You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa ai sai ki je ki ™arata da shi. Saboda"

"Mijin ki dai Ziyadatu sai gani a gaban hukuma ina bada bahasi. Tunda na ke ban taSa zuwa Chaji Ofis ba sai akan mijinki. Daga ™arshe me ya tsinana min?. ˜wandala bai ce ungo Baba ka sa kati a waya ba kuma na san yana turawa Adamu kuWi. Ba laifinsa bane, ke kika nuna masa cewa Adamu ne Ubanki ba ni ba"""

"Ya nuna kansa ya ce ""Ni ne nan Lawallin Baba Haruna na ke kula da tarbiyyanki har shi Alhaji Jalal Win ya"

"ganki ya ce yana so. Ko ba haka ba?"""

"Na goge hancina na ce ""haka ne""."

"'To kin gani. Ni na miki tarbiyya"" ya faWa yana bugan ™irjinsa."

"""Shi Adamun yaushe yake zama a gari. Zakari ko idan ya tafi wajen gadinsa yana saka ido a lamarinki ne?."

"Ni ne nan na saka ido a tarbiyyanki, ba dan na saka miki ido ba sadda kika fara Jami'a Allah ne kaWai ya san abinda za ki zama"""

""" Iyi!"" Ya wani zaro ido"

""" 'Yanmata nawa ne suke zuwa Jami'a su lalace. Amma na tsaya tsayin daka akanki saboda na ri™e"

"Amanar da Sadiqu ya bar mini."""

"""Ga ki nan"" ya nuna ni. ""Da me kika saka min?. Ke da Mijinki sai dai ku hau mota ku yita yawo a gari ba"

"za ku zo ku sada zumunci ba. Yara nawa ne a gidan nan suka gama Sakandare suna zaune ba Makaranta ba aiki amma ki gagara Waukansu aiki, Ziyadatu. Eh?"""

Na yi shiru dan na san duk faWan da yake kuWi yake nema. Wannan tarihin da yake ta karantowa duk dan

na bashi kuWi ne.

Na san za su ga ba™ina saboda ban Wau kowa a gidanmu na bashi aiki ba. Bana son haWa business da

"aurena ne. Idan aka samu matsala ba zai mana daWi ba da ni da su duka. Kuma in dai yaran gidanmu dana sani ne to babu wanda zan iya bada shaida akansa, gara ma matan, amma mazan sai a hankali, akwai dai dama-dama a cikinsu su kuma basa bu™atan aiki suna da buga-bugar da suke yi."

Bayan na fito Maman Suwaiba ta jani Wakinta ta ce kada na Waga hankalina akan abinda Baffa Lawalli ya

"faWa, wai Jalal ya cewa su Baffa Zakari da Baffa Lawallin su kawo masa sana'ar da suke son yi zai basu jari. Wai Baffa Zakari ma na shirin barin aiki ™arshen watan nan, amma shi Baffa Lawalli sai ya Wau abin da zafi wai Jalal ya rena masa wayo. Ni dai ban ce mata komai ba."

Lokacin dana dawo gida bayan Magariba kwantawa na yi akan gado ina tunanin 'yan'uwana. Baffa

"Lawalli ganin wacce za ta fitar dashi daga Talauci yake mini. Dukiya kuma ba tawa bace, ko shi Jalal"

Winma ba nasa shi kaWai bane balle ya ri™a kashewa 'yan'uwana kuWi. Ni kuma Restaurant Wina yanzu aka

"buWeta, bamu ma san ko za mu Waure da ciniki ba balle mu yi maganar riba. Kafin na baro gidan dai na"

yiwa Baffa Lawalli transfer Win dubu ishirin. Da dubu goma cash na yi niyyar bashi amma yadda ya buge da yi mini faWa yana mini karatun shi yayi mini tarbiyya sai na ga idan na bashi dubu goma ma renawa zai yi.

Kai! Allah dai ya sa na wanye da kowa lafiya. Gobe zan yiwa Jide magana ko za a samu space da za a

Wauki staff ko biyu ne na Wauki yaron Baffa Lawalli Waya na Baffa Zakari Waya.

Ba a jima ba na fara juyi ni kaWai bacci ya ™i zuwa mini. Kewan Jalal nake. Tun safe da ya mini text bai

"sake yi mini wani ba, da kuwa sai na ga text Winsa biyu ko uku a rana."

Wayata na jawo na shiga Whatsapp Wina sai na ga yana online na tura masa sallama. Bai buWe ba sai

wajen minti uku kafin ya min reply wai na yi ha™uri yana video call da Junior ne.

Na tambayeshi video call kuma. Dama ba a gida Waya suke bane?. Ya ce min wai tunda ya tafi bai samu

ganin Junior ba sai Wazu ne bayan ya yi waya da Kakar yaron ta haWasu a waya. Ashe Matar tasa Soye Junior ta yi a wajen Mamanta.

Na ce Allah ya kyauta. Ya tambayeni ya jikin Kaka na ce masa da sau™i tana gaishe shi.

Haka kawai sai na tsinci kaina da jan hirar tamu. Na faWa masa abinda kitchen staff Wina Zainab ta yi a

Gidan Girki.

Na ce masa zan sacking Winta ™arshen wata ya ce hakan ya yi dai-dai saboda chanja mana ingriedients na

nufin za ta iya saka wani abun a gaba da zai lalata mana abinci.

Na ce masa ina so na Wauki yara biyu a gidanmu na basu aiki a Restaurant Win. Ya ce zai tambayi

Manager Plaza Win ya ji ko akwai vacancy a wajensu koda na mutum Waya ne.

Kan kace me mun share awa Waya muna chatting muna tattauna abubuwan da suka shafi business.

"Shi da kansa ya ce na kwanta tunda zan yi fitar sassafe. Na yi masa sallama, ina shirin sauka ya turo last"

"message Winsa: I LOVE YOU, Sunshine."

Na manna wayar a ™irjina ina murmushi...

CHAPTER FIFTY SIX

ZEEY

"˜arfe shaWaya na safiyar ranan Alhamis kenan na gama shiri zan je gidan Hajiya, ta kirani wai na zo na"

mata miyan kukan wai Saurayin Janan zai zo ta sa an yi masa girke-girke ita kuma ba za ta iya ci ba.

Dama ban je Gidan Girki ba. Da safe na je School mun yi wani test ™arfe takwas na safe daga nan na

tattaro na dawo gida saboda kaina dake ciwo. Sati guda kenan back-to-back idan na fita Restaurant bana dawowa gida sai ™arfe biyar ko shida na yamma. Allah ya buWa mana a satin mun samu order daga gidan Sarki. An yi wani bikin naWin Sarauta shine aka bamu order yin abinci na kwana biyu. Mun sake samun wani order daga wani babban Wan Kasuwa ana bikin 'yarsa muka musu abincin ranan Kamu. Wannan ya sa na ja ragamar girkin da kaina saboda kar a samu matsala su Sata mana suna.

Lokacin dana ke kulle Wakina sai na ji ™aran shigowar text a wayata. Ko ban duba wayar ba na san Jalal ne.

Cikin sati Waya wani sabon shiri muka ™ulla har mamakin kaina nake ni da na yi ta cika bakin ba zan kula

shi ba har sai ya saki Cassandra.

SO wani wawan abu ne.

"Ba fa wai na dena jin haushin Jalal gabaWaya bane, har yanzu ina jin haushin abinda ya mini amma kuma"

wani mugun sonsa da nake ji sai ya danne fushin dana ke mishi ya mayar da shi kewa. I MISS HIM SO MUCH.

"Ni dama ban iya soyayya ba, idan na fara son mutum to da dukkan zuciyata nake yi. Lokacin da muka yi"

soyayya da yaya Aminu har bayan mun rabu ban dena son shi ba sai a hankali soyayyar ta fara raguwa har kuma na rufe komai.

Bana tunanin na yiwa yaya Aminu irin son da na ke yiwa Jalal yanzu. Ni kaina ina mamakin yadda nake

wani mahaukacin sonsa. Shi yasa duk da ina fushi da shi hakan bai hana ni jin daWin hiran da muke idan muna chatting ba.

Mun jingine maganar Cassandra a gefe. Ba ya mun maganarta nima bana tambayarsa labarinta. Idan

abinda ya faWa kafin ya tafi gaskiya ne to duk rintsi zai tsinke ala™ar dake tsakaninsu kafin ya dawo gareni.

Ko maganar Junior bana yi masa. Tunda ya ce min yaron yana wajen Maman Cassandra kuma suna waya

"sai na ja bakina na tsuke. Tunda yaron na nan lafiya, shikenan babu abinda zan iya masa sai addu'ar samun nasara, which ina yi kullum."

Hirarmu da shi ta fi karkata kan business Wina. Kuma sosai nake jin daWin yi masa taWin Gidan Girki.

"Gidan Girki, ko gidan Drama."

"I LOVE YOU AGAIN, SUNSHINE."

Na karanta abinda ya turo. Ina ga dai kafin ya tafi sai da ya sha la™anin kalaman soyayya. Murmushi ne

"ya suSuce min dana sake karanta text Win. A kullum sai na samu sa™on I Love You sau uku a rana. Ban taSa nuna masa abinda ya ke turowa yana tasiri a zuciyata ba, amma kuma ni kaWai na san sau nawa nake maimaita sa™onnin nasa a rana. Tilawarsu nake duk dare kafin na kwanta idan muka gama chatting da shi. Kuma hakan ba shi zai hana na tisasu bayan sallar Asuba ba."

Wata™ila da ya buWa mini zuciyarsa tun farkon aurenmu da ba zan yi kokonton soyayyarsa gareni ba.

Lokacin dana isa gidan Hajiya sai na samu an cika dining da abinci kala-kala ko ina sai ™anshi yake.

"Hassana data buWe min ™ofa ta fara min gulmar wai yanzu Saurayin da ya yi girkin ya tafi, ashe ma namiji"

ne Chef Win.

Na ce ina Hajiya wai tana falon sama na wuce saman dan na gaishe da Hajiya kafin na koma kitchen na yi

mata girki.

"""Lale Marhaban! Ai yanzu nake cewa zan sake kiranki ashe kina tafe"""

"Na yi murmushi na risina na ce ""Hajiya, Ina kwana"""

"""Lafiya, Ziyada. Daga can Plaza kike ne?"""

"""A'a"" na ajiye jakata a gefe na gyara zamana."

"""Ban ma le™asu ba yau. Na dai je School da safe mun yi test. Sadda kika kirani ma ban jima da dawowa"

"ba"""

"""Allah Sarki. Ya test Win?. Kina dai samun lokaci kina karatu ko?"""

"""Ina karatu sosai Hajiya"""

"""Allah ya sa a gama lafiya"" na amsa da Amin."

"""Hajiya, ina Janan ne?"""

"""Yanzu ta shiga Wakinta ina ga shiryawa za ta yi. Khalifa ya shigo gari yana gidan yayarsa daga can zai"

"taho nan"""

"""Ayya! Allah ya kawo shi lafiya"" Hajiya ta ce Amin."

Lokacin dana mi™e zan tafi sai Hajiya ta tambayeni fatan babu matsala na ce mata babu.

Na sauka ™asa na samu Hassana mai aiki na tambayeta me suke da shi a ™asa.

Lokacin da nake tu™a tuwon shinkafa tsinin takalmin Janan da gudunta ya tabbatar mini Saurayinta ya

iso dan na ji ™aran shigowar mota gidan.

Yau dai zan ga Mi Amor da Janan ke ta wa™arsa tun zuwana gidan.

Bayan na gama kwashe tuwon ban fito ba na ce Hassana ta je ta Wauko min gyalena dana bari a falon

sama. Matar aure nake babu mutunci na wuce ta gabansu babu mayafi.

Da ta kawo min na gyara mayafina da kyau sannan na fito.

Suna zaune a falo. Hajiya na kujerar mutum Waya ita kuma Janan da ba™on namu suna zaune a two

seater. Yadda ta Janan ke yi ka ce za ta shiga jikinsa ne.

"""Zo, zo, 'yata ku gaisa da Khalifa"" na ™arisa wajensu na gaishe shi bayan Hajiya ta ce masa ni ce matar"

Jalal.

"Sai wani shan ™amshi yake yana wani amsawa a da™ile, na ce kan buuu ya jima bai buWe baki yayi"

"magana ba. Ko lokacin da Jalal yake jin kansa kafin mu yi aure ba zai min haka na ™yaleshi ba balle wannan guntun. Khalifa kyakyawa ne kam, sai dai guntu ne. Ga masu son farin namiji zai musu kyau overrrr amma irinmu da muke son ba™in mutum,to a kai kasuwa."

Na tabbata yadda Janan ta saka takalmi mai shegen tsinin nan idan ta tashi sai ta fi shi tsayi. Na yi

"mamakin wannan ne Khalifan da take ta rawar jiki a kansa. Koda yake abincin wani, guban wani."

"""Ashe kai ne KHALIFAN?"" na kausasa ™arshen dan ya tabbatar jinsa ya fi ganinsa a wajena. Daga yanayin"

"yadda ya wani haWe gira na san ya ji zafin hakan. Aikin Sur in ji tusa!. Ni da nake da miji dogo santalele zai tsaya yana wani ja min aji, mtswww!."

Wucewa sama na yi na barsu a falon. Šakin Jalal dake gidan na shiga dan na yi sallar Azahar. Dana idar

na fito daga Wakin dan na Webi abinci dan yunwa nake ji. Tuwon zan ci nima dama na ce Hassana ta kawo abincin sama tunda dining Win ™asa kam Mai girma Janan ta cike shi da abinda Chef Winta ya girkawa Khalifanta.

Ai ina fitowa na samu Hajiyar ma abincin take ci. Sai na ji babu daWi na Webi nawa na koma Waki sai kawai

na zauna nima a wajen na fara ci.

"""Wallahi miyar kukan ki daban ce. Sau dubu idan Hassana ta yi miyar Kuka idan na taSa naki sai na ji"

"banbanci, kuma ba Hassana kaWai bafa. Na rasa ya aka yi duk sadda nake cin miyanki sai na ri™a tunowa da Kakata, Allah ya ji™an Hajiya. It's like kamar ita ta yi miyan"""

Na yi murmushi. Nima ban san sirrin ba. Yau har tsayawa Hassana ta yi wai ta ga yadda nake yi saboda

"itama Hajiya ta dinga yaba nata. Ban Soye mata yadda nake yi ba. Wata™ila banbancin yana daga ha™urin jiran ruwan kukan ya tafasa da kyau ne kamar yadda Kaka ta koya min kafin a kaWa, ko kuma dai hannuna ne tunda akan ce girki hannu-hannu ne. Allah ne masani."

Muna cikin cin abinci Hassana ta zo wai idan akwai sauran tuwon za a kaiwa Khalifah ya ce Tuwo zai ci.

"""Sai dana cewa Janan a mishi Tuwo ta ce wai Tuwo bai dame shi ba, ai gashi nan. Abubuwan da ta sa aka"

"masa dai shi ya saba shi a chan UK Win""."

"Ina ganin Hassana tana Soye dariyarta, da alama akwai gulma a bakinta kenan."

Ta Wauki ragowan Tuwon ta wuce da shi ™asa.

Bayan na ci abinci Wakin Jalal na wuce dan na Wan kwanta na huta kafin la'asar sai na wuce gida ko kuma

na le™a Gidan Girki.

Ban jima da fara bacci ba na ji ana ™wan™wasa min ™ofa.

Na mi™e da ™yar dan bacci ya fara min daWi na je na buWe ™ofar...Janan ce.

"Ta wani shigo fuuu ta ce ""Na zo ki bani maganin da kike sakawa a abincinki"""

Na haWe gira dan ban fahimci me take nufi ba.

"""Tell me why Khalifah zai cinye ™aton Tuwon da Hassana ta kawo mishi. Me kike sa a ciki?. Shi yasa"

"tunda kika yiwa Hajiya girki sau Waya Hajiya bata dena yabon abincinki ba har yau. Yanzu kuma, Khalifana"

"da ba ya son cin Tuwo shine yake tambayar wai idan da ™ari yana so miyar ya masa daWi..."""

"""Ki ce ya je Gidan Girki ya siya a chan"" na faWa ina dariya."

"""Allah ba wasa nake ba"""

"""Maza ai suna da munafurci. Dama dai yana son cin Tuwon ke ce dai ba ki gano hakan ba"" na faWa ina"

dariya.

"""It's not funny, Ziyadah. Allah ban taSa ganin Khalifah ya cinye ™aramin Tuwo bama balle babban Tuwo"

"haka"""

"""Ba mamaki dan bai taSa cin mai daWin nawa bane. Amma ki biya ni Miliyan goma na koya miki sai ki"

"dinga yi masa idan kuka yi aure"""

"Ta watsa min harara tana faWin ""Allah ya kiyaye in zama Cook. Zan dai nema masa wacce ta iya Local"

"Dishes ta dinga masa duk sadda yake so"""

"""Uhumn!"" Na faWa ina jijjiga kai. Janan bata san karatun aure ba. A yadda nake ganin Khalifan nan ba"

mamaki idan suka yi aure yace ba ya son 'yar aiki a gidansa.

Na san idan muka samu zama da Hassana za ta min gulmar abinda ya faru har ya ce Tuwo zai ci.

Da yamma lis na koma gida dan ban tashi daga baccin dana yi da wuri ba.

"Da dare da Jalal ya chatting Wina sai nake faWa masa Khalifah ya zo, na tambayeshi ya aka yi suka fara"

soyayya da Janan.

Ya ce min Uncle Win Khalifah abokin Daddynsu ne ™ut da ™ut. Sadda Khalifah ya zo London karatu shine

"Uncle Winsa ya ce ya zauna a gidansu. To a wannan zaman ne suka saba sosai da Janan daga baya kuma suka fara soyayya. Dake yana son boko sosai wai ba zai yi aure ba sai ya ™are Phd Winsa shine fa aka Waga auren har sai yanzu daya gama degree Winsa na uku. Na ce ikon Allah! Na tambayeshi yaushe auren ya ce min sai ™arshen February. Yanzu muna November, da Wan sauran lokaci."

Ban faWa masa yadda Khalifan ya wani sha min ™amshi ba lokacin dana gaishe shi. Amma daga yadda ya

Wan bani labarinsa sai na fahimci mugun girman kai gare shi. Yadda Janan ke ta rawar ™afa a kansa. Allah

dai ya sa yana sonta.

***

Bayan sati Waya da zuwan Khalifa wata ranan Asabat ina Gidan Girki sai ga Janan ta zo office Wina wai

tana so na koya mata yadda ake yin Tuwo da miyar Kuka mai daWi irin nawa.

"""Shi kaWai zan koya tunda Mi Amor yana so"" ta faWa tana wani haWe fiska dan kar na mata dariya."

Ni ce dai nan CHEF ZEEY data kira da Local Chef.

"""An gama ranki shi daWe"" na faWa nima ina haWe rai."

"""Nawa za ki biya?"""

"""Sai na biya?. Kina matar Yayana Win"""

"""Matar Yayanki nake ai ba Malamarki ba"""

"""Whatever, nawa zan tura miki?"" Ta faWa tana Waga wayarta irin dana faWa za ta min transfer Winnan."

"""10 Million"""

"""10 Million! You're not serious. Dan za ki koya min abu Wayan shine zan baki 10 Million. 10 Million fa"

"budget Win kayan kitchen Wina ne"""

"""Iyi. Idan kika yi siyayyar kayan kitchen Win ai sai kin iya amfani da su kafin su ci kuWinsu ko"" na faWa ina"

dariya

"""Dariya ma kike min ko. To na fasa ma ba sai kin koya min ba. Kuma zan kira yaya Jalal na faWa masa"""

"""Ki ro™e ni ki ce 'Anty Chef Zeey, dan Allah ki koya min yadda ake Local Dishes wanda zai ja hankalin"

"Mijina, yanzu na gane cewa Maza sun fi son abincin gida' kin ga sai na koya miki ko sisinki ba zan karSa ba"""

"""Sai na baki ha™uri?. You know what, manta kawai"" ta tashi fuuu ta fita tana faWin ta fasa ma ba zata"

koya a wajena ba.

Maza kenan!

Janan dai dana sani data ™wammaci ta ri™a cin pizza da shawarma kullum da ta ci Tuwo ita ce wai ke son

na koya mata girki. Daga sanin Hajiya Layla har zuwa yau bana tunanin Janan ta taSa shiga Kitchen ta dafa ruwan shayi ma balle wai ace Shinkafa ko Tuwo.

Sai ga shi son namiji ya chanjata rana Waya? Ikon Allah!.

Fushin Janan ko kwana biyu bai kai ba. Hajiya ta kirani wai Dan Allah na zo zan fara koyawa Janan girki.

"Ai kuwa dana je gidan na zage na dinga yi mata dariya, wai ashe Hajiyar ce ta ce idan bata tsaya ta koyi girki ba ba za ta barta ta je Dubai da China siyayyar kayan kitchen da kayan Waki ba."

Kai Jama'a! da gaske fa Janan bata iya komai ba. Ko lokacin dana ke koyawa Hayfa girki 'yar Hajiya

Maryam ban ga irin wannan kwaSar da Janan ke yi ba. Ai Hayfa ma nata da sau™i ta Wan iya dafa su Indomie da su soya ™wai. Har Jollof Rice ta Wan iya kafin mu fara class da ita amma wannan yadda ka san 'yar shekara takwas nake koyawa girki haka muke da ita. Komai bata iya ba. Idan ta yi wata tambayar ma idan na kalleta sai na rasa abin faWa. Hassana ce 'yar dariya idan ta ji muna drama da ita. Ni kam abin ma ya dena bani dariya sai mamaki.

Like na san a gidan kuWi da jin daWi ta taso amma koyon girki ai bana Wan talaka kaWai bane. Abu ne da

duk min kuWinka dai za ka kowa ko dan sha'awa ko kuma dan Sacin rana. Maza dayawa sun iya girki balle

Mace. To ko matar jikan Queen Elizabeth an ce tana girki. Na taSa ganin video a YouTube an nuna tana

girki. Kuma ta ce lokaci zuwa lokaci tana yiwa Mijinta da 'ya'yanta girki dan tana jin daWin hakan.

Koda yake itama an ce 'yar Talaka ce kafin ta auri Prince William Win.

To ko kuma dai Talaka kaWai ya kamata ya iya girki ne?...

"A haka dai muka yita gurgurawa, a yi faWa a shirya. Tun tana yi dan Hajiya har ta zo ta saduda fa ta gane"

koda za ta Wauki mai yi mata girki akwai ranan fa da Khalifah zai bu™aci ta yi masa da kanta. Kuma da

alama Khalifan na ta Wan packaging ne. A waje zai nuna baya son gargajiya a gefe kuma yana so.

Ranan da ya sake zuwa dake da safe ne Masa muka yi masa da Danderu. Ni dai dan Hajiya na yiwa ba

dan shi ba. Janan har da ma™ale masa tana nuna masa hannunta wai har ™onewa ta yi wajen juya Masa.

Ku ji fa!.

A hankali sanyin December ya shigo wanda ya ™ara mini kaWaici da kewar Mijina.

Yanzu kam na saduda ko da ba zai rabu da Cassandra ba in dai zai dawo gareni ya bani kaWan daga

kulawarsa zan zauna da shi a hakan.

Zuciyata da gangan jikina suna kewarsa. Duk lokacin dana kwanta na tuno da ranan dana sha kashi a

hannunsa sai na ji ina tsirtar da ruwa.

Ina ga har da laifin sanyi a yadda nake missing Winsa sosai.

A January za mu yi Jarrabawar First Semester. Bana son samun Spill Over dan haka na sakawa kaina

karatun dole. Ko na fita aiki idan ina zaune a office babu abinda nake handout Wina nake Waukowa na

Wan lelle™a sama-sama.

"Ni ba guruwa bace a Makaranta, na san kaina, in dai na yi tisin karatu a ™alla sau biyar kafin exams to da"

wuya ka ga na manta abubuwan dana karanta. Allah na gani idan na karSi BSc Certificate Wina to ni da Karatu mun yi hannun riga kenan.

"Kafin mu shiga January Janan da wata ™anwar Hajiya dake Lagos suka tafi Dubai siyayya, wai har India da"

China za su je.

"Har yanzu dai bata iya abubuwa dayawa ba, amma dai babu laifi ta Wan fara iya wasu."

"Gidan Girki kuwa har yanzu Masha Allah, muna samun mutane musamman masu order daga gida. Sai"

dai fama da matsalar Staff. Mun sallami Zainab Jide ya kawo mana wasu guda biyu mace da namiji. Namijin sunansa Sanusi sai macen sunanta Majida.

Da aka fara exams sai na maida hankalina gaba Waya kan karatu. EDD Win Faty ya faWa cikin Exams dan

"haka sai addu'ar kada ta haifu take sai bayan mun gama Exams. Kai ciki bai karSeta ba, ta yi wani ™iba ne ta kumbura ta yi ba™i ga Pimples da ya cika mata Fiska. Ba ™aramin tausayinta nake ji ba musamman idan na tuna halin da take ciki. Ta auri ma™aryaci. Ya mata al™awarin zai barta ta cigaba da sana'arta idan sun yi aure ta zo ta aureshi ya ™i fir ta cigaba da sana'ar Make up Winta kuma ba wai yana da halin ciyar da ita da kyau bane. Gaskiya lamarin aure sai da addu'a da Istigfari. Ba za ka taSa sanin gaskiyar namiji ba sai ka aure shi."

A yadda ta faWa mini dai wai idan ta haihu zata koma sana'arta ko yana so ko baya so wai ta gaji da bani-

bani da take yiwa mutane. Ni dai ce mata na yi Allah ya taimaka. Ah to! Yanzu na ce mata ta yiwa Mijinta bore ta zo gobe su shirya da mijinta ta ce ai yiwa Miji biyayya sunna ne shi yasa ta watsar da sana'ar Make up ta ri™e Miji. To ba da ni ba.

A hankali idan ta nitsu za ta nemawa kanta mafita. Ko Make up Winne ko wata sana'ar daban ne dai dole

ta yi idan tana so ta siyawa kanta mutunci ta kuma samu kwanciyar hankali. Dan BABU mugun ciwo ne. Allah ya rabamu da BABU.

Saura Exams biyu mu gama Faty ta haihu. Ana gobe zamu rubuta Paper ta haihu da dare ta samu Wanta

namiji.

Bata samu zuwa Exams Win ba wanda ta sani Automatic Spill Over biyu kenan.

Ban samu na je na dubata bama sai bayan kwana huWu da haihuwar.

"Dama cikin ya sakata ™azanta to

Please Login or Register in order to submit comment