You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zaburowa (Alamar taji tsoro kenan). Tana cewa"" Inalillahi wa ina ilaihirraji'un!!!"

"mi ke faruwa, mi ye ya same ni?""."

"Inna Saude ta ja mugun tsoki ta ce ""ubanki ne shegiya bak'ar munafika, kinsan aikinki bayan kinyi sallah,"

"zaki zo ki kwanta, uban waye zai yi miki wanke- wanke da wanki da share -share"".?"

"Ta ce ""inna dan girman Allah kiyi hak'uri, wallahi barci ne ya kwashe ni ban sani ba,bayan nayi sallah ""."

"""Yoonih ni ina ruwana da wani sallarki ko barcinki, 'yar iskar banza bak'ar karuwa.Wadda tayi gadon"

"mugun hali ga Amine tsohuwar 'yar bariki"".Cewar Inna Saude ta na huci kamar tsohuwar karya."

"Aisha ta dubi Inna Saude, tana hawaye cikin b'acin rai da jimamin abinda Saude ta ke mata."

"Inna Saude ta ce mata ""lafiya kike kallo nah?, ko akwai abinda zakiyi saboda na zagi munafukar uwarki,"

to bari kiji ni da kike gani na nan.

"Ko uwar ki ta buga da ni ta bar ni daram, dangin mayu kawai ""."

"""Kiyi hak'uri Inna ki daina zagar min mahaifiya, saboda kin fi kowa sanin ba ta duniya. Duk abinda zakiyi"

"min kiyi, banda zagar min uwa wacce banida kamarta a fad'in duniyar nan ""."

"Inna Saude ta k'ara hasala, ta daga hannunta fa shara ma Aisha mari mai kyau na k'warai."

"Ta ce ""to bari kiji na fad'a maki, kinyi k'adan ki hana min zagin shed'aniyar uwarki. Ko ubanki da ya haife"

ki bai isa ya ja da ni Saude ba. Balle keh karan kad'in miya.

"Aisha taja majina tana shassheka, ta ce ""to Inna Allah ya baki hak'uri ya kuma huci zuciyarki""."

"""Da hak'uri ya mutu sadakar nawa ki ka bani, annamimiya, bak'ar annoba gadon mugun abu. Dalla ta so"

"kada ki b'ata min lokaci""."

"Inna Saude ta sa hannunta, ta fisgo Aisha da karfin tsiya zuwa wurin wanki. Ta jawo ta."

"Ta ce ""ta fara shara da wanke -wanke, sannan ta yi wankin kayansu, ga kuma girki na can yana jiran ta""."

"Aisha ta dubi tulin wankin da aka tara mata, ga uban tulin kwanoni da yawa. Tana share hawayenta, tana"

k'ara tausayawa rayuwar tah.

"Ta fara kauda duk wasu abubuwan gida, sannan ta fara Sharah ."

"Inna Saude ta na ganin Aisha ta fara shara, ta yi shigewar ta d'aki."

"Bayan Inna ta shige d'aki, ta iske Asiya kwance tana barcinta cikin kwanciyar hankali."

"Ta tashe ta daga barcin. ""ke tashi dan ubanki bana son sakarci ""cewar Inna Saude."

"Asiya ta tashi ,tana xumb'ura baki ta ce ""haba Inna wannan wa ne irin rashin imani ne?, mutum yana"

"barcinsa .Zaki zo ki tada shi, to yanzu mi ye zan yi miki kuma? ""."

"""Yi hak'uri shalele nah, 'ya ta kainah farin cikin rayuwata, dama kayan ki ne zance ki je ki kaima shegiyar"

can Aisha ta wanke miki.

"Kin san bana son ki wahala, sannan ki dawo kije d'akin Abu ki karasa ya siyo mana kayan shayi ""."

"Asiya ta ce ""Ai ke Inna ahankali ake tayar da mutum, ba da hauka ba"". Tana harhad'a kayan wankinta."

"Inna Saude ta ce ""ko ni yi hak'uri d'iyar kwarai, ba na sakewa kinji ""."

"Asiya ta ce ""to da kin kyau ta min""."

"Ta kwaso uban kayanta, ta kawo zata aje, alokacin har Aisha ta gama shara wanke -wanke ne ta ke yi,"

"kuma ta d'ora tukunyar dahuwar shinkafa _(Kalubale gare mu mata, kada ki ce sai d'iyar ki ta girma. Sannan zaki fara koya mata girki, yarinya tun ta 8year's zaki dinga koya mata aza ruwan zafi da sauran ayyukan gida masu sauk'i irinsu wanke -wanke da share -share da dai sauransu. Abin haushi da takaici zakiga yarinya ta girma har ta isa aure amma ko dahuwar shinkafa bata iya ba. Ya kamata iyaye mata mu gane, icce tun yana d'anye ake lank'wasa shi da zarar ya riga ya bushe shi kenan. Allah ya sa mu dace"

"baki d'ayanmu ,mu kula iyaye mata)_. Asiya ta kalli Aisha, irin wulak'antaccen kallo na rainin wayo ta ce"

"""keh! Banza, jaka ga wanki na nan. Sauran ka da ki wanke ya wanku, dan ubanki 'yar iska karuwa kawai."

"Aisha ta nisa sannan ta dubi Asiya ta ce ""Asiya kenan, ke ba sa'ar yi na ba ce, darajar mahaifinmu kike ci"

"shiyasa duk abinda ki ke mini na ke k'yale ki, amma babu komai akwai lokacin da zaizo wanda ko kud'i za'a ba ki. Ba zaki iya cimin mutunci ba."

"Asiya tace ""k'aryarki tasha k'arya,dangin mayu ba abinda zaki iya. Sannan kuma babu wannan lokacin"

""".Taja wani uban tsaki ""Mtssssss ""."

"""Adaibi duniya a sannu, duniyar nan ta ishi kowa riga da wando. Wanda bai zo ba ma jiransa ta ke"

""".Cewar Aisha."

"""Ba za'a bi a sannu ba d'in, na d'auka ko akwai abinda zaki iya min. Bak'ar munafuka kawai da ke""."

"Ta ja k'afafunta, ta wuce tana ta bala'i da zage -zage."

"A'isha ko kara tanka mata bata yi ba, ta yi tagumi sannan ta ce ""Allah ya shirya Inna Saude da Asiya, Abu,"

"idan masu shiryu wa ne. Yasa su ga ne gaskiya d'aya ce""."

"Asiya kuwa tana zuwa bakin k'ofar d'akin Abu, ta afka cikin d'aki ba ko sallama barai gaisuwa."

Ta iske shi kwance daga shi sai singlet da guntun wando.

"Ta kalleshi ta ce ""wai Inna Saude tana kiransa, ya siyo kayan shayi ""tana yamutsa fuskarta."

"Abu ya tashi zaune, saman katifarsa. Ya dube ta sannan ya ce ""to yaji tazo ta zauna, yana son magana da"

ita.

"""Haba Abu daga aike na d'akinka, sai na zauna so ka ke Inna ta yi min fad'a ""cewar Asiya."

"Abu ya zare mata idanunsa masu ban tsoro (saboda ko kallon idanun Abu kayi sau d'aya, kasan ba"

"k'aramin d'an duniya ba ne) .Yace mata ""zata zauna ko sai ya fad'ama Inna Saude abinda ya ga tana yi, ita da Rabi'u sannan da k'awarta Larai ita da Ila, sun b'oye alungu suna yi."

"Aranazane Asiya ta dubi Abu, ta ce masa ""dan Allah yaya Abu ka rufamin asiri, kada Inna taji ta kashe ni"

""",tana hawaye."

"Dama abinda Abu kawai ya ke so, taji tsoronsa domin ta bashi had'in kai akan ya cimma burinsa. Wanda"

shi kad'ai yasan abinda ya ke k'ullawa.

"Abu ya jawo hannunta, ya aza ta saman cinyoyinsa, yana lallashinta yana shafar jikinta."

"Ya ce mata ""karta damu ba zai fad'ama Inna ba, muddin yasa ta tayi masa wani abu tayi. Kuma wai yana"

"sonta, sannan ta daina kula Rabi'u ""."

"Ta dubesa sannan ta ce ""mi ya ke so tayi masa ne? ""."

"Yayi kissing d'inta ,sannan ya ce ""wai kullum ta dinga zuwa d'akin sa tana masa tausa, sannan idan tana"

son wani abin d'adi ta fad'a masa ko dai wani abu wanda baifi k'arfinsa ba.

"Ita kuma Asiya da yake Shed'aniyar kan ta ce ,ta k'ara langwab'ewa tana shagwab'a ta ce ""babu matsala"

"Abu, duk abinda ka ke so zan yi maka shi, karka damu ai ""."

"Abu ya ce mata ""To yaji amma tasan yanada kishi sosai, kada ya k'ara ganin ta da Rabi'u. Yana shafar"

"k'irjinta k'anana da su ka fara fitowa, suna nishin d'adi."

"Ta k'ara rungume shi, tana kai masa sumba, tana nishi ta ce ""karka damu sweety ina son ka. Bana son"

b'acin ranka.

"Ya k'ara rungume ta, yana jin dad'in maganarta har cikin zuciyarsa. Yasa blanket ya rufe su, suka kwanta"

suna kissing junansu.

Wannan kenan.

Aisha kuwa har ta gama wanke- wankenta da dahuwar shinkafa.

"Ta d'ebo ruwa ta ciccika randuna, ta aza ruwan zafi ta shige wanka."

"Acan gidansu Asma'u zaune da mahaifiyarta suna fira, har da Abbas."

"Mama Habiba ta dube su ta ce ""ya kamata Auta ku k'ara komawa gidansu Aisha, ku dibo tah ya ta"

"k'arasa da jikin na ta""."

"""Hmm Mama wankan da ki ka ga nayi yanzu, ai can zan je yanzu nan. Amma ni Inna Saude na ke tsoro,"

"kin san halin ta na rashin mutunci ""."

"Mama ta ce ""ke ina ruwanki da rashin mutuncinta, ai indai duniya ce zata koya mata hnkali ""."

"Abbas ya dube ta ya ce ""Ai tare zamu je da ke, saboda nima na k'ara yi mata ya jikin. Sannan ni agani nah"

"ba ruwanki da Saude ko Asiya, saboda ba wurin su zaki je ba ""."

"Mama Habiba ta ce"" fad'a mata dai gaskiya, ba wurinta zaki je ba ina ruwanki da ita ""."

"Mama ta mik'e,ta shige d'aki ta had'o sabulun wanki da na wanka da kayan k'walliya ."

"Ta ce ""gashi ta kaima Aisha kuma tana gaishe tah ""."

"Abbas ya dubi Maman tasu, ya ce ""Mama wannan duk Isha za'a kaima, lallai kina ji da wannan d'iyar ta ki."

"To mi za'a ba ni ?""."

"Mama tayi murmushi ta ce ""to za'a baka biskit da minti idan kana so ""."

"Asma'u ta k'yalk'yale da dariya ta ce ""to kai Yayana kaji abinda Mama ta ce, kamar k'aramin"

"yaro ta gani a nan ""."

"Abbas ya harare ta ya ce ""kin fa raina ni fa, ba biskit za'a ba ni ba, dan tama tsitsi za'a ban""."

"Mama tayi dariya, ta ce ""kaifa Abbas wasa ta ke maka, ina ruwan sarkin zuciya ""."

"Asma'u ta ce ""yayanah yi hak'uri wasa nake maka ai, kasan ai tsakanin mu bata galan ""."

"Abbas ya murmusa ya ce ""k'anwatah kina tunanin har akwai abinda zai sa yayanki, yayi fushi da ke"

"ne?Babu shi soyayyar mu daga jini ta ke ""."

"(dukkan su su ka k'yalk'yale da dariyar farin ciki, Allah ya bamu k'annen k'warai da yayan nen k'warai."

Ameen)

"Su ka mik'e tare,suka ce ma ""Mama za su wuce can gidan su Aisha ""."

"Mama ta ce ""Allah ya kaisu lafiya, su gaida mata Aisha ""."

"Suka ce ""Amin Mamanmu, Allah ya bar mana ke""."

"Ta ce ""Amin "",cikin tsananin farin cikin had'in kan yaranta."

"Suka kama hanya, suna tafiya suna fira.Da gani babu tambaya 'yan gida d'aya ne, saboda tsananin kamar"

da su ke da juna na jini guda.

"Aisha ce zaune tana k'walliya, bayan ta gama aikin da duk Inna Saude ta saka tayi. Duk jikinta ciwo ya ke"

mata saboda gajiyar da ta yi.

"Kuma abin takaici da haushi ko abincin k'warai bata sa ka mata, sai dai ta sa ka mata d'an kad'an. Ta"

"had'a da k'anzon tunkunya ta ci, tasha ruwa sannan ta ji dama-dama."

"Acan cikin d'akin Abu, bayan ya gama lagudar Asiya ko'ina a jikinta duk ya lasheta. Sunyi wankah tare"

acan toilet d'in sai da sunka d'ade nishin su d'ai ka ke ji.

"Bayan sun fito, suna shiryawa su na fira. Ayayinda ya ke cema mata ""kar ta bari Inna Saude ta fahimci"

"alak'arsu ""."

"Asiya ta yi murmushi ta ce ""Ina wasa ne, da zan bari Inna ta fahimci mai muke ciki ""."

"Ya ce mata ""kin kyauta baby nah, dan Allah ki cika alk'awari, kullum kiyi wasa da hnkalin Inna ki zo kinji""."

"Ta sumba ce shi, sannan ta ce ""babu matsala a wurina. Gobe ka xo min da tsire da lemun k'walba ""."

"Ya ce mata ""ba damuwa duk abinda ki ke so, zaki samu karki damu ""."

"Ya d'auko #1000 ya bata ya ce mata ""gashi ta sayi duk abinda ta ke so ""."

"Ta amsa mashi ta ce ""Godiya nake ""."

"Ta fito daga d'akin su, ta iske Inna Saude zaune tana jiranta."

"Inna Saude ta dubi Asiya ta ce ""ke tun d'azu nake jiranki, baki dawo ba sai da na kira Almajiri. Ya siyo min"

"kayan shayin, mi ya tsaida ke can d'akin Abu kuma? ""."

"Asiya ta k'ara tamk'e fuskarta, saboda kada Inna Saude ta kawo mata wargi."

"Ta ce ""to da kika aike ni, ai na fad'a masa, sai na wuce gidansu larai ko ""."

"Inna Saude da ta ga kamar Asiya ta hasala, ta ce ""ba wani abu yasa tayi mata wannan tambayar ba, illah"

"saboda kada ta yarda da Abu domin bana k'warai ba ne. Amma tayi hak'uri bata yi zaton tayi gidansu larai ba ne """

"Asiya ta ce ""to taji babu komai ai ""."

"""Ga abincinta nan ta ci wai har da nama ta siyo musu ""cewar Inna Saude."

"Ta ce ""to ""suna cin abinci suna fira, hankalinsu kwance."

Suna magana su ka tsinkayo muryar Asma'u ta na sallama. Babu wanda ya amsa mata daga cikin su.

"Inna Saude ta so tazo ta ci ma Asma'u mutunci, Asiya ta hana ta."

"Aisha na jin muryar Asma'u ta shek'o da gudu, su ka rungume juna. Suna farin ciki da murna da ganin"

junansu.

"Aisha bata ma lura Abbas ba, sai daga baya."

"Ta gaida shi ya amsa mata, yana kallonta yana murmushi."

"Ta ja su d'aki, ta shimfid'a musu tabarma su ka zauna. Ta d'ebo ruwa a randa masu sanyi ta aje musu."

"Abbas ne ya fara magana, ya ce ""mata ya jikin na ta? ""."

"Aisha ta ce masa cike da kunya ""Yaya Abbas naji sauk'i wallahi ,ya su Mama,ya gida? ""."

"""Duk qalau su ke ""cewar Asma'u."

Asma'u ta mik'a mata ledar da Mama ta basuwa akawo mata.

"Ta ce ""mata ya jikin ta? Gashi Mama ta basuwa akawo mata ""."

"""Naji sauk'i ""cewar Aisha."

"""Allah ya kara kawo sauk'i ""inji Asma'u."

"Abbas ya ce ""Amin ya fiddo wani box k'aramin ya ba Aisha tare da kud'i ya ce ""shi zai tsaya waje har su"

"gama, saboda sunfi sakewa ""."

"Bayan fitarsa, Asma'u ta ce ""Aisha naga kin k'ara ramewa wai har yanzu, ba ki daina saka damuwar Inna"

"Saude a zuciyarki ba"""

"""Ba haka ba ne Asma'u, duk yau a tsaye na yini ina aiki kamar jaka. Ba kiga wanki saman igiya ba, duk ni"

"nayi nasa "".cewar Aisha."

"Asma'u ta ce ""karki damu da wannan, komai yayi farko zaiyi k'arshe, kuma kowane mutum da irin na shi"

"jarabawar rayuwa. To ke naki kenan, hak'uri da juriya shi ne jigon zaman rayuwa, kuma ako'ina mutum"

"ya tsinci kansa dole sai yayi da mutanen duniya. Zaki ga wani baka yi masa komai ba, amma ba ya sonka. Wani kuma komai baka had'a da shi ba sai ya so ka. Allah ya baki ikon cinye jarabawar ki Aisha."

"Aisha ta ce ""Ameen ""nagode sosai da shawararki Allah ya bar zumunci""."

"Ta ce mata ""Ameen""cewar Asma'u."

"Suna fira cikin farin ciki da murna, Asma'u ce ta b'ude box d'in da Abbas ya ba Aisha.Sark'a ce masifar"

kyau da zoben ta da 'yan kunnenta.

"""Wow! Masha Allah ,suna da kyau sosai yi yadda suke shining sosai, yaya Abbas ya iya zab'e"" cewar"

Asma'u .

"Aisha ta yi murmushi ta ce ""wannan iyayin naki yayi yawa wallahi ""."

"Asma'u ta ce ""ba zaki ga ne ba""....."

"_Ku biyo ni, domin jin yadda abin zai kasancewa._"

_*Muje Zuwa*_&&&&&&

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_~Fans kuyi hak'uri, na canza sunan novel daga *KISHI KO HAUKA* zuwa *KISHIN JAHILCI* Dalilin da yasa"

shi ne sunan littafin wata marubuciya ne.~_

```Hak'ik'a kin nuna k'warewarki da bajintarki wurin fadarkar da mu Ummie Adnan (marubuciyar Hauwa

"jidda, kina raina Ummie.``` "

*PAGE* 36-40

Haka Inna Harira ta cigaba da musgunawa rayuwar gidan Malam Isiyaku.

"Babu mai jin dad'inta, daga ita sai d'iyar ta Laure ke jin dad'insu."

"Ita kuma lnna Mariya, bayan ya saketa ta koma gidansu. Da yake iyayenta sun rasu, daga ita sai yayanta"

mai suna Sani da matarSA ladidi ke zaune cikin gidan.

"Da ta dawo gidan , ta fara sana'ar sayar da kayan miya cikin gida. Su kuwa su Abdullahi da Atikah suna"

zuwa makarantar Allo da boko.

"Ita da Ladidi zaman su akwai fahimtar juna, babu tashin hnkali balantana fad'a."

"Zama ne mai cike da son zumunci, da k'aunar juna. Malam Sani shi ke ciyar da itada yaranta."

"Ladidi macece wadda babu ruwanta, da kuma son zumunci. Akwai ta da tausayi da hangen nesa, karamci"

da mutunci sune halinta.

Shiyasa Inna Mariya bata fuskanci wani k'alubale ba.

*****************

Adalilin wannan mummunar d'abi'ar da Inna Harira keyi ne ta kawo wannan k'warto ta kawo wannan

"k'warto, har ta gamu da wani k'warton mai suna IDI."

Wanda ta fi sonsa duk a cikin k'wartayenta. Haka suka cigaba da mu'amala da juna kamar mata da miji.

"Malam Isiyaku da Inna Hajjo na cikin gidan, suna ganin komai babu bakin magana. Abin akwai tausayi da"

"ban takaici _(yana daga cikin mugun asiri, zamanin nan na mu. Da yawa mutane ba su yarda da k'addara"

"ba. Allah ya tsare mu baki dayanmu)_. Haka su ke rayuwa idan yayi cinikin robobi ta amshe riba, ta bar ma shi uwar kud'in."

"Ta mayar da su photon k'arfi da yaji, da shi da inna Hajjo."

"A haka rayuwar ta cigaba da tafiya, gidan Malam Isiyaku cike da k'unci da ikon Inna Harira na bak'in"

zaluncin ta. Da rashin tsoron gamuwarta da Allah mad'aukakin sarki.

BAYAN SHEKARA BIYU

"Alokacin ne Inna ta sa ke b'ullo da wani nau'in zaluncinta, a cikin gidan."

"Ya za mana babu abinda ta ke yi,sai tara mazan banza da bacci. Alokacin ne ta ce ""ta gaji da cida k'artin"

"banza, ta rabama Malam Isiyaku da Inna Hajjo tsohuwa kashi biyu""."

Inna Hajjo tayi mata share -share da dahuwar abinci. Shi kuma Malam Isiyaku yayi wanki da wanke -

wanke (Kaji rashin imani da zalunci).

"A haka Hajjo zata yi mata dahuwar abinci da shara. Idan baiyi d'adi ba, ko kuma shara ba tayi kyau ba Ta"

samu bulalar icce tana jigbar tsohuwar mutane.

"Wata rana har da marinta take yi, ko ta d'unguje tah."

"Shi kuma Malam Isiyaku har da zagin ta ke, idan baiyi mai kyau ba. Ko ta hana sa hak'k'insa na aure."

Malam Isiyaku har hawayensa da kukan bak'in cikin wannan na Inna Harira.

"(hak'ik'a na tausayawa rayuwar gidan Malam Isiyaku, akan irin halin da suka shiga na bak'in cikin da"

"k'angin rayuwa. Allah ya k'addara masa auren muguwar mace, azzaluma kuma mushirikah). Ya zaiyi da rayuwarsa, hak'ik'a duk Inna Hajjo ce sanadi kuma kunsan *DUK TSUNTSUN DA YA JA RUWA* shi ruwa kan doka......"

"Rayuwar gidan ta cigaba da tafiya, cike da rashin imani da dangana."

"Ana nan kwatan!! Sai ga ciki ya bayyana, ga jikin Inna Harira galma. Mutanen garin Shiko suna ta"

"gulmace -gulma ce da zund'enta amma ko shifa da b'oye, Saboda kowa na gudun ai mishi mugun asiri ya lalace ga banza."

"Da yake aikin asiri ne, babu abinda Malam Isiyaku ya nuna saima farin cikin sa."

"Da taga ta samu ciki, ta sa shi ya siyo rago da tinkiya domin suna."

"Da yake tasan ba cikinsa ba ne, tasa aka kira mata Idi wai ya zo tana kiransa."

"Bayan ya xo ne, tayi masa shimfid'a ta kawo abinci mai rai da lafiya ta aje masa."

"Bayan ya gama kintsa cikinsa da abinci, ta kawo bayani ta gaya masa cewa ""tana d'auke da cikinsa har na"

"tsawon wata biyar ""."

Idi ya zabura! da k'arfi yana hiri -hiri da idanunsa.

"Sannan ya nuna Inna Harira da yatsa, ya ce ""k'aryar ta sha k'arya tsohuwar karuwa, ya za'a yi ba ni kad'ai"

"ke kwana da ke ba. Ki rasa wanda zaki k'aba ma cikin shege sai ni ""."

"""hmm lallai ka ci moriyar ganga. dole ka nuna mugun halin ku na maza, to wallahi bari kaji ni da kyau"

"Idi. Ko ka k'i ko ka so wannan cikin na ka ne ""Cewar Inna Harira ta na huci cike da b'acin rai."

"""Idan kina son kanki da arzik'i ,ki daina danganta ni da shegen cikin ki ko ki je abaki sayen zubar da ciki."

"Ya zube sannan zamu shirya"".Cewar Idi cikin hargowa."

"""Kai! Kai! Kai! Idiiiiiii,,,, idan kayi sammakon rashin mutunci. To atafe na kwana, wallahi na shafe ka da"

"rashin mutunci. Kuma ciki ne bazan zubar ba, dole dan kutumar ubanka, ka kar6esa"".Cewar Inna Harira cike da bala'i da masifa."

"Idi ya ce ""ke dakata bana son jahilci da hauka, yanzu ya kike son ayi? ""."

"Inna Harira ta ce ""Ai da ka bari mun zuba, agani waye zai sake ma d'an uwansa "".Tana harararsa"

"Idi yayi murmushi, (a cikin zuciyar sa, akwai abinda ya ke sonyi). Sannan ya ce ""bashi na ja miki, bana son"

"tashin hnkali. Ki bar cikin ki ai babu damuwa ko""."

"""Ai dama ba zubarwa zan yi ba ehee, yanzu abinda za'a yi ka dinga aiko kud'in rainon cikin duk wata"

"dubu biyar.. Sannan nasa Isiyaku ya sayi rago da tinkiya, bamuda matsala da wannan. Abinda zaka tanada shi ne :fulawa, sugar, man gyad'a da sauran kayan taron suna, kana jina ko? ""."

"Idi ya ce mata ""Ina jinki galma, sai mi kuma ko kin gama lissafin ne? """

"Ta ce ""Eh na gama lissafin ""."

"Idi yasa hannu cikin aljihunsa, ya d'auko dubu biyar yaba Harira. Ya ce mata ""Ga na wannan watan""."

"Inna Harira ta sa hannu ta karb'a, ba ko godiya barai kallon k'warai."

"Ta amshe tana zaginsa, acikin zuciyarsa."

"Ya mik'e ya ce mata ""zai wuce sai wani watan ko? """

"Inna Harira ta ce ""ya dinga zuwa, yana dibin lafiyar d'ansa ko 'yarsa to ""."

"Idi ya ce ""ba matsala karta damu, zai dinga zuwa akai -akai ""."

"Ta ce ""to""."

"Ya kama hanya, yayi wucewarsa gidansu."

"Yana zuwa gida, yayi wanka ya sake cin abincinsa. Ya jawo bakkorsa yana sa kod'add'un kayansa ciki da"

sauri-saurin alamun barin gari.

"Yana gamawa, ya kama hanya sai tasha, ya tari mashin zuwa Rijiyar mai kabi. Yayi tafiyarsa (kunji halin"

"mayaudaran maza, masu cin moriyar ganga. Allah ya k'ara shiryamu)."

*BAYAN WATA GUDA*

"Inna Harira ta ji shiru, Idi bai zai zo ba. Ta aika kiransa akace mata baya nan."

"Taje da kanta nemansa, bata ganema komai ba, ta zauna gidan da Idi ya ke zaune ta aza musu cin"

mutunci da tozarci.

"Tun 10:am xuwa 3:00pm,tana masifa da bala'i."

"Da ya ke ana tsoronta kamar ciwon ajali, ba wanda ya kula ta. Da akaga abin bana k'arewa ba ne, kowa"

ya barta gidan. Tayi ta gaji sannan ta k'ara gaba.......

*BAYAN WATA HU'DU*

Inna Harira ta haifi d'iyar ta mai kamada Idi sak.

"Ta ci suna Saudatu (saude) ,cikin mutanen gari babu wanda ya zo sai 'yan uwanta. Ko su ana gama bikin"

kowa ya kama gabansa. Suna zaginta da gulmata tare da tsine ma halinta.

"A haka Laure da Saude suka tashi da rashin tarbiya da kuma rashin kunya, tsakanin su akwai tazarar"

shekaru har shidda.

Laure ta ba Saude shekara shidda.

Haka suke cike da rashin rashin kamun kai da rashin kunya akodayaushe.

"Ahaka tafiya, tayi tafiya har Laure ta kai goma sha takwas, ita kuma tanada shekara sha biyu."

"Alokacin ne Laure tayi suna a karuwanci a garin Shiko, ita tayi uwarta ma Inna Harira ta yi. Saboda su"

tara abin duniya da dogon buri na duniyar nan yana cikin zuciyar wad'annan bayin Allah.

"Itama Saude ta na d'an tab'awa, amma ba wai kamar su ba."

"Bayin Allah nan wato Malam Isiyaku da Inna Hajjo, suna nan yadda suke bata canza zane ba. Sai dai sun"

k'ara tsufa saboda wahala da matsin rayuwa. Kuma har yanzu tana saka su aiki idan basu yi dai -dai ba.

Tayi musu mugun hukunci mai tsananin wahala.

"Mutanen garin Shiko,sun k'ara tsorata da halin Inna Harira (galma) da d'iyanta. Saboda d'iyan basu baro"

"komai ba na mugun halin ta,saima abinda ya k'aru musamman Saude....."

"A haka dai ake zama da guguwar annoba, wato su Inna Harira da d'iyanta."

"Mai garin ya zama photo Shima, yana masifar tsoron Inna Harira da d'iyanta."

"Saboda idan ka shiga gonarsu, to ka shiga ukku ko ba'a kai ka wurin boka ba ."

"Suna da wasu 'yan daba majiya 'karfi,'karti su hud'u. Zasu su d'auko ka, su kawo ka gidan su a tub'e"

mutum daga sai singlet da guntun wando.

"Abaka mugun kashi, su kawo da dakakken tankwa da gishiri, ashafa maka inda aka ji maka ciwoo"

kayi ta kuwah. Babu mai kawo maka agaji.........

"Haka suke gudanar da rayuwarsu, ci keda zalunci da cin amana..............."

*Muje zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_Wannan shafin sadaukarwa ne, ga KISHIN JAHILCI FANS. Hak'ik'a comments d'inku yana sanya ni farin"

ciki._

*PAGE* 41-45

"Wasu Mutanen garin Shiko,ganin irin zaluncin da cin amanar da Inna Harira ke yi da d'iyanta."

"Yasa duk wata hanyar da suka san, zasu gamu da ita da d'iyanta suke canza hanya."

Suna nan suna cin karensu babu babbaka. Kwatsam!

Itama Laure sai ga cikin ya bayyana gare ta.

"Alokacin da cikin ya bayyana, Inna Harira bata ji dad'i ba duk da tasan ita ce silar tab'arb'arewar tarbiyar"

yaranta.

"Ta bi duk wata hanya, na bin bokaye da 'yan bori tana amso magani. Saboda cikin ya zube amma ina har"

yanzu shiru babu labarin zubewar cikin.

"Duk inda suka je, ita da Laure sai dai. Bokayen sun amshe musu kud'i suna cikasu da k'aryayyakin banza"

"da na yofi, suna basu magani amma cikin har yanzu shiru. Kamar an shuka dussa."

"Malam Isiyaku da Inna Hajjo tsohuwa, suna nan yadda suke takure, lalace abin akwai tausayi da ban"

mamaki.

"Inna Hajjo ta kira d'anta, suka keb'e a cikin d'akin ta."

"Inna Hajjo ta kalli d'anta Malam Isiyaku,cike da tsananin tausayi da yin NADAMA akan abinda ta"

"aikatawa Mariya da d'iyanta. Acan baya,"

"Sannan tace ""d'ana Isiyaku ina ro'konka da ka yafe min abinda nayi maka abaya. Hak'ik'a NA TAFKA"

"BABBAN KUSKURE a rayuwata, na zama nice silar rabuwarka da matar ka Mariya ta k'warai. Mutuniyar kirki, mace mai mutunci da karamci, ladabi da biyayya. Ga ta hak'uri da kawaici"", (Inna Hajjo ta ja majina da hawaye saman fuskarta yab'e -yab'e). Ta cigaba da cewa ""Dan Allah ka yafe min, idan ka samu Mariya da yaranta ka maida

Please Login or Register in order to submit comment