You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ne da k'addara ta ""...."

"Habiba ta ce ""hak'ik'a mun gamsu da bayananki,, kuma gaskiya ki ka fad'a Aminatu.. Allah ubangiji ya"

"k'ara sanyaya miki zuciyar ki ya kuma cire miki damuwa ""..."

"Hussaina ta ce ""Amin, ki k'ara hak'uri Amina. Komai yayi farko yanada k'arshe,,,wata rana sai labari""...."

"""Insha Allahu,, zan kasance mai d'aukar maganganunku,, zan kuma k'ara hak'uri da juriya akan lamarin"

"duniya.. Saboda nasan komi bayada tabbas,, kuma hak'uri yana kai mutum ga nasara a rayuwa "".Amina ta fad'a cike da sanyin jiki...."

"Haka dai suka kama lallashinta,, tare da nasihohi da kalamai masu kwantar da hankali...."

"Kowace daga cikinsu, ta kama mata aiki,, suka gyara gidan tare da yi mata girki.. Da hirarraki masu dad'i"

wad'anda zai sa tayi saurin samun natsuwa da sakin jiki...

"Bayan sun kammala komi ne,, suka tasa tayi wanka tare da tsantsara kwalliya mai k'yau da gani,, suka"

fashe ta da turare.......

"Sannan Kowacce tayi gidanta,, na aure... _(Hak'ik'a sun burgeni kuma sun bani sha'awa,, Amina ta yi"

"dacen k'awayen k'warai masu halayyar kirki.. Samun k'awayen k'warai a wannan zamanin yanada wahala,, wadda zata so ki da gaskiya da kuma zuciya guda. Amma fa ni ina da sunanta. Allah ubangiji"

ka bamu k'awayen na gari masu son mu da zuciya guda).._

"Basu jima da wucewa ba,, sai ga Aliyu ya dawo daga garin Shiko...."

"Tayi masa sannu da zuwa,, kamar ba wadda ta gama kuka ba..tare da kawo masa ruwa da abincinsa..."

"Bayan ya gama,, tayi masa ban gajiya da kuma tambayar yadda ya baro su Saude...."

"Ya nuna mata,, komai lafiya k'alau..."

"Ta had'a masa ruwan zafi,,, ya shige wanka cike da gajiyar hanyaaaa......"

********************

WASHE GARI

"Bayan Malam Ibrahim (baban su Amina) yayi wanka,,, yayi breakfast. Ya shirya domin zuwa gidan"

yayansa Malam Ayuba....

"Maman Amina da Hadiza, suka yi masa Allah ya kiyaye hanya...."

"Ya ce ""Amin "".."

"Ya yi wucewarsa,, zuwa gidan yayansa...."

"Bayan ya fita ne,, Hadiza ta kalli mamanta ci ke da marairaice fuskarta..."

"Ta ce ""Haba Mama yanzu abinda yaya Aliyu zai yi,, ya da ce fisabilillahi ya rasa abinda zai saka mata da"

"shi sai yi mata kishiya.. Haba duk irin k'yautatawar da ta ke masa ba ya gani ne,,, wannan cin amana ne kuma zalunci ne ""...."

"Mama tayi matuk'ar mamaki da kalaman Hadiza,, ta ce ""Hadiza ba cin amana ba ne. Wannan shi ne dai -"

dai kinsan mu bamu isa mu hana abinda Allah ya k'addaro ba. Yin aure Allah ne ya ce ayi ba fad'ar

"mutum ba,,,kuma bai isa guje ma k'addarsa ba Mu dai mutaya Amina da addu'a Allah ya bata ikon cinye jarabawar rayuwarta ""...."

"""wallahi ina tausayawa Anti Amina,, saboda hak'urinta, juriya da zurfin cikinta yayi yawa... Gashi yanzu"

"za'a yi mata kishiya ta zo tana musguna mata.Kuma abin haushi da k'arin takaici su baba ne zasu nema masa aurenta,, nasan ma shi ne wakili.. Na so kada baba ya saka bakinsa cikin wannan lamari,,, da anbar shi da Baba Ayuba ko auren ya hana masa yi "".Cewar Hadiza ci ke da takaici da jin haushi....."

"Mama ta rik'e baki,, ta ce ""Oh!! ni Salamatu ,,Allah ya had'a ni da kinibabbar yarinya. To idan Babanku"

"bai shige masa gaba ba,,, wa ko ke so ya shiga.. Don za'a yi ma Amina kishiya ai ba gare ta farau ba,, balle a k'are a kanta..Kinga Hadiza don Allah ki daina irin wad'annan maganganu,,, komai na duniya ai d'an hak'uri ne wata rana sai labari,, zai wuce kamar ba'a yi ba ""."

"Hadiza ta ce ""na bari Mama,, Allah ya huci zuciyarki ""....."

"""Babu komai ai,, Allah ya yi miki albarka "".Mama ta fad'a....."

"Hadiza ta ce ""Amin Mama ""..."

"Mama ta cigaba da yi ma nasiha,, tare da nuna mata muhimmanci hak'uri da juriya da iya zama da"

"mutane,,, a rayuwarmu ta duniya.....(kunji uwar k'warai, mai halin dattako da karamci)...."

**********************

"Malam Ibrahim ne,, ya yi sallama a k'ofar gidan yayansa..."

"Bayan wasu mintuna sai ga Malam Ayuba ya fito,,, suka yi musabaha da juna cike da tsananin k'aunar"

juna..

"Yaja Baba Ibrahim,, yayi masa jagora har cikin gidan na shi....."

"Suna shiga cikin gidan,, ya kira matarsa Indo ta kawo musu tabarma ta shimfid'a tare da ruwa...."

"Bayan 'yan gaishe -gaishe na zumunci,,, tare da tambayar kwana biyu..."

"Malam Ibrahim ya natsu,, ya kawo labarin komai ya gaya musu na game da k'arin auren da Aliyu ya ke so"

"yayi... Tare da kuma neman shawararsu da amincewarsu,, akan su bashi goyon baya.."

"Maganar ta basu mamaki k'warai da gaske,, amma ya suka iya da d'an yau..."

"Can Malam Ayuba, ya ce cikin damuwa ""Agaskiya ni ban amince da wannan auren ba,, ta ya za'a yi"

"yarinya ko haihuwa bata yi ba,, ya ce zai mata kishiya yanzu. Don yana son ya nuna mata bata haihuwa,, ai haihuwa ta Allah ce. Yana basuwa aduk lokacin da ya so ""......."

"""Yaya munji ra'ayinka,, wannan ba hujja ba ce,, ya dai nuna yana son k'ara aure ba don Amina bata haihu"

"ba. Yanzu yaya Indo fad'i ra'ayinki ke muke saurare "".Baba Ibrahim ya fad'a cike da natsuwa..."

"Inna Indo ta ya mutsa fuskarta,, sannan ta ce ""Ni dai aganina tunda shi ke da ra'ayin k'ara aure,, to"

"abarshi yayi abinsa ai idan ba zai iya d'aukar nauyinsu ba. Ba zai jajibo ma kansa aure ba,, kuma namiji"

"mijin macce hud'u ne Allah ne ya halatta masa.. Kuma duk wadda yayi aure yana buk'atar ganin magajinsa "".Inna ta fad'a cike da ra'ayi..."

"Hak'ik'a maganar Inna Indo,, ta bala'in k'ona musu rai sosai musamman Malam Ibrahim..."

"Baba Ibrahim ya dube ta,, ya ce ""hak'ik'a maganarki gaskiya ce,, kin kawo hujjoji masu k'arfi kuma abin"

"nazari da tunan. Kuma Insha Allah Aliyu zai yi wannan auren"".Ya fad'a cike da sanyin murya..."

"Baba Ayuba ya harari Inna Indo, cike da takaici ya ce ""wa ya ce ki saka mana, shegen bakinki wanda bai"

"fad'in alkhairi.. Ni ne uban d'a don haka Indo ban amince masa ya k'ara aure ba,, ko akwai wanda ya isa ne ""....."

"""kada Allah ya sa ka amince,, aure ne har anyi an gama. Dama akan wata juyar banza kake so, ka hanama"

"d'ana aure wadda sai dai ta ci tayi k'aton kashi.. To ka sani nima ina da hak'k'i akansa kuma ni ce uwarsa.. Babu shegen munafikin da ya isa ya hana wannan auren "".Inna Indo ta fad'a cike da hargowa tare da"

hararar Baba Ibrahim...

"""Mu zuba mu gani, ni da ke shege ya fasa "".Cewar Baba Ayuba..."

"Baba Ibrahim ya ce ""yaya dan Allah, kuyi hak'uri ku daina fad'a. Wannan magana hukuncinta mai sauk'i"

"ne ai "".Ya fad'a cike da tausasa harshe...."

"""Ai dole ka ce haka Ibrahim,, gashi kana son raba ni da mijina da kuma d'ana "".Inna Indo ta fad'a tare da"

"shigewa d'aki,, ta bugo musu k'ofa da k'arfi ""garararafff!!! Cike da jin takaicinsu...."

"Ibrahim ya dubi yayansa,, ya ce ""dan girman Allah,, yaya kayi hak'uri ka bari ayi auren nan.. Wallahi"

"Amina bata damu ba kuma ta amince domin sunyi waya da Salamatu,, ayayinda ta ke nuna mata da amincewarta yake neman auren.. Kaga idan ka hana zai iya sa Indo da Aliyu su tsani Aminatu,, kuma kaga bamu isa muyi jayayya da k'addara ba,, kaga kuma Ubangiji ne ya halatta masa ya k'ara aure "".Cike"

da lallashin yayansa ya fad'a....

"Baba Ayuba ya ce ""Babu komai tunda Amina ta aminta,, kaje kaida Malam sama'ila wurin nema masa"

"aurenta.. Amma ya sani babu kwabona cikin wannan lamari,, shi da yaji ya gani yaje yayi abinsa,, babu ruwana ""...."

"""A'a yaya idan kana fad'ar haka,, saina ga kamar baka yarda da k'addarar ubangiji ba.Kamata yayi ka"

"sanya musu albarka a cikin wannan auren "".Baba Ibrahim ya ce...."

"Baba Ayuba ya ce ""to naji,, Allah ya sanya alkhairi da albarka a cikin wannan aure. Ya kuma sa ayi lafiya ""."

"""Amin amin "".Cewar Baba Ibrahim..."

"Baba Ibrahim ne, ya ke janshi da fira. Domin ya d'ebe masa takaicin abinda Inna Indo tayi masa.. Hak'ik'a"

ya san d'an uwansa yana matuk'ar k'aunar sa da kuma iyalinsa...

"Baya son duk wani abinda zai b'ata ran Ibrahim,, akwai fahimta, tausayi da tsananin shak'uwa a tsakanin"

su....

"Ita ko Inna Indo tana da halin k'warai,, sai dai masifaffiya ce sannan ta na mugun son d'anta saboda shi"

kad'ai Allah ya ba su.....

"Shiyasa komi Aliyu ya ke so,, da gudu ta ke yi masa. Bata tsaya tayi tunanin abin ya da ce da shi ko bai"

"dace ba,, ita dai burinta ta faranta masa koda zata b'atawa kowa a rai..."

"Haka ta ke macce ce mai son na ta,,, da kanta babu ruwan ta da wani......"

"_*Ko ya abin zai kasancewa,,, ku biyo karku gajiiii *_"

*Muje Zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*Wannan shafin sadaukarwa ne, ga my lovely brother Imran Musa. Ka sani ina matuk'ar sonka yayana,"

kayi abinda uwa zata iya yima d'anta a rayuwata. Daban ka ke a cikin zuciya ta*_

*PAGE* 111-115

"Bayan Baba Ibrahim ya wuce zuwa gidan Malam Sama'ila ne,, Baba Ayuba ya k'walama Inna Indo kira......"

"Yace ""Indo! Indo! Da k'arfi...."

"""Na'am Maigida ""Cewar Inna Indo..."

"Ta fito daga d'akin da saurinta,,, sannan ta ce ""Gani Maigida, wannan irin kira fa.Lafiya dai? ""....."

"""Ba lafiya ba Indo,, ina son naja miki kunne ne akan abinda kika yi d'azu,, kin kunyatani a gaban k'anena."

"Kin nuna min banda wata kima da daraja a idonki,, agaban k'anena zaki dinga kiran d'iyar shi juya,, bayan kinsan Amina d'iya ce agareni..Wannan wane irin rashin mutunci ne,, saboda haka wallahi ki kiyaye ni."

"Na fiki rashin kunya saboda haka idan haka ta sa ke faruwa rayuwa zata b'ace "".Malam Ayuba ya fad'a"

cike da jin haushin Inna Indo...

"Inna Indo da ya ke ma ce ce, wanda bata son b'acin ran mijinta....."

"Tasassauta murya,, sannan ta ce ""Dan girman Allah kayi hak'uri ban fad'i wannan magana ba,, domin na"

"b'ata maka rai ba.. Kawai ni dai aganina a bari Aliyu yak'ara aurensa,, domin naga yana ra'ayin abin,, idan Allah ya k'addara wata k'ila sanadiyyar auro wata k'ila ta samu na ta rabon.. Kasan komi yana da lokacin"

"sa ""......"

"Baba Ayuba ya ce ""Kinsan da haka amma d'azu kina fad'in abinda kika gadama ko,, kina magana kamar"

"wadda batada tauhidi. D'azu abinda kika yi banji dad'i ba wallahi,, kuma kin b'ata min rai sosai ""....."

"""Allah ubangiji ya huci zuciyarka Maigida,, dan Allah ka k'ara hak'uri da ni,, sharrin shed'an ne da rashin"

"danne zuciya.. Amma Insha Allah irin haka ba zai sa ke faruwa ba "".Inna Indo ta ce,, cike da nuna nadamar ta a fili...."

"Baba Ayuba yace ""Babu komi ai ya wuce,, Amma dan Allah ki dinga sanin irin maganganu da zasu fito"

"bakinki,, kiyi tunani da nazari kafin ki furta magana kinji ""...."

"Inna Indo ta ce ""In Allah yarda zan san irin maganganun,, da yadace su fito a bakina.. Ko wannan kuskure"

"ne ""....."

"Baba Ayuba ya ce ""To yayi k'yau,,, Allah ya k'ara rufa mana asiri.. Don Allah a kiyaye kinji ""...."

"""Amin, insha Allahu ""Cewar Inna Indo...."

"Haka dai Inna Indo,, ta ke jan Baba Ayuba da fira.. Tun bai son amsa mata har ya fara amsa mata. Kunsan"

"an ce tsakanin mata da miji sai Allah,, xo mu zauna zo mu sab'a ne.. Dama haka rayuwar ta gada komai na duniya d'an hak'uri ne,, ya zamuyi duniyar ce ta zama haka dama ita duniya ba wurin jin dad'in"

musulmai ba ce.....

**********************

"Malam Ibrahim kuwah,, bayan fitarsa gidan yayansa,, direct gidan Malam Sama'ila ya nufa....."

"Bayan yazo k'ofar gidan ne,,, yayi sallama da k'arfi ta yadda zasu ji...."

"""Salamu Alaikum, salamu alaikum "".."

"""Amin Wa'alaikas Salam "".Cewar Malam Sama'ila daga cikin gida...."

"Malam Sama'ila ya shuri takalminsa da sauri,, ya fito waje domin ya ga kowa ye....."

"Bayan ya fito ne,, sai ya ga Malam Ibrahim ne.. Ya bashi suka yi musabaha tare da gaisawa..."

"Malam Sama'ila ya ce masa ""bismillah, shigo daga ciki mana ""..."

"""Ba sai mun shiga ciki ba Sama'ila,, nan ma yayi ba matsala "".Baba Ibrahim yafad'a....."

"Malam Sama'ila yace ""to babu damuwa,, mi ke faruwa mi ke tafe da kai.. Naga kamar bakinka akwai"

"alamun magana ""...."

"Baba Ibrahim yace ""Eh akwai magana,, ba wani abu bane yakawo ni,, illah yaron wajenmu ke son wata"

yarinya acan garin Shiko.. To shi ne yaya Ayuba ya ce da ni kai da wani muje mu nema masa aurenta domin basa son auren yaja dogon lokaci. Shiyasa na ce bari muzo muyanke shawarar ranar da zamu Je

"can d'in ""...."

"Malam Sama'ila ya ce ""ka barshi jibi sai muje wannan ba matsala ba ne.. Sai a samu k'anen Indo Audu"

"muje tare da shi,, ayi komi gaba gare shi kasan itama tanada hak'k'i matsayinta na uwa ""...."

"""Wannan babu matsala,, maganarka tayi dai-dai kuma haka ya dace. Allah ya kaimu jibi muna masu rai"

da lafiya.. Cewar Baba Ibrahim....

"""Amin amin "".Malam Sama'ila ya fad'a....."

"Malam Ibrahim ya ce ""To ni zan wuce gida,, Agaida su Ladi ""...."

"""Insha Allahu,, zasu ji "".Cewar Malam Sama'ila....."

"Baba Ibrahim ya kama hanyar zuwa gidansa,, shi kuma Malam Sama'ila ya shige cikin gidaaaaa....."

********************

"A bangarensu Inna Harira kuwah,, suna nan suna ta shirye -shiryen kayan biki da kuma sai ma Saude"

kayan d'aki dai -dai gwargwado iya k'arfinsu...

"Inna Harira ta je wurin boka Namuna,, ita kad'ai domin Saude ta mallaki Aliyu da k'yau da k'yau. Sai da ya"

"kwanta da ita sannan ya bata wani garin magani,, ya ce mata a dinga barbad'a masa a cikin abinci da ruwan shansa.. Sannan sai an tashi tsaye suna zuwa wurin boka akai -akai in bashi ba. Asirin zai iya walwalewa a kowane lokaci saboda jikin Aliyu da Amina akwai tsari sosai,, suna yawan yi azzakar da zama da arwala. Sannan kuma iyayensu su na yawan yi musu addu'a,,, sannan Saude ba zata iya raba soyayyar da ke tsakanin su ba.. Ana dai iya shiga a tsakanin su amma ba yanzu ba,, sai nan da lokaci gaba"

"kad'an,, tayi kissa da munafurcin ta tana had'a su fad'a kafin asirin ya fara aiki a kansu... ."

"Inna Harira ta nuna masa babu matsala,, tare da alk'awarin Saude zata kiyaye insha Allah.. Tayi masa"

godiya sannan ta dawo gida...

"Bayan ta dawo ne,, ta wuce cikin d'akin Malam Isiyaku direct....."

"Babu sallama barai gaisuwa,,,ta iske shi zaune yana addu'a. Bayan ya gama shafa addu'ar ne ya jiyo ya"

fuskanci Inna Harira....

"Ya ce ""Mi ke tafe da ke Harira?"".Ya fad'a yana kallon ta..."

"Sai da Inna Harira ta hararesa,, sannan ta ce ""dama ina son in fad'a maka ne,,, Saude ta samu mijin aure."

"Gobe ko jibi zasu zo tambayar aurenta. Saboda haka bama son auren ya wuce sati biyu,, ka zama cikin shiri""......"

"Malam Isiyaku ya nisa,, ya ce ""karki damu Harira yadda kike so haka za'a yi.. Allah ya nuna mana lokacin"

"lafiya,, to ita Laure har yanzu bata fidda miji ba ne? Sai a had'a su tare ayi auren ""..."

"""Amin,, to kuma ina ruwanka da Laure.. Ina ce dai ni ce uwarta kuma ni ce ubanta.. To bata tashi yin"

"aure ba,, ko ana dole ne wai.. Kaji tsohon munafiki Argungumi kawai,, mai halin fir'auna "".Inji Inna Harira cike da masifa da bala'i...."

"Malam Isiyaku ya ce ""Allah ya baki hak'uri Harira,, ni dai tambaya ce kawai nayi kuma na ga nasan idan"

"baki d'auko min hirar auren Saude ba.. Ba abinda ya shafe ni domin kuwa duk abinda kuke yi na kawo ido nasa muku ""......"

"Inna Harira ta ce ""Maganar banza,, idan baka sa mana ido ba. Dama akwai abinda zaka iya yi ne damu,,,"

"shege tsohon banza wanda ya yi hasarar duniya,, wanda bai san ciwon kansa ba.. To tsaya kaji babu shegen da ya isa inji tsoronsa duk fad'in garin nan,, saboda nafi mutum iskanci da iya shege wallahi "".."

"Malam Isiyaku ya dad'e yana tunani a cikin zuciyarsa,, yana cewa har ya koma ga mahallicin shi ba zai"

"daina da nasani da nadamar auren Harira.. Yanzu fa ji abu ba na fad'a ba,, ta game ta raye tana aza masa cin mutunci tare da zaginsa. Ya zaiyi da rayuwarsa,, Allah ya k'addara masa auren iblishiya kuma"

"annoba,, wadda zata iya kashe mutum tun lokacinsa bai yi ba.. Hak'ik'a shi ma kansa yana k'ara tausayawa rayuwar sa da kuma wanda zai auri duk jinin Inna Harira,, saboda yasan duk wanda ya auri Saude ko Laure,, to tabbas ya auri ajalinsa.. Domin ya san ko basu kashe mijin ba suna iya kashe makusanci mutum kuma mafi soyuwa a rai,, shi kansa ya rasa yadda zaiyi da su ne da tuni ya saki Inna"

"Harira,, ya dawo da matarsa Mariya farin cikin rayuwar sa..."

"Malam Isiyaku ya dawo da tunaninsa da kuma natsuwarsa,,,ya ce ""Na rok'e ki Harira,, dan Allah kiyi"

"hak'uri ba domin ni ba.. Idan wannan magana ce ta b'ata miki rai wallahi na barta har abada,, ki yafe min kinji Galma manyan mata. Masu gari ai keda garin Shiko gaba d'ayansa.. . ."

"Inna Harira ta yi murmushin mugunta,, acikin zuciyar ta tana cewa ""shegen yaji tsoro, d'an kutumar uba"

"sai nayi maganin sa. Zaka gane kai k'aramin shege ne ""..."

"Ta dube ta ce ""Komai ya wuce, dan haka a rage sa mana ido.. Domin komi sa idonka babu abinda zai"

"hana muyi ko agaban uban wa ye ""........"

"""Naji dai, Insha Allah "".Malam Isiyaku ya ce....."

"Inna Harira ta fito daga cikin d'akin,,, tana zagin Malam Isiyaku a cikin zuciyar ta..... ......"

********************

"Ta iske Saude da Laure,, suna firar su suna yin dariya cike da walwala da farin ciki....."

"Ta zauna ta kawo labarin komai,,, ta fad'a musu dangane da abinda ya faru tsakanin ta boka da kuma"

Malam Isiyaku.....

"Laure ta ce ""Tabd'ijam! Akwai aiki fa agare ki Saude,, game da mijinki da kishiyarki.. Sannan ga tsohon"

"munafikin nan Isiyaku,, ko idan banyi aure ba,, ina ruwansa dan ubanshi ""....."

"Saude ta ce ""Babu wani aiki gare ni,, ai karen bana shi ke maganin zomon bana.. Sai na gyara musu zama"

"in kuma tarwatsa farin cikin gidansu da kuma b'ata zamantakewar su. Shi kuma Isiyaku sai mun ci kabarin uwarsa Hajjo dan gundunbulin buro uban sa,, shegen tsohon banza mai fuskar kuti -kuti,, da baki"

"kamar sa,, hanci kamar kare da kuma munafikin gemun nan na shi "". "

"Inna Harira da Laure su ka bushe da mahaukaciyar dariya,, akan irin wannan zagi da Saude tayi ma"

Malam Isiyaku.. Can dai suka bar yin dariya....

"Sannan Inna Harira ta ce ""Amma fa Saude,, kin iya mugun zagi fa.. Ai ko ni sai da yaga na haukace masa"

"da zage-zage hankalinshi ya tashi,,sannan ya bani hak'uri. Ai shegen tsoro ne da shi wallahi ""....."

"Laure ta ce ""Ai kinyi min dai-dai Inna,, mazan yanzu idan kana sa ke musu fuska raina ka zasu yi,, su mai"

"da macce baiwarsu,, sannan wulak'anci da kuma raini ""....."

"Saude ta ce ""haka ne kam gsky,, yaya Laure mazan yanzu basuda tausayi ko imani. Saboda haka idan ma"

"ce ta samu dama kada tayi musu da wasa ""..."

"Inna Harira tace "" 'ya'yana Allah ya yi muku albarka,, ina jin dad'in yadda kuke da fahimta da kuma"

"ganuwa "".Ta fad'a cike da jin d'adi....."

"""Amin amin Innarmu "".Suka fad'a tare cike da jin d'adi sosai....."

Inna Harira haka ta ke ta d'ora su Saude kan turbar k'arya.. Tare da nuna musu muhimmanci yin Asiri

"domin kada miji da kishiya su raina ka da sauran jama'a (Allah ubangiji kashirya da duk wad'anda suka b'ace akan gaskiya. Ka basu ikon gane cewa gaskiya gaskiya ce,, kuma k'arya k'arya ce.. Ka karemu daga"

shairin shed'an da duk miyagun mutane da aljannu).... .

*********************

"Abangarensu su Lado da Abubakar kuwah,, iskancinsu ya k'aru fiye da tunanin mai karatu..."

"Domin kuwa yanzu, har gidan mutum suna zuwa su yi matar mutum ko 'yar sa fyad'e batare da shakku"

ba ko tsoro ba. Musamman idan ba su tsoron Maigidan ko shakku.....

"Haka suka cigaba da yin fyad'e ga matan gari da d'iya,, tare da kisan mutane idan akayi jinga da su....."

"Hak'ik'a zuciyar su Abu,, babu tsoro ko tausayi, imani a cikin ta. Basa tsoron uban kowa duk fad'in garin"

Shiko........

"_*Ku cigaba da bina akowane lokaciiiiii,,,, *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*Ban manta daku ba, Firdausi(Ummu Ilham) da Hafsat Abubakar (Ummu Ahmad). Kusani muna tare da"

juna har abadan da'iman.*_

*PAGE* 116-120

***Washe gari ya kama ranar alhamis k'arfe 11:00am na safe Baba Ibrahim yaje yakira Malam sama'ila

tare da Audu k'anen Inna Indo ...

"Domin suje nema ma Aliyu auren Saude,, bayan sun kammala shiryawa. Suka tafi tasha domin shiga"

motar zuwa garin Shiko......

*******************

"Abangarensu Inna Harira,, suna nan dafe -dafe tare da soye -soye. Domin tarbar bak'insu,, saboda kada"

"suyi saurin gano mugun halinsu,, na rashin mutunci da kirki.. Sai da suka jama mutanen garin Shiko"

"kunne,, akan duk wadda ko wanda ya bada labarin mugun halinsu ga bak'in su. Mutuwa ce hukuncinsa"

saboda haka kowane shegen mutum ya kama bakinsa ko suci ubansa......

"Malam Isiyaku ma,, sai da akaja masa kunne tare da k'annen Inna Harira mai suna Mudi. Su dai suna gefe"

suna kallon ikon Allah....

"'Yan gidan hayarta ma,, sai da Inna Harira ta tursasa su suka bata dubu biyu -biyu,,, kowane daga cikinsu"

"domin tarbon bak'inta. Kuma ba wai bashi ba k'yauta,,,suma kansu 'yan hayar sun gaji da halin Inna Harira da d'iyanta na rashin mutunci da tozarci... To ya suka iya,, haka nan suke daurewa suna zama gidan cike da k'unci da ikon Inna Harira.. Wadda bata ganin darajar d'an Adam,, tare da girmama shi.... ."

*********************

"Abangaren gidansu Maman Amina kuma,,, Babanta da Mamanta duk sun chanza mata kayan d'aki sabbi"

"masu k'yau na yayi.. Kuma Hadiza kullum cikin zuwa gidan Anti Amina ta ke,,, saboda ta d'ebe mata kewa da tunanin banza. Wata rana har kwana ta ke acan gidan yayarta,,samarinta idan suna son ganinta sai dai su isko ta can gidan Aliyu......"

"Babu aikin da bata yi ma Amina,, saboda matuk'ar k'aunar da ta kema Amina da kuma tsananin"

"tausayinta..... Ita ce abincinta,, wanki, wanke -wanke da kuma sharar bedroom da parlorn........"

"Su ma dai Hussaina da Mama Habiba,,suna kan jewayo ta,,, tare bata shawarwari akan yadda zata zauna"

"da kishiya cikin lumana da aminci... Amina ta kan k'ara godema Ubangiji Sarki Allah da ya bata k'awaye, 'yar uwa, uwa uba iyaye na gari. Wanda a kodayaushe ta ke alfaharin kasancewarta d'iyar su,,, bata fushi da k'addaran da Allah ya jarabce ta da shi,, ita dai burinta kuma da fatar ta Allah ubangiji ya sa ta gama da duniya lafiya.... Kuma wannan baisa son mijinta ya rage a zuciyar ta ba,, ko kuma taji ta tsane sa... Ita kanta tana mamakin shi wa ne irin so ne ta ke yima Aliyu? Hak'ik'a tasan tana tsananin son mijinta tare da kishinsa mai tsabta,, ya zata yi shi aure muk'addari ne babu wanda ya san lokacin yinsa balle"

mutuwarsa.....

"Amina ta yi nazari da lura da k'yau,, wato shi ne rayuwarta kuma mak'asudin farin cikin ta,, tana yi masa"

"so mai tsabta bata fatar abinda zai zo ya shiga a tsakanin su, amma yanzu tasan ta makara.. Ya zata yi da kudin k'addarar rayuwarsu........."

*********************

"Haka su Malam Ibrahim,, suka je gidansu Saude domin auren d'ansu......"

"Sun daure sunyi musu tarba,, ta mutunci da nuna karamci... Sun gabatar musu da abinci da drinks kala -"

kala......

"Sun ci abincin,, da ya ke Malam Isiyaku da Mudi suna da kamala da mutunci dai-dai gwargwado. Sannan"

ga kwarjinin da Allah ya ba Malam Isiyaku.......

"Bayan sun kammala komai,, Baba Ibrahim ya gabatar musu buk'atar su ta neman auren Saude,, cikin"

k'ank'anin lokaci.......

"Malam Isiyaku da Mudi,, sun amince da buk'atar su inda suka nuna musu da su kawo kud'in sadakinsu"

"idan sunzo da shi,,, su Malam Sama'ila basu yi k'asa a gwiwa ba... Suka bada dubi d'ari kud'in baiko dubun ishirin,,, sadaki kuma dubu tamanin.. Da yake wannan ita ce al'adar mutanen garin Shiko.. Kana biyan kud'in sadaki fiye da abinda na ambata,,, amma lefe sai idan ka gadama ko kanada ra'ayin yi matarka sutura. Idan ma budurwa ce kake so,, ashekarun da akayi muku baiko da ita duk sallah zaka yi"

mata d'inkuna kamar kala bakwai both k'aramar sallah da babba.....

"Kafin kuyi aure kayi mata,,, kayayyaki masu d'an yawa.. To idan aka tashi aure sadaki da sauran abubuwa"

shi kad'ai ya zama dole ka biya.. Amma fa gaskiya suna da yawan kud'in sadaki.....

"Haka dai su Malam Isiyaku,, suka gama abin cikin mutunci da kamala.. Suka sanya d'aurin auren nan da"

"sati biyu masu zuwa,,, ya kama ranar Assabar ta sama Su Baba Ibrahim suka yi musu sallama cike da"

mutunci da girmamawa.....

"Su ma su Mudi,, sun yaba da kirkin su Malam Ibrahim tare da dattijakansu......."

"Su Malam Sama'ila ma,,, sun yaba k'warai da halayyar su Mudi tare da kirkinsu. Suna addu'ar Allah ya sa"

"haka hali Saudatu ya ke. Ba su san muguwar annoba ce Aliyu ya d'auko,,, mai tarwatsa gida.. Basu san mugun hali gado su Saude suka yi,,, ba wai daga sama suka same shi ba..... .."

"Baba Ibrahim suka koma gida,,, suna yabon

Please Login or Register in order to submit comment