You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bana son d'ibar albarka. Laure ba yayarki bace, ai ba cewa tayi"

"zata hana miki aure ba. Don haka ki kiyaye ni bana son fitina da neman fa'da""."

"Saude ta zumb'ura baki tace ""naji Inna kiyi hak'uri,yaya Laure kema kiyi hak'uri dan Allah ""."

"Laure ta ce ""babu komai ai 'yar k'anwatah dama nasan rashin fahimtane. Yakawo haka ""."

"Inna Harira ta ce ""haka ne Laure, dama akodayaushe akowane hali, ina son ku kasance masu fahimtar"

"juna. Saboda haka ke Saude karki damu zakiyi aure. Kuma zamu san abinyi ,zamu je wurin boka mu fad'a masa buk'atar mu ""."

"Saude ta ce ""to Innarmu na gane kuskurenah ai ""."

"Laure ta ce ""ai ya wuce babu kom..........."

"Bata ida maganar ba, saiga Abu ya katseta ya shigo, yana cewa ""Inna na dawoooooo,,,,, da k'arfi."

"Inna Harira tace masa ""Sannu da zuwa, ya shiga cikin d'aki abincinsa na nan ""."

"Abu ya ce ""to Inna inji akwai nama a cikin abincin, saboda kinsan bana cin abinci sai da nama""."

"Saude ta bushe da dariya tace ""diba ka gani mana ""."

"Laure ta hararesa tace ""kai bama son rashin kunya, in zaka ci kaci. In bazaka ci ba kabarshi ""."

"""yi hak'uri Inna, wasa nake muku "".Cewar Abu, ya shige cikin d'aki."

"""Kai dai ka sani ""Cewar Inna Laure."

**********************

*WA CE CE AISHA*

Aisha 'ya ce ga Malam Aliyu da Amina.

"Asalinsu 'yan garin kamba ne, dake cikin jahar kebbi."

Malam Aliyu sana'ar da yake yi itace saida kayan miya. Ya gaji wannan sana'ar ga mahaifinsa Ayuba da

Innarsa mai suna Indo (Aisha).

"Sun kasance sunada matuk'ar rufin asiri sosai, dai dai gwargwado sunada rufin asirinsu. Abokinsa natun"

"yarinta shi ne Malam Adamu, tare suka tashi, tare suka yi wasa. Komai tare suke yi har girmansu."

"Aurensu da Amina ya samu asali ne , sunyi soyayya har tsawon shekaru har shidda da suka wuce. Kuma"

auren zumunci ne. Aliyu da Amina akayi sai dai da son ransu.

Iyayen Amina mai suna Ibrahim da matarsa mai suna Salamatu.

"Baba Ayuba da Baba Ibrahim uwa d'aya, ubansu d'aya."

"Anyi musu auren soyayya ne, da kuma tsananin k'aunar junansu, akwai fahimta da soyayya mai k'arfi a"

tsakanin su.

"D'aya baiyin abu sai da shawarar d'an uwansa. Gulma da tsegumi da zugi, baya tasiri ga soyayyar"

wad'annan bayin Allah.

"Alokacin da za'a yi aurensu, baba Ayuba yaba Aliyu k'aramin gida dai dai gwargwado. A unguwar illelah,"

da yake uwayensu a bayan sabuwar kasuwa suke.

"Gidan k'arami ne, saidai yana da kyawonsa gwargwado. Three bedrooms ne da parlor d'aya tsakiyansu,"

sai kitchen gefensu. Da toilet d'aya ne.

"Babu laifi gidan yayi kyau, amma k'ofa ce amaimakon ya kasance get ne."

Alokacin da aka yi auren su cikin rufin asiri da wadatar zuci. Kowa yayi farin ciki 'yan uwa da abokan

arziki.

Suma kansu ma'auratan sun kasance cikin tsananin farin ciki da murna marar misaltuwa da jin d'adi sosai.

"Haka aka kawo amarya d'akinta, kowa ya watse ya barta daga ita sai halinta."

"Abokai suka rako ango gidansa, aka yi musu nasiha da addu'o'i kowa ya kama gabansa."

Haka suke gudanar da rayuwar aurensu cike da aminta da juna da tsananin k'aunar juna da yarda.

Babu mai son b'acin ran d'an uwansa. Kowa yana gudun abinda zai b'ata ran d'an uwa ko abinda zai

kawo musu sab'ani a cikin zamantakewar su ta yau da kullum.

Babu mai yin abu ba tare da sanin d'an d'aya daga cikin su ba.

"Duk da zama ya kasance ""zo mu zauna, zo mu sab'a ne ""amma wad'annan ma'auratan akwai shak'uwa"

da kuma yarda a tsakanin su....

Haka dai suke gudanar da rayuwar auren su.....

"_Ku kasance da ni, a kodayaushe............... ._&&&&&&"

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

_K'awayenah kuna cikin fadar zuciyata._

Aisha Muktar

Hafsat Nasir

Uwani Muhammad

Maimuna Usman.

*PAGE* 56-60

"Haka rayuwar gidan su, Amina ya cigaba da tafiya cikeda kwanciyar hankali da zaman lafiya."

"Amina mace ce k'yak'k'yawa,fara ce doguwa mai matsakaicin k'iba, mai idanu farare tas kamar madara,"

"muryarta akwai d'adi idan tana magana. Har da beauty point gare ta guda d'aya, idan tana murmushi a gefen fuskarta."

"Muryarta tanada masifar dad'i ga mai saurarenta, gata da gashi har gadon baya. Bak'i k'irin mai laushi da"

santsi.

"Duk mace ta kai, to amina ta wuce nan. Tana da golden eye masu tsananin fari wanda ya k'ara k'awata"

fuskarta.

Shima dai Aliyu ba baya wurin k'yau ba.

"Dogo ne, shi ma fari amma Amina ta fishi haske, yana da kyawo sosai shi ma."

"Amina ma cece mai ladabi da biyayya, hak'uri da kawaici. Batada rowa ko kad'an ,abin hannunta bai"

"tsone mata ido. Ga kyauta da iya zama da mutane musamman mak'wabta ,da abokan arziki."

"Shiyasa kaf fad'in unguwar Illelah area, ake matuk'ar son Amina saboda k'yakk'yawan halayenta na"

'k'warai.

"Gata da son k'ananan yara sosai, duk mak'wabtan ta na kusa da na nesa. Babu mai fad'in mugun magana"

"akanta, saboda ta iya zama a siyasance da mutane da nuna so da zuciya guda."

*WASHE GARI*

"Da safe k'arfe 10:00am ,bayan Amina ta gama ayyukan ta na safe. Ta sallami Aliyu zuwa wajen sana'ar sa"

ta saida kayan miya.

"Ita ma taci abincinta, bayan ta kamalla duk abinda ta ke yi."

Ta zauna tana kallon hausa fim mai suna k'anena.

"Tana zaunenta, ta maida hankalinta, kacokam ga kallonta. Tana cikin kallon sai taji ana sallama a k'ofar"

parlornta.

"""Salamu alaikum, salamu alaikum, ""Cewar wata mai saida kayan mata."

"Amina ta amsa mata ""Amin wa'alaikis salam ,ko wace ce ki shigo ciki mana ""."

"Inna mai kayan mata, ta shigo daga cikin parlorn, bayan ta shiga ne."

"Amina ta dubeta, duba na sani da mutunci ta ce ""Inna Hure ke ce dama, kike ta sallama. Sai ka ce gidan"

"bak'onki ne ""."

"""ba haka ba ne amine, kinsan matan zamanin nan sai a hankali. Kana kuri kasan macce, da ka shigar"

"mata gida kai tsaye. Ta ci maka mutunci "".Cewar Inna Hure."

"Amina tace ""Haka ne kam gaskiya Inna, duk da ba duka aka taru aka zama d'aya ba. Kuma ni aganina"

"lamarin zaman duniyar nan d'an hak'uri. Idan muka yi hak'uri da mutane, wata rana zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba ""."

"Inna Hure ta yi nazari da tunanin duk maganar da Amina ta fad'a gaskiya ne tace ""haka ne kam hak'ik'a"

"Amina ke yarinya ce amma kina da tunanin manya da hangen nesa. Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki, kuma ya baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba ""."

"Amine ta ce ""Amin Inna, yau wa ne kalan magunguna kika zo da su ne, kin zo da zuma da man -zaitun ne?"

"""."

"Inna Hure ta kai mata, kayan matan gaba gare ta, tace ""gasu nan duba ki gani, wanda kike so. Sai ki"

"d'auka, ga su zuma nan da man zaitun ""."

"Amina ta fara dubawa, kowane tana karanta amfaninsa. Da yake tayi primary har k'arshe, ta iya karatun"

hausa sosai.

"Ta d'auki zuma da man zaitun, da yake bata iya shan kayan mata na bature ko na saisuwa. Ta fi son ta"

had'a da kanta.

"Saboda tafi yadda da ta had'a da kanta (mata ku kiyaye so da yawa ,kowane kayan mata ku ka gani. Sai"

"kun saya saboda ku birge d'a namiji, Ai ba sai kin saya ba, zaki iya sayen kayan had'awa. Ki had'a abinki, saboda wanda zaki siye bakisan ingancinsa)."

"Taba Inna Hure kud'inta, Inna Hure ta amshi kud'in ta."

"""Shikenan abinda kike so, daga ciki ne? "".Cewar Inna Hure."

"Amina ta ce ""Eh shikenan, nake buk'ata Inna Hure ""."

"Inna Hure ta maida sauran kayan da Amina, ta fiddosu cikin robarta. Da ta ke saka kayan mata cikinta."

"Ta ce mata ""to ni zan wuce, acigaba da hak'uri. Domin shi aure d'an hak'uri ne kuma zo mu zauna, xo mu"

"sab'a ne, mai hak'uri ya kan da dutse har ya sha romonsa. Dan Allah Amine ki rik'e mijinki hannu bibbiyu. Kada ki bari shed'an ya samu galaba a kanku, banda yarda da K'awayen banza ko gulma da tsegumin"

"mutane.Kinji 'yar nan, Allah ya yi miki Albarka""."

"Amina ta dubi Inna Hure cike da gamsuwa da nasihunta, tace ""Amin Inna Hure, hak'ik'a kin yi bayanin da"

"ba kowace ma ce ce zata bani shawarar k'warai ba. In ba keba wata mata ce zata nuna mini hanyar shiga Aljanna. Wasu ma sai dai su nuna maka suna k'aunar ka abaki, amma cikin zuciyar su ba haka ba ne."

"Nagode da kulawarki da kuma nuna soyayyar ki gare ni. Allah ubangiji ya sa mu dace baki d'ayanmu""."

"""Amin amin 'yar nan, karki damu ai d'a na kowa ne Amina "".Cewar Inna Hure."

"Amina ta ce ""haka ne Inna, Allah ya baki kasuwa. Yasa ki saisuwa gaba d'ayan kayayyakinki ""."

"Inna Hure tace ""Amin Amina, ni zan wuce wurin sayar da kayanah ""."

"Ta d'auki kayanta, ta aza saman kanta."

"Amine ta ce ""to Inna Allah ya kiyaye hanya ""."

"Ta ce ""Amin""."

Ta sa kai tayi wucewarta wurin saida sana'ar ta.

*******************

"Da maraice k'arfe biyar 5:00pm dai -dai, sai ga ya faka mashin d'insa. Ya dawo daga kasuwa, ya bud'e"

"k'ofar gidan, ya shigo da mashin d'insa daga ciki."

"Ya aje mashin d'in sa, a gefe guda."

"Yayi sallama, Amina ta amsa tayi masa sannu da zuwa. Ta amshi kayan da ke hannunsa."

"Ta kama hannunsa, ta jawo shi har cikin d'aki, ta zaunar da shi zaman kujerun d'akin."

"Bayan ya zauna, ta kawo masa ruwa masu sanyi cikin jug d'in silver mai kyau ta aje gabansa."

"Aliyu ya dubi Amina cike da tsananin k'aunar ta, yasha ruwa ya ce ""Alhmdlilah ""."

"Amina tace ""ya kasuwar farin ciki nah "".ta fad'a cike da shauk'in k'aunar mijinta."

"Aliyu yace mata ""lafiya k'alau aminatu tah, komai yana tafiya dai -dai yadda ya kamata ""."

"Amina tace ""Allah ya k'aro bud'i na alkhairi, da kuma nasara ""."

"Aliyu ya ce ""Amin Aminatu,Allah yayi miki albarka, yadda kike faranta min rai da yimin biyayya. Kema"

"Allah ya faranta miki, ya baki aljanna fiddausi ""."

"Amina ta ce ""Amin ""."

"Ta shige cikin toilet, ta had'a masa ruwan zafi, bayan ta gama had'awa. Ta fito daga makewayin."

"Ta zauna kusa gareshi ,"

"tace masa""ga ruwa can makewayi, ya tashi suje ta taya shi wanka."

"Ya mik'e tsaye ya ce mata ""to aminatutah""."

"Ya shiga toilet, ta bashi tana tayasa wanka, bayan kamar minti goma sha biyar. Suka gama wanka, suka"

fito tare.

"Ta shafa mata mai ajikinsa, ta d'auko masa wasu kaya marasa nauyi. Ta sa mata."

"Bayan ya shirya, ta jawo shi falo ya zauna. Ta kawo abinci mai rai da lafiya da lemun k'walba ta aje"

gabansa.

"Aliyu ya yi bismillah, ya fara cin abincinsa. Cike da natsuwa da kwanciyar hnkali."

"Yana ci, yana gyad'a kansa cike da santi da nishad'i."

"Amina kallon sa kawai take yi, tana murmushi cike da k'aunar mijinta."

"Bayan ya kammala cin abincinsa, yasha ruwan lemo ya na fad'in ""godiya ya tabbata ga Allah ubangiji, da"

"ya bashi ikon cinye abincin yau lafiya k'alau. Allah ya basu na gobe mai yawa da albarka ""."

"Amina ta ce ""Amin farin cikinah ""."

"Aliyu ya dube ta, ya ce ""hak'ik'a godiya ya tabbata ga ubangijin sammai da k'assai, da ya bani ma ce ta"

"gari, ba wayona ko dubara ta ba ce. Amina kin kasance mace ta gari, wadda duk namiji yake burin"

"mallakarta, ga ki da hak'uri, biyayya, mutunci, nasaba, k'yawo da sauran su. Kin mallaki duk wasu"

"abubuwan da za'a yi alfahari da su. Ni dai sai dai na k'ara godema Allah mad'aukakin sarki da ya mallaka min ke a matsayi matata ""."

"Amina ta yi murmushi cike da jin d'adin irin yabon halayenta, da mijinta ya ke."

"Amina ta nisa ta ce ""mijina ni ma ina godiya ga Allah sarkin sarakai, da ya ba ni miji mai tausayi, mai"

"k'aunata, wanda ya ke gudun b'acin raina.Ya ke sanyani cikin farin ciki da murna da walwala. Ka sani ka"

"zamo wani bangare a cikin jinin jikina da zuciya ta. A kullum akodayaushe Ina rok'on Allah ya barmu tare ya k'ara dank'on soyayyarmu ""."

"Aliyu ya dubeta, cike da farin cikin kalamanta."

"Ya ce ""Ameen Aminatutah,ki sani ba wa ce macce a cikin zuciyata. In ba ke ba saboda tsananin k'aunar"

"da na ke miki. Bana son in tuna wata rana mutuwa zata rabamu tare "".Ya fad'a cike da sanyi jiki da soyayyar ta a cikin zuciyar sa."

"Amina ta rungume shi, tana cewa ""karka damu mijina, Insha Allahu zamu zauna tare. Idan ma mutuwar"

"ta zo,Allah yasa mu cika domin kuwa Allah mad'aukakin sarki bai barin wani domin wani a duniya. Ina son ka sani, So d'aya ne kuma kai kad'ai nake yi ma shi ""."

"Aliyu ya k'ara rungume ta, yace mata ""Amin, amin Aminatu, hak'ik'a na gamsu da maganarki duk abinda"

"ki ka fad'a gaskiya ne, Allah k'ara hak'uri da juriyan zama da junanmu ""."

"Amina ta ce ""Amin farin cikin rayuwata ""."

"Haka dai sukai ta fira,cike da farin ciki da k'aunar junansu..... .."

**********************

"A can garin Shiko kuma, bayan su Inna sunje wurin wani shahararren boka mai suna Na muna, Boka Na"

muna shima yai suna wurin yi bokanci.

"Suka kawo bayanin abinda ke tafe da su. Suka fad'a masa, sai da ya kwanta da Inna Harira da ita Sauden,"

"sannan ya basu wani ruwan magani yace ""duk wadda ta gani tana so da ta shafa ruwan maganin an gama. Zaizo har gidansu ya ce sonta."

"Suka amshi maganin, sannan suka bashi kud'in sa, suka wuce gida........."

"Bayan sun iso gidansu, suka iske Laure har ta gama musu abinci (da yake bada ita, suka je wurin bokan"

ba).

"Suka zauna suka ci abincinsu tare, suna fira."

"Laure ta dibi su Inna, sannan tace ""Inna inji an da ce, ya gajiyar hanya ""."

"Inna Harira ta ce ""dacewa kam, an dace samun wadda ta ke so kuma yakeda rufin asiri. Shi kad'ai ya rage,"

"saboda haka Saude kada ku kuskura ki jawo min talakan banza ""."

"Saude tace ""Haba inna,,,, sai kace bakisan halina ba. Ni ina ni Ina talakan banza, ai ni da nida talaka sai"

"kallo sai hangen nesa, yayi gabas, ni kuma nayi yamma. Mi zanyi da talaka kuma ""."

"Laure da Inna Harira, suka lale da juna kaman abokanin juna suna dariya."

"Laure ta dubi Saude, ta ce ""ke yi k'anwatah, shiyasa na ke son ki Saboda 'kwak'walwarki tana ja sosai ""."

"Inna Harira ta ce ""haka ne, ai nasan d'a in dai nawa ne, zaiyi halin azo gani. Nasan baku sha nonon banza,"

"kada ku yarda duk wanda ko wadda ta taku, ku take sa. Rashin mutunci da tozarci, da rashin imani da tausayi gadon gidan mu ne, babu sani babu tausay Babu sabo da tunani ""."

"Laure da Saude suka tab'a da junansu, suna dariyar k'eta da mugunta."

"Su kace a tare ""haka ne Innarmu, muna matuk'ar son ki""."

"""Ni ma haka, ina sonku d'iyanah "".Cewar Inna Harira. _(Na koma gefe, ina mamakin hali irin na Inna"

"Harira, yadda ta kema d'iyanta hud'uba da aikata mummunar d'abi'a, kamar mai karantar da su halayen k'warai. Ko kunya bata ji, hak'ik'a akwai mata da yawa wad'anda ba su jin kunyar aikata abinda, bayada ko da agaban 'ya'yansu ne. Sun marya da bin bokaye da malamai kamar ibadarsu. Allah ubangiji ya tsare"

"mu, ya kuma tsare mana imaninmu. Ameen)._"

**********************

"Acan waje Abu zaune da abokinsa mai suna Lado, zaune suna firar su ta iskanci."

"Suna zuk'ar sigari, ga tabar wiwi aje gefen su."

"Ayayinda Abu ya ce cikeda shek'iyanci da shed'anci ""kaifa babah jiya wallahi kaya har guda ukku, na sha"

"zumarsu fa""."

"Lado yace ""haba abokina, lallai kaja kaya. Amma shegen bisa miyasa baka gayyace ni ba, ka samu dad'i"

"ka k'yale ni ""."

"""ba haka bane babah, kasan idan mutum ya shiga wannan duniyar .Baya tunawa da kowa har sai ya fito"

"daga cikinta "".Cewar Abu yana zuk'ar taba."

"Lado shi ma ya zuk'i tabar, sannan ya ce haka ne kam gsky abokina. Akwai manya -manyan kaya da gano"

"mana. Anjima can zamu je musha shagalinmu ""."

"Abu ya bushe da mahaukaciyar dariya ya ce ""Allah kuwa babah, ka ce anjima akwai jin d'adi da nishad'i"

"ko? ""."

"Lado ya ce ""babban jin dad'in ma, zaka ji ka a sama fah""."

"""Allah kuwa abokina? "".Cewar Abu."

"""Eh mana, karka damu ai. Akwai kaya"".Cewar Lado."

"Suka lale da juna, tare da cigaba da firarsu. Cike da shed'anci da iskancinsu.... . . ...."

"_Akwai fa chakwakiya, ku cigaba da bina a hankali .._&&&&&&"

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"*Kuna cikin raina da zuciyata, Soyayyarku tana yawo a gangar jikina. H. A. S (Ummu basmah)"

"marubuciyar Babban kuskure, da Ummu meenal marubuciyar Laifina ne* . "

*PAGE* 61-65

"Su Abu suka cigaba da firarsu, cike da shek'iyanci da iskancinsu."

"Lado ya dubi Abu ya ce masa ""tashi muje can wurin shak'atawarmu kada mu makara, karuwanmu suna"

"can suna jiranmu ""."

"Abu ya ce ""to naji inji dai suna da yawa, saboda kasan ni mace d'aya bata isa ta, ana samun irin biyu"

"zuwa ukku wad'anda zan kwana da su ""."

"Lado ya bushe da dariya yace ""Kai abokina ka cika mayen mata, to ai ko ni nan bana iya yin haraka da"

"mace d'aya kawai. Sai na samu masu manya -manyan kaya""."

"""Ai mata sune jin dad'in rayuwa abokina, idan babu mata ai babu jin d'adi ko. Allah ya kai damo ga"

"harawa, ko bai ci ba yayi birgima ko,,,,, babah "".Cewar Abu,cike da shed'anci."

"Lado ya ce ""Amin amin abokina, maganarka haka take gaskiya ne""."

"Abu ya dubi Lado, yace"" tashi muje can kada lokaci ya k'ure mana ""."

"Lado ya mik'e tsaye yace ""haka ne kam gaskiya, kada mu makara ""."

"Shima Abu ya mik'e, yace ""wannan gaskiya ne ba bah ""."

"Suna tafiya, suna fira cike da iskanci da rashin tarbiya da rashin kunya......."

**********************

"Acan gidansu Inna Harira kuwa, suna zaune suna fira cikin annashuwa da walwala."

"Laure ta dubeta tace ""wai Inna a cikin kud'in da muke samu, mi zai hana mu samu gida Na k'asa mu siye?,"

"mu saka 'yan haya muna samun inda kud'i ke fito mana. Masu d'an kauri ""."

"Inna Harira ta ce ""haka ne maganarki gaskiya ne, yanzu abinda za'a yi shine zamu yi sana'ar cikin gida irin"

"su maggin miya da sabulun wanki da wanka da sauran su. Sannan zamu sayi gidan ai, ai kusan ko dan tsoronmu da ake agarin nan, dole a saisuwa mana gida dan uban mutum. Saboda sun san kaidin sharrina da makircina, idan wanda bai bini a hankali ba K'arshensa insa boka ya sa masa mugun ciwo ko ya"

"nakasa mutum, dan kutumar ubanmu ""."

"Laure da Saude suka kwashe da dariya ,suka ce ""Allah ya bar mana ke Inna, hak'ik'a ke uwa ce abar koyi"

"gare mu. Saboda wanda duk ya biyo halin ki ya dace ""suka fad'a tare."

"Saude ta k'ara cewa, ""haka ne maganar ki Inna, dole muyi kud'i cikin garin nan. Mukece raini, sai gani da"

"hangen nesa. Amma Inna na so ace kinada kishiya, da ban san yadda zata kasance ba. Da ta ci ubanta a hannunki da mu baki d'ayanmu ""...."

"Laure ta amshe maganar da cewa""tabd'ijam ai wallahi da ko lahira, yafi ta jin d'adin garin nan na Shiko"

"Mutanen gari ma, mun zama musu ciwon ido, balantana wai wata kishiya da bata wuce karan kad'in miya ba "".Laure ta fad'a, tana yamutsa fuskarta."

"Inna Harira tace ""fad'a mata, ke dai Laure ai duk matar da tace zatayi kishi da ni Tamkar ta taro aradu da"

"kanta ne, kuma bari kuji bama ni ba, ko ku ne idan mijinku yace zai muku kishiya koda ace ku kuka isketa, sai ta yabawa aya zak'inta. Kasheta zamu sa ayi sannan kafin akashe ta. Sai tasan kishi da d'iyan Harira"

galma ba alkhairi ba ne.

"Kishi ne za'a yi cike da makirci, munafurci, k'ulle-k'ulle, kissa, sannan ga babbar madogaronnu wato ayi"

"mata mugun Asirin da duk wanda ya ganta. Sai ya tausaya mata, amma banda m Kishi ne da za'a yi shi cike da rashin imani da tausayi wanda za'a iya kiransa da *KISHIN JAHILCiii,,* ""."

"Saude tayi kuwahh, ta ce ""maganarki haka take Inna, babu wadda ta isa tayi da mu. Ko 'yar gidan uban"

"waye a cikin garin nan. Koma a ina ne ""."

"Laure tace ""mi ake da kishiya ko bala'in duniya da masifa, Ai ni nan ko kalmar K bana son a ambata. Idan"

"ba dole ba ne, saboda tsananin tsanar kishiya wallahi ""."

"Saude ta ce ""Ina bayanki yaya Laure, maganarki haka take. Da ayimin kishiya in zauna da ita. Gwara in"

"haukace ina yawo tsirara wallahi kuwa""."

"Inna Harira tace ""ba zama ki hauka ce ba, sai dai kishiyar ta ki ta hauka ce"

"Laure ta ce ""haka ne kam Inna, k'anwatah ki daina yi kanki fatar haukacewa, saboda dukkanmu nan baza"

"mu yi juriya da hak'urin haukawacewarki""."

"""Misali kawai ne, yaya Laure ni ma matuk'ar son ku"".Cewar Saude."

"Inna Harira ta ce ""karku damu d'iyanah, muddin ina raye ba abinda zai same ku""."

"Suka ce ""to Innarmu"", a tare da junansu."

********************

"Acan gidansu Amina, Innarsu ce tace ma ""k'anwar Amina mai suna Hadiza, zata bata sak'o akaima Amina"

"_(fans kuyi hak'uri na manta insa Amina, tana da k'anwa a can baya)_."

"Hadiza tace ""Mamanmu amma kinsan a can zan yini, dama ina son zuwa kece ke hana ni zuwa gidan Anti"

"Amina saboda wai bata dad'e ba ""."

"Maman Amina ta dube ta, tace ""ke Hadiza kinfa ishe ni da surutunki, idan kinje karki wuni can ki kwana"

"can. Babu ruwana kinsan dai halin Babanku, baya son yawan fitar nan. Ba tare da k'wakk'waran dalili ba ""."

"Hadiza ta zumb'ura baki, cike da sakarci da shagwab'a ta ce ""haba mama, kinsan fa yadda na shak'u da"

"Anti Amina. ta ya za'a ce ba zanje wurin ta akai -akai ba, muna ganin junanmu, banida wata 'ya uwa ta jini da ta wuceta. Ta ya alokaci d'aya za'a raba hanta da jini ""."

"Jikin Maman Amina, yayi sanyi ta jawo Hadiza, ta zaunar da ita kusa gare ta."

"Tace mata ""yi hak'uri Auta, babu wanda ya isa ya raba ku, ke da 'yar uwarki fa ce Allah. Sannan Insha"

"Allahu zaki dinga zuwa kina ganin 'yar uwarki akodayaushe, zanyi ma Babanku bayanin komi, kinji ko Hadiza tah"".Ta fad'a cike da lallashi da k'aunar 'yarta."

*Muje Zuwa*

*Muje Zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*K'anne nah abin k'auna ta, kusani ina matuk'ar k'aunar ku*_."

_Sa'ima Isa_

_Nusaiba Musa_

_Aisha Rabi'u_

_Shanwila Rabi'u_



*PAGE* 66-70

"Hadiza ta k'ara marairaice fuskarta, tace ""to Mama Allah yasa da gaske kike ""."

"Maman Amina tayi murmushi mai k'ayartar da fuskarta, Saboda Amina duk ita ta biyo wurin k'yau da"

"kamanni, ita kuma Hadiza babanta ta biyo da kamanni (amma fa ko ita, tana da kyau sosai. Amma ita da babanta bak'ak'e ne. Irin ta ake kira da black beauty. Bak'inta mai d'aukar ido ne)."

"Tace ""Ai Auta bazan miki wasa ba ko""? Tashige cikin d'aki, ta d'auko wasu abubuwa cikin bak'ar leda."

"Taba hadiza takaima Anti Amina, Inji Mamansu sannan taba Hadiza kud'in mashin."

"Sannan Maman Amina ta ce ""Allah ubangiji ya tsare ki, duk inda kuka shiga da ke da Amina, Allah yasa ku"

"fita lafiya. Sannan dan Allah ki rik'e mutuncin kanki, ki lura da kanki saboda duk uwayen k'warai suna gudun abin kunya ga 'ya'yansu ""."

"Jikin Hadiza ya k'ara yin sanyi, ta ce Insha Allah, zan kasance mai bin duk wani umurni da kika bani ,zan"

"kasance mai bin d'aukar nasihun gare ni, matuk'ar bai sab'ama mahallicina. Hak'ik'a muna godiya Allah, da ya bamu iyaye na gari da ni da Anti Amina. Ba zamu daina yi muku addu'a ba, Allah yasaka muku da"

"mafificin alkhairi, ya baku Aljanna fiddausi da mu da ku baki d'ayanmu ""."

"""Amin amin Hadiza, muma muna matuk'ar alfahari da samun d'iya masu bin umurnin mu, biyayya, ladabi"

"da k'yakk'yawan halayenku, Allah yasa ku gama da duniya lafiya "".Cewar Maman Amina."

"Hadiza ta ce ""Amin Mamanmu ,to ni zan wuce ""."

"""Allah ya kiyaye hanya ""Cewar Maman Amina."

"Hadiza ta ce ""Amin Mama ""."

Ta sa kai ta wucewarta.

**********************

"Acan su kuma su Abu, da abokinsa Lado."

"Suka isa gidan da karuwai ke sauka. Bayan sun shiga, suka iske magajiya ta tara 'yan mata manya -manya."

"Akwai farare, akwai bak'ak'e da dogaye da gajeru."

Magajiya tana ganin su Abu tayi musu sannu da zuwa. Ta basu wuri suka zauna.

"Bayan sun zauna ne, suka ce mata "" 'yan mata biyu -biyu, suke son ,"

"su kwana da su. Ya za'a yi ne wai? ""."

"magajiya ta bushe da dariya ta ce ""Ai babu matsala, idan aljinhunku a cike yake da masu gidan rana,"

"wannan ba matsala bane""."

"Abu yace mata ""wannan ba matsala ba ne, karki damu. Ai ni kinsan irin matan da nake son in kwana da"

"su""."

"Magajiya tace ""Wannan ba damuwa ba ne ,ni dai inji dumus a hannunah ""."

"Lado ya dubi magajiya, yace ""karki damu , akwai kud'i in dai kud'i ne matsalarki akwai su, yanzu abinda"

"za'a yi shi ne, Ki kira mana duka matan saimu zab'a ko? "".Yasa hannu cikin aljihunsa ya zaro 'yan naira dubu -dubu guda biyar, ya ba magajiya."

"Magajiya tasa hannu ta karb'a, jiki na rawa saboda kud'i."

"Sannan ta ce ""ko kufa ai haka ake son gani ba ku tsaya, kuna yi min cika bakin banza ba""."

Tasa aka kira mata 'yan mata sun jeru.

"Tace musu ""gasu nan, su diba da kyau. Su d'auki wadda ta yi musu ""."

"Lado yace mata ""to magajiyarmu ""."

"Abu da Lado, suka mik'e suna dubawa. Bayan sun gama dubawa ne, suka nuna wad'anda

Please Login or Register in order to submit comment