You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu dad'i saboda ta jiyar da shi dad'in da bai tab'a jiba,,,, a jikin wata mace. Haka suka kwanta"

rungume da juna har sukayi barci...

"Ita kuma uwar banza Saude,,, tana nan tana ganawa Aisha azabar aiki. Tare da marinta idan ta tsaya"

"hutawa,, ta kuma k'ara ja mata kunne akan ta rabuda Abbas. Domin kuwa d'azu ya kawo mata kaya masu k'yau,, Inna Saude tana ganin su ta k'ona su da ashana. Tare da alwashin sai ta rabasu saboda kuwa zata je can wurin boka SIDDARU,,, ta kai masa kukanta. Saboda bata k'aunar ganin Aisha ta kasance cikin farin ciki da nishad'i. Kuma bata son duk wani mai sonta,, saboda har gidansu Abbas ta ke zuwa fad'a domin Abbas ya rabuda Aisha. Babu ranar da bata zuwa cima Mama Habiba mutunci,,,da Mama Habiba ta ga abin nata baya k'arewa to dama kunsan tanada takaicinta. Tana k'ara komawa gidansu Habiba,, ta kama Saude ta yi mata kashin k'warai saida tayi tutu da fitsari cikin wando. Sai ga"

Inna Saude tana kuka tare da majina yabe-yabe a fuskarta. To tun daga ranar bata sake komawa ba...

"A can d'akin Abu kuma, sai da ya k'ara biyar buk'atarshi da Asiya. Tana kuka tana komai ya yi abinda"

"ransa ke so da ita,, bayan ya gama lagudar Asiya ko'ina a jikinta. Ya d'auketa suka shiga toilet tare da yi mata wanka,,suna gamawa ya fito da ita ya shiryata. Shima ya shirya kanshi sannan ya d'auki kud'i dubu"

"goma ya bata,, tare da yi mata alk'awari da dama. Ta amshi kud'in tare da girgizawa komai na jikinta,,"

"tayi mishi kiss da godiya. Ya shafeta sannan yace mata sai ya nemeta idan taji sauk'i sai su d'ora daga inda suka tsaya. Sannan dan Allah ta rik'e mishi amana kada taba kowa jikinta idan ba shi ba,, domin kuwa idan ta ci amanarshi akwai matsala kuma bazai yafe mata ba. Ta nuna masa karya damu ba abinda"

"zai faru kuma zata rik'e Amana,,, tayi wucewarta zuwa d'akin Inna Saude....."

"Tana fita daga d'akin Abu,, yayi murna sosai domin burinsa ya kusa cika a rayuwarshi. Yace ""afili ba ke"

"wayo ba ko Saude har da cema d'iyar ki ta daina kulani,, tare da kirana shege saina yima Asiya ciki. Kuma wallahi sai kinyi nadamar duk abinda kika aikata a rayuwarki. Sai na nuna miki na fiki rashin kunya da imani,, kema zan dawo gareki Saude sai kun zamo abin k'yama da gudu cikin Al'umma. Zaki gane ba'a tab'ani a kwana lafiya "".Haka Abu ya cigaba da shan alwashin sai ya k'untata ma rayuwar su Saude,, tare"

da yi musu abinda har abada ba zasu manta da shi ba.

"A can garin Shiko kuwa,, su Inna Harira da Laure suna nan suna iskancinsu tare da cin Amana da zaluncin"

"da suka sa ba. 'Yan hayansu ma duk shekara sai sun chanxa wasu,, saboda rashin mutunci da hak'uri. Babu wanda suke ragama har 'yan uwansu da 'yan hayansu..."

"Malam Isiyaku kuma yanxu baida wata matsala,, yayima d'iyar sa Atikah aure tunda dad'ewa harta haihu"

"na farko namiji mai suna Usman. Shima Abdullah yayi aurensa tare da matarshi mai suna Fatima,, yana aikin INEC ne. Ya gida gidanshi mai k'yau tare da kula da mahaifansa da kuma Atika. Ya mallaki mai motoci ukku masu k'yau,,, yaso Inna Mariya ta koma gidanshi amma ta nuna masa tana jin dad'in zama da Ladidi Matar yayanta Malam Sani,,,shiyasa yake k'ok'arin wajen k'yautata musu gaba d'aya. Haka dai"

suke gudanar da rayuwar su cike da tsananin farin ciki da nishad'i da jin d'adi sosai...

Dama ance maha k'urci mawadaci...

"_*Ku kasance tare da ni*_ , "

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_*Godiya da jinjina gareku.*_

*YARIMA SUHAIL FANS*

*FATALWAR MIJINA FANS*

*ZURFIN CIKI FANS*

*NAZIR FANS*

*RUD'ANI FANS*

*RUK'AYYATU FANS*

*NA CUCI JAMEEL FANS*

*HISABI FANS*

*HAUWA JIDDAT FANS*

*WAYE MACUCI FANS*

_da duk sauran da ban ambata ba._

*PAGE* 181-185

Haka Abu ya cigaba da iskanci da Asiya cikin gidan ubanta kuma cikin d'akin Abu wanda ya ke mallakinsa

"a yanzu Saude tana cikin gidan amma batasan wainar da ake toyawa ba saboda hauka da wawancinta amma in Aisha ce,,, hatta ds miyau tatofar Inna Saude sai ta sa mata ido saboda tsananin k'iyayya da hassada. Amma Asiya duk abinda zatayi babu mai kwab'arta,,, balantana asa mata idanu ko ayi mata fad'a. Idan taje school yanzu su Kubra sunga yanzu idanunta sun bud'e da yin iskanci,,,, haka yasa suke janta suje suyi zina saboda su samu kud'i. Asiya kuma ta yarda tare da binsu ko'ina suka jata,, amma tana yawan gaya musu akwai wani wanda bata son ya ganta,,, ko yaji labarin abinda ta ke aikatawa. Haka dai zasu nuna mata babu wanda zai sani Insha Allah karta damu,,, haka suke gudanar da al'amarin su a b'oye"

domin ba kowa suke son ya sani ba....

"Abangarensu Aisha soyayyar su tana nan daram,, saboda yana zuwa wurinta akai -akai..."

"Akwai wata rana da Abbas ya zo fira wurin Aisha,,, yana zuwa suka gaisa da Aisha ya d'auki wani abu a"

"cikin leda ya bata. Ta amsa tare da yi mishi godiya,, ya dubeta kallo mai cike da tsantsar k'auna da soyayya..."

"Yace ""my esha ko akwai abinda kike buk'ata,,, ki sanar dani bazan gaji da yi miki hidima ba. Tare da"

"kulawa da ke har k'arshen rayuwata "".."

"Aisha ta dube shi cikin so tace""Na sani Yaya Abbas,, fatarka da kuma burinka bai wuce ace ina cikin farin"

"ciki ba. Amma ka sani nima ina son ka kamar yadda kake sona,, kuma ina godiya da kulawarka gareni Allah ya bar k'auna. Amma ka sani ko ka siyomin abu idan har Inna Saude ta gani k'onawa ta keyi,,, ta tsane ni kamar mutuwarta.Saboda haka ka rage kashe kud'inka akaina domin hasara kawai Inna Saude"

"ke saka,, na fahimci bata son ganina cikin farin ciki a rayuwa "".Ta fad'a cike da sanyin jiki.."

"Yace ""ki daina damuwa da wannan my Esha,, muddin zakiyi farin ciki da nishad'i da abu,, to babu hasara"

"agareni. Dama nasan soyayyarmu kawai ta ke yi ma bak'in ciki to ta cigaba,, domin ruwa ko iska basu isa su rabamu ba. Soyayyar da nake miki ta wuce misali saboda haka ki kwantar da hankalinki ina tare da ke akodayaushe "".."

"Aisha tace ""hak'ik'a nayi matuk'ar godiya ga Allah ubangijin talikkai,, da ya bani kai amatsayin masoyi"

"kuma yayana. Amma ina jin tsoron Inna Saude kada ta rabani da kai,, domin kai kad'ai ne ka ragemin da Asma'u wad'anda Inna Saude bata rabamu ba. Ta rabani da Baba da kuma Kakata da 'yan uwan mahaifiyata ""..Tace tana mai zubar da hawayen k'unci da bak'in cikin rayuwa..."

"""Subahanillah! Aisha ki daina kuka bana son ganin hawayenki,,, saboda ganinsu yana sanyamin zafi da"

"rad'ad'i cikin zuciya. Dan Allah kiyi hak'uri akan dukkan abinda ta ke yi miki komai mai wucewa ne insha Allah,,, Allah shi ne zai miki sakayya tun anan duniya""..Abbas yace tare da mik'a mata handkchef mai k'amshi turarensa,, saboda ta goge hawayenta. Ta amsa cike da shak'uwa da so,,, ta goge hawayenta."

"Sannan tace ""Nagode sosai Yaya Abbas hak'ik'a nayi dacen masoyi,, wanda baya son b'acin raina kuma"

"ka sani ka zamo jigon rayuwata abar tunanina akowane lokaci "".."

"Abbas yace ""karki damu ko babu so ke k'anwatah ce,, kuma 'yar uwata musulma.Saboda haka abar"

"k'aunata ""..Ya d'auki kud'i naira dubu ishirin ya bata,,, Aisha ta k'i amsa saida ya nuna b'acin ran shi matuk'a sannan ta amsa da k'yar...."

"Tace ""Nagode sosai Yaya Abbas ""..."

"Ya harareta da wasa yace ""rik'e godiyarki bana so "".."

"Tace ""Yi hak'uri Mai sona inji kasha gaya mani,, baka son yawan godiya I'm sorry my love "".Tace tana"

murmushinta mai k'yau....

"Abbas yace ""nayi karki damu kinji ko my Esha "".Yana rufe bakinsa sai ga Inna Saude ta fito waje,, domin"

"tayi neman Aisha bata ganta ba,,,shi ne ta lek'o waje ta ganta tare da fitowa.."

"Inna Saude ta dubi Abbas, duba na wulak'anci da k'ask'anci. Tace ""wai kai wane irin mayen mutum ne,,"

"nasha gaya maka ka daina zuwa wurin Aisha. Saboda anyi mata miji amma ka k'i dainawa wace irin zuciya ce da kai,,, na rashin jin magana. To bari kaji wallahi ba zaka auri Aisha ba komi nacinka da zak'ewarka ""tace cike da masifa tare da rik'e k'ungunta.."

"Aisha kuwa gabanta fad'uwa kawai yakeyi, saboda masifar tsoron Inna Saude....."

"Abbas yace ""Bari kiji in gaya maki Saude kike ko wa,,, duk abinda zakiyi Allah ya fiki sannan bazan daina"

"zuwa wurin Aisha ba. Saboda ba d'iyarki ba ce sannan babu abinda ya shafeki a alak'armu da ita,,, saboda haka ki kama girmanki da mutuncinki kafin su zube "".. ..."

"Saude ta kuwwa da k'arfi tace ""Bazan kama girmana ba,,, wallahi sai ka bar k'ofar gidan nan saboda ba ta"

"ubanka ba ce. Sannan rabuwa da Aisha ya zama dole ko ba ni na haifeta ba,,, shege k'warton banza mai lalata rayuwar d'iyan mutane ""."

"Aisha tace ""dan Allah Inna kiyi hak'uri ki koma gida,,, yanzu zan shigo wannan abin da kike yi ba girmanki"

"ba ne wallahi ""....."

"Abbas yace ""my Esha rabuda ita ta gama haukarta,, kuma babu inda zanje ""..."

"""Uwarka ce mahaukaciya ba ni ba,, Habiba mai yawon maula da karuwanci gida gida. Sannan ga"

"munafurci da tsegumi kuma shegiya ce annobar gari "".Cewar Inna Saude cike da makirci da munafurcinta..."

"Abbas ya dube ta cike da tsantsar tsanarta, yace ""ba zanyi miki komai ba ayanzu domin kinci darajar"

"Aisha da Babanta.Amma ki sani wata rana ko kud'i aka baki ba zaki iya zagin wani ba ,,,balantana iyayensa my Esha na barki lafiya saboda idan na cigaba da tsayi,,,, ina saurarenta komai zai iya faruwa ""."

"""Allah ya kiyaye hanya kuma ya huci zuciyarka,,, ina gaida su Mama da Asma'u "".Aisha tace...."

"Yace ""zasu ji "".Ya shiga cikin motarsa yayi wucewarsa zuwa wani wuri.."

"Yana wucewa Inna Saude ta ja hannun Aisha da k'arfi,sukayi cikin gida. Bayan sun shiga cikin gida Inna"

Saude ta kashe Aisha da mari k'yau....

Aisha ta dafe kunci tana hawaye...

"Inna Saude ta nunata da yatsa, tace ""ni zakiyi ma munafurci dan ubanki. In sa ki aiki Aisha kije kina"

"sauraren k'wartonki ko,,,, har da fad'a masa ga abinda na ke yi miki ai duk ina lab'e ina jinki. Yanzu kuma da zai wuce har da ce masa Allah ya huci zuciyarsa,,,, adole an tab'a d'an gaban goshinki mai baki dad'i ko. Saina kashe ki wata rana a cikin gidan nan,,, kuma miki magana kina kukan munafurci 'yar kan babbar"

"buro uba,, munafukar karuwa ""."

"Aisha tace ""Allah ya baki hak'uri Inna "".Tana hawayen rashin uwa...."

"""Hak'urin ubanki da uwarki,, munafuka kawai dallah tashi ga wanki can. Da d'iban ruwa ki yi "".Inna Saude"

tace... .

"Aisha ta tashi ta fara d'ebo ruwa,, tana zubawa cikin randa. Sannan ta d'ebo ruwan wanki ta fara yi......"

"Acan cikin d'akin Abu kuma,, yana nan yana iskanci da Asiya. Yanzu kullum tana d'akinsa kamar mata da"

"miji,,, haka sukeyi akodayaushe. Amma Inna Saude duk abinda suke yi bata sani ba,, saboda rashin sanin ciwon kanta...."

"Bayan sun gama ne,,, sukayi wanka ya bata kud'i sannan ta fita. Shi ma ya nufi wurinsu abokansa Lado da"

"Tanko,, yana zuwa suka shiga cikin d'akin tare da bud'e sabon shafin hira..."

"Abu yace musu ""kunsan wani abu abokaina "".."

"""sai ka fad'a "".Suka ce atare da juna...."

"Abu yace ""bakuyi mamakin na daina kula Laraba,, da sauran 'yan mata na ba ""...."

"Lado yace ""munyi mamaki mana,, munga ka rage yawan iskancinka "".."

"Tanko yace ""Ai shi ne kam ko ka samu sabuwar budurwa ne halan? Kana jin d'adin ka ""..."

"Abu ya yi dariyar shek'iyanci yace ""Abokaina kenan ai kunsan ba abinda na ke b'oye muku,,, na samu"

d'iyar Innata Saude ita ce yanzu nake hutawa da ita. Haka dai ya kawo labarin komai ya gaya

"musu,,, na abinda yake shirin yi da wanda zaiyi babu wani abinda ya b'oye musu...."

"Lado yace ""Shege abokina gaskiya kanada tunani,, gara da kayi mata haka tasan cewa duk iskancinka"

"wani ya fika kuma karen bana shi ke maganin zomon bana ""..."

"Tanko yace ""wannan haka yake Lado,, to ita kuma Saude mi zamu yi mata ne. Idan kayi ma Asiya ciki"

"kuma "".."

"Abu yace ""Ai abinda baku sani ba shi ne,, so na ke idan na gama lalata Asiya. Sai mu dawo kan Saude"

"saboda wallahi sai tayi nadamar duk abinda ta ke yi min. Tare da cemin shege saboda haka ku taro kunnenku ku ji abinda zamuyi mata ""...."

"Tanko da Lado kowa daga cikin su,, ya taro kunnenshi. Abu yayi musu rad'a cikin kunnuwa,,, sukayi"

magana wanda ko ni Mugirat banji abinda suke fad'a ba na abinda Abu ya gaya musu. Balantana na sanar muku...

"Bayan ya gama yi musu rad'a a cikin kunne,,, Lado da Tanko suka bushe da mahaukaciyar dariya. Sannan"

"suka lale da juna suka ce ""Agaskiya abokinmu kanada kaifin tunani da hangen nesa,, Allah ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yayi birgima ""...Haka suka kama kitsa k'ulle k'ullensu,, suna yi suna dariyar mugunta kamar mahaukata....."

Wannan kenan.

Ko mi zasu yi ma Inna Saude?Sai ku biyo ni kuji...

*BAYAN KWANA UKKU*

"Da faruwar wannan al'amari, Inna Saude ta shirya tunda safe ta kama hanyar zuwa garin Shiko. Bayan"

taje ne ta sanar da su Inna Harira abinda take sonyi na zuwa wurin boka SIDDARU.

"Inna Harira tace ""Ai da kin bugo waya kin sanar min,,, da ba sai kinzo ba ni ina iya zuwa miki wurin boka"

"SIDDARU "".."

"Laure tace ""Ai shi ne wallahi sai a raba soyayyar ta su cikin ruwan sanyi. Ba sai kin damar da kanki ba,,,"

"kin tsaya kina ganin bak'in ciki da takaici ""..."

"Saude tace ""haka ne kam Inna amma nafi son inje da kaina. Bana son ina yawan wahalar da ke Inna"

"saboda ke yanzu kinfi kowa buk'atar hutu,, kema yaya Laure nafi son ki hutawarki ""..."

"Inna Harira tace ""miye abin wahala a ciki kuma Saude? "".."

"Laure tace ""Ai shi ne na gani nima,, ke dai kice kinfi son kije da kanki ""...."

"""Gaskiya haka ne nafi son inje da kaina "".Cewar Saude tare da mik'ewa tace musu ta wuce,,, daga can"

"zata koma Kamba. Suka yi mata Allah ya kiyaye hanya,, tayi wucewarta zuwa wurin boka SIDDARU...."

"Saude tana zuwa bukkar boka SIDDARU,, ta shige cikin bukkar saboda bata isko kowa ba. Yayi mata"

"barka da zuwa yana lasar bakinsa. Ta amsa tare da sanar da shi abinda ya kawo ta domin araba soyayyar da ke tsakanin Aisha da Abbas,,, sannan kuma ya bata d'iyarta Asiya maganin farin jini. Ya nuna mata duk abinda ta ke so zaiyi mata tare da bata maganin farin jini na asiya. Wani turare da ke cikin kwalba,,, sannan su kuma su Abbas zai tura musu Aljani domin ya rabasu,,, karta damu zata bashi kud'i ya nuna shi ba kud'i ya ke so ba. Kanta zata bashi shi ne ladar aikinsa da yake itama tana son abin,,,nan ta kwanta ya hau kanta suka kama yin abu guda. Tun tana jin d'adi har ta kai taji ta gaji amma tsoro ya hana mata magana,,,, kai in tak'aice muku dai sai da ya sadu da ita har sau ukku. Sannan ya k'yale ta hakanan ko shi"

saida tayi masa girki sannan ya barta ta wuce gidan mijinta...

"Tana wucewa boka SIDDARU ya k'yalk'yale da dariyar mugunta sannan yace ""Da sannu zaki fad'a tarkona"

"Saude,, ki sani bazan tab'a rabuwa da ke ba haka zanci gaba mu'amala da ke kamar matata. Nayi alk'awarin saina raba ki da mijinki saboda ki zamo tawa ni kad'ai,, babu wanda ya isa ya rabamu "".Haka"

dai ya kama sambatunsa tare da maganganunsa domin cikar burinsa....

"Acan Birnin kebbi gidan Hashim,, Hadiza kullum cikin tunani take da kuka saboda ta rasa mike damunta."

"Ko taso ta nuna da Aisha a k'wak'walwarta,,, sai ta daina aiki kuma tunaninta ya tsaya cak. Tun Hashim yana lallashinta har dai ya dawo shi ma yana cikin damuwa da fargaba,,, domin kuwa baya son b'acin ranta ko damuwarta ko kad'an.. Ko su Jamila da suke yara idan suka ga Amminsu cikin damuwa,,, basa"

walwala da farin ciki a wannan ranar.Shiyasa Hashim ya sameta a cikin d'aki daga shi sai ita....

"Yace ""Haba Ammin Jamil mi yasa kike saka kanki cikin damuwa ne,,, so kike hawan jini ko wani ciwo ya"

"kamaki. Dan Allah ki daina saka damuwa cikin ranki komai yayi zafi maganin shi Allah,,, kuma kinga hatta yaranmu da ni kaina bamujin dad'in kasancewarki cikin wannan hali. Sanar da ni mike damunki kuma mi"

"ya ke faruwa ne? ""..."

"Hadiza tace ""mijina kayi hak'uri domin nasan na saka cikin damuwa,,, ni kaina bansan abinda ke damuna"

"ba amma jikina ya bani wani nawa yana cikin damuwa,,, amma na kasa gano ko waye balle na taimaka mishi. Ka tayani da addu'a ya mijina ""..."

"Hashim ya matso kusa gare ta,, tare da rungumeta saman k'irjinsa yana lallashinta. Yace ""karki damu zan"

kasance mai tayaki da addu'a Allah ubangiji ya ye miki abinda ke damunki matata. Amma don Allah ki

"dawo da walwalarki kamar da,,, ko domin farin cikin yaranmu. Sannan ki sani ina tare da ke akodayaushe"

"akowane lokaci masoyiyata ""..."

"Hadiza tace ""mijina zan rage Insha Allah,,, karka damu Allah ubangiji ya barmu tare har abada "".."

"""Amin amin Amminsu Jamil "".Cewar Hashim..."

"Haka ya cigaba da kwantar mata da lallashinta,,, tare da yi mata kalamai masu d'adi da sa natsuwa......"

"Saude tana komawa gidan mijinta,, babu abinda ta ke sai murna da farin ciki domin cikar burinta. Ta kira"

"Asiya ta bata turaren da boka SIDDARU ya bata,,, ta sanar da ita amfanin maganin tare da gargad'inta akan ta fita harakar Abu. Domin akwanakin baya an sanar da ita an gansu tare,, haka dai Asiya ta nuna mata duk wanda ya gaya mata k'arya yake mata. Inna Saude ta nuna mata babu komai amma dan Allah"

"ta kiyaye,, Asiya ta kama yi mata k'arya har dai Inna Saude ta d'auka gaskiya ne..."

"Aisha baiwar Allah tana cikin d'akinta,, suna waya tare da musanyar kalamai masu dad'in sauraro...."

"Abbas yace ""My Esha ki sani ina matuk'ar k'aunar ki da sonki a rayuwata. Babu abinda nake muradi sama"

"da ke ba,, hak'ik'a kin kasance wata mai haskawa a cikin taurari. Ke ce sinadarin rayuwata kuma abar tunanina dare da rana ""...."

"Aisha ta yi murmushi tace ""ka sani kayi dashe a cikin zuciya ta,, dashen da babu mai iya cire shi a kogin"

"zuciyata,,kaine farin cikina yaya Abbas"".."

"Abbas yace ""Naji d'adi sosai da Allah ya had'a ni da gimbiyar mata,, ko cikin dubu samun irinki yanada"

"wuya my Esha "".."

"""Ko dan Allah ka daina zugani yaya Abbas "".Aisha tace masa..."

"Abbas yace""ba wani zugi sai gaskiya tauraruwar mata ""."

"""To shikenan tun da ka matsa na amsa "".Cewar Aisha..."

"Abbas yace ""ba wani matsawa sai da safe gimbiyar mata,, kina kwana cikin farin ciki tare da tashi cikin"

"k'oshin lafiya "".."

"""Kaima haka, nagode sosai da kulawarka gare ni"". Aisha tace"

"Suka kashe waya a tare, sannan kowa ya kwanta kamar kada su daina waya. Hak'ik'a Aisha tayi kwanan"

"farin ciki da nishad'i a wannan dare. Tare da tunanin mahaifiyarta cike da tsananin kewar Ummanta. Tayi murmushi mai hawaye tace ""Ummana Allah ubangiji ya jik'an ki ya kai haske kabarinki, yasa halayenki na k'warai su biki har cikin kabarinki. Ya kuma baki Aljanna fiddausi da ke da dukkan al'ummar musulmai baki d'aya ""...."

Ni da ke gefe nace Amin amin ya Rabbi.

"_*Rayuwa kenan dama haka duniya ta gada,,, ku cigaba da bi na *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 186-190

"Washe gari tun safe da k'arfe 5:15am ,,,Aisha ta tashi tayi share -share da wanke duk abinda su Inna"

"Saude suka b'ata. Bayan ta kamalla duk wani aiki da ya kamata ta yi,,, ta shiga kitchen ta d'ora musu breakfast alokacin ne aka fara kiran sallar asuba. Tana gama yin abinci ta shige toilet tayi wanka tare da yin alwala,,, ta fito shafa man shafi ga jikinta sannan tayi sallah ta shirya cikin uniform d'inta. Hak'ik'a uniform d'in sunyi matuk'ar karb'ar jikinta,,, tare da yi mata k'yau matuk'a. Bayan ta gama shiryawa ne"

"ta zauna tana karatun qur'ani cikin zazzak'ar muryata,,, saboda jiran ta shinsu Inna Saude...."

"Su Inna su ne basu tashi sai k'arfe 6:50am na safe. Suna tashi sukayi sallar asuba haka nan,,, kodayake"

"sallah ba damuwar tayi ba sai idan sun gadama suke yi. Asiya itama tayi wanka ta shirya cikin uniform d'inta,,, suna gama abinda suke yi suka nufi kitchen atare domin karyawa,, Inna Saude ta sa Asiya ta kira Aisha. Tana zuwa Inna Saude ta d'ebo abinci d'an kad'an wanda ko yaro d'an shekara bakwai,,, baya isar shi ta bata da yake Aisha tanada kud'i sosai a hannunta. Bata wani damu ba ta amsa tana murmushi,, su kam suka d'ibi abinci mai yawa. Suka nufi palourn domin suci abincin tare,,, itama ta nufi d'aki tayi bismillah tare da fara cin abincinta. Suma suka fara cin abinci babu ko bismillah,, suka tsakar cin abinci sai ga Aliyu ya fito daga d'akinsa domin ya yi breakfast,, ya zauna cikinsu su Asiya ya fara cin abinci. Haka suka cigaba da cin abinci har suka kammala,, bayan sun gama ne Inna Saude ta dube shi tace ""Aliyu ina"

"son magana da kai "".. Ba wani ladabi ko girmamawa..."

"Aliyu yace ""Ina jinki Saudatu fad'i maganarki ""...."

"""Dama akan maganar Aisha ce,,, da saurayinta Abbas "".Inna Saude tace..."

"Aliyu yace ""ki fad'amin idan zaki gayamin,,, ina sauri ne kin tsaya kina wani kwane -kwane "".."

"Inna Saude tace ""Hankalina bai kwanta da yaron nan ba,, domin ansha kawomin sukarsa da cewa d'an"

"iska ne. Babu abinda yake yi sai lalata da d'iyan mutane da yi musu ciki "".. ."

"Aliyu yace ""To naji karki damu,,, idan na dawo zanyi tunani da nazari akan maganar ""...."

"""To Aliyu "".Cewar Inna Saude...."

"""ke tashi kije ki kira Aisha,,, ta fito hakanan ku wuce zuwa makarantar boko "".Cewar Aliyu...."

"Asiya tace ""To Baba "".Tare da tashi tsaye tana yatsina fuskarta,,, ta wuce zuwa d'akin marigayiya"

Amina ...

"Tana zuwa babu sallama babu komai ta afka cikin d'akin,,, sai da ta tsaya tayi ma Aisha walak'antaccen"

"kallo,,, mai nuna hassada da bak'in ciki. Tace""keee!Jaka wawuya Baba yana kiranki,,, idan kin gadama ki fito "".."

"""To gani nan zuwa ""Cewar Aisha. Asiya taja mata mugun tsoki tare da wucewarta zuwa palourn.. Aisha"

"ta goya jikkar littafanta sannan ta fito,,, tasa ma d'akin padlock ta kulle domin gudun bincike bincike su Inna Saude. Ta kama hanyar zuwa palourn,, tana zuwa Aliyu yana ganinta ya tusa k'eyarsu waje. Bayan sun fita ne ya ba kowa d'ari biyar biyar domin ko zasu buk'aci wani abu,,, suka yi masa godiya yayi wucewarsa can wurin sana'arsa. Su kuma suka kama hanyar zuwa makaranta,,, Asiya babu abinda take yi saman hanyar illa zagin Aisha. Ita dai ko tanka mata bata yi balle ta kulata,, kunga jinin masifa da bala'i"

gadon mugun hali... .

"Al'amurra haka suka cigaba da gudana,,, cike da rashin imani da tsoron Allah a cikin wannan gida na"

"Aliyu. Haka dai suka cigaba da musgunawa rayuwar Aisha,,, shi kuma Abu ya cigaba da mu'amala da Asiya kamar matarshi ta sunna,,, da yake ta riga ta saba mu'amala da maza kala-kala kullum tana cikin d'akin Abu,,, suna abu guda shi baya gajiya itama haka bata gajiya ko sau nawa zaya kwanta da ita."

"Saude jakar uwa har yanzu batasan abinda ke faruwa da d'iyar ta ba,, wanda ta ci burin ta auri mai kud'i kuma ta kai budurcinta gidan mijinta.. Ina ko zata sani saboda k'wak'walwar kifi gareta,,, sannan bata sani ba komai zasu yi tako suke yi mata .Tare da siyo mata abin d'adi kullum irinsu nama, k'wai, ayaba, lemu, abarba da sauran kayayyakin dad'i. Da suke siyeta ita komi yake wakkana ba,,, saboda takkwalci"

da dak'ik'anci irin na Inna Saude....

********************

*BAYAN WATA GUDA*

"Maganin da Inna Saude ta amso ma Asiya na farin jini,,, wurin boka SIDDARU yayi kama saboda yanzu"

"zaka ga maza sun faka da motocinsu sunzo wurin Asiya wurin zance kuma mafi yawa daga cikin su duk da zina suke sonta bada aure ba,, haka ta ke basu jikinta suna sakar mata kud'i sosai. Tana ba Inna Saude kud'i ita kuma wawuyar doluwar uwa ko tambayarta,,, bata yi ina ta samo kud'i ne? Haka ta ke amshe"

"abinta ta kashe tana cin dad'i,,, haka dai al'amarin ya cigaba da tafiya...."

"Abangarensu Abbas da Aisha tun sati uku da suka wuce,,, ya daina kiranta sannan ya daina zuwa"

"wurinta.. Kullum kullum tayi kiransa amma baya receiving call d'inta,,, haka dai ta cigaba da kiransa tun abin baya damunta har yazo ya fara damunta tana shiga cikin tsananin damuwa da zullumi,,, allah sarki soyayya ruwan zuma ne in kasha ka ba masoyi. Wata rana idan ta kirashi sai dai taji wayarsa switch off,,, to ya zatayi ita kanta batasan ta damu shi ba sai yanzu

Please Login or Register in order to submit comment