You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun biya. Komai cikin girmamawa da sanin darajar d'an Adam,, haka dai aka tsaida lokacin biki nan zuwa wata guda suka dawo gida. Haka dai rayuwar ta cigaba da gudana har lokacin biki ya kawo,, sunyi walima da dinner domin su ba mutane ba ne wad'anda suka fiye k'arya ba. Aranar assabar ne dubban mutane suka sheda d'aurin auren Umar Haruna Mai turare da amaryarsa Rabi'atu Iliyasu,,dubu akan sadaki hamshin. Anyi taro lafiya an watse lafiya amarya ta tare gidan mijinta,, suna gudanar da"

zamantakewar su cike da tsananin k'aunar juna da soyayya da zaman lafiya.

"To bayan auren Khalifa da wata guda,, Alhaji Haruna ya kira Ahmad ya tambayesa ko ya fitar da mata,,,"

"ya nuna masa har yanzu babu wadda ya keso. Alhaji Haruna ya sallameshi tare da sanar da shi sun samo mai mata kuma bada dad'ewa ba za'a yi aure ba,,, saboda haka duk wadda ya samu a matsayin matarsa to ya rik'e ta hannu bibbiyu. Saboda gaskiya sun bashi dama kuma ya tsaya ruwan ido,, Ahmad ya nuna masa babu damuwa zai kasance mai biyayya agaresu,, matuk'ar abinda suka umurceshi bai sab'ama Allah ba. Hak'ik'a yayi matuk'ar jin d'adin kalamanshi tare da sanya mishi albarka,, Ahmad yayi farin cikin"

"da albarkar da yasa masa. Alhaji Haruna ya sallame shi,, shi ma ya juya cikin gida.."

"Tun daga wannan lokacin ne familynsu Ahmad,,, suka fara shiryen shiryen biki har Allah ya had'a Alhaji"

"Mahmud Umar da Aisha a cikin Kamba,, yana yawan ganinta ne idan ta taso daga islamiya,,, yayi matuk'ar bincike akanta sosai kuma ta bashi matuk'ar tausayi.Kuma alokacin farat d'aya ta shiga zuciyarshi,, har dai ya had'u da Malam Adamu yana tambayarsa game da Aisha. Hak'ik'a a wannan ranar Malam Adamu yayi murna sosai domin kuwa yasan Allah ne ya tausayawa rayuwar Aisha. Ya bata miji na"

"bugawa a mujalla kuma d'an babban gida,, kunji yadda auren Ahmad da Aisha ya kasance...."

"Abangarensu Saude kuma suna nan suna k'ara axabtar da Aisha,,, tare k'ara musgunawa rayuwar ta."

"Lado ma ya takura mata sosai saboda kullum sai yazo fira ya dameta da surutun shi,,, kamar ya lasheta saboda naci da son mata. Malam Aliyu yana lura da duk abinda Saude takeyi ma Aisha,, sai dai ya shige cikin d'akinsa yana hawayen k'unci da bak'in cikin rayuwa. Tare da nasanin auren Saude yana kuma rok'on Allah ya bayyana masa komai game da Saude,, shi kansa yana ganin taskon walak'ancin Saude. Saboda bata ganin girmansa balantana ta daraja shi,, kullum cikin iko da mulki take masa kuma shi da gidansa. Akwai wata rana da ta sameshi akan maganar Lado yaga d'iyarsa yana so wato Aisha,,, sai ya tuna maganar da sukayi da Adamu akan kada abari Saude tasan cewa Aisha an d'aura mata aure. Ya nuna ya amince zaiba Lado auren Aisha amma sai ta gama makaranta da wata biyu,, sai ayi auren wawuyar doluwa Saude taji dad'i sosai domin harta d'auka da gaske ya ke. Ashe ita bata sani ba kafin kaga biri,, biri ya ganka kuma komai dabararka da wayonka wani ya fika su. Haka dai zamantakewar"

rayuwar gidansu ke tafiya cike da rashin imani da tausayi....

"Acan cikin d'akin Abu kuma,, Abu ne rungume da Asiya saman jikinsa. Idan kaga yadda suke saika rantse"

"da Allah miji da mata ne,,, saboda kayan da ke jikinsu kamar tsirara suke. Kuma haka suke mu'amalar su babu dare babu rana,, babu safiya babu maraice kullum suna cikin abu guda. Ko gajiya basa yi da juna kamar manyu,, ita dai Asiya bada Abu kad'ai ta ke mu'amala ba da kowa yi ta ke. Amma tafi yi da Abu sosai fiye da sauran,, yanzu da ta ke kwance a jikinsa basu dad'e da gama yin abinda suka saba ba."

"Wannan kusan na biyu kuma a yau ko yanzu tsayawa hutawa sukayi,,, kafin su cigaba da yin iskancinsu. Yanzu idan kaga yadda Asiya ta zama sai kayi mamaki,, saboda duk ta k'ara zama babbar macce komai ya k'ara cikowa nata. Kodayake ba abin mamaki ba ne ga macen da ke mu'amala da kowane namiji. Abu ya shafin k'irjinta yace ""Baby in ji dai ni kad'ai ne,,, kike ba jikinki zanyi bincike in gani. Idan na samu labarin"

"kina mu'amala da wani sai na kasheshi,, sannan in kasheki in kashe kaina saboda kishi "".."

"Sai da gaban Asiya ya bada ""rassssss "".Da k'arfi cikin dauriya tace ""ya za'a yi muna tare da kai,, nayi"

"mu'amala da wani kuma komai na ke kana yi min gwargwadon iyawarka. Sai idan baka yarda dani ba kana iya bincike "".."

"Abu yace ""kiyi hak'uri masoyiyata,, na yarda da ke kinsan inada zafin kishi kuma bana son wani ya shiga"

"cikin gonata ""..."

"Asiya tace cike da kissa da makirci ""kaima kasan ina tsananin son ka,, ya za'a yi na yarda da wani idan ba"

"kai ba. Kuma babu wani a cikin zuciya ta sai kai ""."

Abu yaji matuk'ar dad'in maganarta har cikin zuciyarsa...

"Yace ""wasa na ke miki karki damu ba wani bincikewa da zanyi kinji "".Tare da sake rungume ta yana"

kissing d'inta a ko'ina na jikinta...

Asiya ta ji sanyi har cikin zuciyarta...

"Tace ""thank you so much my love,, ka sani ina matuk'ar k'aunarka a rayuwata,,, da kuma son kasancewa"

"da kai har abada ""."

"""Nima haka ina sonki har cikin xuciyata "".Cewar Abu tare da cire mata kaya,, suna aikata masha'arsu"

suna nishin dad'i..

"Washe gari da safe misalin k'arfe 10:00 am na safe, su Lubna ne da Kubra suka kawoma Asiya ziyara har"

"gidansu. Ta siyo musu tsire da lemun k'walba mai sanyi,, bayan sun gama ci ne sai hira ta b'arke a tsakanin su..."

"Kubra ta dubi Asiya tace ""Asi baby mun bar jinki kwana biyu,, lafiya dai ko kin daina haraka ne? "".."

"Lubna tace ""ai shi ne ko kinyi kud'i ne bamu sani ba? ""."

"Asiya tace ""Hmmm lubcy da kuby ba zaku gane ba,, in daina haraka in ci mi? Ai ko cikin gida ana haraka"

""".."

"Kubra tace ""Haba dai amma ko Asy baby kin k'ware mu,, ashe mu bamu sani ba kina nan kina kwasar"

"dad'inki ,,kiyi iskanci waje kiyi cikin gida ""..."

"Lubna tace ""Lallai kin cika babbar karuwa kuma 'yar bariki,, kina sha'anin ki gaskiya to ki taimaka ki gaya"

"mana wa ne ne gayen da kike hankad'ama buje? "".."

"Asiya tace ""kun cika gaggawa wallahi,, bari dai in sanar muku kun dameni da tambayoyinku"".. Ta kawo"

"labarin alak'arsu da Abu ta sanar da su,, sunyi mamaki matuk'a wai ace kana xina har cikin gidanku. Amma sau d'aya ba'a tab'a kamasu ba."

"Kubra tace ""abin yayi k'yau ta dai a hankali,, kada wata rana a kamasu ""."

"Lubna tace ""haka ne kam gaskiya. Sannan idan Abu yanada abokai suma ta had'asu da su,, kuma ta iya"

"takonta kada ta yarda a kamata "".."

"Asiya tace ""Ina hauka ne da zan bari a kamani,,, karku damu yanzu nan kuwa zan had'aku da abokanin sa"

""".Tasa hannu ta kira Abu a waya tare da sanar da shi,, tana son ganinsa yanzu yanzu da kuma su Lado. Ya nuna mata babu matsala gasu nan tafe,, ta kashe wayar suka cigaba da firarsu cike da tsananin k'aunar"

juna da yarda...

"Basu jima ba saiga su Abu sun shigo har cikin d'aki,,, suna zuwa aka gaisa tare da sanar da su ga"

"k'awayenta nan. Da yake Lado da Tanko manyun mata ne,, suka nasa aransu kowa ya zab'i tasa budurwa. Tanko ya d'auki Kubra Lado kuma da Lubna,, suka samu wuri suka zauna ana fira kowa da tashi gab da gab da juna. Su Abu manya yaja hannun Asiya yace musu yayi fira da tashi,, suka shige cikin d'aki suka barsu. Suna shigewa Tanko yaja hannun Kubra sukayi gefensu,, Lado da Lubna suka yi zamansu tare da fara kissing d'in juna daga had'uwar farko,, kafin kace mi har Lado ya cire mata kaya shi ma ya cire nashi"

suka fara aikata masha'arsu. Acan bangarensu Kubra suma sunyi nisa basa jin kira nishi kawai yake tashi..

"Abu da Asiya suma sun lula duniyar mazinata,, sun d'au lokaci suna abu guda sannan kowa ya k'yale ta"

"shi hakanan. Sai da sukayi wanka sannan suka mayar da kayansu a jikinsu,, kowa ya cika budurwar shi da kud'i sosai domin dubu ishirin ishirin suka basu. Tare da exchanging numbers,, sai da suka siyo musu kayan mak'ulashe suka cika cikinsu. Da zasu wuce saida sukayi sallama da Inna Saude,,, tare da bata dubu biyar domin su siyeta. Ta washe shegen bakin nan tare da yi musu godiya,, Tanko da Lado ma dubu goma suka bata. Inna Saude ta yi matuk'ar farin ciki da murna sosai d'iyarta wai da masu kud'i,,, take alak'a tayi musu godiya har saida sukaji. Abu da su Lado sukayi ma su Kubra rakiyar har waje,,, sannan"

suka tara musu keke napep ta kaisu gida. Bayan sun wuce ne Lado da Tanko sukayi ma su Abu sallama...

"Bayan su Tanko sun wuce ne,, Abu da Asiya suka shigo cikin gida. Abu saboda iya tako har da hararar"

"Asiya tare da cewa yana marinta ,,Asiya ta ja masa mugun tsoki tare da zuwa wurin Inna Saude."

"Inna Saude ta kama yi ma Abu fad'a da masifa,, tare da cewa ""akan mi zai mari Asiya? Itada gidan ubanta"

"bai isa ya hanama d'iyarta. Jin d'adi ba da walawa"",, saboda Abu yasan duk cikin tako ne da raina mata"

"da hankali ko kulata baiyi ba. Ya shige d'akinsa,, inna Saude ta cigaba da yin fad'a Asiya taja hannunta tare da bata hak'uri suka shige cikin d'akinta.."

"Kuji min sakaryar uwa mara wayo,, d'iyan cikinta suna raina mata hankali tare da yi mata wayoo.."

"Wasu Iyaye sunga ta kansu,, saboda 'ya'yansu suna iya tsarasu kuma su yarda,, kamar yadda Asiya ta"

keyi ma Inna Saude koma fiye da hakan.

_*Mu kasance tare akowane lokaci *_

*Allah yasa mudace baki d'ayanmu *&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 200-201

"Asiya taja Inna Saude tana bata hak'uri,, suka shige cikin d'akinta shi kuma Abu da yake d'an duniya ne"

"fad'an Inna Saude ko akwalar rigarsa,,babu abinda ya dame shi saboda akwai wani k'uduri daya k'udurta a cikin zuciyarsa game da ita wanda shi kad'ai yasan abinda zai yi da shi dasu Lado abokaninsa..."

"Aisha dai babu ruwanta da harakarsu,, daga ta dawo makarantar boko sai tayi abincin dare da rana tana"

"kamallawa idan lokacin islamiya yayi sai ta shirya zuwa makaranta,,, haka ta ke tafiyar da rayuwarta cike da natsuwa da tsabta.Shi kuma Aliyu bai faye zama gida ba,,, saboda Saude shi ma ci masa mutunci da tozarci ta ke babu abinda ya dameta. Saboda gudun fitinar Saude shiyasa baya zama gidan sosai,,, shi ma kansa Saude ta ishesa ya rasa yadda zaiyi da ita ne,,, amma yana yawan rok'on Allah ya kawo masa"

mafita....

********************

"Wata rana ne Asma'u da Zainab,,, suka kawoma Aisha ziyara har gidansu. Bayan sun iso ne ta kawo musu"

"ruwa da danbun nama,, ta zauna a cikin su suka ci a tare da juna bayan sun gama ci ne,,,sai fira ta b'arke a tsakanin su..."

"Asma'u ce ta dubi Aisha,, tace ""k'awata kinsan wani abu kuwa? Labarin da nake ji gaskiya ne a wurin"

"Mama saboda nasan ba zata min k'arya ba ""..."

"Aisha tace ""Asma'u ke kuma wa ne irin labari ne kika ji?,, wanda ya baki mamaki "".."

"Zainab ta harareta da wasa,, tace ""ke fa akwai ki da rashin ganewa fa da wuri ""...."

"Asma'u tace ""to bari mu fito miki gwari gwari,, saboda barin kashi a cikin ciki baya maganin yunwa."

"Dama ba wani abu bane munji labarin aurenki a wurin Mama "".."

"Aisha tace ""Eh mana wallahi haka ne,, nima bansan lokacin da aka d'aura aurenba. Sai da Baba Adamu ya"

"kirani ya gayamin abinda ke faruwa,, ya kuma ja min kunne akan kada in kuskura koda wasa nayi wannan maganar,, ko in sanar da wani har yaje kunne Inna Saude ""..."

"Zainab tace ""Agaskiya mun tayaki murnar aurenki,, duk da yake ko ke bakisan mijin ba.Amma gaskiya"

"Baba Adamu yana sonki kuma ya cika amini na gari "".."

"Asma'u tace ""karki damu Aisha Allah ne ya tausaya miki,, ya kawo miki agaji alokacin da kike buk'atar"

"taimako. Idan Allah ya yarda Saude ba zata sani ba,, ke dai ki kasance mai biyayya da hak'uri a rayuwa ""."

"""Haka ne kam gaskiya,, nima ni kaina ba wani damuwa nayi ba. Alokacin da naji anyi min aure saboda"

"agaskiya na gaji da zalunci da cin amanar Inna Saude da Abu,, ga Asiya itama ba wani ragamin ta ke ba "".Cewar Aisha.."

"Asma'u tace ""to ai yanzu komi zai wuce kamar ba'a yi ba,,, saboda nasan da mun gama makaranta za'a"

"kai ki gidan mijinki,,, kinga kuwa komai zai zo miki da sauk'i "".."

"Zainab tace ""haka ne gaskiya kam kinga komai zai zo miki cikin ruwan sanyi,, komai zai zo ya wuce kamar"

"ba'a yi ba ""...."

"Aisha tace ""gaskiya ne kam,, Allah ubangiji ya sa mu dace baki d'ayanmu "".."

"Asma'u da Zainab tace ""Amin amin wlh ""...."

"Suka cigaba da firarsu cike da tsananin k'aunar juna da yarda,,, suna bata shawarwari ta yadda zata"

zauna da mijinta lafiya. Tare da hak'uri da juriya akan zamantakewar rayuwa....

*********************

"Su Abu da abokanin sa su Lado,, sun cigaba da iskancinsu da su Kubra .Domin alak'arsu yanzu ta yi k'arfi"

"fiye da tunanin mai tunani,,, haka suka mayar da d'iyan mutane kamar matansu,, kullum suna tare da su suna cikasu kud'i...."

"Haka al'amari suka cigaba da tafiya,, Inna Saude duk batasan abinda ke faruwa ba,,, har yanzu saboda"

rashin sanin ciwon kai....

"Acan garin Shiko kuwa Inna Harira da Laure,,, babu abinda suke yi sai iskancinsu da zalunci."

"Laure ta dubi Inna Harira tace ""Inna wai bakiga wani canji ga Iskiyaku ba? "".."

"Inna Harira tace ""Wa ne irin chanji kuma Laure,, wai shin mi kika gani yanzu? "".."

"""Abinda na gani shi ne yanzu ba kika yadda Isiyaku ke saka tufafin k'warai ba,,, kuma masu k'yawo sosai."

"Kuma ba yanzu ya daina cin abincin gidan nan. Sannan zaki ganshi akodayaushe yana cikin walwala da farin ciki "".Cewar Laure.."

"Inna Harira ta nisa sannan tace ""nima na lura da wannan alamomin,,, sai dai na rasa mi ke sanya shi"

"yawan yin farin ciki da nishad'i. Ko kinji wani labari ne wanda ya ke sanyashi cikin murna da farin ciki? "".."

"Laure tace ""nima kaina ban sani ba,, amma ya dace ki bincika domin gano bakin zare. Kuma musan"

"abinda ya ke ciki,,, kada aje asirinmu ne ya ke shirin tonuwa "".."

"""Ina wannan ba zai tab'a yiyuwa ba!! Isiyaku ba za tab'a dawowa cikin hayyacinsa,,, muddin ina raye ko"

"zan yi yawo tsirara wallahi. Bazan tab'a yadda ba "".Cewar Inna Harira cike da tsananin tashin hankali.."

"Laure tace ""kwantar da hankalinki Inna,, wannan ba abin damuwa ba ne. Zamu san yadda zamu b'ullo"

"ma al'amarin Isiyaku da sauran mutane ""..."

"Inna Harira tace ""ta ya kike son hankalina ya kwanta,, alhalin asirinmu yana gab da tonuwa ""..."

"""Yaushe nayi da ke asirinmu zai tonu,, nifa bana son rikicin tsufa. Kuma yaushe kika je wurin boka"

"SIDDARU amso magani domin kada asirinmu ya tono? Ni fa bana son abu da gaggawa "".Laure tace..."

"Inna Harira tace ""kuma haka ne fa yi hak'uri,, kinsan ni da saurin rikicewa da kuma rashin hak'uri""...."

"Laure tace ""ai ba abin rikicewa ba ne,, na gaya miki zamuyi bincike akai ""..."

"Inna Harira tayi ajiyar zuciya da k'arfi! Tace ""to babu damuwa Allah yasa ba asirinmu ba ne zai tono "".. ."

"""Amin yauwa ko kefa yanzu naji magana "".Cewar Laure.Haka Laure ta cigaba da kwantar mata da"

"hankali,, tare da shawarwari akan yadda zasu b'ullo ma lamarin Malam Isiyaku..."

**********************

"Asiya suna zaune da Inna Saude suna fira,, tare da cin nama da korawa da ruwan lemu kala-kala."

"Alokacin ne Asiya ta dubi uwar tace ""wai Inna har yanzu ba'a yi baikon Aisha da Lado ba? Ko so kike wani mai mugun kud'i yace yana sonta a d'auka abashi ""."

"Inna Saude tace ""wannan ba zai tab'a yiyuwa ba! Muddin ina raye Babanta ne yace abari ku k'arasa"

"makaranta sai ayi maganar aurensu ""."

"Asiya tace ""ke gani kike Baba yana son wannan auren,,, anya ba wayo yake miki ba? "".."

"""Ni k'aramar yarinya ce da xai mini wayo,, kuma idan ki manta bari in tuna miki. Kin mance da asirin da yi"

"masa wanda baya iya k'etare umurni na "".Cewar Inna Saude cike da cika baki.."

"Asiya tace oh! Na tuna amma karki dogara da wannan,, saboda akowane lokaci asirin zai iya warwarewa"

"""..."

"Inna Saude tace ""keeee!! Zanci ubanki fa kiji min shegiyar yarinya mai bak'ar fata,,, idan ya warware ki"

"zuba ruwa k'asa ki sha. Wanda batasan zafin uwarta ba da kishin kanta ba wawuya kawai ""."

"Asiya tace ""Allah ya baki hak'uri Inna ba fata na ke ba,,, ai magana ce ta kawo magana. Tare da baki"

"shawara "".."

"""Maganar ubanki Asiya wallahi ki kiyaye ni bar ganin ina sonki,,, zan iya cin mutuncinki 'yar iskar banza"

"argunguma. Wadda bata iya magana ba,, dama nasan ba wani sona kike ba tunda har kike fatar asirina ya tonu "".Cewar Inna Saude.."

"Asiya ta mik'e tsaye tace ""nace kiyi hak'uri nifa bana son mutum mara hak'uri da juriya,,, sannan miye ya"

"kawo batun rashin so? "".Ta yi wucewarta cikin d'aki batare da k'ara sauraren abinda zai fito,,, daga bakin Inna Saude ba."

"Inna Saude tace ""ai dole ki shige cikin d'aki,, saboda kinsan bakida gaskiya Asiya. Da ni kike a cikin gidan"

"nan zaki gane kurenki "".."

"Duk abinda suke fad'a,, Aisha tana cikin d'aki tana jinsu. Babu abinda ta ke tunani illa rashin tausayi da"

"rashin imaninsu. Ta kance ""Allah ubangiji na rok'e ka,, ka gwadamin na bar gidan nan lafiya. Kafin su Inna Saude su kasheni kamar yadda naji ance itace silar mutuwar mahaifiyata. Babana kuma Allah ka yaye mishi abinda ke damunshi,,, wannan auren da suka yimin Allah ya sa shi ne mafi Alkhairi a gareni da"

"rayuwata ""."

"A haka dai Aisha take tunanin mahaifiyarta,, tare da zubar da hawayen k'unci da damuwar rashin"

"mahaifiyarta. Da kuma Kakarta da dangin mahaifiyarta,, ko Inna Indo rabonta da ganinta gidansu yayi wuce tunaninta. Saboda ita kanta tana mamaki mi yasa duk son da su Maman Amina suke mata da Inna Indo,, aka wayi gari babu mai kulata su Habiba ma da suke kulata ada kowa yanzu bata gani,,, babu mai tausayinta babu mai kulawa da damuwarta sai Baba Adamu. Ko k'ila domin ya gagari su Inna Saude ne da uwarta Harira,, saboda a rayuwar su sun tsani suga mutum yana tausayin Aisha a rayuwa. Basu son suga kowa ya rab'eta matuk'ar zata yi farin ciki a rayuwa,,, sun fison suga ta dawwama cikin bak'in ciki"

har k'arshen rayuwarta...

"Haka al'amurran suke tafiya cike da rashin tsoron Allah,,, da rashin imani. Babu abinda Saude tasa ma"

"gaba sai cin amanar Aisha,, tare da zaluntarta a cikin gidan nan. _(wai miyasa mata muka d'auki d'an kishiya,,, ba d'anki ba ne mu daina hakanan babu k'yau ko ga addinin musulunci. D'a na kowane domin kuwa koda kai ka haifi d'a bakasan iyakacin wanda zaici moriyarsa,, kuma ai d'an kishiya yana iya kasancewa shi ne zaka mora ba d'anka ba. Don Allah mu gyara zamantakewarmu tsakaninmu da kishiyoyinmu,,, saboda kishi ba hauka ba ne. Wad'anda suka fimu daraja sunyi kishi amma ba irin na mu"

"ba,,, Allah ubangiji ya sa mu gyara zamantakewarmu da kishiyoyinmu).._"

"Babu abinda ke cikin zuciyar Aisha,, illar tsananin kewar mahaifiyarta tare da k'aunarta. Ko shi kanshi"

"Aliyu yana tsananin tausayin Aisha amma yana mugun tsoron halin Saude,,, domin kada ta salwantar mai"

"da d'iyarsa farin cikin rayuwarsa. Saboda ita kad'ai ya ke gani ya tuna da Amina tare da jin wani sanyi har cikin jikinsa,,, hak'ik'a nima ina matuk'ar tausayawa rayuwar su Aisha.."

"Abu da Asiya sun k'ara jonewa tamkar mata da miji,,, babu abinda suke yi illa iskanci batare da"

mahaukaciya Saude ta lura ba...

"Su kansu su Lado yanzu suna jin dad'in,,,mu'amala da su Kubra babu abinda ya ke raba su idan ba ciwo"

ba...

"Haka rayuwar take gudana,,, cike da tsananin jin dad'insu..."

"Allah ubangiji ina rok'on ka,, kayi mana maganin abinda bamu iya yima kanmu. "

"_*Fans ku k'ara tayani da addu'a,, ina cikin matuk'ar damuwa*_ "

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

"_Wannan shafin sadaukarwa ne gare ku , *Ummu Habiba, Ummie Adnan, Aisha, Princesss Maryam,"

"Fairoxa Barhama, Bannah, Shammy, Ummu Hibbatullah, Mamyn deejah*. Hak'ik'a comments d'inku"

"yana matuk'ar sani farin ciki da nishad'i,, ina muku so mai tsabta.._ "

*PAGE* 202-203

"Rayuwa ta cigaba da tafiya,, alokacin ne su Aisha suka fara rubuta waec d'insu.Inna Saude ita kuma"

"batada aiki sai tambayar Asiya inji sun kusa kammala makarantarsu,, Asiya ta kan nuna mata da sauran lokaci idan suka kusa gamawa zata sanar mata ta kwantar da hankalinta. Haka dai Inna Saude ta ke bincike domin kada abin yazo mata girshi,,shi ma Lado yana yawan zuwa zance wurin Aisha. Duk dai babu abinda ta ke ce masa saboda tsabar takaicinsa da ta keji da kuma haushi,,, shi ne zaita surutunshi da shegen dogon bakinsa ya k'ara gaba. Batada iko ko halin k'in saurarensa,,, saboda Inna Saude ko Abu mugun bugu suke mata kamar jaka. Babu ruwansu da ta girma ta wuce bugu,, su dai burinsu da kuma fatarsu shi ne su k'untata mata. Amma Asiya 'yar gaban goshi babu mai takura mata duk abinda ta so shi ta ke yi,,, babu mai sa mata ido ko tsamgwamarta. Haka suka cigaba da rayuwarsu cike da tsananin"

rashin tausayi da tsoron Allah... .

*********************

"Acan garin Shiko kuwa Iya Delu ce,,, ta kawoma Inna Lanti ziyara domin suyi gulmar da suka saba...."

"Iya Delu ta karkace baki tace ""Lanti "".."

"""Na'am Delu "".Cewar Inna Lanti.."

"Iya Delu tace ""wai kinsan shawarar nan da muka ba Harira,, har yanzu bata neme mu ba balantana"

"muce ta d'auki shawararmu. Matar nan fa muguwar munafuka ce saboda bata yarda da mu ba ""..."

"Inna Lanti tace ""waye ya gaya miki wannan maganar? Nima nasan bata d'auki shawararmu ba,,, amma"

"ba wai domin bata yarda da mu ba. Laure nan da kike gani ita ce bata yarda da mu ba,, saboda idan kina lura ko gidansu muka shiga bata gaishemu. Kuma ta kama harararmu kenan har mu fito gidan ""."

"Iya Delu tace ""Lallai kuwa biri yayi kamada mutum,, maganarki haka take Lanti. Amma zata gane batada"

"wayo ita Lauren,, sai mun koya mata hankali. Ni wallahi duk zuri'a indai ta Harira ce na tsanesu fiye da tunaninki "".. ."

"Inna Lanti tace ""Idan kika bud'e zuciyata kika ga yadda na tsani Harira,, sai kinyi mamaki ji na ke kamar in"

"dab'a mata wuk'a ta mutu,, kowa ya huta da annobar garin Shiko "".."

"Iya Delu tace ""da sannu zamuyi galaba akanta,, mi kike ci na baka yana zuba. Ai sai munga bayanta da ita"

"munafukan yaranta "".."

"Inna Lanti tace ""gaskiyar maganarki Delu zasu gane shayi ma ruwa ne,,, da mu suke zance bada wasu ba"

""".."

"Iya Delu tace ""ganewar ma sai sunyi nadamar duk abinda suka aikata,,, a rayuwarsu sai sunyi kuka da"

"idanunsu ""..."

"Inna Lanti tace ""k'warai da gaske zasuyi kuka da nadama a rayuwa ""."

"""haka ne gaskiya "".Cewar Iya Delu. Haka dai suka kama tsara irin muguntar da zasuyi ma Inna Harira da"

"su Laure,, tare da yi musu fatar Allah ya sa duk abinda suka k'ulla ya warware asirin ya koma kansu...."

"Ni kaina ina mamakin rayuwar nan tamu ta chanza,, kaine zaka d'auki so, yarda, da amana kaba mutum."

"A k'arshe shi ne zai fara cin amanarka,, yardar da kayi masa da nuna masa so duk sun tashi a banza,,"

Allah ubangiji ina rok'on ka ka bamu masoyan gaskiya .

**********************

"A gidansu Maman Amina,, Hadiza ce ta zo ganin mamanta tare da yaranta da cikinta sabon shiga. Wanda"

"bai wuce wata biyu ba,, fira suke suna tattaunawa cike da tsananin k'aunar juna..."

"Maman Amina ta kalli Hadiza tace ""kinzo kuwa adai dai lokacin da na ke buk'atar ki "".."

"""Mi ye buk'atarki Maman mu? "".Cewar Hadiza.."

"Maman Amina tace ""kinsan Amina ta rasu ta bar Aisha,, to da mukayi -mukayi Babanta ya bamu ita ya k'i."

"Shi ne mu ke mata aike akai akai to da matar Saude,, taga abinda muke yi ma Aisha baiyi mata dad'i ba. Shi ne ta kaimu har da ke aka shiga tsakaninmu da Aisha,,, idan baki manta na kan yawan aiko miki da addu'o'i da rubutun magani na kariya. Nima wani malami ne da babanki ya kira ya taimakamin da su,,, shi ne ya nunamin ko munji sauk'i kada mu kuskura muje gidan Aliyu domin ceton Aisha. Mu k'yale ta"

"komai zaizo k'arshe,, Allah cikin ikonsa shekaranjiya Malam Adamu mutumen kirki ya ke gayamin anyima"

"Aisha aure da wani acan birni,,, nayi matuk'ar farin ciki sosai koba komai ba zata rage zama cikin uk'ubar"

"rayuwa "".."

"Hadiza wasu hawaye masu zafi da

Please Login or Register in order to submit comment