You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rad'ad'i,, suke fitowa daga cikin idanunta tace ""Babu komai haka Allah"

"ya k'addara,, shiyasa na ke gaya maki ina yawan mafarkin wani nawa yana cikin uk'ubar rayuwa. Amma sai gashi an shiga tsakanin mu balantana taji sanyin maraicin uwa,, Insha Allah babu damuwa Allah zai yi mata sakayya tun anan duniya. Sannan zan sanar da Babansu Jamil abinda ake ciki domin inyi ma d'iyata"

"sayayya ta gani ta fad'a,, yaushe ne zata tare ne? ""..."

"""Suna gama makaranta suka ce,, saboda kinsan ba'a son Saude ta san halin da ake ciki. Saboda tana iya"

"wargaza komai ba imani ne da su ba ""Cewar Maman Amina cike da zullumi.."

"Hadiza tace ""kwantar da hankalinki Mama,, idan Allah ya yarda ba zata sani ba. Komai tayi itada Allah"

"saboda gaskiya ba zan tab'a yafe mata rabani da tayi da d'iyar Auntyna (Allah ubangiji ya jik'an ki da rahama). Ta cuce mu k'warai da gaske "".."

"Maman Amina tace ""itada da Allah mu barta ga Rabbis samawati "".."

"""Wallahi kam "".Cewar Hadiza.Suka cigaba da firar abubuwan da ya kamata,, su saye kafin Aisha ta tare"

gidan mijinta. Sannan kuma da mamakin rashin mutunci da imani irin na Saude....

********************

"Adamu ne zaune da matarsa Hussaina,, tare da yaransu ukku na farko Amir ya zama d'an saurayi,, na"

biyu Amira ce sai d'an autarsu Sa'id...

"Hussaina tace ""Baban Amir ai ni ba k'aramin dad'i naji ba,,,da aka d'aura auren Aisha. Saboda yarinyar"

"taga jarabawar rayuwa "".."

"Adamu yace ""ni kaina nayi matuk'ar farin ciki da murna sosai,, da mahaifinta ya amince batare da"

"gardama ba. Ai Saude ta yi abinda takai a duniya,, mace babu imani babu tausayi "".."

"Hussaina tace ""wannan mata anyi shed'aniyar mace,, mu kanmu sai da ta shiga tsakanin mu da Aisha."

"Anya kuwa batada sa hannu akan mutuwar Amina?Saboda ko ciwon da tayi ba irin na mutane ba ne "".."

"Adamu ya dubi Hussaina yace mata ""zato dai zunubi koda ya zamo gaskiya,, sannan idan ma da sa"

"hannunta komai daren dad'ewa gaskiya zata yi halinta. Kuma asirinta sai ya tonu "".."

"""Wannan gaskiya ne Baban Amir,, Allah ubangiji ya k'ara karemu daga muyagun k'addarori "".Cewar"

Hussaina..

"Adamu yace ""Amin amin,, tashi yanzu ki d'ora mana abincin rana kada lokaci ya k'ure "".."

"""To Maigida "".Hussaina tace tare da mik'ewa zuwa aza sanwar abincin rana.."

**********************

Su Abu ne zaune suna firar duniya..

"Alokacin ne Lado ya kalle su,, yace ""kunji maganar da ke yawo agari kuwa? ""."

"Tanko yace ""ya za'a yi mu sani,, sai ka fad'a muji daga bakinka "".."

"Abu yace ""bar shege yasan duk bamu jiya ba,, shiyasa ya ke mana tambayar rainin wayo "".."

"Lado yace ""dad'i na da Abu akwai ka da iya bak'ar magana,, to tsaya kuji wallahi Aisha an d'aura mata"

"aure da wani saurayin birni. Saboda haka ni dai bana k'ara zuwa wurin matar wani,, kada yaji labari yasa 'yan sanda su kamani a banza da yofi "".."

"Tanko yace ""Ai ta huta da cin amanar bak'ar munafuka kuma azzaluma Saude,, saboda gaskiya matar"

"nan tana gana mata azaba tare da nuna mata alamar ba ita ta haife ta ba "".."

"""Ai wannan ba wani matsala ba ne,, abinda ya kamata kawai ka d'an rage kulata. Ko shi abinda zaisa ka"

"dinga kulata akai akai,, saboda kada Inna Saude ta gano anyi mata aure. Wallahi kam in ta gano sai ta"

"wargaza musu aure,, ta bani tausayi ne shiyasa bana son ta sake shiga k'uncin rayuwa. So na ke Saude ta fara girbar abinda ta shuka da hannunta "".Cewar Abu cike da shed'anci da rashin kunya..."

"Lado yace ""Eh fa haka ne gaskiya abokina,,amma kanada hangen nesa da sanin ya kamata "".."

"Tanko yace ""Abu kayi bakada matsala,, maganarka haka take ya kamata Aisha ta d'an huta da azabar"

"Saude. Taji dad'i itama ko ya ya ke a rayuwarta,, yarinyar akwaita da hak'uri da juriya ga girmama na gaba "".."

"Abu yace ""Maganarka Tanko haka ta ke,, Allah dai ya kawo ranar tonuwar asirin su Saude. Su walak'anta"

"da tozarta a cikin duniya,, saboda sunyi abubuwa marasa k'yau a duniya da walak'anta mutane "".."

"Lado yace ""Amin amin wlh zalunci irin na wasu baiyi ba,, musamman masu yin shirka da tsafi ""."

"""Haka ne kam gaskiya "".Cewar Tanko,, suka yi ta firarsu cike da walwala da annashuwa..."

**********************

"A birnin kebbi gidansu Khalifa,, Ahmad da Khalifa zaune suna fira...."

"Khalifa yace ""Ahmad ya kamata muje muga matarka,, acan Kamba saboda da akayi aurenku kana"

"England to gashi ka dawo "".."

"Ahmad yace ""you are disturbing my life i don't have time for seeing anybody,,, ka gane ko. To wai ma"

"miye matsalarka idan ba muje ganinta ba ""."

"Khalifa yace ""is not good for you guy,, ace an aura maka yarinya ko sau d'aya baka tab'a zuwa wurinta ba."

"Ko kana fushi ne da auren da iyayenmu suka yi maka,,ko you are not in love with her? ""."

.

"Ahmad tace ""i don't said that ka gane ko,, kuma ya za'a yi na guji zab'i iyayena. Ko da ace bana sonta"

"zanbi umurni iyayenmu,, so don't worry yourself i can't even managed with her ""..."

"Khalifa yace ""managed kuma.To naji bro which time are we going to see her?""."

"Ahmad yace ""kasa mana lokacin da kanka mana bro,, you are talking too much "".."

Khalifa yace I'm talkative(mai yawan

"magana),, to babu damuwa yaushe zaka je cin abincin amaryata Rabi'atu? "".."

"""idan banje ba what are you going to do? Dole ne saina je kaifa ka takurama rayuwata "".Cewar Ahmad"

cike da gajiya da surutun Khalifa...

"Khalifa yace ""is not by force but you must go fa,, kai fa Ahmad wata rana bakada kirki wlh kuwa. Gidan"

"nawa ne baka son zuwa saboda raini ko "".. ."

"Ahmad yace ""sorry bro don't angry with me,, wlh zanje wasa kawai na ke maka. Gidanka ma zan fara"

"zuwa before muje wurin yarinyar nan ""..."

"Khalifa ya hararesa da wasa yace ""yarinya ko matarka kuma bro ?"".."

"""Oh I forgot, i mean my lovely wifeey,, ina jin ta har cikin zuciyata da rayuwata "".Cewar Ahmad cike da"

zolayar Khalifa..

"Khalifa yace ""ta so muje gida nayi mantuwa ka rakani "".."

"Ahmad yace ""OK no problem "".Ya tashi tsaye suka jera tare da junansu.."

"Suna zuwa parking space,, suka shiga cikin wata mota had'add'a mai k'yau .Khalifa ya tuk'asu suna tafiya"

"suna fira cike da nishad'i da shak'uwa,, sun d'an jima kad'an suna tafiya sannan suka kawo bakin get d'in gidan Khalifa. Suka yi horn Maigadi Hassan yazo da sauri,,, ya bud'e musu get suka kunna kan motarsu sai cikin gidan,, suna shiga cikin parlorn subhanalillah!! Sai da naji tsoro saboda gidan gaskiya ya had'u ba k'arya,,, masu kud'i suna jin dad'insu. Domin yadda aka tsara ginin gidan kamar ba za'a mutu ba,,, agefe akwai swimming pool da ruwa masu sanyi a cikinsa. Ga kuma gardener komai zaka iya samu a cikinta fannin fruit kala kala,, bari mu dakata hakanan saboda idan nace zanyi bayanin komi na gidan saimu"

dad'e bamu gama ba...

"A parlorn ma komai yayi k'yau matuk'a,, sai da suka yi sallama sannan Ahmad ya samu wuri saman"

"kujera ya zauna. Shi kuma Khalifa ya koma hanyar bedroom d'insu yana cewa ""My luv where are you I'm coming back to you now, I will like to see your cute face before anything else ""..Ya shige cikin d'akin."

"Ahmad yayi tsaki yace ""wawa so yana son maida shi mahaukaci "".Ya kunna tashar arewa 24 yana"

kallonsa...

"Khalifa ya shiga d'aki Rabi'atu ta rungume shi,, tana masa sannu da zuwa. Khalifa ya dubeta taci kwalliya"

"cikin atamfarta light blue and brown,, tayi matuk'ar k'yau saboda tanada k'yawo dai dai gwargwado..."

"Rabi'atu tace ""muje kayi wanka sannan mu dawo ka ci abinci "".."

"Khalifa yace mata ""ba ni kad'ai na ke ba my luv,, ni da bro Ahmad ne. Kuma kinsan zai iya cewa an k'yale"

"shi ""..."

"Rabi'atu tace ""babu matsala muje in gaisa da shi ""..."

"""Thank you my love "".Cewar Khalifa.."

"Ta d'auko gyalenta babba ta yafa,, mai kalar light blue and white. Suka jera tare har cikin parlorn,, bayan"

"sun shiga ne Rabi'atu ta gaida Ahmad cikin girmamawa da ladabi. Ya amsa mata cikin sakin fuska,, taje ta"

"kawo musu abinci da lemun kwali da kuma danbun kifi. Tana ajewa ta d'auko musu kofi da swan water masu sanyi ta aje,,, sannan ta basu wuri domin suji dad'in sakewa suci abincin.."

"Ahmad da Khalifa sukayi bismillah tare,, sannan suka fara cin abinci cike da natsuwa da kwanciyar"

"hankali. Babu abinda kakeji idan ba k'arar chokali ba,, bayan sun kammala ne suka sha ruwa tare da yin hamdalah.."

"Ahmad yace ""Masha Allah bro matarka ta iya abinci mai dad'i sosai,, kayi dacen mace ta gari ""..."

"Khalifa yayi murmushi yace ""Godiya na ke sosai tunda yau ba'a kushe mu ba,, kaima zakayi dacen mace"

"ta gari mai tarbiya karka damu bro ""."

"""Allah ya sa "".Cewar Ahmad.."

"Khalifa yace ""Amin "".Suka cigaba da firarsu cike da shawarwari na al'amarin rayuwa,, da kuma"

"zamantakewar su ta yau da kullum. Sun dad'e suna fira sannan Ahmad yace zai wuce gida,, Khalifa ya kira amaryarsa Rabi'atu suka k'ara gaisawa. Tare da yi mishi agaida mutanen gida,, Ahmad yaji dad'i sosai tare da bata k'yautar naira dubu d'ari biyu. Rabi'atu ta k'i amsa sai da Khalifa ya saka baki sannan ta amsa,, yayi mata sallamar zuwa gida suka wuce direct wurin parking space. Khalifa yayi ma Ahmad sai da safe sannan ya juya zuwa cikin gida,, Ahmad ya shiga motarsa tare da danna horn Mai gadi ya b'ude"

masa get. Shi ma mai gadi ya bashi k'yautar naira dubu goma sannan ya wuce zuwa gida.

"Hassan Mai gadi ya dad'e tsaye yana Ahmad,, godiya tare da yi masa addu'ar gamawa lafiya da duniya,,"

"saboda yayi matuk'ar farin ciki da murna da kud'in da ya bashi. Hak'ik'a haka ake son mutum mai yawan k'yauta muddin yanada abin basuwa,, sai ka ga wasu ko gasu da abu suna jin bak'in cikin bawa wani,, sai"

dai abun ya lalace a banza saboda matuk'ar rowa da mak'o...

"Ita dama haka duniya ta ke idan wani ya k'i ka,, wani zai soka a rayuwar duniya."

_Mai hak'uri yakan dafa dutse har ya sha romonsa.._

"_*Ni Mugirat addu'ar ku na ke buk'ata,, akodayaushe my fans. *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_Hak'ik'a *Ummu Afan* marubuciyar *Akwai lokaci*,, ban manta da soyayarki da kulawarki a gare ni ba,,"

ki sani ina matuk'ar k'aunar ki fiye da tunaninki. Wannan shafin sadaukarwa ne gare ki my sister._



*PAGE* 204-205

"Aisha da Asiya sun fara waec d'insu lafiya,,, har sun kusa gamawa Asiya da su Kubra basu karantu. Babu"

"abinda suke yi sai biyar maza da malamai 'yan iska irinsu masu yin zina,,, Aisha kuma da su Asma'u,,, Zainab babu abinda suke yi illa karatu babu kama hannun yaro. Haka al'amarin nasu ya cigaba tafiya cike"

da kwanciyar hankali da maida hankalinsu ga karatu.....

"Abu da su Lado kuwa babu abinda suke yi,,, sai kwana da su Kubra kamar matansu na aure. Kullum suna"

"manne da yaran mutane,,, a rana guda suna kwanci da su sau uku a yini,,, babu gajiya ko gundura.. Shi Lado ma yana d'an kula Aisha amma ba kamar da ba,,, ko shi saboda kada Inna Saude ta gano an yima Aisha aure,,, shiyasa yake d'an kulata gudun Saude kada ta gano wani abu dangane da aurenta. Inna Saude tana k'ara jaddada ma Lado cewa ya cigaba da shirye shiryen aurenshi da Aisha,, babanta ya ce tana gama makaranta da wata biyu za'a yi aurensu. Lado ya kanyi mata godiya tare yi mata alkhairi,, na kud'i ko abubuwan more rayuwa,,, Inna Saude ta yi masa godiya babu iyaka tare da washe rub'ebb'en bakinta,, mai shegen wari da d'oyi Malam Aliyu shi ma kansa tana yawan damunshi da maganar"

"auren Aisha da Lado,,, ya kan bata hak'uri tare da nuna mata ta bari har lokaci yayi,, za'a yi aurensu wato"

"idan ta gama makaranta bayan wata biyu. Inna Saude tana washe bakinta cike da jin d'adi da murna,,"

"saboda burinta ya kusa cika na ganin Aisha ta k'ara shiga cikin k'uncin rayuwa da wahala,, bak'in ciki,,"

"tozarci. Babu abinda ta tsana a rayuwarta irin masu nuna suna son Aisha ko tausayinta idan ka nuna kana yi to Saude zata tsaneka a rayuwarta. Ni kaina ina mamakin wannan irin hali na Inna Saude,, su dai a rayuwarsu da su da mahaifiyarsu babu abinda suka tsana idan ba kishiya ba, ,, da kuma yaran kishiya. Kishi a k'asar hausa mata sun mayar da shi kamar wani ibada ko abin ado da tink'aho,, mata da yawa daga cikin mu basu yarda da k'addara ba,, basu yarda da abinda Allah ubangiji ya halatta ma maza shi ba. Babu wanda ya isa ya haramta shi ba duk duniyar nan ana son komai zakayi,,, ka yi tunani da nazari kafin ka aikata shi,, idan zakayi abu ka dinga sara kana dibin bakin gatarinka. Komai masifarki,, bala'inki,, jidalinki da son azama miji fad'a da masifa,, baki isa ki gujema k'addararki ba na ya k'ara aure. Duk biyar bokaye, malamai, 'yan tsibbu,, basu isa su hana mijinki k'ara aure ba. Sai dai imaninki da kud'inki su k'are a banza,,, kuma da kin mutu a wannan lokacin wutar jahannama ce direct makomarki. Kinga anan bakiji dad'in duniya ba kuma lahirar ba zakiji dad'in ta ba,, Allah ubangiji ina rok'on ka kasa mata su gyara zamantakewarsu tsakaninsu da kishiyoyinsu,, ya kuma k'ara mana juriya da hak'urin zama da kowane"

irin mutane a rayuwarmu .

********************

"Acan gidansu Abbas kuwa,,, Abbas ne zaune da Asma'u suna fira cike da nishad'i da jin d'adi sosai..."

"Asma'u ta dubi Yaya Abbas tace ""Yaya Abbas kaji wani labari kuma wai? ""."

"Abbas yace ""Na'am k'anwatah sai kin fad'a mana "".."

"Asma'u tace ""Anyi ma Aisha aure tun kwanakin baya da suka wuce,,, saboda ta samu sa'ida da sauk'i a"

"rayuwa. Saboda haka miye gudunmuwarka ga Aisha ta? "".."

"Abbas ya yi huci mai zafi,, da k'unar zuciya yace ""Allah sarki duniya kenan a rayuwata,, ban tab'a zaton"

"ba nine zan kasance miji ga Aisha ba. Amma yanzu k'addara ta riga fata kuma k'addara ce ta rabamu. Ta sanadiyyar Saude ita ce silar rabani da farin cikin rayuwata,, abar begena dare da rana ""..Yace alokacin"

ne hawayen bak'in ciki da k'uncin rayuwa suka fito masa..

"""Subhanalillah!! Yaya dan Allah ka yi hak'uri da k'addararku,, banyi tsammanin wannan maganar zai"

"sanyaka hawaye da bak'in ciki ba. Bazan sake ba yaya domin damuwarka itace damuwata,, sannan farin cikin ka shi ne nawa. Bana son ganin hawayen jarumin Yayana,, amma ina son ka k'ara hak'uri da yadda da k'addara ce ta raba ku ba Inna Saude,, saboda idan Allah bai k'addara rabuwarku ba,, bawa yayi kad'an ya rabaku a rayuwa. Allah ya riga ya hukunta ba matarka ba ce tun ran gini ran zane,, kuma matar mutum kabarinsa. Ako'ina ta ke a fad'in duniya sai ya aureta Yayana,, Allah ubangiji ya huci zuciyarka ya k'ara sanyaya maka zuciya,, ya kuma musanya maka da mafi Alkhairi a rayuwarka "".Cewar Asma'u cike da tsananin tausayin yayanta,, tare da sa handkchief tana goge masa hawayensa cike da k'aunar"

yayanta..

"Abbas yace ""Amin amin k'anwatah,, nagode matuk'a da addu'arki gareni. Ki sani na yarda da k'addara ta"

"kuma nasan shi ne mafi alkhairi a rayuwata,, amma ki sani shi so farat d'aya ya ke shiga,, fitar da shi a cikin zuciya alokaci guda bazai tab'a yiyuwa ba. Da kad'an kad'an zai fara fita sannan mutum ya dage da addu'ar Allah ya fitar masa da shi a cikin zuciyarsa. Har ya zamana babu ko kad'an a cikin zuciyar mutum"

"""..."

"Asma'u tace ""haka ne gaskiya kam,, to ya zamuyi sai hak'uri. Lamarin duniyar nan sai mutum ya kai"

"zuciyarsa nesa da kuma hak'uri da dangana a rayuwa "".."

"Abbas yace ""tabbas maganarki haka yake k'anwatah,, saboda haka idan lokacin tarewarta ya kusa."

"Please let me know i will try my best Insha Allah,, kin gane ko true love na ke yi ma Aisha,, ba wai na k'arya ba but she is my lovely sister ""..."

"Asma'u tace ""Insha Allah my big brother i will tell you if d time coming,, don't worry about that you are d"

"one that make me happy on d earth. Kuma ka sani kai abin alfahari ne ko acikin yanne,, kuma muna godiya sosai tare da soyayyarka gare mu. Allah ubangiji ya saka maka da mafificin Alkhairi ya kuma k'ara"

"bud'i na alkhairi ""...."

"Abbas yace ""thank you I'm really appreciate it,, karki damu k'anwatah babu abinda na ke k'auna da so"

"sama da ke. Saboda haka komai zan iya miki to make you happy,, bloody sister i luv u for ever in my life "".."

"Asma'u ta yi murmushi cikin jin dad'i,, tace ""luv you too my big brother you are the best. Kuma nima ina"

"matuk'ar ji da kai a rayuwata,, Allah ya baka mata ta gari musha bidiri "".."

"Abbas yace ""Amin amin k'anwatah ta kaina "".."

"Haka dai suka cigaba da firarsu,, cike da son juna da tsananin shak'uwa a tsakanin su...."

*******************

"Inna Saude ce ta dubi Asiya,, tace ""Asiya "".."

"""Na'am Inna "".Cewar Asiya."

"Inna Saude tace ""Naga fa kwanakin nan kin cika yawo Asiya,,, sannan naga kin k'ara cika da bud'ewa"

"kamar babbar mace mai aure. Mi kike ci wai shin Asiya da kika zama haka? ""..."

"""Haba Inna wannan wane irin tambayoyi ne haka,, kamar wadda aka ce miki yawon iskanci yake yi,, ko"

"ya ke zuwa inda mutum bai dace ba. Ni fa bana son irin hakanan rayuwata b'aci ta ke sosai Inna,, dama nasan kin daina sona kuma baki yarda da ni ba. Da akwai yarda da ba zaki yimin wad'annan tambayoyin ba,, ko anfara kawo miki tsegumi da anyi ance ne? Ni fa gaskiya ki daina min irin haka bana son hakanan"

"wallahi "".Cewar Asiya cike da tsananin b'acin rai da takaicin Innarta.."

"Inna Saude da taga rayuwar Asiya,,, tayi matuk'ar b'aci sosai. Sai ta k'ara sassauta muryarta tare da"

gyara kalamanta sosai...

"Tace ""Haba Asiyata kiyi hak'uri 'yar leleta,, ni fa ba haka nake nufi ba. Kawai tambaya ce nayi saboda"

"insan inda kike zuwa domin wata rana,, amma tunda kinga kamar ina zarginki.. Allah ubangiji ya baki hak'uri ya kuma huci zuciyarki Asy babyna,, 'ya guda tamkar dubu a gare ni ""..Tace saboda tana tsoron"

"kada Asiya ta samo kud'i ta hana mata wurin samarinta,, da kuma k'wartayenta ."

"Asiya ta jama uwar mugun tsoki ""mtsssss "".Sannan tace ""maganar banza da yofi sai an b'ata ma mutum"

"rayuwa,,, sannan daga baya azo ana wani kanikancin munafurci. To bari kiji idan kika matsamin wlh Inna"

"zan bar miki gidan,,, in shiga yawon duniya saboda ni na tsani shegen sa idon nan da kike yima Aisha,, tana hak'uri ni bazan iya ba gaskiya "".."

Inna Saude tayi matuk'ar tsorata d al'amarin Asiya ..

"Sannan tace ""haba dai koni 'yar Inna kiyi hak'uri,, wlh na tuba bana sakewa. Duk abinda zakiyi bazan"

"k'ara yi miki magana ba,, koma miye kike yi balantana ni Bana zarginki da komai sai alkhairi,, kuma nasan ba zaki tab'a bani kunya ba 'yata ta kaina farin cikin rayuwata ""...."

"Asiya ta harari Inna Saude,, tace ""naji fad'i sauran gani kuma wlh idan kika kuskura kika k'ara,,sai kinga"

"hukunci da zanyi miki gaskiya na ke gaya miki Inna ""..."

"Inna Saude tace cike da tsoro ""bazan k'ara ba ma wlh Asiya ta,, ki gafarce ni kinji 'yata ""..."

"""Naji "".Cewar Asiya cike da tsananin takaicin Inna Saude,, ta shuri takalminta cike da b'acin rai da"

"damuwa. Ta bar Inna Saude cike da tsananin tsoron fushin Asiya da kuma damuwarta,, amma a cikin zuciyarta ta yanke shawarar zata lallasheta,,, koda zuwa anjima ne har ta huce. Saboda bata son b'acin"

ran Asiya ko kad'an a rayuwarta..

********************

"****Washe gari da safe misalin k'arfe 10:30am na safe,, bayan Aisha ta kamalla duk ayyukan ta na gida"

"da safe. Da yake ranar lahadi ce sai tayi wankanta mai k'yau da tsari,, ta shirya cikin lace d'inta mai milk and light pink colour. Tana cikin fesa turare saiga kiran wayarta ya shigo,, a fuskar wayar suna ya fito wato Baba Adamu,, tayi receiving call. Ta gaida shi ya amsa mata,, bayan sun gama gaisawa ne ya ke sanar da ita yanzu yanzun nan tazo gidanshi,, mijinta zai zo gidanshi yau saboda su gana da juna. Sai da gabanta ya fad'i domin batasan wane irin tarba mijinta zai mata ba,, ta dai amsa ma da baba Adamu to domin ba zata iya musa mishi ba,, suka yi sallama ya katse wayar. Ita kuma bayan ta gama fesa turarenta ta d'auko hijabinta kalar milk tasa haka ma takalminta da jikkarta duk kala d'aya ne. Ta kulle d'akinta sannan ta nufi d'akin Inna Saude tace mata zata fita gidan wata k'awarta,, Inna Saude ta harareta da k'yau,, domin ko mak'iyin Aisha ya ganta yasan ta had'u ba k'arya. Inna Saude ta nuna mata babu komai Allah ya kiyaye hanya,, saboda ita azatonta duk yawon karuwanci Aisha zata je. Batasan duk wanda Allah ya tsare ba ya tsaru har abada ba,, Aisha ta sa kai tayi fitowarta tana fitowa .Ta yi tafiyar a k'afa saboda daga nan zuwa gidan baba Adamu babu nisa gaskiya,,, maza sai kallonta suke saboda tsananin k'yawon"

ta da kuma dirin da Allah ya bata..

"Aisha ta yi sallama,, aka amsa mata sannan ta shiga cikin gidan direct. Tana zuwa ta iske Mama Hussaina"

"zaune tana kallo,, yayinda Amira ke jera abinci kala kala da drinks saman dinning table. Aisha ta duk'a har k'asa ta gaida Mama Hussaina,, Maman ta amsa mata fuskarta cike da fara'a da murna,, Amira da Sa'id suma suka gaisheta tare da zama kusa gareta. Aisha ta amsa musu cikin sakin fuska da farin ciki,, suka zauna suna tayi mata surutu da hira,, wani ta amsa musu,, wani kawai tayi murmushi akan"

shirmensu..

"Suna tsakar fira sai ga sallamar baba Adamu,, suka amsa mishi Sa'id ya shek'a da gudu yayi masa oyoyo"

"oyoyo. Baban ya d'aukeshi tare da bashi cholate ya amsa yana jin dad'i sosai,, yana zuwa ya zauna kusa ga Mama Hussaina,, Aisha ta gaida shi cike da ladabi da girmamawa. Ya amsa mata cikin sakin fuska da walwala.."

"Baba Adamu yace mata ""ta k'ara kimtsa kanta su Ahmad suna kan hanyar zuwa ""."

"Tace masa ""to"".Cike da kunya da biyayya."

"Aisha da Amira da Sa'id suka shige cikin d'aki,, suna ta bata labarai masu dad'i da ban dariya. Aisha babu"

abinda ta ke yi idan ba murmushi ba..

"Acan palourn baba Adamu da Matarsa Hussaina,, babu abinda suke yi suma sai firarsu cike da tsananin"

"nishad'i da walwala. Suna tsakar fira ne sai sukaji k'arar mota baba ya umurci Mama Hussaina da ta shige cikin d'akinta,, kafin yayi musu iso sannan su gaisa,, tace masa to tayi wucewarta zuwa cikin d'akinta. Shi kuma ya fita waje su Khalifa suka fito daga cikin motarsu suka gaisa da shi ,,, tare da yin musabaha cike da tsananin girmamawa da ladabi,, yayi musu umurni da su shigo daga ciki. Suka shiga daga cikin parlorn tare da zama saman kujeru,, kowane daga cikinsu yayi shigar mutunci da kamala. Khalifa yayi shigar shadda light blue da hularsa da takalminsa,, shi kuma Ahmad yadinsa milk yasa anyi masa aiki da zare dark brown,, hularsa da takalminsa duk kalarsu d'aya. Baba Adamu ne ya gabatar musu da kayan motsa baki,, dukkansu sun d'an ci abincin batare da nuna k'yama ko tsangwama irin na masu kud'i ba. Suna"

"gamawa ya shiga cikin d'aki ya turo musu Aisha,, koda ta shigo parlorn da sallama Khalifa ya amsa mata,,"

ta gaishe su cike da girmamawa. Khalifa ya d'ago kansa ya kalleta yace wow! masha Allah she is very

"beautiful,,hak'ik'a Allah yayi halitta mai k'yau a nan. A cikin zuciyarsa sannan ya amsa mata gaisuwarta,,, shi kuma gogan ko kallonta bai yi ba danne dannen wayarsa kawai yake yi.."

"Khalifa yayi gyaran murya sannan yace ""Malama Aisha ina son ki bamu aron hankalinki,,, domin mu"

"tattauna akan wata muhimmiyar magana da mu da ke ""."

"Tace ""Ina saurarenku ba matsala "".+Tace cikin kunya da natsuwa.."

"Khalifah yace mata ""ni dai da farko sunana Umar amma gidanmu,, ana kirana da Khalifa saboda sunan"

"kakanmu da nakeda shi. Wannan kuma (ya nuna Ahmad) sunan shi Ahmad shi ne mijinki kuma abokin rayuwarki,, yanzu zan sanar da ke d'an tak'aitaccen tarihinmu Ya bata labarinsu kamar yadda na"

"baku a can baya babu abinda ya b'oye mata dangane da su,, ya kuma k'ara musu da nasiha da suyi hak'uri da juriya da juna. Domin zaman aure ba zaman wasa ba ne kuma aure amana ne duk wanda ya ci amanar wani sai amana ta ci shi,, hak'ik'a yayi musu nasihohi da wa'azi mai ratsa zuciyar mai saurare. Ya kawo musu hadissai da ayoyin qur'ani mai girma,, ya kuma nuna musu muhimmanci

Please Login or Register in order to submit comment