You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ziya ta fara bidiyo. Sun saba ganina ina yi fa amma kullum zan yi haka za ka ga suna shigowa gulmar abinda na ke yi.

"""Wai ba za ku je Islamiyya bane kam!"" Na korasu ganin sun fara distracting Wina. Idan ina period ba"

™aramin masifa na ke ba. I guess gaskiyar Likitoci da suke cewa period yana sakawa mata mood swing.

Muna gama recording na zauna a tabarma a ™ofar Waki na fara editing videon while Kaka ta juyewa yaran

kunun da muka yi ta ajiye min kaWan in case zan sha.

Dana gama editing sai na shiga Waki na kulle na ri™e wayata na fara yin voiceover. Ba ni da microphone

"yanzu, da ina da wani wireless microphone amma ban san wa ya taka min transmitter Win ba ya zo ya dena yi."

Ina gama voiceover na ™arisa editing Win na posting videon tareda tagging wacce ta aiko min kayan.

By the time na gama shiri na fito ™arfe shaWaya ta cika. Haka dai na fito da sauri na samu Keke na wuce

"gidan matar. I make sure na Wauki extra pad dan ba™ona Wan iska ne, zai iya disgracing Wina a ko'ina. Mata masu heavy bleeding suna fama..."

***

Matsalar gida a GRA shine buga gate. Lokacin dana isa gidan sai dana yi ta faman buga gate kafin daga

baya har na ji haushi zan tafi aka buWe. Kuma fa na yita kiran matar tun kafin na iso amma bata Wauka ba.

"""Wa kike nema?"" Wani yamutsatstsen tsoho ya tambayeni fiskarsa a Waure. Da alama shine Maigadi."

"""Hajiya Maryam"" ""ta san da zuwana"" na ™ara da haka dan kar ya Wauka maula na zo yi gidan."

Wani kallon sama da ™asa ya min kafin ya ce na shigo.

Kai Allah ya tsinewa Talauci. Yanzu dan zan shiga gida mai GATE shine ake min wannan wala™ancin...

"""Ai mun yi ta jiranki. Kin san ni bana so ana wasa da lokaci"" matar ta kalleni sannan ta ce ""I DON'T LIKE"

"IT"""

"""Dan Allah ki yi ha™uri, Hajiya. Wani uzuri ne ya ri™e ni"" na faWa a ta™aice saboda na san ni ce da laifi"

tunda dai ™arfe goma na safe muka yi zan zo.

"Kitchen Win gidan ta wuce da ni sannan ta ce bari ta kira min Hayfa, wato 'yarta da zan koyawa girki."

Na tsaya a kitchen Win na fara duba ledojin ingriedients Win da suka siyo dan na tura musu list last week.

Na fi minti ishirin ina tsaye kafin Hayfa ta fito sai wani tura baki ta ke irin an takurata Winnan.

Da headphone a kunnenta ta shigo kitchen Win ko magana bata min ba. Na yi ™o™arin gaisheta ma amma

ko amsawa bata yi ba. Ta ja kujera ta zauna sai danna waya ta ke yi.

Ni dai biyana aka yi dan haka babu ruwana da attitude Winta. Zan yi abinda aka ce na yi ne na tafi.

"Miyan kuka zamu fara yi amma ko kallo ban isheta ba, duk bayanin dana ke yi mata akan yadda ake"

miyar kuka ta yi yau™i ta yi daWi hankalinta na kan wayarta.

Sai da Hajiya Maryam ta shigo ta mata masifa ta karSe wayan daga hannunta kafin ta taso daga kan

"kujeran ta tsaya kusa da ni. Daga masifar da Hajiyar ke yi na fahimci wanda Hayfan za ta aura a ™asar waje yake da zama, kuma specifically zan koya mata abincinmu na gargajiya ne saboda yana so sosai. Da alama babban mutum za ta aura dan na ji Hajiyar na faWin kada ta manta da mahimmancin wannan auren."

"A yadda na Wan fahimta, kamar yarinyar bata son auren. Ita kuma Hajiyar ta Wauki maganar auren kamar"

"ranta. Koma wanene za ta aura dai ban sani ba, dan basu faWi sunansa ba."

"Na dai fahimci wani abu kafin na tafi, wato suma mutanen gida mai GATE suna fama da tasu matsalar..."

***

JAYKAY

"Yau Sunday, yana gida tun safe babu inda ya je. Bayan ya karya keSewa ya yi a Wakinsa shi kaWai kamar"

maye yana tunani. Wannan kaWaicin shi ya ke tuna masa da abinda ya rasa lokacin da ya ajiye takardar

aikinsa. Kafin ya dawo Nigeria bai san komai ba sai tu™in jirgi. It's all he ever knows. It's all he ever wants.

Tun yana yaro yake son jirgi. Ko a toys Winsa jirgi ya fi so. Yana shekara takwas ya tabbatarwa iyayensa

cewa Pilot ya ke son zama idan ya girma. Yana gama Secondary School Daddy ya tura shi Oxford Aviation Academy ya fara Pilots training a can. Yana samun Commercial Pilot License Winsa ya samu aiki da British Airways a matsayin First Officer. Shekara da shekaru yana aiki da su har ya excelling zuwa Senior First Officer. Lokacin da ya samu Airline Transport Pilot License (ATPL) Winsa kuma aka promoting Winsa zuwa Captain.

Shi Captain ne for good 5 years kafin wannan accident Win da ya faru shekaru uku da suka wuce wanda

ya chanja komai na rayuwarsa.

"Ranan Alhamis ne, ba zai taSa mantawa ba. Yana iya tariyo abinda ya faru tiryan-tiryan kamar yau abun"

ke faruwa...

***

SHEKARA UKU DA SUKA WUCE

Captain Jalal Maiya™i yana shiga cockpit wajen zamansa a cikin jirgi ya fara yin system checkings na

"™arshe. Bayan ya gama duba komai tun daga flight plan, har zuwa adadin fuel levels da ake da shi. Sai ya fara addu'o'in da ya saba duk lokacin da zai tashi."

Wayarsa ce ta yi vibrating yai kamar ba zai duba ba sai kuma ya ciro wayar yana tunanin wata™ila Jamal

ne ya ke son faWa masa cewa ya isa Abuja lafiya.

Bai kamata ya duba wayarsa a wannan lokacin ba. Bai kamata ya amsa waya ba a irin wannan lokacin.

Amma ganin sunan Wan'uwansa ke kira sai ya ce bari kawai ya Wauka ya faWa masa zai kirashi idan suka sauka.

"Lokacin da ya Wau kiran maimakon muryan Jamal sai ya ji muryan wani yana faWin ""Hello, Hello, Allah"

"yiwa mai wayan rasuwa. Muna hanyar Asibiti da sauran waWanda suka yi hatsarin amma shi mai wayar ya cika ku samemu a Asibitin..."""

"""Captain"" Copilot Winsa ya kira shi."

A birkice ya juyo ya kalleshi ™wa™walwarsa bai gama processing abinda ake faWa masa ba.

"""Are you Okay?"" Copilot Win ya tambaya."

GyaWa kai ya yi ya mayar da hankalinsa wajen jirgin yana kashe wayar tasa gaba Waya.

Hankalinsa rabuwa ya yi kashi-kashi. Waye ya kira shi da wayar Jamal? Wani irin prank zai masa da cewa

wai mai wayar ya rasu. Ina Jamal ya ke?. Sun yi waya da Jamal jiya da daddare akan zai je Abuja gidan Uncle Winsu wajen matar da zai aura sati uku masu zuwa.

Har ya yi taxi a runway aka bashi clearance suka tashi hankalin Captain JK Maiya™i baya jikinsa. Tarin

tambayoyine marasa amsa suka cika masa kwanya.

A haka dai ya cigaba da tu™a jirgin har Allah ya kaisu lafiya. Sai dai saboda bashi da nitsuwar zuciya sai ya

yi misjudging altitude ya sauka da sauri wanda hakan ya sa jirgin ya bugi ™asa da ™arfi har sai da tayoyin jirgin suka fashe. Fasinjojin jirgin suka ruWe kowa ya fara ihu. Babu wanda ya ji ciwo amma kowa ya tsorata da fashewar tayar hatta sauran Crews Win dake cikin jirgin sun Wan girgiza.

Emergency crew ne suka shigo da sauri aka fara duba mutane ana fito da su a hankali

"""Are you okay, mate?"" Copilot Winsa ya tambaya yana dafa kafaWarsa."

Captain Jalal ya gyaWa masa kai. Wayarsa ya ciro ya kunnata. Numbar Jamal ya sake kira amma sai ya jita

a kashe. Nan fa hankalinsa ya sake tashi. Ya kira numbar Hajiyarsu amma ba a Wauka ba. Numbar Uncle Idris ya kira ya kuwa ci sa'a aka Wauka. Sunan Jamal ya fara ambata yana tambayar ko ya isa Abuja lafiya. Daskarewa ya yi a wajen lokacin da ™anin mahaifinsu ke faWin Allah ya yiwa Jamal rasuwa motarsa ta yi hatsari. Har Airline safety officers suka zo suka tafi da shi for questioning komai duhu ya ke gani.

"Jamal ya rasu kaman yaya? Jamal fa, Jamal ™aninsa, his best friend, his best buddy."

Tambayoyin da officers Win suka masa da kuma wayarsa da aka karSa ne aka gano cewa already kafin a

tashi maganar mutuwar Wan'uwansa da aka masa ya taSa shi. Nan take aka bashi temporary suspension for negligence.

"Bayan ya gama serving suspension Winsa sai ya applying zai dawo tu™i, amma Aviation Authorities suka"

"hana shi dawowa saboda lokacin da aka masa Medical assessment an tabbatar yana fama da depression saboda rasuwar Wan'uwansa kuma ya ™i ya je ya yi therapy. Saboda mahimmancin Aviation Safety Laws sai aka ™i mayar masa da license Winsa na tu™in jirgi. Option Win aiki off-air suka bashi, suka ce ya koma Sangaren Air Traffic control ko kuma Flight Instructor amma ya ™i. Wannan ya sa shi rubuta resignation letter ya basu."

Shekara uku da suka wuce kenan da faruwar hakan. Bayan ya ajiye aikinsa ne ya dawo Nigeria saboda ya

"kula da Kamfanin da mahaifinsa da kuma ™aninsa suka bari. It was not easy for him. Kula da kamfani, matsalar aurensa, surutun Hajiya, da kuma rayuwa da sanin cewa Jamal ya tafi kenan ba zai sake dawowa ba..."

CHAPTER FIVE

ZEEY

A gajiye na shigo gidanmu da yammacin ranan Lahadi. ˜arfe biyar da kusan minti arba'in da tara kenan.

"Daga GRA nake gidan Hajiya Maryam da nake koyawa 'yarta girki. Two weeks kenan da fara class Win kuma saura sati biyu mu gama, dama class Win na wata Waya ne, duk weekend muke yi."

"Ba laifi Hayfa ta fara sake fiska da ni, and tana Waukan class Win serious saboda Hajiya da ta kasa ta tsare"

"akan sai ta koya. Hasashena ya yi gaskiya, Hayfa bata son mutumin da za ta aura. From 'yan maganganun dana tsinta a zuwan da na yi gidan na fahimci akwai wacce Hayfan ke so amma iyayenta basa son shi. Kamar dai Saurayin ba shi da kuWi ne. Shi kuma wannan da ake ™o™arin molding masa Hayfa saboda ta"

fitting irin macen da ya ke so tabbas ba ™aramin mai kuWi bane duba da cewa su Hajiya Maryam ma suna

da kuWin babu laifi amma suna so su yi abinda zai faranta masa rai.

Girki a wajena ba abun wahala bane duba da cewa tun banida wayo na ke yi. Amma a wajen Hayfa da ta

"tashi da masu yi musu aiki a gida dole ta kalleshi a matsayin aikin wahala. And a fahimtata cuisine Win turawa ta ke son ci har ma ta ce min ta iya dafa dayawa daga ciki. Amma dangin Tuwo namu na gargajiya bata iya ba, dan ba ci take ba."

Hayfa ta bani tausayi. Aure za ta yi saboda biyayyar iyaye ba wai saboda soyayya ba. Nima mai maganar

"ban san wani irin aure zan yi ba idan lokaci ya yi. Currently bani da Saurayi, and technically mutum Waya na taSa soyayya da shi. Ba zan ce babu masu sona ba, cikin mutanen Anguwa, School, har ma da masu bina DM suna mini tayin soyayya. But right now gaskiya ban shiryawa soyayya ba, balle kuma aure."

"Ban sani ba ko zan iya soyayya a gaba ba, amma a yanxu soyayya shine ™arshe cikin lissafina."

At 24 na sani da na ™are Makaranta su Baffa Lawalli za su min chaaaa! akan maganar aure. A yanzunma

dai ana kan yin maganganu ™asa-™asa akan na ™i aure na sako Boko da neman kuWi a gaba.

"Sai dai fa su yi ha™uri, dan ni da batun aure sai na cimma burina na mallakar Restaurant a garin Zaria..."

Ina shiga sashenmu dana ga wani ba™in takalmi da ya lotse ta tsakiya a ™ofar Wakin na san Umman Fada

ce ta zo. Umma Halima ita ce ™anwar Babana da suke uwa Waya uba Waya. Tana auren wani Bafade a cikin Fadan Zazzau shiyasa kowa ke kiranta Umman Fada.

"Da Sallama na shiga Wakin, na tadda Umman Fada tana cin tuwo. Tulelen cikinta dana gani ya sani"

mamakin wannan rashin lissafin irin nata. Ga shi nan fama suke da mijinta amma sai zubo 'ya'ya ta ke. Yanzu wannan cikin idan ban manta ba haihuwa na bakwai ko na takwas kenan.

"""Ziyadatun, idonki kenan?"" Ta faWa tana suWe hannunta."

Umman Fada da Baffanmu Adamu da ke Katsina ke kirana da ZIYADATUN.

Ance Babana ya saka mini suna ZIYADA ne saboda na yi tsawon rai. Lokacin da iyayena suka yi aure ba a

damu da gwaji kafin aure ba. Wata™ila da sun yi gwaji da sun gano cewa dukkansu AS ne wanda hakan

ke nuni da cewa akwai high chance na za su haifi 'ya'ya masu sickle cell.

Kafin a haifeni sai da Ummana ta haifi 'ya'ya uku suna mutuwa. Bayan ta sake yin wani Sari sai aka samu

cikina.

Kaka ta ce lokacin da aka haifeni Babana babu abinda ya ke faWa sai addu'ar na yi tsawon rai.

"Lokacin da Ummana ta ke haihuwa suke mutuwa babu abinda ba a faWa ba. A ce Aljanu, a ce jifa, a ce"

"mayu, kai har cewa aka yi Kaka ce ke cinye yaran. Sai a yaro na uku da aka haWa da Asibiti kafin aka tabbatar musu yaron sickler ne. Kafin ni babu yaron da ya kai shekara biyu cikin 'ya'yan da suka haifa. Shiyasa lokacin da na cika shekara uku ba ™aramin murna iyayena suka yi ba, duk da kuwa lokacin haihuwata an tabbatar musu a Asibiti cewa ni AS ce ba Sickler ba kamar sauran."

Kafin na cika shekara huWu Umma ta sake haihuwa. Sulaiman sunansa. Iya abinda zan iya tunowa

gameda Sulaiman shine kullum bashi da lafiya. That's the only memory da nake iya tunawa akansa.

"Bayan rasuwan Sulaiman zaman iyayena sai ya ™i daWi, ™arshe har ya kai ga saki. Kaka ce ta ri™e ni"

yayinda Babana ya ke gwada mini tsantsan soyayya. Har Private School ya sakani maimakon sauran yaran gidan da suke zuwa Makarantar Gwamnati. Shekara Waya da rabi da rabuwan iyayena ko wani auren Babana bai yi ba Allah ya masa rasuwa. Hatsarin mota. Dama Babana Direba ne...

Wanka na yi na chanja kaya zuwa wata doguwar rigan material mai hannun shimi da nake sawa a cikin

"gida. Fitowa na yi ™ofar Waki na joining Kaka da Umman Fada akan tabarma, cikin akwai zafi, NEPA sun"

Wauke wuta.

Umma ta ce yaushe zan je wajen Umma a Kaduna na ce mata kafin Azumi zan je idan muka gama bikin

™awata Faty.

Sai bayan Isha Umman Fada ta tafi ita da zugan 'ya'yanta guda huWu da ta zo da su. Bata tafi ba sai dana

"bata cash Win dubu biyu da al™awarin zan aika mata dubu biyar ta account Win babban Wanta. Na tambayeta ina account Winta da Yaya Aminu ya buWe mata farkon fara aikinsa da Bankin FCMB, tace mini wai account Win ya samu matsala an rufe."

"Na rakata har bakin titi bayan ta yiwa sauran 'yan gidan Sallama, na tara mata Keke na biya kuWi sannan"

na juyo.

Ina shigowa wani Wan gidanmu ya biyoni wai ana min magana a waje. Sharewa na yi dan na san ba zai

wuce Waya daga cikin 'yan zaman Majalisa dana wuce bane. Bani da lokacinsu.

Ina alwalar sallar Isha Faty ta kirani. Kaka ta mi™o min wayar na karSa ina ™o™arin swipping in Wau kiran

amma ruwan da ke yatsata ya hana shi yi. Na goge hannuna a jikin rigana amma kafin na Wauka kiran ya yanke. Sake kiranta na yi dan na san ta yi fushi dani. Yau ya kamata in rakata Kasuwa amma saboda zan je gidan Hajiya Maryam na ce mata ta yi ha™uri.

"""Bestie dan Allah ki yi ha™uri, yanzu na ke cewa Kaks dana yi Isha ke zan kira sai kuma kika rigani"""

"Ta ce ""ba wani, cewa fa kika yi daga GRA gidanmu za ki zo amma na ji ki shiru har dare"""

"""Sorry, Bestie Wallahi ban bar gidan da wuri bane, kuma ina zuwa gida na tarar Umman Fada ta zo"""

"""Yanzu dai ki yi sallah sai ki kirani mu yi magana"""

"""Ki ce akwai labari kenan"""

Kafin na ™are maganar ma ta kashe wayar.

Sake alwala na yi daga farko dan ban san daga ina na tsaya ba.

Bayan na yi sallah mun fi minti arba'in muna whatsapp call da Faty. Rikicin da suka yi da wasu Anties

"Winta akan siyayyar da ake ta ke faWa min, wai ita ce za ta yi aure amma duk abinda za a siya ba choice Winta ake dubawa ba sai abinda suka ga dama suke siya. Na dai bata ha™uri na ce mata dama biki ya gaji haka. Na ce mata ta bari gobe za mu haWu sai mu ™arisa maganar."

Social media pages Wina na shiga ina ta reply comments Win mutane da duba DM's Wina. Sai dana ji na

fara kallon rubutu bibbiyu kafin na ha™ura na ajiye wayar na fita na je na yi fitsari na dawo na ja mana ™ofa na saka sakata na kwanta akan gado. Tsohuwata tuni ta yi bacci abinta. Lokacin dana rufe idona maimakon bacci sai lissafin kuWaWen dana tara da kuma wadda na ke shirin tarawa suka fara zuwa mini. Na fara plus da minus na kuWaWen da ke accounts Wina.

"Bikin Faty zai ci min kuWi, but it's worth it. Faty ta worthing ko nawa zan kashe mata. Azumi ya kusa, zan"

yiwa Ummana cefanen Azumi ga kuma kayan sallah da zan mata da ita da ™annena biyu da ta haifa bayan ta sake wani auren a garin Kaduna. Ga ™ananun bani-bani daga 'yan gidanmu.

"Wash! Allah ya cigaba da buWa mini kawai, ina Wan samun kuWin amma bu™atun sun yi yawa."

Ina ta lissafi har bacci ya Waukeni ba.

***

JAYKAY

Breakfast suke yau safiyar Monday shi da Hajiya da Janan da kuma Junior da shima ya ke cikin uniform

zai tafi Makaranta.

Wayarsa ce ta fara ringing.

C. MARIA da ya gani a jikin screen Win wayar ya saka shi Waga ido ya kalli Hajiya wacce hankalinta ke kan

"abincin data ke ci. Mi™ewa ya yi ya Wau wayar tareda barin wajen dinning Win. Kwana nawa kenan yana so ya yi magana da Cassandra amma bata bashi dama ba, daga ta ce tana meeting da client Winta sai kuma ta ce ta gaji za ta kirashi idan ta huta."

"""J Love"" muryanta ya doki kunnensa lokacin da ya ce 'Hello' bayan ya koma falo can nesa da su Hajiya"

kada su jiyo shi.

"""I'm sorry J Love, I've being meaning to call you, I was just super busy, work has..."""

Katseta yai ta hanyar faWa mata cewa zai je office idan ya samu dama zai kirata su yi magana.

Lokacin da ya koma dinning ya zauna suna haWa ido da Hajiya ya ji gwiwarsa ta yi sanyi. Yadda ta kalleshi

ya san ta fahimci da Cassandra yai waya.

Bata ce komai ba amma gaba Waya sai ya ji ya rasa appetite Winsa. Tea kawai ya kurSa ya mi™e ya ce zai

wuce office.

"""Yaya Jalal ka jirani mu tafi tare pleaaaase"" Janan ta faWa tana rushing abincin da ta ke ci."

"""Ki zauna ki ci abincinki a hankali, ba kina da motarki ba"""

"Hajiya ce ta yi maganar. Janan ta ce ""Na manta ban ce Isa ya kai min wajen Mechanic ba, jiya da nake"

"dawowa daga Mall ta bani ciwon kai kafin ta tashi"""

"""5 minutes"" Jalal ya faWa sannan ya bar wajen."

Bai kai ma lokacin ba Janan ta fito suka shiga mota Driver ya wuce da su Kamfani. A cikin motar hankalin

"Janan na kan wayarta yayinda na shi hankalin ya tafi zuwa neman mafita wa kansa gameda aurensa da Cassy. Dole ne su nemi mafita mai Worewa, wannan rayuwar da suke ba rayuwane da za a kira shi da aure ba. Ko lokacin da ya ke Captain da baya samun isashshen lokaci duk sanda ya samu hutu baya wasa da zuwa wajen matarsa da Wansa. But this! This is different. Zaman da suke yanzu it's like kowa zaman aikinsa ya ke yi. Shi ba zai iya barin Nigeria ba saboda Kamfaninsa, sannan itama Cassandran ta ce ba za ta iya barin Fashion brand Winta ba, and certainly ba za ma ta iya zama a Nigeria ba."

There has to be a way. Ba zai samu mafitar wannan matsalar ba har sai dukkansu sun cire son zuciya...

CHAPTER SIX

ZEEY

Hassada mugun ciwo. Yau ina shiga sashen Baffa Lawalli sai na ga abin mamaki. Cousin Wina Mardiyyah

ce ta ke content irin nawa. Taliyan murji za ta dafa kuma uwarta ce ke ri™e da wayar Vivo na Mardiyyan tana recording komai. Yara sun tafi Makaranta dan haka sashen nasu ya yi shiru. Nima Kaka ce ta aikoni in karSi abu a wajen Maman Suwaiban da babu abinda zai kawoni.

Ikon Allah! Tunda Ziyada ta fara samun alkhairi da girke-girken Hausawa da ta ke nunawa ai dole suma

su fara ko za su samu kuWin da ta ke samu.

Hmm! Allah ya basu sa'a.

"Ina ga mantawa suka yi shekarana huWu ina yin food content bana samun komai, sai wata shida da suka"

wuce da Allah ya Waukaka min abin kafin na fara samun alkhairi.

Ko magana ban musu ba na faWi sa™on da ya aikoni na karSa na wuce. Mardiyyah sai wani rarraba idanu

ta ke irin na kamata red-handed Winnan.

"Ba yau ta fara kishi da ni ba. Tun lokacin soyayyarmu da Yaya Aminu ta saka mini ™ahon zu™a, a wai wai"

"da nake ji wai itama son shi ta ke. Ba sa'ata ba ce, dan zan iya bata 2yrs ko ma ya fi. Shekaranta huWu kenan da gama Sakandare, ba Makaranta, babu komai. Though na ji an ce tana koyan Winki yanzu."

Ina komawa sashenmu na faWawa Kaka abinda na gani. As usual Kaka bata Wau abin da zafi ba sai cewa

"ma ta yi "" kowa rabonsa zai ci. Allah ya basu sa'a"""

"""Kaks, kin san fa hassada suke min saboda sun ga na fara samun alkhairi"""

"""Ziyadatu kenan, na san me kike tunani ai. Kin san mutane nawa suka fara sai da Tuwo a gidan nan"

bayan na fara sun ga ina samun alkhairi. Ba a cikin gidan nan bama hatta a layinmu zan iya irga miki

"mutane uku da suka fara sana'ar Tuwo bayan na fara. Daga ™arshe wa kika tashi kika gani yana sana'ar?"""

"""Ke"" na faWa saboda tun da na taso ita kaWai na gani tana sana'ar Tuwo."

"""To kin gani"""

"She's right. Mardiyyah za ta iya fara food content saboda ta ga ina yi, amma wannan ba zai hanani"

"cigaba da samun Waukaka a harkar ba, na riga na yi mata nisa."

"""Yanzu Kaka sanda kika fara tuwo a gidan nan sai da aka samu wanda suka fara sana'ar? Baaba Tabawa"

"ce ko?"""

"Kaka ta yi murmushi ta Santari goron dana karSo mata daga wajen Maman Suwaiba ta ce ""ke dai bari"

"kawai. Komai me wucewa ne, ba ga shi ya wuce ba"""

"""Ya wuce kam. Amma ni dai sai kin bani labarin komai idan na dawo daga gidansu Faty"""

Black hand bag Wina na Wauka na mata sallama na fita. Kaka kenan. Ita sam bata da hayaniya. An ce babu

"irin muzgunawar da Uwargidanta bata mata ba. Mahaifiyarsu Baffa Lawalli ta rasu lokacin ina JSS 2. Masifaffiyar mata ce ta ™arshe. Baaba Tabawa ake kiranta. Ita ce Uwargida a wajen Kakana Malam Haruna, an ce tsabar yadda ta hana shi ™ara aure bai iya auren 'yar Zaria ba sai a Kano yai nemansa a Soye har magana ta faWa ya auro Altine ™anwar abokinsa."

"Baaba Tabawa ta haifi 'ya'ya bakwai, Waya ya rasu tun yana jariri. Umma Hadiza ita ce babba, sai Baffa"

"Lawal, Baffa Adamu da ke Katsina, Baffa Mamman, Baffa Zakari da kuma Umma Binta."

"Ita kuwa Kakata Altine 'ya'yanta biyu ne suka yi tsawon rai, Babana da kuma ™anwarsa Halima. Sauran"

tun suna jarirai suke mutuwa. Wata™ila suma Sickle

Please Login or Register in order to submit comment