You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bak'in zaluncin da sukeyi da cin amana yana nan"

bawai sun daina ba ne.

"Saima abinda ya k'aru, ana nan Inna Harira ta tara su domin tayi magana da su."

"Inna Harira tace ""ba domin komi na tara ku ba, sai don ke (ta nuna Saude ) saboda akwanakin baya kin"

"nuna kina son aure, munje wurin boka ya bamu magani. Mun baki amma shiru ko har yanzu baki samu wanda kike so ba? Naji shirun yayi yawa ""."

"Laure tace ""haka ne kam gaskiya, idan maganin baiyi ba. Sai ki fad'a mana asake wani shirin ko""."

"Saude ta k'ara marairaice fuskarta, kamar zata yi kuka."

"ta ce ""banyi amfani da shi ba, har yanzu saboda ban samu wanda na ke so ba. Amma yanzu na san zan"

"samu saboda na fara cin kasuwa irin garin Rijiyar mai kabi, kamba,k'yangakwai da sauran da garuruwan da ke kusa gare mu ko Allah zai sa na dace da irin wanda na ke so ""."

"Inna Harira tace ""hakan yayi k'yau, na zata ko maganin ne baiyi aiki ba. Karki damu zaki samu kiyi auren ""."

"Laure ta ce ""wannan gaskiya ne Inna,, kuma idan ta samu mijin za'a kai shi wurin boka domin a magance"

"shi ya zama bai ganin kowa sai ke ""."

"Inna Harira tace ""maganarki haka take Laure, zata ji dad'i sosai idan ta yi auren mijin zai zama mata ke"

"kuma ki zama miji ""."

"Saude tace ""godiya nake sosai Inna Harira da yaya Laure ashe kuna matuk'ar sona da son farin cikina ""."

"Laure ta ce ""Saudatu mu burinmu ki kasance cikin farin ciki da walwala. 'Yar k'anwatah ""."

"Inna Harira tace ""hak'ik'a maganarki haka yake, duk fatarmu ku kasance cikin koshin lafiya da farin ciki."

"Muddin ina raye ba abinda zaku nema ku rasa ""."

"Saude tace ""Muna godiya gare ki innarmu, muna sonki sosai ""."

"Laure ta ce ""tabbas muna sonki Inna, domin kulawar da kike nuna wa garemu. Allah ya k'ara nisan"

"kwana ""."

"Inna Harira ta ce ""Amin ""."

"Suka cigaba da firarsu, cike da kwanciyar hankali .. _(Nace idan su Inna Harira suna abubuwan da"

"ran su ke so sai nayi ta mamakin wad'annan bayin Allah, Anya suna tuna mutuwa da kwanciyar kabari da hisabi kuwa?. Hak'ik'a wanda duk yayi nisa ba yajin kira, Allah ya k'ara shiryamu da mu iyalanmu baki"

"d'aya, Amin amin). .._"

"_*Ku cigaba da kasancewa,tare da niiiiiiii *_"

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 81-85

"Aliyu da Amina haka suke gudanar da rayuwar aurensu, cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali"

Babu abinda ta nema ta rasa.

"Komai nasu kansu a had'e ya ke, babu fad'a ko tashin hankali."

"Ana nan wata rana, sai suka samu sabbin mak'wabta, wad'anda suka taso daga Dolekaina zuwa Kamba."

Su ne Shehu da Habiba (Mamansu Abbas) tare da d'an su Abbas.

Dawowarsu Kamba ya zamana yau da gobe ita Habiba tana shiga gidan Amina. Itama wata ran tana shiga

"wurin Habiba,kunsan ance yau da gobe bata bar komi ba."

"Sai ga shak'uwa da sabo ya shiga tsakanin wad'annan bayin Allah, Amina da Habiba."

"Ya zamo k'awance mai k'arfi da shawara da junansu, d'aya baiyin abu sai da sanin d'an uwansa, kansu ya"

"zamo a had'e yake. Idan d'aya yayi abin dad'i ya kan aikama d'an uwansa. Shawararsu da komi ya zamo d'aya, kunsan an ce so gamon jini ne, to jinin wad'annan k'awayen ya gamu sosai."

"Amma shi Shehu mijin Habiba, yafi Aliyu kud'i gaskiya. Saboda yana da rufin asiri sosai kuma shago"

"garesa babba na kansa, mutum ne shiru shiru wanda baya son tashin hankali ko fitina."

"Amina kuwa saboda k'aunar da ke tsakanin su da Habiba,ya zamana Abbas baida wurin zuwa sai wurin"

"Amina, duk abinda yake so tana bashi ko ta siya masa."

Harda shagwab'a yake yi mata saboda bata son b'acin ran Abbas ko kad'an. Har da wanke -wanke da

shara Abbas yake yima Anti Amina (hakan yake kiranta da shi).

"Ahaka suke gudanar da rayuwar su, cike da farin ciki da tsananin shak'uwa."

*******************

"A shiko Inna Harira ta sake zama mai kud'i sosai, saboda ya ki haram ya ki halat."

"Su Laure karuwanci da iskanci ya k'aru, ba abinda su ke sai amshe ma mazan mutane kuma 'yan iska"

"kud'in hannunsu, alokacin kuma Saude ta k'ara d'aukar wanka da yawan cin kasuwanni. Saboda babu abinda yake gurinta irin ta samu miji irin wanda ta ke so ko ta halin k'ak'a ko ana ha maza ha mata."

"Shiyasa ta nacema zuwa cin kasuwa, agaruruwa da dama."

"Abu ma da Lado, abin nasu sai cigaba ya ke. Sun mayar da sab'on Allah kamar ruwan sha, basa jin kunya"

"ko kuma tsoron mahallicinsu, sau da yawa haka zasu tare d'iyan mutane a hanya, suyi musu fyad'e. Su bar yarinya nan kwance ga k'asa."

"A haka dai rayuwar garin ta cigaba da tafiya, cike da k'unci da rashin kwanciyar hankali da walwalah."

*********************

"Agidansu Hadiza ma, Maman Amina ta yawan barinta ta kaima 'yar uwarta ziyara ko wani sak'o haka."

"Suna jin labarin Amina sosai, saboda zuwan da Hadiza keyi akai akai. Ba'a sati biyu bata je wurin Antinta"

ba.

"Adamu ma da matarsa Hussaina,suna yawan kai musu ziyara. Itama Amina da mijinta suna zuwa"

gidansu.........

*********************

BAYAN SHEKARA UKKU

"Abubuwa da dama sun faru, agidansu Aliyu da Amina."

Saboda har yanzu Amina ko b'atan watan bata tab'a yi ba. Tun abin baya damunsu na rashin samun cikin

"Amina. Har yazo tana yawan damuwa da yin hawaye. Duk da yake Aliyu shima ya damu sosai, baya nuna mata yakan lallashe ta. Tare da nuna mata Allah ne ke badawa ga wanda yaso kuma alokacin da yaso, ba k'arfi ba ne ko dabarar mutum ba. Da irin wad'annan kalamai ne yake sanyaya mata zuciya tare da k'ara"

mata k'arfin gwiwa.

"A haka dai suke zaune zaman lafiya. Duk da idan suka tuna da rashin haihuwa, sukan kasance cikin bak'in"

"ciki amma ya zasuyi duk abinda Allah ya tsara ma bawa babu mahani, tun ran gini ran zane. Kuma komai muk'addari ne daga Allah ."

"Habiba idan taga Amina cikin hali, ta kan lallashi Amina tare da bata maganganu masu dad'i da tausasa"

halshe. Tare da nuna tausayin ta ga Amina.........

*******************

"Aliyu da Adamu suna yawan zuwa cin kasuwanni, a gari -gari domin sayo kayan miya da abubuwan"

buk'ata cikin sauk'i da arha.

Sun sha had'uwa da 'yan mata kala -kala masu nuna musu so.

"Sukan nuna basuda ra'ayi ko nuna musu alamar suna sonsu, kowane daga cikinsu yana matuk'ar son"

matarsa.

"Koda yake aure nufin Allah ne, idan Allah ya k'addara babu mahani ko wanda ya isa ya hana shi........"

*********************

"A wata rana, ranar laraba a garin Shiko.Aranar ne ake cin kasuwa a garin Shiko."

Irin wad'annan lokuttan ne Saude ke yawan shiga kasuwa ko zata dace da wanda ta ke muradin aure ko

ta ke so.

"Saboda tafi son mai abin hannunsa, kuma namiji mai k'yau."

"Burin duniya, ta dangana shi da idan tayi aure zata ci duniyar ta da tsinke. Saboda tsananin kwad'ayi da"

buri na cikin zuciyar Saude.......

"Saude ta je cin kasuwa,,,,,,, tana cikin sayayyar kayan abin miya ne.Sai ga su Aliyu da abokinsa Adamu"

"sunje sayayya suma,,,,,, a wurin mai saida hoda da sark'ok'i ne. Saude ta yi gamdakar da Aliyu,,,, alokacin da ta saki da hanci tana kallonsa cikin tsananin so da sha'awa."

"Aliyun baima lura da ita ba, saboda hankalinsa ya d'auku ga wata sark'a domin ya saima Aminarsa."

"Itama Saude ta zo sayen hoda, alokacin ne tayi tozali da Aliyun."

"Suna magana da mai saida kayan kwalliya,"

"Aliyu ya ce ""nawa wannan sark'a Malam ""."

"Mai saida kayan kwalliya, ya ce ""ka bada naira dubu ""......"

"Adamu ya ce ""mi ye sauk'inta Malam ""."

"""Babu wani sauk'i gaskiya "".Cewar mai saida kayan kwalliya."

"Aliyu ya ce ""kamar ya babu wani sauk'i, ai naga ga komi akwai rangwame ko ""......."

"Saude ta tsagal ta chafke maganar ta ce ""ilu ka taimaka, ka saisuwa musu mana, ai gara ka saisuwa da"

"rangwame. Kuma kowa nason sauk'i ""."

"Ilu ya ce ""to Hajiya, duk yadda kike so haka za'a yi, karki damu fa ""."

"Ilu mai saida kayan kwalliya ya dubi su,Adamu ya ce ""ku kawo d'ari bakwai na bar muku ""."

"Adamu yasa hannu a aljihunsa, ya d'auko d'ari bakwai ya ba Ilu."

"Ya juya ya dubi Saude ya ce mata ""mun gode sosai 'yar uwa ""."

"""karku damu fa, ai yiwa kaine "".Cewar Saude cike da kwarkwasa."

"Aliyu dai ko kallo, bata ishe sa ba. Domin ya lura kanta na hayak'i kuma ya ga alamar batada kunya ko"

kad'an.

"Bayan sun gama, sayen abinda zasu saya. Suka kama hanya zasu wuce........"

"Saude ta tasha gabansu, ta kalli Aliyu tana yamutsa fuska ta ce ""Kai Malam baka san anyi maka, abin"

"alkhairi ba kayima mutum godiya ko "".Ta fad'a cike da yanga da yauk'i."

"Adamu ya dubeta da murmushi, ya ce ""Ai ke k'anwatah, haka Aliyu ya ke mutum ne wanda babu"

"ruwanshi da kowa musamman wad'anda basu shafe shi ba ""."

"Saude ta ce ""har da wanda yayi masa, abin k'warai bai san yayi godiya ba""."

"""Haka yake ba zaki iya chanza shi ba gaskiya "".Adamu ya fad'a."

"""To Malam Aliyu, ina son magana da kai "".Cewar Saude."

"Aliyu ya harari Saude, sannan yaja mata tsoki ""Mtsss ""ya k'yaleta."

"Saude ta dubi Adamu, ta ce ""dan Allah kayi masa magana, ya tsaya ya saurari uzurinah. Ba k'yau"

"walak'anta d'an Adam fa ka gaya masa mana gaskiya ""."

"Adamu ya ce ""to k'anwatah "".Ya dubi Aliyu yayi masa alama da kai, ya tsaya ya saurareta ba k'yau"

walak'anta 'ya mace.

"Aliyu ya gyad'a kai, alamar to."

"Dak'yar ya bud'i baki, ya ce mata ""lafiya mi take buk'ata da shi ""."

"Saude cikin zuciyar ta, ta ce ashe haka yake da dad'in murya shiyasa baya son yi magana."

"Adamu ya ce ""mata Ana magana fa k'anwatah ""."

Firgigit!! Ta dawo cikin hayyacinta.

"Sannan ta dubi Aliyu, ta ce ""dama ba wani abu ne, zan fad'a maka abinda ke cikin zuciya tah. Tun lokacin"

"da idanuna suka yi tozali da k'yakk'yawar fuskarka,numfashina ya shak'i daddad'an k'amshinka ,kunnena ya saurari zazzak'ar muryarka. Naji aduk duniya babu wanda nake so, kuma nake muradi ya zamo uban 'ya'yana idan ba kai ba, rashinka zai iya sa rayuwata ta tagayyara. Ka taimaka ka amshi soyayya ta domin"

"samun farin ciki nah da natsuwa tah"".Ta fad'a cike da shauk'in k'aunar Aliyu."

"Aliyu da Adamu kuwa, k'amewa sukayi cike da mamakin furucin Saude. Saboda agaskiya sunyi matuk'ar"

mamakin maganganun Saude.

"Can dai Adamu ya daure, ya ce mata ""baiwar Allah ya sunanki? ""."

"Ta ce masa ""Saudatu ""."

"Adamu ya ce ""Amatsayinka na d'iya mace wad'anda aka fi sani da kunya bai kamata ta ce tana son d'a"

"namiji ba ""."

"""Aganinka ba, ai so makaho ne idan ya tashi shiga baya sallama, balantana neman izni. Kuma so alokaci"

"guda yake shiga "".Cewar Saude."

"Aliyu bai so tab'a mata ba, amma da yaga tana son b'ata musu lokaci ga banza.Ya kalleta ya ce""kehhh!!!"

"Dakata bama son shirmen banza da yofi, daga ganina bakisan inda ni ke ba, ba kisan wane ne ni ba. Zaki zo kina yi mana magana da yaudararrun kalamanki, to bari kiji ni Aliyu bana son ki! Kuma bazan tab'a aurenki ba. Kuma daga rana ta yau kada ki k'ara nuna kin sanni ko kin tab'a ganinah"".ya fad'a cike da"

zafin rai.

"Yaja hannun Adamu da k'arfi suka wuce, suka barta tsaye."

"Saude ta nisa ta ce ""wallahi! Wallahi! Aliyu ko ka k'i ko ka so, saina aureka ko ta halin k'ak'a, amma ba"

"komai mu zuba mu gani ni da kai shege ya fasa. Zaka san wa ce ce Saude d'iyar Galma. Sai kayi nadama a rayuwarka Aliyu "".ta fad'a cike da b'acin rai..........."

"_*Kuyi hak'uri banida lokaci sosai,,,. *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 86-90

"Ilu mai saida hoda, da yaga Saude ta yi tsaye cikeda takaici, ya kira ta, bayan ta je wurinsa."

"Ya dube ta, ya ce ""lafiya Saude naga kin tsaya. Mi ke faruwa ne? ""Ilu ya tambaye tah."

"Saude ta dubi Ilu cike da b'acin rai, ta ce ""Mutumen nan bai da mutunci, wanda bai son magana, Wankan"

"tarwad'a dogon nan ""."

"""Eh na gane shi, mi yayi miki ne? "".Cewar Ilu...."

"""Daga kawai nayi mishi magana, na ce bai iya godiya ba ne. Kasan abokinsa kawai yayi mini godiya, shi"

"ne na ce masa malam babu magana. Ashe ma yana magana duk iskanci ne da rainin wayo wallahi, ni kuma na ce masa ina son shi kuma na gani na k'yasa. Kuma wallahi saina aure shi dole, ya nuna baya sona kuma ya walak'anta ni, Amma zai gane shayi ma ruwa ne, zai gane kurensa, Ni na fad'a maka sai ya dawo garin nan da k'afafunsa ya ce sona a hauka ce, bai san wa ce ce ni ba Allah na ke gaya maka"

""".Saude ta fad'a cike da hasala."

"Ilu ya yi dariya, ya ce ""haba mutuniyata, ke ma kika tsaya cewa kina son shi wannan duk b'ata lokaci ne."

"Da kinsan sunan shi ai shikenan, sunanshi Aliyu mutumen garin Kamba ne, yana da mata d'aya amma Allah bai bashi haihuwa ba har yanzu. Kinji tak'aitaccen labarin abinda na sani game da shi ""."

"Saude tace ""godiya nake Ilu, zanje gida yanzu karka damu zan baka goron albishir da kuma taimakona da"

"kayi, na fad'a min d'an wani abu game da Aliyu ""."

"""Karki damu Saude, ai ana tare kuma yi wa kaine. Allah ya sa ki samu Aliyu "".Ilu ya fad'a."

"Saude ta zaro dubu d'aya ,ta ba Ilu ta ce ""Ai na kuwah gode k'warai da gaske. Allah ya bar zumunci ""."

"Ilu ya sa hannu ya amshe kud'in, ya ce mata ""Amin amin,,,, nima na gode sosai fa, duk abinda ki ke son"

"tambaya karki ji komai ki tambaye ni. Idan na sani zan sanar da ke ""."

"Saude ta ce ""Babu damuwa, ni zan wuce gida. Karka ji komai duk abinda ban sani ba zan tambaye ka ""."

"Ilu ya ce ""to babu matsala, Allah ya kai ki gida lafiya. Ki gaida su Inna da Laure ""."

"Saude ta ce ""Amin,,,,, zasu ji da naje gidan kuwah ""......."

"Ilu ya ce ""To,,, ""...."

Saude ta kama hanya tayi wucewarta zuwa gidansu...........

**********************

"Su Aliyu da abokinsa Adamu kuwa, bayan sun iso gida."

Kowanen su ya shiga gidan sa ya kintsa.

"Bayan awa ukku, Adamu ya aiki yaro domin akira masa Aliyu...."

"Yaro ya shiga gidan, ya fito ya ce masa. Wai yana zuwa, ya d'auki murtala ya ba yaron. Yaron yayi godiya"

ya yi wucewarsa....

"Bayan wasu mintuna, sai ga Aliyu ya fito daga gida."

"Yayi masa sallama, suka yi musabaha da juna. Suka samu wuri suka zauna ga bencin k'ofar gidan."

"Aliyu yadubi Adamu, ya ce ""ya dai abokina, wani abu ya faru ne ?"""

"Adamu ya ce ""Ai kafi kowa sanin abinda ya faru, mi yasa kayi haka abokina? .Baka tsoron abinda zaije ya"

"dawo ne, baka tsoron kaidin mata. Kasa ni walak'anci baya da k'yau ko ga addinimu na musulunci, abinda kayi gaskiya bai da ce ba. Kuma bai kamata ba, ni dai gaskiya ce nake fad'a maka ko don nan gaba"

"""."

"Aliyu ya yi shiru, yana nazari da tunani. Can ya ce""Adamu kayi hak'uri nasan ban k'yauta ba. Yarinyar ce"

"na lura batada kunya ko kad'an, da kuma alamun kamun kai shiyasa nayi mata haka. Kasan kuma ni bana son takura ko damuwa, Amma Insha Allah zan kiyaye gaba ""."

"Adamu ya ce ""ba komi Aliyu, dama mutum ya kanyi kuskure daga baya ya dawo ya ga ne abinda ya yi bai"

"da ce ba. Saboda haka karka damu, Allah ma muna masa laifi, mu neme sa gafara ya yafe mana. Abinda za'a yi idan muka koma ka nemi gafarar yarinyar kaji ""."

"""karka damu Adamu, da mun koma zan nemi yafiyar ta idan Allah ya yarda "".Aliyu ya fad'a......"

"Adamu ya ce ""Allah ya sa mu k'ara ganinta abokina ""."

"""Amin abokina "".Cewar Aliyu......"

"Suka kama firarsu, cike da nishad'i da kwanciyar hankali..........."

*********************

"Saude kuwa tana komawa gidansu, abinci kawai ta ci sannan ta yi wanka."

"Ta samu Inna Harira da Laure, ta kawo bayanin komi ta fad'a masu...."

"Inna Harira ta yi dariya, ta ce Lallai yaro bai san wuta ba, sai ya taka. Ai kin bani haushi da kika tsaya ya"

"gaya masa yana walak'anta ki, da kizo kawai ki gaya min. Sha yanzu magani yanzu ""."

"Laure ta buga tsaki ""mtsssss ""sannan ta ce ""Aikin banza da yofi, ai zai gane bayada wayo shi Aliyun. Don"

"ma kin ya samu kince kina son sa,mi aka yi akayi shi. Ni wallahi ban d'auki namiji abakin komi ba, fa ce rigar da zan iya sawa na canza akowane lokacin da na ke so ""."

"""To ya zanyi? Yaya Laure so ne sanadi, shi yaja mini shiga wannan hali "".Saude ta Fad'a cike da"

marairaicewa.

"Laure tace ""na sani 'yar k'anwatah, karki damu komai zai zama dai -dai""."

"""haka ne kam gsky, yanzu abinda za'a yi ku tashi mu tafi banga ta zama ba. Mu je can wurin boka"

""".Cewar Inna Harira."

"Laure ta ce ""A'a Inna kin manta ne ya bamu ruwan maganin da batayi amfani da shi ba. Ta fara gwadawa"

"ynz idan bai yi ba, sai mu sake komawa wurin boka ""."

"Inna Harira ta ce ""Kinga ko wallahi har na manta, ke Saude ki tari wani satin idan ya dawo sai ki shafa"

"maganin, in yaso daga baya mu koma mu amso miki na mallaka ""."

"""To Inna haka zanyi ai, zan shafa maganin ranar wata laraba idan sun dawo shi da abokinsa "".Saude ta"

fad'a.

"Laure tace ""hakan ma yayi ,karki manta fa ""."

"""Bazan manta ba yaya Laure "".Cewar Saude."

"Inna Harira ta ce ""ta manta, ta rasa Aliyun domin kuwa daga yanayin labarin sa. Sai yayi jiji da kai ""."

"Laure ta bushe da dariya, sannan ta ce ""ke Inna akwai ki da ban dariya wlh. Har kinsan sai yayi ji da kai"

"daga labari ""."

"""Eh mana, ni ai ba yarinya ba ce irin ku, daga bada labari zan iya fahimtar wani abu "".Inna Harira ta fad'a."

"""haka ne maganarki Innah "".Cewar Saude ta na murmushi......."

"A haka dai suka cigaba da firarsu, da kuma shawarwari ta yadda zasu b'ullo ma Aliyu. Da yadda zai shiga"

"hannun Saude bata re da wahala ba, ko wani b'acin rai ba.........."

"_*Kuyi manage da wannan page,,,,,. *_"

*Muje Zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_Ki sani kina cikin zuciyatah, k'aunar da nake miki daga Allah Zainab Usman_ "

"_*Godiya da jinjina gareka, Dr Zain ka sani ban manta da halaccin ka gare ni. Allah ya bar k'auna"

*_

*PAGE* 91-95

"Abu da shi da abokinsa Lado, rayuwar su ta k'ara zama abar tsoro ga mutane. Domin kuwa har hayar su"

"ake d'auka saboda su kashe rai ba'a bakin komai ya ke gare su ba. Sun mayar da yin fyad'e, zina da kashe rayuka kamar ruwan wanka."

"Babu tausayi ko rahama, dangane da al'amurransu......."

"A haka dai suke gudanar da rayuwar su, cike da rashin tsoron Allah mad'aukakin sarki........"

*********************

"A can gidan su Aliyu, Amina ce zaune suna fira. Bayan ta kamalla ayyukan ta na gida......"

"Ayayinda Aliyu ya ke ce mata ""Aminatu tah ki sani ina matuk'ar k'aunar ki a rayuwa ta, sonki ya riga yayi"

"gini a cikin jinin jikina. A duk duniya baya ga iyaye na wallahi babu wanda nake so sama da ke, shiyasa bana fatar ko wani abu da zai zo ya shiga a tsakanin mu wanda zaiyi sanadiyyar rabuwar mu "".Ya fad'a"

cike da sanyin jiki.

"Amina tace ""wallahi mijina, ina ji kamar yadda ka ke ji. Ka sani nima ina matuk'ar k'aunar ka, wanda nima"

"bana fatar wani ya rabamu fa ce mutuwa. Ko itama dan ya zama dole ne babu yadda mu ka iya ""......."

"""Ki daina fad'ar mutuwa aminatu tah, wallahi hankalina tashi ya ke. Bana fatar ki mutu ki barni cikin"

"duniyar nan mai cike da 'k'unci da bak'in cikin rayuwa.Akullum addu'a ta shi ne Allah ya bamu 'ya'ya na gari wad'anda zamu basu cikakkiyar tarbiya da gata idan muna raye "".Aliyu ya fad'a cike da shauk'in"

k'aunar matarsa.

"Amina ta ce ""Amin ya farin cikina, Amma ka sani dole duk musulmin k'warai ya dinga tunawa da mutuwa."

"Ta haka ne zai dinga jin tsoron had'uwarsa da ubangiji Allah. Sannan zai kasance duniya ba zata shagaltar da shi ba da abinda ke cikinta ""."

"""Maganarki haka take Amina, hak'ik'a ina k'ara godiya ga Allah mad'aukakin sarki. Da ya bani ma ce mai"

"ilmi da kaifin tunani, tausayi, biyayya da kuma sanin ya kamata. Allah ubangiji na rok'e ka, ka bamu 'ya'ya na gari "".Aliyu ya fad'a...."

"Amina ta ji dad'in addu'arsa, har cikin ranta... Ta ce ""Amin mijina ""."

"Aliyu ya dube ta, yace ""Aminatu ki sani ke ce farin cikina, kuma ke ce rayuwata. Ina son ki da son"

"k'yakk'yawan halayyarki, bana fatar wani abinda zai rabamu komi k'ank'antar shi, An hallacci sonki daga jinin jikina ""."

"""Na sani ya kai mijina, ni ma ina tsananin son ka. Da sonka na ke rayuwa kuma da shi zan mutu. Dai -dai"

"da rana d'aya bana fatar abinda zai zo ya shiga a tsakanin mu. Ka sani har abada ni ta ka ce, kai na wa ne. Ruwa ko iska ba su isa su rushe ginin da kayi a cikin zuciya tah ba "".Amina ta fad'a cike da tsananin"

k'aunar mijinta.

"Aliyu ya ji dad'in kalamanta sosai. Ya dube ta ya ce ""godiya na ke da wannan soyayyar ta ki gare ni. Allah"

"ya bar k'auna sannan ya yi mana katanga da duk mai son shiga a tsakanin mu ""........."

"Amina ta ce ""Amin farin cikin rayuwata, mallakin zuciya tah ""....."

"Aliyu yayi murmushi, ya ce ke ce tauraruwar zuciya tah, kuma fitila mai haskaka duk ilahirin jikina ""."

"""Godiya na ke ya kai uban 'ya'ya, tauraro mai kyalli a cikin zuciya tah "".Amina ta fad'a cike da son"

mijinta........

"Aliyu ya ce ""Allah ya barmu tare ""........"

"Ta ce ""Amin""."

"Haka dai suka cigaba da firarsu, cike da nishad'i da kwanciyar hankali. Da kuma shawarwari akan wasu"

matsalolin na yau da kullum...........

********************

"A wata ranar laraba ne a garin Shiko, Saude ta tashi da wuri tayi wanka da kwalliya. Kamar wadda zata"

"gurin party, ta kawo kaya masu bayyana jiki ta sa......"

"Bayan ta kamalla shiryawa ne, ta fito ta ce ma Inna Harira da yaya Laure zata wuce can cin kasuwa....."

Inna Harira ta d'auko kud'i masu yawa ta ba ta.....

"Bayan ta b'ata kud'in ta karb'a... Sannan ta ce ""To Saude ki kiyaye yadda zaki yi amfani da maganin da"

"boka ya basuwa.Saboda ina jiye miki nadama idan aka samu matsala, domin ni dai gaskiya babu ruwana. Idan ba ki yi da k'yau ba ""...."

"Saude tace ""Inna zan kiyaye, karki damu ba za'a samu wani matsala ba "".."

"Laure ta ce ""Dan Allah k'anwatah ,ki kiyaye domin samun nasararki shi ne nasararmu, matsalarki ita ce ta"

"mu. Ki lura da k'yau kinji ko ""."

"""Babu damuwa Yaya Laure zan kasance mai cika umurninku da kuma yi muku biyayya tare da sanyaku"

"cikin farin ciki "".Saude ta fad'a."

"Laure ta ce ""To karki manta fa, sannan karki damu idan maganin ya fara aiki. Zamu je wurin boka domin"

"ak'ara mallaka miki shi ""."

"inna harira ta ce ""haka ne kam, sai kin mallaki Aliyu yadda ranki ke so. Kin juya shi son ranki yadda ko"

"kara kika aza masa, ki kace kada ya ta ka. Ba zai taka ba ""........"

"""Allah ya bar mana ke Innarmu, to zan wuce can kasuwa "".Cewar Saude."

"Laure ta ce ""Allah ya kiyaye hanya ""."

"""Amin "".Cewar Saude........."

Tasa kai tayi wucewarta wurin zuwa kasuwa.......

"Ta bar su nan, suna fira ta yadda zasu b'ullo ma al'amarin Aliyu da kuma yadda zasu magance shi.........."

*********************

"Acan gidansu Aliyu, aranar Adamu ya sallama mishi domin ya fito su je cin kasuwa a garin Shiko."

"Kowa ya yi sallama da iyalinshi, sannan suka je tasha......"

Suka shiga motar zuwa garin Shiko.........

*******************

"Bayan sun sauka lafiya,,,,, suka kama yin sayayyar kayayyaki har saida suka gama....."

"Bayan sun gama, suka je wurin Ilu mai saida hoda..."

"Ilu na ganin su yayi murmushi,,,,,,sannan ya ce ""musu sannun su da zuwa, su Aliyu ne a garin namu ""."

"Suka ce masa ""Yauwah, eh mune ""."

"Ilu ya ce ""To madallah, haka ake so lafiya dai na ga kunyi shiru? ""."

"Adamu ya ce ""lafiya k'alau, dama ba wani abu ba ne. Wannan yarinya mai suna Saudatu muke son gani"

"yanzu ""."

"Ilu ya ce ""karku damu, bata nesa da zuwa yanzu. Ku samu wuri ku zauna ga tabarma nan "".Ya fad'a (A"

"cikin zuciyar sa yana mamakin halin Saude, na rashin imani da tausayi. Daga ganin Aliyu kenan har ta magance shi, in ba haka ba miye ya kawo shi wurinta. Lallai wannan Saude ta cika shed'aniya uwar ibilisai kuma tayi iya makirci da kissa. Allah ya k'ara kare mu daga shairin mugayen mutane masu halayya"

irin su Saude)........

"Aliyu yace ""to mun gode da karamci ""."

"Ilu ya ce ""Babu komai wallahi ""......."

"Haka suka zauna ,suna firar su cike da shak'uwa da k'aunar juna........"

********************

"Saude ce na hango, tana tafiya tana yanga

Please Login or Register in order to submit comment