You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tarbiya da kuma karamcin gidansu Saude......."

********************

"Alal hak'ik'a a wannan ranar Inna Harira, Laure, Saude sun kwana da tsananin farin ciki na cikar burin"

Saude.......

"Saude ta yi murna da farin ciki mai yawa,,,, domin azahirin gaskiya baki tab'a zato ko tsammanin Aliyu zai"

"zamo miji a gare ta ba.. Ta sha alwashi kuma ta d'au aniyar zata rik'e bokaye da 'yan bori hannu bibbiyu,,, saboda ta sa aranta su ne suka sa akayi auren ba Allah ba......."

"Su Inna Harira sun yanke shawarar,,, zata tafi da Abubakar domin ya zamo mata garkuwa ko katanga a"

"gidan auren ta... Kuma yarda ta amince da buk'atar su,,,, saboda tasan ko Abu shegen kansa ne..... ."

"Ta k'uduri niyar sai ta tarwatsa musu duk wani farin ciki da walwalarsu,,, sai ta zamo musu guguwar"

"annoba mai tarwatsa gida,, duhu mai kauda haske, bak'in ciki mai gusar da farin ciki... Sannan zata zamo musu mugun ruwa mai rushe duk wani ginin da suka gina shi akan farin ciki da nishad'i.. Zata yi musu kishi mai cike da k'unci da tarin damuwa da namada wanda za'a iya kiransa da *KISHIN JAHILCI*. Zasu"

yaba ma aya zak'inta.........

_£Agurguje*_ .

After two weeks

"Rana bata k'arya,,, sai dai uwar d'iya ta ji kunya..."

"Ayau ne mutane da dama suka sheda d'aurin auren Aliyu Ayuba da Amaryarsa Saudatu Isiyaku,,, akan"

"sadaki dubu tamanin,,,a k'ofar Masallacin da ke garin Shiko........"

"A ranar kar ku so k'in ganin Ango,,,, ya ci wanka farar shadda tare da kwad'onsa kalar dark brown da"

"hularsa da takalminsa,,,, komai yayi cif-cif yayi matuk'ar k'yawo sosai Ya ta gaisawa da 'yan uwa da"

abokan arzik'i ....Cikin farin ciki da walwala da annashuwa.......

"Abangarensu Saude,, bayan ta ji an d'aura mata aure kamar ta zuba ruwa tasha ga k'asa,,, babu kunya ko"

"kuka ita da kanta ta ke shan hakin maye da na matse gaban ma ce, har da na k'ara girman breast ta ke"

"shafawa.. Cike da zumud'in zuwa gidan miji,,, bata jin kunyar kowa ko agaban mutane farin ciki ta ke nuna......"

"Mutane suna ta ayyukansu,, na hidimomin biki....."

******************

"Acan gidansu Aliyu,, suna nan suna ta hidimomin biki,,, hak'ik'a Inna Indo ta tara 'yan uwa da abokan"

arzik'i na nesa da na kusa.... .

Farin ciki kawai ta ke da murna tare da nishad'i....

"Acan gidansu Amarya ma,,, tun ana sauran kwana biyu aka je,,, aka yi jeran d'akin Saude.. Aranar Amina,"

"Hussaina da Hadiza. Sun sha zagi da habaice -habaice wurin dangin Saude,,, har da ce ma Amina juya sai dai ta ci tayi kashi.. Babu haihuwa aranar Amina ta zubar da hawayen bak'in cikin su Hussaina suna"

"lallashinta,,, ta k'ara tabbatarwa ita kam tayi bankwana da farin ciki da nishad'i har Abada.."

"Dad'in abin daga Amina har su Hadiza,,, babu wadda ta kula su.. Shi ne abinda ya k'ara k'onama dangin"

"Saude rayuwa,,, tare da k'ara tsinema su Amina...."

"Su ma su Amina sunyi hidima,,,, ta tara su Hussaina, Mama Habiba da su Maimuna tare da k'aunar ta"

Hadiza... Da kuma sauran k'awaye da mak'wabta da abokan arzik'i Da sauran mutanen da ta ke huld'a

da su......

"A haka dai, akayi taron biki,, mutane suka fara watsewa zuwa gidajen su......"

"Masu kai Amarya kawai,,, suka tsaya jiran lokacin kai Amarya da dare......."

K'arfe 9:00 dai -dai abokanin Ango suka kawo motoci domin d'aukar Amaryah.......

"Su Laure da k'awayen Inna Harira guda biyu,,, suka lullub'e Saude da gyale mai k'yau. Sannan suka saka"

"ta cikin mota,,, suma suka shiga babu wasu k'awaye ko mutane da yawa masu rakiyar Amarya zuwa gidan mijinta........"

"Ahaka dai abokan Ango suka ja mota zuwa hanyar Kamba,,, tare da su Laure da Amarya Saude babu ko"

d'igon hawaye ko razana........

"_Ku biyo ni domin kuji yadda zamantakewar su,,,,, zata kasance. .._&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By Sis Nerja'art_

"_*Ina Gaisuwa ga k'awayen juna,, 'yan ukku masu k'aunar juna...*_"

Masa'udat Abdullahi

Maimuna Usman

Saratu Shehu

*PAGE* 121-125

Suna ta tafiya a cikin motar har suka kawo Kamba.. Unguwar illelah area da ke cikin garin Kamba....

"Abokanin Ango suka faka motarsu waje,, su kuma su Laure suka fito daga cikin motar da Amarya,,"

alokacin ne k'awayen Inna Harira suka yi gud'a na alamun sun kawo Amarya Saude....

"Suka ja hannun Saude sai cikin gidan.. Babu a shiga da k'afar dama balantana ayi bismillah,,, duk jahillai"

"ne da shed'anun mata aka tara. Suka kaita har cikin parlorn ta,, suka samu wuri saman kujeru suka"

zauna.....

"Alokacin ne Laure ta dube su,, tace"" Iya Delu da Inna Lanti ba fa anan zamu kwana ba komai dare.. Ya"

"kamata kuyi mata nasihar da zakuyi mata,, sai mu wuce gida yanzu "".."

"Iya Delu da Inna Lanti,, suka kalli juna tare,,, suna wani k'yafce -k'yafcen idanu... ..Na shed'anci......."

"Iya Delu tace ""Wa ne nasiha za'a yi mata yanzu,,,ai yaran yanzu kunsan komai na abinda ya danganci"

"aure.. Balle Saude da ta saba ba maza sarin jikinta suna kwasar gara ""...Ta fad'a cike da shek'iyanci...."

"Inna Lanti ta ce ""haka ne kam gaskiyar maganarki Delu,,, ai ke Saude ba yarinya bace,, a wannan harka"

"kawai da yazo ta b'ude cinya ya kwashi rabonsa.. Kishiya kuma idan ta bari ta raina ta itace cikin matsala. Ba mu ba mu dai mun kawo ta ne don su ci uban juna "".."

"Laure da Saude,, suka dubi junansu"

"Sannan Laure tace ""Dad'ina da ku Iya Delu bakuda kunya balle mutunci... Nasan sanda kuka yi k'urciya"

"kun buga buro uba,,, da duniyanci ""..."

"Saude ta ce ""Ai su Inna Lanti anyi tsofaffin banza,, Da tsufanku bakujin kunyar zina ""...."

"Sukace tare ""Kamar ko kun sani,, ai da k'urciya munyi bada sari kamar yadda uwarku ke badawa.. Kuma"

"ita ma da kuke gani tsohuwar banza ce,, ta ma fimu rashin imani da tausayi ""....."

"""Ya isa abar maganar,, kunsan gidan suruki kuke kada ya jiyo ku. Asirin mu ya bayyana "".Laure ta fad'a......"

"Iya Delu tace ""Ai munyi shiru,,, mu rufama kanmu asi...."

"Kafin ta kammala maganar ne,,, sai ga abokanin Ango su Adamu da Shehu (Baban Abbas) da wasu"

"mutum biyu sunyi sallama. Sun shigo cikin parlorn,, bayan sun zauna anyi gaishe -gaishe. Sai ga Aliyu"

shi ma ya shigo parlorn.....

"Aka had'a su tare,, akayi musu nasiha da wa'azi da addu'o'i masu ratsa jiki. Tare da nuna musu"

muhimmanci zamantakewar aure da kuma hak'uri da juriya a rayuwa....

"Bayan gama komai na al'ada,,sai suka aje musu ledar kaza da drinks,,tare da umurta su Iya Delu su taso"

su kaisu can Kamba. Su iya Delu suka tashi tare da yi musu bankwana da kuma fatar zaman lafiya mai

d'orewa.......

"Suka watse aka bar daga Amarya sai Angonta.. Aliyu ya yi Saude nuni da su tashi suyi d'aki,,, ya shiga"

"d'akin ita ta bishi..Ya umurce ta je tayi alwala bayan ta yi da yake shi ma yayi,, ya jata raka'a biyu na godiya ga Allah....."

"Bayan sun kammala sallah,, suka yi addu'a. Aliyu ya yi mata wasu d'an tambayoyi game da addini,amma"

Saude ko tambaya guda bata amsa ba.. Bai wani mamaki ba saboda aikin asiri....

"Ya ce mata yana zuwa,, ya d'auki leda d'aya ta kaza domin ya kaima Aminarsa.. Ya fita daga d'akin ya nufi"

na Amina......

"Hak'ik'a Saude taji zafin wannan abu da yayi mata,, wato har daren farkonta sai ya nuna mata matarsa"

"tana matuk'ar muhimmanci a wurin sa ko. Zasu ci ubansu daga shi har ita sai sunyi nadamar sanin Saude a rayuwar su. Idan ya mayar da ita shashasha ba,,, har daren farkonta sai ya tuna da matarsa,, lallai"

kuwah za'a yi tashin hankali da bala'i a cikin gidan nan. Haka dai ta yi ta k'ulle-k'ulle a cikin zuciyar tah.....

**********************

"Shi kuma Aliyu yana shiga tare da sallama a bakinsa,,, ya aje ledar gefen gado tare da k'urama Amina ido"

"saboda ta jima da kwanciya ... Yana kallonta cike da tsananin k'aunar ta da kuma tausayi,,hak'ik'a Amina ta yi masa halaccin da ba kowace mace ce zata iya yima mijinta ba...Ta sadaukar da rayuwarta da farin cikin ta domin samun farin cikinsa,,, shi kansa yana ganin baiyi ma Amina adalci ba saboda bata rage da"

"komai na jin dad'i ba,,, a zamantakewar rayuwar su ta aure......."

"Bayan ya gama k'are mata kallo,, ya sumbaci goshinta tare da yi mata addu'ar gama lafiya da kuma sanya"

mata albarka........

"Ya kashe mata wutar d'akin,, sannan yaja mata k'ofa ya rufe...... ."

**********************

"Bayan ya fito daga d'akin Amina,, ya shigo d'akin Saude ya iske har ta sa kayan barci. Ta kwanta shi ma"

ya zo ya kwanta kusa gare ta cike da murmushi ..Tare da rage kayan jikinsa zuwa masu sauk'i....

"Haka dai sukayi mu'amala ta auratayya,,, batare da Aliyu ya samu Saude budurwa ba. Aliyu ya ji haushi"

"da takaici sosai,,, amma bai nuna mata ba......"

*********************

"****Da safe k'arfe 5:50am bayan sallar asuba,, Amina ta gyara bedroom da palourn ta,,, tare da girka"

ma Amarya da Ango breakfast da wuri.... ....

"Bayan ta gama komi,,, ta shiga tayi wanka tare da tsantsara kwalliya mai k'yau da gani. Ta sa lace mai"

"kalar blue and lemon green,,, dogowar riga ce kuma tayi mata k'yau matuk'a....."

"Ta feshe jikinta da turare,, da kuma humra mai k'amshi.."

"Bayan ta kamalla ne,, ta dawo palourn ta kunna TV show tana kallo.. Hankalinta kwance ga kuma wani"

masifar k'yau da k'ara.......

"Acan bangare su Saude,, bayan sun yi sallar asuba sai da Saude ta sa ke jan ra'ayin Aliyu suka biyama"

"juna buk'atar su,, tare da sa ke komawa barci....."

"Idan baku manta ba,, kunsan Saude ta riga ta saba mu'amala da maza kala-kala. Shiyasa abu kad'an baya"

"isar ta,,, ta fiso kodayaushe aita yin abu guda.........."

"Sai wajen k'arfe 10:30am suka tashi da barci,, bayan sun tashi suka yi wanka tare da shiryawa tare...."

"Saude atamfa ta saka red and white,, shi kuma Aliyu yadi fari ya saka mai k'yau da gani......."

"Saude cike da kwarkwasa da karuwanci,,, taja hannunsa sai parlorn. Bayan sun iso ne Amina ta yi musu"

barka da kwana.. Aliyu ya amsa Saude ma ta amsa tana yatsina fuska tare da d'an d'ingishi a k'afa wai ita kenan ya same ta budurwa......

"Amina tayi musu bismillah tare da nuna musu abinci,, ta kuma yi serving d'in su tare.... ."

"Suka fara cin abinci,, cike da natsuwa da kwanciyar hankali....."

"Saude ce keyi tana satar kallon Amina,, tare da jin haushi da bak'in ciki na ganin Amina ta zarce ta komi."

Wanda ake bid'a ga mace a rayuwa.

"Ta d'auka k'yawon Amina bai kai haka ba,,, amma sai ta ganta ta wuce zato da tunaninta...."

"Ahaka dai suka cigaba da cin abinci,, har suka kammala......."

Bayan sun gama cin abinci ne. Aliyu ya yi musu nasiha da su zauna lafiya tare da hak'uri da juriya a

"zamantakewar su... Yana kuma gargad'insu akan bai son tashin hankali da bala'i, da neman magana. Kowace daga cikin su taja girmanta da kuma tsayawa inda Allah ya aje ta. Amina ita ce uwargida taja girmanta, Saude ita ce k'arama ta tsaya ga kanta. Baya son abinda zai kawo sab'ani a tsakanin su,, don haka dan Allah su kiyaye ,,ya raba musu kwana.. Kowace daga cikin su kwana biyu zata yi tana girki idan"

ya kammala sati guda a d'akin Saude.... .

"Sun amince kuma babu wadda ta yi mishi musu,,, haka suka cigaba da fira shi da Amina... Saude dai bata"

saka musu baki ba akan jin bak'in ciki da haushin Amina..

"Haka dai Saude ta cinye kwanakinta bakwai,,, a gidan Aliyu cike da tsananin nishad'i da jin d'adi....... ."

*********************

After one weeks

"Saude ta amshi yin girkin gida,, ranar da ta fara yin girkin gida. Babu dad'i ballai d'and'ano haka nan ta"

"dafa shinkafa duk ta chab'e,, miya kuma ta cika gishiri da tankwa......."

"Kowa daga cikin su ya kasa cin abincin,, dole babu yadda suka iya sai da suka jira Amina ta sake yi musu"

jollof rice and beans. Haka suka ci cike da jin d'adin girkinta......

"Washe gari ma haka Saude ta sa ke kwab'a musu abinci mara dad'i,,, dole kuma sai da Amina ta d'ora"

"wani.Ganin irin yadda bata iya abinci ba ko kad'an,,, Aliyu ya dakatar da ita ga yin girkin gida.. Tare da jin"

"haushinta da takaicinta cikin ran shi,, amma ba ya iya nuna mata ko afuska.. Ganin irin abinda yake faruwa yasa yaje gidansu Amina,,, ya rok'i Mama akan ta bar Hadiza tana zuwa tana taya Amina girki..... ."

"Mama ta amince bata re da nuna wata damuwa ba,,,, haka dai Hadiza ta cigaba da zuwa da rana tana"

taya Amina ayyukan gida...

"Ita kuma shegiyar ba abinda ta iya sai kwana da miji,, sannan ga shegen cin kamar rak'uma,,, an iya ayi"

wanka da kwalliya ana jiran dawowar miji.. D'akin ta ma ba'a kodayaushe ta ke shararsa ba.... .

"Idan tayi kwalliya,, Amina ta yi ta kanji bak'in ciki tare da yi mata tsaki da harara a kowane lokaci......"

"Amina tana lura da ita,,, amma ko kula ta bata yi balantana ta damu....."

"Ganin Amina bata kula ta ba,,, yasa taji haushi sosai.. Ta d'au niyar canza takon salonta......."

"Ana nan wata rana,,, Saude tana son ta nuna Amina mugun halinta na aiki,,, ta iske bokiti cike da kayan"

"Amina ta wanke abinta fes,, sai kawai Saude ta d'auki bokitin ta yarda ga k'asa. Tare da sa k'afarta tana taka kayan ta yadda zasu mak'al-mak'al da daud'a......"

"Bayan ta gama taka su yadda ta ke so,,, ta samu wuri bakin k'ofar d'akin ta ta zauna jiran Amina...."

"Bayan wani lokacin,, sai ga Amina ta fito daga d'akinta domin ta shanya kayanta ga igiyar shanya.. Tana"

"zuwa wurin bokitin ta iske kayanta barbaje ga k'asa walak'ance... Ta dubi Saude cikin lumana ta ce ""Saudatu dan Allah ko kin bar k'ofar gida bud'e ne,,, har awakin mak'wabta sun shigo sun zubar mini da"

"kaya.. Ko baki sani ba ne? ""....."

"""ban gane na bar gida bud'e ba,,, to bari kiji in gaya maki ni nan Saude ni na zubar miki da kaya... Ko"

"akwai abinda zaki iya yi min ne,,, kuma wallahi ba ni ba ce akuya uwarki ce Salamatu akuya da ubanki"

"Ibrahim tsohon bunsurunta mai mata ciki har aka haife ku ke da Hadiza "".Saude ta fad'a cike da cin mutunci da tozarci...... Tana zabure -zabure kamar 'yan dambe........"

"Amina ta ce ""Haba Saudatu mi ye yayi zafi haka?,,, har da zaki watsemin wankakkun kayana.. Na"

"tambaye ki kuma kizo kina zagin iyayenah,, iyayenah basuyi miki komai ba. Don Allah ki daina zaginsu duk abinda zaki yi ya tsaya iya kaina "".Ta fad'a cikin tattausan lafazi mai dad'i........"

"Saude ta matso kusa ga Amina,, ta kalleta sama da k'asa tare da yi mata walak'antacce kallo....."

"Ta nuna ta da yatsa,,, ta ce Amina ki ke ko wa,, to bari kiji ni da kike ganina nan bana tsoron uban kowa."

"Ciki kuwa har da ubanki,, sannan kaya ne na zubar kuma na taka su to sai me,,, mi zaki iya yi? Na zagi ubanki da uwarki kuma ba zan daina zaginsu ba har k'arshen rayuwata ba.. Dan gundunbulin kutumar"

"ubanki k'warton mata kuma b'arawo,, idan baki d'auki mataki ba shegiya ki ke,, 'yar iskar banza karuwa"

"""......"

"Hak'ik'a ran Amina idan yayi dubu,, to ta b'aci da ya ke ba ma ce ce mai son fitina ba.. Ta dubi Saude tace"

"""Ashe haka ki ke Saudatu,, ai ni banga abin fitina ba ko fad'a a nan ba. Kuskure ne kin riga kinyi kuma ya wuce ""....."

"""kuskure kuma,, to ba kuskure ba ne da gan gan na yi shi.. Ba wani kanikanci da zaki yi ma magana ta.."

"Ke fa ni zaman kishi ne ya kawo ni,,ba zaman lafiya kuma idan ke shegiya ce kuma munafika,,, ki k'yale ni wallahi ni da ke a cikin gidan nan ba za'a yi mai k'yau.. Duk kika koma yi min shisshigi sai na ci Ibrahim mai fuskar rak'umi da rashin kauri kamar taliya.. Kana ganinsa kaga tsohon banza kuma azuraki "".Cewar"

Saude cike da hargowa da tashin hankali......

"Amina da ta ga abin na Saude kamar shafar Aljannu,, ta ce ""Idan maganar da nayi ce ta b'ata miki rai,,"

"Allah ya baki hak'uri Saudatu ""....."

"""da hak'uri ta mutu sadakar nawa Salamatu ta ba ni,,,, - KISHIN JAHILCI ne kuma yanxu muka fara da ni"

"da ke a cikin gidan nan.. Babu shegen da ya isa ya rabamu wlh,,, kuma ki sani sai na salwantar da rayuwarki,, sai kin zama abar k'yama ga kowa. Tsohuwar iblishiya kawai da ke gadon mugun abu "".Saude ta ce cikin raini da walak'anci......"

"Amina ta dubeta,, ta ce Allah ubangiji ya raba ni da KISHIN JAHILCI ya kuma tsare ni daga shairin ki."

"Sannan ina son ki sani mutuwa ta da rayuwa baga hannunki ya ke ba,, a hannun Allah ya ke,, Allah ya yi tsari da ke. Na barki lafiya Saudatu ""...."

Amina ta fad'a tare da shigewarta a cikin d'akinta.......

Saude ta d'aga murya da k'arfi.....

"Ta ce ""da ki tsaya a gwabza idan ba tsoro ba!! Don ubanki wallahi sai kinyi nadamar tsayawa musanyar"

"kalamai da ni Ba'a tab'a da Saude d'iyar Galma a kwana lafiya,,,, kuma daga yau bari kiji kin riga kinyi"

"bankwana da kwanciyar hankali da farin ciki,,, kin k'ulla aure da masifa da bala'i da jafa'i ko shegen mijinki bana tsoron shi balantana ke karan kad'in miya.. Idan kin cika fito waje wallahi da sai nayi miki bugun halaka,, in da ke ki in daki banza dangin mayu dangin tsiya da talauci.. Sirrinki a tafin hannuna ya ke babu abinda ban sani ba ,,,game da ke tsinana d'iyar tsinannu "".Haka dai Saude ta zauna tana ta zagin"

"Amina da iyayenta,,, ta dad'e tana yi sannan ta gaji ta shige cikin d'akinta........"

"Aranar Amina tayi kwanan bak'in ciki da damuwa,,, mara misaltuwa. Ita kanta tasan Aliyu ya jajibo musu"

"annobar da zata iya kashe su gaba d'ayansu.. Ta dad'e tana kukan zagin iyayenta da Saude tayi,, tasan wannan farawa ne akan nan gaba. Wannan wa ce irin k'addara ce? Mai cike da k'unci da tarin damuwa,, bata saba da tashin hankali ba ko damuwa,,, amma yanzu ya zatayi guguwar annoba ce ta bayyana a"

cikin gidan su........

"Aliyu ya na dawowa kuma,,, Saude ta kwashe k'arya da gaskiya ta gaya masa. Wai Amina ta zagi iyayenta"

har ce mata akuya kuma annoba.....

"Aliyu tara su su duka yayi fad'a tare da nasihohi,,, inda ya nuna musu shi baison tashin hankali da fitina...."

"Ya ce ma Amina ai duk laifinta ne domin ita ce babba saboda haka taja girmanta,,, kuma ta sake zagin"

"iyayen Saude da ce mata akuya.. Idan ba haka rayuwar ta zata b'aci kuma ya iya korarta,, ta bar masa gidansa saboda bata tashi tadda mugun halinta ba sai da ya k'ara aure don ta raina sa.."

"Haka dai ya samu Amina,, ita kad'ai da cin mutunci. Saude kamar ta zuba ruwa tasha a k'asa a kan jin"

dad'i.........

"A wannan dare Amina tayi kukan bak'in ciki da damuwa,,, saboda bata tab'a zaton har akwai ranar da"

"Aliyunta zai ci mata mutunci ba akan wata,, bata tab'a zaton har ranar da Aliyunta zai juya mata baya ba. Sannan kuma ya fifita wata akanta. .. _(kiyi hak'uri Amina hak'ik'a kin bani matuk'ar tausayi,,, komai"

yayi farko zaiyi k'arshe. Allah shi ne zai yi miki sakayya tun anan duniya)_.... ......

"Haka rayuwar Amina ta cigaba,,, da tafiya cike da k'uncin rayuwa da bak'in cikin muguwar Kishiyarta........."

"_*Ko zaman na su,,,, zai iya chanzawa ne ..Sai ku biyo ni jiiiiiiii *_&&&&&&"

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 126-130

"****A bangarensu Inna Harira da Laure kuwah,, bayan ta yi aure suka cigaba da iskancinsu tare da"

zaluntar mutanen gari......

"Arayuwarsu ba su k'aunar mutanen garin Shiko ko kad'an,, domin cewa suke su duka munafukai ne"

"kuma masu sama mutum ido ne... 'Yan hayar su ma rashin mutunci da tozarci suke musu idan ka bari ko naira biyar ta rage baka biya su ba,,,, sun sa ma zuciyar su rashin kunya da rashin tausayi......"

"Ana nan wata rana,,. Laure ta kalli Innarta,, ta ce ""ni kuwah Inna sai yaushe za'a kai Abu gidan Saude..."

"Kuma sai yaushe zamu sa ke komawa gidan boka ne? "".Ta ce tana aikin k'ulla miyar kad'i da gishiri na saisuwa....."

"Inna Harira ta ce ""ba yanzu zamu koma ba,,, saboda abada d'an lokacin da Saude zata fara fitowa..."

"Kuma na gaya muku boka ya ce a yanzu ba kowane irin asiri zaiyi tasiri akansu ba,,, Amma zamu sa ke komawa zuwa wani lokacin... Batun maganar Abu kuma jibi zamu ce shi Aliyun ya xo ya d'aukesa,,, idan bai zo babu matsala Lanti ko Delu sun san gida zan basu kud'in mota su kaishi can wurin Saude... Ai ba"

"zan bari 'yata kishiya ta wahalar da ita ba muddin ina raye ""......"

"Saude ta ce ""hmm Inna da kam yafi,,, saboda naji mutane na cewa matar nan ta Aliyu duk ta shanye shi,,,"

"baya ganin kowa sai ita... Mugun sonta ya ke,,, wai ko wuta aza ga hanya ta ce ya tsallaka,,, zai tsallake saboda mugun bid'a da yin asiri "" ..Laure ta ce cike da gulma da tsegumi......"

"""Ato taje ta yi mana,,, idan asiri ta ke tak'ama da shi ta kawo gidanshi,,, saboda wallahi ko zanyi yawo"

"tsirara bazan tab'a barin ta salwantar min da Saude ba... Kowace hanya zanbi sai na bi domin in k'wato mata hak'k'inta,,, saboda haka Laure sha kuruminki Harira tana tare da ku akodayaushe,, akowane lokaci... Kada kuji shakku ko tsoron uban kowa,, ni na baku dama ""..Cewar Inna Harira......"

"Laure ta ce ""ai shiyasa muke jin dad'i saboda samun uwa ta gari irinki,,, mai son farin cikin d'iyanta.."

"Allah ya bar mana ke Inna ""...."

"""Amin amin ""Cewar Inna Harira........"

"Suka cigaba da shawarwarinsu,,, ta yadda zasu samar ma Saude jin dad'i mai d'orewa,,, tare sanin hanyar"

da zasu bi su kashe Amina bayan Saude ta azabtar da ita cikin wahala da k'unci..... ..

********************

"Acan gidansu Amina kuma,,, bayan Hadiza tana zuwa taya Anti Amina ayyukan gidan,,, to bayan ta dawo"

ne tayi wanka tare da cin abinci....

"Ta samu Mamanta zaune,,, ita samu wuri kusa ga mahaifiyarta,,, ta zauna......"

"Ta dubi Maman ta ce ""Agaskiya Mama ni na gaji da zuwa gidan Yaya Aliyu... Domin taya Aunty aiki,,, ita"

"matarsa babu abinda ta iya sai kallon banza da hararar mutane,,,, tana habaice -habaice tare da zaginsu... Wallahi Mama zuciyata ba zata iya d'aukar walak'ancinta ba tare da rainin wayo,,, idan ba haka wata"

"rana sai an kwashe ta saboda kashin k'warai zanyi mata wallahi "".Ta fad'a cike da jin haushi da"

takaici........

"""Haba Hadiza da girmanki da wayonki zaki biye mata,,, idan ta zage ku baya lik'ewa ga jikinku.. habaice -"

habaicenta ai na banza saboda ba duka ba ne. Na rok'e ki Hadiza da ki kasance mai hak'uri da juriya

"akan mutane da kuma rayuwar duniya,,, duniyar nan ba matabbata ba ce ,,sannan ba'a nan zamu zauna ba din-din Saboda haka ki k'yale ta kada ki nuna mata kin maji abinda ta ke fad'a,,, ki fita batun ta"

"""......Mama ta fad'a cike da tausayawa rayuwar Amina......."

"Hadiza ta ce ""to Mama amma kin san babu dad'i wlh ,,,,ai kishi ba hauka ba ne sannan ba JAHILCI ba ne..."

"Wallahi ni Aunty Amina na ke tausayawa ba kowa ba,,,, hak'ik'a tana da matuk'ar hak'uri da kawaici,,, da"

"ni ce ita da akwai masifa da bala'i wlh.. Saboda agaskiya yaya Aliyu duk chanza mata kamar ba shi ba Mama ""....."

"""Hadiza akullum ina nuna mi ki muhimmanci hak'uri a rayuwa.. Hak'uri shi ne jigon zaman rayuwar"

"duniya gaba d'ayanta,,, ina son mu taya Amina da addu'a akan Allah ubangiji ya kare ta daga shairin mugayen mutane.. Ina so kuma ki zama kamar Amina ko ki zarce ta ,,,don haka dan Allah ki yaye ""...Inji"

Mama......

"Hadiza ta ce ""Insha Allah Mama zan kiyaye,,, zan kwatanta in ga ni ko zan iya amma hak'uri Mama halitta"

"ce cikin jikin d'an Adam idan yayi maka shi ka da ce,,, idan baiyi maka ba babu yadda zaka iya yinsa ""..."

"Mama ta ce ""haka ne hak'uri baiwa ne,,, sai wanda Allah ya ba. Amma zaka iya kwatantawa ai kuma"

"zaka iya ""...."

"Hadiza ta ce ""wannan gaskiya ne,, Allah ya bamu hak'uri da juriya,,, na zaman rayuwa......."

"Mama ta ce ""Amin haka ya da ce,,,, ki ce tun d'azu Hadizatu......."

"""To Mama ""Cewar Hadizatu..........."

"****Cigaba da firarsu kawai suka yi,,,, cike da nishad'i da jin d'adi.. Tare da nuna Hadizatu muhimmanci"

hak'uri a rayuwar duniya da kuma bata shawarwarin k'warai ta yadda zata iya zama da kowa......

**********************

"*****A can gidan su Aliyu,,, Inna Indo ce zaune take cin kwad'on ramarta wadda ta ji k'uli -k'uli da"

maggi...... Tana ci tana kad'a kai akan dad'i......

"Alokacin Malam Ayuba ya na zaune,,, saman tabarma yana diba littafan addini... Alokacin ne Inna Indo ta"

"d'ebo masa ta shi rama,, ta ce gashi ya ci Ya nuna

Please Login or Register in order to submit comment