You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren Cassandra zai iya raguwa a

"zuciyarta idan ya auri wata matar. Sai dai kuma, idan ya ce zai auri wata a yanzu, tabbas zai samu matsala da Cassandra. Auren kotu suka yi, dan haka a dokar ˜asar England da Wales ba shi da damar auren wata mace har sai idan ya rabu da Cassandra."

Rabuwa da Cassandra kuma a daidai wannan gaSar ba abu bane mai sau™i. Sannan babu makawa

Cassandra za ta yi amfani da Junior ta muzguna mishi ta hanyar Waukeshi daga wajensa.

Wani tunanine ya faWo masa. Idan har zai samu wacce zai aura cikin sirri ba tareda Cassandra ta ji labari

"ba, to zai iya samun damar cika umurnin Hajiya."

"Kotu ta Waura musu aure da Cassandra, wacce zai aura kuma aure za su yi na musulunci. Na bayar-Na"

"karSa, cikin sau™i a shafa Fatiha ba tareda an yi wata hayaniya ba. Then a hankali sai ya san yadda zai samu mafita daga auren Cassandra, ta yadda za su rabu kuma a bashi custody na ri™on Wansa."

Saudah ce ta fara zuwa masa lokacin da ya keSe a office shi kaWai bayan sun ™ar™are meeting Winsu

wanda fiye da rabin abinda aka yi a wajen bai sani ba.

Ya girgiza kai saboda Saudah ba za ta taSa yarda ta yi auren da babu hidima ba. Idan kuma har ta amince

"to ba lallai Mommynta da sauran 'yan'uwanta su yarda ba. Ko lokacin da aka shirya aurenta da Jamal, ba"

™aramin biki na gani na faWa aka shirya ba. Sai kuma Allah bai nufa ba.

"Sannan, auren Saudah na nufin ba zai taSa yun™urin rabuwa da ita ba, saboda Hajiya."

Ba shi da aboki a garin nan. Sau tari abokanan Jamal ne ya ke Wan fita da su idan har ya bu™aci shiga

mutane. Bai san ina zai samo budurwa da zai convincing ta yarda ta aure shi ba.

"Haka dai ya wuni a office, rabi aiki, rabi tunani."

Bai dawo gida da wuri ba. Lokacin da ya shigo gidan sai ya samu Hajiya da Junior da Janan suna cin

abincin dare.

Ya gaishe da Hajiya sannan ya wuce sama.

Ganin Cassandra yayi ta ajiye kwalin pizza a kan gado tana aiki a Laptop Winta.

Ya fara ™o™arin cire blazer Winsa ko magana bai mata ba. Sai ta kalleshi ta ce masa wai ya nema mata

"inda ake siyar da pizza mai daWi, wannan da Janan ta kawo mata babu daWi da ™yar ta ci slize Waya."

"""When are you going back?"" Ya tambaya ba tareda ya amsa ™orafinta ba."

"""Missing me already, ain't ya?"" Ta faWa tana wani faWaWa murmushinta."

Juyawa ya yi ya cigaba da cire kayansa bai kulata ba.

˜arfe shaWaya da rabi na dare da ya kwanta bayan ya gama bitar schedules Winsa na gobe sai ya ji

"hannun Cassandra tana ™o™arin wasa da sandar girmansa. Ta cigaba da ta™alarsa har sai da ya biye mata. Duk da ya biye mata Win, amma jikinsa ne kawai ke goganta amma zuciyarsa da nitsuwarsa basa tareda ita. Ita kanta ta ji banbanci tsakanin jiya da yau. Sau Waya da suka yi sai ya lafke with the pretense cewa a gajiye yake, amma deep down sha'awarta ce baya yi."

Wani abu ne ya faWo masa. Akwai wacce ta driving daWewar da ya yi yana gurzan Cassandra jiya. Ba wai

"saboda ya jima bai taSa mace bane. Ba wai saboda ya missing Cassandra bane. Duk da yana hana kansa irin wannan tunanin, amma macen da ta saka shi cikin matsananciyar sha'awa jiya ,ba Cassandra bace."

Da safe da ya je gaida Hajiya bata kawo masa maganar da suka yi jiya ba. Maganar rabon kayan sadaka

da ake duk Azumi ta fara masa. Ya ce mata ta rubuta masa budget idan ya dawo sai ya duba.

"Yau Asabat, ba zai je office ba. JK Plaza zai je ya duba da kuma wasu gidajensu da ake ginawa."

Ranan Monday Cassandra za ta koma London. Idan ta tafi zai samu nitsuwar zama ya nemawa kansa

masalaha ta hanyar binciko yarinyar da ta dace da sharuWWan Hajiya.

˜arfe biyar na yamma ya shigo gidan bayan ya gama duba duka sites Win da ake yi musu aiki.

Dariyar Hajiya ya fara jiyowa tun kafin ya shiga falo.

A tsaye ya samesu. Hajiya na yiwa yarinyar da ke ri™e da ™atuwar leda magana. Kamar tafiya za ta yi

amma maganar Hajiya ya tsaida ita. Kallo Waya ya mata ya ganeta. Ba ya tunanin zai iya mantawa da cute lips Winta nan kusa.

Jalal ya gaishe da Hajiya zai wuce ta ce masa dan Allah ya kai mata Ziyada gida Direbanta baya nan.

"""Hajiya da kin barshi kawai, ina fita zan tsai da keke"" yarinyar ta faWa tana avoiding idanunsa."

"""Haba Ziyadah, ai ba za a yi haka dani ba. Ba zan tasoki daga gida kuma na ce ki kama hanya ke kaWai ba,"

"ga Magariba ta doso"""

"Hajiya ta kalli Jalal ta ce ""please, ka sauke mini ita a gidansu"""

Juyawa ya yi waje ba tareda ya ce komai ba. Yarinyar ta sake yiwa Hajiya godiya sannan ta biyoshi.

"Ta wutsiyar ido ya hangota ta bayansa tana tafiya a hankali, kamar tana tsoron idan ta bishi zai saceta."

"Matsoraciya ce, amma sai baki."

"Idan har akwai wani dalili ma da zai sa ya saceta, to abu Waya ne. Those damn kissable lips."

Shi ya fara shiga motar yayinda ta ja ta tsaya a bakin ™ofar gaba. Jiya Direbansa ya Wauki uzuri ya tafi gida

"wai za a yi bikin ™annensa biyu, dan haka tun jiyan shi yake driving kansa."

Tana tsaye bata buWe ™ofar ba. Ya kalleta ta cikin window sai tura baki ta ke kamar akwai abinda ta ke

faWa. Probably part 2 na masifar ranan ta ke yi.

Ganin bata shigo ba sai ya danna horn wannan ya sa ta yi saurin buWe ™ofar ta shigo.

"Yana gani ta zauna can nesa kusa da window, ko kallon inda yake ta ™i yi."

Ya ja motar suka fita daga compound Win. Sai da suka yi nisa bata yi magana ba sai ya Wan juyo ya

"tambayeta ina ne anguwarsu ""Ghetto"" ta faWa tana kallon cikin idanunsa."

"Ta ™ara da cewa ""ka ajiyeni a titi zan hau Keke na ™arisa gida. Na san mota irin taka bata da ce da"

"anguwar ghetto irin namu ba"""

"Wani Wan faint murmushin gefen baki ya yi. Hasashensa ya yi daidai, Wazu practicing part 2 na masifar da"

za ta masa take. Wato har yanzu bata manta da abinda ya faru a restaurant ba.

""" Na farko umurnin Hajiya na ke cikawa. Na biyu idan ba zaki mini kwatancen unguwarku ba, zan juyar"

"da motar nan na mayar da ke wajen Hajiya"""

"Shiru ta yi tana tura baki, sai can ta faWa masa sunan unguwarsu. Ta juyar da kanta gefe tana kallon titi,"

"sai ya ji ™asa-™asa tana faWin ""sannu Wan Hajiya, mijin Baturiya, Mtssw""."

"""Da ni kike?"""

"Juyowa ta yi da sauri ta ce ""ni ba da kai nake ba"""

"Ya Wan kalleta kaWan bai ce komai ba, sannan ya maida hankalinsa kan tu™in da ya ke yi..."

CHAPTER EIGHTEEN

ZEEY

Yau Asabat ina wanki da safe kusan ™arfe goma nema sai na ji wayata na ringing a Waki. Na je da sauri

zan Wauka sai na ga wayar ta katse. Hajiya Layla ke kirana. Na danna mata kira amma sai ta kashe kiran ta sake kirana.

"""Ziyadah, yanzu na ga wani video a page Winki. Ai Wallahi kin tayar mini da kwaWayi sai ki san yadda za ki"

"yi dani"""

Ta faWa bayan mun gaisa.

Ni dai na san ban Waura sabon video ba. Akwai dai wani video na tallen garin Wanwake dana yiwa wata

kwanaki shine ta ce dan Allah za ta biyani na sake reposting mata a page Wina tunda za a fara Azumi. To shine na sake sakawa yau da safe. Ba sabon video bane.

To ko kuma dai videon Wanwaken take nufi?

"""Ziyadah ai ki zo ki min Wanwaken nan a gida na ci. Ya yi min kyau a ido"""

"Ashe shi Winne. Na sa dariya nace ""Hajiya ai kin girmi Wanwake"""

"""Ziyada ai ba za ki gane ba. Ni dana shekara Arba'in a turai ina gudun abincin gida, sai gashi na dawo"

"Nigeria yanzu babu abinda na fi so sama da abincinmu na nan. Kin san shiyasa fa na sallami Chef Win daya ke mana girki da. Na sa aka kawo mini Hassana"""

Ta ™are da cewa idan bana komai wai na zo gida na yi mata Wanwake. Na ce mata wanki nake amma na

kusa gamawa idan na gama zan zo. Daga haka ta min sallama.

"Ni garin Wanwaken dana yi amfani da shi a videon ma ya jima da ™arewa, amma dai zan duba a Kasuwa."

Lissafina na zuwa gidan Faty yau sai dai kuma gobe. Dama cewa nake idan na gama wanki zan je gidanta

"na faWa mata halin dana ke ciki, dan ta tayani jaje. In ma akwai wani tsohon saurayinta mai suna Muhammad da za ta iya haWani da shi sai na duba na gani ko za mu dace."

Bayan na gama wanki sai na shirya na fita. A hanya na tsaya na sayi garin Wanwake. Ban samu wanda

"nake nema Winba, amma dai na samu wani mai kyau dana taSa amfani da shi. Na wuce gidan Hajiya Layla."

Tana ganina ta fara murna kamar irin ta ga ™awarta Winnan. Gaskiya matar bata da girman kai.

Har kitchen ta biyoni ina kwaSa Wanwake tana min hira. Ta tambayeni ya shirin Azumi na ce mata

"Alhamdulillahi. Ta ce akwai abincin sadaka da wata mata ke musu duk Azumi tana tunanin ko ta bani aikin wannan karan, sai na ce mata gaskiya ba zan iya ba, saboda muna exams kuma idan na gama zan je Kaduna ziyara wajen Ummana. Ta ce mini babu komai."

Ina cikin jefa Wanwake bayan Hajiya ta tafi amsa waya a Waki sai ga wata Baturiya ta shigo kitchen Win. Da

farko sai dana Wan tsorata dan motsin mutum kawai na ji. Na Wauka ma Hassana mai aikin Hajiya ce sai na ga wata farar Baturiya kyakykyawa tana sanye da wando blue jeans da farin v neck top.

"""Are you the new Maid?. Where's the other one?. You know what, just make me some tea, I'll be on the"

"balcony"" ta juya ta bar kitchen Win tun ma kafin na bata amsa."

Sai da ta tafi ma na ji haushin meyasa ban ce mata ni ba Maid bane.

Da Hassana ta shigo kitchen Win sai na ce mata wata Baturiya ta shigo tana nemanta wai ta haWa mata

tea ta kai mata.

"""Ke bar jarabbiyar matar nan fa. Sai shegen jarabar shan tea. YallaSai idan zai sha koffee ko shayi shi da"

"kansa yake shigowa kitchen ya haWa abinsa. Da wuya kiga ya saka ni aiki. Amma wannan matarsar komai sai an mata. Idan an matan ma fa Wan Tank you Win nan ba zata faWa ba sai dai ta dinga ™orafi ba a haWa mata shayin da kyau ba. Shegiya."""

Na buWe baki ina kallonta. YallaSai?. Jalal Maiya™i take nufi. Shine ke auren Baturiya. Awwo! Ashe

"shiyasa ya ke cewa idea Wina bai dace da restaurant Win da zai buWe ba, saboda shi ya ™i jinin ba™in fata a rayuwarsa. Tsabar bai yadda da matan Hausawa ba, da Baturiya ya ™are. Lallai da zafinsa mijin Baturiya."

Haka dai na ™are aikin da zan yi. Dana gama Wanwake na zubawa Hajiya. Tana ci tana santi wai duk randa

take son cin Wanwake ni zata kira na zo na mata saboda nawa ya fi na Hassana daWi. Na yi murmushi kawai ina jinta. Yau ma na zo ne kawai saboda ina ganin girmanta kuma dama ina son abinda zai Wauke min hankali daga cakwakiyar dana ke ciki.

"Na Wan jima a gidan, dan bayan mun gama cin Wanwaken sai Hajiya ta fito da wasu kaya ta min kyautarsu."

Har da wani babban Swiss Lace wai in kaiwa Kaka. Na yi mata godiya. Muka tsaya kallon wani film Win Marigayi Ibro a tashar DaWin Kowa. Da aka gama sai na ce mata zan tafi.

"Kwatsam sai ga Jalal ya zo, ta ce masa wai ya kaini gida."

"Ina ganinsa wani haushinsa ya taso mini. Wato shi komai namu baya so, matar ma bai ga wacce ta mishi"

a duk faWin Arewacin Nigeria ba. Kai ko Bayarabiya Musulma bai gani ba sai Baturiya farar fata ce ta

burgeshi. To Allah ya bamu ha™uri mu ba™a™en fatan.

"A mota tunda na kira shi da Šan Hajiya, mijin Baturiya ya jiyo ni, sai na juyar da fiskata gefe ina kallon titi."

"Da muka iso unguwarmu na ce masa ba sai ya shiga lungunmu ba, amma ya dage wai aikin da Hajiya ta saka shi shine ya kaini har gida. Na ja ™aramar tsaki a raina sannan na nuna masa inda zai shiga. Da muka bi ta kan wani kwatami sai na Wan juyo na kalleshi ko zai yi ™orafi sai na ga fiskarsa normal. Haka dai na dinga nuna masa hanya har muka iso ™ofar gidanmu."

"Na yi masa godiya na wawuri ledar da Hajiya ta bani zan fita sai na ji ya ce ""ina so mu yi magana"""

"""Magana?, wace magana kuma?"" Na faWa ina hararansa. Har yanzu ina jin haushinsa, haushin aurensa da"

"Baturiya. To wai ma miye nawa a cikin kalar matar da ya aura ne?. Still, ina jin haushinsa, dan haka ni da shi babu wata magana a tsakaninmu. Ya katse min tunani da faWin"

"""I just want us to talk. Ba faWa ba. Just, REAL talk"""

"Na Wan sake hannun ™ofar na fuskance shi da kyau na ce ""Ina jinka. Amma ka yi sauri dan ka ga ana kiran"

"Sallah"""

""" gobe ki zo JK Plaza, 10AM sai mu yi maganar"""

Na yi se™e™e ina kallonsa. Wannan Wan Hajiyar ba ™aramin Wan renin wayo bane. Ya ce za mu yi magana.

"Na bashi dama, yanzu kuma wai in zo in sameshi a plaza gobe. Sai kace zamansa nake yi."

"""Ni fa idan ba za ka yi maganarka yanzu ba, shikenan na yafe"""

"""Zeeyadah, right?"" Ya Waga mini gira."

"Na Wauka Hajiya Layla ce ta iya kiran sunana. To ga wanda ya fita. Kai, ba iya faWin sunan bane."

"Munafurcin da zuciyata ke shirin yi ne ya bani mamaki. From normal bugu da take, 'yar munafuka kawai"

sai ta ™ara gudu daga jin wannan Jalal Win ya kira sunana.

Idonmu ya haWu briefly kafin na Wauke idona da sauri dan kada na faWa tuggun da zuciyata ke ™o™arin

kitsa mini.

Kuma fa ban ga laifinta ba tunda Mission Wina yanzu shine OPERATION FIND BOYFRIEND.

"Idan na shiga gida zan gargaWeta, wannan ba candidate da za a duba bane. Dan haka ABORT MISSION,"

ABORT MISSION.

"""Yana da mahimmanci mu haWu gobe"""

"""10AM, Please"""

Ashe fa magana yake. Na Wan yi gyaran murya ina ™o™arin processing me ya faWa. Na buge da abort

mission ban ji abinda ya faWa da kyau ba.

"""Zan duba, idan na samu lokaci zaka ganni"" na ™ara masa da cewa ""Dan ka ganni a Ghetto ba yana nufin"

"bani da abin yi bane. Ina da abubuwan yi masu yawa"""

"""Alright, Miss Ghetto. Sai gobe ko"" ya faWa yana ™o™arin tada motarsa."

Wato har da wani Miss Ghetto. To Wallahi Šan Hajiya zan kira shi nima.

"Na buWe ™ofar na juyo na ce ""To, Mr Šan Hajiya a gaida min Hajiya"""

"""Za ta ji"" ya amsa irin bai ji haushi Winnan ba."

Na fita daga motar na banko masa ™ofa na yiyo gidanmu.

"""Wancan motar Alhaji Nafi'u ne?"" Na waiga da sauri dan ban lura akwai mutum a wajen ba. Baffa Zakari"

"ne ke Alwalar sallar Magariba. Yana sanye da uniform Winsa, ina ga daga wajen aiki ya ke."

"""Ba shi bane"" na amsa masa tun ma kafin watarana ya ga motar Jalal ya ce zai masa maula."

"""Shine Saurayin naki?"""

"""Baba ba shi bane. Idan saurayina ya shigo gari zan kawo muku shi har nan ku gaisa"" daga haka na wuce"

"shi, na shiga gida."

JAYKAY

"Daga gidansu Ziyada, sai Jalal ya tsaya a wani Masallaci ya yi sallar Magariba kafin ya wuce gida. Wani"

nishaWi ya ke ji a zuciyarsa da ya jima bai ji irinta ba.

Da ya isa gida sai ya samu Hajiya da Junior suna cin abincin dare. Zama ya yi shima ya fara serving kansa.

"Hajiya ta tambayeshi ko Ziyada ta isa gida lafiya, ya ce ta isa lafiya."

Janan da Cassandra basa nan. Wai Janan Wince ta kai Cassandra wajen da za ta samu abinci mai kyau. Ya

"girgiza kai kawai. Lokacin da Chef Winsu yake nan, idan Cassandra ta zo gidan shi yake dafa mata duk"

"abinda ta bu™ata, saboda Internationally train Chef ne."

Amma tunda Hajiya ta sallameshi ta kawo musu Hassana sai dukkansu suka fara adopting cin abincin

Nigeria. Janan ce dai babu fancy restaurant Win da bata sani a Zaria ba. Ta kan iya hawa mota ta tafi Kaduna dan kawai ta je ta ci abinci ta dawo. Junior shi ya fi kowa saurin adjusting. In fact ranan da Jalal ya ga tuwon Semon da yaron ya ci a gabansa sai da ya yi ta mamaki. Hajiya ta koya yaron cin abinci mai nauyi kuma yaron yana jin daWin hakan ba kaWan ba.

Bayan ya dawo daga sallar Isha sun jima suna lissafin budget Win Azumi da Hajiya.

˜arfe goma ta wuce kafin ya baro Wakinta. Har lokacin Janan da Cassandra ba su dawo ba.

Ya shiga Waki ya cire kayansa ya yi wanka ya saka kayan bacci. ˜arfe shaWaya da kwata Cassandra ta buWe

™ofa ta shigo.

Warin giyar da ya ji ne ya saka shi kiran sunanta a fusace.

"""Maria! Are you drunk?"""

"""Relaxxxx mate! I'm not drunk"" ta yi tangal-tangal ta zo ta faWa kan gado."

Janan. Sunan da ya zo masa baki kenan. Ya tashi da sauri ya fita zai je Wakin Janan amma sai ya ja ya

tsaya jin muryan Hajiya tana masifa. Ya jiyo muryan Janan tana yiwa Hajiyar bayani.

"""Ni fa tun ™arfe tara muka rabu da ita. Kawai ina shirin tahowa gida ta kirani wai in zo in Wauketa bata"

"san inda take ba. Shine na kira Amir, da ™yar muka gane kwatancen wajen muka je muka Waukota"""

"""Me yasa ba ki kira shi mijin nata ya je ya Waukota ba. Janan na hanaki yawon banzan nan. Wallahi ki"

"kiyayeni. Ki kiyayeni, Janan"""

Juyawa ya yi da baya ya koma Wakinsa dan idan Hajiya ta ganshi faWan zai koma kansa. Yana shiga Waki

"sai ya kira numbar Amir. Amir cousin Winsu ne. Abokin faWan Janan. Lokacin da suka dawo Zaria shi ya koyawa Janan yawo. Ga shi dai ™aninta ne dan za ta iya bashi 3yrs ma amma tafiyarsu ta zo Waya. A yi daWi, a yi faWa."

Amir ya ce masa ai yanzu Hajiya ta fatatttakeshi daga gidan bayan sun kawo Cassandra gida. Da ya bashi

"labarin inda suka samu Cassandra, sai da Jalal yayi mamakin yadda aka yi ta san wajen. Koda yake za ta iya searching google ta nemi inda ake nightlife a garin Zaria."

Pillow ya Wauka ya kwanta a couch dan ba zai iya kwana gado Waya da Cassandra tana warin giya ba.

Minti biyu da kwanciya sai ya ji ya takura. Mi™ewa ya yi ya zo ya buga bayan Cassandra da ™arfi ya ce ta

"je ta wanke jikinta. Ta buWe ido tana masa tanSele, haushi ya kama shi ya jawota da ™arfi ya turata cikin banWaki ya ce ta yi wanka. Ya zo ya cire duka zanin gadon da duvet da komai ya kwashesu ya fita. Laundry room na ™asa. A hankali ya ke takawa kar a jiyo shi duk da yanzu ya ji shiru Hajiya ta gama yiwa Janan faWa."

Yana zuwa Wakin wanki ya jibge kayan a ™asa ya fito ya koma Waki har lokacin Cassandra bata fito daga

"banWaki ba. Haushi ya cika shi kawai ya Wau wayarsa ya fita daga Wakin ya tafi Wakin Junior. Idan ma bacci ta yi a banWakin ita ta sani, wannan bai dameshi ba."

Junior ya jima da bacci. Haka ya squeezing jikinsa a gadon yaron ya kwanta yana tantamar ya kwana a

wajen ne ko kuma ya tafi guest room a ™asa ya je ya kwanta.

Akwai Wakin Jamal a sama. Amma tunda aka kwashe kayan ciki Hajiya ta sa aka rufe babu wanda ya sake

shiga cikin Wakin.

Haka dai Jalal ya ha™ura da sake fita ya kwanta kusa da Wansa. Da Asuba da ya tashi sai ga shi ya tashi da

"ciwon jiki. Ya dropping ™asa, ya fara push-up saboda ya Wan warware muscles Winsa."

Lokacin da ya shiga Wakinsa sai ya samu Cassandra a yashe akan gado daga ita sai towel. Ya girgiza kai ya

wuce banWaki dan ya yi alwala.

Bayan ya dawo daga sallar Asuba da ya shiga gaida Hajiya abinda ta fara tambayarsa shine yaushe Cassy

"za ta tafi. Ya ce mata gobe Monday. Ta Wan yi shiru sai kuma ta ce ""Ina so ka yiwa ™anwarka magana. Jiya ita da Amir ™arfe shaWayan dare suka shigo gidan nan. Daga yanzu na saka doka, duk inda za ta je ™arfe takwas na dare ya mata a gida. Wani batun fita shan ice cream da dare na cancel Winsa daga yau. Nan ba London bane. Yanzu mutane za su fara nuna mini yatsa suna faWin ai ga 'yar Hajiya Layla nan tana yawon"

"dare. Ka ja mata kunne."" Ta Wan yi shiru, sai kuma ta sake cewa ""Maganar matarka ta je club bai shafeni"

ba. Amma ni ban yiwa Janan tarbiyyan da za ta je neman 'yan giya a Club ba. Wannan ya zamo na farko

"kuma na ™arshe a gidan nan""."

"Yet again, ta sake nuna masa illar auren Cassy."

Ha™uri ya bata ya ce mata zai yiwa Janan magana.

˜arfe tara da rabi na safe yana shirin fita Cassandra ta tsare shi ta fara bashi ha™urin abinda ta yi jiya.

Wai ta masa al™awarin ba za ta sake shan giya ba har ta bar Nigeria.

"""Suit yourself, Cassandra"" ya faWa yana bangajeta ya fice daga Wakin. Akwai abu mai mahimmanci dake"

"gabansa, dan haka ba zai bari ta Sata masa rai ba."

Lokacin da ya shiga mota sai ya turawa Ziyada text yana mata tuni da ™arfe goma ne fa haWuwarsu.

"Jalal yana tu™i, amma jin kansa yake cikin wani nishaWi."

"Idan Allah ya taimakeshi, a yau Winnan zai samowa kansa irin matar da Hajiya ke so."

CHAPTER NINETEEN

ZEEY

Uban wa ya ke min kiran sassafen nan ina cikin mafarki me daWi?. Uban waye wannan da zai kirani

safiyar Sunday ina cikin bacci mai daWi?.

"""Ziyadatu ba wayarki ke ™ara ba?"" muryan Kaka yasa na buWe idanuna na fara laluben wajen pillow zan"

jawo wayar ashe wayar tana ™asa. Maybe cikin bacci na bugota ta faWi dan na san dai gefen Pillow nake ajiyeta.

Na sa hannu na Waukota lokacin har ta gama ringing.

Ina ganin sunan wanda ya kira na ji sauran baccin dake idanuna ya washe.

Jalal ne ya kirani. JALAL MAIYA˜I. Kuma ba sassafiya bane kamar yadda nake tunani. ˜arfe goma na safe

har da minti goma.

Yaushe na yi bacci har haka?.

Na fara tariyo abinda ya faru daga Daren jiya zuwa yau. Jiya da dare ni da yaya Aminu mun jima muna

chatting akan hukuncin da su Baffa Adamu suka yanke. Ba ni na faWa masa ba. Magulmatan gidanmu ne suka faWa masa. Nan an yi abu ranan Jummu'ah amma sai gashi Asabat shi da ya ke Yola har ya ji labari. Na san ba zai wuce waccar Mardiyyan bane ta faWa masa. Hassada da kishi su za su yi ajalin yarinyar nan idan bata dena ba.

Babu wata matsaya da muka cimma after hours da muka kwashe muna chatting akan maganar. Wai shi

"lallai dai mu dawo da maganarmu, shine Muhammad Win da zan gabatarwa su Baffa Lawalli.

Please Login or Register in order to submit comment