You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai babu komai,, shigo mu shiga ciki ""."

"Baba ya shiga ciki,, Adamu na biye da shi a bayansa...."

Bayan sun shiga cikin gida. Baba ya k'walama Maman Amina kira ta xo....

"Tazo tace ""gani lafiya dai? Wannan kira haka "".(bata lura da Adamu ba )..."

"Baba ya ce ""lafiya k'alau,, kawomin tabarma da ruwa ""."

"Ta ce ""to ""."

"Ta juya ta shige cikin d'aki,, bata jima ba. Ta kawo masa tabarma da ruwa masu sanyi a kofi..."

"Ta shimfid'a musu tabarma,, har yanzu bata lura da Adamu. Sai da ta ji gaisuwa daga sama. An ce mata"

"""An wuni lafiya Mama "".cike da girmamawa."

"Sannan ta lura da shi,, ta amsa mashi da sakin fuska tare da murmushi..."

"Ta ce ""lafiya k'alau,, ya iyalinka da su Aliyu? ""."

"""kowa k'alau ya ke "".Ya ce mata..."

"Bayan sun gama gaisawa ne, ta mik'e ta shiga cikin d'akin domin ta basu wuri su zanta..."

"Ta tsinkayo muryar Adamu,, yana cewa ""ta dawo wurinsu yazo gaba d'ai...."

"Tadawo,, ta samu wuri ta zauna kusa ga Baba.."

"Bayan ta zauna,, kuma yaga hankalinsu da natsuwarsu duk ya dawo kanshi... Ya kawo labarin komai from"

"A to Z,,, ya fad'a musu ba abinda ya rage daga cikin labarin....."

"""Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Shi ne kalmar da suka fad'a a tare.."

"Sunyi shiru na d'an wani lokaci,,, can kuma Baba ya nisa,,, ya ce ""wannan ba wani abu ba ne,, dama komi"

"ya samu bawa muk'addari ne daga Allah.. Ka fad'a mishi zan samu Yaya Ayuba domin asa lokacin zuwa ganin iyayen yarinyar ""..."

"Adamu ya ce ""to Baba,, kuna ganin hakan ba zai zamo matsala ba ""."

"Baba ya ce ""insha Allah, babu wata matsala da zai zamo sai Alkhairi ""."

"""Allah yasa ""Cewar Adamu.."

"Mama dai ba abinda ta ce,,, saboda zullumi da kuma tausaya wa d'iyar ta,,, mafi soyuwa a ranta. Can dai"

"ta daure ta ce ""Amin "".."

"Adamu ya yi musu sallama,,, Baba yayi masa rakiya sai k'ofar gidan. Ya shigo ciki,, ya zauna..."

"Bayan ya zauna ne,, ya dubi Maman Amina. Ya ce ""ki daina damuwa,,, komai yayi farko zaiyi k'arshe."

"Kuma mutum baya auren matar wani,,, wannan ita ce k'addaran Amina. Mu yi mata addu'a Allah ya bata ikon cinye jarabawar rayuwarta ""...."

"Maman Amina ta ce ""ba komai na kema tunani ba,,, illa wa ce irin mace ce zai d'auko ma Amina. Kasan"

"yarinyar akwai hak'uri da zurfin ciki,, bana fatar abinda zai zo ya hana mata jin dad'i a rayuwar aurenta.. To ya zamuyi k'addara ta riga fata ""."

"""Haka ne hak'uri kawai zamuyi,,, tare da k'ara taya ta da addu'a,,, Allah ya kare ta daga shairin masu"

"sharri dana mutum ko aljan "".Baba ya fad'a cike da tunani."

"Mama tace ""Amin amin,, yaushe zaka isko Yaya Ayuba ka gaya masa ne? ""."

"""Ina ganin gobe ko jibi zan je wurin sa "".Baba ya fad'a."

"""Allah ya kaimu lfy "".Cewar Mama."

"Baba ya ce ""Amin""........."

"Suka cigaba da firarsu,,, cike da tunani da shawarwari akan lamarin duniya....."

*********************

"Aliyu ya na sauka garin Shiko,, direct wurin Ilu mai saida hoda yaje ya tambaye sa,, ina ne gidansu"

Saudatu.. Ilu baiyi mamaki ba saboda yasan halinsu Saude da uwarsu game da yi ma mutane asiri..

"Bai tsaya ja masa aji ba,, ya kira wani yaro yayi masa bayanin da ya kai Aliyu gidansu Saude. Ya d'auko"

naira hamshin ya ba yaro....

"Yaro ya amsa masa,, yayi godiya.."

"Ilu ya yi ma Aliyu nuni da yabi duk inda yaron ya bi... Yayi masa godiya tare da cewa ""to nagode Ilu..."

"Ilu ya ce ""Babu komai ai zama d'aya ""...."

"Yaron ya kama hanya,, Aliyu yabi bayansa har suka kawo wani gida mai ginin k'asa anyi plaster da"

sumunti....

"Daga kasuwa zuwa gidan,, babu nisa sosai..."

"Shi ma Aliyu ya d'auki naira hamshin ya ba yaro,,, yayi godiya tare da shiga cikin gidan..."

"Bayan wasu mintuna,, sai ga yaron ya fito. Ya ce ""ance ya shiga daga ciki ""."

"""to "".Aliyu ya fad'a."

"Yaro yayi ficewarsa,, zuwa gida yana mai dad'in kud'in da ya samu har naira d'ari....."

"Aliyu ya yi musu sallama,, suka amsa masa. Dole ne yasa suka amsa mishi saboda kada ya gano mugun"

"halin su da wuri,, domin kunsan yi sallama ko amsa sallama ba d'abi'ar su ba ce...."

"Bayan ya shigo,, ya samu wuri har an shimfid'a masa tabarma,, an je masa drink mai sanyi da soyayyar"

kaza...

"Ayadda ya sami su Inna Harira da Saude,, abin sai ya baka mamaki domin kuwa kowacce daga cikinsu"

tasha hijabi har k'asa da kuma k'amshi turare da ya ke tashi...

Ya duk'a har k'asa ya gaida Inna Harira da Laure..

"Suka amsa mishi cikin sakin fuska,, kamar mutanen kirki da mutunci.."

"Alokacin ne Inna Harira,, ta ce masa ""idan da gaske ya ke yana son Saude,, ya turo magabatansa ayi aure"

"da wuri. Domin kuwa baban Saude baya son dogon zance cewa da Malam Isiyaku ""."

"Ya zaro dubu hud'u,, ya bata ya na cewa ""babu matsala, ko ni ashirye na ke. Da na koma gida zan turo"

"magabata nah ""."

"""yayi k'yau,, Allah shi yi albarka d'an nan. Har da hidima haka "".Inna Harira ta ce tare da amshe kud'in ta"

soke a zanenta.

"""Babu komi, ai an zama d'aya ""Aliyu ya fad'a cike da kunyar suruka..."

"""to yayi k'yau ""Cewar Inna Harira,, tayi Laure alamun da su shige cikin d'aki,, su basu wuri.. Suka shige"

d'aki tare da juna.....

"Aliyu yadubi Saude cike da k'auna,, yace ""Ina fatan kin san dalilin da yasa na zo wurin ki. Ba komi ba ne"

"illa na kamun da tsananin k'aunar ki,, da son ki zamo abokiyar rayuwata,, wato mu had'u a inuwa guda shi ne aure. Saboda haka ina rok'on ki da ki amshi soyayya ta da hannu bibbiyu kuma da zuciya guda ""."

"""hmm Aliyu,ai ni tuni zuciya tah ta aminta ka zamo abokiyar rayuwarta,,, ka sani ina matuk'ar k'aunar ka"

"da gaskiya da zuciya guda har zuwa gangar jikina "".Saude ta fad'a cike da makirci da yaudara..."

"Aliyu ya ce ""nagode sosai da kika amshi soyayyata,, bata re da jamin aji ba. Ko kwana -kwana ""."

"""Mi ye abin jan aji ga abinda ka ke so,, kuma ka ke muradi.. Ai tunda ina son ka babu batun jan aji anan"

""".Saude ta fad'a cike da makirci."

"Ya dd'auki ledar da ya kawo mata,, da wadda Amina ta basuwa ya bata.Duk ya mik'a mata tare da bata"

naira dubu biyar 'yan d'ari biyar -biyar...

"Yana cewa ""na kuwa gode sosai,, ga wannan ledar kayan kwalliya ne ba yawa,, ta biyu kuma Amina"

"matata ta ce in kawo miki ""."

"Ta so ta nuna mishi b'acin ran ta,, akan abinda Amina ta kawo mata. Tare da jin haushi da ya ambaci"

"sunan matarsa. Amma sai ta daure, ta b'oye b'acin ran ta,,, tare da shan alwashin sai ta ga bayan Amina."

"Zata nuna mata ta rashin imani da tausayi,, ita zata gwada ma kissa da munafurci. In ba munafurci ba mi ye na yi mata aiken wani abu.. Haka dai tayi zage -zage a cikin zuciyar tah."

"Sannan ta ce ""Ai kuwa ka ce mata nagode sosai,, Allah ya sa ka da alkhairi kuma ina gaida ta ""."

"""zata ji insha Allah,, ai na manta ita ma tana gaida ke "".Cewar Aliyu..."

"Saude ta ce ""Ina amsawa "".."

"Haka suka cigaba da firarsu,, tare da musanyar kalamai masu dad'i ga juna. Kowane yana k'ok'arin ya"

burge d'an uwansa....

"_*Ku kasance tare da ni Mugirat, ina matuk'ar k'aunar masu bibiyar labarina *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing by~Sis Nerja'art_

*PAGE* 151-155

"Bayan ta gama bata shawarwari,,, Habiba tace mata ita kam zata wuce gidansu.. Amina tayi mata godiya"

"sosai tare da bata turare da sabulun wanka mai shegen k'amshi,,, da k'yar Habiba ta amsa saida Amina ta nuna mata b'acin ranta sannan ta amsa tare da yi mata godiya sosai...."

"Suka fito tare domin yi ma Habiba rakiya,,, Saude najin muryarsu ta fito da saurinta cikin d'akinta.. Ta"

dube su duba na walak'anci da rashin mutunci....

"Tace ""keee!! Habiba ba na hanaki shigo mana gida ba,,, uban waye yace ki shigo mana cikin"

"gida ..Shegiya munafuka baki iya zama gidan mijinki,,, sai kin shigo kina mana munafurcin da kika gada ga uwarki munafuka "".Tace cike da son jin dalili..."

"""Hmmm Saudatu kenan ba zan daina shigowa cikin gidan nan ba,,, saboda ba dominki na ke zuwa ba.."

"Kuma bari da kike cewa in daina shigo muku gida,,,, ni ba bak'uwar arzik'i ba ce,,,je kiga gidan mijina ya wuce tunaninki kuma yafi wannan akurkin gidan da ki ke tink'aho da shi,,, sannan idan kina cin mutuncinki ki daina sawa da ni. Idan ba haka ba wata rana sai an kwashe ki,,, saboda dukan k'warai zanyi"

"miki,, idan yaso Aliyu ya kaini police station ""...Cewar Habiba..."

"Saude ta ja tsaki ""Mtssssss ""sannan tace ""k'arya banza dama kina da gidan da yafi wannan kike zuwa na"

"mu... Mak'aryaciyar banza karuwa annobar gari,,, dama ai kwad'ayi ne ke kawo ki da kuma munafurcin da kika sa ba da kike cewa zaki buge ni idan baki buge ni ba shegiya kike kuma uwarki da zina ta haife ki.. 'Yar iskar banza argunguma banza mai rayuwar 'yan tasha ""... ."

"Habiba tace ""duk abinda kike yi ki cigaba Saudatu,,, wata rana ba zaki yi ba.. Ba zan bugeki a cikin gidan"

"mijinki ba,,, amma ki sani wata rana idan kere na yawo zabo ma yana yawo zasu had'u "".... ."

"Tana gama fad'in haka,,, taja hannun Amina.. Domin ta raka ta wajee....."

"Saude tayi kuwwa da k'arfi,,, kamar sabuwar kamun haukah..."

"Tace ""Wallahi ko mun had'u dan kutumar buro uban ki,, ba abinda zakiyi min saboda da haka ki iya kama"

"lizamin,,,, shegen bakinki shegiyar karuwa mai bi gida -gida yawon maula da karuwanci,,, babu shegiyar da ta isa ta hana min abinda naga dama a cikin gidan mijina ""......"

"Babu wadda ya kulata daga cikin su,,, ta kama fad'a da masifa da bala'i....."

"Amina ta raka Habiba,, bakin garka"

"suna firar su cike da shak'uwa da k'aunar juna... Can dai suka yi sallama da juna cike da kewar juna,,,,"

"Habiba ta yi gidan mijinta,,, Amina ta juya zuwa cikin gidan mijinta....."

"Tana shigowa ta tarbeta da bala'i da masifa,,, ta kama cewa ""shegiya 'yar iskar banza argunguma,,,"

"karuwa dama ke jawo su.. Ana zuwa ana zagina tare da cimin mutunci akanki,,, wallahi Allah ya isar min tsakanina da ke akan zagin da kike sa ana min,,,,, cikin gari gaba d'aya"" Ta kama zage -zage da tsine -"

tsine.......

"Amina tace ""ke dai akeji anyi ma akuya wanka,,, ki cigaba abinda kike yi,,, zakiyi nadama anan gaba ""....."

"""Uwarki ce zata yi nadama ba ni ba,,, ba abinda zan gani sai alkhairin Allah... Shed'aniya uwar ibilisai"

"argunguma kuma kuchakar k'arya "".Cewar Saude....."

"Amina tace ""ke dai ake ji,,, karki bari ki cigaba duniya ce ""...."

"Amina tayi shigewar d'akinta,,, ta fita batun ta......"

"Saude ta ari bakinta,,, ta cigaba da cin mutunci tare da tonon asiri... Da zage -zage,,,, babu kunya barai"

"tsoron Allah,,,, haka dai ta cigaba da tonon silili... Harta gaji sannan ta yi shigewarta d'akinta... ."

********************

"A can d'akin Tanko kuwa,,, Abu zaune yana zuk'ar sigari Laraba ce kwance saman jikinsa tana shararsa..."

Tare da kissing d'inshi ko'ina a cikin jikinsa....

"Tanko ya dube su,,, yace ""Malamai fa karku fara yi min iskancinku,,, cikin d'aki ku bari har in fita waje.."

"Sannan ku yi abinda zakuyi ""....."

"""Babah karka dame mu,,, ko yanzu zamuyi iyaka ka rufe idanunka... Idan baka iyawa ka tashi ka fita waje"

"""...Abu ya fad'a cike da shed'anci da rashin kunya....."

"Tanko yace ""idan nak'i fita mai zakuyi min,,, ni da d'akina zaku fara yimin iskanci ""..."

"Abu yace ""bismillah yanzu ina fisshe ka da k'arfi,,, tambad'a zamu fara ba iskanci ba""..."

"Tanko yace ""ku dai ake ji yanzu,,, na fita na barku lafiya ""..."

"Yasa kai yayi wucewarsa,,, zuwa waje......"

"Bayan Tanko ya wuce waje,,, Laraba ta k'ara langwab'ewa ga jikin Abu... Tace ""masoyina ""...."

"""Na'am jinin jikina "".Cewar Abu...."

"""Dama kud'i nake so,,, kamar dubu ukku domin in shiga ankon Jummai k'awata "".Cewar Laraba...."

"Abu yace ""bakida matsala muddin muna tare Laraba,,, karki damu masoyiyata ""...."

"Yasa hannu cikin aljihunsa,,, ya d'auko dubu biyar ya bata....."

"Laraba ta k'ara rungume shi,,, cikin dad'in k'yautar kud'in da ya bata,,, tana mai farin ciki... Tare da yi"

masa godiya.. .

"Shima ya rungume ta,, yana shinshinar jikinta. Ya fara lasar ko'ina a jikinta,,, da kuma shafar k'irjinta.."

Nan ta kama masa suka fita cikin hayyacinsu...

"Tare da lulawa duniyar mazinata. (Allah ubangiji ya tsare mu,, ya tsare mana imaninmu. Allah ya kare mu"

daga shairin shed'an la'ananne).....

*********************

BAYAN KWANA BIYU

"Inna Indo ce ke shiryawa,,, tana sa kayanta domin zuwa gidan d'anta Aliyu....."

"Inna Indo ta dubi Baba Ayuba,,, tace ""to ni Malam zan wuce yanzu,,, can gidan Aliyu domin naji mi ke"

"hana masa zuwa gidanmu "".... ."

"""To Indo dan Allah ki kula,,, kuma kibi maganar a hankali cikin lumana da ruwan sanyi,,,, kada kije ki aza"

"musu masifarki ko bala'i. Ta yadda ba zasu fahimceki ba,,, komai sannu a hankali ake binsa,,, kinji ko Indo "".Cewar Ayuba cike da lalama...."

"Inna Indo tace ""Insha Allahu Maigida,,, babu abinda zai faru sai alkhairi.. Ba zaka same ni cikin masu son"

"zuciyarsu ba""....."

"""Allah ya sa haka,,, Allah ubangiji kuma ya kiyaye hanya "".Cewar Baba Ayuba ...."

"Inna Indo tace ""Amin Malam "".Ta sa kai tayi wucewarta zuwa gidan Aliyu..."

*********************

"A nan gidan Aliyu kuma,,, Saude ke ta aza ruwan masifa da bala'i,,, Aliyu yana kama mata. Saboda wai"

"taje kitchen ta d'ebo abinci,,,, domin ta ci haka kawai ta bangaji Amina,,,, abincin ya zube kuma plate d'inta ya fashe... Shi ne ta kwashe k'arya da gaskiya,,,, ta gayama Aliyu wai Amina ta bangajeta. Domin"

kada taci abinci kuma plate d'inta ya fashe......

"Saude ta kama masifa,,, tana cewa ""kaga irin abinda na ke gaya maka,,,, idan baka nan Amina babu irin"

"walak'anci da rainin wayon da bata yi min... Kawai hak'uri nakeyi bana fad'a maka saboda kada kace ina son had'aka da matarka "".Ta fad'a cike da makirci da kissa....."

"Aliyu yace ""ki dinga fad'a mani duk abinda,,,, ta keyi miki Saudatu.. Wallahi Amina na kusa kora ki gidan"

"uban ki,,,, saboda nagaji da mugun halin ki... Na rashin son zaman lafiya da kawaici,,,,, wannan wane irin son jidali ne da tashin hankali "".. Yace cike da b'acin rai......."

"Saude tace ""Ato gaya mata kai dai,,,, ni ban san abinda nayi mata ba duk ta tsaneni... Tsana mai ciwo"

"haba Aunty Amina nifa k'anwarki ce ba kishiya ba,,,, KISHI ai ba hauka ba ne Anti ta... Dan Allah ki yafe min duk abinda nayi miki domin bana son tashin hankali,,,, ko damuwarki "".Tace cike da munafurci da"

dad'in baki...... .

"""Dan Allah ki daina damar da kanki Saudatu,,,, ki k'yaleta ni zan gyara mata zama saboda bata gaji da"

"kashin da,,,, na bata ba.. Wallahi saina d'auki mummunan mataki akanki Amina,,, domin kuwa gaskiya kin kusa bar min gida "".Cewar Aliyu cike da jin haushin Amina.."

"Saude ta marairaice fuskarta,,,, cike da azuzanci tace ""Dan Allah mijina,,, kada kayi mata komai ka k'yale"

"ta,,,, idan ta nice na yafe mata... Na bar maganar har abada ""....."

"Aliyu yace ""idan kin k'yaleta,,,, ni bazan k'yaleta ba,,, saboda na gaji da mugun halin ta wlh "".."

"Amina imani da mamakin makircin Saude,,,, yayi mata yawa saboda abin yayi mugun b'ata mata rai"

"sosai.. Batasan sanda hawaye masu zafi na bak'in ciki ,,,,suka fito mata ba... .."

"Can ta daure tace,, cike dakewa""Haba Yaya Aliyu ya kamata,,, kafin ka yanke hukunci ka saurari"

"kalamaina.... Saboda ka gano bakin zaren,,,,,ba wai kayita aza mini laifi ba ni kad'a........."

"Kafin ta k'arasa maganar Aliyu ya kashe ta,,,,, da mari biyu masu k'yau. Wanda sai da ganinta da jinta ya"

d'auke na wasu lokutta.....

"""keeee!!! Dan ubanki har kin isa ki nuna mini yadda zanyi hukunci,,,,, cikin gidana dan kin raina ni,,,, zan"

"halaka ki in halaka banza... Duk kin wargazamin gidana tare da b'ata min gida na "".Cewar Aliyu....."

"Amina ta dafe kuncinta,,, inda ya mareta. Tana kuka tana cewa ""Ai dama haka zaka ce,,, komai nayi nice"

"da laifi koda bisa kuskure ne. Na gaji da tozarta ni da kake yi Aliyu,,,, wallahi na gajiiiii "".Ta sake fashewa da wani kuka mai ban tausayi......."

"""Idan ke gaji ki barmin gidana Amina,,,, dama uban wa? Ya tare ki ba kunada gida ba. To kije"

gidank........

"Bai k'arasa maganar ba,,, saiga sallamar Inna Indo ta shigo cikin gidan.... ."

"Aliyu kawai ya amsa mata,,, Saude da Amina duk shiru sukayi.."

"Inna Indo ta samu wuri ta zauna,,, tace ""Aliyu fad'an wa nakeji har waje,,,, ke kuma Amine mi ya same ki"

"kike kuka? "".."

"Aliyu da Saude suka yi tsuru-tsuru,,, saboda gudun masifar Inna Indo....."

"Aliyu ya daure yace ""Babu komai Inna,,, kanta ne ke ciwo ""."

"""Ya zaka ce min ciwon kai ne,,, zai sanya Amine kuka.. Ke sanar dani mi ke damunki? Kada kowa yasa min"

"raggan bakinsa "".Cewar Inna Indo...."

"Amina ta d'ago kanta,, ta kalli Inna Indo idanunta duk sun kumbura,,, akan yawan kuka ga kuma shatin"

hannu Aliyu nan da ya mareta....

"Ta kawo labarin komi,,, ta gaya Inna Indo tun farkon abinda suke yi mata,,,, na walak'anci da k'ask'anci"

"har iya yanzu da ya mareta,,, akan Saude babu abinda ta rage ko ta k'ara..."

"Inna Indo ta buga k'irjinta da k'arfi,,, tace ""mari! Kuma Amine miyasa tun farko baki gaya mani ba?. Lallai"

"biri yayi kamada mutum,, dama cin amanar da kake yi kenan da zalunci,,, shi ne ke hanaka zuwa gaishemu ko ""... .."

"Aliyu yace ""wallahi ba haka ba ne,,, ita ce bata iya zama ga kant......"

"Inna Indo bata yi wani jinkiri ba,,, ta kashe shi da mari hud'u masu k'yau. Kafin ya k'arasa maganar sa......."

"Ta nuna shi da yatsa tace ""to bari kaji ,,,wannan baya nufin saboda kayi aure ka walak'antar da matarka"

"ba... Aliyu na tsani azzalumi kuma bana son mai zalunci,,, duk son da nake maka baya hana inci mutuncinka. Idan naga ka kauce hanya,,, kuma wallahi daga yau sai yau kada ka k'ara dukan Amina,,, akan bare na dai gaya maka,,, idan ba haka ba wallahi sai rayuwarka ta b'ace,,, saboda ba jakar gidanku ba ce. Kee!! Kuma na rantse da Allah idan baki daina had'asu fad'a ba,,, kin kusa barin gidan nan saboda ba gidan ubanki ba ne... Ni zaki kawowa iya shege da iskanci a cikin gidan d'ana,,, to ba zan d'auka ba"

"shegiya annobar wahala.. Babu abinda ban sani ba game da asalinki,,, kinzo kinsa d'ana ya daina zuwa"

"ganina kwata -kwata. To na shafe uwarki a iskanci da rashin kunya,,,, ki kiyaye ni Saude bana son k'ulle-"

"k'ulle da salon munafurci da azuzanci,,,, annoba kawai dangin karuwai kinzo kin tarwatsa farin cikin gidan d'ana,,, to bokanku yayi k'arya kuma Saude ba zaku tab'a k'arshe mai k'yau ba,,, da ke da uwar ki"

"Harira ""....."

"Saude ta zumb'ura baki tace ""To ni yanzu Inna mi nayi miki yanzu kuma ""......"

"""kinci gundunbulin buro ubanki,,, shegiyar yarinya la'ananna,,, 'yar iskar banza argunguma "".Cewar Inna"

Indo cike da masifa.....

"Aliyu ya gurfana k'asa,, kamar zaiyi kuka yace ""dan girman Allah Inna kiyi hak'uri,,, wallahi bazan k'ara ba"

"nasan nayi kuskure ,,,amma ina son kiyi min uzuri kuma ki tayi ni da addu'a. Insha Allah bazan sake ba ""....."

"""kuskuren buro ubanka Aliyu,, nayi maka uzuri amma ka sani bazan d'auki,,, ka walak'anta matarka akan"

"wata ba "".Cewar Inna Indo...."

"Aliyu yace ""Insha Allahu na daina Inna ""......."

"""da yafi kam "".Cewar Inna Indo...."

"Inna Indo ta yi musu nasiha da wa'azi,,, tare da basu shawarwari akan su zauna lafiya.. Ita bata son"

neman magana da son fitina da neman fad'a... Tace kada ta kuskura ta sake kama Aliyu ya nuna

"banbanci a tsakanin su,,, tare da goyon bayan guda. Ta k'ara ja ma Saude da Amina kunne akan kowa ta"

"tsaya ga kanta,,, sannan zata rink'a zuwa akai akai domin taga ya suke gudanar da zamantakewar su,,, ta yau da kullum. Ta umurci Aliyu da yayi adalci a tsakanin su,,,, banda son zuciya ko nuna fifiko,,, idan ta"

"same shi da wannan sai taci mutuncin shi,,,, tare da b'ata masa rai... ."

"Kowa daga cikin su,, ya nuna ya aminta da maganarta. Tare da bata hak'uri akan dukkan abinda ya faru,,,"

sun nuna sunyi nadamar abinda ya faru. Kuma ya wuce har abada......

"_*Anya kuwa sun daina fad'a da juna?,,,sai ku biyo niiii*_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_*Aunties d'ina kusani ina matuk'ar k'aunarku a cikin zuciya tah*_

Aisha Aliyu

Naja'atu Aliyu

Hassana Usman

Rashida Usman

Zainab Usman

Ik'ilima Usman

Sumayya Usman

Halira Ibrahim

*PAGE* 106-110

"Aliyu da Saude bayan sun gama fira ne,,, yayi mata sallamar zuwa gidan. Ta yi masa rakiya kamar kar su"

"rabu da juna,,, cike da nishad'i da farin ciki mara misaltuwa ya bayyana ga fuskar Saude..."

"Bayan ta dawo da yi masa rakiya ne,,, ta shige cikin gidansu....."

"Ta shigo gidansu,, hannunta rik'e da ledodi guda biyu...."

"Ba sallama ba komi,, ta iske su Inna Harira zaune suna jiran dawowarta,, har sun yi zaune saman"

tabarma. Suna firar su.....

"Itama ta samu wuri ta zauna,, kusa ga Inna Harira......"

"Saude ta mik'a musu ledodin.. Sannan ta ce ""gasu nan wai d'aya ta sa ce,, shi da kansa ya siyomin."

"D'ayan kuma mai sabulu da turare,,, wai inji makirar matarsa kuma munafuka,,, ta ce a kawo min.. Shi kuma dan yana wawa wanda baisan ciwon kansa ba,, ya kawo min har da cewa inji matarsa ""Ta fad'a"

cike da takaici....

"""Yau ga bak'in munafiki,, har kuna yin fira sai ya yi miki maganar azurakar matarsa.. Shi adole mai mata,,"

"dad'in abin dai bata haihuwa juya ce "".Laure ta ce cike da masifa da bala'i...."

"Inna Harira ta ce ""ku daina damun kanku,, ku barni da shegen gora zanyi maganinsa,, daga shi har juyar"

"matarsa.. Sai ya gwamma ce da bai k'ara aure ba,, ita kuma zata gane kishi da ke ba alkhairi ba ne agare ta. Wallahi dukkansu sai sunyi nadama a rayuwarsu "".Ta fad'a cike da b'acin rai..."

"Saude ta ce ""Ai Inna idan na shiga gidan,, wallahi ko mak'iyinta sai ya tausaya mata. Saboda na lura tun"

"yanzu matar nan argungunma ce,, amma ba komai zata san kishi da ni ba zai haifa mata d'a mai ido ba ""...."

"Laure ta ce ""haka muke son ji Saude,, karki yi mata da wasa.. Bari dai muga abinda ya kawo miki ""...."

"Ta sa hannu ta b'ude ledodin,,, ta Aliyu kayayyakin kwalliya ne irinsu powder, eyeliner, eyeshadow,"

"mascara, performs masu shegen k'amshi guda hudu. Na Amina kuma sabulun wanka da wanki ne,,, sai itama tasa turare guda mai k'amshi...."

"Kowane daga cikinsu,, ya yaba da k'yawon kayan,, amma Amina baiwar Allah tasha zagi da tsinuwa a"

"wurin su.. Sun kuma sha Alwashin sai sun hana mata jin dad'i a rayuwar ta,, sai sun nuna mata ba'a kishi da su akwana lafiya......"

********************

Bayan Aliyu ya fita zuwa garin Shiko.. Sai ga Hussaina ta tafi har gidan Mama Habiba ta fad'a mata

"wannan labari,, ita kuma ta shirya suka shigo wurin Amina domin su k'ara lallashinta tare bata hak'uri......"

"Suka shigo suka samu Amina,, tayi kuka har idanunta sun kumbura sosai akan kuka,, kuma sunyi ja"

sosai.....

"Suka zo kusa gare ta,, suka zauna tare da cewa ""Subahanillah!!! Cike da tausayawa..."

"Suka saka ta tsakiyansu,, tare da share mata hawayenta....."

"Mama Habiba ta dube ta,, cike da tsananin damuwa da tausayinta. Ta ce ""dan Allah Amina kiyi hak'uri,,"

"komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba. Hak'ik'a na san kishiya tana da zafi da rad'ad'i,, to ya zamuyi mu mata idan ba hak'uri da juriya akan haka.. Idan baka danni zuciyar ka ba,, zata kaika ta baro domin Allah ne ya ce su auri mata biyu zuwa hud'u.. Wa ye ya isa duk duniya ya haramta abinda ya halatta musu,, wallahi babu shi saboda haka shi ne jigon zaman rayuwa ta duniya.. Ako'ina kake dole sai kayi juriya da"

"hak'uri da mutanen da ka ke zaune da su ""..."

"Hussaina ta ce ""wannan magana ta ki gaskiya ce Anti Habiba,,, Amina hak'ik'a musan kishiya batada dad'i"

"ko kad'an.. Amma mun san ki da hak'uri, kawaici, juriya, ladabi da biyayya to ki k'ara akan wanda muka sanshi da ke,,, sannan kada ki rik'e ta mugun nufi idan ta zo. Ki amshe ta da zuciya guda,, duk sharrin da"

"tazo da shi zai koma ga kanta,, ki saki kowa ki kama Allah mad'aukakin sarki.. Shi ne zai kare ki daga"

"dukkan shairin ta ""...."

"""Haka ne kam gsky,, ki daina saka damuwa da tunani cikin zuciyar ki Allah ubangiji ya k'ara tsare ki"

"daga shairin masu sharri dana mutum ko aljan "".Cewar Habiba...."

"""Amin summa amin ""Cewar Hussaina cike da tsananin tausayi......"

"Sai asannan Amina ta d'ago kumburarrin idanunta,,, sunyi jajir da su ta ce ""Nagode da nasihunku gare"

"ni,,, ba wai ban yarda k'addara ta ba ne. A'a na yadda da k'addara mai k'yau ko mara k'yau,,, kuma na"

"ba Aliyu goyon baya d'ari bisa d'ari ya k'ara aure domin nasan Allah ya halatta masa,, wa ce ce ni da zan"

"haramta.. Kunsan abin yanada matuk'ar zafi da ciwo ne shiyasa,, na bari hawaye yana zubowa ko zanji dama-dama a cikin zuciya tah,,, ba wai ina fushi

Please Login or Register in order to submit comment