You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Harira mahaifiyarki k'awayen juna ne,,, tun"

"muna yara kinga kuwa babu abinda bazan iya yi miki ba.. Muddin zaki samu daraja da d'aukaka a wurin miji,,,, kuma ya fifita ki akan wata ""..."

"Saude tace ""Nagode sosai Iya Delu,,, hak'ik'a nasan ke mai k'auna ta ce Allah ya bar soyayya ""....."

"""Amin amin "".Cewar Iya Delu.."

"Iya Delu ta mik'e tsaye,, suma suka tashi tsaye domin rakata bakin garka..."

"Suka fito daga cikin d'akin,, alokacin ne suka iske Amina baiwar Allah tana jajjagen kayan miya. Suna"

"isowa kusa gare ta suka kalleta sama da k'asa,,, kallo mai cike da walak'anci da raini..."

"Amina na ganin Iya Delu,, ta duk'a har k'asa tace ""ina yini Inna,,, ya aka baro mutanen gida? "".."

"""idan ban wuni ba,,, zaki ganni shegiyar mata munafuka.. Ni zakiyi ma salon munafurci da azuzancinki"

"dan ubanki,, wato ke ga ta k'warai ko to Allah ya fiki duk salon kisisinarki da munafurcin ki zaman Saude daram a cikin gidan nan,, babu abinda zaki iya yi mata,, kuma wallahi kika koma gani na kika gaisheni saina ci kutumar buro ubanki. 'Yar iskar banza karuwa kuma juyar banza wadda bata haihuwa sai dai kici"

"kiyi k'aton kashi "".Cewar Iya Delu cike da tijara da cin mutunci..."

"""Ai Iya matar nan da kike ganinta,, muguwar munafuka ce babu abinda ya ke cikin zuciyarta sai"

"munafurci da k'ulle-k'ulle. Gaisuwar nan ma da tayi miki duk cikin kissa ne wai don ta saye zuciyarki "".Cewar Saude..."

"Abu yace ""ni wallahi yanzu ina marinki,,, in mari jakar banza.. Idan ba munafurci ba ina ke ina mu,, mi ye"

"had'in kifi da kaska ""...."

"Iya Delu tace ""gaya mata kai dai Abu,, ni ko uwarta bata isa ta saye zuciyata ba balantana ita shegiya"

"kuma munafuka ""...."

"Amina tana jin su kuma k'ala bata k'ara ce musu ba,,,, bayan gaisuwar da tayi ma Iya Delu.. Cigaba da"

jajjagenta kawai tayi taba iska ajiyarsu a kwandon shara..

"Sai da suka yi ma Amina ta tas,,, da zage-zage da komai sannan suka fita waje domin rakiyar Iya Delu...."

"Suna kawai bakin garka,,, Saude ta juya ta koma gida,, shi kuma Abu shi yayi ma Iya Delu rakiya har tasha"

ta wurin sabuwar kasuwa a garin Kamba....

"Saida Abu yaga tashin motarsu,, Iya Delu sannan ya juya domin komawa gida..."

**********************

"Saude tana shigowa gida,,, ta d'ebo k'asa cike da hannunta. Ta zuba cikin jajjagen Amina acikin turmin"

"daka,, duk jajjagen sai da ya b'aci da k'asa sosai baida sauran amfani...."

"Amina ta juyo da sauri tace ""Haba Saudatu wai ke wace irin ma ce ce wadda bata son zaman lafiya,,, ko"

"kad'an wannan abin da mi yayi kama.. Ke ba iya yin girki ba nazo ina son na had'ama mana abinci,,, zaki zo ki zuba k'asa a cikin turmi.. Wai mi kika d'auki kanki ne? ""..."

"""Na zuba k'asa acikin jajjage,, mi zaki yi kuma da kike cewa bana iya yin girki uwarki ce bata koyamin ba"

"shiyasa,,, ban iya girki ba wallahi Amina ni da ke a cikin gidan nan dole wani ya fita ya bar d'aya.. Ko ni ko ke juyar banza annobar wahala"".Cewar Saude.."

"Amina tace ""ke dai na fahimci komai naki,, idan ba'a yi rigima ba bakyajin dad'i. Wai mi yake damun"

"rayuwarki ne? Kishi ba jahilci ba ne kuma ba hauka ba ne,,, na rasa inda kika dosa da wannan masifaffen kishin na ki ""..."

"""Ai komai nake nufi kinfi kowa sani,,, nayi zafin kishi ga uwarki Salamatu na koya.. Idan kina son mu"

"zauna lafiya kice Aliyu ya sake ki domin ni kad'ai ya dace ni,, da ni yafi dacewa mu rayu da juna har abada,,, bada ke ba sannan ina son ki sani babu ke babu farin ciki da nishad'i muddin kina tare da Aliyu"

"muradin raina. Kwanciyar hankalinki kawai ki rabu da shi rabuwa ta har abada "".Cewar Saude..."

"Amina tace ""kee Saude!! Ban tab'a zaton bakida hankali ba sai yanzu,,, ban tab'a zaton kinada matsalar"

"k'wak'walwa ba sai a yanzu ajahilcinki da tunaninki nabar miki Aliyu ke kad'ai saboda ke kika fara aurenshi kafin ni,,, saboda kina ganin ke yafi dacewa da ke saboda son zuciya irin na ki.. To bazan bar miki Aliyu ba saboda idan ma bari ne,,,, ni ya kamata kibar min mijina domin atare kika isko mu amma zuwanki yasa kin tarwatsa mana duk wani farin ciki da nishad'inmu. Tare da kwanciyar hankali da jin"

"d'adi ""."

"""Na tarwatsa muku gida sai me,,, ba ni ce mara hankali gyatumarki ce da gyatuminki ne mahaukata.."

"Kuma bazan bar miki Aliyu ba miye zaiyi da juya mara haihuwa,, ai ko shi ya gaji da ke da kuma mugun halinki na munafurci da azuzanci"".Cewar Saude cike da masifa da bala'i.."

"Amina ta zubar da jajjagen da Saude ta b'ata a k""asa,,,sannan ta shiga kitchen ta sake d'ebo wani kayan"

miya... Ta fara jajjagawa..

"Sai asannan tace ""ke dai kika sani,, ko waye ya zagi iyayen wani nasa ya zaga.. Hak'ik'a kin raina da"

"iyayenki shiyasa bakida wani aiki sai zagin iyayen wasu,,, nagode duk abinda kike ki cigaba amma ki sani wata rana baza kiyi ba ""...."

"Saude tace ""idan na cigaba ai babu abinda zaki iya yi min,,, ko zaki je ne ki kira karuwar k'anwar ki Hadiza"

"tazo ta bani kashi,,, kamar yadda kika kirata a wancan karo... To bari kiji babu shegiyar kuma 'yar iskar da na ke tsoro a cikin ku daga ke har Hadiza .Aliyu ne dai bazan bar miki shi ke kad'ai ba saboda nafiki buk'atar sa,,, idan banda ki raina min da wayo zaki zo kina cewa banida hankali,,, tambad'add'a mai halin b'era "".Haka dai Saude ta cigaba da cin mutunci tare da zage-zage,,, da kuma tofin Allah tsine ma Amina"

tare da 'yan gidan su... .

"Haka ta cigaba da cin mutunci,, tayi ta gaji sannan ta k'ara gaba. Amina bata sake tanka mata ba domin"

"ta kula da cewa kwata -kwata Saude batada hankali,,,, kuma bata yi gadon halin k'warai ba... ..."

********************

"Acan cikin kasuwa rumfar su Aliyu,,, su Adamu zaune suna fira cikin mutanen cike da raha da farin ciki....."

"Alokacin ne Adamu ya dubi Aliyu,,, yace Abokina yana ga tun d'azu,,,muna magana baka saka bakinka"

"ba""..."

"Aliyu yace ""babu komai,,, rayuwar yau da kullum ce sannan kasan wani abu ""......"

"""Sai ka fad'a Aliyu "".Cewar Adamu..."

"""Wallahi Adamu ina cikin damuwa,,, na rasa dalilin da yasa na auri Saudatu... Sannan nakan rasa dalilin"

"da yasa ko Saude tayi wani abu wanda bai dace ba,,, bana iya yi mata magana ko fad'a. Sannan wani lokaci nakan ji tsanar ta amma wani sashe sone zai rinjayi k'iyayyar da na ke mata.. Ya zanyi da rayuwa"

"tah Adamu? "".Cewar Aliyu..."

"Adamu yace ""addu'a zakayi Aliyu domin ita ce takobin mumini,,,, alokacin baya da ka nuna kana son"

"Saudatu nayi matuk'ar mamaki abokina,,, domin nasan kai ba mai ra'ayin k'ara aure ba ne... Amma na"

"tabbatar akwai wata a k'asa ya zakayi da k'addarar ubangiji,, hak'uri zaka yi kawai tare da dagewa da yawan yin addu'a,,, nima zan taya ka da addu'a Allah ya ye maka abinda ke damunka "".."

"""Insha Allah abokina,,, zan dage da yawan yin addu'a domin kuwah jikina yana bani,,, ina cikin"

"gagarumar matsala da damuwa... Kuma naji na rage yawan son Aminatu tah "".Cewar Aliyu..."

"Adamu ya dube shi cike da tausayawa,,, yace ""karka damu abokina dukkan tsanani yana tare da sauk'i..."

"Sannan ka cigaba da hak'uri Allah ya na tare da masu hak'uri,,, duniya matabbata ba ce wata rana sai labari ""."

"""zan kasance mai d'aukar shawararka Adamu,,, nagode sosai da nuna kulawarka gare ni,,, Allah ya bar"

"zumunci "".Cewar Aliyu..."

"""Amin ya abokina "".Fad'ar Adamu...."

"Adamu ya cigaba da kwantar ma Aliyu da hankali,,,, tare da k'ara bashi shawarwari na k'warai.. Da kuma"

nuna masa muhimmanci hak'uri da kawaici akan dukkan abinda Saude zata yi masa a zamantakewar rayuwar su na aure...

**********************

"Acan gidansu Amina kuma,,, Mamansu ce zaune tana gyare -gyaren kayan miya,,, Hadiza tana kusa gare"

ta tana tayata......

"Suna firar su cike da kwanciyar hankali da jin d'adi,,, can fira ta yi bala'in dad'i.. Hadiza bata san lokacin"

"da ta kwashe labarin fad'ansu da Saude ba ta gaya ma Mamansu,,, batasan tayi sub'utar baki ba sai da ta"

gama ba Mama labarin komai.. Sannan ta hankalta da katob'arar da tayi na sakin magana batare da sanin bakinta ya furta ba......

"Mama ta dube ta, tace ""Oh ni d'iyar mutum biyu jikar mutum hud'u,,, yanzu Hadiza sai da kika biyewa"

Saude kukayi fad'a ko a cikin gidan mutane.. Allah ubangiji ya k'ara shiryaki Hadiza bakyajin magana

"wallahi,,, sai da na ce miki kada ki kuskura ki kulata amma ina ya shiga ta nan,,,, ya fita ta can saboda kunnen k'ashi gareki "".."

"Hadiza tace ""Amin amin Mama,,, dan Allah kiyi hak'uri da ni wallahi banida laifi zuciyata bazata iya"

"daurewa ba,,,, wata shegiya tana zagin iyayenah kuma koda naje ba ni na fara yi mata bak'ar magana ba,,, ita ce silar fara zagina batare da nayi mata komi ba.. Shin ni miye laifina? Ko saboda Anti Amina tana k'yale ta shiyasa iskancinta ya ke k'ara yawaita,,, hak'uri yana da k'yau amma idan yayi yawa yana ja"

"maka raini da walak'anci sosai a wurin mutane Mama,,,, banida laifi ita ce bata zama ga kanta "".."

"Mama tace ""ni dai na gaya maki Hadiza,,, ki dinga hak'uri tare da kai zuciyarki nesa,,, kada wata rana kizo"

"kiyi abinda zaki dinga da na sani.. Ban jaki da wani dogon surutu ba ""..."

"""Insha Allah Mama zan dinga kwatantawa ai,, kuma ba zanyi abinda zamuyi da na sani ba,,,, 'yar uwa ta"

"na ke k'watarwa 'yanci ba komai ba "".Cewar Hadiza...."

"Mama tace ""Allah ya sa adai k'ara hak'uri da juriya ,,,akan lamarin duniya da kuma mutane.. Domin"

"kinsan mutanen duniya sai a hankali,,, kuma naman jiki yake iri d'aya zuciya tasha banbanci,,,, wasu da yawa daga cikin mutane basuda imani ""......."

"""haka ne Mama insha Allah zan kiyaye,,,, Allah ubangiji ya sa mu dace baki d'ayanmu "".Cewar Hadiza...."

"Mama tace ""Amin "".... ."

"Hadiza da Mama suka cigaba da firarsu,,,, tare da shawarwari da nasihohi ga 'yarta. Akan zamantakewar"

rayuwa ta yau da kullum...

*********************

"Abu kuma bayan ya dawo daga rakiyar Iya Delu,,, ta bugo k'ofa da k'arfi ba sallama balai salati...Ya shigo"

"yana tafiya guda-guda yana doro,,,, kamar gidan uban shi..."

"Amina ta gefe tana wanke -wankenta,, ita ko kallo bai ishe ta ba."

"Ya dubi Amina yace ""ke bakijin ina ta sallama,,, ko amsawa bakiyi don kina shegiyar mata kuma"

"munafuka "".."

"Amina ko tanka masa bata yi ba,,, balai ya samu damar k'ara ci mata mutunci,,, ta k'yale shi ta cigaba da"

aikinta.

"Abu ya hasala akan k'yalesa da tayi,, yace ""keee zanci ubanki fa,,, wai miyasa ina magana kina k'yale ni"

"don kutumar uwarki. Yau naga tsinannar mata la'ananna,,, wadda tayi gadon mugun hal........."

"Kafin ya k'arasa maganar,, Saude ta chafke maganar da cewa ""bar shegiya d'iyar banza,,, mara zuciya"

"kullum nayi zagi nayi jan maganar. Amma bata tankawa saboda kada inci ubanta tare da yakutartar gyatumarta... Idan ba tsoro ba ki tanka wallahi da sai munyi miki bugun kawo wuk'a,,,,, mun barki"

kwance rai a hannun Allah..

"""fad'a mata dai Inna Saude,,, ko ni nan kad'ai na isheki.. In baki mugun matsiyacin kashi in daki banza"

"kuma jakar mata "".Cewar Abu.."

"Saude tace ""ai ko da ka birgeni Abu,,, koda yake matsalar matsoraciya ce wallahi ai ni ta bani kunya ""..."

"""Nima haka Inna ta matuk'ar bani kunya"".Cewar Abu cike da shed'anci da rashin kunya..."

"Saude tace ""Ai shi ne k'yale banza mai banzar rayuwa,,,, zo muje d'aki."

"Abu yace ""to"".Suka yi shigewar d'aki suna zagin Amina tare da d'aukar alk'awarin ganin bayanta.."

"Amina tana wanke -wanke,, bata ce musu komai ba. Hawayen bak'in ciki ne ke kwaranya daga idanunta,,,"

saboda bata tab'a zaton zata tsinci kanta a cikin wannan rayuwar ba mai cike da k'unci da tarin damuwa da rashin kwanciyar hankali...

"Bata d'auka masifar Saude ya kai haka ba,,, da me zanji da shi a rayuwata ni Aminatu,,, da masifar Saude"

"ko da ta dangin Saude.. Hak'ik'a tasan bata yi dace da abokiyar zama ta k'warai ba.Tayi nadamar har ta kasance matar Aliyu ta farko domin ta san duk ta sanadin shi ne ta ke had'uwa da masifar Saude da bala'inta,,, ya zata yi ne? Ji ta ke kamar tayi kuwwah ko zata ji sanyi a cikin zuciyarta.. Saude ta zamo mata k'adangare bakin tulu babu yadda zata iya da ita. _(sau da yawa mu mata, muna had'uwa da jarabawar rayuwa akan kishiya.. Wata idan tazo burinta shi ne ta k'untata miki da ke da yaranki,,, wata ma zata yi sanadin da mijin zai tsane ki a rayuwarsa,, wata kuma da k'arfi da yaji zata fidda ke daga cikin yaranki ta kuma rabaki mijinki uban 'ya'yanki. Haba mata muji tsoron Allah Mu tuna zamu mutu za'a binne mu daga mu sai halinmu,,,, a cikin kabari duk abinda mukayi zamu taras da shi a cikin kabarinmu,,, sannan Allah baya yafe maka cutar da ke tsakaninka da wani. Ma'ana idan ka cutar da wani dan Allah mata mu gyara zamantakewarmu tsakaninmu da kishiyoyinmu,,,,kishi ba hauka ba ne sannan ba jahilci"

ba ne. Allah ya bamu ikon gyarawa ))))_

_*luv you my fans*_&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 141-145

Haka dai Amina ta cigaba da wanke -wankenta cike da k'unci da tarin damuwa tre da tunanin rayuwarta

"ta baya,,,, mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali. Acan baya bata tab'a zaton zata kasance cikin bak'in ciki ba,,, balantana damuwa da matsalar rayuwa."

"Bayan ta kamalla aikinta ne,,, tayi shigewar ta cikin d'akin da saurinta. Saboda gudun masifar Saude da"

tashin hankali irin na ta....

**********************

"****A can gidan Malam Isiyaku kuma,, Inna Harira da Laure muguntarsu da neme -nemen asiri sai k'ara"

"gaba yake. Babu abinda suka saka gaba idan ba neman duniya tare da burika da ke cikin zuk'atansu,, sun mayar da zina abin ado da tink'aho a wurin su,,, basa shakku ko tsoron uban kowa a cikin garin...."

"Wata rana Laure ce da Inna Harira,,, suna magana...."

"Alokacin ne Inna Harira tace mata ""Laure ya fa kamata kije ki k'ara dibo,,, 'yar uwarki saboda tun lokacin"

"da ku ka kaita baki sa ke komawa ba ""..."

"""To Inna so kike kullum ina kan hanyar zuwa Kamba,, ai saboda kada tayi kewa ne aka kai mata Abu.. Ba"

"ita taji tana iyawa ba ,ai aure ne dole ya sanya mata dokar fita .Tana zaman zamanta lafiya ta ce ita aure ta ke so"".Cewar Laure.."

"Inna Harira ta harari Laure,, tace ""ji min 'yar iska idan baki zuwa kada ci kani ,,,,da surutun ki na banza."

"Ko bak'in ciki kike ji ne saboda tayi aure ke bakiyi ba. Daga cewa ya dace ki je ki duba k'anwarki zaki zo,,, kina son b'ata min rai a banza. Dama ke bakisan k'anwa ba ""...Ta fad'a cike da hasala..."

"""A'a Inna Allah ya baki hak'uri,, amma miye na jin bak'in ciki saboda Saude tayi aure,, ganin nayi ta"

"ragewa kanta jin dad'i ne. Saboda kema kin san da cewa idan bada asiri ba,, k'arya Aliyu ya dubeta ya ce yana sonta da aure,,, to miye abin damuwa tunda ko ni naso aure zan iya zuwa wurin boka,, saboda in mallaki muradin raina "".Cewar Laure cike da jin haushin maganar Inna Harira...."

"Inna Harira tace ""komai ya wuce,, kema kiyi hak'uri akan maganar da na fad'a miki yanzu. Rayuwata ce"

"ta b'aci na zata kina mata bak'in ciki ne alhalin ba haka ba ne,,, a zuciyarki nasan kina matuk'ar son 'yar uwarki """

"""Babu komai Inna,,, dama nasan rashin fahimta ne ya kawo haka.. Amma zan samu lokaci inje ganin"

"Saude,,, karki damu Innarmu "".Cewar Laure... ."

"""To babu matsala,, kisa lokaci da wuri dan Allah.. Sannan ku dinga hak'uri da juriya da junanku,,, saboda"

"ina son zumuncinku ya d'ore ko bayan raina "".Inna Harira ta fad'a...."

"Laure tace ""zamu kiyaye Inna,, karki damar da kanki kuma da nasa lokaci zan sanar da ke ""..."

"Inna Harira tace ""babu damuwa,, Allah yayi muku albarka "".."

"""Amin amin "".Cewar Laure...."

"Suka kama firarsu,, cikin jin dad'i da kuma kwanciyar hankali.. Tare da shawara ta yadda zasu ga bayan"

Amina baiwar Allah..

**********************

"Acan kasuwa Malam Isiyaku ne,, zaune tare da d'iyansa Abdullah da Atika suna fira cikin farin ciki da"

nishad'i...

"Kallo d'aya zaka yima Malam Isiyaku,,, za kaga tsantsar farin ciki ya bayyana a fuskarsa..."

"Saboda damuwar da yake ciki ada,, ya rage ta yanzu ya mik'a lamarinshi a wurin Allah mad'aukakin sarki.."

Tare da addu'ar Allah ya kawo k'arshen zaluncin su Inna Harira da d'iyanta....

"Haka dai yake gudanar da rayuwar sa,,, idan yana son ganin d'iyanshi. Tare da cigaba da sana'ar shi cikin"

"kwanciyar hankali,, saboda a yanzu Inna Harira ta daina karb'ar kud'in shi,, tunda akodayaushe kud'i"

"suna shigowa a kowane lokaci,, da na 'yan haya da na saida kayan miya da kuma na yawon karuwancinsu...."

"Shi dai Malam Isiyaku,, babu ruwan shi da harakarsu. Ya kawo ido yasa musu baya ce musu ehh ko a'a,,,"

kullum addu'arshi Allah ya sa su gane gaskiya d'aya ce...

**********************

"Acan gidan Aliyu kuma,, Amina ce bayan ta kamalla girkin gida,,, ta yi shigewarta d'aki domin ta yi"

wanka...

"Tana shiga d'aki,, sai ga Saude tana tafiya sannu-sannu,,, tare da lallab'awa a hankali..."

"Ta b'ude kular abincin Aliyu,, ta zuba maganin da Iya Delu ta kawo mata,,, na cikin gorar yoghurt sannu a"

"hankali ta zuba maganin tare da gaurayashi da miya.. Batare da anyi saurin ganowa ba,,, tana gama zubawa ta mik'e sannu tana waige -waige saboda kada wani ya ganta,,, ta fice ta bar parlorn da"

saurinta...

"Amina kuma,, har ta gama wankanta. Ta samu wuri ta zauna kusa ga dressing mirror tana tsantsara"

"kwalliyarta Mai k'yawon gani,,, bayan ta gama ne,, tasa atamfarta mai k'yau mai ratsin pink colour and orange,,, half gown ce amma tayi masifar yi mata k'yau,,, ta kawo turare ta saka k'amshi kawai ke tashi."

Tana gamawa ta fito palourn ta zauna....

"Bata jima ba sai ga Saude ta fito,,, itama taci kwalliya atamfarta green and yellow,,, ba laifi tayi dama"

amma bata ko kama k'afar Amina ba wurin k'yau....

"Itama ta samu wuri ta zauna,, tana yamutsa fuska tare da wurgawa Amina mugun kallo da harara.."

"Amina ko kulata batayi ba,,, ta cigaba da kallonta..."

"Sun d'an jima a zaune,, babu mai yima d'an uwansa magana.. Ita Amina bata son jidali da fad'a,, ita kuma"

Saude fad'an ta ke so da cin mutunci tare da zage-zage..

"Suna nan zaune saiga Aliyu,,, ya dawo daga kasuwa.. Suka yi masa sannu da zuwa,, sannan Saude ta je ta"

"rungume shi tare da amsa kayan da ke hannunsa saboda yau girkinta ne.. Ta jawo hannunshi ta kai shi ya zauna saman kujera,,, taje ta kawo masa ruwa masu sanyi ya sha...."

"Bayan ya sha ta yi serving d'in su abinci,, suna ci babu mai magana cikinsu sai k'arar chokali...."

"Haka suka kama cin abinci,, har suka kammala... Suna gamawa Aliyu ya mik'e ya shige toilet da sauri"

domin yayi wanka ko zaiji dad'in jikinsa....

"Ya d'an jima sannan ya fito,, ya sanya kaya marasa nauyi. Ya nufi palourn...."

"Yadda ya barsu haka ya iske zaune,,, kowace tayi shiru babu wani fira ko magana....."

"Aliyu ya samu wuri a tsakiyarsu ya zauna,,, sannan ya dube su yace ""Na iskeku lafiya,,, ya hidimomin"

"gida,, ku lafiya kuke duk kunyi shiru babu wani fira? ""...."

"Amina tace""lafiya k'alau mu ke "".."

"""k'arya ta ke ba lafiya ba "".Cewar Saude.."

"Aliyu yace ""to ina jinki,, mi ya faru? ""..."

"Saude cike da makirci da munafurcinta,,, tare da iya shara k'arya. Ta kawo labarin fad'ansu da Hadiza,,"

"duk ta kwashe ta gaya masa k'arya da gaskiya.. Har da cewa wai Amina ce ta sa Hadiza ta mareta har da dukanta sai da tasa aka yi,,,, tare da zagin iyayenta.."

"Hak'ik'a rayuwar Aliyu yayi matuk'ar b'aci, zuciyarsa kuma ta tafasa k'warai,,, ya dubi Amina kallo mai"

cikeda tsananin b'acin rai.......

"Yace ""Amina abinda Saudatu ta fad'a gaskiya ne,, kuma anyi haka? "".."

"Saude tace ""kana zaton zanyi maka k'arya ne,,, da zaka tsaya tambayar ta ""..."

"""keee! Yi min shiru,, bada ke nake magana ba "".Aliyu yace...."

"Amina jikinta a sanyaye,, tace ""anyi haka amma da yawa maganganunta duk k'arya ta ke min. Ta ya za'a"

"yi na sa Hadiza ta daketa kamar jaka ""."

"""Dallah rufamin baki!! Wato idan bana nan abinda kike k'ullawa kenan ko,,, ina miki kallon mai hankali"

"ashe bakida shi.. Idan banda rashin kunya da rainin wayo ita Hadiza,,, daga zuwa taya ki aiki zata bugarmin mata wai harda marinta. To daga yau ta tsaya can gidan ubanta,, kada in sa ke ganinta a gidan nan,, sannan wallahi Amina ki kiyaye zan walak'anta ki fa... Mara mutunci wadda batasan k'addara ba"

""".Cewar Aliyu cike da takaicin Amina...."

"Saude wani irin dad'i ta keji,,, ta had'a su fad'a a tsakanin su har da yi ma Amina gwalo tare da kallon"

banza...

"Amina tace ""Hmmm Aliyu ba sai ka zagi ubanmu ba,,, sannan nasan kana son matarka.. Sannan Hadiza"

"baza ta k'ara zuwa gidanka ba,,, kuma dad'in abin munada gida balai har kayi mana gorin gida.. Wallahi ban tab'a zaton haka kake ba,,, daga kawai matarka ta gaya maka gaskiya da k'arya saika hauni da cin"

"mutunci tare da tozartawa,,, ba komai dama ai d'an Adam butulu ne ya kan manta alkhairi "".."

"Aliyu ya nuna ta da yatsa,,, yace ""k'arya zata yi miki ai Saudatu bata miki k'arya,,, mugun halinki ne ya"

"tashi a kwanakinnan toni bazan d'auka ba.. Sai ki gayamin waye butulu a tsakanin mu ""."

"Amina tace ""kowaye ya san kanshi,,, ba sai na fad'a ba.. Sannan ina son ka sani aure amana ne duk"

"wanda ya ci amanar wani,,,, sai amana ta ci shi kuma wanda ya ci tawa bazan tab'a yafe masa ba "".."

"Aliyu ya zaburo da k'arfi!!Sai wurin Amina yace ""naga alamar kanki yana hayak'i,, uban wa ya ci amanar"

"ki? "".(kunsan abu da aikin mugun sihiri da tsafi)..."

"""Kai dai ka sani "".Cewar Amina..."

"Aliyu zuciyarsa tana azalzalarsa ,,, idanunshi sun rufe.. Bai tsaya b'ata lokaci ba ya fisgo Amina da k'arfin"

"gaske!! Ya kasheta da mugun marirrirka guda hud'u masu bala'in birkita k'wak'walwar d'an Adam,,, asanadiyar haka sai da bakin Amina ya fashe da jini yau tare da jin rad'ad'i mai zafi Ta duk'e k'asa tana"

"hawaye masu masifar ciwo,,, saboda walak'anci irin na d'a namiji yasa k'afa yana shurinta kamar ya"

samu k'wallo.. Tun tana wayyo Allah har yazo muryata ya shak'e ba'a jin maganarta..

"Saude na ganin kamar zaiyi kisa ,,,,sannan ta shiga a tsakanin su tare da cewa""haba mijina farin cikin"

"rayuwata,,, dan Allah ka k'yale ta hakanan ai ta daku sosai. Zo mu je d'akina ""."

"""da ki k'yale ni nayi mata,,, bugun walakanci wlh gobe ko ance tayimin rashin kunya,,, ba zata yi ba.. Ko"

"tasa Hadiza ta buge ki,,, ni zata kawoma iskanci da rashin kunyarsu.. Sai nayi maganinki a cikin gidan nan "".Aliyu ya fad'a cike da zafin rai da haushi.. ."

"Saude tace ""Allah ya yi huci zuciyarka jarumina,, rabuda ita hakanan ai ni na yafe mata ""."

"Ta fad'a tare da jan hannunshi zuwa,,, cikin d'akinta..."

"Amina ta share fuskar ta tsab,,, da tayi yab'e yab'e da hawayenta.. Ta samu ragga ta goge jini tare da"

shafar kumburarren bakinta. Ta rarrafa ta shige cikin d'akinta ta gasa jikinta sosai da bakinta.. Saboda

duk ciwo suke mata sosai saboda kashin da Aliyu ya bata..

"Amina ta yi kukan bak'in ciki,, tare da jama Saude Allah ya isa yafi a k'irga.."

"Ta yi nadama a rayuwarta,, tare da bak'in cikin kasancewar Saude a matsayin kishiyarta,,, matar da bata"

"ganin kowa da kima da daraja,,,matar da batada tausayi da imani. Matar da babu abinda ke gabanta illa neman duniya da d'aukaka,, hak'ik'a Amina taga jarabawar rayuwa da kuma k'uncin rayuwa,,, saboda tun lokacin da Saude ta shigo cikin rayuwar su. Farin ciki, walwala, annashuwa, zaman lafiya da kwanciyar hankali yayi k'aura daga gidansu.. Amina kuka takeyi mai cike da tausayawa rayuwarta,, domin zuciyarta ta riga ta sanar da ita Saude ganin bayanta kawai ta ke son gani.. Wata k'ila idan taga"

gawar ta zata saduda tare yarda makamanta..

"""Oh ni Aminatu!!! Naga ta kaina hak'ik'a ina cikin k'angin rayuwa,,,, da kuma k'addarar muguwar kishiya.."

"Sai yaushe zanyi farin ciki a rayuwata,, sai yaushe zan daina zullumi da fargaba akan kishiya?. Wayyo ni kaina ji nake dama ba'a halicce ni ba,, ji nake dama ban tab'a sanin Yaya Aliyu ba.. Wa zan gaya ma damuwata ko zanji sanyi a cikin zuciya ta,, ya zanyi da k'addarata ko zata iya chanzawa zuwa gaba"

""".Cewar Amina cike da tsananin kuka da tausayin kanta... ."

"Acan cikin d'akin Saude kuma,,, Aliyu da Saude suke soyewarsu.. Cike da jin d'adi da farin cikin su,,,"

Saude ce rungume da shi ga jikinta yayi kane -kane kamar yaro k'arami.. Babu babu abinda suke illa zuba rikitacciyar soyayya tare da nuna k'aunar juna.....

"Can dai Saude tace ""mijina dan Allah kada ka k'ara yi ma Amina,,, mugun duka ko so kake mutane su fara"

"zagina,,, suna cewa na mallake ka"".."

"""kiyi hak'uri Saudatu, bana son b'acin ranki,,, ni kaina basan sanda na daketa ba. Kawai ji nayi kamar ana"

"ingiza ni,,,,

Please Login or Register in order to submit comment