You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata shi baya cin abinda zai sashi zawooo,,, ko"

ciwon ciki.......

"Inna Indo ta dube shi,,, ta ce ""Amma Malam baka san dad'i ba... Kai komi ba ka son ci sai dai abu mai"

"nauyi,,, komai ka ce b'ata ciki ya ke yi... Hmm su Malam manya kenan ""........."

"Malam ya ce cike da tsokana da raha ""to acici sarkin santi,,, ci abinki anjima kiji dad'in zawooo,,, ni dai"

"ina gefe na babu ruwana.. Ke komi ki dai sama cikin nan na ki ""........"

"Inna Indo ta yi murmushi ta ce ""domin mi aka yi mana ciki,,,, ba domin abinci ba da kunu Ai yana da"

"k'yau mutum ya san hak'k'in cikinsa ""..."

"""Wato ni ban san,, hak'k'in cikina ba,,, saboda banyi masa d'ure-d'ure ba ko ""....Cewar Malam...."

"Inna Indo ta ce ""ka sani mana,,,, rufamin asiri in mutu maza su kaini mak'abarta.. Kada kasa mata su"

d'auke ni zuwa can.......

"Malam yayi murmushi mai bayyana hak'ora,,,,, ya ce ""to na rufa miki asiri ""........"

"Inna Indo ta ce ""godiya na ke maigida ""........ta fad'a tana dariya.........."

*********************

"*****Agidan Aliyu kuma,,,, zaman Amina cikin gidan yanzu ta dawo shiru -shiru ko magana bata son yi,,,,"

idan ba ya kama dole ba...

"Saboda yanzu Saude iskancinta da shed'ancinta ya k'aru sosai,,, ko wani abu irinsu bokiti, plate,, kula"

"Amina ta mance da su waje,,,, 'd'auka take yi tana fashewa ga k'asa A wannan lokacin ko kaya Amina"

"batada damar shanya ta barsu.... Batare da Saude tasa reza ta yayyagasu ba,, ,ta hanama Amina aje duk wasu kayayyakin aikinta a waje Babu halin tayi mantuwa to aranar sai rayuwarta ta b'aci,,,, imani da"

mamaki yasa Amina ta ke kasa yi mata magana. Alal hak'ik'a Amina na ganin walak'ancin Saude da cin

mutunci..... ..

"Babu ranar da Saude bata ci ma Amina mutunci ba,,,,, tare da zagin iyayenta........."

"Kuma ta saka yi mata magana,,, balantana ta gaya ma Aliyu... Wanda ko shi yanzu yana kula ta amma ba"

sosai ba..... .

"Ta kawo na mujiya tasa musu,,,, wad'anda basu ci basu sha... Akullum rok'on ta Allah ubangiji ya kare ta"

"daga shairin Saude da zuri'ar su,,, saboda ta fahimci mutane ne da basu da tausayi bale imani......."

"Saude ta riga ta iya munafurci da kissa,,, saboda zata asamo mata ledodin sabulun wanka mai shegen"

"k'amshi da na wanki,,, tare da sayen takarda nama da dakakken k'uli -k'uli......."

"Wanda duk safiyar Allah,,, kafin gari ya ida wayewa ta ke zubarwa abakin k'ofar ta,,,, saboda Amina ta"

san Aliyu ya ke siyo mata kayan dad'i da sabulun k'amshi Ta kuma sani ta riga ta ije gwamnatin

"Amina,,, ta kafa ta ta gwamnatin......."

"Amina idan ta gani,,,, nuna mata ta ke kamar bata ga komai ba. Hakan ne yasa Saude ta k'ara tsanar"

"Amina fiye da komai a duniya,,,,,, tare da shan Alwashin sai ta kashe Amina a doron k'asa. Sai ta"

"k'untata mata kuma ta bata bak'ar wahala,,,, kafin ta kashe ta tabar duniyar gaba d'ayanta. (Ni kaina"

"ina mamakin mugun hali irin na su zuri'ar su Saude. Sun mayar kashe rai ba'a bakin komai ba,,, tare da"

"nuna kishin jahilci a filin wuri,,,, sau da yawa abin na matuk'ar bani mamaki. Zaka ga mace ta isko uwargida da mijinta amma sai ta nuna miki ta fiki k'aunar sa da kuma masifaffe kishi a kansa,,,, wai miyasa mata muke yin haka ne.. Ta ya zaki iske wadda ta yi shekaru da mijinta ki nuna mata ke fita sonshi tare da buk'atar shi Dan Allah mata mu gyara zamantakewarmu tsakaninmu da"

"kishiyoyinmu,,,kishi yana da zafi kuma gaskiya ne,,, amma muyi hak'uri muyi koyi da matan manzon"

Allah (S. A. W).....

"Saude dai ta takura ma Amina,,,, kamar ciwon ajali yadda ta d'auki kishi ko ibadar ta bata d'auketa haka"

nan ba...... Ta mayar da kishin jahilci kamar ibadarta... .

"Koda yake karku damu,,, mugun hali gadon shi tayi ga uwarta Harira,,, ba wai daga baya ta fara ba......."

Arayuwar su Saude su tsani kishiya da kuma d'iyan kishiya........

_*Zasu zauna lafiya kuwah? Sai ku biyo ni kujiiiiii*_&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 131-135

"***Washe gari da safe misalin k'arfe 12:00pm na rana,,,, Amina ce ke share filin gida,, tana kwashe"

sharar da tayi... Haka ta kama yi har ta kammala sharar da kwashewa......

"Tana gamawa bada jimawa ba,,, ta shige cikin d'akinta... Tana shigewa Saude tana kwaso shara daga"

"d'akinta,, tana zubarwa inda Amina ta share tas... Sai da ta b'ata duk inda Amina ta share tsab,,, bayan ta lalata ko'ina sannan hankalinta ya kwanta....."

"Zuwa wasu mintuna,, sai ga Amina ta fito daga cikin d'akinta... Tana zuwa tsakar gida sai ta ga an b'ata"

"mata shara ko'ina yayi kaca-kaca babu k'yawon gani,,, tayi matuk'ar mamaki na ganin ma kamar bata yi shara ba kuma ko'ina ya b'aci sosai......"

"Sai kawai Amina ta ce""Subahanillah!!wai waye ya b'ata min shara ne? Mutum yayi wahalar shara an"

"b'ata masa wuri babu k'yawon gani... Wai wannan wane irin masifa ne da son fad'a ""......."

"""keeee!!! Amina nina b'ata miki shara,, ko akwai abinda zaki iya min ne... Shegiya juyar banza wadda"

"bata haihuwa sai dai kici kiyi k'aton kashi,,,, wawuyar doluwa banza mai banzar rayuwa "".Saude ta fad'a cike da masifa,,, tare da fitowa cikin d'aki a hanzarce rik'e da k'ugu......"

"Amina ta dubeta,, ta ce ""Saude kenan,, da haihuwa da rashinta duk na Allah ne... Kuma komai yanada"

"lokacinsa,, idan Allah ya k'addara zan haihuwa babu makawa sai na haihu,,,, idan kuma banida rabo to shikenan wannan yana daga cikin KUNDIN K'ADDARA TA... Sannan ina son ki sani abinda kike min ya ishe ni,,, shiru -shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne""......."

"Saude ta ce ""maganar banza na zata zakiyi zuciya yanzu,,, sai kiyi ciki bak'ar karuwa annobar gari.. Da"

"kina nufin k'yale ni kike yi yanzu,, to idan baki tanka mini ba uwarki maziya ce kafin ta auri ubanki... Idan ke cika munafuka kuma tambad'add'a ki zo ki buge niii ""...Ta ce tana matsowa kusa ga Aminaaa......"

"""Dakata!! ki tsaya ga jikinki kada ki kuskura,,, ki k'ara matsowa kusa gare ni... Saboda wannan raini da"

"walak'anci yayi yawa Saudatu,,, a duniya miye na tare miki kefa kika fara iskoni tare da miji nah sannan kifi jin haushi da zafin kishi,,, kishi ai ba hauka ba ne "".Cewar Amina cike da rashin fad'a...."

"Saude ta ce ""Mtssssss aikin banza kishi hauka ne,,, kuma miji ne ya had'amu ni na isko ki amma na fiki"

"muradinsa.. Saboda ko banza ke juya ce baki haihuwa,,, ni kuma ina ran na cika masa gida da d'iya.. Saboda haka ki daina had'a kanki da ni,,, kuma ya ce min shi yanzu ba wani sonki ya ke ba,,, domin bakida amfanin komai sai dai kici kiyi k'aton kashi,,, saboda haka tun wuri ki sani Aliyu ba ya k'aunar ki"

"kuma baya ra'ayin ki... Nawa ne ni kad'ai kuma domin aka halicce shi "".."

"Amina ta ce ""Hmm Saudatu kenan,, kina bani mamaki aduk lamarin ki baki saka Allah a gaba. Ko kin"

"kirani da juya ba zan damu ba,,, saboda nasan komi yana da lokacin sa,,,, kowa bai wuce k'addara shi ba tun ran gini ran zane... Saboda haka ki koma islamiya ko zaki samu tauhidi a zuciyarki ""........."

Saude ta yima Amina walak'antaccen kallo mai cike da raini.....

"Ta ce ""ba zan koma islamiya kuma ubanki ne jahili ba ni ba,,,,, har akwai shegiyar da ta isa ta gayamin"

"magana,,, to wallahi ba zaki tab'a jin dad'in gidan nan ba muddin ina cikinsa. Saboda ni na zamar miki"

"guguwar annoba kuma cutar ajali,,,, zakiyi nadama Amina a rayuwarki wallahi ""..."

"""Babu abinda zan gani sai alkhairin Allah,,, kuma duk sharrin da kika k'ullo ya koma ga kanki... Saboda"

"Allah ya fiki baya kwana kuma baya angaje "".Fad'ar Amina cike da tsananin mamakin halin Saude...... ."

"Saude ta ce ""abbb zancen banza! Na d'auka ko duka na zakiyi,,, ashe ma ke matsoraciya ce sannan"

"ragguwa,,, ai Aliyu ya ce wai jikinki yake yi ranar da duk yake a d'akinki sannan daurewa kawai ya ke hana kwana da ke,,, saboda baya gamsuwa da ke ""..Cewar Saude"

"""ko ina wari da rashin gamsar da shi babu abinda ya shafe ki,,,, sannan Alhamdulillahi "".Amina ta fad'a"

tare da wucewar ta cikin d'akinta... ...

"""Yi hohoho!! Wata taji kunya miji baya sonta,,, ya ce ko bak'in kare ya fiki sannan kina mugun d'oyi da"

"wari Amma saboda rashin zuciya ta manne ma miji,,,, shegiya dangin mayu masu maida mutum"

"alade,,, su mai da k'adangare zaka saboda mugun asirinsu da shegen bid'e -bid'ensu "".Saude ta ce da k'arfi,,, tare da zama tana cin mutunci Amina tare da habaice-habaicenta...."

"Dole zuwa anjima,,, bayan Saude ta tashi zaune daga wurin ta shige cikin d'akinta. Sannan Amina"

baiwar Allah ta sake share wurin tare da zubar da sharahhh......

********************

"Bayan kwana ukku da faruwar wannan al'amari,,, Mama Habiba da Hussaina sun shigo gidan domin su"

gana da Amina....

"Suka shiga d'akinta,,, suka iske ta zaune tana karatun littafan addini......"

"Suka yi mata sallama,, ta amsa musu tare da yi musu sannu da zuwa. Suka samu wurin zama suka"

zauna... .

Amina ta kawo musu ruwa tare da kayan marmari...

"Bayan ta zauna ne Mama Habiba ta dube ta,,,, ta ce ""ke kuwah Amina miya same ki naga duk kin rame,,,"

"ko kinsa ma kanki tunani ne a banza da yofi "".."

"Hussaina ta ce ""gaya mata ke dai Anti,,, ke rigani fad'a a baki na riga a zuci Amina ki gaya mana miye"

yake damunki kuma mi ke faruwa ne?...

"Amina ta nisa ta ce ""Anti Habiba, Hussaina. Hak'ik'a ina cikin damuwa da rashin walwala,,, saboda Saude"

"masifaffiyar mata ce kuma fitinanniya,,, fad'an safe daban na rana daban na dare daban... Kullum cikin fad'a ni ban saba da wannan rayuwar ba,, alal hak'ik'a Aliyu ya d'auko mana annobar da zata kashemu daga ni har shi,,, wannan wace irin rayuwa ce mi muka d'auki kishi wai mata... Ai kishi ba hauka ba ne duk abinda na aje ga fili sai Saude ta lalata shi,,,, ya zanyi da rayuwa tah ni Aminatu hak'ik'a nayi nadamar amince masa da nayi akan ya k'ara aure..... Da nasan haka ne da tun farko ban amince masa ba,,,, wallahi bana son tashin hankali bale damuwa. Ta ce alokacin hawayen bak'in ciki suna zuba daga"

idanunta....

"Anti Habiba ta ce ""ban fahimce ki ba Amina,,, wai mike faruwa ne? "".."

"Itama Hussaina ta ce ""nima ban gane kan maganarki ba,,, sanar damu abinda yasa ki hawaye Aminatu... ."

"Amina ta ja majina cike da k'unci da tarin damuwa,,, ta kawo labarin komai tun daga ranar da aka kawo"

"Saude,,,,, zuwa yanzu babu abinda ta b'oye musu..... ..."

"""Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!! Wannan wace irin mata ce ""Habiba da Hussaina suka fad'a tare... ."

"Habiba ta dubi Amina cike da tsananin damuwa da tausayinta,,, ta ce Dan girman Allah Aminatu,,, ki"

"k'ara hak'uri wannan ita ce k'addararki.. Babu yadda zakiyi ki guje ma abinda Allah ya rubuto miki tun ranar gini,,, ranar zane.. Hak'ik'a kina cikin k'unci da damuwa,, to ya zakiyi duniyar guda nawa ce,,"

"sakayyarki a wurin Allah tana nan tafe.... Na tabbata irin su Saude ba zasuyi k'arshe mai k'yau ba ""......"

"""Haka ne kam gaskiya,, hak'urin nan dai da muka saba baki shi zamu baki Domin ba zamu baki"

"muguwar shawara ba,,, ki je ki aikata abinda za'a zo ana nadama. Kiyi hak'uri Aminiyarmu Allah zai miki"

"sakayya tun anan duniya zata ga abinda ta shuka,,,, zata girbe shi da hannunta kuma bata isa ta hana miki haihuwa ba.... Lokaci ne kawai baiyi ba ""....Hussaina ta ce cike da lallashi..... ."

"Habiba ta ce ""Akullum abinda na ke gaya muku kenan,,, hak'uri da juriya su ne jigon zaman rayuwar"

"duniya,,, ako'ina ka ke kuma ako'ina kaje sai kayi hak'uri da irin mutanen da Allah ya had'a ka da su...."

"Duk wadda ya zage ka ka barshi ga sarki Allah,,, zamu tsayu gaban Allah aranar da kowa yake nafsi -nafsi da kansa """

"Hussaina ta ce ""wallahi kam Anti,,, Amina ki saki kowa ki kama Allah.. Zaki samu duniyarki tayi k'yau da"

"lahirarki,,, hak'urin nan da muka sanki da shi to dan Allah ki lunkashi sau dubu Zaki samu natsuwar"

"zuciya ""..."

"""Zan k'ara hak'uri akan abinda duk ta ke min Insha Allah,,,, nagode da k'aunar da kuke nuna min,,,"

hak'ik'a nayi dace da k'awayen arzik'i kuma 'yan uwa masu amana da rik'on gaskiya... Allah ubangiji ya barmu tare da juna har abadan da'iman...

"""Amin amin"".Suka fad'a atare da juna...."

"Habiba da Hussaina haka sukayi bata shawarwarin k'warai,,, tare da kwantar mata da hankali Bayan"

"anjima kad'an ta kawo musu abinci suna ci,,, tare da kayan marmarin da ta kawo musu tun d'azu"

"Bayan sun gama cin abinci,, suka sake bud'e sabon shafin fira.... ."

"Zuwa wani lokaci,, suka ce mata su zasu gida.. Dan Allah ta k'ara hak'uri lamarin duniya sai da hak'uri da"

kawaici...

"Amina ta nuna musu Insha Allah,, zata kiyaye tare da rako su filin gida..."

"Suna fitowa suka iske Saude ta yi zaune,,, ta fara zage-zage da habaice -habaice tare da tsine musu"

albarka.....

"Tana ganinsu ta ce musu ""munafukan banza an fito,,, ai dama tun d'azu nake wurin nan naji kuna"

"zagina... To ta Allah ba ta ku ba karuwai tambad'add'un la'anannu Allah masu shige-shige da yawon munafurci... Don kutumar ubanku kada ku sake shigowa gidanmu,,, saboda ba gidan tsohon k'warton ubanninku ba ne.... Miyagun mata masu bak'ar aniya dangin mayu da talauci kawai da ku "" ta fad'a"

cike da masifa.....

"""Anya matar nan tanada hankali kuwah,, ko sabon kamun hauka ce ""..Cewar Hussaina...."

"Habiba ta ce ""da gani babu tambaya fa,,, gaskiya matar nan ta haukace,, Amina ya kamata ki sanar da"

"Aliyu akaita kware. Ko zata samu lafiya"".."

"""zan sanar da shi,,, amma ina ganin haukar ba mai warkewa ba ce fa.. A haka zata tabbata ""..Amina ta"

fad'a tana kallon Saude... ..

"Saude ta yi kuwwa da k'arfi ta ce ""kune mahaukata kuma 'yan iska ba ni ba... Sheguna wad'anda basu iya"

"zama gidajen aurensu,,, sai sun bi k'ofa -k'ofa suna yawon munafurci da tsegumi Allah ubangiji ya"

la'anceku masu muguwar bid'a da shige-shige wallahi saina ci gundunbular kutumar babbar buro

ubanku!! Kwad'ayayyin banza wad'anda aka haifa babu jini sai da aka sob'o... Saboda ba kuda tsarki a

"wurin Allah ""Haka dai Saude ta kama zaginsu tare da tsine musu albarka"

"Dad'in abin burgewa,,, bayan saka mata magana babu wanda ya sake kulata. Tayi zage-zagenta ta gaji.."

"Su kuma Amina ta raka su bakin garka,,,, suka yi sallama da juna,,, ta juyo ta shige d'akinta..."

"Ta bar Saude zaune tana ta b'acin ta,,, tare da d'aukar alk'awarin sai taga bayan Amina... Saboda abinda"

suka yi mata ya bala'in b'ata mata rai...

"Ta dad'e zaune tana cin mutunci da tozarci,,, sannan daga baya ta shige cikin d'akinta cike da takaicin"

maganganu su Habiba............

Wannan kenan.

**********************

"****Washe gari da safe k'arfe 11:20am na safe,,, bayan Amina da Hadiza sun gama had'a"

breakfast....Sun karya suka gyara ko'ina da ko'ina a cikin gidan.... .

"Saude na ganin Hadiza,, ta hau bakinta da cin mutunci da tozarci"

"Ta kalli Hadiza ci ke da raini da k'ask'anci,, ta ce ""an je an kira tsohuwar karuwa annobar gari.. Domin"

"suzo suyi mata taron dangi,,,, dangin tsiya taulalin juyoyi kuma bak'ar ashana k'ona gari,,, karuwan banza """

"Hadiza ta ce ""Hmmm Saudatu kenan,, dama mai zuwa wurin bokaye da malamai,,,, shi ke zargi wani"

"dama abinda ka keyi hairan ko shairan zaka d'auka kowa ma yana yi... Kuma babu abinda ban sani ba game da ke uwarki da kuma 'yar uwarki Laure,,, abin kunya gadon shi kuka yi har da cikin shege sai da Laure yayarki tayi,,, kema kuma shegiya ce kuma babbar karuwa kuma mai bin mazan mutane.. Sannan na fad'a da babbar murya!! uwarki Harira da Laure babu shegen da bai ci su ba,,, kuma har yanzu cinsu ake yi,,, ke kuma kafin kiyi aure babu k'aton da bai ci ki ba har warin k'anenki kin bashi kuma ya ci Da"

"ke da rashin son zaman lafiya kunci buro uban ku shegiya wadda ta yi gadon mugun hali ga Harirah ""...."

"""Rasssss !!!Sai gaban Saude ya buga da k'arfi......"

"Hak'ik'a idan baki yasan abinda zai fad'a,,, baisan abinda za'a mayar mai da shi ba"

"Saude ta yi kuwahh!! da k'arfi,,, tayo cikin Hadiza tana cewa ""wallahi yau saina ci ubanki Ibrahim da"

"uwarki mazinaciya Salamatu.. Shegu d'iyan banza yau saina murji bakin ki karuwar gida kawai da ke,,, tsohuwar karya aladan"

"Hadizatu bata bari Saude ta k'arasa maganar ta ba,,, kaji kauuuuuu!! Ta shata mugun mari biyu mai rai"

da lafiya....

Wanda sai ta Saude ta lula a wata duniya .

"Hadiza ta nuna ta da yatsa,,, ta ce ""bari kiji na gaya maki duk abinda zakiyi ya tsaya akanmu,,, amma"

"banda zagin iyayenmu.. Idan bakisan darajar na ki ba to mu munsan darajarsu,,,,, na rantse da girman Allah Saude na shafe ki a iskanci da rashin mutunci Saboda da ni idan rayuwa tah ta b'ace, zan iya aikata komi kuma Anti Amina jinina ce kuma 'yar uwata duk wanda baya son ta,,,, to nima bana k'aunar shi har"

"abada"""

"Amina da taga abin bana k'arewa ba ne,,, ta ce ""Haba Hadiza bai kamata ki biye mata,,, wannan bai dace"

"da ke ba ""..Zata ja hannun Hadiza zuwa d'aki,,, Hadiza ta jaye hannunta da k'arfi......."

"Ta ce tsayaaa Anti!! Duk ke kika jama kanki raini da walak'anci,,, saboda hakurinki yayi yawa... Wallahi ko"

"ni ko Saude a gidan sai an kwashi wani daga cikinmu,,, bazan k'yale ta ba saboda na fahimci bata gadi mutunci ba,, yi tafiyar ki d'aki barni da ita "".."

"Saude ta d'ago kunburarrar fuskarta da tasha ,,,ta kalli Hadiza ci ke da tsananin tsana.... . ."

"Ta ce ""Hadiza ni kika mara wallahi sai kiyi nadamar marin da kika yi min,,,,,, akan wannan marin sai kinyi"

kukan da baki tab'a yi ba da ke da iyayenku Sai nuna miki ba'a tab'a Saude d'iyar Galma akwana

"lafiya "". Ta fad'a tana share bakinta saboda jinin da ya fito mata akan mariii"

"Hadiza ta ce ""Ashe k'aryar iskanci kike tak'ama da shi,,, na d'auka mugun duka zakiyi mini yanzu,,,"

"saboda haka duk abinda zakiyi ina nan ina jiranki,,,, so na ke gobe ko yanzu in mutu a d'auki gawata. K'aryar banza kawai """

"Saude ta ce ""zaki gani komi zai faru da ku,,, sai kunyi kuka wanda ya fi bugu zafi tare da nadama mara"

"amfani "".. Ta shigewar ta cikin d'akinta"

"""Babu abinda zamu gani sai alkhairin Allah "".Cewar Hadiza"

"Hadiza ta dubi Amina,,, taga tayi shiru kuma jikinta duk yayi sanyii......"

"Ta ce ""ya naga jikinki yayi sanyi,,, ba duk ke kika jama kanki raini ba Kina kallonta tana zagin iyayenmu"

"kina k'yaleta,,, to ai ki cigaba wata rana kashi zata baki ""..."

"""to ya zanyi ?kisan bana son tashin hankali da fitina, shiyasa kawai nake k'yale ta "".Cewar Amina..."

"Hadiza ta ce ""yayi k'yau je kiyi ta k'yale ta ""..."

"""To mi zanyi mata Hadiza? """

"""ke kika sani,,, ni babu ruwana je kiyi ta sanyin zuciya ""Tayi mata gatse......"

"""Haba yi hak'uri 'yar k'anwatah """

"""Babu komai Anti,, Allah dai ya sauwak'a "".."

"""Amin "".."

"Amina ta shige cikin d'akinta,, ayayinda Hadiza ta yi wucewarta zuwa gidansu"

"****Da misalin k'arfe biyar na maraice,,, sai ga Iya Delu da Abu sun shigo cikin gidan,,, babu sallama"

"babu komai,,, direct sai d'akin Saude tana zaune tana cin tuwo da miyar kub'ewa d'anya"

"Suna shigowa tayi musu barka da zuwa,,, tare da nuna musu tsananin farin cikin ta"

"Ta shimfid'a ma Iya Delu tabarma,,, tare da kawo musu abinci da ruwa.. Iya da Abu su daddage suna ta"

zankad'a babbar loma tare da wage k'aton bakinsu suna cin abinci kamar kamun yunwa .

"Bayan sun gama cin abinci ne, Iya Delu ta gaya mata cewa Inna Harira ta ce a kawo Abubakar"

"Saude ta ce ""babu komai ai ""sannan ta kawo labarin fad'ansu da su Hadiza ta gaya mata,,, amma bata"

"fad'a mata cewa Hadiza ta mare ta saboda abin kunya ne gare ta.. Ta mare ta bata rama ba,, ta nuna cewa Inna Harira taje wurin boka ta amso mata maganin da za'a sakama Amina mugun ciwo......"

"Iya Delu ta ce ""to babu matsala,, gadai wani na mallaka da tace in baki ""Ta mik'a mata ledar garin magani"

cikin gorar yoghurt. Saude ta amsa ta

"ce ""Iya Delu kice mata nagode sosai,, sannan kada ki manta taje ta amso mini maganin wurin boka"

"Abu ya chafke maganar,, ya ce ""Inna Saude sun fa sake komawa wurin boka ya ce musu,,, ki fara aiki da"

wannan magani kuma har yanzu da sauran lokaci kafin asiri ya fara aiki akansu. Wai sai nan gaba

"Delu ta ce ""waya gaya maka Wannan maganar?"".."

"""kaka Harira da Inna Laure, sune suka fad'amin na gaya miki ""..Cewar Abu"

"Saude ta ce ""Babu damuwa,,, zan jira lokacin duk sai sunyi kuka da idanunsu... Shegu dangin mayu kawai"

"da su ""......"

"Iya Delu ta karkace baki ta ce ""kwantar da hankalinki,,, duk sai sun ci kutumar buro uban su... Mi ki keci"

"na baka na zuba,,, ai ni da kike ganina ko son jin sunan kishiya bana so,,, balantana ace ina da ita ai kashe ta zanyi in kashe banza... Ni nan banida imani ko tausayi ko kad'an shiyasa ta mu tazo d'aya da Lanti da Harira,,,, mu sa akashe rai bamu d'auke shi a bakin komai ba """

"Saude ta ce ""haka shi yafi dacewa ai ,babu sani babu sabo, babu tausayi babu imani """

"Abu ya ce ""Ai ko ni kad'ai zan iya kashe mutum,, saboda haka babu d'iyar shegiyar matar da ta isa ta ta"

"kamu a cikin gidan nan """

Saude da Iya Delu suka fashe da dariyar k'eta......

"Iya Delu ta ce ""sai d'an Innarsa,, barewa bata tuma d'anta shi koyi rairahe koshi ya zo tuma ya ke......"

"""Fad'i ki k'ara fad'a Iya Delu,,, wannan haka yake sai ni d'an Laure jikan Harira Galma ""Abu ya ce....."

"Saude tace ""maganar ka haka take tabbas "".... .Saude ta fad'a....."

"""wallahi kam ""Cewar Delu...."

"Suka cigaba da firarsu ta yadda zasu b'ullo ma lamarin Amina,,, tare da shan alwashin ganin bayanta,,,"

domin Saude ta mallaki Aliyu da komai na shi ita kad'ai...... .

"_*Har ila yau ku cigaba bina,,, domin jin yadda zata iya ka ya a tsakanin su....................."

*_&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 136-140

Suka cigaba da firarsu ta yadda zasu b'ullo ma lamarin Aliyu da Amina. Tare burin mallakar Aliyu ga

Saude ita kad'ai..

"Alokacin ne Iya Delu ta kalli Saude,, tace ""to ni Saude so na ke in wuce gida yanzu,,, saboda kada maraice"

"tayi k'warai. Ina nan zaune gashi ni kad'ai zan wuce can gida "".."

"Saude tace ""Haba Iya yanzu yanzun nan zaki wuce gida,,, mi kike tsoro kada kiyi dare ai ba miji gareki ba"

"balantana kiji tsoron kada ya yi miki fad'a ko?""..."

"""Ai shi ne nima na gani,, ayyah su Iya na fahimci kamar tsoro kike ji kada 'yan fashi su tare ko.. Karki"

"damu babu abinda zai same ki muddin mu ne tantiran gari "".Cewar Abu cike da shed'anci da rashin kunya...."

"Iya Delu tace ""Kunji mun 'yan iskan yara,, ai ko naji tsoro ai tsoro gaskiya ne. Kai da kake cewa in kwantar"

"da hankalina,, ai naga batare zamu koma ba ko? zaka zo kana min wasu maganganu na banza ""..."

"""A'a Iya ayi hak'uri ba fad'a ba ne "".Cewar Abu."

"Saude tace ""Allah ya baki hak'uri Iya Delu,, ni wasa ce kawai nake miki. Ina laifin wanda ya zo ya kawo"

"maka ziyara da kuma son cigabanka,,, Allah ya bar zumunci da k'auna ai ni nagode sosai wallahi "".."

"""Amin amin inda gaske kike ja'irar yarinya "".Fad'ar Iya Delu..."

"Saude tana gama fad'ar wannan magana,,, ta shige cikin d'akinta.. Ta d'aukoma Iya Delu sabulun wanki"

"guda hud'u tare da kud'i d'ari biyar,,,, ta bata domin ta yi kud'in mota zuwa garin Shiko..."

"Iya Delu ta amsa tare da godiya,,, sannan ta yi murna da farin ciki sosai ga wannan k'yautar da Saude ta"

bata....

"Ta kalli Saude,,, sannan tace ""to ni zan wuce gida,,nagode sosai da nuna kulawa ""...."

"""Ai ni ce da godiya wallahi,, saboda gaskiya kinada k'ok'arin zuwa ziyara da kuma kawo min abinda zai"

"amfane ni. Kinga kuwa ni ya kamata in gode miki sosai ba ke ba "".Cewar Saude.."

"Iya Delu tace ""karki damu Saude,, ai ana tare saboda ni da

Please Login or Register in order to submit comment