You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haihuwar ma dai bai chanja komai ba, Matar dana samu da ita kuma"

itama wata ™azamar ce tunda ta ™i tsaftace gidan. Dana shiga Wakinta kaman zan yi amai saboda ™arni.

Subhanallahi!.

Faty ta ce Dan Allah na zo mata Suna. Wai na yi ha™uri na manta da abubuwan da suka faru mu koma

"kamar da. Wai yadda na yi ta shige da fice a bikinta na daure na zo a yi hidimar suna da ni. A take na ce mata ta yi ha™uri Jalal ya ce ba zan zo Suna ba, daga Barka shikenan. ASTAGHFIRULLAH nima na shiga sahun masu ™arya da sunan Miji. Jalal bai hanani zuwa Suna ba, dana ce masa zan zo mata barka ne na ce ina ji ba zan je Suna ba, sai bayan Sunan zan nemi lokaci in sake zuwa ya ce mini ba komai. Dubu talatin ya tura min in bata na haWa da nawa dubu goman na kawo mata Cash dan na lura kamar Mijinta na da access da account Winta. Na haWo da rigan yara guda biyu dana siya a Plaza da kuma Pampers mai guda hamsin. Ai na mata. Lokacin aurenta ma dana yi ta up and down na kashe kuWi na yi ta zirga-zirga da me ta saka min. Ta ro™eni kuma na yafe, amma maganar BESTIE BESTIE ya ™are kenan kuma sai a wata duniyar idan ana yi..."

JAYKAY

A Sangaren Jalal cikin wata biyu da ya yi a London sun yi zama a Kotu sau biyu akan maganar ri™on Wansa

"Junior. Abinda Cassandra ta faWawa Kotu shine wai zaman Junior a Nigeria akwai hatsari. Tana tsoron saboda rashin tsaro a Arewacin Nigeria Wanta zai iya faWawa hannun Kidnappers ko kuma 'yan Ta'adda, ko kuma ma rikicin rashin tsaro ya jawo masa mummunan Trauma a rayuwarsa. Sannan ta sake gabatar da cewa Jalal ya auri wata matar a Nigeria dan haka baya kula da yaron yadda ya kamata wai baya ma zama da shi a gidan Kakarsa yake zama kuma Kakar yaron bata kula da shi saboda bata son Cassandra. Ta cakuWa ™arya da gaskiya ta faWa. Sai dai Kotu ta yi watsi da maganar auren Jalal saboda baya cikin abinda za su duba tunda case Win Divorce da ake daban da wannan na neman Custodyn Muhammad Junior."

Shi kuma Jalal ya gabatar da cewa yana neman full Custody na Wansa ne saboda Cassandra tana shan

giya (Alcohol abuse). Saboda haka zamansa tare da Cassandra zai iya jawo masa hatsari sannan ya gurSata tarbiyyansa.

Da aka ce ko suna da shaidar cewa tana shan giya ta bugu har ta fita hayyacinta sai Lawyan Jalal ya fito

da wasu takardu ya mi™awa Al™ali.

"""He's my son. Why would I do anything to hurt him?"" Cassandra ta faWa da ™arfi."

Al™ali ya Waga kansa ya tambayeta ko ita ce aka kamata da laifin tu™i cikin maye watanni biyu da suka

wuce.

Cassandra ta zaro ido.

Al™alin ya sake Waga wani takarda ya ce shekara huWu da suka wuce an kamaki da laifin cin zarafin

Sakatariyarki mai suna Jessica Edwards inda Kotu ta sa kika biyata taran kuWi Euro dubu goma shabiyar.

"""It was a mistake, your Honour"" Cassandra ta faWa a ™o™arinta na son kare kanta."

Al™ali ya cigaba da kallon takardun da aka bashi daga baya ya tambayi ina yaron yake aka ce yaron yana

waje tareda Kakarsa. Ya ce a kawo masa yaron Chamber sa zai gana da shi...

CHAPTER FIFTY SEVEN

"""Darling, you have to choose me, okay?"" Cassandra ta faWa da ™arfi lokacin da aka wuce da Junior ta"

gabansu.

Jalal ko War bai ji ba da yadda Cassandra ke ro™on Junior ya zaSeta ba shi ba. Ya riga ya san yadda yaron

ke son Hajiya ba zai amince ya cigaba da zama wajen Mamansa ba.

Amma duk da haka sai ya fara addu'ar samun nasara a ransa. Allah ya tabbatar masa da burinsa. Ita

kuwa Cassandra sai sintiri take a wajen. Ba zai yiwu ta rasa Wanta sannan ta rasa Jalal ba. Divorce petition Winsu yana gaban Al™ali kuma yadda Jalal ya WaWWaureta da cewa idan ta ™i amincewa da sakin zai nemi rabin dukiyar data samu bayan aurensu sai ta fara saduda da lamarin. Duk abinda ta samu ta same shi ne bayan aurensu da Jalal dan haka idan Lawyansa ya bu™aci a raba dukiyartata biyu a bashi rabi a matsayin compensation ko Alimony babu yadda za ta yi.

"Idan har babu wanda ya janye Sakin tsakaninsu ya tabbata kenan wata shida bayan shigar da ™aran,"

aurensu zai warware. Yanzu saura watanni uku da kwana goma shaWaya aurensu ya ™are.

Bayan minti talatin da shigar Junior chamber Al™ali sai aka kirasu. Suna shiga Cassandra ta yi kan Junior

za ta rungumeshi yaron ya yi sauri ya faWa jikin jalal ya ™an™ameshi. Tunda Cassy ta Waukeshi daga Nigeria sai yau ya ga Babansa ido-da-ido.

Lokacin da Jalal ya gano yaron na wajen Maman Cassandra Lawyansa ne ya ce ya barshi a can saboda su

samu hujja a gaban Al™ali na cewa Cassandra ta hana shi ganin yaron.

Abinda yaron ya yi sai ya sake tabbatar wa mutanen da ke wajen cewa Jalal ne zaSinsa.

Dukkansu suka kasa kunne lokacin da Al™ali ya fara karanto hukuncin da Kotu ta yanke.

"""The Court awards full custody of MUHAMMAD JALAL MAIYA˜I, age nine, to his father, Mr. Jalal Kabeer"

"Maiya™i"""

"""NO...Nooo"" Cassandra ta yi ihu tana mi™ewa."

Lawyanta ne ya zaunar da ita yana cewa ta kwantar da hankalinta a gama karanto hukuncin Kotun.

Shi kam Jalal tunda Al™ali ya ce ya dam™a masa gabaWaya ri™on Wansa sai ya fara Hamdala a zuciyarsa.

"Al™ali ya cigaba da bayani, inda ya bawa Cassandra damar zata iya zuwa ganin Junior a Nigeria a duk"

lokacin da ta ke so amma sai da izinin Jalal. Sannan sau biyu a shekara dole ne Jalal ya tura yaron hutu wajen Cassandra har zuwa lokacin da yaron zai cika shekara 18 ya zaSi inda zai zauna da kansa.

Jalal kam ba shi da matsala da wannan tsarin. Dan dai sau biyu a shekara ya tura mata Junior hutu ai ba

komai bane. Dama ri™on yaron ya dawo hannunsa shine cikar burinsa.

Shi da Lawyansa suka tsaya cika takardu yayin da Cassandra ta tsugunna gaban Junior tana masa masifar

"me ya faWawa Alkali lokacin da ya tambayeshi da wa zai zauna. Yaron ya yi shiru bai amsa ba. Da ta ga ya tsorata da yadda take masifa sai ta kwantar da murya ta fara cewa ""I'm going to be a good mother from now on. I won't yell at you again, I promise. Please stay with me, okay"" sai kissing Winsa take tana jaddada cewa za ta Waukaka ™ara ta karSe shi, ba za ta bari ya koma Nigeria ba."

Lokacin da Jalal ya fito daga office Win Alkali ya zo zai tafi da Junior sai Cassandra ta rike yaron tana

masifar ba zata bari ya tafi da shi ba.

"""He's my son"" ta faWa da ™arfi kamar za ta yi kuka."

Sai da Lawyanta ya jata gefe ya mata magana sannan ta ha™ura ta sakewa Jalal Junior.

Maman Cassandra ta ce za ta aikowa Jalal kayan yaron gidansa. Ya ce mata Passport Win yaron kawai

yake bu™ata.

"""Dad, ka kaini wajen Hajiya"" Junior ya faWa lokacin da suka shiga mota."

"""Zan kaika wajen Hajiya, da Janan, da Zeeyadah, da kowa ka ji"" ya faWa yana kissing goshinsa."

"Matseshi ya yi a jikinsa kamar za a ™wace masa shi a cikin motar, a haka har Lawyansa ya sauke su a"

Family house Winsu na London...

***

ZEEY

"Wallahi idan kana business ko, idan Staff ba su sa maka hawan jini ba za su iya haukatar da kai."

Jiya-jiya aka yi case Win wani Waiter Winmu da yake karSan kuWi a personal account Winsa a VIP section

Winmu.

Wai ashe idan za su biya kuWi sai ya ce musu POS Winmu na Gidan Girki yana da matsala zai bada account

"su tura kafin a gyara. A irin haka a irin haka sai da ya rafke kuWi ya kai dubu Wari biyu da talatin ba a gane ba sai jiya da wani ya kira Manager ya ke ™orafin ta ya zai biya kuWi a account Win waiter ba Account Win Restaurant ba. Shine fa Jide ya ankara ya ri™e yaron ko sunansa ban sani ba sai jiyan, wai Kelvin."

Yau kuma na shigo na samu ana case wai an kama Kitchen Staff Wina Majida tana satan kayan abinci da

Ingriedients Win Kitchen.

Kaina ya Wau zafi da aka faWa mini. Lokacin da aka Wauketa na ganta shiru-shiru da ita har nake cewa Jide

yarinyar tana da hankali ashe-ashe.

Da Jide ya tsareta da tambayoyi me yasa ta ke satan mana ingriedients da spices bata bamu amsar

"gaskiya ba sai da ta ji zancen za a kira mata Police, Waiter da aka kama jiya ma yana hannun 'yan Sanda har yanzu."

Farko ta ce mana gida take kaiwa saboda gidansu akwai matsalar abinci da ta ji an fara karanto Hadisan

'yan Sanda sai ta ce wai content ta ke yi da shi tana da TikTok da Instagram page. Ai kuwa da aka duba Majida's Meals a TikTok sai ga ta nan har da followers dubu biyu. Ikon Allah!. Ba ka da gashin wance ka ce kitson wance za ka yi. Ni sadda na fara food content Wina da iya abinda Allah ya hore mini nake yi. Da murhun itace na fara na koma gawayi kafin na fara amfani da gas cylinder dana siya mana. Da naga ma an fi samun engagement idan na yi girki a murhu sai na fi yi da shi.

Rasa ma me zan faWa mata na yi. Na barta da Jide su je can su ™arata. Ba za su samin hawan jini ba ana

zaune ™alau.

"Washegari ina zaune a office Wina sai ga Jide, ya ™wan™wasa min ™ofa ya tsaya daga bakin ™ofar ya ce"

"""Big Madam, ana son ganin ki""."

"""Dan Allah Jide kar ka ce wani rikicin ne ya sake Sullowa. Na gaji"". Na faWa ina murza goshina."

"Dariya ya saka yana faWin ""barin turo miki shi"""

Maida hankalina kan ™ofar na yi ko sakan biyar ba a yi da fitan Jide ba sai ga shi an buWe ™ofar. Wa zan

gani face mutumin dana ke mafarkin ganinsa a kullum

JALAL. JAY Wina.

Ban san sadda na mi™e tsaye ba ina tunanin shi Winne ko ba shi bane. Na ™urawa fiskarsa ido ban ko

™yafta ba.

Takowa ya fara yi a hankali yana nufoni bugun ™irjina yana ™aruwa.

Har yanzu kallonsa nake na kasa magana. Na kafe shi da idanuna wanda ya sakani lura da wrinkles Win

daya taru masa a gefen idanunsa.

Matsowa ya yi kusa da ni idanunsa suka sauka akan lips Wina. Na san me yake shirin yi kuma ina maraba

"da hakan, ilahirin jikina yana maraba da taste Win lips Winsa akan nawa, yaushe rabon?."

Na Wan buWe bakina and kafin na gama bashi access tuni ya haWe bakinmu ya shiga kissing.

"Na faWa jikinsa na saka kuka bayan ya raba kiss Win. Dukan ™irjinsa na fara yi ina faWin ""shine ka tafi ka"

"barni ko waiwayowa baka yi ba. Shine ka tafi ka barni saboda saboda..."" ya rufe min baki da nasa na yi shiru ina mayar masa da zazzafan kiss har da tallafo kansa sosai."

Jiya da dare fa mun yi chatting kuma bai ce min zai shigo Nigeria ba.

Sake narkewa na yi a jikinsa ina sha™ar daddaWan ™amshinsa.

I Love Him.

"I Love JALAL so much. Na faWa a zuciyata a dai dai lokacin ya furta min ""I MISS YOU SO MUCH, Sunshine"""

na ji wasu ™walla sun zubo mini.

Mantawa na yi a ™aramin office Wina muke.

Mantawa na yi da muryoyin mutanen da ke shige da fice cikin Restaurant Win.

Mantawa na yi da cewa watanni kusan uku baya na yi i™irarin dena son shi.

All that matters shine ya dawo gareni. Ban san me ya dawo da shi ba. Ko ya samu abinda ya je nema ko

bai samu ba.

Kai koda a ce idan na je gida yanzu zan samu Cassandra da gaba Waya danginta a gidan ba zai chanja

"cewa ina son Mijina ba, kuma na shirya nuna masa soyayyar Aure."

Ya tattaro fiskata ya ri™e zuwa lokacin hawaye ya gama Sata mini fuska.

"""Please ki dena kuka. Bana son ganin hawayenki"""

Ya kissing tsakiyar goshina da kuma karan hancina sannan ya fara goge min hawayen.

**

"""Shine ba ka ce min za ka dawo yau ba"" na faWa a shagwaSe lokacin da muka shiga mota zai kai mu gida."

Yo! Me zan tsaya na yi a Restaurant bacin Mijina ya shigo gari.

"""Saboda na ga soyayyar dana gani a ™wayar idanunki Wazu"""

"""Ni babu abinda ka gani a idanuna"""

"""Aka ce ido dai baya ™arya kuma sun fallasa sirrin dake cikin zuciyarki"""

"""Babu wani sirri a zuciyata. Kai dai ka sake binci™e"" na faWa ina juyar da fiskata."

"Kamo hannuna Waya ya yi ya haWe yatsunmu ya ce ""abinda na ke ji gameda ke ya fi abinda na gani a"

"idanunki, Zeeyadah"" ban juyo ba amma murmushin da ya suSuce min ya fallasa tasirin kalamansa a zuciyata."

Gaskiya tafiyarsa London akwai alkairi tunda yanzu ya koyi bayyana abinda ke ransa.

Muna shiga falon gidanmu ya sake rungumata sosai kamar an ce masa zan gudu. Kafin na ankara mun

"fara kissing junanmu kaman wanda an ce daga yau ba za mu sake haWuwa ba. Lokacin da ya Waukeni ya yi sama dani already na manta da batun jan aji na sallama masa kaina, ya yi duk abinda ya ga dama da ni."

Kash! Bai yi abinda nake tunanin ba duk da na ga tsananin kwaWayin hakan a idanunsa.

Kwanciya muka yi a gadona muna mayar da numfashi bayan ya birkitani da rikitattun kisses Winsa.

Sai dana fara dawowa hayyacina sannan na tambaye shi ina Junior?. Ya ce min yana wajen Hajiya.

"""Alhamdulillahi"" na furta a fili."

Can ya tashi ya ce min yana zuwa. Ina ga Wakinsa ya je bayan kamar minti uku sai ga shi ya dawo. Copy

ne na takardar yarjejeniyar Custody Win Junior da aka bashi.

"Ban tsaya karanta dogon turancin da ke jiki ba nace ""yanzu shikenan kai zaka ri™e Junior?"" Ya gyaWa min"

kansa.

"""Masha Allahu. Allah ya kaWe fitina ya baka ikon ri™e shi da Amana"" ya amsa min da Amin."

Divorce Petition na gani Saro-Saro a takarda na biyu da ya bani. Na Waga ido ina kallonsa dan ban san me

hakan ke nufi ba.

"""Maganar rabuwata da Cassandra yana Kotu. Ina da sauran wata uku kafin auren ya warware gabaWaya"""

ya yi min bayani.

Ikon Allah. Allah Waya gari banban. Yanzu dai saboda auren Kotu suka yi dole dai sai kotun ce za ta raba

su.

Wai yanzu a 'waiting period' suke. Idan waiting period ya ™are shikenan Kotu za ta bada Final Order

wanda shine lasisin raba aurensu. Daga nan Jalal Maiya™i da Cassandra Morgan za su kasance ba mata

da miji ba.

"Yayinda mu a nan Aure ke rabuwa da kalmomi uku rak! NA SAKE KI. Shi Bature, ko in ce Auren Kotu yana"

da na shi tsarabe-tsaraben.

Bayan Maghriba muka je gidan Hajiya dan na yi mata Barka. Dake Janan bata nan ita Waya muka samu da

shalelen jikanta Muhammad. Mun samu yana kwance a jikinta wai ashe wai tunda Jalal ya kawo shi ya ™i

barin jikinta.

Itama Hajiyar har fara'arta ya dawo sosai.

Allah Sarki sai dana ga rama a jikin yaron. Ashe ba ubansa kaWai ne ya rame ba har da yaron.

"""Haka kawai kun Wagawa yaro hankali yana zaman-zamansa. Jibi fa yadda yaron nan ya koma daga Wan"

"wata uku da ya yi baya nan. Kun katse masa Makaranta, kun birkita shi"""

"Haka Hajiya ta yi ta yiwa Jalal faWa, har nima sai da faWan ta shafeni. Jalal dai ha™uri ya yi ta bata yace"

daga yanzu zai ri™a kula da lamarin yaron sosai. Sannan zai ri™a zuwa mana weekend gidanmu tunda dai

Hajiya ba zata sake mana shi gaba Waya ba musamman yanzu da ake gab da auren Janan.

Bamu bar gidan ba sai bayan Isha. Lokacin da muka koma gida bayan mun yi shirin kwanciya ina jikin

Jalal ya kanainayeni sai ya fara bani labarin haWuwarsa da Cassandra.

Dana fahimci bai shirya taSani ba sai nima na sake jiki da shi babu wancan tunanin a raina na buWe

kunne ina jin tarihin rayuwarsa dan ya faro ne daga kusanci da kuma soyayyar dake tsakaninsa da

™aninsa JAMAL.

"""Ban taSa faWawa kowa wannan ba sai ke"" ya faWa sadda ya karanto mini yadda ya biyema Cassandra"

"har ya kwana da ita da yadda ta ce masa tana da ciki da yadda ta saka shi Waukan al™awarin aurenta bayan cikin ya zube. Har zuwa yadda aka kira shi watarana yana shirin tu™a jirgi aka ce masa Jamal ya rasu. Yadda hakan ya jawo ya tafka kuskure lokacin da Jirgi ya zo sauka, da yadda hukumar kamfanin jirgi na British Airways suka bashi suspension suka saka shi yin Therapy na dole. Bayan ya dawo kuma suka ce ba shi da nitsuwar da zai sake tu™a jirgi sai dai ya yi aiki a ™asa shi kuma ya ajiye aikin saboda babu abinda yake so sama da tu™in Jirgi."

Lokacin da ya faWa mini Cassandra ta faWa mishi cikin farko ba nashi bane sai na ji tausayinsa. Koda yake

"™addararsa ce ta zo da hakan, sannan shima har da laifinsa. Da bai kusanceta ba da ba za ta yi masa"

™aryar ya mata ciki ba.

"Kamo hannuna ya yi ya sar™e da nasa ina jin nauyin da numfashinsa ya yi, abubuwan da ya faWa sun taso"

masa da ciwon da yake fama da shi shekara da shekaru.

"""Na san ban kyauta miki ba, Zeeyadah"" ya yi shiru."

""" Ni da kike gani MATSORACI ne"" ya faWi kalmar matsoraci da Wacin abin a muryarsa."

Na fara girgiza masa kai.

"""Shi yasa Hajiya ta ke cewa Jamal ya fini a komai"""

"""Ba haka bane"" na faWa da sauri."

"Ya yi dariyar takaici ya ce ""sai dana kai shekara 40 tukunna na fahimci a rayuwar nan idan kana tsoro ba"

"za ka iya cimma komai ba. Da bani da tsoro da ban yiwa Cassandra al™awarin aurenta ba. Da bani da tsoro dana rabu da Cassandra a lokacin dana shirya zama a Nigeria. Da bani da tsoro, da ban aureki ba sai dana warware Aurena da Cassandra"""

"Ya Wan yi shiru sannan ya ce ""kin san yaushe na fara rage tsoro?"""

Na girgiza kai.

"""Lokacin dana tinkareki da maganar deal Winnan"""

Na waro idanuna waje.

"""Yes, Sunshine. Ke kika chanjani. Kuma har a yanzu ma fushinki da tsoron rasaki shi ya bani ™warin"

"gwiwar rabuwa da Cassandra"""

Ya yi shiru ina jin fitar numfashinsa da bugun ™irjinsa yana ™aruwa. Wani nitsuwa ne yake sauka mini a

yanayin da muke ciki. A yanzu ko shakka babu ya cire min duk wani trace na kokonto da nake da shi akan son da yake mini.

JALAL YANA SONA. TUN KAFIN NA FARA SON SHI.

"""I Love You, Zeeyadah"""

"""Wannan Tsohon kuma matsoracin yana matu™ar ™aunarki"""

"""I LOVE YOU TOO"" na furta a hankali. ""Wannan 'yar Ghetton dai tana sonka sosai"""

Wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke wanda hawaye suka biyo bayan hakan.

Na juyo na fuskance shi na sa hannu na fara goge masa hawayen. Na sani abubuwa dayawa ne suka saka

shi zubar da ™walla. Nadama. Kewa. Soyayya. Da kuma Godiya.

An ce Maza basa kuka.

An ce bai kamata Namiji ya yi kuka ba.

An ce kuka alama ce ta rauni.

"Ni babu ruwana da 'an ce', abinda na sani shine Allah ya halicci ŠAN ADAM da rauni. Kuma babu laifi"

"idan NAMIJI ya zubar da ™walla, a mafi aksari Jarumta ke saka hakan ba gazawa ba."

"""Thank you"" ya furta yana kissing hannuna lokacin dana gama goge hawayensa."

Ban iya bacci da wuri ba. Na buWe idanuna tar bayan Jalal ya jima da bacci. Labarinsa ne ya tsaya mini a

rai. Na dinga jinjina lamarin Allah da yadda yake tsara ™addarar mutane daki-daki har watarana ka ga

™addarar wasu mabanbanta mutane sun haWu waje Waya.

"Wata™ila da ba™ar fata, 'yar Nigeria Jalal ya aura ba Cassandra ba, da ni da shi ba za mu taSa kasancewa"

tare ba.

˜ila shigar Cassandra rayuwarsa ita ce sababin jawo zaren ™addararmu ta haWu waje guda.

"Babu abinda zan ce sai dai na ™ara yiwa Allah Godiya, domin shine Ubangijin da ya halicci ˜addara yake"

kuma jujjuyata cikin ilimin Ghaibunsa wanda babu wani Mahalukin da ya san ya yake abinsa sai shi Win dai JALLA JALALUHU...

CHAPTER FIFTY EIGHT

JAYKAY

Washegari da Asuba Jalal ya tashi zuciyarsa cike da farinciki. Ya ™urawa Ziyadah dake bacci idanu yana jin

so da ™aunarta na ™ara shigarsa.

"FaWa mata labarinsa da kuma sirrin da yake ta Soyewa shekara da shekaru alkhairi ne, gashi ya taimaka"

masa wajen ™ara samun fahimtar juna. Wani sanyi yake ji yana jinsa kamar wani sabon mutum.

Al™awari ya Waukanma kansa cewa daga yanzu ba zai sake Soye mata komai ba. Kuma zai ri™a jaddada

mata irin soyayyar da yake mata.

Ziyada Alkhairi ce a rayuwarsa.

Tun yana London ya kira Janan ya ce mata za a haWa bikinta da Reception Win aurensa da Ziyada. Ai

kuwa sai da ta yi ta ™u™™uni wai zai Sata mata shiri kafin daga baya tace masa babu matsala.

Duk da yana son sake kasancewa da ita amma sai ya baiwa kansa ha™uri zuwa lokaci kaWan da zai

bayyanawa duniya cewa Ziyada matarsa ce.

Mi™ewa ya yi ya shiga banWaki ya Wauro Alwala. Yana shirin fita Masallaci bayan ya yi Nafila Raka'a biyu a

Wakin sai Ziyada ta tashi.

"Da ya dawo daga Masallaci kuwa sai ya samu bacci ya Wauketa akan sallaya, da alama ba ta yi bacci da"

wuri ba jiya. Shi kam rabonsa da bacci mai daWi irin na jiya tun kafin Cassandra ta zo Nigeria.

˜o™arin Waukanta yake ya kaita kan gado ta buWe ido.

"""Ki yi baccin ki"" ta rufe idanunta amma da ya gama shimfiWata akan gadon sai ta tashi zaune ta ce ""Zan"

"fita aiki. In haWa maka breakfast? Me za ka ci?"""

"""Koma ki kwanta. You need to rest"""

"""Ina na ga ta rest. Staff Wina dukka basu da hankali, daga masu satan kuWin customers sai masu sace"

"mana kayan abinci a kitchen. Ni Wallahi har na fara gajiya da business Winnan"""

Ya yi shiru yana kallonta har ta gama bashi labarin abinda ya faru.

Ba maganar sata bane ma matsalar Gidan Girki. Jiya kafin ya je office Winta sai da ya zauna kamar

customer a VIP space Winsu ya bada order dan yaga ya kyawun service Win wajen yake. Yadda Waiter Win

"ya treating Winsa ko haWi babu da yadda ya kamata a yiwa VIP customer. Cewa ya yi a kira masa Manager,"

da Jide ya zo ya ganshi sai ya fara sara masa yana dariya. Sun Wan jima suna magana da Jiden ma kafin ya kai shi wajen Ziyada.

Hanata fita Restaurant Win ya yi ya ce ta kwanta ta huta.

Sai ™arfe tara na safe ta sauko za ta haWa musu Breakfast. Biyota ya yi kitchen Win yana ganin yadda ta ke

ta dibi-dibi tana neman abinda za ta haWa musu.

"""Me za ka ci?. Ko in maka chips da Kifi tunda an ce kana so?"" Ta faWa tana Wan dariya."

"Girgiza kansa ya yi ya tako inda take tsaye ya rungumeta ta baya ya ce ""Ki yi abinda kika saba yi duk"

"safiya"""

"""To...ni fa Wumame na fi ci da safe"""

"""Nima shi zan ci"""

"""Anya zai ishemu mu biyu. Tuwon fa babu yawa"" ta faWa tana buWe fridge."

Bayan minti talatin suka zauna

Please Login or Register in order to submit comment