You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yauk'i..."

"Tare da girgiza komai na jikinta yana rawa, da kuma bank'are k'irjinta tare da turo shi. Babu kunya ko"

tsoron Allah atattare da ita.......

"Haka dai tayi ta tafiya, har ta kusa ga wani lungu inda mutane basu cika wucewa ba. Sannan daga nan"

tana tsinkayo su Ilu da Aliyunta...

"Ta d'an jima tana kallon Aliyu, cike da so da shauk'in begensa...."

"Sannan ta ga giftawar wani yaro, ta kira sa ta bashi kud'i naira hamshim.."

"Ta nuna masa su Aliyu ta ce"" can take son ya kaita wurin wancan mai farar shadda kuma wankan"

"tarwad'a ,kar ya yarda ya aje ta setin Adamu. Ai ya gane ko ""."

"Yaron yace mata ""Eh mana, ya gane ""."

"Ta d'auko kwalbar maganinta, ta shafa a fuskarta sannan ta ce ""Yana kaita wurin kawai yayi wucewarsa ""."

"Yaro yace mata ""to Anti ""..."

"Ta duk'e kanta k'asa, yaro yaja ta kamar makaho da d'an jagora. Sai wurin su Aliyu...."

"Yana kawo ta dai -dai wurin Aliyu, ya juya ya yi tafiyarsa....."

"Adamu ya dubeta, ya ce ""Malama Saudatu lafiya dai, ya garin? ""."

"Saude ta marairaice fuskarta, kamar da gaske. Amma kanta a duk'e ga k'asa..."

"Ta ce ""lafiya k'alau, kaina ne kawai yake min ciwo ""."

"""Ayyah Allah ya sauwak'a "".Cewar Adamu da Aliyu.."

"Aliyu ya kalleta, yayi murmushinsa. Ya ce ""ya kamata ki d'ago ki kalle ni. Domin maganar ta nada"

"muhimmanci, ko da yake ba komai. Saudatu ina neman yafiyar ki akan abinda nayi miki a wancan sati, nasan nayi kuskure amma dan Allah ki taimaka min ki gafarce ni Ba domin halina ba ""."

"Saude kuwa dad'i ne da murna, suka hana mata saurin yin magana. Daddad'ar muryarsa tana mata yawo"

a kunne. Shauk'in k'aunar sa tana d'awainiya da ita......

"Can ta d'ago fuskarta, suka kalli juna cikin ido da ido.."

"Alokacin da Aliyu ya kalli Saude, zuciyar sa ta buga da k'arfi ""rasssss "".Ya ji wani abu yana masa yawo duk"

"a ilahirin jikinsa, yaji wani bangare na zuciyar sa ta kamu da tsananin son Saude, yana fisgar sa. Ya kuma"

sani Saude ba k'yakkyawa ba ce. Bak'a ce ba za'a kira ta mummuna ba. Sannan ba za'a kira ta da k'yakk'yawa ba..

"Can Saude ta katse shirun, ta ce ""karka damu Aliyu, ai ni tuni na riga na yafe maka. Kuma kowane"

"mutum bai wuce yin kuskure ba ""."

"Adamu ya ce ""mun gode sosai da karamcinki ""."

"""karku damu, ai yi ma kaine "".Saude ta fad'a cike da makirci da kissa."

"Aliyu yace mata ""Nagode da kika fahimceni. Allah ya bar zumunci ""."

"Saude ta dube shi, cike da so ta ce ""Ai an zama d'aya, kuma komai ya wuce har abada (Ina mamakin"

"Saude yadda ta ke magana kamar ta k'warai, tare da nuna natsuwa da hankali. Kaji makira ta iya pretending fa. Allah ya yi mana katanga da duk mai halin irin na su Saude da Innarta)........"

"Adamu ya ce ""to mun gode kuwa, to mu zamu wuce sai gani na ukku ""."

"Saude ta ce ""Babu matsala, Allah ubangiji ya kiyaye hanya ""."

"""Amin ""Cewar Aliyu."

Sai da suka yi ma Ilu mai saida hoda sallama sannan suka yi wucewar su tasha domin su shiga mota zuwa

gida........

"Bayan sun wuce ne, Saude ta ce ma Ilu mai saida hoda zata je ciki ta siyo abu..."

"Ya ce mata ""to ""...."

"Tayi wucewarta, tayo siyayyar ta mai yawa. Bayan ta dawo ne."

"Ta d'auki kud'i naira dubu ta ba Ilu mai saida hoda, ya k'i amsa......"

"Ta dube shi da kyau, ta ce ""Ilu mi kake nufi ne wai na baka kud'i ka k'i amsa ko raina ne halan ?""."

"""Ai dole na k'i karb'a, ni ba kud'i zaki bani ba yanzu. D'akina zamu je na hole da ke na awa biyu ko kuma"

"na tona miki asiri "".Cewar Ilu mai saida hoda."

"Saude ta ce ""Haba Ilu nah, ai abin bai kai haka ba. Na yadda mu je d'akin na ka to ""."

"Ilu ya ce ""to "".Ya had'a kayayyakinsa ya kulle a shago......."

"Yayi gaba Saude ta na biye da shi, har d'akinsa....."

"Suka yi ta aikata iskancinsu, ci ke da nishad'i da jin d'adin su....."

"Sun dad'e suna abu d'aya, sannan su ka bari...."

"Saude ta kama hanyar zuwa gidansu,,, cike da farin ciki da nishad'i saboda yau taji dad'in mu'amalar ta"

"da Ilu........ (Allah ya tsare mu, ya tsare mana imaninmu daga Fad'awa tarkon shed'an )......."

"*Ku cigaba da bi na, sannu a hankali ......* ."

*Muje zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*Allah ubangiji ina rok'on ka, yabaki lafiya sister Najer'art da ke da dukkan al'ummar musulmai masu"

"fama da lalura ta rashin lafiya. Kisani kin kasance jigon rayuwata kuma mai k'auna ta, ina miki soyayyar"

da babu k'arya a cikin ta.*_

*PAGE* 96-100

"Bayan Saude ta iso gidansu, babu sallama kawai ta fad'a cikin gidan su."

"Tana shiga ta wuce toilet tayi wanka, bayan ta gama tayi kwalliya tare da fesa turare....."

"Tafito daga d'akin su,,, ta nufi na Innar su, Ta shiga ciki ta iske Inna da Laure suna cin naman kaza da"

lacasera...

"Saude ta samu ta zauna kusa ga Laure. Sannan tasa hannunta a cikin naman, tana ci,,,,,, can ta ce ""Amma"

"fa yaya Laure,,, da kun k'ware ni idan har ban zo da wuri ba, Wannan irin dad'i kam gaskiya naman akwai dad'i sosai wallahi "".Saude ta fad'a tana cin naman kaza tare da shan lacasera......"

"Laure ta harareta da wasa, ta ce ""miye abin k'waruwa kuma ciki, kinzo kinata mana santi da shegen"

"bakinki na son dad'i. To ma ai idan mun cinye ba zaki rasa nama a kasuwa ba ""."

"""Hmm Yaya Laure, ai son dad'i gaskiya ne. Wannan naman daban ya"

"ke da sauran,,, Saboda gaskiya Shamsu mai kaji ya iya gashin kaza da iya sa mata kayan had'i domin tayi"

"sosai fa "".Cewar Saude...."

"Sai alokacin Inna Harira tayi magana, tace ""kin fa ishe mu da shegen santin nan na ki,,, daga babu wani"

"labari sai surutun ki na tsiya. Ke ya batun maganin da kika shafa acan kasuwa,,, anya akwai alamun nasara kuwah? ""....."

"Laure ta ce ""Ai shi ne kam gaskiya,,,, daga zuwanki babu bayanin komi. To ya abin ya kasance da ku kayi"

"ido hud'u da Aliyu sarkin girman kai? ""."

"""Agaskiya Inna akwai alamun nasara,,,, saboda da muka yi ido hud'u da shi ya dad'e yana kallona... Har"

"da murmushinsa na gani kuma ya bani hak'uri.... "".Cewar Saude....."

"Saude ta basu labarin komai,,,, daga farko har k'arshe........."

"Inna Harira da Laure,,,, suka bushe da mahaukaciyar dariya....."

"Can Laure ta daina dariyar,,, sannan ta ce ""Lallai magani ya fara aiki,,,, duk girman kansa ya fara shigowa"

"hannun ki alamu ma ya nuna ya kamu da cutar sonkiiii ""...."

"Inna Harira tace ""bar shege shi ba yace ba girman kai ya ke tak'ama da shi ba. Ko Malam Isiyaku da ya ke"

"tak'ama da malamanci,,, sai da na yi shige da fi ce na kama d'an iskan ga hannuna. Balantana shi wawan banza ""."

"Saude tab'ata fuska, tace ""Dan Allah ya isa,,, ku daina ce masa mai girman kai. A hakan na ke son abina ""."

"Inna Harira tayi mata dak'uwa, ta ce ""to shegiya sarkin son miji,,, idan kika je gidansa ki bari so ya rinjaye"

"ki,,, karki tsaye kin dai san ba ke kad'ai ba ce matarsa ""....."

"""Ke kuma Inna, ai tasan da wannan. So muke idan ya fara zuwa zance sai mu k'ara kai shi wurin boka,,,,"

matarsa ta rasa ga ne kansa ta yadda babu wadda zai dinga so da k'auna idan ba Saude ba. Ya zama

"baya ji,, baya ganin kowa sai ita "".Laure ta fad'a...."

"Inna Harira ta ce ""Ai to nasan da wannan,,, tunatarwa ce na ke mata. Kinsan halin Saude wata rana bata"

"saka lissafi cikin lamarin ta ""....."

"""A'a Inna ina sa lissafi mana,, ai kinsan duk son da na ke mishi. Na fi son kaina,,,,bazan yarda ba ya kawo"

"min wargi,,, sai na juya shi fiye da tunanin ku. Zan shayar da ku mamaki wallahi,,,, nice fa Saude d'iyar galma Harira ai bamu gadi abin k'warai ba ""..Saude ta fad'a cike da cika baki...."

"Laure da Inna Harira, suka sake dariyar mugunta....."

"Sannan Laure ta ce ""Da ko kin k'yauta ma kanki,,,,, saboda gaskiya za kiji dad'in aure kuwah "".."

"Inna Harira ta ce ""haka ne,, zata ji dad'i idan ta rik'e bokaye da 'yan bori... Babu abinda zata nema ta rasa"

"""."

"""Nama rik'e ai Inna,,, koyi da ke wajibi ne agare mu. Saboda kada maza su raina mu ko su walak'anta mu"

"""..Saude ta fad'a."

"Laure tace ""Wannan wajibi ne muyi koyi da mahaifiyar mu ""."

"""Haka nake son ji 'ya'ya ,k'yawon d'iya su gadi uwarsu "".Cewar Inna Harira...."

"A haka dai Inna Harira, take ma d'iyanta hud'ubar tsiya. Tare da musu nuni da su rik'e bokaye da 'yan"

"bori hannu bibbiyu. (Allah ubangiji ya bamu iyayen k'warai,,, masu tsoron gamuwar su da Allah da koyi"

ga ma'aikin Allah Annabi Muhammad (S. A. W).......

**********************

"Shi kuma Malam Isiyaku, idan ka gansa sai ka tausaya masa ..Yana wajen sana'arsa ko yana gida baka"

ganin ya fito daga cikin d'akinsa idan ba wata lalura ta taso masa ba....

"Kodayaushe yana cikin d'akinsa,,, yana ibada tare kai kukansa ga Allah sarki...."

"Da yaga damuwa tayi masa yawa,,, yakan tafi gidansu Mariya. Domin ayi masa sallama da Abdullah da"

"Atika d'iyansa,,, ya gansu yaji dad'i sannan ya siya musu abubuwa tare da yi musu ihsani..."

"Wata rana suna gaisawa da Sani yayan Mariya,, wani lokacin ko da yake zuwa baya nan..."

Sau da yawa ya kan ba 'ya'yansa sak'o zuwa ga Innarsu Mariya. Ko na gaisuwa ko na wani abu mai

muhimmanci....

"Ya zaiyi da rayuwarsa,,, Allah ya jarabce shi da auren makirar macce mara imani,,, wadda babu tsoron"

Allah ko kad'an a cikin lamarin ta. Ita dai buk'atar ta ta samu duniya kawai shi ne agaban ta....

"Hak'ik'a ya san yayi rashin uwa ta gari,, Inna Hajjo tare da mata ta gari abar alfahari da duk wanda ya"

mallake ta...

"Wani bangare na zuciyar sa,,, soyayyar Mariya yana taso masa. Awani lokacin tsanar ta ya ke taso masa.."

"Ya zaiyi da k'addaran rayuwarsa sai dai hak'uri,,, saboda komi yana lokacin sa....."

******************

"Aliyu da abokinsa Adamu, lafiya k'alau suka koma gidajensu. Tare da tsarabobin da suka yi ma matansu,,,,"

cike da murna da farin ciki......

*BAYAN KWANA BIYU*

"Amina duk ta rasa gane kan Aliyunta,,, sau da yawa tana ganinsa yana yawan tunani da damuwa,,, ga"

"yawan shiru -shiru da rashin walwala.. Ta kan same shi cikin damuwa zata tambaye shi,,,"" mi ya ke"

"damunsa wai ko mi ke faruwa ne,, baka da lafiya ne? ""Da ire -iren wannan tambayoyi take masa. Amma"

ya kan nuna mata babu komai ko gajiya ce...

"Ta kan nuna masa ta yarda da maganarshi,,, tana mamakin sauyawarsa alokaci guda kuma yawan tunani"

da yake yi....

"Wata rana ya kan d'an daure,,, yayi mata fira domin kada ya sanya ta a cikin damuwa ko shakku a kansa..."

"Ba komai ne ke damunsa ba,,, illa tsananin soyayyar Saude tare da tarin k'aunar ta cikin zuciyarsa.. Ba"

"laifinsa bane, shi kansa ya san idan ya ce zaiyi aure bai k'yauta ma Amina ba.."

"Saboda bata rage shi da komi ba,, a rayuwarsa laifin zuciyar sa yake bani. Saboda mi zata so Saude?"

"Wanda ya san a komi na mata Aminarsa ta zarce Saude. Ba'a ma gama su ta ko'ina,,, ya zai yi da abinda zuciyar sa ke k'ok'arin tursasashi da kuma nuna masa abinda ya ke muradi dai -dai ne..."

"Da yaga damuwa na batun yi masa illa,, yace ma matarsa zai fita..."

"Ta ce masa ""Adawo lafiya ""."

"Yace mata ""Allah ya sa "". ya sa kai yayi wucewarsa, waje wurin Adamu..."

"Yana zuwa ya iske Adamu zaune saman kujera,, yana shan iskah waje,, Aliyu shi ma yaja kujera kusa ga"

re shi ya zauna.. Suka yi musabaha da juna...

"Bayan sun gaisa ne,, Aliyu ya dubi abokinsa cike da tsananin damuwa da zullumi..."

"Ya ce masa ""Adamu ina cikin tsananin damuwa, da kuma zullumin abinda na keji a cikin zuciya tah."

"Nasan zaka fahimce ni tare da bani k'yakk'yawar mafita. Ka fahimce ni da idon basira Adamu ba laifi na bane "".Ya fad'a cike da zullumin Maganar da zata fito daga bakinsa..."

"Adamu ya yi shiru,, can kuma ya ce ""ka kwantar da hankalinka Aliyu,,, ka sani bakada wani amini da ya"

"fini mun kasance mun san halin junanmu tun muna yara.. Insha Allah zan baka shawarar da ta da ce,, karka ji komai fad'amin mi ke faruwa? ai abokin kuka shi ake fad'a ma mutuwa ""."

"Aliyu yayi huci mai zafi,, sannan ya ce ""ya zanyi da rayuwa tah Adamu,, anya kuwa nayi ma Amina adalci?"

"ni nasan ban k'yauta mata ""."

"""Haba Aliyu ka fito fili,, kayi min bayani ta yadda zan gane.. Ban fahimceka ba,, mi ya sami Aminar wai?"

""".Adamu ya ce."

"""Adamu kayi hak'uri da abinda kunnenka zai jiyo...Na kamu da tsananin k'aunar Saude yarinyar da ke"

"garin Shiko "".Aliyu ya ce cike da damuwa..."

"Adamu ya zabura da k'arfi!! Ya ce ""wace Saude ce ka ke nufi Aliyu? Kar dai ace yarinyar da ka tsane ta,,,"

"yanzu ita ce ka koma so "".Ya fad'a cike da tashin hankali.."

"""Eh ita nake nufi,, sonta na ke da aure wallahi "".Aliyu ya ce kai tsaye.."

"Adamu ya k'ara shiga cikin tashin hankali,,, tare da share zufar da ke zubo masa...."

"Yace ""Inalillahi wa ina ilaihirraji'un!!! Ta faru ta k'are,, an yi ma mai dame d'aya sata.. Dama ga irin"

"abinda ake wa gudu kenan,,mi ka gani a jikin wannan kucakar bak'auya wanda Amina bata da shi,,, wannan wane irin rayuwa ce "".Ya fad'a da zafin rai."

"Aliyu ya ce ""Babu abinda Saude zata gwada ma Amina,, amma ina son ka sani ba laifi na bane,,, so ne"

"sanadi. Abinda kawai na ke so ka taimaka ka gaya ma baba na cewa na samu matar aure "".ya fad'a cike da marairaicewa.."

"Adamu ya buga uban tsaki cike da jin haushin maganar Aliyu""mtsss"". sannan yace ""maganar banza ni ne"

"mara kunya ko,, ka je da kanka ka fad'a mana.. Ni ba za'a ci amana da ni ba,, Allah ya sa ni babu ruwana ""."

"Aliyu ya k'ara matsowa kusa Adamu,, ruwan hawaye ya cika masa ido,,,ya aza hannunsa bisa ga cinyoyin"

Adamu..

"Ya ce ""Ya kai Adamu ka riga ka fi kowa sanin halina,, wallahi na rasa yadda zanyi da zuciya ta ne.. Ni ma"

"ba'a son raina ba ne,, na rok'e ka da ka taimaka min wlh ji na ke idan ban aure ta ba. Zan iya mutuwa abokina "".Ya fad'a cike da sanyin jiki.."

"Adamu ya kalli Aliyu cike da tsananin tausayinsa,, domin ya fahimci baya cikin hayyacin sa,, ba yin kansa"

"ba ne. Ya lura akwai wata a k'asa,,, ya fahimci Saude mugun asiri tayi ma abokinsa. Ya zai yi dole ya taimaka masa ya aure ta,,, ya san Amina mai hak'uri da yadda k'addara zata yi tawakalli da jarabawar"

rayuwarsu...

"Adamu ya nisa, sannan ya ce ""karka damu abokina,, zanyi magana dasu baba zan fahimtar da su.. Kai"

"kuma ka fara fad'ama Amina maganar domin karta fara ji a gari,, ka lallashe ta da maganganu masu dad'i ""."

"""Insha Allahu Adamu zanyi iyakar bakin k'ok'arina,,, nasan Amina ba tada matsala. Ba zata yi wuyar"

"shawo kai ba "".Aliyu ya fad'a cike da k'warin gwiwa."

"Adamu ya ce ""Allah ya sa ""."

"""Amin "".Cewar Aliyu."

"A haka dai suka cigaba da firarsu, duk da firar suna yinta ne cike da fargaba da zullumi."

"Shi Adamu ya na fargabar yadda zai tsaya ya fuskanci iyayen Aliyu,, ta yadda zai b'ullo musu domin su"

amince da auren Aliyu..

"Shi kuma Aliyu,, yana fargabar yadda Amina zata d'auki maganar aurensa. Ta kuma fahimce shi batare"

da wani damuwa ba..

"Haka suka cigaba da firarsu,, ta yadda zasu b'ullo ma lamarin......"

*Yanzu labarin ya fara. *

_*MUJE ZUWA*_&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_*Wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkan masoyana a duk inda kuke a fad'in duniya. Ku sani ina

"matuk'ar son ku a rayuwata, ban da kamar ku.*_ &&&&&&"

*PAGE* 101-105

"Aliyu yakoma gidansa, cikeda zullumi da fargabar yadda zai sanar da Amina,,, k'udurinsa na niyar k'ara"

"aure. Ba wai yana tsoran ta ba ne,,, kunya ya keji ya dube ta ido cikin ido ya ce zai yi mata kishiya.."

"Duk da ya san Amina macce ce,,, mai matuk'ar k'aunar abinda ya ke so da kuma tsananin hak'uri da"

kawaici da juriya akan duk abinda bai sab'ama mahallici sarki Allah....

"Yana dawowa,,, tayi masa sannu da zuwa,,, tare da kawo masa abinci da ruwa a cikin kofi.."

"Ya zauna ya ci abincinsa,,, sai da ya k'oshi. Bayan ya gama yayi hamdala ga Allah sarki,,, sannan ya dubi"

Amina cike da tsananin tausayinta da k'aunar ta.. Yana tausayinta akan abinda zai fito daga bakinsa...

"Yayi huci mai zafi,,, sannan ya ce ""Amina ""."

"Ta ce ""Na'am farin ciki nah ""."

"""Ina son ki sani komai ya faru da mutum,,,, muk'addari ne daga Allah. Sannan bawa bai isa ya guje ma"

"k'addararsa ba,, duk abinda ya faru walau farin ciki ko bak'in ciki daga Allah ne.. Dan Allah kada ki yi min mummunan fahimta,, ki fahimce ni da idon basira kuma kiyi min uzuri.. Aduniya Amina babu abinda na ke so da k'auna sama da ke,, wannan abu da zanyi ba'a son raina ba ne wallahi.. Kuma k'addara ta ce ko mun k'i ko mun so sai ya faru,, saboda haka Aminatu tah kiyi hak'uri da juriya da abinda zan gaya miki"

"dan Allah "".Aliyu ya fad'a cike da kunya da sanyin jiki bata re da ya kalli Amina ba,,, cikin ido da ido ba...."

"Amina jikinta yayi matuk'ar sanyi,, tare da tausayin mijinta..."

"Tace ""Haba farin cikina,, domin mi kake bani hak'uri,, saboda mi ka ke fargabar sanar dani abinda ya"

"zama dole in sani.. Na yadda da k'addara ta Aliyu,,na san komi Rubutacce ne daga rabbi,,, kuma ina rok'on Allah kada ya kawo rana d'aya da zaka ji tsoron yi min magana ko sanar da ni wani abu... Ai kai shugaba ne agare ni kuma aljanna ta tana k'ark'ashin tafin k'afarka,, ka fad'i buk'atar ka ya kai farin"

"cikina.. Ni kuma zan bi umurni ka cikin gaggawa "".Ta fad'a cike da ladabi da biyayya."

"Hak'ik'a Aliyu ya ji dad'in kalamanta,,, sosai har cikin zuciyarsa.. Ya k'ara yabawa da tarbiyar da ta samu"

"daga gidansu,, tare da nuna juriyarta da hak'urin ta....."

"Yace ""hak'ik'a na ji dad'in maganarki,, dama nasan ba za'a samu matsala daga gare ki ba.. Ina rok'on"

"Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki,, ya kuma baki aljanna fiddausi da ke da dukkan mata masu irin halayenki ""...."

"Ta ce ""Amin ya farin cikina ""..."

"Aliyu ya ce ""dama ba wani abu ba ne,,, illa na ga wata yarinya acan garin Shiko,,, kuma ina son na aure"

"tah.. Sunanta Saudatu,, shi ne na ce bari in gaya maki domin neman yardarki da shawararki,,, mi ki ke ga ni,, mi ya kamata nayi? "".Ya fad'a cike da tausayin kansu....."

"Hak'ik'a maganarsa,, ta girgiza Amina domin taji matuk'ar fargaba da zullumi a cikin zuciyar ta.. Sai da"

"gabanta ya buga da k'arfi ""dummmm!!! Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Tayi ta maimaitawa a cikin zuciyar ta,,, sannan taji dama-dama da sanyi cikin zuciyarta...."

"Amina tadube shi,, kallo mai cike da tsananin k'aunarsa da fahimta...."

"Tace ""hak'ik'a kayi tunani mai k'yau ya mijina,, domin shi aure raya sunnah ne na annabi Muhammad (S."

"A. W) ne..kuma kowane mutum ana son yayi koyi ga annabawan Allah,, Allah ubangiji ina rok'on ka ya sanya ma wannan auren da zaka yi albarka,, ya kauda duk wata fitina da sharrin masu sharri a cikin sa.. Kuma ya bamu zuri'a d'ayyiba tare da juriya da hak'urin zama da junan mu "".Ta fad'a cike da mutuwar"

jiki...

"""Amin amin,,nagode sosai da addu'o'inki garemu.. Hak'ik'a Amina samun mace irin ki a wannan zamanin"

"yana da wuya,, mai son duk abinda mijinta ya ke so ko da ace ita bata amince ba,, Allah ya gwada mani kin haihu Aminatu tah. Sannan Allah ya bani ikon yin adalci a tsakanin ku "".Aliyu ya fad'a yana mai sanya"

mata albarka..

"""Amin mijina,, soyayyar da zan nuna maka kenan,, ka gane ina matuk'ar k'aunar duk abinda ka ke so.. Ko"

"da ace mahaukaciya ce balle mai hankali.. Mijina ina matuk'ar k'aunar ka a rayuwata,, hakan ba shi ne zai sa na haramta abinda Allah ya halatta maka ba.. Ina son duk abinda ka ke so koda ace abin shi ne zai zamo ajalinah "".Amina ta fad'a cike da dauriya da halacci..."

"Aliyu yace ""na sani Amina,, ai ke 'yar aljanna ce.. Babu abinda ba zaki iya yi min ba,, muddin kina da hali,,"

"Allah ya raba ki da bak'in cikin duniya da lahira ""."

"Amina tace ""Amin ya mijina,, idan kaje gida ka fad'a ma Baban Hadiza,, yaje nema maka aurenta.."

"saboda babanka idan shi ya fara sani zai iya hana ka cikar burinka ""...."

"Aliyu yace ""Insha Allah,, haka za'a yi Aminatu tah ""."

"Haka dai Aliyu,,yacigaba da yi mata fira.. Tana amsa masa cike da tsananin juriya da hak'uri irin na Amina"

"_(Anya kuwa ana samun mata masu irin wannan halin musamman alokacin da mijinsu zai yi musu kishiya,,, su danne kishinsu tare da ba zuciyar su hak'uri.. Kada mijin ya fahimci halin da suke ciki.. Allah"

ya sa mu dace baki d'aya)....._

********************

Adamu ya

"koma gidansa,, cike da damuwa tare da fargaba...."

"Bayan yayi wanka ne,, ya ci abincinsa cike da rashin walwala...."

"Dama matarsa Hussaina ta lura,, yana cikin matuk'ar damuwa.. Sai da ta bari ya kammala cin abinci"

amma baici ko rabi ba. Ta dube sa cike da tausayi da lallashi....

"Ta ce ""Baban Amir,, lafiya mi ke faruwa,, wa ye ya b'ata maka rai a waje ne? ""Ta ce cike da nuna ta damu"

da shi...

"Adamu ya ja gwauron numfashi,, mai zafi na bak'in ciki.. Sannan ya kawo labarin komai ya gaya mata...."

"Hussaina ta zabura da k'arfi!!! Tare da bugun k'irjinta,, tana cewa Inalillahi wa ina ilaihirraji'un!!! Duniya"

"zaki damu?,, wasu dai sunyi hasara a rayuwar su. Saboda basu tsoron Allah kwata -kwata a zuciyarsu "".Ta fad'a hawaye na kwaranya daga idanunta cike da tausayin k'awarta kuma aminiyarta ."

"""Miye abin kuka Ummu Amir,, addu'a ya kamata ki tayata ba kuka zakiyi ba.. Shiyasa bana son fad'a miki"

"irin wad'annan abubuwa,, saboda na san akwai ki da arhan yin kuka.. Goge hawayenki matata,, bana ganinsu domin kuwa ganinsu yana k'onamin zuciya tah "".Adamu ya ce cike da tausayi da tarin damuwa..."

"Hussaina ta goge hawayenta,, sannan ta ce ""Babu komai ,,Allah ya sa wannan shi ne ya fi zama alkhairi,,"

"ya basu juriya da hak'uri ""."

"""Amin amin,, ya matata dama haka ya kamata,, ki ce tun farko ba yin kuka ba. Ni ma ina jin kaina kamar"

"yadda kike ji,, to ya zamuyi sai hak'uri.. Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba "".Adamu ya ce."

"Hussaina tace ""Amin, Allah ya k'ara tsare mun k'awata,, ya kuma sanyaya mata zuciyar ta ""....."

"Adamu ya ce ""Amin ""....."

"Haka suka cigaba da fira,,,sama -sama saboda kowane daga cikinsu yana cikin matuk'ar damuwa..."

"Tare da tarin zullumi da kuma tunani,,, da sak'e -sak'e cikin zuciyar su......"

*********************

*BAYAN KWANA BIYU*

"Aliyu ne ya tashi da tsananin buk'atar ganin Saude,,, yayi sakko tun da safe bayan ya karya,,, yayi wanka"

"yayi shirinsa mai k'yau... Yace ma Amina xai je wurin Saude zance ""...."

"Batare da wani damuwa ba,, ko b'ata rai,,,ta d'auko turare mai k'amshi tare da sabulun wanki da na"

"wanka,, tasa cikin wata leda bak'a mai k'yau...."

"Ta mik'a masa,, ta ce ""Ga shi nan ya kaima Saudatu,, kuma tana gaishe tah idan ya je ya fad'a mata don"

"Allah ""....."

"Ya amsa yana mai jin dad'in karamcin matarsa ,,ya ce karki damu Insha Allah,,, sak'on ki zai isa gare ta.."

"Na kuma gode da karamci da mutunci ""...."

"""Babu komai,, ai yi wa kaine. Kuma an zama d'aya,,Allah ya nuna mana lokacin aure lafiya "".Amina ta ce."

"""Amin amin,, Aminatu tah,, Allah ya bar k'auna da zumunci "".Aliyu ya fad'a cike da shauk'in k'aunar"

matarsa.

"Tace ""Amin ""."

"""To ni zan wuce,,, ko akwai abinda ki ke buk'ata? ki taimaka ki fad'a min "".Aliyu ya fad'a cike k'aunar tah."

"""A'a bana buk'atar komai wallahi,,, fata na kuma shi ne ka dawo cikin k'oshin lafiya. Allah ya kiyaye"

"hanya "".Amina ta fad'a cike da tsananin k'aunar mijinta....."

"Yace ""Amin Nagode da kulawa ""......."

"Ya sa kai,,, yayi wucewarsa zuwa garin Shiko......"

*******************

"Adamu kuwa tun safe,, yayi wanka ya shirya zuwa gidansu Amina...."

"Yana zuwa k'ofar gidan,, ya samu yaro ya aike sa domin ayi masa sallama da Maigidan (mahaifinsu"

Amina)...

"Yaro ya shiga cikin gidan,, bai dad'e ba. Sai gashi ya fito..."

"Ya ce ""Maigidan yana zuwa ""..."

"Adamu ya ce ""to ya gode ""."

"Yaron ya yi wucewarsa,,, zuwa wasa cikin 'yan uwansa yara....."

"Ba'a jima ba,, sai ga Baba Ibrahim ya fito. Ya bashi hannu suka yi musabaha tare da gaisawa...."

"Bayan sun gama gaisawa ne,,, sai Baba Ibrahim ya ce ""ya shigo cikin gidan,,, saboda shi ba bak'o ba ne."

"Daga yau idan yazo ya daina tsayawa waje. Ai d'an gidane domin an riga,, an zama d'aya ""."

"Adamu ya duk'e kansa,,, cike da ladabi da biyayya. Ya ce ""ayi hak'uri Baba insha Allah,, ba zan sake ba ""."

"Baban ya ce ""to

Please Login or Register in order to submit comment