You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alk'awarin insha Allah ina jibi suna nan tafe da k'anenshi da abokaninshi. Malam Adamu shi ma yayi farin ciki matuk'a,,, suka cigaba da maganganunsu bayan sun"

kammala ne. Kowa ya katse wayarshi.....

*********************

"Acan gidansu Maman Amina kuwa,, akodayaushe tana tuna Aminarta. Tare da yi mata kuka da addu'ar"

"samun rahamar ubangiji Allah,,, Baba Ibrahim ne idan ya ganta yake yawan lallashinta tare da kwantar mata da hankali. Shi zai nuna mata muhimmanci hak'uri da juriya a rayuwa tare da nuna mata illar yima mamaci kuka,, ya zasu yi ne? Wanda ya basu Amina kuma yafi sonta ya karb'i abarsa. Allah sarki duniya rai ba'a bakin komai ya ke ba,,, mu kasance masu k'yautata mu'amalar mu da mutane,, kuma mu kasance masu hak'uri da irin mutanen da Allah ya had'a mu da su. Maman Amina ko ta so ta tuna da tanada jikanya Aisha,,, k'arfin sihiri da tsafi baya bari ta tuna da komai a cikin zuciyarta,,, sau da yawa da"

dama tana son tunawa amma ina bata iya tuna komai a rayuwarta ta baya.....

"Haka dai al'amarin gidansu Maman Amina,,, yake tafiya cike da d'umbin tausayi da jink'ai....."

"Acan gidansu Inna Harira kuma,,, washe gari tun safe taje wurin boka SIDDARU. Ta amso maganin da"

"kada asirinsu yayi saurin tonuwa,,, saboda bata son duk abinda zai kawo musu matsala a rayuwa. Kuma ta tsani asirinta ya tonu duniya kowa yasan abinda suke aikatawa,, boka SIDDARU ya bata magani kuma ta amsa tare da bashi kud'i,,, tayi masa godiya tare da komawa gida.. Boka SIDDARU kallonta kawai yake yana yin mahaukaciyar dariya mai cike da k'azanta,,,tana dawowa gida tayi amfani da maganin boka ya"

bata babu b'ata lokaci.

"Inna Harira tace ""Laure babu wanda yazo nema na ne? ""..."

"Laure tace mata ""tsofaffin banza su Iya Delu da Inna Lanti sun zo nemenki nace musu baki nan kinje cikin"

"gari "".."

"Inna Harira ta yi dariyar tsaffi,, tace ""Allah sarki k'awayen k'warai,, ashe saida suka zo bid'ata,, kee kuma"

"Laure ki fita cikin idona k'awayen nawune tsoffin banza. Ba uwayenki ba ne ko kuwa wani reni ne ya shiga a tsakanin mu ?"".."

"Laure tace ""ba wani raini ai gaskiya na fad'a,,, su kullum basuda aiki sai tsegumi da anyi ance ""..."

"""To idan sunyi tsegumi da anyi ance,, ina ruwanki? Naga yanzu kanki yana hayak'i fa. Ki bini a hankali"

"kinji ko "".Cewar Inna Harira.."

"Laure tace ""ya isa kada ki cikani da shegen surutun ki,,, kin tsufa Inna amma sai k'ara rikici kikeyi.Karki"

"damu yau ina bar miki gidan saboda na lura abokaninki sun fini a wajenki,,, kinfi sonsu bisa da ni ""..."

"Inna Harira tace ""yi hak'uri Laure abin ba haka ba ne,,, wallahi babu wadda ta ko kama k'afarki a wajena."

"Ki k'ara hak'uri da ni wata rana sai labari d'iyata ta kaina kinji ""..."

"Laure tace ""ai haka kike cewa kullum,, sai kinyi abu kizo kina damuna da inyi hak'uri ""..."

"""Allah ya huci zuciyarki Laure na,, ki sani banida tamkarki a ko'ina. Saboda haka ne yasa bana son b'acin"

"ranki ""Cewar Inna Harira cike da lallashi...."

"Laure tace ""babu damuwa komai ya riga,, ya wuce har abada ""...Ta mik'e ta yi wurin wanke wanke ta"

fara yi....

"Ita kuma Inna Harira tayi batun d'ora tukunyar dahuwar abinci,,, na rana saboda su gama da wuri..."

**********************

"Misalin k'arfe hud'u da rabi na yamma,, sai ga su Inna Lanti da Iya Delu sun sake dawowa. Suna zuwa"

"suka iske Inna Harira tana zaune tana k'ulla kayan miyar da suke saisuwa,,, suka samu wuri sunka zauna tare da gaisawa. Alokacin ne Laure tana cikin d'aki tana jinsu. Inna Harira ta kawo musu soyayyen nama da swan water masu sanyi,,, suka fara ci suna jin d'adi gasu dama da mugun kwad'ayi da tsananin son abin duniya. Haka dai suka kama ci naman tare da korawa da ruwan sanyi,,, har suka kammala. Bayan"

sun kammala ne Iya Delu ta dubi Inna Harira....

"Tace ""kee kuwa Harira in tambaye ki? ""..."

"Inna Harira tace ""ina jinki tambayeni ""..."

"Iya Delu ta karkace shegen bakinta,,, tace ""Hmmm wai ya batun matsayin aurenki da Malam Isiyaku,,,"

"sannan kuma ya batun mijin d'iyar ki Saude. Mi zai hana ta je wurin boka SIDDARU ya bata maganin,,, da zata kashe shi ta mallaki dukiyar shi gaba d'ayanta ""....."

"Inna Lanti tace ""Ai shi ne nima na gani,, kibi shawarar Delu zakiga amfaninta. Saboda zaku k'ara yin kud'i"

"a cikin garin nan na Shiko,,, kuma zaku k'ara shanawa ""...."

"Inna Harira tace ""To zanyi ma Saude maganar,,, inji mi zata ce domin kunsan mai d'aki shi yasan inda"

"yake mishi yo-yo ""..."

"Iya Delu tace ""Dad'ina da ke Galma bakida wayo,,, gaki kamar ga fuska kinada wayo amma bakida shi "".. ."

"Inna Lanti tace ""gaya mata dai ana nuna miki hanyar arzik'i,,, kina kaucewa bar ganin kina cikin gidan"

"mijinki wlh idan ya dawo cikin hayyacinsa... Hmmm kashinki ya bushe domin bazan iya misalta miki kalar d'umbin walak'ancin da zaki sha ba "".."

"Inna Harira tace ""ai na d'auki shawararku Delu da Lanti,,, amma ina son ku sani dole zanyi tunani da"

"nazari akai. Ba wai haka kawai zan yanke shawara ba,, na yarda da ku ba rashin yarda ba ne zaisa inyi haka ba "".."

"Iya Delu tace ""duk shawarar da kika yanke muna nan muna jiranki ""..."

"Inna Lanti tace ""haka ne kam gsky,, ke dai yi tunani mai k'yau ""....."

"""Zanyi tunani karku damu "".Cewar Inna Harira...."

"Duk mugun k'ulle-k'ullen da sukeyi,,, tare da Inna Harira muguwar shawara. Saude tana nan lab'e tana"

"jinsu,,, tayi matuk'ar mamaki da maganganunsu,,, kuma taji dad'in da Inna Harira tace musu sai tayi"

"shawara. Domin tasan kashe wani a yanzu zai iya zama sanadiyyar tonon asirinsu,,, haka ta samu wuri cikin d'aki ta zauna tana mamakinsu......"

"Inna Harira tace ""zanyi tunani mai k'yau,,, tare da yanke hukuncin da ya dace "".. ."

"Suka ce atare ""To yayi k'yau ""..."

"Sannan suka cigaba da firarsu,,, ta yadda zasu b'ullo ma lamarin Malam Isiyaku da Aliyu..Bayan sun jima"

"sosai sukayi ma Inna Harira sallama,,, tare da fitowarsu suna tafiya suna gulmarta tare da zaginta.."

"Iya Delu ce ta dubi Inna Lanti tace ""kuji min bak'ar shegiyar mata,,, mai bak'ar rowa ta zata sonta har"

"cikin zuciya. Da muke bata shawara batasan mun tsaneta bama son ta ko kad'an ""...."

"Inna Lanti tace ""hmm ai ni bakisan yadda na tsaneta ba,, na tsaneta kamar mutuwata,, saboda ta samu"

"d'akin k'warai da mijin na gari. Amma ta tsaya tana wasa da damarta bata godema Allah ba ""....."

"Iya Delu tace ""ai shi ne kuma Lanti,,, amma kuma Harira akwai rowa ki diba ki gani duk yawan zuwan mu"

"gidanta. Sai yau ta kawo mana nama da shegiyar rowarta ,,,kuma babu kud'in mashin ballai wani k'yautatawa ""...."

"Inna Lanti tace ""haka ne Allah yayi ma Galma sauk'in rowa,, amma naso tayi saurin d'aukar maganar mu."

"Saboda ta fad'a cikin ramin muguntarmu""..."

"Iya Delu tace ""ai ta gama fad'awa tunda ta yi yarda da mu "".."

"Inna Lanti tace ""kuma haka ne kam gsky ""...."

"Suka kama gulmar Inna Harira,, tare da zaginta da kuma tsine mata albarka. Har suka isa gidan su kowa"

"ya shige da yake mak'wabta ne,,,kusa ga juna..."

*******************

"Ayaune agidan Malam Adamu sukayi girke-girke,,,tare da siyo drinks kala-kala domin tarbon bak'insu"

"daga Birnin kebbi. Alhajin birni ne mai suna Alhaji Mahmud Umar Mai turare da k'annenshi Alhaji Haruna Umar,,, da abokanin sa guda biyu Alhaji Haruna da alhaji Yakubu. Sunzo sun faka manya - manyan motocinsu,,, daga babu tambaya kasan sun jik'u da naira kuma k'ushoshin gwamnati ko kuma manyan 'yan kasuwa,,, sun shiga har parlourn Adamu anyi musu tarba mai k'yau,,, cikin karamci da mutunci sun kintsa cikinsu babu tsangwama ko nuna k'yama irin na wasu masu kud'in. Bayan kamalla komai ne suka biya sadakin Aisha dubu arba'in,,, tare da sauran kud'in abubuwa na al'ada. Amma sadaki kawai suka amsa,, Adamu da Shehu mijin Habiba da wani Muktar. Sune suka d'unguma zuwa babbar"

"Masallaci aka d'aura auren Ahmad Mahmud Mai turare da Amaryarsa Aisha Aliyu,,, abisa sadaki naira"

"dubu arba'in .Hak'ik'a wannan ranar an tara mutane da dama,, duk da yake auren ya zama girshi babu"

"zato.Babu tsammani haka akayi taron aure lafiya,,, aka watse lafiya komai yayi k'yau da matuk'ar burgewa. Masha Allah komai yayi k'yau matuk'a,,, nima kaina abin yayi mini dad'i sosai ko ya Saude zataji,,, idan taji labarin an d'aura auren Aisha. Kunsan dai tanada burin ba Lado aurenta,,, gashi kuma"

anyi mata aure da wani wanda bamu sanshi ba. To ya abin zai kasancewa kuma wane ne ya auri Aisha......

_*Wane mataki Inna Saude zata d'auka ne?Sai ku biyo ni kujii *_

*Luv you my fans.*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 196-197

"Bayan an kammala d'aurin auren Ahmad Mahmud Umar Mai turare da amaryarsa Aisha Aliyu,,, wanda"

"ya tara jama'a duk da yake auren girshi ne. Babu zato babu tsammani kuma kowa ya watse ya kama gabansa,, saboda an gama lafiya k'alau babu fad'a balantana tashin hankali..."

"Abangaren Inna Saude tana cikin gida,, batasan abinda yake faruwa ba. Kuma mutane kamar had'in baki"

"Babu wanda ya kawo mata gulma ko tsegumi,, saboda idan baku manta ba kowa haushi take bashi,, saboda bata ragama kowa komai tsufanka tana iya yaga maka rigar mutunci. Tare yi ma mutum cin"

"mutunci na walak'anci,, ayanzu ma zaune suke suna fira ita Asiya.."

"Alokacin Asiya ta dubi uwar tace ""Inna wai ina Aisha take ne? Na ga ban ganta ba,, sannan ya maganar"

"had'ata aure da Lado abokin Abu ne. Ya kamata tun yanzu su fara fahimtar juna saboda aure ba wasa ba ne ""."

"Inna Saude tace ""Tana nan cikin d'aki tana goge mana kayanmu,, nina bata gogan kayanmu. Sannan"

"maganar aurenta da Lado zanyi ma Abu magana,,, domin ya sanar da Ladon "".."

"Asiya tace ""Da yafi kam gaskiya,, saboda kinga bata iya tsayi ga kanta. Musamman idan taga maza kamar"

"tsohuwar karyar da ta shekara bata yi iskanci ba ""..."

"Inna Saude tace ""Ni tsorona ma kada ta koma yin iskancinta,,, taje ta kwaso mana cikin shege kodayake"

"babu abinda ya dameni. Saboda ni ba uwarta ba ce Allah yasa tayo cikin shege d'ari,,, babu abinda ya dameni kuma bai shafeni ba ""..."

"Asiya tace ""ai shi ne na gani nima,, ni so na kema tayi cikin shege. Ko kunyar duniya da walank'ancin"

"mutane ta gani,, domin su mutane muggan munafukai ne ""..."

"Inna Saude tace ""haka ne kam gaskiyar maganarki,,, ni so nake tayi cikin shege. Saboda aduniya babu"

"wadda na tsana sama da ita,, da za'a bani wuk'a ace in kashe mak'iyina. Ita ce ta farko da zan fara kashewa,,,bak'ar karuwa annobar gari ""...."

"Asiya tace ""Ai bana mamakin lamarinta,, saboda da zafi zafi akan bugi k'arfe. Ki sanar Abu tunda wuri"

"domin ya sanar da Lado da wuri,,, domin aure ba abin wasa ba ne ""...."

"Inna Saude tace ""karki damu zan sanar da shi da kaina,,, saboda nima bana son Aisha ta samu wani mai"

"kud'i. Ta rayu cikin jin dad'i ko farin ciki,,,na fiso rayuwarta ta tabbata cikin k'unci da tarin damuwa har k'arshen rayuwarta ""..."

"Asiya tace ""haka ne nima na tsani Aisha,, kamar yadda na tsani mutuwata. Saboda ta fini komai na mata"

"sannan a makaranta ma,,, tayi mini fintinkau. Shi ke k'ara sa ni tsanarta ""..."

"""karki damu d'iyata muddin ina raye,, babu ke babu bak'in cikin rayuwa. Saboda haka kada wata"

"shegiyar karuwa annobar gari,, ta dame ki "".Cewar Inna Saude.."

"Asiya tace ""shiyasa na ke jin d'adi,, saboda samun uwa ta gari irinki. Hak'ik'a nayi dacen uwa wadda bata"

"son kukana ""."

"Inna Saude tace ""haka zakiyi ta jin d'adi saboda akan son da na ke miki babu abinda,, bazan iya yi akanki"

"ba domin farin cikinki "".."

"Asiya tace ""Godiya sosai na ke Innata ""...."

"Inna Saude tayi murmushi tace ""godema Allah ""."

"Haka dai suka cigaba da firarsu,, cike da tsananin farin ciki.Ita kuma Aisha tana cikin d'aki tana musu"

"gogar kayansu,, duk abinda suke fad'i tana jinsu har cikin d'akin Maganar ke zuwa hak'ik'a tayi kukan maraici da bak'in ciki,, domin a rayuwa ta rasa mi ta tarema su Inna Saude da Asiya. Da suka yi mata muguwar tsana irin haka,, taga ai ita ba itace da laifi ba domin ba ita ta had'a Inna Saude da Ummanta"

"Amina kishi ba. Wannan wa ce irin rayuwa ce wai,, mi mata suka d'auki kishiya wai? Ai kishiya 'yar uwa"

"ce ba abokiyar gaba ba. Dan Allah mu daina k'ok'arin hana abinda Allah ya halatta musu,, mu yi hak'uri"

"da juriya domin samun k'yakk'yawan sakamako a gobe k'iyama. Mu sa ni da cewa duniya ba wurin zama ba ne na din-din,, ko muna so ko bama so dole mubarta har abada..."

********************

*WANENE AHMAD UMAR MAI TURARE?*

"Asalinsa shine Baban shi Alhaji Mahmud Umar Mai turare,,, d'ane ga Umar Mai turare da Hafsa. Su biyu"

"kawai iyayensu suka haifa daga Mahmud sai Haruna k'annenshi,, Babansu asalin sana'ar shi shine saida turarurka da kayayyakin sawa domin shi d'an kasuwa na k'warai. Kuma yana da arzik'i sosai shi ma gado yayi ga Babansa,, Alhaji Haruna Umar da Mahmud Umar Mai turare kasuwanci shi ne jigon rayuwarsu,, sun gaji kud'i ne ga Babansu Umar Mai turare ya rasu a shekarun baya ya bar musu kud'i masu tarin yawa. Wad'anda ko su ba zasu iya k'idaya tarin kadarorinsa ba balantana tsabar kud'insa ba,,, ciki kuwa harda kamfanoninsa da gidajen man fetur da filaye,, gidaje, shagogi da gidajen noma da sauran abubuwan da ya mallaka. Hak'ik'a arzik'i na Allah yana basuwa ga wanda ya gadama,, aduk lokacin da ya so. Shi Alhaji Mahmud Umar Mai turare, matarsa d'aya mai suna Hajiya Mufida,, da kuma yaransu Ahmad shi ne babba sai Abdulrahman shi ke mai masa,,, sai k'anwarsu kuma autarsu Fatima. Su ukku ne"

ga iyayensu sun samu ilmi both boko da arabic...

"Alhaji Haruna Umar Mai turare,, shi ma matarshi d'aya mai suna Halira. Da yaransu Umar suna masa"

"lak'abi da Khalifa sai k'anwarshi Ummul khairi,, suma su samo tarbiya dai dai gwargwado da kuma ilmin zamani da na addini. Basuda wata matsala a rayuwarsu..."

"Atsakanin Ahmad da Khalifa duk kusan lokaci guda ne,, saboda babu wata tazara a tsakanin su. Haka a"

"tsakanin Fatima da Ummul khairi,, shi dai Abdulrahman shi ya fita daban a cikin su,, Ahmad da Khalifa duk a waje sukayi karatunsu a k'asar India,, Shi Ahmad Mahmud ya karanci medicine ne shi kuma Khalifa ya karanci Business.dukkansu sunyi karatu mai tsawo har digiri na biyu (Master degree).Kuma suna da k'yawon fuska saboda asalin ubannan su fulanin usuli ne,, suna zaune ne cikin jahar kebbi a unguwar gesse phase II. Haka ma gidajensu suna kusa da juna saboda son juna da tsananin zumuncinsu,, baka gane wa ne ne d'an wa ne a cikin su saboda basu nuna ma yaransu bambanci ko kad'an. Kowa yanada d'aki a gidan Babanshi ko k'anen Babanshi,, kan family a had'e yake babu gulmace gulmace ko munafurci, kowa sha'anin gabansa yake yi sannan kowa daga cikin su Ahmad da Khalifa suna kasuwanci,, sannan suna aikin gwamnati kud'i suna fito musu a ko'ina. Akwai shak'uwa da k'aunar juna a tsakaninsu komai tare suke yi harta yawo tare suke zuwa. Amma fa Khalifa yafi Ahmad yawan surutu da son tsokana,, Ahmad bai fiye shiga sha'anin da bai shafe shi ba saboda yanada miskilanci da rashin son yawan"

magana....

"Dr Ahmad Mahmud Mai turare yana aiki a Federal Medical Center Hospital da ke Birnin kebbi,, sannan"

yanada shagogi na kansa da yake yin business d'in shi.

"Shi ma Khalifa yana aiki a company su,, sannan yanada shagogi wanda yake yin business d'insa."

"Kowanensu ya mallaki gidan kashi da kuma gidaje masu yawa,,, ko motocin da suke hawa idan mutum ya gani yasan naira tayi kuka anan. Haka suke gudanar da rayuwar su cike da tsari da kuma had'in kai,, domin d'aya baiyin abu sai da shawarar d'aya. Idan ka ga yadda suke tafiyar da rayuwarsu sai sun baka"

sha'awa da burgewa. Saboda lamarinsu babu cutarwa da munafurci ko kad'an....

"Ahmad dai dogo ne fari k'yakk'yawan gaske,, na bugawa ga mujalla yana saje ga fuska wanda ya k'ara"

"k'awata k'yakk'yawar fuskarsa. Ga k'aramin bakinsa wanda ya ke d'auke da k'ananan hak'ora, bakinsa pink colour ne kamar mai shafa jambaki idan yayi murmushi. Wow! Masha Allah har da dimples d'insa suke bayyana,, gefen hagu da dama gashi da suma mai k'yawo tamkar balarabe saboda mugun k'yawonta. Tafiyarshi ma abar kallo ce baga mata ba har maza saboda shi mutum ne mai aji,, wanda yasan kanshi idan yana magana muryarshi tanada dad'in d'and'ano saboda ya iya magana mai d'adi sosai. Kai in tak'aice muku dai Ahmad duk inda namiji mai k'yawon sura da halitta ya kai,, shi ya wuce nan saboda gashi da k'yawon halitta gana zuciya domin kuwa family d'in gidan Mai turare akwai k'yauta da sanin darajar mutane. Musamman talakawa da makafi da guragu,, har dai Ahmad idan yayi maka k'yauta zama guda saika suma domin dad'i,, abin hannunshi bai rufe mishi ido ba saboda shi yanada sanyin hali"

da sauk'in kai. Baida rowa ko kad'an kuma kowa na shi ne....

"Aisha haka ta cigaba da fuskantar,, walak'anci da tsamgwamar Inna Saude babu abinda ta ke mata sai"

"k'ara azabtar da Aisha. Duk ya ke batasan an d'aura aurenta ba da wani,, amma harda sa Abu ya kira mata Lado wai in yana son Aisha,,, ta bashi daga nan zuwa su k'are makaranta. Ya shirya domin an yi musu aure Lado yayi matuk'ar farin cikin wannan tayi da ta yi masa na auren Aisha,,, domin kuwa yasan idan ya aureta ya dace kuma ya samu k'yakk'yawar mace abar nunawa ga gari. Yana zuwa fira wurin Aisha kusan kullum kullum kuma dole ta fita ta saurare shi,, ranar da duk ta kuskura bata fita jin kira na Lado ba,, Abu da Inna Saude suke kamata suyi mata mugun bugun da sai ta gaza ta shi. Bayan sun bata kashi kuma dole taje ta saurare shi da kukanta da komai ,,,sannan daga baya ta dawo tayi jinyar jikinta. Asiya na gefe idan banda dariyar mugunta babu abinda ta keyi mata,, itama har yanzu alak'arsu da Abu tana daram. Suna yin abinsu a b'oye babu wanda ya sani,, kullum suna tare da juna babu abinda ya ke"

rabasu sai rashin lafiya...

"Aisha haka ta ke daurewa tana kula Lado,, ba domin ranta ya so ba. Sannan suna makaranta"

"akodayaushe saboda sun kusa fara waec da neco. Amma yanzu irin matsin da su Inna Saude suke yi mata,, jin ta ke dama ba'a halicce ta duniya ba. Domin cin amana da zalunci ya k'aru fiye da lokuttan baya,, saboda yanzu rayuwarta kawai suke bid'a domin har gobe ana sallamawa ace ana kiran Aisha. Daga manyan masu hali sai masu rufin asiri,,, shi ne abinda ya ke k'ara sa zuciyarsu tafasa tare jin tsananin bak'in ciki da hassada. Basusan abinda Allah ya tsara ba,, babu wanda ya isa ya hana faruwar hakan kuma komai zakayi ka dinga sara kana dibin bakin gatarinka. Kada ka raina halittar Allah saboda bakasan baiwa da darajar da Allah yayi masa,, duk abinda zakayi ka shuka Alkhairi. Aisha ta cigaba da hak'uri da juriya akan lamarinsu Inna Saude,, tare da addu'ar Allah ya kawo mata k'arshen wannan"

masifa da bala'i da ta ke cikinsa....

"Idan ta keb'e tana yawan kai kukanta,,, ga Allah ubangijin talikkai da yaye mata abinda ke damunta da"

kuma faruwa da ita. Ya kuma mata k'arshen wannan masifa.

Nace Amin.

"Shiyasa akodayaushe ake son mutum,, ya kasance mai hak'uri da juriya saboda rayuwar nan da kuke gani"

"batada tabbas. Hak'ik'a duk zaluncin Saude da cin amanar da tayi zata girbi abinda ta shuka da hannunta. Saboda tun anan duniya Allah zai nuna mata abinta,, mata masu mugun *KISHIN JAHILCI* don Allah a"

kula kuma arage adinga kai zuciya nesa....

&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 198-199

"Sanadiyyar auren Ahmad Mahmud Mai turare da amaryarsa Aisha Aliyu,,, ya samo asali ne daga wurin"

"kakarsu ta wurin uba wato Hajiya Hafsat,, tana cikin gidansu amma bangarenta daban. Tun farko itace tasa su da su nemo duk budurwar da suke so matuk'ar tanada tarbiya,, zasu aureta shi da Khalifa. Da yake shi Khalifa yanada yarinyar da yake so nan da nan batare da b'ata lokaci ba,, ya sanar mata yanada yarinya mai suna Rabi'atu kuma sun jima suna soyayya. Hak'ik'a Hajiya Hafsa tayi matuk'ar murna sosai,, alokacin ne ta juya gefen Ahmad tana tambayarsa. Khalifa sai k'unshe dariya yakeyi saboda yasan"

"Ahmad baida yarinya,,, 'yan mata sun sha taronsa da kalmar soyayya ya k'yaleki ko kallo ba ki ishe sa ba."

"Ahmad yadubi Hajiya da yake haka suke kiranta,,, ya nuna mata shi baida budurwa sai dai idan ya samu"

"zaiyi auren. Hajiya ta kama fad'a tana cewa ya za'a yi yayi budurwa shi da ko sakin fuska bayada shi,,, to yanzu nufinsa ba zaiyi aure alhalin yanada kud'in da zai iya d'aukar lalurar mata hud'u,,, balantana guda ta nuna bazai tab'a yiyuwa ba Khalifa yayi aure shi bai yi ba. Zata yi magana da su Alhaji Haruna za'a bashi lokacin da zai fitar da matar aure,, idan wa'adin da ya cika bai nemo mata ba su zasu aura masa duk wadda suke ra'ayi khalifa ne ya bata hak'uri tare da nuna mata zasu nemo mata karta damu,, shi kuma Ahmad k'ala bai sake cewa ba saboda takaici wai ace kamarsa za'a yi ma auren dole,, Khalifa ne yayi mata sallama shi Ahmad wucewarsa kawai yayi akan takaicin maganarta. Hajiya Hafsa ta dad'e tana mamakin Ahmad tace ""yaro kamar mai shafuwar aljannu,, da anyi masa maganar aure sai ya b'ata rai yana fushi da mutane. Ni bansan mi ke damun Ahmad ba wannan karon bazan lamunta ba,, dama ansha yi masa maganar aure yana wani kakkaucewa shi adole ga mai wayo. Wannan karon ba zakayi muna wayo ba ko kayi kumburi kamar fulawa,,, saboda bazai tab'a yiyuwa ba mu sa maka idanu mu k'yale ka"

"ba,, sai abinda ranka ke so "".Haka dai Hajiya ta kama maganganu tana sababinta na tsofaffi...."

"Su kuwa su Ahmad suna fita,, sai gidansu Khalifa suka wuce direct. Suka shige cikin d'aki alokacin ne"

Khalifa ya dafa kafad'ar Ahmad...

"Yace masa ""Bro what is wrong with you? Miyasa ba zaka samu wata daga cikin masu sonka ba,,, ka fitar"

"da mata kowa ya huta da yi maka magana "".."

"""God forbid amma wlh Bro kana son k'ara b'ata min rai,,, mi zanyi da wad'annan 'yan matan da ba"

"domin Allah suke son mutum ba masu shegen kwad'ayi da son abin duniya "".Cewar Ahmad.."

"Khalifa yace ""I'm sorry Bro wannan ba abin damuwa ba ne,, da zakayi fushi duk macen da kace kana so"

"bazata k'i ba. So don't worry yourself my Bro,saboda zaka iya auren duk irin macen da kake so do you understand me? ""..."

"""I understand you khafila i'm falling hungry,, let me go and get something to eat ""Cewar Ahmad.."

"Khalifa yayi murmushi yace ""kaji acici ba baka son yi aure,, amma baka wasa da cikinka i'm waiting for"

"you Bro don't leave me alone ""..."

"Ahmad yace ""OK don't worry i'm coming back now,, kuma kaje kayi taking bath kafin na dawo "".."

"Khalifa ya hararesa da wasa yace ""if not mi zakayi? Banson iya yi ba ruwanka ko banyi wanka ba,, kaje"

"dai ka dawo ina jiranka "".."

"Ahmad ya tashi tsaye yace karka yi mana nothing concern me,, kama zauna da dirty ""..Ya kama hanyar"

fita d'akin yaja handle k'ofa ya fita...

"Khalifa kuma murmushi kawai yayi,, tare da tashi ya d'auki towel d'insa ya shige toilet domin yayi"

wanka....

**********************

"Abangaren Hajiya Hafsa bayan anyi kwana biyu da faruwar wannan al'amarin,,, tasa Alhaji Mahmud ya"

"kira mata Haruna da kuma matansu. Suka tattauna akan maganar Ahmad da Khalifa na batun aurensu,,"

"alokacin ne ta sanar da su Khalifa ya tsaida mata shi kuma Ahmad baida ko budurwa,,, saboda haka ta gaji da ganin su babu aure. Domin kowane daga cikinsu yanada abinda zai iya d'aukar lalurar matarsa,,"

"kuma sun san da cewa ba tun yau ake bin Ahmad ya fitar da matar aure ba,,, yana musu yawo da hankali."

"Mahmud da Haruna sun bata hak'uri tare da cewa zasu je har gidansu Rabi'atu domin nema ma Khalifa aurenta,, shi kuma Ahmad zasu bashi lokaci daga nan zuwa bayan auren Khalifa. Idan yaso idan bai fitar da mata ba zasu nemo masa da kansu karta damu,, su dai iyayen mata babu abinda suka ce illah nuna amincewarsu da wannan shawara. Hajiya taji dad'i sosai matuk'a tare da sanya musu albarka da kuma nasiha,, tare da k'ara nuna musu su rik'e zumuncinsu karsu bari wani yaga fili balle ya shiga a tsakanin su. Haka dai ta cigaba da basu shawarwari akan zamantakewar rayuwa har daga baya kowa ya kama"

gabansa.

"Bayan wata d'aya da faruwar wannan lamari ,,har Alhaji Mahmud yaje tare da abokanin sa nema ma"

"Khalifa aure gidansu Rabi'atu. Sunje anyi musu tarba ta mutunci da karamci,, tare da sa musu sadaki kuma

Please Login or Register in order to submit comment