You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi musu."

"Magajiya tace ""kowa ya ja tasa, su shiga d'aki. Suyi abinda suke so ""."

"Abu yace ""to magajiya, godiya mu ke ""."

"Abu ya ja Lado, suka shige d'aki, da 'yan matansu kowa biyu -biyu. Suka shige d'aki tare, kowa ya kama"

nashi 'yan matan biyu. Kowane da nashi d'akin........

********************

"A nan gidan Aliyu kuwa, Amina ce bayan ta gama abincinta na marece ta shiga toilet tayi wanka, bayan"

ta fito daga wanka. Tayi k'walliyarta mai kyau cikin atamfarta mai sirkin purple and green light.

"Tayi masifar kyau, cikin atamfar kuma ta karb'i jikinta. Saboda dama Amina k'yakk'yawa ce."

"Bayan ta kamalla, ta zauna tana kallon ta cike da kwanciyar hankali da walwala."

"Tana cikin parlor, tayi nisa da kallo. Can taji anyi sallama........."

"""Assalamu Alaikum, mutanen gidan ga "".Cewar Hadiza,cike da murnarta."

"Amina ta ce ""Amin Wa'alaikis Salam, murya wa na ke ji? Kamar Hadizanmu ""."

"Hadiza tashigo cikin parlorn, tana cewa ""nice Anti Amina, Amarya ""Ta fad'a cike da zolayar Antinta."

"Amina ta rungume 'yar uwarta, cike da farin ciki da murna."

"Ta ce ""k'anwatah ashe ana ganinku, na zata ba zaki zo ba, Har na fara fushi da ke. Ya gida, ya su mama"

"da baba? ""."

"Hadiza ta mik'a mata ledar da ke hannunta, sannan ta ce ""Ayyah Anti Amina, kiyi hak'uri da 'yar"

"k'anwarki. Wallahi ba laifi ba ne, Mama da Baba suke cewa basa son na faye takura miki. Kuma duk suna lafiya k'alau, sannan sun ce agaishe ki ""."

"""Mi ye abin takurawa, a cikin zuwa gidana. Ina amsawa, dan Allah Hadiza ki dinga zuwa lokaci -lokaci,"

"kina raina wallahi Kuma zaki dinga d'ebemin kewar gida "".Cewar Amina, cikeda da murna."

"Hadiza ta ce ""Insha Allah, zan dinga zuwa akai -akai kuma munyi magana da Mama Ta amince zata barni"

"ina zuwa, lokaci -lokaci. Saboda haka karki damu 'yar uwa ta ""."

"Amina ta ce ""Mi yake cikin ledar da aka kawo min, ko kayan dad'i ne? "",,,ta fad'a cike da tsokana."

"Hadiza tayi murmushi, sannan ta ce ""diba ki gani mana, Mama ce ta ce akawo miki. Hmmm,,,abin dad'i"

"ya wuce, abinda kike ci lemu, abarba da ayaba da sauran kayayyakin dad'i ""."

"Amina ta bud'e ledar, taga kayayyaki irinsu, aya, dabino, madarar gwangwani, kwakwa, humra mai"

"k'amshi, sabulun wanka mai shegen k'amshi, da dai Sauran abubuwan buk'ata na mata."

"Amina, bayan ta gama dubawa ta ce ""Amma ko naji d'adi wallahi, Allah ya saka da alkhairi. Ki ce Mama"

"na gode k'warai da gaske, Allah ya k'ara bud'i na alkhairi .Tashi ki shiga kitchen ki d'ibi abinci ""."

"""Amin Anti ""Cewar Hadiza."

"Ta tashi ,ta shige cikin kitchen zata ta d'ebo abinci taci."

Bayan ta shige cikin kitchen domin ta d'ebo abinci ta ci.

"Tana shiga ta d'auki plate d'aya, ta d'ebo abinci shinkafa ne da sphagetti da stew, da naman kaza."

"Ta ciko plate d'inta fam da abinci, ta je wurin fridge. Ta d'auko hollandia da swan water, ta nufi wurin"

anti tah a parlorn.

"Bayan ta shigo parlorn, ta samu wuri ta zauna ga kujera."

"Amina ta dubi Hadiza, da murmushi tace ""Acici kin ciko plate ko da abinci, to maza ki cinye dukah ""."

"Hadiza ta fara cin abincinta, sannan ta ce ""bari inci abina, in bak'e lokac........."

"Kafin ta gama k'arasa maganar anyi musu sallama,,,,,,"

"""Salamu Alaikum""Cewar maimuna (k'awar Aminatu ce tun suna yara, tare suka tashi, da yin wasa tare da"

juna).

"""Amin Wa'alaikis Salam "".Cewar su Amina."

"Maimuna ta shigo har cikin parlorn, ta samu wuri ta zauna."

"Amina tace ""sannu da zuwa, dama kina hanya maimuna .shine baki sanar dani ba ""."

"""Yauwa kedai Amina, nima hanya ce ta biyo da ni gidanki "".Cewar Maimuna."

"""Ina wuni Anti Maimuna ""Cewar Hadiza tana murmushi."

"Maimuna ta kalli Hadiza, tana murmushi, tace ""Lafiya k'alau Hadiza, Acici 'yar k'anwarmu ""."

"Hadiza tayi murmushi, cikeda kunya tana duk'e kai tana cigaba da cin abinci."

"Amina tace ""Maimuna ya labarin duniya, da jin d'adin ki, cike da farin ciki. Ta tashi, ta bud'e fridge ta"

"d'auko maltina da ruwan swan water, ta aje agaban Maimuna."

"""Godiya nake k'awata, amma jin dad'i na gare ku Amare. Cewar Maimuna."

Maimuna ta d'auki ruwan ta sha.

"""Anti bari a d'ebo miki abinci ko? "".Cewar Hadiza."

"Maimuna ta ce ""Alhmdlilahi wallahi a k'oshi na ke k'anwarmu ""."

"Amina ta bushe da dariya, tace ""kwaji da iyayinku, ni dai kam ""."

"Maimuna ta ce ""ba wani iyayi, sai gaskiya. Da ta karrama ni da abinci, keda zallar ruwa kika kawo mini fa"

"""."

"Amina tace ""yayi muku kyau da munafurcin ku. Wato ni ban karrama ki ba ko "".Tana fad'a tana dariya,,,,,"

"Maimuna ta ce ""Mun dai jiya, munafurcin ma iyawa ne, kin gane ko ""."

"""A'a ban gane ba, ku dai kuka iya "".Cewar Amina."

"Hadiza ta ce ""Su Anti dai acigaba da sha'ani kawai ""."

"Amina da Maimuna suka fashe da dariya. Hadiza ta shige cikin d'aki, ta barsu suna fira cike da nishad'i da"

jin d'adi sosai.........

**********************

"Acan gidan Magajiya, su Abu ne suka fito daga cikin gidan. Cike da nishad'i."

"Suna tafiya suna fira, Abu ya kalli Lado ya ce""kasan wani abu, yau fa garau nake ji na Saboda gaskiya"

"haraka tayi dad'i kuma na samu sugar baby, mai d'and'ano ""."

"Lado yace ""ni ma haka, yau na shana sosai da kasancewa cikin jin dad'i. Amma sha'anin akwai dad'i sosai"

"wlh ""."

"""Abin ba'a cewa komai, sai godiya. Cewar Abu, cike da rashin kunyarsu da mummunar d'abi'ar su."

"Haka suka isa kamo hanya, suna tafiya cike da shed'anci da rashin kunya."

"Duk wadda suka gamu da ita, in dai budurwa ce. Sai sun taru sun matse ta, suna shafar jikinta da duk"

inda ya birge su. Tare da yi ma d'iyan mutane kiss. Haka suke tafiya har suka isa gidanjensu.

Sannan kowa ya kama gabansa.....

********************

*BAYAN KWANA BIYU*

"Su Inna Harira, sun sayi gidan har da takarda da shedu kuma an sheda."

"Gida ne, na jar k'asa. Anyi masa plaster da sumunti, yanada girmansa dai -dai gwargwado. Yana da"

k'yawon sa.

Gidan d'akuna hud'u gare sa da falo sai toilet biyu da kitchen biyu. Haka su Inna Harira suka saka 'yan

"haya, mutum hud'u duk wata #5000 ne ga kowane mutum d'aya da matarsa da yara. Idan kanada su."

"Sai da suka biya Inna Harira kud'i hannu cash, sannan ta bari suka shiga gidan hayan."

Sai da ta aza musu dokokin kada abar mata gida da k'azanta da rashin tsabta.

Su Saude har sun fara sana'ar saida kayan miya. Kuma suna samun riba sosai.

"Karuwanci da tantiranci, na amshe mazan mutane kud'i sai abinda ya cigaba."

"Ayayinda Saude ta tsaya, ruwan ido ta k'i ta shafa maganin balle ta samu mai sonta."

"Kowane namiji ta gani, sai tace ""baiyi mata ba "".Alokacin da suka ga kud'i sun fara zauna musu sai rashin"

mutuncinsu da zaluncinsu ya k'aru fiye da lokacin da.

"Haka suke gudanar da rayuwar su, kamar ba zasu mutum ba, sun riga sun k'ulla abota da shed'an. Ko"

k'adan basa tunanin lahirarsu da abinda zasu isko.

"Su dai duniya kawai, suka sama gaba a rayuwar su."

"Cin amana, zalunci, rashin kunya da rashin mutunci, bin bokaye da 'yan bori, zinace -zinace da had'a"

husuma. Sun mayar da su kamar ruwansu.

"Sallah akodayaushe bata dame su ba, sai sun gadamar yinta sukeyi. _(Ni kaina ina mamakin rayuwar"

"gidansu Inna Harira, ina cewa Anya kuwa suna tuna mutuwa? anya suna tuna kwanciyar kabari, anya suna tuna hisabi da busa k'ahu.? Aranar da mace mai ciki zata haifi abinda ke cikinta, aranar da mace zata guji mijinta shi ma mijin ya guje ta,aranar da d'a ko d'iya zata ga uwarta ta shek'a, aranar da d'an uwa zaiga d'an uwansa ya gudu. 'Yan uwa muji tsoron Allah, mu tuna zamu mutu abinne mu daga mu sai halinmu. Duniyar ce dole mu barta ko muna so, ko bama so. Allah ubangiji ina rok'on ka, kasa mu cika da"

"imani da imani, mu mutu. Muna musulmai)._"

"Inna Harira ce, zaune tare da d'iyanta suna k'idayar kud'in da suka samo wurin yawon karuwancinsu."

"Sai ga Abu ya dawo, ba sallama. Balantana gaisuwar kirki.."

Ya samu guri ya zauna kusa gare su.

Ya ce Inna Harira.........

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_Story and written by Mugirat Musa_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_'Diyana, farin cikin rayuwata. Kusani ina matuk'ar k'aunar ku a cikin zuciyatah._"

_Aisha yasmin Bilyaminu_

_Maryam Bilyaminu_

*PAGE* 71-75

"Abu ya ce ""Inna Harira, nima abani kud'i in samu abinda Zansa ma aljihuna."

"Inna Harira tadubeshi, tace ""kamar ya in baka kud'i, mi zaka siya mai amfani idan aka baka kud'in? ko"

"kuwa so kake a baka kud'i ka kashe ga banza ko? ""."

"Abu yace ""kamar ya nakashe kud'i ga banza, ke komai na ki sai kinyi ma mutum gori. Sannan ki bashi"

"abinki da kuma shegen bak'in jinininki da kwakwazo, in kina bani ki bani kawai "",Abu ya fad'a cike da hasala."

"""Ba za'a ba ka ba, wawan yaro kawai, kai bakasan zafin neman kud'i ba, za kazo kace a baka kud'i, kana"

"damun Inna da batun banza"".Cewar Laure ta fad'a, tana hararar Abubakar."

"Inna Harira tace ""Waye ya saka bakinki? , ke kuma ina ruwanki da shiga maganarmu .Ba abinda ya shafe"

ki........

"""Inna Allah ya baki hak'uri ""Cewar Saude."

"Inna Harira ta ce ""Amin idan da gaske kuke, ai tasan batada gaskiya. Shiyasa tayi shiru ""."

"Laure ta mik'e tsaye, tace ""to Inna ayi hak'uri, bana sake tsoma bakina cikin lamarinku, ke da Abu ""."

"Ta sa kai, tayi shigewar ta d'aki."

"Saude dai ma tamik'e, tace ""Na barku lafiya, ayi lafiya ""."

"""To Allah ya sa ""Cewar Inna Harira."

"Itama Saude tashige cikin d'akin, taba Inna da Abu fili."

"Bayan sun shige d'aki, Inna Harira ta maida kallon ta ga Abubakar."

"Sannan Inna Harira, tace ""fad'amin kaman nawa ka ke so?D'an Inna karka ji komai ""."

"Abu ya k'ara marairaicewa, kamar mace yace ""ko dubu shida ne, ina so insa a aljihuna ""."

"Inna Harira ta d'aga zanen ta, sai ga siket d'inta na sawa ga jiki ya bayyana, samansa akwai 'yar jikka ta"

d'aure irinta mutanen da.

"Ta d'auko kud'i, ta k'irga naira dubu dubu guda bakwai,"

ta bashi.

"""to ga kud'in nan, ka Lallab'a da su. kayi maneji har akoma samun wasu kaji Abu nah "".Cewar Inna Harira."

"Abu ya amshi kud'in cike da murna da farin ciki, yace ""Allah ya bar mana ke Inna. shiyasa nake masifar"

"sonki, saboda duk abinda nake so kina min""."

"""Amin amin Abu, idan banyi maka ba, tunda ina dashi. Wa zanyi ma "".Cewar Inna Harira."

"Abu yace ""haka ne kam gaskiya, to ni zan fita yanzu nan ""."

"Inna Harira ta ce ""baka bari ka ci abinci ne ""."

"""Na ci a waje mana, karki damu Innata "".Cewar Abu."

"Ya sa kai, yayi wucewarsa waje........"

*********************

"Acan gidansu Aliyu, bayan Maimuna da k'anwarta Hadiza sunyi wucewar gida."

"Tad'ora tukunyar abinci na dare, bayan ta kamalla ta shiga wanka."

"Tana fitowa daga wanka, tayi k'walliyarta mai kyau. Tashirya cikin wata doguwar riga bak'a mai flower"

pink da aka yi mata k'walliya da shi.

"Tayi kyau, kuma rigar ta k'arb'e ta. Ta feshe jikinta da turarurka."

"Tajera ma mijinta, kulolinsa saman ledar k'asa."

"Tasamu wuri ta zauna, tana kallonta."

"Tana tsaka ga kallo, sai ga sallamar mijinta."

"Ta mik'e ta amshi jikkar da ke hannunsa, tare da ledojin da ya shigo da su. Ta amsa sallamar shi tare da yi"

masa sannu da zuwa.

"""Yauwa ya gida. Ya hidimomin gida da kad'aici? "".Cewar Aliyu cike da raha."

"Amina tayi murmushi, tace ""lafiya k'alau, kuma Alhmdlilah. Ai su Hadiza da Maimuna sun zo,"

"tawuce wurin fridge, ta d'auko masa ruwa masu sanyi ta kawo masa."

"Yad'auka yasha, bayan yasha ya ce Alhmdlilah, dama kince k'anwar mu Hadiza da k'awarmu sunzo. To"

"abani tsarabar da suka kawo mana ""Ya fad'a cike da tsokana."

"Amina tace ""Sun dai kawo mana ziyara, dama mi kake so su kawo mana ne? ""."

"""Ai kuwa sun kyauta, saboda ba su bar min matata cikin kewa ba. Allah ya basu ladar zumunci da kulawa"

""".Cewar Aliyu."

"Amina ta ce ""Amin farin cikinah, ai sun k'yauta min wallahi. Ta shi muje kayi wanka, sannan kazo ka ci"

"abincinkah""."

"Ya ce ""to Aminatutah, farin cikin rayuwata "".Ya mik'e suka jera tare cike da farin ciki da k'aunar juna."

"Bayan ya fito daga wanka, ta shirya shi."

"Ta jawo shi parlorn, tasa masa abinci suna ci tare. _(Allah ubangiji ya ba mu mazajen k'warai, wad'anda"

zasu so mu tsakani da Allah. Ba domin wani abu ba. Ameen)._

********************

"Acan gidansu iyayen Amina, bayan Hadiza ta koma gida. Ta iske babanta da mamanta suna fira."

"Tayi sallama, suka amsa mata."

"Bayan ta samu wuri, ta zauna."

"Tace ""Washhhh,,,,, wallahi na gaji sosai ""."

"Baban ya ce ""Hadiza kinyi k'ok'arin ziyara ai, wai shin kinyi wani aikin ne can? ""."

"Maman Amina ta cafke maganar ,tace ""ba wani Aikin da tayi ragganci ne da son jiki irin na Autah, ko"

"ak'asa kika zo ne? ""."

"Hadiza ta duk'e kai, tana murmushi tace ""A'a Mamanmu, ba'a k'asa na zoba. Saman mashin nazo, Anti ta"

"bani kud'i naira d'ari da dubu ukku da kuma wasu abubuwa wai in kawo muku ""."

"Maman Amina tace ""kaji d'iyarka ko, dama nasan ba'a k'asa tazo ba, son jiki ne irin nata ""."

"Baba ya ce ""Ai tayi k'ok'arinta Salamatu, saboda ziyarar da takai ko Hadiza. Allah yayi miki Albarka."

"Hadiza da Mama suka ce""Amin "".Ta ba Mama kud'in da ledar da ke hannunta."

"Mama ta ce ""ma baba ga su, """

"Yace mata ""A'a su aje wurin su, suna samun na kashewa, Shi yanada kud'i cikin aljihunsa""."

"Mama ta ce ""babu komai ai ""."

"Hadiza tashige cikin d'aki, zuwa wanka."

"Mama ta tashi, tana wasu gyare -gyare."

"Baba shima, ya shige cikin d'akinsa........"

********************

"Acan kuma bayan Abu, ya amshi kud'i wurin inna Harira. Direct wurin abokinsa Lado ya wuce."

"Bayan ya zo saman benchi, k'ofar gidan su Lado. Yasamu yaro ya aika domin akira masa Lado."

"Bayan Lado ya fito tare da yaron, Abu ya bashi naira ishirin. Yaron yayi godiya ya wucewarsa."

"Lado yakalli Abu, yace ""shegen bisa, ina ka samo mana kud'i ne, har da wani yin k'yautar naira ishirin ""."

"Abu yabushe da dariya, sannan yace ""Ai kai dai bari, shege shi ke maganin d'an iskah fa .Ai ina zuwa gida,"

"na iske su Inna Harira suna k'idayar kud'i .Shine na nuna mata kud'i na ke so, har Innata wadda ta haife ni ta nuna mata kada a bani. Wai bani iya maida taro sisi wai, har da fad'a sai da Inna Harira tayi mata .Ta"

"ce ina ruwanta ""."

"""Kai abokina, hak'ik'a na k'ara tabbatarwa Inna Harira tana sonka sosai, wani abu sai kakah "".Cewar"

Lado.

"Abu yasa hannu a aljinhunsa, ya d'auko kud'i dubu bakwai. Yace ""maganarka gaskiya ne Lado, Inna"

"Harira na sona sosai. Kama gani dubu bakwai ta bani duk da dubu shidda na rok'eta ""."

Lado yayi kuwwa irin na tantiran 'yan iskah.

"Yace masa ""Yau akwai sha'ani babah, zamu yi haraka sosai fa ""."

"Abu ya ce ""haka ne, tashi muje can gidan magajiya, mu sha shagalinmu ""."

"""Hakan za'a yi fa ""Cewar Lado, ya mik'e tsaye."

"Suka kama hanya, suna tafiya suna fira. Cike da nishad'i da jin d'adin su."

*********************

"Acan gidansu Inna Harira, bayan ta fita unguwa."

"Saude ce zaune tare da Laure, suna hayaniya akan kud'i."

"Ayayinda Saude take cewa ""yaya Laure duk ita ta b'ata Abu da shegen son kud'i. In ba shi ba, ya za'a yi"

"mu da wahala ana d'aukar kud'i ana ba wannan shegen d'an naki, mara tarbiya. B'ataccen banza ""."

"Laure ta dubi Saude ta ce ""Amma Saude kin bani mamaki, ban tab'a zaton irin wad'annan maganganun"

"zasu fito a bakinki ba. Dan buro uba bakiji abinda nace ma Inna ba alokacin da zata bashi kud'in ba, ba"

"gabanki aka yi komai ba. Miyasa da Inna na nan bakiyi magana ba sai yanzu?Kuma kike cewa Abu shege ne, ai ke ma shegiyar ce ""."

"Saude ta ce ""Ai gani nayi mu ke zuwa muna bada jikinmu sannan abamu kud'i, da kike cewa ni shegiya ce"

"ai gara ni, saboda ubana yana raye, Keda kika sa aka kashe uban d'iyan ki fa? ""."

"""Zanci buro uban ki Saude, ke karki raina min da wayo, ke kad'ai kike zuwa neman kud'in ne? Da kike"

"cewa nasa ankashe uban yarona, Ni kad'ai ce nasa ko har da ku "".Cewar Laure cike da masifa."

"Saude ta ce ""Ai d'an ki ne, aka d'auki kud'i masu yawa Inna ta bashi""."

"Laure ta ce ""Ai to kisan Innah ta bashi zaki zo kina min maganar banza da wofi "",,,,,,,"

"Saude ta ce ""Dole inyi magana, saboda ina da hak'k'i akan ku........"

"Kafin saude ta k'arasa maganar, sai ga Inna Harira ta shigo, ta katse ta, tana cewa ""ke!!! Saude bana son"

"rashin kunya da rashin mutunci, Laure ba yayarki ba ce ba, Da zaki tasa ta gaba da cin mutunci. Miyasa bakida dangana a rayuwarki ne, koma miye baki bari in dawo gida. Sai ki fad'a min""."

"Saude ta ce ""to ba ita ba ce..........."

"""Ita ce mi? bana son d'iban albarka, waye ya tambaye ki, Laure mi ya faru Mi yahad'aku fad'a ke da 'yar"

"uwarki? "".Cewar Harira."

"Laure ta kawo bayanin komi, ta fad'a ma Inna Harira."

"Inna Harira tace ""Wai ni galma, Allah ya had'a mu da 'yar iskar yarinya. Da kike cewa Laure ta kashe 'Dan"

"Ladi so kike ki tona mana asiri .Asani mu ka kashe shi, 'd'iyar banza kuma kud'i cikin nawa ne na d'auka na ba Abubakar. Ba na ku ba, saboda haka kada in sake jin an tada maganar, bata hak'uri ke Saude""."

"Saude ta ce ""Inna kiyi hak'uri, na d'auka kud'in Mune. Yaya Laure Allah ya baki hak'uri kuma ya huci"

"zuciyarki ""."

"Laure tace ""Babu komi ai, ya wuce amma atunani nah, Ko ke da kud'i ke mai iya d'auka ne ki bashi ""."

"Inna Harira ta ce ""Tabbas maganar ki haka yake gaskiya. Saude ki dinga tunani da nazari, bakida wata"

"'yar uwa da ta wuce Laure haka itama, ki dinga aiki da tunani, shin idan ba nan wata rana bazaku had'e kanku ba? ""."

"""kiyi hak'uri Inna, bazan k'ara ba "".Cewar Saude."

"Inna Harira ta ce ""na yi kema Laure, ki daina biye mata. Babba hak'uri a ka sani da shi ""."

"Laure tace ""to Inna ayi hak'uri, ni ma bazan k'ara ba ""."

"Inna Harira ta ce ""naji dad'i sosai, dama haka nake son ji daga gare ku. Ayi hak'uri da junan ku ""."

Haka Inna ta kama yi musu fad'a da nuni da hak'uri da junansu. _(Na koma gefen ina mamakin Inna

"Harira, ashe shegiyar matar tasan miye kalmar hak'uri Duk abinda ta ke yi iya shege ne da iskanci, da rainin wayo)._"

"A haka dai, Inna Harira ta sa su gaba da fad'a da nuna b'acin ran ta akan abinda Saude ta aikatah."

Saude hak'urin da taba su yafi a k'irga...........

"_Ku cigaba da bi na, sannu a hankali Ni Mugirat._"

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*Hak'ik'a so gamon jini ne, jinina ya had'u da na ki, Soyayyar mu daga Allah yake, Halira Aliyu (Maman"

Abdul)*_ D'D'D'D'D'D'

*PAGE* 76-80

"Inna Harira tayi musu fad'a sosai, tare da nuna tsananin b'acin ran ta."

"Abu da Lado kuwah, direct gidan Magajiya suka nufa."

"Bayan sun je can, suka zab'i wad'anda suke ra'ayi daga cikin karuwan na gidan. Suka shige cikin d'aki da"

'yan matan su.......

*WASHE GARI*

"Da k'arfe 11:00am na safe, bayan Amina ta gama duk ayyukanta na safe, Sai Aliyu ya kira ta zasuyi bak'i,"

Malam Adamu da Matarsa Hussaina suna nan tafe yau. Saboda haka gashi nan dawowa daga kasuwa.

"Bayan ya dawo, ya siyo kaji ukku da kayan miya da sauran abubuwan buk'ata na gida."

"Amina ta aza dahuwar abinci, kaji ta fara soyawa, bayan sun soyu tasa cikin wata kula mai kyau."

"Tayi musu sakwara da miya taji kifi sosai, k'amshi duk ya mamaye gidan da k'amshin abincin ta."

Bayan ta kamalla tasa cikin kuloli irin wad'ancan suma masu k'yau.

"Ta kawo komi ta jera, saman ledar tsakar parlorn."

Aliyu ne ya taya ta gyara kitchen da kuma wanke-wanken kayan da suka b'ata.

"Bayan sun gama komi, suka shiga wanka tare da shiryawa tare."

"Amina atamfa tasaka light blue and red, tayi light make up d'inta."

"Shi kuma Aliyu, shi ma shadda yasa light blue anyi masa aiki da zare dark blue."

"Masha Allah, duk sunyi k'yau sosai. Dama k'yawo ne ya had'u da k'yau."

"Suka samu wuri, suna ta fira cike da nishad'i da jin d'adi."

"Bayan wasu 'yan mintuna, sai ga Adamu da matarsa Hussaina sunyi musu sallama."

"Aliyu da Amina suka amsa musu tare da yi musu, sannu da zuwa."

"Suka yi musu iso, bayan sun gaisa sannan suka yi musu iso zuwa wurin abincin da suka girka."

"Bayan sun zauna ne, Amina tayi serving d'in su abinci. Suka yi bismillah tare da fara cin abinci cike da"

natsuwa.

"Bayan sun kammala, cin abinci ne. Amina ta ce ""Hussaina ta so muje, cikin d'aki muyi fira can. Sai mu bar"

"musu nan su tattauna ""."

"Hussaina ta ce ""to hakan yayi k'yau ""."

"Adamu yadubi Amina, sannan yace ""babu inda zakuje, komi zakuyi kuyi gabanmu. In ba salon gulma ba"

"da munafurcinku na mata"".Ya fad'a cike da tsokana da barkwanci."

"Amina tayi murmushi tace ""to matsi bakinmu, ina ruwanka ne wai. Bama son sa ido fa ""."

"Aliyu ya ce ""karka takura musu, ai gara su keb'e saboda su zanta da juna. Muma muyi namu fira ko? "".Ya"

fad'a yana murmushi.

"""Kaifa Aliyu na lura da kai baka son atab'a maka Amina 'yar gaban goshinka. Ji yanzu nan ka wani chafke"

"magana, kana wani juya ta "".Adamu ya fad'a da murmushi."

"""Eh ai ba komi, kasan bana son abinda zai tab'a ran Aminatutah, abinda take so shi na ke so, abinda bata"

"so bana son shi. Ba juya magana nayi ba har da lank'wasa nayi "".Cewar Aliyu cike da jan magana."

"Adamu yace ""yayi maka k'yau, kayi k'ok'ari ai ""."

"Amina ta dubesu, tace ""mu dai zamu shiga ciki ""."

"Itama Hussaina ta ce ""Lallai kam, idan kun gama dramar, zamu dawo, Baban Amir ka kirani a waya ""."

"""ba zan kiraki ba, idan na tashi wucewa ta zanyi "".Adamu ya fad'a."

"Hussaina ta ce ""to kafi jirgin sama tashi da gudu ""."

"Suka fashe da dariya, gaba d'ayansu."

"Amina da Hussaina, suka shige cikin d'aki."

"Bayan sun shige d'aki, Adamu ya dubi Aliyu duba ta natsuwa da fahimta."

"Yace ""Amma abokina kayi dacen mata ta gari, ga tarbiya, natsuwa ,hankali, k'yau, tsabta, uwa uba kuma"

"ta iya girki sosai, daga ganin yadda ka koma ansan kana cikin kwanciyar hankali sannan ka k'ara godema Allah da yabaka mace saliha abin so ga kowane d'a namiji ""."

"Aliyu yace ""Ai Adamu kullum cikin godema Allah nake, hak'ik'a nayi dacen matar k'warai mai ado da iya"

"kwalliya, sannan akodayaushe ta ganni ina farin ciki shine gurinta. Shiyasa nake matuk'ar gudun b'acin ran ta da kuma nuna mata kulawa da soyayya, aduniya baya ga iyayena babu wadda nake k'auna kamar Aminatu, saboda ita tana kulawa da ni sosai ""."

"Adamu ya ce ""Haka ne maganarka Aliyu, yanzu idan mutum ya samu mace tagari yagodema Allah domin"

"itace jin dad'in duniya, Sau da yawa zakaga wasu basuyi dacen mata ba, za kaga wasu matsaloli suna ta bayyana daga baya. Bayan anyi auren ""."

"""Haka ne kam gaskiya, da ni da kai munyi dacen mata na gari. Saboda kaima nasan matarka batada"

"matsala "".Aliyu ya fad'a."

"Adamu ya ce ""Hussainatah batada matsala kam, Allah ya k'ara rufa mana Asiri duniya da lahira ""."

"Aliyu ya ce ""Amin amin abokina ""."

Suka kama firarsu cikeda da walwala da nishad'i.

**********************

Acan cikin d'akin kuma.

"Hussaina ce ta dubi Amina, ta ce ""Aminatu kin ganki kuwa, kin canza kin k'ara k'yau sosai wlh. Daga"

"ganin ki ansan bakida matsala, agaskiya Aliyu yana matuk'ar k'aunar ki da kuma kulawa da ke ""."

"Amina tayi murmushi, sannan tace ""wannan zigin fa, har da cewa na k'ara k'yau. Ai dama da k'yawo kuka"

"aure ni "".Ta fad'a cike da tsokana."

"""Ba wani da k'yawon ki muka aure ki, kin san baki kai haka ba alokacin da kina gida. Sannan ga wata 'yar"

"k'iba ta hutu da ki ka k'ara "".Cewar Hussaina tana dariya."

"Amina tace ""naji to, kun iya kulada iyali""."

"Ta mik'e tsaye ta bud'e drawer, ta d'ebo ma Hussaina kayayyaki irinsu sabulun wanki da na wanka da"

"turaren wuta da na d'aki, ta saka cikin bak'ar leda."

Ta ba Hussaina.

"Hussaina tace ""har da d'awainiya haka, Aminatu? ""."

"Amina ta ce ""ba ke na ba ba, d'ana Amir naba ayi masa wanka da wanki. Ina Amir d'in ya ke da baki zo da"

"shi ba? ""."

"""Amir godiya yake Amina, yana can gidan su babansa. Kinsan na yaye shi tunda dad'ewa shiyasa banzo"

"da shi ba "".Cewar Hussaina."

"Amina ta ce ""Allah sarki, Allah ya raya mana Amir, hakan yanada k'yau gaskiya ""."

"Hussaina ta ce ""Amin ya Allah ""."

Ahaka suka cigaba da firarsu cike da nishad'i da shak'uwa.

"Bayan sun jima sosai a gidan, sai Adamu ya kira matarsa awaya ta fito su wuce zuwa gida."

"Ta fito, Amina da Aliyu sukayi musu rakiya har waje. Suka tara musu mota har gida. Aliyu ne ya biya"

drivern kud'in sa.

"Bayan wucewar su, suka koma gida suna mai tsananin farin ciki da murnar wannan ziyara da suka kawo"

musu............

**********************

"Acan garin Shiko kuma, su Inna Harira da su Saude kud'i sun zauna musu sosai. Saboda ga kud'i duk wata"

"na haya dubu ishirin, ga saida kayan miyar da suke yi, suna samun riba sosai ga kuma na yawon karuwancinsu."

"Ahaka dai suke gudanar da rayuwar aurensu, amma fa

Please Login or Register in order to submit comment