You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ. &&&&&&

*KISHI KO HAUKA*

&&&&&&

_*Story and Written By~ Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

page 1-5

"Wata yarinyace k'arama wadda ba zata wuce shekaru goma sha biyu ba zaune karkashin icce tana kuka,"

"a cikin zuciyarta tana cewa ""sai yaushe ne zanji dad'i a rayuwata ni Aisha, tunda Ummana ta rasu tabar ni wajen inna saude nake fuskantar k'alubalen rayuwa,"" tana share hawayenta tana shassheka tana tunanin rayuwarta ta baya, sai ga Asma'u k'awarta tazo tana cewa ""Aisha Inna Saude tana can tana jiranki"" bata lura da kukan da Aisha take ba, sai da taji shiru sannan ta lura tana hawaye tace"

"""subhanallah aisha me akai miki kike kuka, miye ya sameki k'awata.?"""

"Aisha ta d'ago kanta duk idanunta sunyi ja tace ""Asma'u ina cikin tashin hankali, Inna saude bata barina"

"naji da maraicina, zagi da duka duk ina shansu ga k'azafi da sharri kala-kala take mun, aikin gidan duk ni"

"nakeyi Asiya d'iyarta bata aikin komai, abin haushi da takaici ta shiga tsakanina da babana, "" nan ta sake"

fashewa da wani sabon kuka.

"Asma'u ta nisa sannan tace ""kiyi hak'uri Aisha komai yayi farko yana da karshe, zai zo ya wuce kamar"

"ba'a yi ba, sannan ni a ganina kin saba da kowane irin wahala da Inna Saude zata baki, ki barta da Allah shi zai miki SAKAYYA kinji ki daina kuka k'awata, nan Asma'u ta share mata hawayenta tace ""tashi muje"

"gida kada maraice yayi. """

"Aisha tace ""to k'awata nagode da kulawarki gareni Allah ya barmu tare. "" Asma'u tace ""amin."""

"Acan gidansu Aisha, Inna saude ce zaune tana ta bala'i da masifa tana cewa ""y'ar iskar yarinyar nan"

"tambad'ad'd'iya daga aiken ta ta siyo min gishiri da maggi ta je yawon gantalinta, zata ci ubanta a gidan nan"" tana fad'a tana kunfar baki. Sai ga Abu d'an y'arta ya shigo yana cewa ""Inna me ya sameki kina ta"

"fad'a, tun daga waje ake jiyo muryarki lafiya dai me akai miki.?"""

"Inna tace ""ina fa lafiya 'yar banzar yarinyar nan na aiketa tun safe har yanzu bata dawo ba, sai na ci"

"uwarta Amina, bata san ko uwarta ta buga dani ta barni ba, bata sani ba nice wadda nai sanadiyyar mutuwar uwarta ba, bata san nice na magance ubanta ba baya ganin kowa sai ni."""

"Abu yayi maza ya rufe ma Inna Saude baki yace ""Inna ki rufa mana asiri kada wani ya ji, wannan wa ne"

"irin tonon silili ne, so kike ki tona mana asiri haba Inna. """

"Inna Saude ta nisa sannan tace ""nayi shiru Abu, kasan ban iya b""acin rai ba, amma wani mataki ya"

"kamata mu d'aukar mata. "" Abu yace ""Inna kenan dad'ina dake akwai son zalunci da mugunta, ki barta ta dawo saina ci ubanta. """

"Inna tace ""yauwa d'an albarka haka nake son ji. "" Abu yace ""karki damu Inna, ina Asiya taje ne banji"

"motsinta ba.?"""

"sai Inna tace ""d'iyar albarka ta tafi yin wasa"" yace ""to shikenan."""

"Aisha da Asma'u suna tafiya komawa gida suna hira, inda Asma'u tace mata ""yau zaki shigo gidanmu"

"muyi wasa ne.?"""

"Aisha tace ""rufa min asiri yau nasan saina sha wahala wurin Inna da Abu. """

"Asma'u tace ""waishi Abu ya dawo gidan ku da zama ne halan.?"""

"Aisha tace ""hmm ai Abu yafi d'an masu gida, tare da shi ake cin amanata."" Asma'u tace ""Allah ya"

"sauwak'a."" Aisha tace ""amin."""

Suna isowa kowa ya kama hanyar gidansu.

"Tana shiga gidan ta iske Inna Saude zaune da Asiya tana shagwab'a tana cewa ""Inna kud'i nake so ki bani"

"zan siyi minti da biskit. "" Inna tace ""karki damu shalelenah."" suna tsaka da magana saiga Aisha tayi sallama, babu wadda ta amsa mata, Asiya tsaki taja tana cewa ""y'ar iska ta dawo mai bin maza."" Inna Saude ta harare ta sannan tace y'ar iska shed'aniya gidan ubanwa kika fito, tun d'azu da na aikeki sayen maggi da gishiri shegiya d'iyar munafuka."" Inna ta shak'uro Aisha ta mareta, Aisha tayi kuwa tace ""wayyo Inna dan Allah kiyi hak'uri wallahi ban samu shagon Idi ba saida naje wani shago mai nisa. "" Inna Saude"

"ta sake jibgarta tace ""k'arya kike makira annamimiya wanda tayi gadon mugun hali. """

"Suna cikin haka sai ga Abu ya shek'o da gudu daga waje yana cewa ""Inna k'arama shegiyar banza. """

"Asiya tana gefe tana ta dariyar mugunta tana cewa ""Inna yi ta bugunta yar iska."""

"Abu ya d'auko icce busasshe ga tsawo ga kauri ya buga ma Aisha, sai da tayi tsalle tana kuwwa ya d'ibi"

"fuskarta ya dauketa da mari biyu masu kyau, saida jinta da ganinta na wucin gadi suka d'auke."

"Inna Saude ta rik'eta da kyau tace ""yi kashin shegiya dangi mayu, aini Amina tabar min bala'i da masifa a"

"duniya, yau ni Saude naga makirar yarinya da salon munafurci. """

"Suka samu Aisha baiwar Allah suna ta jibgarta, Abu ya buga Inna ta buga saida sukayi mata bugu-bugu"

suka ga sun yi mata jina-jina suka shige d'aki.

"Nan suka barta kwance da k'yar take nishi, ga kwancin bulala nan ga jikinta rud'u -rud'u, da kyar ta"

rarrafa ta shige d'akin Ummanta wanda a yanzu matsayin nata ne.

"A gidansu Asma'u zaune take da mahaifiyarta suna fira yayin da Inna ta dubeta tace ""yau kuma Asma'u"

"ina kika baro Aisha ne baku zo tare ba.?"""

"Asma'u ta kalli Mamanta ta marairaice kamar zatayi kuka, sannan tace ""Mama tare muka dawo gida,"

"kinsan naje nemanta gidansu har Inna saude tace ta aiketa, toh shine naje nemanta na isketa zaune karkashin icce tana ta kuka, Mama ta bani tausayi wlh. """

"Maman tayi shiru sannan tace ""to auta idan kika sameta tana kuka ki dinga lallashinta ai komi hakuri"

"akeyi, kuma komai yana da lokacinsa saboda a gaskiya Saude bata da imani ko kadan, babu tausayi ko"

"rahama ga lamurranta, kedai ki taya Aisha da addu'a kawai Allah ya kawo mata karshen zaluncin saude da Abu. """

"Asma'u ta share hawayenta tace ""amin Mamana, ina yaya Abbas yaje, tunda na dawo banji motsinsa"

"ba,"" Mama tace ""ya fita babanku ya aikesa tashi ki je d'aki abincinki na nan. """

"Asma'u tace ""to Mama ta mik'e ta shige daki....."

_more comments more typing _

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHI KO HAUKA*

&&&&&&

_*Story and written By~ mugirat musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

page 6-10

"Mama ce zaune tana aikin tankadar garin tuwo, ita kuma Asma'u ta fito daga wanka tana kwalliya."

"Mama ce ke ce mata me takeyi har yanzu bata gama ba, Asma'u ta shagwabe fuska kamar Mama na"

"ganinta tace ""Mama fa na fito daga wanka tun d'azun, kwalliya ce nake yi yanzun nan so nake naje gidansu Aisha ta rakani kasuwa."""

"Mama tayi shiru na tsawon lokaci sannan tace ""to shikenan amma dan Allah Asma'u karku dad'e, saboda"

"kinsan halin babanki da yazo ya tarar da baki nan ni zai d'orawa laifi kinji auta ta. """

"Asma'u tayi murmushi tace ""karki damu Mama baza mu dad'e ba insha Allah. """

"Mama tace ""da yafi, "" ta mik'e ta shige kitchen tana k'ok'arin had'a wuta ta aza abinci."

"Daga waje Abbas ne ya faka mashin d'insa a k'ofar gidansu hannunsa na hagu rik'e da leda, ya kashe"

mashin din bayan ya cire makulli.

"Ya shigo da sallama, Mama ta amsa mashi, Asma'u tana jin muryarsa ta sheko da gudu ta rungume shi"

"tana cewa ""oyoyo oyoyo yaya Abbas, ina kaje ina ta nemanka.?"" cikin shagwabarta, Mama ta harareta sannan tace ""to sarkin tambaye-tambaye, ai kya bari har ya huta ko sannan ki dame shi da tambayoyi."""

"Asma'u ta zumb'ura baki tace ""yaya Abbas kaji abinda Mama ke cewa ko.?"""

"Abbas yayi murmushi yace ""yi hakuri yar k'anwata, ai babu mai shiga tsakanin mu."""

"Mama ta shiga d'aki ta d'auko tabarma da ruwa ga kofi ta shimfida masa, ta aje ruwan gabansa tace"

"""kwaji da iyayinku."""

"Asma'u ta kwashe da dariya sannan tace ""yeh yayana yana sona."" itama ta samu wuri kusa da yayanta ta"

zauna.

"Abbas ya dauki ruwan da Mama ta kawo masa yasha, sannan yace ""Alhmdulilah"""

"mama tace ""to ya kasuwar, inji akwai ciniki sosai, ina ka baro Malam.?"""

"Abbas yace ""mungode Allah ana samun ciniki sosai."" Mama tace ""masha Allah haka ake so dama."""

"yace mata baba yana shago shima gajiya ce yasa ya dawo gida, mama tace ""to yayi kyau, Allah ya"

"taimaka."""

"Yace ""amin"" ya juya ya dubi Asma'u yace ""k'anwata ya naga kinyi shiru lfy dai, kuma wannan kwalliyar fa"

"sai ina.?"""

"Asma'u tace ""gidansu Aisha zanje na ganta ta rakani kasuwa."" Abbas yace ""to mi zaki siyo a kasuwa"

"auta?"" tace ""kayan kwalliya."""

"Mama tace ""yawon da suka saba kawai suke son zuwa."" Abbas yayi murmushi ya mika ma Mama ledar"

"da ya shigo da ita, kayan cinye-cinye da wasu takalma guda biyu masu kyau, ta amsa tace ""masha Allah yayi masa albarka,"" Asma'u tace ""amin Mama."" Mama ta mik'e tace zata shiga kitchen ta duba girkinta, sukace to bayan shigewar Mama kitchen Abbas ya zaro kudi dubu d'aya da dari biyu yace gashi ta sayi"

"kayan kwalliya, tace ""to nagode yayana Allah ya saka da alkhairi."" yace ""amin."""

"Yace mata shi zai rakata gidansu Aisha, in ya so ya tarar musu mashin shi ya dawo gida tace to."

"Suka mik'e tare Asma'u ta lek'a kitchen tace ""Mama mun wuce,"" mama tace ""a dawo lafiya."" tace"

"""amin."""

"Suka fito k'ofar gida zasu wuce Asma'u tace ""yaya bada mashin zamu ba.?"" yace mata ""a'a da k'afa zamu,"

"nan da gidansu Aisha sai munje da mashin."" Suka kama hanyar zuwa gidansu a"

Aisha suna tafiya suna fira.

"Acan gidansu Aisha kuma bayan Inna Saude da Abu sun bata mugun kashi, tana kwance d'aki dak'yar"

"take nishi tana hawaye mai ban tausayi tana cewa a cikin zuciyarta ""wayyo ni Aisha naga takaina, sai yaushe ne zanji dad'i a rayuwata? sai yaushe ne zan kasance cikin farin ciki? na fahimci Inna Saude rayuwata take nema ba komai ba, gwamma mutuwata da wannan da na tsinci rayuwata, Allah sarki duniya Ummata Allah ya jikan ki da rahama, da kina nan nasan da rayuwata bata kasance haka ba."" _(ni kaina na tausayawa rayuwar Aisha na koma gefe ina kuka hakik'a na tabbata rashin uwa ga rayuwar d'anta babban rashi ne. Allah ubangiji ya jikan kakanninmu, uwayenmu, yayyinmu, k'annanmu,"

magabatanmu da dukkan musulmai baki daya). Ameen_

A yayin da Inna Saude ke zaune da Abu ga Asiya suna cin tsire ga ruwan lemu suna korawa da shi suna

fira da dariyarsu.

"In da Inna ke cewa ""naman akwai dad'i sosai,"" Abu yace ""dad'ina dake Inna akwai kwad'ayi da son abin"

"duniya."" Inna ta hararesa tace ""masa to zageni ni Abu, saboda kai nasan baka da albarka, baka gadi mutunci ba."""

"Abu yace ""tsaya Inna dad'ina da ke baki da hak'uri, komai naki sai kin had'a da zagi to ni wasa ne nake"

"miki."""

"Inna tace ""yanzu naji magana,"" Asiya dai tana jin su ba tace komai ba, can tace ""Inna dai a rink'a kai"

"zuciya nesa, koda yake babu mai shiga tsakanin ku."""

"Inna tayi mata dakuwa tace ""ungo gidanku yar iskar yarinya, uban wa zaki yi ma wa'azi ko nasiha, tun"

"kafin ki fito duniya nasan da wannan,"" Abu yace ""haba kiyi hak'uri da keda yar lelentaki."" Asiya ta cire hannunta ta shige d'aki tana zumbura baki da gunaguni, Abu ya kalli Inna yace ""kin gani abinda nake gaya maki, gashi nan tayi fushi da ke."" Inna taja tsaki tace masa ""taje tayi ta fushi ni ina ruwana, saboda"

"taga ina son ta zata kawo min rainin hankali."""

"Abu yace mata ""Allah ya baki lafiya."""

"Inna tace ""yoh nih ai gara ni da kai, kai banda shaye -shaye da yi ma yaran mutane fyade da kisa, mai ka"

"iya."""

"Sai da gaban Abu ya buga da k'arfi ,sannan yace ""Inna kenan laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani,"

"amma ni ban tab'a yi ma wani asiri wanda yayi sanadiyyar mutuwa ba, ban tab'a zuwa wurin boka dan amagance wani ba,"" Inna najin Abu ya fara tona mata asiri cikinta ya murda tana k'uri -k'uri da ido ta chafke maganar sannan tace ""haba Abu d'ana matsalata da kai bakasan ba'a ba, yi hakuri d'ana na kaina."

""""

"Yayi murmushi saboda yasan lagon Inna fiye da kowa, yace mata ""to yanzu naji magana, ina yarinyar nan"

"Asha.?"""

"Inna tace ""tana rai ga hannun Allah, wanki na nan na ajema shegiyar,"" Abu ya kyalkyale da dariyar"

"mugunta yace ""yo Inna babu imani babu tausayi, Inna tace fad'i ka k'ara, fad'a babu sani babu sabo."""

Suna dariya suna tsara yadda zasu kara musgunawa rayuwar Aisha.

"Acan kasuwa baban Aisha ne zaune cikin rumfa da wasu masu zama kusa garesa suna firar duniya, a"

"yayin da shi yake saida kayan miya irinsu tarugu, albasa, tumatur, tattasai da sauransu, bayan ya zauna ya kira wani yaro dan makwabcinsa mai suna sule ya had'a masa kayan su tumatur da sauransu ya ciro dari biyar ya bashi yace masa ga kayan miya ya kai masa gida, sannan ya biya shagon idi ya sayi shinkafa"

"kwano guda ya kaima Saude,"

"Sule ya amsa masa yace to, bayan wucewar Sule abokin baban Aisha mai suna malam Adamu ya matso"

"kusa gare shi yace masa ""wai abokina mike faruwa kwanakin nan ina yawan ganinka cikin damuwa kuma shiru -shiru,?"" baban Aisha yace masa ""ni kaina bansan abinda ke damuna ba, kadai tayani da addu'a,"" malam Adamu ya dubi abokinsa cikin tausayawa ya ce insha Allah Aliyu zan kasance mai tayaka da"

"addu'ar Allah yayaye maka abinda ke damunka. """

"baban Aisha yace ""Amin nagode kwarai abokina."""

"Abbas da Asma'u bayan sun isa kofar gidansu Aisha sukayi sallama babu wanda ya amsa, alhalin suna"

"jiyo muryar Inna Saude da Abu suna fira, bayan kamar minti ashirin sunyi jira har sun gaji sai ga Inna"

"Saude ta fito tana cewa ""uban waye ke damun su da kuwa,"" tana kamowa taja ta tsaya tana hararar su"

"tace ""ke Asma'u bana ce miki kada in kara ganin ki kofar gidan nan ba? makirar yarinya mai siffar mayu,"" Abbas ya dubeta yace ""Inna ba tashin hankali ya kawo mu ba, wurin Aisha muka zo. "" Inna tayi kuwah tana fad'in ""kwarai yau naga ta kaina ni Saude d'iyar galma dama kaine kwarton Aisha, wanda kuke"

"iskanci tare.?"""

"Abu najin kuwar Inna ya sheko da gudu waje yana cewa ""lafiya dai Inna mike faruwa.?"""

"Inna ta nisa tana fyace majina ""ina fa lafiya dama abinda nake gaya muku kenan, wannan y'ar iska"

"yarinyar nan ce _(ta nuna Asma'u)_ tazo tare da kwarton su ita da Aisha,"" Abu ya wage baki yana cewa"

"""buro uban nan, yau zanci ubanshi kuwa, yau ga tsinanne mai fuskar biri yayi cikin Abbas zai kai mashi bugu."""

"Abbas ya murd'e masa hannu sai da Abu yace ""wayyoh Inna,"" sannan ya dauke shi da mari biyu masu"

kyau wanda saida ji da ganin abu ya dauke na wucin gadi.

"Inna Saude ta na ganin abinda Abbas yayi ma Abu ta koma gida ta rarumo icce zata buga ma Abbas,"

"Abbas na hankalce da ita tana zuwa zata buga masa yasa kafarsa ya kwashe ta ta fad'i kasa kwance, sai da bakinta ya fashe da jini sosai tana jin zafi itama tayi kuwah tana cewa ""azo ataimake ta ga Abbas nan yazo har k'ofar gidanta yana bugunta,"" Asma'u na ganin mutanen unguwa sun fara taruwa, kuma"

hankalin kowa baya wurinta ta lallab'a ta shiga cikin gidan.

"Anan waje kuwa mutane suka taru suna kallon yadda Abbas ke bugun Abubakar kamar ya samu jaki, ita"

"Saude tunda ya kwashe ta take kwance ga kasa baki na yoyon jini tana hawayen azaba, a yayin da mutane suka zama yan kallo babu mai yunkurin taimakawa su Saude, saboda Saude mace ce wadda bata da mutunci ko kad'an, bata ragawa kowa a cikin unguwarsu, babu mai sonta saboda mugun halinta kowa bata ganin girman mutum ko gemunka ya naja a k'asa ko tafiya kakeyi furfura na zuba, makira ce kuma"

shedaniya ce ta kwarai.

"Can na hango malam Adamu yana ta sauri ya iso nan, bayan isowarsa ya dubi mutane yace ""mi ke"

"faruwa duk yawan su ace sun kasa raba fad'a,"" wani daga cikinsu wanda yafi kowa tsaurin ido ya ce masa malam matar nan da kake gani bata da mutunci, bata san darajar dan adam komi tsufar mutum tana iya"

"ci masa mutunci ko ba haka bane jama'a.?"""

"Mutane suka ce ""maganarka haka take lado."""

"malam Adamu yayi shiru sannan ya dube su duba ta fahimta yace ""ai ba haka ake yiba, komai rashin"

"mutuncinta kuna martaba igiyar auren da ke kanta kaga Abbas sake Abu kada ka k'ara yin haka kaji, sannan wai miye dalilin faruwar wannan abin."""

"Abbas ya kawo bayanin komi yayi ya fad'ama malam Adamu. Malam yace ""kayi hak'uri, ku kuma kowa ya"

"kama gabansa,"" mutane suka fara watsewa Saude ta tashi da kyar ita da Abu tana zage -zage wai malam Adamu bakin munafik'i ne, ya za'a yi Abbas ya ba Abu kashi itama ya bangaje ta baiyi mai komai ba, saboda idan mijinta ya zo zata gaya masa kuma kowane shegen cikin unguwarmu ko munafiki tana iyawa da shi. "" Abu na cewa ""Inna mu shiga barni da shi zan rama mana wlh, saina halakashi"" suka"

d'unguma zuwa cikin gida saboda su malam Adamu basu yi niyar shigaba saida suka ji kuwar Asma'u.

"Da sauri suka shiga suka iske Asma'u zaune kusa ga Aisha wacce da kyar take numfashi, jikinta duk yayi"

"mugun zafi, malam Adam yace ""subhanalillah mi ya same ta?"""

"Asma'u wadda ke kuka ga majina yabe-yabe tace ""nima ban sani ba yaya ataimaka akaita asibiti bana"

"son nara sa Aisha,"" Abbas idanunsa sunyi ja saboda tsananin bacin rai da tausayin Aisha yace mata ""to asma'u zata warke insha Allah*"

"malam Adamu yace ""to yanzu abinda za'a yi d'auko ta mu je asibiti,"" Abbas ya d'auko hijabin Aisha yace"

"Asma'u tasa mata, bayan tasa mata ya sunkuceta su malam suka take masa bayan."

"Bayan wucewarsu Abbas ne, Inna ce zaune tare da Abu tana gasa masa jikinsa da ruwan zafi saboda"

"kashi da yasha, tasha alwashin sai taga bayan Aisha, shi kuma atbbas sai ta k'ulla mai sharrin da har ya mutu bazai tab'a mantawa da ita ba......"

_*More Comments more typing*_

_*Muje Zuwa*_&&&&&&

*KISHI KO HAUKA*

&&&&&&

_*Story and written by mugira musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_*Wannan page d'in nakine Sister Nerja'art kiyi yadda kikagadama da shi hakika ke masoyiyatace ta

gaskiya.*_

page 11-15

Bayan wucewarsu abbas ne inna saude na gasa ma abu jikinsa da ruwan zafi saboda duk yaji ciwo a

"jikinsa, inna saude ke ta fada tasha alwashin sai ta ga bayan aisha sannan ta ce abbas zai gane fada da ita ba alkhairi ba ne sai yayi nadamar abinda yayi mata,"

abu ya dubeta yace ni dai dan allah kin isheni da mita baki barni da ciwon jikinaba kinzo kinata sababi

alhalin ganki ya jibge ni ba abinda kin

"ka yi kuma wlh karki kuskura ki jawo mana wata masifar ki bari har na warke sannan musan abinyi,"

asiya na zaune tana kallon diramar innarta da abu. Inna taja tsaki sannan ta ce dad'ina da kai mugun

raggo ne ga masifar tsoron tsiya.

abu yace mata to inna nasan halinki ina iya sake tadda mana wata masifar alhalin ni ban warke ba

"nakara shan wani bugu saboda yanzu da nasha kashin nan ni kadai nasan yadda nake ji ga jikina, akan mugun halinki da rashin imaninki,"

inna ta zaburo masa kamar zata bugeshi tace karka yi min bura'uba shegen yaro wanda ba'a san

"ubansaba, mahaukaci kwarton banza."

abu ya kalli inna ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yace yoonih saude ai duk kanwar ja ce kema ai

"shegiya ce ba'a ubanki ba,"

"ta zaburo zata kai masa chafka, asiya tayi maza ta rike kafar uwar tana cewa don allah inna kiyi hakuri"

kinga bayada lafiya.

Inna ta ce sakeni inci ubansa shege annoba taulalin wahala

abu ya yi murmushi yace har akwai wata annoba duk fadin unguwar nan in ba keba to tunda bakida

mutunci ko kadan to wallahi saina tona miki asirin da duk kika yi a shekarun baya kinsan ko alade ya fiki farin jini a unguwar nan

ai inna sai da ta razana kirjinta ya buga da karfi sannan ta zauna kusa gareshi ta ce don allah abu kayi

hakuri ka rufamin asiri nayi maka alkawarin ba ni sake yi maka wani abin kwatankwacin wannan

abu yayi murmushi cikin zuciyarsa zaki gane ke karamar shedaniya ce wlh saina nuna miki na fiki rashin

mutunci

asiya ce tadafasa tace masa yaya abu inna na maka magana kayi shiru mi kake tunani

abu ya nisa sannan ya dubi inna saude ya ce komai ya wuce

inna tayi murmushi can sai ga sule ya shigo yana sallama hannunsa rike da ledodi biyu

"babu wanda ya amsa masa ya shigo ciki ya gaida inna saude da abu, abu ya amsa inna saude ta harare sa"

ta ce mi kazo yi tsohon munafiki da ido kamar mujiya

"sule ya kalli inna yace babansu asiya yace in kawo muku kayan cefane ,"

inna saude ta warce ledodin guda biyu tace inji malam ko ya baka ka kawo mana to ina chanji dan iskan

"yaro,"

"sule ya zumbura sannan yace ni fa inna saude aiko ni kawai yayi bana iya cin mutunci, inna tace uwarka"

"ce yar cin mutunci, mahaukaciya"

"abu dai babu abinda ya ce mata saboda duk jikinsa ciwo yake masa, yayinda asiya taga inna saude ta aza"

dan mutane masifa ta ce sule tafiyarka gida kaji

"ya ce to ya juya ya wucewarsa, asiya ta dubi inna saude sannan ta ce dan Allah kiyi hakuri yaron nan fa"

bai miki komai ba

"ina jinki makirar yarinya cewar inna saude, asiya ta nisa ta ce Allah ya baki hakuri."

"Bayan fitar su abbas daga gidansu aisha direct asibiti suka wuce, suna zuwa aka amshe ta. aka basu gado"

"dakin su room 3, tare da nurses and doctor Sadik ke kula da ita."

"bayan aune -aunen jini da bincike doctor sadik yace yana son kebewa da su, abbas suka mike zuwa office"

din doctor

ayayinda suka bar asma'u wurin aisha kwance ana mata karin ruwa.

"suna shiga suka samu wuri suka zauna, doctor sadik ya dube su ya ce waye mahaifin yarinya ko yayanta,"

abbas ya kalli malam adamu shi ma ya kalli abbas.

"malam adamu yayi karfin halin cewa agaskiya ni aminin mahaifinta ne tare muka tashi tun muna yara,"

wannan kuma (ya nuna abbas dan makwabcinsu ne da aisha da kanwarsa asma'u kawayen juna ne)

doctor sadik ya nisa sannan ya ce ok babu damuwa amma agaskiya nayi mamakin da a ce yarinya

karama kamar wannan ta kamu da ciwon ulcer kuma hawan jini ya kusa kamata sannan akwai damuwa da zazzabi da rashin kwanciyar hankali.

Malam adamu da abbas suka hada baki wurin cewa ina lillahi wa inna ilaihirraji'un cikin jimami da

"tausayawa,"

doctor sadik yace saboda haka tana bukatar kulawa da kwanciyar hnkali kuma a samu babbar mace

"wadda zata dinga kulawa da ita saboda zata yi kamar kwana biyu zuwa ukku a asibiti, malam adamu ya ce ok ba matsala insha allah. Yaja abbas suka fito gefe yace masa yanzu abinda za'a yi kaje gida ka fadama mahaifinka da mahaifiyarka ni kuma zan tafi can rumfa na fada ma malam aliyu(baban aisha"

"kenan),"

abbas ya ja wani gwauron numfashi sannan yace haka za'a yi baba daga nan sai na zo tare da mama

"malam ya ce to ni zan wuce na fadama aliyu, abbas ya ce masa allah ya kiyaye."

"Abbas ya nufi dakin da aka kwantar da aisha ya iske asma'u har ta ci kuka ta gaji, har ta fara gyangyadi ya"

"kalleta cikin tausayawa saboda yasan irin mugun shakuwar da suka yi da aisha haka suke kaman yan tagwaye ko'ina tare kake ganinsu hatta kaya wasu iri daya suke sa wah, ya shafa fuskarta yana goge"

"mata hawayenta ya ce kanwata kiyi hakuri zata warke insha Allah bana son ganinku cikin damuwa, Allah"

"zai canza ma aisha sauyin rayuwa,"

asma'u ta bude idanunta tana murmushi ta ce yaya har ka dawo tun dazu ina jiranka kaje gida ka

"gayama baba da mama kada suga dadewarmu,"

abbas ya ce mata karki damu yanzu nan zanje na fada musu ke ki tsaya har in dawo kinji kanwata

autarmu .

asma'u ta ce to yaya sai ka dawo kazo mana da abinci ya ce mata to ya sa kai yayi ficewarsa.

"Acan gidansu asma'u kuwa mama tayi jiran su abbas har ta gaji basu dawo ba, har abbansu ya dawo"

daga shago ya ke tambayar ta ina su abbas

ta ce masa ai yaje rakiyar asma'u ta je gidan su aisha tayi mata rakiya kasuwa su siyo kayan kwalliya.

abba ya dube ta sannan ya ce kaji matsalar mata ke da nace miki bana son asma'u na yawan zuwa gidan

nan saboda kinsan halin saude kaf unguwar nan babu wanda baisan halin mutuncinta ba da bala'i gashi yanzu kin bari sunje Allah dai ya san mi zai faru

mama ta ce kayi hakuri abbansu wallahi aisha ce ta ke bani tausayi sosai bazan iya silar rabuwar su da

asma'u ba saboda sunyi wani irin shakuwa wanda rabasu yakeda wuya kuma naga aisha abin atausayawa marainiyar allah

abba yayi shiru yana nazari can yace haka ne habiba zancenki abin dubawa saboda kin fini gaskiya da

"hangen nesa, mama tayi murmushi na jin dadin zancensa ta ce nagode

Please Login or Register in order to submit comment