You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma rayuwata ce ta b'aci sosai shiyasa "".Cewar Aliyu.."

"Saude ta shafi gashin kan Aliyu,, cike da makirci da kissa.. Tace ""na sani mijina kasan ina matuk'ar"

"k'aunar ka,,, amma dan Allah ka dinga kai zuciyarka nesa,, kaji Aliyuna""..Cike da shagwab'a tayi maganar..."

"""karki damu Saudatu, nima ina son ki kuma Insha Allah zan dinga kiyayewa matata ""..Aliyu yace......."

"Saude tace ""Godiya na ke mijinah "".Ta saka harshenta cikin bakinsa,, shi ma ya kama.. Suka lula duniyar"

ma'aurata....

"Aranar sun gurji juna,, kamar sabbin ma'aurata da k'yar suka daina.... .."

*******************

"Abu kuwa yana cikin gari,,, har yayi sabon aboki mai Tanko tare suke cin d'iyan mutane tare da yi musu"

"fyad'e.. Ana ma ya samu waya ya kira Lado akan ya dawo garin Kamba,,, saboda sunfi mata masu k'yau da manyan kaya.."

"Lado ya nuna masa babu komai,, zai dawo Kamba.. Ya dubi hanyar shi nan da kwana biyu idan ya shirya"

zai dawo Kamba..

"Tanko ya dubi Abu yace ""Dan and Allah mi k'omin wayata,, kada ka cinye min kati "".."

"Abu ya harare sa yace ""kaine matsiyaci mara kud'i ba ni ba "". Ya mik'a masa wayarsa..."

"""Naji dai sannu k'aruna uban kud'i "".Cewar Tanko bayan ya amshi wayarsa...."

"""Yauwa Ba bah, naga wata yarinya ina son ta fa "".Abu yace...."

"Tanko yace ""Da aure ko da haraka? ""."

"Abu yace ""Da haraka dan ubanka,,, da aure zanso wannan 'yar iskar yarinya wadda kowa d'agama buje"

"take yi,,, ya shiga ciki ""..."

"Tanko yace ""ya isa shegen gora,,, idan dai Laraba ce zan turo maka ita. Bakada damuwa kaji abokina""....."

"Abu yace ""Yauwa yanzu naji magana,,, bakada matsala Ba bah "".Ya fad'a cike da shed'anci da"

shek'iyanci...

"""Sai kai Abu mai buhu-buhun 'yan mata "".Tanko ya fad'a...."

"""Nagode nagode Babah "".Cewar Abu cike da shed'anci da rashin kunya......."

"Suka lale da juna,,, tare da cigaba da maganganun su na batsa. Da iskanci su ko kunyar mutane basa ji,,,"

suna iya sakin magana ko agaban kowaye...

_*Mu kasance tare akodayaushe my fans*_

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 146-150

"Bayan Saude sun gama abinda suke yi,,, Aliyu yayi barci mai ci keda da jin d'adi...."

"Sai da Saude ta bari yayi nisa cikin barci,,, sannan ta saci jikinta a hankali ta sauka a gadon sannu -sannu"

kamar b'arauniya... Tasa takalminta ta juya ta b'ude k'ofar d'akin a hankali ta fita ta nufi d'akin Amina.....

"Amina tana zaune tana shan shayi,,, bayan ta gama gasa jikinta da ruwan zafi sosai. Tana shan shayi"

"kamar wadda bata son sha a hankali,,, cike da tunani da tarin damuwa.."

"Haka kawai taji an bud'e k'ofar d'akinta,,, da k'arfin gaske ""garaffff!! An turo k'ofar da k'arfin gaskee.. Sai"

"da gaban Amina ya buga da k'arfi ""rasssss ""Domin duk azatonta Aliyu ne,, ya shigo domin ya k'ara bata mugun kashi saboda ta fahimci baya cikin hayyacinsa,,, tana ganin Saude taji dama-dama duk da tasan ko ita ba alkhairi,,, ya kawo ta d'akinta ba tasan ganin Saude masifa ne kuma bala'i ne gare ta.. Saboda"

tasan babu alkhairi a cikin zuciyarta ko tausayi....

"Saude tana shigowa,, saida ta kalli Amina sama da k'asa taga duk bakinta da jar fatarta sun kumbura,,,"

akan tasa Aliyu yayi mata..

"Saude ta fashe da muguwar dariya,,, wadda sai da tayi ta k'oshi sannan ta daina. Tace ""dama na gaya"

"maki ba'a ja da ni,,, akwana lafiya yanzu wannan duka da nasa aka yi miki.. Wallahi farawa ne sai kinyi"

"nadama a rayuwarki,,, sai kin gwamma ce dama baki auri Aliyu ba,, sai na walak'anta ki a rayuwa nasa"

"kin zama abar k'yama da gudu a cikin mutane.. Shegiya ashe ke k'aramar 'yar iska ce tunda har kika yi ma namiji kuka,, sai na halaka ki na salwantar da farin ciki da jin d'adinki "".Ta fad'a cike da nuna tak'ama da"

izza....

"Amina ta kalli Saude,, da jajjayen idanunta wad'anda suka sha kuka... Tace ""Duk abinda zakiyi Saudatu,,"

"je kiyi na barki ga Rabbis samawati.. Ki sani Allah baya kwana baya angaje sai yayi mini muguwar sakayya akanki ,,kada ki d'auka duk abinda kike yi kinci bilis,,, ki jira sakamakonki Saudatu.. Sannan rayuwa tah da mutuwa ta ba'a hannunki yake ba,, a hannun Allah ya ke na barki da ubangijin talikkai akan abinda kike"

"min da ma wanda zaki yimin nan gaba "". ...."

"""Na zata zaki zo ki rama bugunki ne akaina ne,,, bari ma kiji baki ganin da kayan barci ba..Aliyuna yana"

"gama dukanki kamar jaka mu shige cikin d'aki,,,, muka soyewarmu mun darji juna kamar ba gobe ba,,, mun bar jaka aladanya da kumburarren jiki da baki.. Shegiya karuwar mata shed'aniya,,, dama abinda na ke gaya miki kenan k'uncin rayuwa da bak'in ciki,,, yanzu kika fara fuskantar shi har abada babu ke babu"

"farin ciki da nishad'i "".Saude tace cikeda tink'aho da nuna isa.."

"Amina tace ""Ai bazan hanaki aikata,, duk abinda kika gadama ba Saudatu.. Kibi duniya a sannu wata rana"

"ko ance ki zalunci wani ba zaki iya ba,,, na yarda da k'addara ta nasan Allah shi ne zai saka mani akan dukkan abinda kike yi.. Karki bari ki cigaba indai duniya ce wanda bai zo ba ma jiransa ta ke ""......."

"Saude ta girgiza komai na jikinta,,, tare bank'are k'irjinta.. Tace ""nayi duk abinda zaki ce baya tab'a"

"damuna.. Saboda ina tare da zumar rayuwata,,, dama burina shi ne Aliyu ya zama ni kad'ai yake kulawa,,,"

kuma Alhmdlilah burina ya cika wata sai dai ta hangi miji daga nesa.. Kinga bari inje wurin zuma in bashi

"dad'i shi ma ya bani kada ya tashi ""...."

"""ke ya shafa bani ba,,, duk abinda zakuyi baya tab'a damuna "".Cewar Amina cike da rashin son fad'a.."

"Saude ta yi kuwah tace ""Hohohoho!! Wallahi k'arya ki ke bak'in ciki ne yayi miki yawa,, to aike kwana da"

"ke bayada wani amfani saboda ba haihuwa kike ba "".."

"Amina tace ""Naji dai ai haihuwa ta Allah ce,,, bani zan bai wa kaina saboda haka ke da ke haihuwa,,,, je ki"

"haihun mana tun lokacin baiyi ba""..."

"Saude tace ""kada ki kuskura ki gayamin maganar banza,,, na rantse da Allah yanzu inyi miki bugun"

"mutuwa,,, saboda na lura ke 'yar iska ce mara tarbiya,,, ubanwa zaki nunawa iya shege da salon karuwancinki wanda kika gada ga uwarki... Bak'ar annoba dangin tsiya taulalin wahala ""...."

"Amina tace ""ke dai akeji,,, banda lokacinki ""......."

"""Kar ki yi lokacina dan ubanki,,, zaki gane kurenki.. Kuma ke k'aramar 'yar iska,,,sai naje har gidan ku na"

"cima tsohuwar ki mutunci,, da kuma tsohon ubanki bunsuru Alade "".Cewar Saude....."

"Amina tace ""kije mana ko yanzu,, wa ye ya hanaki.. Dallah fitarmin daga cikin d'aki!! Ko in sab'a maki"

"kamannu ""...."

"""Har d'aki gareki ko akurkin kaji,,, zan fita amma ki sani ba ke ba farin ciki har abada.. Sai kinyi kukan da"

"baki tab'a yi ba a rayuwar ki"".Saude tace tana fad'a ta sa kai,,, ta fita daga cikin d'akin......"

"""da dai ki tsaya ki gani,,, wallahi dukanki zanyi sai dai Aliyu ya sakeni. Wannan wace irin rayuwa ce"

"kullum cikin tashin hankali da bala'i,,, daga an gama wannan sai wannan. Mutum ba safiyar da bai"

"tassuwa jidali cikin gida ba,,, idan kina jin takaici na ne ai nima ina ji,,, amma sai nayi hak'uri na barma Allah... Komai -komai masifa da bala'i da tashin hankali "".Cewar Amina cike da jimami da zullumi..."

**********************

"Acan gidan Iyayen Aliyu,,, Inna Indo ce ke magana da Baba Ayuba akan Aliyu..."

"Alokacin ne Inna Indo tace ""Maigida kwana biyu naji shiru,,, Aliyu ya daina zuwa gaishemu tunda yayi"

"aure nan. Shin ko lafiya suke bamu sani ba ""..."

"Baba Ayuba yace ""To ni zanje in kirashi da kike wannan magana,,, ba ke dai buk'atar ki yayi aure ba,,,"

"kuma yayi miye damuwarki yanzu ?""."

"""Haba Maigida ai abin ba fad'a ba ne,,, magana ce kuma naga duk abinda ya shafi Aliyu ya shafemu. A"

"matsayinmu na iyayenshi,, dama ina son in nemi izini a wurinka,,, domin inje in dubo su sannan naga ita ma har yanzu shiru babu labarin ciki,,, ko wani abu ""...Cewar Inna Indo......"

"Baba Ayuba yace ""na baki izini ki fita,,, idan ke shirya dama ku mata tunaninku k'arami ne.. Ba kin sashi"

"ya k'ara aure ba ne domin ya samu haihuwa,,, ai shi Allah ba'a yi masa wayo,,, komai da kike gani yanada lokacinsa,,, ga irin ta nan ke dai kika sani Indo "".."

"""Haba Malam mi yayi zafi haka? Dan Allah ka daina min irin wad'annan maganganu bana jin dad'in"

"su ,,,kuskure ne na riga na yi shi kuma na fahimci kuskurena tunda dad'ewa"".Cewar Inna Indo....."

"Baba Ayuba yace ""to naji na daina,,, amma ai gaskiya ce na fad'a maki Indo ""......"

"""Nagode Malam Allah ya k'ara bamu ikon gyarawa,,, da kuma yarda k'addara mai k'yau ko mara k'yau"

""".Inna Indo tace....."

"""Amin amin Indodoo ta Malam Ayuba "".Cewar Baba Ayuba...."

"Inna Indo tace ""Godiya na ke Maigidana ""Tana dariya..."

"Inna Indo da Baba Ayuba,,, haka dai suka cigaba da firarsu cike da jin d'adi tare da kuma shawarwari"

akan maganar Aliyu... Ta rashin zuwansa gaida iyayenshi kamar yadda yake yi acan bayaaa...

*********************

"Acan gidan Aliyu kuwa,,, Amina ce zaune take cin abincinta ita kad'ai batare da su Aliyu ba.. Saboda"

"d'azu ta fad'a musu ta gama abinci,,, Aliyu yace mata kar ta jira su taje taci abincinta,,,, ita kad'ai shi da shi da Saudatu zasu ci. Saboda yanzu basu gama soyewa ba,,, sai zuwa anjima zasu fito.."

"Hak'ik'a wannan maganar,,, tayi bala'in k'onama Amina rayuwa,,, amma sai ta danne b'acin ran ta bata"

"nuna musu komai ba... Saboda tasan anyi haka ne domin a b'ata mata rai,,, tayi juyarwa ta d'akinta ta zauna tana cin abinci,,,, cike da k'unci da tarin damuwa......"

"Bata ci abinci komai ba,,, taji ta k'oshi saboda tsananin damuwa da zullumi... Ta lula duniyar tunani da"

nazari.....

"Ta yi nisa da tunani ne,, Mama Habiba ta shigo cikin room d'in ta ,,,tana ta sallama ba'a amsa ba.. Sai da"

"ta shigo har cikin d'aki ne.. Taga Amina ta lula kogin tunani,,,, ta tab'a ta da k'arfi....."

"Adalilin haka saida Amina,,, ta firgita da k'arfi!! Tana zazzare idanu cike da tsananin tsoro da kuma"

shakku......

"Habiba ta dubi fuskar Amina da kuma kumburarren jikinta,,,, tace ""Subahanillah!! Mi zan gani ni Habiba,,,"

"Amina jimuwa kika ye,,, yaushe abin ya faru baki sanar da mu ba? ""...Tace cike da tsoro da fargaba....."

"Tace ""ba jimuwa nayi ba Anti Habiba,,, wani tashin hankali ne da bala'i da ya kunno a cikin gidan"

"mu"".Amina tace tana fitar da hawaye masu zafi da rad'ad'i,,, daga idanunta..."

"Habiba tace ""wannan wane irin bala'i ne ya kunno muku?,,, amma ban fahimci maganarki ba Amina ,,ya"

"dace ki sanar dani yadda zan gane. Abinda kike nufi ""....."

"Amina tace ""Ina Hussaina ta ke ne? Naga ban gan ta ba "".."

"""Tana gida bata jin d'adin jikinta ne,,, shiyasa baki ganmu tare ba.. Ki bani amsata ina tambayarki,,, kina"

"tambayata "".. Cewar Habiba cike da rashin kwanciyar hankali... ."

"Tace ""Allah ya bata lafiya ,,sai naje dubo jikinta ""...."

"""Amin kefa nake saurare Aminatu "".Habiba ta fad'a cike da zullumin maganar da zai fito a bakin Amina...."

"Amina ta gaya mata,, irin kashin da Aliyu ya bata,,, tare da cin mutuncin da Saude ke yi mata.. Babu"

"abinda ta b'oyewa Habiba,,, tana fad'a mata tana kuka cike da b'acin rai da bak'in ciki... Hak'ik'a wannan labari ya tashi hankali Habiba tare da rikita mata tunaninta,,, itama batasan lokacin da hawayen bak'in ciki da na tsananin tausayin Amina ba,,, ya fara kwaranya daga idanunta.. Tasa hannu ta share da sauri"

"domin kada Amina ta gani,,,, ta karya mata zuciya..."

Ta dubi Amina cike da tsananin tausayawa da damuwa....

"Tace ""Amina ba abinda zance miki illa,,, kiyi hak'uri komai na duniya yanada lokacinsa... Amma hak'uri ne"

"shi zaisa kaga k'arshen komi,,, a rayuwa wallahi na k'ara tausaya miki Aminatu.. Ki k'ara hak'uri da juriya zakiga sakayyarki tun anan duniya,,, Saudatu kinci amanar rayuwa to ki sani ba zaki yi k'arshe mai k'yau ba.. Allah ya walak'anta rayuwarki tun anan duniya Saudatu,,, ya kuma nuna miki duk abinda ki ka shuka ki girbe shi da hannunki.. Aminatu ki k'ara hak'uri akan wanda nasan ki da shi,,,, kuma danne zuciyarki ki"

"maida komai ba komai,,, Allah yana sama kallon azzalumai .Shi zai mi ki sakayya ""....."

"Amina tace ""ba komai ne ke b'ata min rai ba,,, irin kashin da Aliyu ya bani,,, tare da cimin mutunci akan"

"Saudatu.. Nakanyi matuk'ar mamaki akan anya ba'a canza mini Aliyuna ba,,, anya shi ne mai k'aunata tare da gudun b'acin raina. Anya shi ne wanda ke son duk abinda na ke so?""Ta fad'a tana mai sake fashewa da kuka mai ciwo....."

"""Shi ne Aliyunki Aminatu,,, sai dai ki sani ba'a cikin hayyacin kansa yake ba... An shiga a tsakanin ku"

"hak'uri kawai zakiyi,,, tare da yawaita addu'a akan Allah ubangiji ya kawo muku k'arshen wannan bala'i da iftila'in rayuwa.. Ki daina kuka bana son Ina ganin kukanki,,, saboda yana k'ara tayar mini da hankali da kuma sani cikin tsananin damuwa "".Cewar Habiba cike da mutuwar jiki......."

"Tasa hannu ta sharema Amina hawaye,,, cike da tausayawa rayuwar Amina......"

"Amina tace ""Na daina Anti Habiba,,, Insha Allah zan dinga yawan kai kukana ga Allah... Akan ya yaye min"

"dukkan damuwata ""...."

"""Hakan shi yafi dacewa Aminatu "".Cewar Habiba cike da lallashinta......"

"Amina tace ""Zan daina kulasu,,, in Allah ya yarda ""...."

"""kin ko k'yautama kanki Amina "".Cewar Habiba...."

"Mama Habiba ta cigaba da lallashinta,,, tare da gaya mata maganganu masu sanya zuciya natsuwa,,, da"

kuma kwanciyar hankali. Ta k'ara bata shawarwari masu matuk'ar muhimmanci a zamantakewar rayuwar duniya... ..

"_*Muje zuwa,, domin jin yadda zata kaya a tsakanin su *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_&Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 156-160

"Inna Indo tacigaba da yi musu nasihohi,,, tare da nuna musu muhimmanci hak'uri da juriya a rayuwa."

"Nima kaina da nake gefe hak'ik'a Inna Indo tayi matuk'ar burgeni da bani sha'awa,,,, dama haka rayuwar ta gada,,, duniya ce sai hak'uri da kawaici akan mutane....."

"Bayan ta gama yi musu nasiha da wa'azi tanuna musu zata wuce zuwa gida,,, kuma dan Allah su k'ara"

hak'uri akan lamarin duniya da zamantakewar rayuwa....

"Alokacin ne ta dube su,,, tace ""to ni zan wuce gida,,, dan Allah ku had'a kanku ku zauna lafiya.. Zan dinga"

"lek'owa akai -akai,,, kunji ko ""... ."

"Aliyu yace ""Insha Allah Inna,,, zamu gyara zamantakewarmu ""....."

"""To Allah yasa,, ke kuma Saudatu ki zauna ga kanki,,,, ke kuma Amina duk abinda sukayi miki ki bugo"

"waya ki gaya mani "".Cewar Inna Indo...."

"Saude tace ""zamu zauna lafiya Inna karki damu ""....."

"Itama Amina tace ""babu komai Inna,, Insha Allahu zan sanar da ke duk abinda ya taso ""...."

"""Yayi k'yau Allah ya yi muku albarka,,, ya baku zaman lafiya mai d'orewa har abada "".Inna Indo tace....."

"""Amin amin "".Suka fad'a a tare....."

"Amina da Saude suka had'ama Inna Indo kud'i da sabulun wanka da wanki masu k'amshi,,, suka bata"

dubu biyu... Inna Indo ta amsa tare da k'ara sanya musu albarka a rayuwa.....

"Shima Aliyu ya bata dubu biyar,,, tare da bata turare guda mai k'amshi ta kaima babanshi.. Yayi mata"

"alk'awarin zuwa gaida su akowane lokaci,,, shima ya rakata tare da su Amina... Suka tara mata mashin,,, ta hau mashin Aliyu ya ba mai mashin d'ari biyu,,,, yaja mashin suka wuce zuwa gida...."

"Bayan Inna Indo ta wuce zuwa gida,,, suka koma gida kowa ya kama aikinsa... .."

**********************

Tanko da Abu suna zaune suna firar su bayan wucewar Laraba gidansu...

"Wayar Tanko tayi ringing,,, yana ganin nombar Lado ya mik'ama Abu,,, yace masa ""ana son magana da"

"shi ""...."

"Abu ya amshi wayar,,, tare da danna receiving call...."

"Yace ""Hello abokina ya kake? "".."

"""lafiya k'alau Abu,, gani nan saman hanyar zuwa Kamba"".Cewar Lado..."

"Abu yace ""Allah ya kawo ka lafiya,, sai kazo ""..."

"Lado yace ""Amin amin saina zo ""......"

"""To abokina sai kazo "".Cewar Abu...."

"""Sai anjima "".Lado yace,, sannan ya kashe wayar shi.."

"""To yayi ""Cewar Abu.."

"Abu ya mik'ama Tanko wayarshi sannan yace ""Lado yace ya kusa shigowa cikin garin nan "".."

"Tanko yace ""Ashe dai kace zamu cika mu ukku,,, muji dad'in k'ara holewa da k'yau babah "".."

"""Wallahi kam babah,,, maganarka haka take "".Abu yace...."

"Suna firar su,, saiga kiran Lado,,, ya sake shigowa cikin wayar Tanko.. Sukayi receiving tare da yi ma mai"

mashin kwatancen inda zai kawo Lado....

Lado ya sake kashe wayarsa....

"Bada jimawa ba,, mai mashin ya kawo Lado wurin su Abu ya aje kusa ga su Tanko....."

"Abu yana ganin Lado,,, suka rungume juna. Tare da tsananin farin cikin ganin juna,,, shi ma Tanko yana"

"ganin abinda Abu yayi,,, shi ma ya rungume su yana mai farin ciki...."

"Bayan sun gama farin cikin ganin juna,,, suka biya mai mashin kud'insa,,, mai mashin ya tadda babur d'in"

"shi ya wuce,,, zuwa wurin sana'ar sa...."

"Abu da Tanko suka d'auki jikkar kayan Lado,,, suka shigar da kayan cikin d'akinsu na kwartanci da"

iskanci.....

Suka yi shigewarsu cikin d'akinsu.....

**********************

"Inna Indo ta koma gida,,, bayan ta huta ta kawo bayanin komi ta gayama Baba Ayuba.. Akan irin abinda"

ke faruwa a gidan Aliyu....

"Baba Ayuba ya nuna matuk'ar b'acin ran shi,,, tare da kama fad'a kamar ya ari bakin kura..."

"Yasa hannu ya d'auki wayarsa,,, ya kira yayi masa tatas.. Tare da ci masa mutunci akan abinda yayi ma"

"Amina,,, yaja masa kunne akan kada ya k'ara ji ko ya k'ara gani,,,,Idan ba haka sai ya wulak'antashi da tozarta shi....."

Aliyu babu abinda yake yi sai bashi hak'uri akan ba zai sake ba. Kuma yayi nadamar abinda ya aikata

kuma insha Allahu ba zai k'ara ba.........

"Baba Ayuba ya yi masa nasihohi da wa'azi,,, tare da nuna masa muhimmanci adalci da rashin nuna"

banbanci a tsakanin matanshi.. Aliyu yaji dad'i sosai matuk'a kuma yayi godiya ga mahaifin shi.......

"Suka yi sallama da juna,,, Baba Ayuba ya kashe wayar shi.. Suka cigaba da firarsu cike da jin d'adi sosai da"

farin ciki...........

**********************

"Acan gidansu Aliyu,,, kuma zamantakewar su yayi dama -dama.. Saboda yanzu sun daina takurawa"

"Amina sosai,,,, sai dai kishin da ba za'a rasa ba domin wannan kunsan cikin jini yake,,,, haka kishin ya"

kasance yayi sauk'i sosai... Saboda Aliyu yanzu yana shakkun tab'a ta domin gudun masifar Inna Indo da fad'an Baban shi...

"Amina taji dad'i sosai,,, saboda yanzu sun sake mata mara tayi fitsari Ba za'a rasa habaice -habaicen"

"Saude da zage -zagenta,,,Amina bata damu da ita ba saboda.. Yabawa ma tankawa ne,,,, ta riga tasa Saude a cikin kwandon shara...."

"Abin yana cima Saude rai,,, saboda ganin Amina ta fita batun ta batada lokacinta. Ga bak'in cikin yanzu"

"Aliyu yana shakkar tab'a lafiyar jikin Amina,,,, kuma sannan ko tayi k'ulle-k'ulle da zuge -zuge baya kulata,,,, shi ne abinda yake k'ara k'onama Saude rai. Tare da shan alwashin sai ta ga bayan Amina,,,,"

kuma sai ta kuma k'untata ma rayuwar Amina... ..

"Haka dai suka cigaba da rayuwarsu,,,, cike da sauk'in rayuwa da kishin jahilci mai cike da rikitarwa......"

**********************

*BAYAN WATA HUD'U*

"Abubuwa da dama sun faru,,,, na farin ciki ko bak'in ciki a cikin zamantakewar su Saude da Amina..."

"Alokacin ne ciki ya bayyana,,, ga su Amina hak'ik'a Aliyu yayi kukan farin ciki a wannan ranar,,, ya kuma yi"

"godiya ga Allah mad'aukakin sarki.. Inna Indo ma tayi matuk'ar farin ciki da murna,,, kowa fad'ama ta ke zata samu jikoki a wannan lokacin.. Ita ma har da sadaka sai da ta yi....."

"Agidansu Amina ma sunyi matuk'ar farin ciki,,, da tsananin murna a cikin gidan.. Hadiza ma ba k'aramin"

"dad'i taji ba,,, saboda Antinta zata samu nata d'a ko d'iya... Hak'ik'a a wannan ranar wad'annan gidajen sun kasance cikin tsananin farin ciki da murna mara misaltuwa... Ko tsammani ni kaina ni Mugirat na"

taya su murna da matuk'ar farin ciki.....

"Haka dai suka cigaba da rainon cikinsu,,, cike da kwanciyar hankali da jin d'adi.. Saude ta nuna matuk'ar"

"bak'in ciki akan cikin da Amina take da shi,,,, domin bata so Amina ta samu ciki,,, ta so cikin ya zube ko ta halin k'ak'a.. Saboda ita kad'ai take so ta haihu a cikin gidan Aliyu,,, babu yadda zata yi ko tayi maganin da k'ulle-k'ulle baya ci,,,, dama zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana maxuru ana shaho sai yayi..."

"Sannan sara da sassak'a baya hanama gamji tofo,,, haka dai aka cigaba zaman tare cike da makircin"

kishi.....

"ita Amina dai,,, babu ruwan ta.. Ta cigaba da rainon cikinta cike da jin d'adi da farin ciki,,, wata rana har"

"da hawayen godiya ga Allah ta keyi tare da nafiloli na godiya ga Allah... Akan Allah ya sauketa lafiya,,,, ya kuma tsare ta da abinda yake cikin cikinta........."

********************

BAYAN WATA BIYAR

"Alokacin ne Allah ya sauke su Amina lafiya,,, Amina ta fara haihuwa ranar littinin ta haifi d'iyar ta mace"

"k'yakk'yawar yarinya,,, mai k'yawon gaske son kowa k'in wanda ya rasa.. Hak'ik'a aranar dangi da iyayen Amina,,, sunyi matuk'ar farin ciki da murna......"

"Sati na zagayowa yarinya,,, ta ci suna Aisha yasmin... Aka yi biki kowa ya watse,,,, itama a ranar Saude ta"

haihu ta samu d'iyar ta mace mai kamada ita sak.. Kunga kenan tsakanin su shi ne sati guda........

"Sati yana k'ara zagayowa,,, yarinya ta ci suna Asiya.. A wannan ranar su Inna Harira da Laure sunzo,,, har"

da su Inna Lanti da Iya Delu sunzo biki saboda biki na farar kaza balbela ba gayyarta ake ba... Hak'ik'a aranar su Inna Harira sun baza haukarsu sosai.....

"Nima a ranar na saci cinyar kaza,,, alokacin ne Inna Harira ta bugamin uban harara Tare da ja min"

tsokiii...

"Na kwashi gudu,,, saboda gudun masifar Inna Harira ."

"Haka dai suka cigaba da gudanar da bikinsu,,,, cike da jin d'adi da farin ciki..."

"Aka gama bikin kowa ya kama gabansa,,, tare da addu'ar Allah ubangiji ya raya ya bari akan sunnah...."

"Nace ""Amin ya Allah "".Ina gefensu na b'oye....."

"Kwanaki suna ta tafiya,, satikka suna ta gudu,, watanni sun zama kamar kwanaki k'alilan... Haka dai suka"

"cigaba da rainon d'iyansu ci keda da kulawa da basu tarbiyar da suka gada... Aliyu yana k'ok'arin kamanta adalci a tsakanin su,,, duk abinda ya siyoma Aisha shi zai siyoma Asiya babu wani banbanci ko wariya. Saude kuma ba haka ta ke so ba,,, ta fison a fifita ta akan Amina. Sannan a fifita Asiya akan"

Aisha....

"Tayi alk'awarin sai taje amso magani,,, can garin Shiko domin ta juya Aliyu son ranta,,, kuma sai abinda"

"tace... Ta kuma sha alwashin sai ta yima Amina,,, mugun asirin da zai kashe ta har abada......"

"Abangarensu Abu da abokaninsa,,, iskancinsu sai gaba yakeyi.. Su kashe rai abiya su ba'a bakin komai ya"

"ke ba ,,,,ga kuma tare d'iyan mutane tare da yi musu fyad'e. Sun addabi mutanen gari musamman"

masu d'iya mata......

"Amma ko shi da b'oye sukeyi,, saboda Kamba ba kamar Shiko bace. An sanya matakan tsaro sosai ana"

"nemansu ruwa a jallo,,,, a cikin garin Kamba,, shiyasa suke kaffa -kaffa domin gudun samun matsala......."

"Koda yake Hausawa sunce rana dubu ta b'arawo,,, rana guda ta mai shi..."

_*Muje zuwa wai mahaukaci ya hau kuraaaa *_&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_*Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk masu suna Aishat da ke fad'in duniya. Ku sani ina matuk'ar

k'aunar masu sunanku. *_

"_Aishat Usman ki sani cikin ruhin zuciya ta,,, ina son ki da gaskiya..._ "

*PAGE* 161-165

"Bayan haihuwarsu Saude da wata hud'u,,, ta nemi izini wurin Aliyu akan tana son taje garin Shiko. Bai"

"musa mata ba ya kawo kud'in mota ya bata #1000 tare da yi mata fatar asauka lafiya.. Ta shirya tsab ta goya d'iyar ta Asiya,,, ta wuce tasha ta samu motar zuwa Shiko...."

"Bayan ta wuce ne Aliyu ya zo har d'akin Amina,,,, ya d'auki Aisha mai sunan Mamansa yana mata wasa."

"Ita kuma tana k'yalk'yatar dariya irinta yara,,, ya dubi Amina kallo mai cike da k'aunar da ta dad'e a cikin jinin jikinshi...."

"Yace ""Maman momina ""..."

"""Na'am "".Cewar Amina..."

"Aliyu yace ""Saudatu ta wuce garinsu yanzu,,, saboda mi zaki dafa mana? "".."

"Tace ""Duk abinda kake so kuma kake ra'ayi,,, shi xan dafa mana "".."

"Yace ""a'a ba haka bane nake nufi ba,,, mi zai hana ki yi mana farfesun kaza da coconut drink,,, kawai ya"

"ishe mu.. Idan muka ji yunwa anjima na ciko mana leda da nama ko ""...."

"Amina tace ""Haka zanyi,, idan har zai sanyaka farin ciki da nishad'i ""...."

"Yace ""Nagode Allah yayi miki albarka ""..."

"""Amin amin "".Cewar Amina,, Aisha ta tsandara musu kuka,,, alamar ta fara jin yunwa.. Amina tayi sauri"

"ta amsheta a hannun Babanta.. Ta fara bata nono tana sha,,, sannan ta yi shiru.. ."

"Aliyu ya cigaba da yima Amina fira,,, tana amsa mishi dai dai gwargwado,,, duk da yake tayi matuk'ar"

"mamaki akan sake mata fuska da yayi.. Saboda gaskiya idan har Saude tana nan ko dariyarsa da k'yar ta ke gani,,, sannan idan ba ranar girkinta ba ne baya magana ko fira da ita.. Ita kanta yanzu Amina bata fiye shiga lamarinsu ba,, idan ka ganta a parlorn to su Hussaina da Habiba ne,,, suka kawo mata ziyara. Idan ba haka ba kodayaushe tana cikin d'akinta,,, saboda gudun fitinar Saude,,, domin har yanzu Saude"

"bata chanza

Please Login or Register in order to submit comment