You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halinta ba saima abinda ya k'aru,,, fiye da lokuttan baya......"

********************

"Saude tana zuwa gidansu,,, su Inna Harira da Laure suka yi mata tarba mai k'yau... Suka cika mata"

"gabanta da kayan dad'i Saude ta kwance Asiya a bayanta ta mik'ama Laure.. Ta amsheta ta goya ga bayanta,,, ta fara cin abincinta sai da ta k'oshi. Sannan ta tashi ta shiga wanka..."

"Bayan ta fito daga wanka, ta canza wasu kaya masu k'yau. Ta kawo k'orafinta na son zuwa wurin boka"

"SIDDARU,,, ta gaya musu....."

"Inna Harira da Laure suka nuna mata,,, babu matsala.. Suka yanke shawarar Laure ta zauna gida,,, goye"

da Asiya kafin su dawo saboda kada abar gida babu kowa.

"Laure ta amince tare da nuna musu babu komai,,, sai sun dawo.. .."

"Inna Harira itama,,, ta shirya suka kama hanyar zuwa gidan boka SIDDARU.... ."

*********************

"Suna zuwa basu wani isko layi ba,,, saboda mutum biyu suka iske layi... Ko su ana gamawa da su,,, layi ya"

"kawo kan su Inna Harira boka SIDDARU ya umurce su.. Akan su shigo daga cikin bukkar,,, suka shiga suka zauna...."

"Boka SIDDARU ya bushe da mahaukaciyar dariya,,, alokacin ne komai da ke cikin dajin ya kama rawa da"

"girgiza.. Bayan ya gama dariya ne ya kama yin wasu sabbatu,,, a cikin wani yare wanda shi kad'ai yasan mi yake cewa... Can ya dube yace ""Aljani k'addaru ya riga ya sanar dani,,, mi ke tafe da ku.. Saboda haka ku sani buk'atarku zata biya na kashe Amina,,, amma ku sani akwai sauran lokaci,,, ya kamata ku k'ara jira ku 'yan Adam kun cika gaggawa akan buk'atarku.. To ku sani abin nan zai faru ku jira lokaci kawai zatayi mutuwar walak'anci da k'ask'anci.. Mu bama son mai gaggawa a cikin lamarin mu "".Yace cike da"

"tsawa tsawa, muryarshi kamar tusar jaki ."

"Inna Harira tace ""to boka ayi hak'uri,, zamu k'ara jiran lokacin.. Sai dai wani hanzari ba gudu ba,,, ak'ara"

"bamu maganin k'ara mallakar Aliyu ""..."

"Saude tace ""gaskiya ne boka sannan uwarsa tasa mani idanu,,, kuma bata sona so na ke abani maganin"

"da zan halaka ta ""....."

"""Za'a baki maganin mallakar Aliyu da kuma na rufema uwarsa baki,,,, amma ki sani babu maganin da zai"

"iya halaka Innarshi ,,,sai dai a rufe mata baki ya zama ko tana kina wani abu. Wanda bai dace ba bata iya yi maki magana "".Cewar boka SIDDARU cike da shed'anci da rashin imani........"

"Suka ce tare ""Wannan ma yayi babu damuwa boka d'an boka,,,, jikan boka kaine gagara badau uban"

"ibilisai,, kaine gobarar wuta mai k'one gidaje,,, kaine guguwar annoba mai tarwatsa maza. Haka dai"

"suka kama yi masa kirari,,, yana jin dad'i...."

"Can yace musu suyi shiru,,, ya d'aga hannunsa sama yana karanta karatun tsafi... Ba'a jima ba sai ga wani"

"ruwan magani da laya biyu sun bayyana,,,, a hannunshi.Ya d'auki maganin na ruwa ya basu yace"" Saude da shi zata rink'a wanka akodayaushe,,, laya d'aya ta gina rami tasa,,, d'ayan kuma tasa a k'ark'ashin"

"gadonta. Aliyu zai zama mallakinta har abada ""...."

"Saude tace ""to boka SIDDARU "".Tasa hannu ta amsa....."

"""To boka SIDDARU miye ladar aikinka,"".Cewar Inna Harira....."

"Yace musu ""kud'i zasu bashi sannan Saude ta shiga d'akinshi,,,, zasu gana......"

"Inna Harira tace cike da tsoro ""boka bata dad'e da haihuwa ba ""..."

"Yace ""bana son gardama!!! Idan baku shirya ba,,, ku mik'omin maganina ku tafi.. Amma ku sani aljani"

"k'addaru zai iya shanye muku jini akodayaushe,,,, kuma a kowane lokaci "".Ya fad'a musu cike da tsawa mai firgitarwa..."

"""Kayi hak'uri "".Inna Harira tace cike da masifar tsoron shi..."

"Saude tace ""yi hak'uri boka,,, na amince da buk'atar ka domin biyan buk'ata ta "".... ."

"""Haka na ke sonji d'iyar k'warai "".Cewar boka SIDDARU..."

"Inna Harira ta bashi kud'i dubu goma,, sannan ya umurce ta akan ta fita waje ta tsaya,,,, jiran Saudatu.."

Ba'a son ranta ba ta fita waje ta tsayaaa...

"Boka SIDDARU yaja hannun Saude,, suka shiga d'akinsa.. Akwai gado da kujeri a cikin d'akin...Komai dai"

yayi k'yau a cikin d'akin na shi.

"Ya kwantar da ita yana kissing d'inta,,,tare da cire mata kaya suka lula duniyar mazinata.."

"Sun dad'e suna abu guda,,, sai da yayi awa biyu cur saman kanta... Sannan ya sauka daga baya ya"

"k'yaleta hakanan,, Saude ta yi wanka cikin toilet d'in shi sannan ta mayar da kayanta.... ."

"Anan waje kuwa Inna Harira tayi jiran Saude,,, har ta gaji domin kuwa sai da rayuwarta ta b'ace...."

"Saboda yana boka ne shiyasa taji tsoron yi masa magana,,, idan ba haka ba da sai taci mutuncin ko uban waye... Ba'a jima ba sai ga Saude ta fito,,, suka kama hanya domin su shiga mota zuwa gida.."

"Alokacin ne Inna ta dubi Saude,,, tace ""Hmm yau kam kinsha gurzan k'ato Saude,, shiyasa tun farko"

"banso ki amince ba "".."

"""To ya zanyi Inna biyan buk'ata ai yafi dogon buri,,, wallahi na tsani kishiya a rayuwata. Na tsani in bud'e"

"ido ina ganin Amina,,, a matsayin kishiyata saboda ta fini komai,,, kuma ta zarce ni a komai na mace.. Kinga kuwa dole inyi koma miye domin ganin na ga bayanta "".Cewar Saude..."

"Inna Harira tace ""haka ne kam kinada gaskiyar ki Saude,,, ko ni ce sai inda k'arfina ya k'are muddin akan"

"kishiya ne.. Saboda da kishiyar gida gwamma ta waje ""....."

"Saude tace ""wallahi kam ai shiyasa na tsaneta,,, fiye da komi a rayuwata.. Ai zata gane kurenta "".."

"""Haka na ke sonji 'yata,,, karki raga mata ko kad'an ne ""..Cewar inna Harira."

"Saude tace ""Wa ni in raga mata,, ina hauka ne. Ai da ni da kishiya nesa da nesa......."

"""Da kin k'yautama kanki "".Inna Harira tace,,, suna kawowa bakin titi suka tari motar zuwa cikin garin"

Shiko.........

**********************

"Suna dawowa gida,, Saude tayi wankan tsarki.. Sannan ta k'ara cin abinci ta d'an huta kad'an,,, sun ba"

"Laure labarin duk abinda ya faru da su gidan boka SIDDARU. Amma basu fad'a mata ba boka yayi zina da Saudatu,,, Saude ta ba d'iyar ta nono sai da ta k'oshi. Sannan ta ba Inna Harira dubu goma,,, yaya Laure dubu biyar k'yauta sannan tace musu zata wuce zuwa gida,,, sukayi mata godiya tare da rakata har waje babu hijabi balantana mayafi.Koda yake karkuga laifinsu wanda yayi nisa baya jin kira,,, sai dai muce"

"Allah ubangiji ya k'ara shiryar da mu hanya madaidaciya ,,,Ameen..."

"Saude tana komawa gidan,,, tayi wasu ayyukan ta Aliyu ya shigo yayi mata sannu da zuwa,,, tare da"

kawo mata nama cikin leda mai yawa. Tare da lemun k'walba da ruwa masu sanyi..

"Ta amsa taci cike da jin d'adi da murna. Ta so ta tambaye shi ko Amina batayi abinci ba ne,,, amma da"

yake taga kayan kwad'ayi ta manta......

"Ta cigaba da harakokin ta na gida,,, tare da sanya ma Aliyu ido saboda kada ya kula Amina baiwar"

Allah.....

Bayan wasu kwanaki Saude tayi amfani da duk maganin da boka SIDDARU ya bata. Nan ta ke magani ya

"fara aiki Aliyu ya k'ara tsanar Amina fiye lokacin baya,,, kashi ya bata na k'warai tare da walak'anci da"

"k'ask'anci iri -iri na duniya,,, to Amina ta ganshi baya sonta baya son 'yarta Aisha. Hak'ik'a a wannan lokacin kamar Amina ta had'iyi zuciya ta mutu akan damuwa da bak'in ciki da k'uncin rayuwa.."

"Alokacin ne Sauce ta k'ara bayyana musu mugun halinta,,, na rashin tausayi da imani. Ta cigaba mulkar"

gidan cike da zalunci da cin Amana..

*BAYAN SHEKARU GOMA SHA 'DAYA*

"Abubuwa da dama sun faru na bakin ciki da na farin ciki,, saboda a wad'annan shekarun Amina da"

"Aisha,,,sunga tasko da walak'ancin duniya. Saboda Saude ta sha gama Aisha da babanta wai ta zageta ko kuma ta aiketa ta k'i zuwa,,, sannan ta yi mata rashin kunya. Shi kuma Aliyu babu bincike babu komai,,, ya kama Aisha yana ta kashi kamar jaka babu tausayin kada yaji mata ciwo. Amina baiwar Allah ko kallon shi bata yi alokacin da yake bugun Aisha,,, saboda cewa yakeyi ita ke d'aure mata gindi. Cewa ta ke ita babu ruwanta ya kashe ta,,, idan ya kashe ta ya binneta ai 'yarsa ce babu abinda ya dameta.. Haka dai yake mata jina-jina sannan ya k'yale ta,, Saude da Asiya suna gefe suna abinda ke faruwa tare da jin d'adi"

sosai......

"Haka abubuwan suke faruwa a cikin gidan,,, Saude kawai ke jin d'adin gidan da ita da Asiya. Amina"

k'uncin rayuwa da bak'in ciki kawai ta ke fuskanta a rayuwar ta......

"Wata rana bayan Aliyu ya fita zuwa wurin sana'ar sa a kasuwa,,, Saude ta kira Aisha zata aike ta saboda"

"ta siyo mata klin domin ta yi wanke wanke,,, alhalin ga d'iyar ta Asiya nan zaune tana wasar k'asa,,, bata aiketa ba sai Aisha.."

"Aisha tace mata ""kullum kullum ni kike aiki,,, banda Asiya idan nace kuma ta zo ta rakani.. Sai kice a'a na"

"tafi ni kad'ai yau kam bani zuwa ko'ina Inna ""......."

"Saude tace ""Ga buro uba, kinci uwarki shegiyar yarinya kawai...Wadda tayi gadon mugun hali ""....."

"Aisha tace ""ba dai uwata ba ni kam Inna ""...."

"Asiya ta tashi daga wasar k'asa tace ""keee!! Dan ubanki kada ki kuskura ki zagi Innata, yanzu inci dorin"

"uwarki Amina "".Tace cike da masifa..."

"""Barta tayi min rashin kunya,,, in bugi jaka inci gundunbulin buro uban ki.. Shegiya d'iyar matsiya kuma"

"karuwa,,, wallahi ko uban ki bai isa in fad'a yana fad'a ba.. Dangin mayu da talauci "".Cewar Saude cike da masifa da bala'i....."

"Aisha ta murgud'a musu baki,, irin na k'urciya tace ""ni kam ba ubana ba ""..."

"Asiya tace ""sai dai uban wa?. Inna zaki zaga kenan ""...."

"""Bar shegiya annobar gari "".Saude bata yi wani b'ata lokaci ba,,, ta kashe Aisha da mari mai k'yau... Aisha"

"sai da taga taurari sun gifta mata,,, ta hauta da bugu itada Asiya,,, kamar sun samu jaka suna bugunta......"

"Can Amina tana cikin d'akinta,, taji kuwwar Aisha tana cewa ""wayyo Ummana kizo ki ceceni zasu kashe"

"ni da kingin raina ""....."

"Amina ta shek'o da gudu daga cikin d'akinta,,, tana cewa ""Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!! Wannan wane"

"irin masifa da bala'i Saudatu,,, kashemin ""ya kuke sonyi saboda bak'in ciki da hassada.. Wallahi bazan bari kuma Allah ya isa tsakanina da k......"

"Bata k'arasa maganar ba,, Saude ta rarumo k'aton icce ta bugama Amina a kai,,, sai da kanta ya fashe da"

jini ta fad'i k'asa ta suma....

"Saude tace ""gobe ma ki koma 'yar kan dorin uwa,, karuwar banza argunguma annoba....."

"Tana wannan maganar saiga sallamar Hussaina da Habiba sun shigo,,, saboda su tafi gidan biki"

mak'wabta....

"Suna ganin abinda yake faruwa, suka k'araso da saurinsu. Suka ce tare ""mi zamu gani Saudatu Ina lillahi"

"wa inna ilaihirraji'un!!! Yanzu duk ke kika yi wannan aika aikar,,, saboda tsananin *KISHIN JAHILCI* da hauka ""......."

*Muje zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 166-170

"Habiba tace ""wannan wane irin rashin imani da rashin tausayi ne, so kike ki kasheta da ita da d'iyarta.."

"Wannan abin yayi yawa gaskiya saboda kishin ya zama jahilci da hauka "".."

"""Wallahi abin babu tsoron Allah a cikin sa,, kefa kika iskota tare da mijinta. Sannan kizo kina nuna kin fita"

"sonshi tare da buk'atar shi,,, wannan ba zai tab'a yiyuwa ba. Kina nunama mutane hauka da zafin kishi ke adole gaki mai kishi,,, ba fa gareki ba farau ba zama da kishiya balle ak'are a kanki "".Cewar Hussaina cike"

da tashin hankali da zullumi..

Sukaje suka samo mai motar haya domin ya d'auki su Amina ya kaisu asibiti.. Bayan sun dawo ne...

"Saude tace ""Buro uban su ta bugi Amina da Aisha,, duk abinda zasuyi suzo suyi mata,, shegu dangin"

"mayu karuwai 'yan iskan banza har kunada bakin da zaku zageni.. To idan baku rama mata ba kunci kabarin babbar buro uban ku,,, kwad'ayayyi mazinata kawai da ku"". Haka ta kama zaginsu tare da tsine"

"musu albarka,,, abun k'arin takaici mai mota yaja motarsa suka wuce. Tare da zuba mata k'ura hak'ik'a"

tayi bak'in cikin wannan abin da su Habiba sukayi mata... .

********************

"Suna fita Saude ta kira Inna Harira,, saboda taje wurin boka SIDDARU domin ta gaji da ganin Amina a"

"raye,,, Inna Harira ta kwantar ma Saude da hankali.. Tare da nuna mata zata je wurin boka SIDDARU yanzu,, Saude tayi mata godiya tare da nuna harda maganin magance mutane tana so. Inna ta nuna babu matsala,,, sannan sukayi sallama da juna.. Inna Harira tare da cema Laure ta tsaya,,, ta fake gida yanzu zataje wurin boka SIDDARU,,, yanzu yanzun nan zata dawo.. Laure ta nuna mata babu matsala"

tare da yi mata Allah ya kiyaye hanya....

"Inna Harira tace ""Amin""Ta sa kai tayi wucewarta wurin boka SIDDARU....."

"Acan asibiti suna zuwa aka amshi su Amina,,, aka kwantar da saman gado ma'ana an basu gado.. A"

"asibitin su Habiba ne suka kira Iyayen Amina da na Aliyu,,, sannan suka sanar da Aliyu abinda ake ciki,,, shi dai Aliyu bai wani damu ba balantana ya tayar da hankalinshi. Saboda ayanzu ba wani son Amina yake ba ko ita Aisha baya nuna mata so kad'an,,, Maman Amina ce ta sanar da Hadiza halin da suke ciki. Hankali tashe Hadiza sukazo tare da mijinta mai suna Hashim,,, da yaranta biyu Jamil da Jamila 'yan tawaye ne. Tayi aure ne a shekaru bakwai da suka wuce,,, sunzo nan Kamba tare mijinta da yaranta.. Da yake su suna zaune a Birnin kebbi can yake da zama,,, haka dai suka cigaba da jinyar Amina cike da tsananin damuwa da tausayinta. Da yake abin akwai asiri cikinsa babu wanda ya tambayi ba'asi ko dalili ba,,, saboda duk an rufe musu baki. Haka dai cigaba da jinyar Amina cike da kulawa da nuna mata so,, su Habiba suna zuwa akai akai domin dibin Amina tare da zuwa mata da kayan marmari... Hak'ik'a Amina"

"taga gata da so ta kowane bangare guda biyu,,, wato iyayenta da na Aliyu da su Habiba...."

"Haka dai suka cigaba da basu kulawa,, har sai da sukayi sati biyu sannan aka sallame su ita da Aisha...."

Suka wuce zuwa gida....

*********************

"Bayan tafiyar Inna Harira zuwa wurin boka SIDDARU,,, Malam Isiyaku bawan Allah yana nan cikin gidan"

"babu ruwanshi da harakokin su,,, hidimomin gabansa kawai ya keyi.. Babu abinda ya shafe shi da harakokin su Inna Harira,,, ya kawo idanu yasa musu wad'anda basu ji basu gani.. Gaisuwa kawai yake had'ashi da su bayan shi babu wani abu,,, ko shi wata rana idan sun gadama agaisa idan basu gadama kallon banza kawai suke yi masa.. Malam Isiyaku yana kanje wurin sana'ar sa,,, sannan kuma idan Abdullah ya dawo daga makaranta yana taya mahaifinsa sana'a. Domin ayanzu ya zama saurayi sosai,, saboda yanzu yana last year a Aleiru University Birnin kebbi,, Kebbi State ita kuma Atika ta zama budurwa sosai har batun aurenta ake yi da saurayinta Tukur,, yana aiki a wani kamfani.. Itama tana yawan zuwa kawo masa fura da nono,, saboda taga yana son fura sosai ita kuma tana son faranta masa,,, yana yawan yi sa musu albarka tare da godiya ga sarki Allah.. Da yasa d'iyansa suka zama na k'warai,, idan ya gansu yana kasancewa cikin matuk'ar farin ciki da nishad'i muddin yana tare da su. Yana yawan basu sak'o zuwa ga Mariya abar begenshi dare da rana,, haka yake gudanar da rayuwar shi cike da farin"

ciki da walwala.... ..

"Inna Harira kuwa tana zuwa wurin boka SIDDARU,, ta kawo bayanin komi ta fad'a masa tare da neman"

"maganin magance mutane.. Saboda gudun matsala da tonuwar asirinsu,, boka SIDDARU ya nuna mata babu matsala.. Yanzu lokacin da asirin zai tasiri ga jikin Amina,, ya nuna mata za'a turama Amina mugun ciwo wanda zai zama ajalinta. Saboda kada azargi Saude nan ta ke, ya kawo garin magani ya bata domin Saude ta yi hayak'i da shi domin magance mutane da matsalarta.. Inna Harira ta yi godiya sosai sannan ta bashi kud'i naira dubu ishirin,, ya amsa tare bata magani.. Ya nuna mata karta damu Amina ta kusa barin duniya,,, domin kuwa zata yi mutuwar walak'anci da k'ask'anci a rayuwar ta. Inna Harira ta yi masa sallama ta wuce gidansu,,, cike da matuk'ar farin ciki mara misaltuwa saboda burin Saude ya kusa cika na"

mallakar Aliyu ita kad'ai a rayuwarta...

*********************

"Inna Harira tana dawowa gida,,, ta sanar da Laure duk abinda boka SIDDARU yace. Itama tayi matuk'ar"

"murna da farin ciki domin cikar burin 'yar uwarta. Nan da nan bada b'ata lokaci ba suka samu mai motar haya,, suka bashi sak'o zuwa ga Saude ya amshi sak'on cikin bak'ar leda mai k'yau. Sannan suka bashi"

"kud'insa naira d'ari biyar,,, ya amsa ya kama hanya......."

"Bayan an sallami Amina da Aisha,, daga asibiti suka dawo gida da 'yan rakiyarsu su Habiba da Hadiza.. Sai"

"da suka yi mata gyare -gyare da tsabtace mata muhalli,,, suka yi mata abinci ta ci sannan suka ce zasu wuce gida. Suna jin Saude tana zage-zage da habaice -habaice tare da tsine musu albarka.. Kamar zata buge su in tana abu kamar mahaukaciya.. Abin burgewa babu wanda ya kula ta daga cikin su,, suka yi ma Amina sallama kowace tayi gidan mijinta... Hak'ik'a wannan abin yayi matuk'ar k'onama Saude rai tare"

"da jin haushi,,, ta kuma yi alk'awarin sai taga bayan gaba d'ayansu..."

"Mai motar haya ya kawo mana Saude sak'onta,, ya nuna mata sak'on daga garin Shiko ya fito. Gaba"

"garesa tayi waya da Inna Harira tayi mata bayanin duk abinda boka SIDDARU yace,,, suka gaisa da juna sannan suka yi sallama.. Hak'ik'a Saude ta kasance cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa da murna wanda bata tab'a ji ba,,, a rayuwarta akan murna da farin ciki taba mai motar haya naira dubu k'yauta.. Yayi murna sosai tare da yi mata godiya ya yi wucewarsa zuwa wurin sana'ar shi,,, Saude ta ji dad'i sosai"

nan da nan ta turara hayak'in maganin da boka SIDDARU ya bata.. Tare da kwanar farin ciki da nishad'i...

"Haka dai ta cigaba da amfani da maganin,, cike da jin d'adin cikar burinta..."

*WAIWAYE ADON TAFIYA*

Alokacin da Aliyu yayi ma Amina fad'a akan kada Hadiza ta sake zuwa masa gida. Washe gari aranar ne

"Amina ta kai ziyara gidansu,,, tare da rok'on Mamansu akan kada Hadiza ta k'ara zuwa inda ta ke,,, kuma ta gode domin yanzu tana iya komai da kanta. Maman Amina ta tambayeta dalili amma bata gaya mata komai ba illa tana nuna mata Aliyu,,,,baya son zuwan Hadiza gidan baya ga haka batace mata komai ba,,, itama Hadiza tayi tayi Amina ta gaya mata gaskiyar magana.. Amma Amina tak'i sanar da ita gaskiyar lamarin,, alal hak'ik'a Amina tana da matuk'ar hak'uri da zurfin ciki. Kuma kunsan ciki ba domin tuwo kawai aka yi sa ba,,, saboda wasu sirruka da kuma rufa asiri.. Haka dai ta yini gidansu,, sukayi fira cike da"

nishad'i da jin d'adi sosai....

"Bayan wasu kwanaki Hadiza ta had'u da Hashim,,,, cikin mota kusa ga INEC office.. Yayi mata sallama ta"

"k'i amsa mishi,,,shi kuma ya kama binta da mota bata sani ba. Har suka iso gida ta shige cikin gidansu,,, Hashim ya samu yaro akayi masa sallama da Baba Ibrahim. Bayan mintuna kad'an saiga baba Ibrahim ya fito,, Hashim ya gaida shi cike da ladabi da girmamawa,, sannan sukayi musabaha da juna.. Hashim baiyi nauyin baki ba ya kawo bayanin cewa yaga Hadiza yana son ta da aure,,, Baba Ibrahim yayi mishi wasu tambayoyi hashim yana bashi amsa. Bayan ya gama tambayar shi ne ya gano Hashim d'an abokinsa ne Kabiru,, wanda sukayi wasa tun suna yara. Yasan Hashim tun yana k'arami sannan Alhaji Kabiru"

mutumen kirki ne....

"Baba Ibrahim ya amince masa da ya turo magabatansa,, domin asa lokacin aure babu matsala.. Hak'ik'a"

"Hashim yayi murna sosai da farin ciki a wannan rana,,, yayi ma Baba Ibrahim godiya sosai sannan ya wuce gidansu....."

"Baba Ibrahim ya sanar da baba Ayuba,, duk abinda ake ciki shi ma yayi murna domin shi ne uban d'iya..."

"Bayan wasu kwanaki Hashim ya turo magabatansa wurin baba Ayuba,, har ansa lokacin auren nan da"

"sati biyu... Haka dai kowane bangare suka cigaba da shirye shiryen bikin auren. Ana nan sati biyu ta cika aka d'aura auren Hashim Kabiru da Hadiza Ibrahim,,, akan kud'in sadaki dubu talatin. A wannan ranar"

duk wani masoyin Maman Amina ya ta yasu murna da farin ciki....

"Amarya ta tare gidan mijinta,, suna tafiyar da rayuwar aurensu cike da aminta da juna da tsananin"

"k'aunar junansu. Hak'ik'a Hadiza tayi dacen mijin k'warai domin kuwa Hashim yana mugun sonta,,, tare da nuna mata kulawa. Sannan baya son b'acin ranta ko kad'an,, haka suke gudanar da rayuwar aurensu"

cike zaman lafiya da soyayya mai tarin yawa... ..

*BAYAN WATA BIYU*

"Alokacin ne Amina ta kamu da tsananin rashin lafiya,, aka kwasheta akayi asibiti da ita. Bayan sun je can"

"likitoti sunyi bincike iyakar bincike,,, amma ba'a gano musabbabin ciwonta ba.. Bayan sunyi sati guda kuma aka maidata gida,, Aisha babu abinda takeyi sai kuka. Su ma su Habiba da iyayenta da na Aliyu hankalinsu yayi matuk'ar tashi,,,, saboda tsananin tausayinta da kuma fargaba. Haka dai ciwo ya cigaba da cin jikin Amina,, ta fara fitar da jini mai shegen wari da d'oyi.. Hak'ik'a hankalin duk wani mai imani ya tashi idan mutum,,, yaga yadda Amina ta koma sai ya tausaya mata banda Saude.. Maman Amina hankali tashe ta kira Hadiza ta sanar da ita abinda ya ke faruwa,,, Hadiza hankalinta yayi k'ololuwar ta shi ta sanar da Hashim.. Cike da tsananin damuwa da zullumi,, nan da nan suka shirya tare da yaransu sai cikin Kamba,,, sun shigo kamar k'iftawa da bismillah.. Suna zuwa suka d'auki Amina sai asibitin F.M.C da ke cikin Birnin kebbi,,, tana samu kulawa sosai domin agaskiya Hashim ya kashi kud'i sosai.. Tayi sati biyu nan ma saboda har nan su Habiba da iyayensu suka zo nan domin jinyarta,, bayan sati biyu Amina ta zama kamar horror da skeleton domin ko'ina a jikinta.. Yana fitar da jini mai mugun wari,, hankalin dangin Amina da na iyayenta da duk wani masoyinta ya tashi. Kowa ka gani banda kuka babu abinda"

"suke yi,,, haka dai suka koma da ita gida saboda nan suma,,,"

basu gano komai

ba.....

"Haka dai ta cigaba da wahala da ciwo,, Aliyu ko kallo bata ishe sa ba.. Babu ruwanshi da shiga sabgarta"

"duk tana cikin jinya cewa yakeyi bai zuwa d'akinta. Saboda mugun warin da Amina ta keyi,, gashi yanxu babu d'igon sonta ko kad'an a cikin zuciyarsa. Saude da Abu suna gefe suna kallon duk wani shige da ficensu,, hak'ik'a tayi murna da farin cikin wannan abu da ya samu. Tare da sanar da su Inna Harira suma sunyi matuk'ar farin ciki da murna,, domin kuwa har da party suka had'ama Saude saboda murnar cikar"

burinta da kuma shirin mallakar Aliyu ita kad'ai a rayuwar ta..

"Haka Amina ta cigaba da zama da ciwo a jikinta,, har dai ta kai sai anyi mata wanka da bata abinci."

"Hadiza ce ta dawo gidan gaba d'aya da zama,, tana jinya tana kuka tare da tausayawa rayuwar Amina."

"Suma su Habiba suna zuwa dibin Amina idan suka zo suna taya Hadiza kula da ita,,, tare da yawan yima Amina akan matuk'ar tausayinta.."

"Aisha ma tana lab'ewa wani lungu,, tasha kukanta na bak'in ciki da k'uncin rayuwa akan ciwon Amina"

mahaifiyarta.... .

*Muje Zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_Ina neman alfarmarku masoyana, akan ku tayani da addu'a Allah ubangiji ya yaye min abinda ke"

damuna. Ya kuma musanya min da mafi alkhairi a rayuwata. _

*PAGE* 171-175

"Haka Aisha ta ke b'oyewa ta sha kukanta,, mai cin rai na bak'in ciki da k'uncin rayuwa _*(fans kuyi"

"hak'uri na manta in sanar da ku,, Aisha da Asiya suna zuwa makarantar boko da Islamiya. Kuma a primary six suke sun kusa gamawa)*_.. Haka suka cigaba da jinyar Amina cike da tsananin tausayi,, babu abinda suke yi idan ba kuka ba. Wato idan kasan Amina a ada to yanzu idan ka ganta,,, kana rantsuwa da Allah kace ba ita ba ce saboda duk an chanza mata kamanni da halitta,,, ta koma kamar ba mutum ba saboda tsananin ramar da ta yi da kuma tsananin wari da ke fita a cikin jikinta ,,alal hak'ik'a ko ni na tausayawa rayuwar Amina.. Saboda taga k'unci da jarabawar rayuwa,,, wannan yana daga cikin"

kundin k'addararta .....

*BAYAN WATA GUDA*

"Ciwon Amina ya k'ara tsanani sosai,, dole yasa aka mayar da ita asibiti.. Iyayenta da na Aliyu da kuma"

"'yan uwa da abokan arzik'i babu abinda suke yi idan ba kuka ba,,, kowa ka gani yana cikin bak'in ciki da zullumi tare da tsananin fargaba.. Saboda tsoron ko ba zata tashi ba,, haka dai likitoti suka taru akanta domin gano mi ke damunta. Haka dai suka cigaba da jinyar Amina a asibitin har tayi kwana biyu,,, taji dama saboda tana iya magana kad'an kad'an.. Ta rok'i likita akan tana son ta gana da 'yan uwanta,,, likita bai hana ba saboda yanada matuk'ar tausayi da jink'ai. Haka yaje ya kirasu Malam Ibrahim tare da su Habiba,, har da Aliyu sai

Please Login or Register in order to submit comment