiska na ce ""babu"""

"""To shikenan, je ki"""

Na mi™e ina lissafin ma™udan kuWaWen da na ke binsa bashi har yau babu ranan biya. Ni Ziyada na sake

bashi aron dubu hamsin. Allah ya kiyaye...

"Har zan fita sai ya ce "" Wancan Alhajin da ya ke zuwa wajenki har yanzu kuna tare ko?"""

"""Baba na sallameshi"" na faWa da Wan ™arfi dan bana son ya sa rai da Alhaji Nafi'u."

"""Kin Sallameshi saboda me?. Mutumin arzi™i Azumin da ta wuce rabin buhun sugar da katan Win taliya fa"

"ya kawo mana"""

"""Ni dai na sallameshi"" na sake jaddada masa dan kar ya sa rai da kwaWayin kuWin Alhaji Nafi'u"

Bai ce min komai ba nima na fita.

Ina zuwa sashenmu na cire Hijabi na hau gado na kwanta na shiga CapCut na fara editing videon da zan

Waura gobe. Saboda school yawanci a weekend na ke yin shooting Win video idan na samu time sai na editing na Waura. Sau biyu a sati na ke Waura recipe amma wani lokaci na kan Wan Waura random vidoes na wasu abubuwan ko kuma idan Kaka tana wani abu sai na Wauketa na Waura.

Letter *Z* ne ya popping a saman notification bar Wina. Ina ganin Z zuciyata yai wani ras. Ko ban duba

"wa ya turo min ba, na san mutum Waya ne ke chatting Wina da suna haka."

Ban buWe ba na cigaba da editing da nake yi sai ga wani sa™on ya shigo

"""Na san ba ki yi bacci ba, zan kira, plzzz ki Wauka"""

Ko gama processing kalmomin ban yi ba kiransa ya shigo. Na bi screen Win da kallo har yau ban chanja

sunan dana saving contact Winsa da shi ba *My Ameend'*

Sai da ta kusa yankewa sannan na Wauka amma na yi shiru...

***

JAYKAY

A gajiye ya shigo gidan. Today was super hectic. Amma Alhamdulillahi akwai positive response daga

investors Win da suka zo. Idan har sun gama shawara there's possibility sati mai zuwa za su turo Lawyers

Winsu a zo a yi yarjejeniya.

Lokacin da ya shigo gidan main parlour Win babu kowa dan haka sai ya shiga Wakin Hajiya ya sameta tana

"sallar Magariba, bai jirata ba sai ya wuce nasa part Win dan ya yi wanka ya chanja kaya. Da ya fito daga banWaki sai ya buWe closet Winsa zai Wau kaya, tsayawa ya yi cak yana kallon wajen, wasu kayan bacci guda biyu da aka jera kusa da pyjamas Winsa ne ya tuna masa da cewa yana da MATA. Matar da ke wata duniyar bata da niyyar rayuwa da shi a inda ya ke. Shekaransa biyu kenan da dawowa Nigeria permanently da zama. A cikin shekara biyun da yai a Nigeria Cassandra ta zo masa Nigeria ne sau biyu. A shekarar farko ta zo ne lokacin Christmas ta tafi bayan New Year. Kwanaki 15 ta yi a Nigeria kullum sai ta tuna masa da hakan. A shekara na biyu kuma ta masa kwana 10. Wannan shekaran ma ya sani bata da niyyar zuwa sai ™arshen shekara kamar yadda ta saba."

Yana tura mata Wansu Junior London ya je ya mata vacation idan aka yi hutun Makaranta. Yanzu kamma

"kamar yadda bata damu da yaron nasu ba shima yaron ya fara jin daWin Nigeria, bai damu da rashin mahaifiyarsa kusa da shi ba. Idan ba an yi hutu ba baya ma maganar zai je London."

"Wai shikenan, a haka za a cigaba da auren?."

Ba zai iya abandoning Kamfanin da mahaifinsu ya kafa ya koma London ba. Balle ma bashi da wani

"identity yanzu a can. Idan ya je ba™in cikin abinda ya rasa ne zai hana shi sukuni. Gara yana nan Nigeria kusa da Hajiya, kusa da ™anwarsa Waya da ta rage masa. Kusa da 'yan'uwa da abokan arzi™i..."

Wani ba™in comfy shirt mai laushi ya ciro ya saka ya haWa da wata ba™ar wando. Da alwalarsa dama ya

fito saboda idan ya gaida Hajiya sai ya wuce Masallaci ya je ya yi sallar Isha.

Lokacin da ya shiga Wakin Hajiya sai ya samu ta idar da sallah tana jan carbi.

"Ya gaisheta, ta amsa masa sannan ya ce mata zai je ya yi sallar Isha."

"Ta ce da shi ""Muhammad yana Wakinsa sai ka Waukeshi ku tafi tare"". Ya mi™e ba tareda ya ce komai ba ya"

fita.

Šakin Junior ya shiga ya kira yaron suka fito za su je Masallaci tare.

Suna saukowa falo sai ga Janan ta shigo gidan tana ma™ale da waya a kunnenta sai masifa ta ke yi.

"""Ya Jalal Barka da dare"" ta faWa za ta haura sama ya ce mata"

"""Kin je office yau?"""

"""Na je manaaa"" ta faWa sannan ta haura sama tana cigaba da wayarta."

JayKay ya ri™e hannun Wansa Junior suka wuce Masallaci...

CHAPTER THREE

ZEEY

"""Hellloo"" na faWa da muryar bacci. Jiya ban kwanta da wuri ba sai ™arfe Waya da rabi na dare. Bayan"

wayarmu da Yaya Aminu sai dana jima ina sa™e-sa™e kafin na samu na ™arisa editing da nake yi.

"""Sayyada, ™arfe bakwai saura baki tashi a bacci ba"" ai tunda ya ce Sayyada na ji duk wani baccin da ke"

idona ya washe saboda Sacin ran da ya taso mini.

Haba! Sama da shekara Waya kenan amma mayen mutumin nan har yanzu bai iya kiran sunana ba. Idan

"ba zai iya kiran Ziyada ba, to ya kirani da Ziya ko Zeey kamar yadda aka fi kirana da shi mana. amma ya wani kakaSa mani Sayyada, kuma fa a hakan wai so yake ya aureni. Allah ya kiyaye na auri mutumin da ko sunana ba zai iya furtawa ba."

Na haWu da Alhaji Nafi'u ne a bakin ATM wata ranar Asabat ina cikin sauri zan cire kuWi katin ATM Wina

"ya ma™ale. Ga shi ranan Asabat, gashi ba ATM machine Win Bank da nake amfani da shi bane, ga shi ina"

bu™atar kuWi cash da gaggawa zan wuce Asibiti wajen Kaka.

Haka na kama faWin Innalillahi na rasa ya zan yi.

Alhaji Nafi'u da shima ya zo cire kuWi a Waya ATM Winne ya fito ya fara tambayata me ya faru. Na nuna

masa machine Winne ya haWiye min kati kuma ina bu™atar kuWi.

Haka ya shiga kwantar min da hankali yana faWin za a iya resolving matsalar. Muka samu securityn Bank

"Win muka masa bayani, ya ce mana gaskiya sai dai Monday mu dawo. Nan na sake rikicewa. ˜arshe dai Alhaji Nafi'u ne ya bani aron kuWin ya karSi numbata ya kaini har gida daga nan muka wuce Asibiti. Ranan Monday ma sai ga shi ya zo har gida, ya Waukeni muka je Banki aka bani ATM card Wina."

Da zan mayar masa da kuWin sai ya ™i karSa.

Tun daga nan fa Alhaji Nafi'u ya manne min wai shi a dole sona ya ke. Tun day one da ya faWi hakan na ce

"masa bana ra'ayinsa ba zan iya aurensa ba, amma haka ya nace."

Abinda ya sa ma ya fita min aka shine halinsa na burga da son nuna shi wanene. Ba wani kuWi ne da shi

ba amma sai shegen burga da kuma ™arya. Wannan ya sa tun farko-farko na ce masa tafiyarmu ba zai yiwu ba. Amma kullum maganarsa shine ba zai taSa ha™ura da ni ba matu™ar ba aure na yi ba.

Daga nan kuma ya fara cusa kansa wajensu Baffa Lawalli yana musu kyauta. Duk abinda ya musu sai ya

faWa min As if so ya ke na ri™a rubuta list Win alkhairin da ya ke yi musu ta dalilina.

Idan 'yan mutuncina suna kusa na kan fita idan ya zo. Amma tunda muka yi faWan ™arshe da shi sai na

dena fita.

Ina godiya da alkhairin da ya yi mini a baya duk da ma ba ni ke tambayarsa ba ya ke yi. Amma tuni na

ha™ura da alkhairin Alhaji Nafi'u. Shi duk abinda zai maka to haka zai yi ta nanata maka ai ya yi maka kaza da kaza. Kyautarsa kullum tana zuwa da gori ne. Wannan ya sa fir na dena karSan komai daga hannunsa tun ma kafin mu yi faWa.

Tsakanina da Alhaji Nafi'u babu yaudara. Tun ranan farko na ce masa ban amince da tayin soyayyarsa ba.

Haka lokacin da yawan gorinsa ya isheni haka na zage na gaggaya masa maganganu na ce kar ya sake kawo min ko tsinke bana bu™ata. Yai ta bani ha™uri amma ban sake karSan ™wandala daga wajensa ba. Wannan ya sa ya mayar da hankalinsa wajen yiwa su Baffa Lawalli hidima.

"""Sayyada, jiya ina ta kiranki kin ™i ki Wau wayata"""

Šan tashi na yi zaune ina tsaki a raina. What is so hard a kiran suna ZIYADA

"""Alhaji Nafi'u me kake nema a wajena?"""

"""Allah Sarki Gimbiyata, ki yi ha™uri na tashe ki a bacci. Tun jiya na ke son jin zazza™ar muryanki amma kin"

"hanani"""

"Na Sata fuska na ce "" Alhaji idan baka da abin faWa ni zan kashe wayata"""

"""Allah ya huci zuciyarki"""

Chanjin muryarsa ya tabbatar min ya ji haushin abin dana faWa. Ban damu ba tunda na masa kora da baki

na masa kora da hali duka ya ™i ya ha™ura da ni.

"""Dama Baffanki Lawal ne ya kirani jiya ya ce na bashi aron dubu hamsin. To na tura masa kuWin tun jiya"

"na ji shiru har yanzu bai kirani ya ce min ya ga kuWin ba"""

"""Kai! Innalillahi..."" na faWa ina kama kaina. Wani irin zubar da mutunci ne wannan dan Allah. Shikenan"

"'yan'uwan Babana babu abinda suka sani sai kwaWayi, kwaWayi, kwaWayi."

Saboda alkhairin da Alhaji Nafi'u ke musu ya sa na ke Wan Waga masa ™afa ban masa koran wala™anci ba

tuntuni.

Kalmomin rashin arzi™in da Alhaji Nafi'u ya faWa min watannin baya da tayin banzan da ya min ya ci a ce

na yi nesa da shi tun da jimawa amma kwaWayayyun 'yan'uwan Babana suna kashe mini gwiwa.

Shi ya sa nake so na yi kuWi.

Shi ya sa nake so na buWe restaurant Wina.

Shi ya sa nake so na fi ™arfin wala™anci.

"Alhamdulillah yanzu ina samu, amma a lokacin dana ke cikin tsananin fafutukar ganin na gina kaina"

Alhaji Nafi'u ya min gorin da ba zan taSa mantawa da shi a rayuwata ba.

"""Sayyada kin ce ba za ki aureni ba. Ga shi dana Wan ri™e miki hannu sai ki fara masifa. Mi kika Waukeni ne."

"Watana nawa ina zuwa gidanku ina yiwa Baffanunki hidima amma Wan kiss Winnan idan na ce ki min ba za ki min ba. Na san yanzu kin fara samun kuWi kin fi ™arfina, amma kada ki manta abubuwan dana yi miki a baya da wanda na ke yiwa 'yan'uwanki har yanzu..."""

Kalamansa kenan a hirarmu ta ™arshe a cikin motarsa. A ranan muka yi baran-baran na ce masa kar ya

"sake zuwa wajena. Na ce masa ya lissafa duk abin da ya taSa yi min Insha Allahu zan biya shi. Da ya ji haka sai ya fara bani ha™uri wai shi ba haka yake nufi ba. Dama halinsa kenan, sai ya gama min gori sai ya fara bada ha™uri."

"Amma ranan kam ban saurareshi ba. Na shata layi tsakaninmu. Babu Ziyada, babu Alhaji Nafi'u."

"A ranan bayan na shigo gida sai dana sha kuka kamar raina zai fita. Ban faWawa Kaka abinda ya faru ba,"

na yi mata ™aryar maraicin mahaifina ya saka ni kuka saboda abubuwanda su Baffa Lawalli suke min a

gidan.

"Yanzu ma cike da hawaye a idanuna na shiga Bank app Wina na nemo account numbar Alhaji Nafi'u, dake"

na taSa mayar masa wani kuWi da ya taSa turo min na san ba zan rasa account Win a wajen History ba. Transfer Win Dubu hamsin na masa sannan na sharing receipt Win kuWin ta whatsapp Winsa na rubuta

"masa kuWin da ya bawa Baffana ne, amma daga yanzu kada ya sake yiwa wani nawa hidimar kuWi da"

sunana.

KuWin dana tara zan yi hidimar bikin Faty da shi na tura masa.

"Ba nauyin kuWin nake ji ba, Wacin abinda Baffa Lawalli ya yi nake ji."

"Ta ya zai je ya ro™i Alhaji Nafi'u aron kuWi, Fisabilillahi!."

Ina ganin kiran Alhaji Nafi'u na shigowa wayata na yi saurin katse kiran na dannawa numbarsa BLOCK.

Wannan shine karo na ™arshe da zan entertaining Winsa a rayuwata.

Zafin maganganunsa na ranan suka sake dawo min. Wato idan ba zai sameni a mata ba to ya sameni a

karuwarsa. Duk wata hidima da ya taSa mini a baya ba dan Allah bane.

Shi ya sa nake son yin kuWi domin na tsira daga jarrabawar Talauci.

Tun dana taso ina da himmar neman kuWi. Ko shi Alhaji Nafi'un sai dai in ™arya zai min ban taSa

"tambayarsa naira Waya ba, kuma ba da 'yan chanjin da ya ke bani na dogara ba."

Ni fa a kan neman Halal babu aikin da ba zan iya ba. Kafin na zama CHEF ZEEY Win da aka sani yanzu ina

da tarin backstory na irin ayyukan dana yi saboda in samu kuWi.

Lokacin ina Secondary daga JSS 1 har zuwa SS2 na yi aiki a Restaurant har guda biyu. Na yiwa wata mata

Bayarabiya mai abinci aikin wanke-wanke da shara da serving customers. Da ta zo ta bar anguwarmu sai na koma wani fancy Restaurant da ake cewa Zikk's Foods. A nan na yi aiki a kitchen ina musu girki.

Lokacin da Kaka ta dena Tuwo idan aka samu aikin yin Tuwon biki ni na ke zuwa na yi musu. Tukunya ko

namba nawa ne ina tu™awa babu matsala.

Har yanzu part of side business Wina bayan food content ana iya Waukana hire na je na yiwa mutane

abinci.

"Akwai wata Anty Shukura da muka yi aiki da ita a Zikks Foods tana da Catering service yanzu, idan aiki ya"

samu tana kirana. Sannan daga Instagram da wata mata ta mun magana in zo har gida in koya mata abincin gargajiya sai na fara faWawa mutane za a iya hiring Wina koyar da girki.

I'm not lazy. Ni ZIYADA bani da lalacin neman kuWi. I Have To.

Ina neman kuWi ne saboda gudun wala™anci. Saboda gudun mutane kamar Alhaji Nafi'u. Because ko Sule

"Waya namiji ya baka one way or the other sai ya maka gori. KaWan ne masu yi dan Allah, babu gori, babu"

wala™anci...

Raina a Sace na fito daga Waki na Wau buta na yi hanyar banWaki.

Kaka tana Dama koko a wani ™aton bokiti.

"""Kin tashi. Ya ciwon kan?"""

"""Da sau™i"" na shige banWaki. Šazu da Asuba da Kaka ta tasheni sallar Asuba ce mata na yi kaina na ciwo"

shine ta barni. Truly kaina na wani mugun sara mini ne tun jiya da dare da muka gama waya da Yaya Aminu.

Dana fito daga banWaki sai na ja ruwa daga rijiya na cikata butar na fara alwala. Kafin na gama yara har

sun fara shigowa da kofi a hannunsu karSan kunu. Na ja tsaki na shige Waki na shimfiWa sallaya na tada

sallar Asuba. Dana idar na jawo wayata na duba agogo ™arfe 6:52AM.

Allah ka yafe ni.

Ban cika makara sallar Asuba haka ba. Kaka ce alarm Win dake tashina Sallah. Ko babu Alarm ™arfe uku

da rabi na yi tsohuwar nan take tashi ta fara hidima. jikinta ya riga ya saba da tashin dare.

Addu'o'in dana saba na yi daga littafin Hisnul Muslim da ke wayata. Na haWa da Salati da addu'ar RABBI

"INNI LIMA ANZALTA ILAYYA MIN KHAIRIN FA˜IR. Wannan addu'ar ita ce sirrina. Sirrin rage mini ™uncin Talauci. Da wannan addu'ar Food content creation Wina ya fara bun™asa. Tun daga lokacin dana fara ganin ™arfin addu'ar, ban saketa ba har gobe. Da ita da addu'ar HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL sune sirrin samun nasarana."

Na Wan mi™e akan sallaya na shiga Instagram dan na yi replying DM's Wina. Akwai wata mata mai siyar da

spices a Kano da muka fara maganar zan mata talle ban sani ba ko ta ga reply Win dana mata jiya.

Ina cikin danna waya Faty ta chatting Wina ko na yi Assignment Win Dr. Bello na ce mata ban yi ba.

Ba a jima ba Kaka ta ™wala min kira ta ce na zo na juye ruwan wanka na.

Muna da class ™arfe 8AM amma a yadda maganar Alhaji Nafi'u ya Sata mini rai ina ga sai dai na je class

Win ™arfe 10AM kawai...

***

JAYKAY

Idan aka tambayeshi me ya burgeshi gameda Cassandra Maria Morgan shekara shabiyu da suka wuce

"har ya faWa soyayyarta, har kuma ya ji ba zai iya auren wata mace ba sai ita ba zai iya bada"

™wa™w™waran amsa ba.

Ba Love at first sight bane. Taimako ya mata lokacin da ta samu matsala da booking Win jirginta. An yi

cancelling flight Winta saboda matsala ita kuma tana son zuwa ta je ta ga Kakarta da bata da lafiya a Asibiti.

Kuka ta ke yi lokacin da ya zo wucewa wasu authorities suna bata ha™uri. Lokacin yana First Officer wato

"Co-Pilot. Ya gama aikinsa zai fara hutunsa kenan a ranan ya haWu da Cassy a Airport tana ta ihu. Ta bashi tausayi sosai, wannan ya sa ya tsaya ya ji bayaninta ya kuma yi 'yan kiraye-kiraye har ya sama mata wani jirgin na wani Airline Win daban."

Suka gi exchanging contact ta tafi. A Lokacin da ta dawo London sai ta inviting Winsa for Lunch dan ta

masa godiya. Ba su sake haWuwa ba bayan nan amma suna waya lokaci zuwa lokaci.

Bayan 'yan wasu watanni da ya sake samun hutu ya zo London sai suka haWu a gidanta.

"Cassandra tana da kyau sosai. Mahaifiyarta Spanish ce, Mahaifinta ne English. Ta fi kama da matan Spain"

dan haka tana da albarkar ™irji da ya ke iya Waukewa duk wani namiji mai lafiya hankali idan ya samu dama. Maybe ya faWa soyayyarta ne. Maybe kuma kaWaicin da suka samu ne ShaiWan ya samu dama akansa. Maybe sha'awace kawai tsakanin namijin da bai taSa yin hakan ba da kuma macen da ta ke bu™atar su yi hakan.

He felt guilty bayan abinda ya gitta tsakaninsu. Amma a wajen Cassandra dama ta jima tana muradin

hakan saboda tuni ta yi nisa a soyayyar Jalal Maiya™i.

Daga wannan lokaci dai guragurbin soyayyarsu ta samu gindin zama a zukatansu. Shekara biyu bayan

haWuwarsu ya gabatar wa iyayensa cewa zai auri Cassandra. Lokacin Daddynsu yana da rai. Shi bai objecting auren kamar yadda Hajiya ta yi ba.

Nauyin al™awarin da ya yiwa Cassandra ya sa ba zai iya juya mata baya ba. Wannan ya sa ya dage cewa

"ita Win kawai zai aura, ko Hajiya tana so, ko bata so."

Yanzu da ya ke ri™e da waya yana kiran Cassy shine komai ke dawo masa. Shi ba dutse bane. Shekaru uku

"da suka wuce duka a rikice ya ke saboda mutuwar Wan'uwansa, amma yanzu da ya Wan fara sassautawa ransa yana bu™atar kulawa, yana bu™atar nitsuwa da matarsa. Zuwan sau Waya a shekara ba tsari bane da zai iya jura."

Dole ne su yi magana. Dole ne su samu mafita. Musamman yanzu da Hajiya ta fara kawo masa maganar

Saudah. Ba zai iya auren Saudah ba. Ba zai ma iya auren kowacce macce ba matu™ar yana auren Cassandra saboda auren Kotu suka yi. Akwai abubuwa da dama da za su rushe idan ya ce zai yi wani auren ko kuma ya ce zai saki Cassandra.

Har lokacin da wayar ta gama ringing ba a Wauka ba. Jalal yai ajiyar zuciya yana cire wayar daga

kunnensa...

CHAPTER FOUR

ZEEY

"""Sannu kin ji, Sannu Ziyadatu. Wannan jinya duk wata Allah ya kawo miki sau™insa"""

Wani sharp zafi na ji a tsakiyar marata.

Na Wan bo™are bayana kamar mai yin sujjada na tsaya a haka har sai da zafin ya sake ni sannan na gyara

kwanciyata akan pillow ina cigaba da fitar da nishi.

Ya Allah! Duk macen da bata ciwon cikin period ko kuma zuwan period baya bata wahala to ta godewa

Allah.

Tun da Magaribar jiya na ke jin cramps. Na sha pain reliever na Wan samu relieve kaWan na yi bacci ina

addu'ar Allah ya taimakeni kada ciwon ya tashi min tsakar dare. Ai kuwa ™arfe biyun dare na tashi da amai da gudawa. Sai da na amayar da komai na cikina amma still ban dena jin aman ba. Sau uku kenan ina sintirin banWaki. A daren Kaka ta je ta Wauko gas ta kawo na kunna mata dan bata iya kunnawa ba ta Waura min ruwan zafi. Ruwan zafin na Wan sha kaWan na sake watsa wasu maganin da ban san adadinsu ba a baki saboda na samu na ji relief da wuri. Ina da aiki gobe. Akwai kayan da aka kawo min zan yi video

na yi tallensa sannan akwai matar da ta biya ni kuWi 'yarta za ta yi aure tana so na je na koya mata yadda

ake abincin gargajiya.

Ina kwance Kaka ta dinga matsa min marata da ruwan zafi har sai da ruwan ya yi sanyi.

Haka na dinga jujjuyawa ina nishi har Asuba kafin na Wan samu relief har bacci ya Waukeni bayan na sake

shan wasu pain relievers Win dan na amayar da wanda na sha.

Ban tashi ba sai ™arfe tara na safe. ˜arfe goma zan je gidan matar nan ga kuma na yiwa vendor Win da ta

turo min garin kununta al™awarin yau zan mata video na posting.

Ina tashi daga kan gadon idona ya kai kan stain Win dake bedsheet. Nan take raina ya sake Saci. On top

kana fama da ciwon mara da ciwon kwankwaso haka za ka yi ta fama da matsalar stain.

"Yaye zanin gadon na yi na ajiye gefe, idan na gama tsaftace kaina zan dawo ta kansa. Na buWe akwatina"

na Wau pad da pant na wuce banWaki. Ina ciki Kaka ta ™wan™wasa min ta ajiye min ruwan zafi kusan cikin bokiti. Na ji daWin ruwan dan duk da har yanzu ina jin ciwon ciki jikina ya Wan warware sosai bayan na yi wanka da ruwa mai zafi.

Na fito looking clean and ready to face the day. Ina shiga Waki na ga Kaka ta riga ta shimfiWa sabon

bedsheet akan gadon ta Wauke wanda ya yi staining Win.

Anya zan iya surviving a wani wajen idan babu Kaka?

Kaya na saka sannan na kira matar da zan je gidanta na ce ta yi ha™uri zan Wan zo da latti ta expecting

Wina zuwa ™arfe shaWaya ba goma ba kamar yadda muka yi magana.

"""Ziyadatu za ki ci Wumame ne?"" Kaka ta ™walo min kira"

"""a'a"" na faWa ina Wan matsa marata"

In dai ina period to ranaku ukun farko bana iya cin komai. Ko zan ci sai dai na forcing kaina na ci cokali

biyu ko uku haka idan ba haka ba sai amai.

Kwalin garin kunun da aka aiko min na fito da shi na buWe ina tunanin ya za a yi na yi videon. Dana gama

Wan joting abinda zan yi sai na fito da ringlight Wina da ™aramin tripod da kwalin garin kunun.

"""Yanzu za ki yi musu bidiyon?"""

"""Yanzu zan yi, Kaka. Tun jiya ta ke ta min masifa wai ta aiko kaya ban mata video ba"""

Roughly na faWawa Kaka yadda zan yi and she was on board muka fara recording. Kusan shekara uku

"kenan ina food content ta riga ta gane yadda na ke abubuwana, duk da ma dai watanni shida da suka wuce ne na fara Waukan abin seriously har na sayi tripod. Ringlight kuwa dama Yaya Aminu ne ya siya min tun da jimawa."

Bana nuna fuskata shiyasa Waukan videon ya ke min sau™i. Kaka ce ta yi kunun ni kawai ina saita mata

yadda komai zai tafi ne. Muna cikin yi yaran gidanmu suka fara taruwa wai Anty

Please Login or Register in order to submit comment