You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hak'uri da kawaici a zamantakewar rayuwar mu ta yau da kullum. Bayan ya gama ne ya tambayesu ko akwai wata magana"

ne?..

"Sai alokacin ne Ahmad ya d'ago kai ya kalli gefen Aisha,,, suka yi ido hud'u da juna. Subhanalillah!! Dama"

"ashe haka yake da tsananin k'yawo ai wannan yafi kamada larabawa ko indiyawa shiyasa ya ke ji da kansa,,, tace a cikin zuciyar tah."

"Can ta tsinkayo muryar sa yana mata magana,,, cikin zazzak'ar muryarsa yace mata ""Aishat hak'ik'a duk"

"abinda ya samu bawa muk'addari ne daga Allah,,, bawa bai isa ya gujema k'addararshi ba. Saboda haka muyi hak'uri da juriya da junanmu,,,nasan maybe kinada wanda kike so amma k'addara ta rabaku kiyi"

"hak'uri. Wannan yana daga cikin kundin k'addararmu,,, sai dai muyi hak'uri da kawaici k'addara ce ta"

"gifto a tsakanin mu itace sanadin aurenmu ""..."

"Aisha tace ""Insha Allahu zan kasance mai d'aukar nasihunku,,, kuma zan kasance mai biyayya da ladabi"

"muddin muna tare a rayuwa,,, matuk'ar ina matsayin matarka. Allah ubangiji ya bamu juriya da hak'urin xama da juna ""..."

"""Amin amin matarmu "".Cewar Khalifa cike da zolayar Aisha...."

"Khalifa yace ""Alhamdulillahi godiya ya tabbata ga Allah ubangijin talikkai,,, da yasa kuka fahimci juna"

"batare da wani tashin hankali ba. Sannan ana son mutum ya kasance mai fahimta da sauk'in kai a rayuwa,,, da kuma yima juna uzuri da kuma yafiya a rayuwa ""..Haka dai ya cigaba da yima Aisha nasiha da bata misali daban daban game da rayuwa,,, su d'an jima sosai,,, sannan Khalifa ya kira baba Adamu a waya ya shigo da Mama Hussaina. Suka gaisa da juna sannan Ahmad yayi musu k'yauta mai tsoka,, suka shige cikin d'aki,, Ahmad ya dubi Aisha yace mata ko tana buk'atar wani abu. Ta nuna masa bata buk'atar komai,, ya d'auki kud'i masu yawa ya bata tare da nuna mata,, zasu wuce can kasuwa su gaida babanta Aliyu. Khalifa ya fita can waje wurin motarsu ya d'auko ledodi manya guda uku,, biyu nata d'ayan ta ba su Mama Hussaina.Tayi musu godiya sosai sannan tayi musu rakiya har waje wurin motarsu,, suka shige"

tare da yi mata sallama.

Ta juyawarta zuwa cikin gida....

Suma suka ja motarsu suka nufi hanyar zuwa kasuwa..

*Muje zuwa. *&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*Ina tayaki murnar kammala littafinki mai suna RUD'ANI,, abinda kika fad'a dai dai Allah ubangiji ya"

"baki lada. Wanda kika yi kuskure ubangiji Allah ya yafe miki kurakurrenki,, hak'ik'a novel d'inki ya ilmantar da mu da nishad'antar da mu,, Allah ya sa ki fi haka Balkisu Lashminzy...*_"

"_Mama Hafeeza, Ummu Ihsan,, marakish,, Maman Abdul hak'ik'a na yi matuk'ar farin ciki da nishad'i"

"comment d'inku,, Allah ubangiji ya bar k'auna da soyayya._ "

*PAGE* 206-207

"Khalifa da Ahmad suna tafiya cikin mota,,, suna firar su cike da shak'uwa da k'aunar juna,, har suka kawo"

"cikin kasuwa. Suka samu wurin da ake parking d'in motoci,, suka parker motarsu. Suna parkawa suka fito daga cikin motar tare da isa kusa ga wani mai shago,, mai shagon na ganin manyan mutane ya washe baki tare da gaida su. Suka amsa mishi tare da tambayarshi ko yasan wani Malam Aliyu mai saida kayan"

"miya,, mai shagon ya nuna musu ya sanshi daga sun k'arasa gaba,, su k'ara tambaya Insha Allah za'a"

"nuna musu shi. Sukayi masa godiya tare da yi masa alkhairi,, ai kuwa mai shago sai godiya yake zuba"

"musu tare da washe bakinsa. Haka dai suka yi d'an tafiya kad'an sannan suka sake tambaya,, suna tambaya aka nuna musu shi daga inda suke suna hango shi yana kasa kayan miya yana saisuwa..."

"Suka yi godiya ga maishi,, tare da bashi k'yauta. Shi ma yaji dad'i matuk'a tare da gode musu. Suna"

"k'arasawa wurin baban Aisha suka yi masa sallama,, ya amsa musu tare da ce musu yana zuwa su bari ya sallami wani yaro.."

"Suka ce to sai da ya k'ulla ma yaron kayan miya,, sannan yazo kusa ga su Khalifa. Yana tambayarsu mi"

"suke buk'ata,, Ahmad da Khalifa suka kalleshi cike da tsananin tausayawa,, suka ce basa buk'atar komai wurinsa suka zo.. Ya gyara benci tare da yi musu bismillah su zauna,,suka samu wuri saman benchi suka zauna. Shi ma Aliyun ya zauna yana mamakin ganin bak'uwar fuska,, domin shi dai yasan a rayuwarsa bai tab'a ganin larabawa ba a fili. Saboda shi azaton shi larabawa ne ko indiyawa musamman ma Ahmad,,"

shi da yake fari tas kuma yafi Khalifa fari sosai..

"Suka bashi hannu suka yi musabaha,, bayan sun gaisa ne. Sai Khalifa yayi gyaran murya yace ""Ina yini"

"Baba ya kasuwanci? "".."

"""Lafiya k'alau yaro,, kasuwanci kuma mun gode Allah ubangiji "".Cewar Malam Aliyu.."

"Khalifa yace ""Masha Allah nasan baka sanmu ba,, shiyasa kake mana kallon rashin sani "".."

"Aliyu yace ""k'warai kuwa ban sanku ba gaskiya "".."

"Khalifa yace masa ""mu ba wasu ba ne illa ni sunana Umar,,,amma da Khalifa ake kirana saboda sunan"

"baban iyayena naci. Wannan kuma (ya nuna Ahmad) sunan shi Ahmad kuma shi ne mijin 'yarka Aisha,,,"

"ma'ana dai surukinka ne Baba. Shi ne dalilin da yasa muka zo wurinka domin mu gaisa kuma musan juna "".."

"Malam Aliyu ya washe baki,, alamun farin ciki da murna. Sannan yace ""Alal hak'ik'a na yi matuk'ar farin"

"ciki da murna sosai akan wannan ziyara,, da kuka kawomin bansan da wane irin baki zan gode muku ba. Sai dai ince Allah yayi muku albarka d'iyannan "".."

"Khalifa yace ""Amin amin Baba ""..."

"Sai asannan Ahmad yayi magana,, yace ""mu ya kamata muyi maka godiya Baba,, saboda irin karamci da"

"halaccin da kayima mahaifinmu. Wato na d'aukar d'iyarka ka bani aurenta,, batare da sanin koni waye ba,, inada kirki ko banida shi,, zan iya kula da ita ko bazan iya ba. Mun gode k'warai da gaske matuk'a"

"Baba ""."

"Malam Aliyu yace ""karka damu Ahmad ai an zama d'aya,, ni dai fatana kuma burina shi ne ka rik'e ta"

"amana. Saboda yarinyar nan marainiya ce batada uwa,, ka kula da ita bisa ga amana da tausayi wlh ba yanxu naso yi mata aure ba. Dole ne tasa saboda matsawar muguwar kishiyar uwarta,, ita ta ke cin"

"amanarta tare da matsama rayuwarta kaji dalilin da yasa nayi mata wannan auren "".."

"Khalifa yace ""karka ji komai Baba insha Allah,, zamu rik'e maka ita amana. Kuma ya zama dole mu kula"

"ita domin hak'k'i ne wanda ya rataya akanmu ""."

"Ahmad yace ""idan Allah ya yarda karka damu,, zan kula da ita fiye da yadda zan kula da kaina. Zan bata"

"kulawa na musamman saboda ita d'in amana ce agareni ""..."

"""Allah ya sa mu dace baki d'ayanmu "".Cewar Malam Aliyu.."

"Suka ce ""Amin "".Atare da juna,, haka dai suka cigaba da firarsu cikin girmamawa da kunyar Malam Aliyu."

"Bayan sun jima sosai sai suka ce masa to su zasu wuce can gida,, baba Aliyu ya nuna musu babu matsala kuma ya gode sosai da ziyara. Khalifa ya zaro kud'i masu yawa ya bashi baba Aliyu,, ya k'i amsa. Suka yi suka yi bai amsa ba sai da Ahmad yace ai ba domin yana auren 'yarshi sukayi masa k'yauta ba. Domin Allah suka bashi sannan da k'yar ya amsa yayi musu godiya,, tare da rakasu har motarsu. Sai da yaga wucewarsu sannan ya koma rumfarshi ta kayan miya,, yana mai godiya ga Allah ubangijin talikkai da ya ba Aisha miji nagari kuma mai rufin asiri. Alokacin da za'a bud'e zuciyar baba Aliyu cike ta ke da tsananin"

"farin ciki da nishad'i,, saboda samun mijin k'warai ga Aisharsa mafi soyuwa a ransa..."

*********************

"Su Aisha kuwa har sun kamalla waec d'insu lafiya,, sauran neco aka basu hutun kwana goma kafin su fara"

neco. Suka watse kowa ya dawo gidansu cike da tsananin murna da farin ciki mara misaltuwa...

"Anan gidansu Aisha ta fita tana can gidansu Asma'u,, Inna Saude ma taje unguwa yazo taje wurin boka"

SIDDARU..

"Tana zuwa boka SIDDARU yayi mata barka da zuwa,, yana lasar baki.."

"Yace ""Saude mi ke tafe da ke yau kuma? Har na d'auka ko kin manta da ni a rayuwarki ""."

"Inna Saude ta cire hijabinta tace ""wlh ban manta da kai ba boka SIDDARU,, kawai da ayyuka suka yi min"

"yawa shiyasa kaji ni shiru ""..."

"Boka SIDDARU ya dubi Saude da ta cire hijabi,, yaga kwana biyu ta k'ara cika da k'yau. Da yayi bai lashi"

"zumarta ba. Sannan yace ""To yayi k'yau haka nake son ji,, shigo muje d'aki akwai wani magani da na had'a miki mai k'arfi na mallakar miji ""..."

"Saude tace ""To"".tare da binshi har cikin d'akinsa,, ya umurceta ta zauna saman gadonsa,, ta zauna."

"Shi kuma ya je can wani wuri,, inda yake ajiye magungunnansa, ya d'auko wani ruwan magani ya kawo"

"ma Saude. Ta shanye tare da shafa mata wani turare na magani,,, ya shige wanka cikin toilet d'insa..."

"Bayan ya fito ne yasa wasu kaya marasa nauyi,, can naga Inna Saude tana ta matse matse gabanta yana"

"mata k'aik'ayi. Tana ganin boka SIDDARU ya fito ta rungume shi da saurin tana hawayen buk'ata,, wato nan ne na gane boka SIDDARU sihiri yayi mata domin ya biya buk'atarshi da ita. Da yaga ta rungume shi shi kuma ya samu abinda yake so k'ara cire mata kaya yayi,,shi ma ya cire nashi suka afkawa juna a"

haukace cikin tsananin buk'atuwa. Suna ta abu guda wato a ranar boka SIDDARU ya biya buk'atar shi da

"Saude ya kai sau biyar,, bayan sun gama bai barta taje ko'ina ba saboda maganin bai sake ta ba. Ina"

ganin kafin ya saketa ak'alla sai tayi kwanaki kamar uku zuwa hud'u...

"Shi kam boka SIDDARU haka ya mayar da,, Inna Saude kamar matarshi yana mata abinda ya ga dama,,"

tare da biyan buk'atar shi..

"Acan gidansu Asma'u kuma zaune suke da Aisha,, suna firar su cike da shak'uwa da kuma yarda.."

"Asma'u ta dubi Aisha tace ""Aisha "".."

"""Na'am "".Cewar Aisha.."

"Asma'u tace ""ya kamata ace mun had'u da Zainab,, munyi shawara akan wane irin program ne zamu yi"

"before ki tare. Kinsan fa muna gama neco da wata biyu za'a kai ki gidan mijinki ""..."

"Aisha tace ""hmm na sani ai duk abinda kukayi dai dai ne,, idan ta ni ce walima kawai is okay domin"

"albarkar aure ake nema ba wani abu ba ""."

"Asma'u tace ""haka ne fa ustaziya,, yanzu dai yaushe angon na ki zai zo mu ganshi,, muma ya ganmu "".."

"Aisha ta yi murmushi tace ""naji dai ba komai,, wlh na manta kwata kwata ban gaya miki ba. Ai jiya sunzo"

"shi d'an uwansa,, kinga ledodin da ya kawo mini guda biyu d'ayan ta su Mama Hussaina,, na basu abin su "".. Ta mik'a mata ledodin domin suga ko miye yake ciki.."

"Asma'u tace ""ikon Allah k'awata kinga mijinki har kin manta da ni,, lallai kam gaskiya soyayya tayi dad'i"

"sosai ""..Tace tare da bud'e ledodin,, ta farko duk dogayen riguna ne guda shidda da hijabbai masu k'yau guda hud'u,, ta biyu kayan kwalliya ne irinsu powder,, eye shadow,, eyeliner,, mascara, performs masu shegen k'amshi guda biyar,, jambaki da sauran kayayyakin kwalliya. Sai da Aisha ta d'ibama Asma'u komai daga ciki,, hatta su dogayen riguna biyu ta bata hijabi ma biyu.Da k'yar ta amsa domin saida Aisha"

"tayi fushi sannan ta amsa,, tana bata hak'uri akan abinda tayi.."

"Asma'u tace ""Aisha ya sunan mijin naki da kuma d'an uwansa? ""..."

"Aisha tace ""Asma'u kenan ba dai tambaya ba,, sunan shi Ahmad d'an uwansa Khalifa amma na gaskiya"

"Umar "".."

"Asma'u tace ""wow nice names lokacin da kika ga Ahmad,, mi kikaji game da shi. Kina sonshi ko bakya son"

"shi,, yanada k'yau ko bayada shi? ""."

"Aisha tace ""ke wlh kin cika yawan tambaya,, at the same time kinyi min tambaya kusan hud'u Mr"

"lecturer. You can ask me something ni wannan banda amsarsu,, ki bari idan suka zo zakiga tambayoyinki gare su,, sannan batun ina sonshi ko bana son shi bai taso ba,,dole ne in rufama kaina asiri kafin Abu ko"

"Lado wani cikin su ya taushe ni yayi mini fyad'e. Inga taskon duniya da walak'anci ""."

"Asma'u tace ""haka ne kam gaskiya Aisha,, amma Allah ubangiji ya k'ara tsare ki daga shairin su Abu,,"

"Saude, Asiya,, Lado da sauransu marasa imani da tsoron Allah ""."

"""Amin amin "".Cewar Aisha cike da tsananin tunani da nazari..."

"Haka dai suka cigaba da fira,, da kuma shawarwari ta yadda zasu gabatar da abubuwan biki idan lokacin,,"

tarewar Aisha ya k'araso zasu buga abubuwa su raba domin nuna muryarsu da farin ciki..

**********************

"Abu da Asiya suke zaune cikin d'akinsa,, suna cin naman kaza da ruwan lemo suna korawa. Cike da"

"tsananin jin dad'i,, haka dai suka kama ci har suka gama cin naman kaza..."

"Bayan sun gama ne Abu ya dubi Asiya,, yace ""Asiyana kinga yadda kika k'ara k'yawo sosai da cika "".."

"Asiya tace ""Nagode sosai ai duk kulawarka ce,, kesa na k'ara k'yawo da cika sosai. Kasan kana bani dad'i"

"sosai da abubuwan k'ara lafiyar jiki ""..."

"Abu ya bushe da dariya,, yana shafar jikinta yace ""Asy baby my zumata wlh bakisan yadda na ke jin"

"dad'inki ba. Kina sa ni cikin farin ciki da nishad'i sosai,, saboda haka babu abinda bazan iya yi miki ba a rayuwata ""..."

"Asiya tace ""ai shiyasa na ke k'ara k'aunarka,, ka sani nima kana sanyani cikin farin ciki da walwala. Kuma"

"komai kake so shi zanyi maka masoyina ""."

"""Allah kuwa na ko gode sosai matuk'a "".Cewar Abu cike da tsananin k'aunar ta da jin dad'i sosai.."

"Asiya tace ""da gaske nake wlh habibina,, ai kasan yadda na ke son ka. Ba zan iya rabuwa da kai ba"

"sannan ba zanyi ma k'arya ba ""."

"""Wannan gaskiya ne masoyiyata "".Cewar Abu,, tare da cire kayan jikinsa tas sannan ya cire ma Asiya."

"Babu jimawa suka afkawa juna suna abu guda cike da tsananin jin dad'i da abinda,,, suka saba..."

"Acan d'akin Tanko,, shi da Lado da su Kubra zaune suna fira cikin farin ciki da murna..."

"Kubra tace zaune a cinyar Tanko,,tace ""masoyina kwana biyu rashin ganinka yasa na rame matuk'a "".."

"Tanko yace ""Haba dai kuby baby wlh ina matuk'ar son ki,, ai kinsan na damu da ke sosai fiye da tunaninki"

""".."

"Kubra tace ""haka ne zumar rayuwata "".."

"Tanko yace ""Ashe dai kin gane mai sona "".."

"Lado ne yake shafar Lubna,, yana cewa ""lubcy baby idan babu ke bazan iya rayuwa ba "".."

"Lubna tayi dariya tace ""Allah kuwa Ladona nima kasan ina matuk'ar begenka,, dare da rana kaine farin"

"cikin rayuwata ""..."

"Lado yace ""da gaske my baby gaskiya nayi dacen masoyiya ta k'warai "".."

"Lubna tace ""kad'an ma ka gani idan nice lubcyn babynka ,,komai zan iya yi maka wlh ""."

"Yace mata ""ya gode da k'auna ""..."

"Can naga Tanko ya haye ruwan cikin Kubra,, sun fara aikata masha'arsu. Shima Lado ya haye Lubna suna"

"aikata irin abinda su Tanko keyi,, ni dai naga ikon Allah ciki d'aki d'aya suna aikata iskancinsu,, kowa yana ganin kowa babu kunya barai tsoron Allah.. Haka dai suke gudanar da rayuwar su cike da k'azanta da"

rashin kunyarsu...

"Shi ma boka SIDDARU haka ya kama gurzar Inna Saude,,, kamar matarsa kullum kullum sai ya kwanta da"

"ita fiye da sau hud'u. Baya gajiya da ita saboda ya riga ya saba iskanci da mata kala kala iri iri da yawa,,, kodayake Inna Saude ita ta kai kanta da kuma burinta na duniya na banza,, ace mutum shi a rayuwar sa bai dogara ga Allah ba sannan baiyi imani da k'addara ba. Wannan wace irin rayuwa ce muke ciki da mata mafi yawancin mu indai akan kishiya,,, bama tsoron gamuwar da Allah mad'aukakin sarki,, mu bi duniya a sannu domin ba gidan zama ba ne. Sannan ba matabbata ba ce rayuwar nan da muke ciki,, idan wata rana kaine wata rana ba kai ba ne ka wuce kabar duniyar kamar ba'a tab'a halitta ka ba,, mu kiyaye"

dan Allah mata...

"Boka SIDDARU bai bar Inna Saude ta dawo gida ba,,, sai da tayi kusan kwana hud'u ga na biyar. Ya bar ta"

ta koma gidan mijinta...

"Kafin ta dawo gida,, shi ma Abu ya gurji Asiya fiye da tunanin mai karatu. Kullum kullum suna manne da"

"juna,,, kamar mata da mijinta itama ke masu girki suna ci. Aisha tana gefe tana kallon ikon Allah,, tana mamakin halinsu Abu da Asiya yadda suke mannewa juna kamar miji da mata. Ita kanta Asiya wata rana daga ita sai bireziya da guntun zane ta ke zama waje,, kuma wata ran Aisha tana kallonta zata shige cikin d'akin Abu ta dad'e.Aisha takan jiyo dariyarsu har da wasanninsu,, takan tausayawa Asiya tare da"

"addu'ar Allah ubangiji ya shirye su,, yasa su gane gaskiya gaskiya ce kuma k'arya k'arya ce..."

"Bayan dawowar Inna Saude dole tasa,,, daga Asiya har Abu kowa ya kama kansa. Suka yi kamar d'ai da"

"duniya babu jituwa a tsakanin su,,, suna hararar juna tare da yin kamar suna mugun jin haushin junansu. Da yake Inna Saude dak'ik'iya ce har yanzu bata gano komai ba,,, game da abinda suke aikatawa. Amma Aisha ko tari tayi sai tasa mata ido,, sannan ga wani mugun tsanar Aisha da ta k'ara ji fiye da lokuttan"

"baya,,, shiyasa ta k'ara cigaba da azabtar da Aisha tare da k'untatama rayuwarta.."

"Cin amana da zalunci da rashin tsoron Allah,,, daga cikin jininsu Saude yake gado tayi a wurin Innarta"

"Harira tsohuwar banza,,, mai halin banza da yofi Allah wadaran da masu irin halin su Inna Harira da Laure..."

"_*Allah ubangiji ya rabamu da bak'in cikin rayuwa,,, yasa kuma mu dace. *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*Sister Hafsat hafnan na tayaki murnar kammala littafinki mai suna FATALWAR MIJINA,, abinda kika"

"fad'a dai dai Allah ubangiji ya baki lada wanda kika yi kuskure,, ubangiji Allah ya yafe miki kurakurrenki albarkacin annabinmu Muhammad (S. A. W). Allah ya k'ara basira da d'aukaka ya sa kifi haka har"

abada.._

*PAGE* 208-209

"Inna Saude bayan dawowarta daga wurin boka SIDDARU,, Aliyu bai tambayeta ba ina tatafi kwana hud'u,,"

"itama dai bata iya tuna abinda ya faru kwata kwata. Saboda boka SIDDARU bai barsu banza ba,, daga ita har Aliyun. Shi kuma boka ya k'ara magance shi ta yadda ko Inna Saude ta yi abinda ba dai dai ba,, bai isa yayi mata magana ba. Domin an rufe mishi baki bai da ikon yin magana,,, shiyasa Inna Saude ta ke yin abinda taga dama kuma alokacin da taso. Sai ma k'ara k'aimi wurin musgunawa rayuwar Aisha da cin Amana,, akullum ta kanyi ma Malam Aliyu tunatarwa akan Lado da Aisha,, ya kan nuna mata ta k'ara hak'uri har yanzu basu gama exam ba. Idan suka kamalla komai zai zama dai dai idan Allah ya yarda,, ta kan nuna mishi taji dad'in maganar shi,, saboda ita a duniya burinta shi ne Aisha ta tabbata cikin bak'in ciki da k'uncin rayuwa da wahala,, bata son duk wani mai son Aisha ko tausayinta. Domin ta tsani kishiya da d'an kishiya a rayuwarta,, bugu da k'ari har yanzu ba wani abincin kirki ta ke ba Aisha ba,, wanda zata ci ta k'oshi ba. Shiyasa Aisha bata damu ba saboda tanada kud'i sosai a hannunta. Saboda haka itama ta siyo kayan abinci irinsu, kwalin Indomie, spaghetti,,macaroni,maggi star,, mr chef, gishiri da sabulun wanka da wanki da dai sauran abubuwan buk'ata na yau da kullum. A kullum idan ta kamalla abincin gida,, ta keyin nata dahuwar abinci tare da amso kayan miya,, wurin babanta idan tayi sai ta d'iba mishi"

"nashi cikin kula mai k'yau. Itama taci nata sai ta k'oshi,, sannan ta shige toilet domin yin wanka.."

"Aisha tana shiga cikin toilet yin wanka,, Asiya ta lab'ab'o ta juye sauran abincin da Aisha ta rage cikin"

"ledar da tazo da ita.Tayi saurin barin cikin d'akin,, Aisha tana fitowa daga wanka ta gane an shigo cikin d'akinta. Ko da ta dubi abincinta sai taga anjuye sauran,, tayi murmushi mai k'ayartar da fuskarta."

"Saboda tasan ba kowa yake mata haka in basu Asiya ba,,, ta je gaban mirror ta cigaba da yin kwalliyarta"

mai k'yau da gani..

"Asiya tana zuwa d'akinsu suka juye abincin,, itada Inna Saude suna ci suna zagin Aisha. Tare da addu'ar"

"Allah yasa ta k'unso cikin shege domin sunsan k'wartayenta ne ke bata kud'i,, da kuma kawo mata suturu masu k'yau da tsada. Saboda su a rayuwarsu sun tsani suga kishiya ko d'an kishiya cikin farin ciki da nishad'i,, domin sun tsani kishiya da duk wanda keson kishiyarsu. Shi kuma Malam Aliyu idan yaci abincin da Aisha ta aje masa,, ya kan kasance cikin tsananin farin ciki da murna,, da kuma tunawa da Amina masoyiyarsa abar begenshi dare da rana. Domin rabon da yaci abinci mai dad'i har ya manta,, saboda tun lokacin da Amina tana raye,, saboda Inna Saude da Asiya basu barin abincin gida yayi dad'i sosai. Kwashe nama suke yi su cinye abinsu kamar mayyu ko kamun yunwa Uwa shegen"

"kwad'ayi d'iya ma haka akwai son abin duniya,, shiyasa Abu yake samun sa'arsu yana siyo musu kayan"

"mak'ulashe yana gurzar Asiya,, batare da sanin dak'ik'iya Saude ba. "

"Haka dai lamarin gidan yake tafiya,, cike da tsananin zalunci da cin amanar Aisha,, tare da kwashe mata"

abinci idan ta dafa a b'oye suna ci suna zaginta .

*********************

"Su Khalifa suna cikin mota suna fira,, cikin shak'uwa da k'aunar juna. Har suka iso bakin get suka danna"

"horn Mai gadi Hassan,, ya bud'e musu get suka kunna kan motarsu cikin gidan. Suna shiga suka parker motar su wurin parking lot,, suka fito daga cikin motar suka nufi hanyar zuwa palourn,, suna shiga suka"

"yi sallama. Rabi'atu ta amsa musu tare da yi musu sannu da zuwa,, domin sun isketa zaune tana kallon"

hausa fim mai suna namijin kishi. Ahmad ya amsa mata tare da zama saman kujera yana kallon fim d'in da ta ke kallo..

"Khalifa yayi mata kallo mai cike da so da k'auna,, yace mata ""my wife ya gida ya kad'aici,, mun iske ki"

"cikin k'oshin lafiya? "".Yace yana mata murmushi mai tarin ma'ana.."

"Rabi'atu tace ""lafiya k'alau kuka iskeni sweet heart,, kuma gida Alhmdlilah kad'aici bana tare da shi"

"saboda yanzu yanzun nan su Ummulkhairi da Fatima,, suka bar nan ai sunada k'ok'arin ziyara wlh Allah dai ya bar zumunci "".."

"""Amin amin amma yau su Fatima sun k'yautamin wlh,, saboda basu barmin farin cikin rayuwata ba cikin"

"kad'aici ba "".Cewar Khalifa yana murmushi mai k'ayartar da fuskarsa.."

"Rabi'atu tace ""ai nima naji dad'in zuwansu matuk'a,, domin bakaga yadda muke fira ba. Hatta da komai"

"na ayyukan gida sun tayani "".."

"Khalifa yace ""Eh lallai sunci abasu k'yauta ta musamman ko ""."

"Rabi'atu tace ""gaskiya sunci k'yauta,, to bari in baku wuri domin ku kintsa cikinku "".."

"Khalifa yace ""A'a my wife kar muyi haka da ke fa,, yi zamanki mana idan domin bro ne kike jin kunyar"

"zama "".."

"Sai asannan ne Ahmad ya d'ago kanshi yana murmushi,, alokacin ne dimples d'insa ke lob'awa,, kuma"

suka k'ara bayyana tsantsar k'yawon da Allah ya bashi..

"Sannan yace ""Matarmu yi zamanki idan ta nine,, kike jin kunya kada mr love yayi min kukan rashin"

"zamanki kusa gareshi "". "

"Rabi'atu murmushi kawai ta ke yi,, tare da duk'ar da kanta ci ke da kunyar maganar Ahmad.."

"Khalifa yace ""kai bro ka cika sa ido,, mi ya kai kunnenka sauraren abinda muke fad'a ni da my love?"

""".Yana harararshi da wasa.."

"Ahmad yace ""Ai shi kunne ba'a yi mishi shamaki,, ga sauraren magana idan har baki ya furta ta. Kaga"

"kuwa banida laifi a nan ""."

"Rabi'atu dai da taga hankalinsu,, ya d'auku ga yin fira tayi shigewar cikin d'akinta. Batare da sun lura ba."

"Khalifa yace ""yayi k'yau ka cigaba da saurarenmu,, muma zamu rama ne akan Aishat"".."

"""Babu damuwa ai na fison ku rama,, mu je dai muci abinci yanzu bro "".Cewar Ahmad.."

"Khalifa yace ""ai nan kafi auki son cin abinci "".."

"Ahmad yace ""babu komai ai ba ciki hak'k'in sa ai gaskiya ne ""."

"Tare suka mik'e suka nufi dinning table,, kowa yaja kujera ya zauna. Suka d'ebi abinda ran kowa yake so,,"

"tare da yin bismillah suka fara cin abinci hankali kwance cikin natsuwa Babu abinda kake ji sai k'arar chokali har suka kammala cin abinci,, tare da yin hamdalah ga Allah,, suka sha ruwa da hollandia. Sunyi"

"shiru suna hutawa can Khalifa ya dubi Ahmad,, yace ""kasan wani abu kuwa bro ?""."

"Ahmad yace ""sai ka fad'a ina saurarenka "".."

"Khalifa yace ""agaskiya kayi dacen mace ta gari mai k'yau,, ilmi,, ladabi da biyayya,, iya magana,, kunya."

"Kuma duk inda mace ta kai Aisha ta wuce nan she is a beautiful and amazing girl,,, you are always lucky"

"in your life gaskiya. Ka k'ara godema Allah mad'aukakin sarki da ya mallaka maka Eshat a matsayin mata "".."

"Ahmad yayi murmushi mai bayyanar da k'yawon da Allah ya bashi,,, yace ""haka ne gaskiya kam"

"maganarka,, nayi dacen mata ta gari. Ni dai fatana burina shi ne mu zauna lafiya "".."

"Khalifa yace ""insha Allah zakaji dad'in zamantakewar aure

Please Login or Register in order to submit comment