You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma allah da ya bani miji mai saurin fahimta allah ya barmu tare yace mata amin habiba,"

"sun dauko wata kenan suna yi cikin farin ciki da annushuwa sai ga sallamar abbas ya shigo, suka amsa"

"tare mama ke ce wa lafiya dai abbas tun dazu ina kunka shige da kaida asma'u baku dawo ba muna ta jiranku har abbanku ya dawo,"

abba ya tari numfashinta ai kina bari har ya zauna sannan kiyi masa tambayoyi je ki kawo masa

abincinsa ta ce to ta shige.

"Ta kawo masa abinci cikin kula da jug din ruwa masu sanyi a gabansa, abbas ya yi bismillah ya fara cin"

abincinsa a nutse amma kallo daya zaka yi masa ka gane yana cikin damuwa sosai bayan kammala cin

"abinci ya sha ruwa, abba ya ce masa abbas mi ke faruwa ina ka baro kanwar ka, kunje kasuwar ne? cewar mama"

"abbas ya huci mai zafi sannan ya ce a'a bamujeba ya kawo bayanin duk abinda ya faru ya fada su, sunka"

"ce subhanalillah ita saude ta yi ma aisha mugun bugu haka lallai banga ta zama ba, abba ya ce hmmm matar nan batada imani ko kadan yi ma za shirya saina kaiku can wurinta mama ta ce to bayan ta shige daki abba ya ciro kudi dubu ukku ya ce abbas ya siyo abinci restaurant daga can ya isko su can saboda"

"babu lokacin dahuwa,"

"abbas ya amshi kudin ya wuce, mama kuwa ta shiryo har da yar ledar rike ga hannu da flask din ruwan"

zafi su kah shiga motar abban sunka kama hnyar zuwa asibiti.

Malam adamu kuwa bayan dawowarsa daga asibiti sai da ya biya gidansa ya kimtsa sannan ya nufi

"kasuwa wurin abokinsa, yana isa ya iske shi yana harhada kayan, yana shirin komawa gida."

"Yana ganin malam adamu yayi murmushi yace mata inji ba mantuwa kayi ba malam adamu, ya bashi"

"hannu suka yi musabaha ya ce ba mantuwa nayi ba wata muhimmiyar magana ce ta kawo ni wurinka mal. aliyu ya ce to ka bari mu isa gida,"

"mal. adamu ya ce maganar bata gida ba ce, baban aisha ya gyara benci ya ce masa bisimillah ga wurin"

"zauna muyi mgnar, bayan mal. adamu ya zauna ya kawo bayanin komi ya fada masa abinda doctor sadik ya ce,"

mal aliyu sai da gabansa ya fadi dummmm ya ce ina lillahi wa inna ilaihirraji'un to ya zanyi kada yarinyar

nan ta mutu ya ma rikice sosai malam adamu ne ya kwantar masa da hnkali ya ce kar ya damu in allah ya yarda zata warke ya rufe kayan sa su wuce can asibitin ya ce to adamu bayan rufe komai na sa suka

dunguma zuwa asibiti cikin motar wani abokin su....

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHI KO HAUKA*

&&&&&&

_*Story and Written By~ Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_*Kaunarki wani sashe ne a cikin jinin jikina Aunty jamila D. Gada (ummu yasmin) marubuciyar rayuwar

yasmin.*_

page 16-20

"A lokacin da su Abba suka isa asibitin, numbar doctor sadik ya kira ya tambeyishi wane room su Aisha"

"suke shi mahaifine ga abbas,"

doctor ya gaidashi sannan yayi mishi kwatance inda room d'in da su asma'u suke.

"suna gama waya suka shiga cikin asibitin suna wuce d'akuna da yawa, har suka kawo room"

three(females ward) yake a rubuce sama.

"suka bude d'akin suka shiga ciki da sallama, asma'u na zaune ta amsa musu sallamar ta shek'o da gudu ta"

rungume mamanta tana hawaye.

mamanta lallashinta tayi tana share mata hawaye

sannan takama hannunta suka zauna saman gado da yake dakin akwai marasa lafiya da yawa kuma ga

"kujeru na zaman masu jinya,"

"abba yaja kujerar kusa da su ya zauna,"

mama ce ta ce ma asma'u tadaina kuka cuta ba mutuwa bace

"Abbas ya nisa ya ce Allah dai ya bata lafiya, ya dubi asma'u ya ce mata Aisha ta tashi ne"

asma'u ta ce tun dazu bata farka ba saboda anyi mata allurar barci bayan k'arin ruwa.

mama takalli Aisha cike da tsananin tausayi tace Allah ya sauwaka (kallo daya zaka yi ma aisha kasan

tana cikin tsananin damuwa da rashin lafiya har ta dan rame)

Abba yace amin saude kam sai addu'a.

mama tace taje tayi ta yi indai duniya ce ta ishi kowa riga da wando.....

suna tsaka da magana sai ga Abbas ya shigo da sallama asma'u ta sheko da gudu ta rungume sa ta amshi

"ledodin da ke hannunsa,"

"ya samu wuri ya zauna kusa da abbansa, asma'u ta bude leda ta farko, ta juye abincin da ke cikinsa"

"tana ci acikin plate (jolof rice ne), mama ta dube shi tace mi ya tsaida da kai naga ka jima"

abbas ya ce mata wallahi wani abokina ne ya tsaida ni.

"tace masa to,"

Abba ya juya wurin Aisha yaga ta motsa kuma drip na karin ruwa ya kare.

"yace ma abbas yaje ya kira likita. Abbas ya mike ya ce to,"

ya kama handle din kofa ya fita.

"Acan gida kuwa inna saude ce zaune suna magana da abu, inda take ce masa wallahi tunda har akan"

"Aisha abbas ya bugeshi, itama ya bangaje ta wahala yanzu Aisha ta fara,"

abu ya kalleta da kwancin hannun Abbas ga jikinta yace na dai gaya maki ki bari na warke karki sa ke

"jawo mani wani dukah dan Allah, wallahi idan har baki bari na warke ba kika kuma ja mani wani dukan zan nuna miki ni tantirin dan iska ne."

inna saude tace yi hakuri abu ai ina nufin sai ka warke sannan mu d'auki mataki sannan wankin kayanmu

"yana nan yana jiran diyar banzar nan bakar ashana kona gari,"

Abu ya kalli inna ya kyalkyale da dariya ya ce dube ki da Allah da kumburaren bakinki kamar karya .

.

Inna saude ta ce kaifa abu bakada kunya wlh nice mai kamada karya?

abu ya ce mata to aike inna kunya da mutunci gadonsa ake ni kuma ban gada ba gareki

"baka gada ba dai ga uwarka tsinanne, dan banza cewar inna saude."

Naji dai duk mune diyan banza tsinannu da ke da ni. kuma wallahi saude ki bi ni a hankali na fi ki rashin

"mutunci, kuma na"

wuce tunaninki.

inna saude dayake macece mai mugun tsoro ta ce kai wasa na ke maka.

abu ya kalle ta ya ce da ya fi.

"Acan wani lungu kuwa inda mutane ba su cika wucewa ba, Asiya ce zaune da abokiyar ta mai suna larai"

"da maza biyu da kadan su ka girme su,"

"guda sunansa ila, dayan kuma sunan sa rabi'u suna wasar tabe -tabe da shafar junansu,"

"Ila yana shafar jikin larai, har da rungume ta yayi da kissing dinta."

"Shi ma haka rabi'u ya rungume asiya ya kissing dinta tare da shafar ko'ina na jikinta, ayayinda dukkansu"

kana jin nishin su _(Allah ya shirya mana dukkan zuri'ar mu)._

_Wannan kenan_.

"Su malam adamu kuma da shi da baban Aisha, kafin su isa can sai da suka tsaya bakin titi bakin hanya,"

"suka sayi kayan marmari irinsu lemo, ayaba,abarba,da dai sauransu."

"Suna isa dakin, suka yi sallama, aka amsa musu tare da yi musu barka da zuwa."

"su kaga har an cire mata drip gata zaune tana shan tea ga abinci gabanta mai rai da lafiya,"

"babanta ya aje ledar gefenta ya ce mata ya jiki? tace masa da sauki,"

Suna fira inda abba ke musu jaje akan abinda yake faruwa sai ga doctor sadik ya shigo ya rubuta mata

magani sannan yaba Abbas yaje ya soyo magani kuma idan ya yarda jibi zaya sallame tah.

bayan abbas ya fita siyo magani

"doctor sadik ya ce musu ina mahaifin yarinyar,"

"mal. Aliyu ya ce gani, to ina son magana da kai cewar doctor."

yace to doctor ya fita baban aisha yabi bayansa.

suna zuwa office doctor sadik ya zauna a kujera ya ce masa shima bismillah.

"bayan ya zauna domin doctor sadik ya sanar da baban aisha duk abinda ya sanar da su malam adamu, ya"

"rokesa dan Allah ya kula da yarsa saboda tana gab da kamuwa da hawan jini sannan ga ciwon ulcer,"

mal. aliyu yace to insha Allahu zan kula

nan doctor ya sallame shi ya fito. Ya zaiyi shi kansa ya san bai kyautawa aisha ba yana kuma tsananin

tausayin ta da kuma kaunarta har cikin zuciyarsa.

"ko ya so ya wulakanta saude baya iyawa saboda wani abu da yake ji cikin jikinsa, shi kansa ya san yayi"

"babban rashin matar kwarai Amina, mace mai tausayi, mutunci da karamci kuma kowa nata ne,"

"shi kansa saude bata raga masa ko kadan, bata ganin mutuncinsa."

"bawan Allah har da hawaye ke fitowa ga fuskarsa na bakin ciki, ga saude na musgunawa yar lelensa"

amma ya kasa kareta daga wulakancin inna saude da Abu d'an yayarta.

"hakika ya san tunda saude tashigo rayuwarsa ta tarwatsa masa farin cikin gidansa, tawargaza duk wani"

abu da zai sanya shi cikin annushuwa ko walwala.

nan yasa handchef ya goge fuskarsa kamar baiyi kuka ba.

ya nufi hanyar komawa room d'in da su ke.....

"_ku ci gaba da bi na, domin jin wannan labari mai ban tausayi_"

*Muje Zuwa *&&&&&&

KISHI KO HAUKA

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_ina tayaka murnar aurenka yayanah mafi soyuwa a raina, abin alfaharinah *Harisu Musa* tare da"

amaryarsa *Sister Mariya* Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba_ c'c'c'c'c'c'.

Page 21-25

Mal. Aliyu yashigo cikin room din da a ka kwantar da aisha.

"ya iske mama da asma'u zaune suna fira,"

"harka dawo ne baban aisha? cewar mama,"

eh har na dawo ina su mal.adamu da abban asma'u su ka je naga ban gan su ba.

"mama tace masa yanzu yanzun nan suka fita, sunce na fada maka sun wuce sai kun hadu."

ya ce mata to babu matsala nima yanzu zan wuce saina fad'ama saude tazo taga jikin na aishan.

mama ta nisa ta ce babu matsala hakan yanada kyau ai.

"baban aisha yace musu shi zai wuce, insha Allah saude zata zo, asma'u tace baba Allah ya kiyaye, ya ce"

"amin asma'u,"

da zai fita ne yaje wurin aisha yace mata ba wani abinda ke mata ciwo ko take so ya siyo mata?.

aisha ta kalli babanta kallo mai cike da tsantsar tausayi _(saboda tasan duk abinda ya keyi ba bisa

"hnkalin kansa yake ba, ayanzu batada wadda ta tsana fiye da inna saude da abu a rayuwarta, allah ya jikan iyayenmu wadanda suka rigamu gidan gaskiya. Ameen)_"

"tace masa a'a baba ba abinda ya ke mini ciwo, bana bukatar komai a yanzu."

"yace mata to, yasa kai ya wucewarsa gida."

"Bayan wucewar sa, asma'u ta kalli mamanta ta ce jih baban aisha wai har da cewa wai inna saude zata zo"

"tare da shi, sai kace tana jin maganarsa matar da bata ganin kowa da gashi."

"mama ta ce oh ni habiba, auta akwai ki da iyayih, ban hana ki tsoma bakin ki akan abinda bai shafe ki ba?"

yaran zamani na yanzu akwai ku da kinibibi tun baku tafasa ku kone.

Asma'u ta zumbura baki cikin shagwaba ta ce mama ai gaskiya ce na fada kuma duk abinda ya shafi aisha

"ya shafe ni,"

"Gaskiya kika sani yar karama da ke, suna cikin haka saiga abbas ya dawo da ledar magunguna, yayi musu"

"sallama,"

"suka amsa masa, asma'u ta ce yaya sannu da zuwa"

"ya ce mata yauwah auta, yasamu wuri ya zauna yana kallon aisha ya ce ya jiki,"

"ta ce masa da sauki, mama tace yakawo ledar magani aba ta saboda ta ci abinci, ya mika mata ledar"

maganin.

mama ta amshi maganin da kofin ruwa zata ba aisha ta sha.

aisha ta 6ata fuska kamar zata yi kuka tana shagwaba wai ita bata son shan magani

"mama ta lallasheta, wai ta amsa tasha bai da daci sosai"

"ta ki amsa, asma'u ta kalle ta, tayi dariya tace ai mama ba abinda aisha ta tsana irin magani yi hkr kawalli"

ki amsa ki sha.

"ta kyaletah bata ce komai ba, abbas na ganin ta ki amsa da yadda ta ke shagwaba ya ji ta burgesa saboda"

shi mutum ne mai son macce yar shawara.

"Ya amshi maganin da ruwa yana lallashinta yana cewah haba yar kanwata, abar alfaharinah sinadarin"

"rayuwarsa, wai zai siyo mata wani abu kar ta damu idan ta sha maganin, idan bata sha ba kuwa sun bata."

Nan da nan ta amshi maganin ta shanye tana kwabe fuska

"Yauwa ko kefa dai cewar abbas, mama dai tana kallon ikon rabbana, asma'u ce wadda bata gani takyale"

dan haka ta kyalkyale da dariya.

aisha tace yaya ka ganta ko tana min dariya?

kyaletah ai zamu bata da ita idan bata bari ba.

Asma'u ta yi murmushi ta ce kinga wallahi wasa nake miki

mama ita ma dai murmushi kawai take yi.

Acan gidansu aisha kuwah bayan babanta ya koma ya iske saude da asiya da abu suna firar su hankali

kwance.

"ya samu wuri ya zauna, saude babu ko kallon kwarai bare sannu da zuwa,"

"ya kalli inna saude yace mata yana son magana da ita, ya kamata su kebe"

"babu wani kebewa da zanyi, koma miye ka fada gabansu asiya saboda babu bako a nan,"

"ya ce mata tasan aisha batada lafiya miyasa bata fada masaba,"

kuma bata je ganinta asibiti ba?.

"inna saude tace kagama ko? to ba zan je ganin ta ba, ai diyarka ce ba tawa ba, wurin yawon"

"karuwancinta ne da gantalinta, ta jiyo ciwo saboda haka ba abinda ya yi min zafi."

Malam ya kalleta cikin tsananin bacin rai yace yanzu saude diyar ta wa ce kike kira da karuwa?

inna saude tace ai zan kira tah da abinda ya fi karuwa ma

"ba duk kai kake daure mata gindi ba, wai ni zata je ta kira min wannan kwarton nata(abbas) ya zo ya bani"

"kashi, ni da abu."

"Har da tsohon munafikin nan adamu har da zuga shi ya karama mana,"

"to wallahi ka gaya musu sai sun san fada da ni ba alkhairi ba ne, xasu yi nadama a rayuwarsu gaba"

dayansu wallahi.

"malam ya kalleta cikin takaici da ban haushi, ya ma kasa ce mata komai _(kunsan abin akwai asiri a"

cikinsa)_ yasa kai ya wucewarsa zuciyarsa tana k'una da bakin cikin da wannan hali irin na saude.

"Ya barta tana ta bala'i da masifa, bayan ya wuce ne abu ya dubetah yace mata wannan tsohon yana son"

"kawo mata matsala, idan bata kara tashi tsayeba wata ran zai iya basu matsala,"

"Bar bakin munafiki, shege talakan banza to yanzu ya kake ganin za'a yi masa ko na kara komawa wurin"

"bokanmu ne, na fada masa abinda ake ciki ne wai"

Asiya ta kallesu tace wa ne abu ne zasu kara yi masa yanzu kuma?

"Inna saude ta harare ta tace kin ci buro ubanki, shegiyar yarinya uban waye yace ki saka mana rubabben"

bakinki kuma

"Abu ya yi mata mugun kallo ya ce ta tashi ta shige daki saboda bai shafe ta ba, ko ya halaka ta cikin gidan"

nan.

"suf, suf ta wuce cikin daki tana guna guni tare da zumbura bakinta,"

"Abu ya dubi inna ya ce mata yanzu abinda za'a yi ta sake komawa boka, ta gaya masa asa ma baban"

aisha wani mugun ciwo wanda baya iya zuwa ko'ina

tace yauwa dan albarka yanzu na ji magana amma yau ina ganin baka yi shaye shaye ba ko .

"ke tsohuwar banza ina ruwanki da shaye shaye nah, kaina nake shayo ma ko ke da sa idon nan."

inna saude ta daure ta mayar da abin wasa saboda tasan abu ya shafetah da iskanci da rashin imani ko

tausayi.

"ta ce masa yayi hakuri wasa ta ke masa kuma Allah ya bashi hakuri,"

Ya ja mata tsoki ya shuri takalminsa

yayi waje.

*BAYAN KWANA BIYU*

"An sallami aisha daga ta warke, tayi fresh tayi kyau sosai, kamar ba asibiti tayi jinya ba,"

Su mama ne da asma'u su ka rakota har gida.

"Sun sha zage -zage da habaici wurin inna saude, su dai ba wanda ya kula ta, shi ne abinda ya kara ma"

kona ran inna saude tare da alwashin sai taga bayan mama habiba da d'anta.

"shima dai abu ya warke sai dai ba za'a rasa tabon da abbas yayi masaba, duk lokacin da ya tuno abinda"

"yafaru sai ya ji tsananin bakin cikin abin, shi ma yayi alkawarin sai ya rama abinda abbas ya yi masa....."

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHI KO HAUKA*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_Wannan shafin sadaukarwa ne ga masoyan juna na hak'ik'a. Hafsat hafnan (marubuciyar Hibbatullah)

da Jamila janaf (marubuciyar nazir). Hak'ik'a soyayyar ku tana birgeni._

"_Kuma ban manta da ku ba, kuna cikin zuciya tah._ "

*PAGE* 31-35

"Asma'u ta ce ""ba za ki ga ne ba ""."

"Aisha ta dube ta, tayi murmushi sannan ta ce ""ya za'a yi na ga ne kuwa? """

"Asma'u ta fisgi kud'in da Abbas ya ba Aisha, sannan ta ce ""dallah bari mu gani abinda yaya ya baki,"

"domin kuwa nasan wannan kulawar da yake ba ki ba banza ba akwai dalili ""."

"""kinga k'idaya ki gani, koma miye dalilin ina ruwanki. Kefa akwai ki da sa ido "".Cewar Aisha."

"Asma'u ta kama kud'in tana k'idayawa, ta ga dubu biyar ne cif -cif.Ta dubi Aisha ta ce ""hmm soyayya"

"ruwan zuma, in ka sha kaba masoyi. Ni da ki ke gani na nan ba'a sa ido kad'ai na tsaya ba."

"Har da sa hanci ina yi, to wai wa zaku b'oyewa soyayya kuke da ke dayaya Abbas? ""."

"Aisha ta dubi Asma'u da sauri, kallo cike da mamakin maganarta."

"Ta ce ""kinsan Allah Asma'u, yaya Abbas bai tab'a cewa yana sona ba. Ko da wasa ne""."

"Asma'u ta ce ""Ai ke baki fahimci inda ya dosa ba, ni na fahimce shi amma bari ki gani komai daran"

"dad'ewa, sai ya furta miki kalmar so ""."

"""Hmm ni idan yace yana sona, mi zance masa ne? "".Cewar Aisha."

"Asma'u ta ce"" mata ai ba yanzu zai ce ya na son ta ba, tana ganin sai nan gaba. Idan sun k'ara girma"

"kuma sun mallaki hankalin kansu. Saboda haka karta damar da kanta, sannan dan Allah k'awata kud'in"

"da yaya ya baki. Kar ki bari yunwa ta halaka ki, saboda nasan ba wani abincin kirki Inna Saude ta ke ba ki ba ""."

"""Insha Allahu Asma'u ba zan bar kaina da yunwa ba, nagode k'warai da k'aunar da ku ke nuna min, ki ce"

"ma yaya Abbas da Mama nagode musu. Kuma ina gaida ta, sai na zo"".Cewar Aisha."

"Asma'u ta mik'e tsaye ta ce ""karki damu Insha Allah, za su ji, kuma ki k'ara kula da lafiyarki Kin dai ji"

"abinda doctor ya ce? Ban da yawan damuwa da sa abi aranki, kinji ko k'awata ?""."

"""kar ki damu komai ya wuce, kuma hak'uri ai ya zama dole a rayuwar mu "".Cewar Aisha."

"Asma'u ta ce ""to yayi ni dai zan wuce gida yanzu ""."

"Aisha ta ce ""to""."

"Ta mik'e tsaye ta ce ""Bari na raka ki, nasan yaya Abbas ya na waje yana jiran mu ""."

"Su ka fito tare, suna tafiya suna fira cikin tsananin shak'uwa da farin ciki."

"Har sun iso bakin k'ofar gida, su ka iske yaya Abbas zaune saman wani benci a k'ofar gidan."

"Aisha ta k'ara gaida shi a kunya ce, tare da yi masa godiya cike da ladabi da biyayya."

"Yayi mata wani irin kallon so, wanda shi kad'ai ya san ma'anarsa, yana murmushi ya amsa."

"""Tun d'azu na ke jiranku, amma kunje kun dad'ewar ku. Auta kamar kin manta ina jiran ki"".Cewar Abbas."

"Asma'u ta marairaice ta ce ""Ayya yaya dan Allah kayi hak'uri, kasan idan muka had'u da isha ba ma son"

"rabuwa ""."

"Abbas ya yi murmushi sannan ya ce""to ku koma kuci gaba, ni bari in wuce ko"".Aisha murmushi kawai ta"

"ke kanta a duk'e, tana wasa da yatsun hannunta."

"Asma'u ta k'yalk'yale da dariya tace ""A'a ni na tashi zuwa gida ai Bata k'arasa maganar ba sai ga Abu"

ya fito daga wani wuri.

"Yana tafiya yana doro, ya zo zai wuce kenan. Gaban su Abbas kamar ya yi musu d'iban albarka sai ya"

tuna kashin da yasha ga Abbas.

"Ya harare su, yaja mugun tsaki""Mtssssss"".Ya wuce cikin gida."

"Abbas ya yi murmusa, ya ce ""to k'anwatah mu zamu wuce ko ""."

"Aisha ta dubi Asma'u cike da tsananin k'aunar juna da shak'uwa ta ce ""yaya Abbas, Allah ya kiyaye ku. Ku"

"gaida min da Mama ""."

"""zata ji ""Cewar Abbas. Asma'u ta rungumeta ta ce ""to Aisha mu zamu wuce gida, ki k'ara hak'uri akan"

"wanda nasan ki da shi. Wata rana sai labari kuma komi ya na wucewa kamar ba'a yi ba, A DUNIYAR MU sai mutum ya kasance mai tsananin hak'uri da juriya da kauda kai, kinji k'awata ""."

"Aisha ta yi murmushi ta ce ""wallahi ban tab'a fushi ba akan abinda Allah ya kaddaro min ba, saboda"

"nasan komi zai wuce""."

"Abbas ya ce ""haka ne kam gsky, Allah ya sa mu dace baki d'ayanmu ""."

"Suka ce ""Ameen """

"Suka ce mata ""yanzu zasu wuce """

"""Allah ubangiji ya kaiku gida lafiya""Cewar Aisha. "".Suka ce ""Ameen ""."

"Suka kama hanyar zuwa gida, Aisha ta yi tsaye tana kallon su, har su ka b'acewa ganin ta sannan ta juya"

ta shige gidansu.

*TUSHEN LABARI*

Inna Saude 'ya ce ga Malam Isiyaku da Harira (Inna Galma ).Asalinsu 'yan garin shiko ne da ke k'arkashin

"Dandi local government Birnin kebbi, Jahar kebbi."

"Malam Isiyaku mutum ne gwargwado mai ilmin addini, ya had'u da Inna Harira a wurin cin kasuwa a"

"wani gari Da yake bata san shima d'an garin shiko ba ne, ta nuna tana son sa."

"Da ya ke Harira irin matan nan ne marasa kunya da mutunci, Malam Isiyaku ya k'i kulata."

"Ta koma gida, ta korawa Innarta bayanin komi, sukayi shige da fice zuwa wurin bokaye da 'yan bori."

"Suna kai kukansu da yake Inna Harira bazawara ce saboda ta tab'a auren wani mai suna Ado, wanda"

sanadiyyar rashin mutuncinta da shige -shigenta ya sake tah.Tana da d'iya guda da shi mai suna Laure

(mahaifiyar Abu).

"Ta wahalar da Ado, alokacin da ya ke aurenta. Mak'wabta da 'yan garin kowa ya san mugun halin Harira."

"Macece da bata ganin girman kowa, mai tsananin son abin duniya muddin zaka bata kwabo domin ta"

"kwana da kai, zata aminta komai kodq ace tayi k'ane da kai. Ga masifa da bala'in tsiya ga tsananin kishi ya wuce tunanin mai tunani."

Bayan sun kai Isiyaku wurin bokaye. Sai kuma Allah ya kaddaro sai ya aure tah.

"Bayan aure ne, tazo da d'iyar ta Laure su ka tare. Haka shi ma Malam Isiyaku da ya ke ta lura yanada"

"addini sosai. Sai da ta kai shi wurin bokaye da 'yan bori aka juya masa 'kwa'kwala da tunaninsa, ya zama baida ikon mata magana ko tayi abinda ba dai -dai ba."

Kuma duk kud'in da ya samo na sana'ar sai da robobi suna hannunta.

Shi ma *k'addara ce* taja masa rabuwa da matarsa ta 'kwarai da 'diyansa biyu. Mace da namiji.

"Sunan matarsa ta farko ita ce Mariya, d'ansa kuwa Namijin sunansa Abdullahi, macce kuma Atikah."

"Mariya mace ce mai kunya, ladabi , hak'uri, biyayya ga mijinta, kuma kowa natane, kuma kunsan komi"

muk'addari ne daga Allah.

"Rabuwar su shi ne :Adalilin mahaifiyar Isiyaku mai suna Inna Hajjo, mace ce mai masifa tsohuwa ce mai"

kishi da surukarta.

"Tun Isiyaku da Mariya tasa musu ido, wai ta asirce mata d'a bai ganin kowa sai ita da d'iyanta, ita ba zata"

"yarda ba, ita da haihuwa wata k'atanyar banza da cin moriyarsa."

Haka Inna Hajjo ta kama sababi da kulama Mariya da d'iyanta.

Sai da tasa Isiyaku ya saketa. Saki d'aya ko ta tsine masa.

"Wannan dalilin ne sanadiyyar rabuwar su, babu fad'a ko cin mutunci."

"Inna Harira kuwa da tazo gidan, da takula Inna Hajjo akwai sa idanu sai da tasa aka rufe mata baki, bata"

iya cewa komi cikin gidan sai dai kallo.

"A haka dai Malam Isiyaku ke zaune da galma, babu jin d'adi ko walwala."

Mutanen garin Shiko babu wanda bai san halin Harira ba (galma). Haka ma tazo iskancinta yasake

"'karuwa da tayi auren. Ko gaban Malam Isiyaku sai ta shigo da wani ta ce masa ""ai d'an uwanta ne "".Su shige d'aki suna iskancinsu."

"Babu kunya bare tsoron Allah, d'iyar ta Laure 'yar shekara hudu koda yaushe tana wurin maza wasa."

"Uwar haka ta ke babu wanda ya isa, yasa mata ido."

"Da kace kayi mata wa'azi ko nasiha, ko wata maganar ta gyara rayuwarta. Sai dai kaji a jikiinka ansa"

"maka ciwo wanda bayada magani. Saboda mugun asiri za'a yi maka kayi ta Wahala, kana kashin kud'i."

"Shi yasa a garin kowa ke bala'in masifar tsoron ta, ko d'iyar ta ce Laure taja magana babu halin bugunta."

"Ko harararta, kowa tsoron uwarta ya ke........"

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHI KO HAUKA*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"*Kin kasance jigon rayuwata, mai kaunata yayar kwarai abin so ga kowace kanwa, Aunty Raheenat M"

Abbakar (marubuciyar Rayuwar saudat) ban manta da ke ba*. .

Page 26-30

*WASHE GARI*

"Da misalin k'arfe 5:50 am na safe, bayan sallar asuba Inna Saude ce ta fito daga d'akinta da kofi r'ike ga"

hannunta.

"Ta nufi randar da suke zuba ruwa cikinta, ta d'ebo ruwa masu bala'in sanyi, ta nufi hanyar zuwa d'akin"

Aisha baiwar Allah.

"Tana zuwa babu ko sallama,ta izah k'ofar dakin ta iske Aisha kwance tana barci .Sai ta zuba mata ruwan"

"da ta d'ebo a cikin kofi, masu masifar sanyi ga jiki ."

"Aisha tana cikin barci taji abu mai mugun sanyi, yana bin jikinta."

"Ta farka da karfi tare

Please Login or Register in order to submit comment