You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'akinta kuma ka ro'kami gafarta. Ta yafemin duk abinda nayi mata, saboda ni"

"kad'ai nasan yadda na ke ji a jikina Isiyaku ""."

"Malam Isiyaku ya rungume Innarsa yana lallashinta ,yana cewa ""Haba Inna ki daina fad'in wannan"

"magana, hankalina tashi ya ke. Kuma nasan ba laifinki ba ne, wannan shi ne 'KADDARA TA. Nasan Mariya zata yafe miki Insha Allahu saboda mace ce mai kunya da tausayi gamida hal"

"acci "".Ya juya fuskarsa yana goge hawayensa, saboda kada Inna Hajjo ta gani ta k'ara rikice masa."

"Inna Hajjo ta ce ""ba zaka gane irin rad'ad'in da na ke ji ba, a cikin zuciyata ba. Na musgunawa baiwar"

"Allah bata min komai. Hak'ik'a Mariya ta cika d'iyar halat. Duk abinda nayi mata bai hana ta yimin biyayya ba da ganin girma na ba. Nasan alhakinta ne da yaranta"".Ta sake fashewa da wani sabon kuka."

"""kiyi hak'uri Innata,nima nasan bai kyauta miki ba, agaba na Harira zata saki aiki ko ta zane ki, ba abinda"

"zan iya yi mata. Ko naso na yanke mata hukunci sai in kasa d'aukar mataki akanta da yaranta, ya zanyi ne"

"Inna?. Ki gafarce ni ya Innata "".Cewar Isiyaku, yana hawaye cikin bak'in ciki da rad'ad'in abinda Harira ke musu."

"Inna Hajjo ta nisa cikin jimami da bak'in ciki tace ""ya kai d'ana ka sani, baka sab'a mini ba ko ka sani"

"bak'in ciki. Akodayaushe baka k'etare umurnina, kana faranta min gwargwadon iyawarka tare da yimin"

"biyayya. Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniya, tare da kai da Mariya da yaranku. Nasan wannan yana daga cikin KUNDIN K'ADDARARMU."

"Ka cigaba da hak'uri ayayinda ka wayi gari bani a duniya, Harira kije duniya ce, Allah shi zai mana sakayya"

"zuwa gare ki. Ba zaki gama da duniya lafiya ba Insha Allahu "".Ta fad'a tana tari sosai."

"""Inalillahi wa ina ilaihirraji'un!! Dan Allah Inna kiyi hak'uri, karki tafi ki barni cikin bak'in ciki da k'uncin"

"rayuwa. Zan k'ara kulawa da ke a rayuwata, kina buk'atar ki kusa gare ni Inna, banida mai sona sai ke da Mariya "".Ya fad'a cike da tashin hnkali da damuwa."

"Inna Hajjo kam, bata ma ji abinda yake fad'a ba. Tarin ya sark'eta da yawa har jini ya fara zuba daga cikin"

bakinta.

"Malam yana ganin haka, ya fita waje da gudun tsiya."

"Ya samu motar haya, da shi da driver suka kamo Inna Hajjo rangai -rangai. Aka saka ta cikin motar hayan."

Suka kama hanyar zuwa asibitin da ke cikin garin na Shiko.

"Suna zuwa aka amsheta, lsiyaku ya sallami driver ya wuce. Yana tausayawa rayuwar su Malam Isiyaku,"

saboda shi ma d'an garin ne sun san halin Inna Harira da d'iyanta.

**********************

"Acan gidan kuwa, su Inna Harira sunji salatin da Malam Isiyaku yayi da kukansa."

"Amma da yake babu tausayi, balai halin k'warai ko niyar taimakonsa basuyi ba."

"Sai ma sha'aninsu da suke yi, da fatar Allah ya sa ta mutu kowa ya huta. Bayan sun gama duk aikace -"

aikacen da zasu yi.

"Suka zauna suna cin soyayyen nama, tare da maltina suna fira cike da annashuwa da tsananin farin ciki."

"Bayan sun kintsa cikinsu, babu wadda ta damu da sallah balle salati(da yake 1:40pm tayi)."

"Suka zauna, suna shirin fita zuwa gidan wani boka wanda ya shahara da tsafe -tsafe da bokanci mai suna"

Boka SIDDARU.

"Boka Siddaru, boka ne da ya shara wurin sihiri da tsafi da kashe rayuwar Al'umma."

"Yana nan a cikin k'urgumin daji, wanda ya ke a tsakanin garin Shiko da garin Rijiyar Mai Kabi ."

"Suka samu motar haya, suka kama hanyar zuwa gidan Boka Siddaru."

"Suna zuwa kan bakin hanya, suka ce ya Sauke su ""ya jira su, yanzu nan zasu dawo. Driver ya ce ""to kar su"

"dad'e dan Allah ""."

"Laure ta ja tsaki ""Mtsss karka dame mu, ba kud'in ka zamu biya ka ba""."

"Inna Harira ta ce ""keh Laure bana son d'iban albarka, wuce muje bana son jaraba ""."

"Ta juya ga driver ta ce masa ""yayi hak'uri dan Allah, k'urciya ne ""."

"Driver ya ce ""Babu Inna ai, ni ban rik'eta a zuciyata ba""."

"Suka shige cikin daji, suna tafiya ayayinda Inna Harira ke ma Laure fad'a akan abinda tayi ma driver."

"Tana cewa ""Haba Laure so kike yayi fushi ko? Ya barmu cikin wannan kusurgumin daji, adinga lura inda zakuyi rashin mutunci mana,""."

"Laure ta ce ""Inna ayi hak'uri, bana son shegen fad'an nan naki da jinini "".Ta fad'a tana zumb'ura bakinta."

Saude dai ba binda ta ce.

"Inna Harira ta ce ""yi hak'uri Laure ta, shawara ce ba fad'a ba""."

"Sai Sannan Saude tace ""haka ne kam, ke yaya Larai kiyi hak'uri ko""."

"Larai ta ce ""na yi, ya wuce ai ""."

"""ko ke fa yanzu "".Cewar Inna Harira."

"Babu wanda ya sake cewa komi, daga cikinsu har suka isa wurin wasu dogayen bishiyoyi ,da bukka a"

tsakiyansu.

"Suna xuwa bakin bukkar, wata babbar Hajiya kawai suka iske layi."

"Ta shiga ta dad'e sosai, bayan fitowarta. Suka shiga cikin bukkar."

"Bayan sun shiga ciki duhun -duhun, ko yatsar ka baka gani, saboda masifar duhu."

"""Gafaranku dai, Sarkin bokaye, kai ne mai raba da d'an ta, kai ne duhu mai gusar da haske ,kai ne"

"tauraruwa mai wutsiya ganinka ba alkhairi ba ne"" (haka dai Inna Harira ta cigaba da yi masa kirari)."

"Tana rufe bakinta, sai suka ji wata muguwar tsawa. Wanda a sanadiyyar yita saida haske ya bayyana,"

cikin wata murya mara dad'in saurare.

"""Ku! Ku! Mi ke tafe da ku, sannan anan ba'a ambaton gafara. Da nida gafara munyi hannu riga. Tayi"

"gabas nayi yamma "".Cewar Boka Siddaru muryasa biyu -biyu cikeda Amo da firgitarwa."

"Ai Laure da Saude, basu san sanda suka saki fitsari cikin wandunansu ba. Uwar tasu kuma firgita kawai"

tayi.

"""Kayi hak'uri ya boka d'an boka, jikan boka "".Cewar Harira, cike da tsananin tsoro."

"Yace musu ""yayi su zauna ""."

"Bayan sun zauna ne, ya ce ""yasan abinda ya kawo su, tun kafin su zo, Aljani k'addaru ya sanar da shi."

"Amma su fad'a da kansu domin wak'a abakin mai ita yafi dad'i""."

"Suka kawo bayanin komi, suka gaya masa."

"Boka ya dube su, ya tsintsire da wata irin mahaukaciyar dariya. Sai da ya dad'e yana dariyar."

"Sannan yanuna cikin da ke jikin Laure, ya ce ""wannan cikin da kuke ganinsa, baya zubuwa.Ko sunk'i ko"

"sun so sai an haife shi, kuma namiji ne zata haifa ""."

"Inna Harira ta yi muguwar ajiyar zuciya, zufa na tsattsafo mata jiki tana sharewa ta ce ""yanzu boka, babu"

"wata hanyar da za'a bi ne ""ta fad'a cikin marairaice da tashin hnkali."

"""Babu wata hanyar da za'a bi Harira, taimakon da zan muku guda d'aya shi ne :suyi k'ok'ari su kashe"

"wanda ya yi mata ciki mai suna 'Dan Ladi. Idan suna son kada duk asirin da sukayi wa mutane, ya walwaale kuma duk abinda suka yi ya bayyana ""."

"Inna Harira ta ce"" to babu matsala zasu yi duk abinda ya ce "",ta fad'a cike da tashin hnkali. Suma su"

Laure duk hankalinsu ya tashi sosai.

"Boka ya d'auko wani garin magani da laya ya basu, Sannan ya ce ""wannan garin maganin, zasu"

"b'arbad'awa 'Dan Ladi a cikin ruwa yasha, bayan ya sha duk jikinsa zai mutu. Sai su samu damar kashe shi, ""abu na biyu kuma zasu sabon kabari na jariri, wanda bai dad'e da rasuwa ba. Sai su saka layar a"

"cikin kabarinsa ""."

Inna Harira ta karb'i maganin da layar ta bashi k'udinsa.

"Ta ce ""godiya muke boka ""."

"""Ba'a godiya anan, ku tashi! Ku tafiiiiii!!!! Buk'atar zata biya "".cikeda da tsawa da hargowa, boka ya"

fad'a. ....

"Basu tsaya, ya gama maganarsa ba. Kowa ya cikama k'afafunsa iska............."

"Sune basu tsaya ba, sai bakin titi wurin driver."

"Suka shige motar, suka yi masa umurni da yaja su da sauri su bar wurin."

"Yaja motar su ka wuce, xuwa gida...."

*BAYAN SATI 'DAYA*

"An sallamo Inna Hajjo tsohuwa daga asibiti, taji sauk'i sosai harda abinci tana ci sosai. Dama ciwon zuciya"

"ne ya kamata, kuma an rubuta musu magani daga asibitin."

Malam Isiyaku ya siyo mata maganin da aka rubuto.

"Tana sha, Alhmdlilah yanzu taji sauk'i da k'arfin jikin na ta."

"Su kuma su Inna Harira, da k'yar su ka samu sabuwar gawar jaririn da aka rufe. Suka saka layar suka rufe."

"Shi kuma 'Dan Ladi, Laure ta yi masa wayo ta kira sa, tayi masa da huwa har da nama. Ta kawo masa"

ruwan maganin da boka ya basu.

"Haka suka zauna da 'Dan Ladi suna fira tana yaudararsa tana cewa ""yau anan zaka kwana mai sona?""."

"""Duk abinda ki ka ce masoyiyata haka zanyi "".Cewar 'Dan Ladi."

"Laure ta ce ""to ""tare da rungume shi tana masa wayo, har ya cinye abincinsa da maganinsa bai sani ba."

Nan da nan ya b'ingire da barcin wahala na Asiri.

"Laure na ganin yayi barci, taje ta fad'ama Inna Harira. Cewa har yayi barci."

"Suka yanke shawarar cewa, ""su bari har anjima zuwa k'arfe 11:00pm na dare. Idan k'afa ta d'auke,"

alokacin suna sa ran kowa yayi barci. Inna Harira ta kira k'artin 'yan daban na su.

"Ta ce musu ""su zo da sha d'aya na dare su kashe 'Dan ladi."

"Su ka ce mata ""to angama ranki ya dad'e""."

"Duk abinda suke fad'a, a kunnen Inna Hajjo. Tana lab'e tana jin su. Tana mamakin su Inna Harira akan"

mugun halin su da rashin imani.

*******************

"Alokacin da dare yayi sosai, k'arfe sha d'ayan dare yayi."

"'Kartin 'yan daban suka shigo, cikin d'akin da 'Dan Ladi yake sai inda yake kwance."

"Inna Hajjo tana jin motsin su, ta shigo tana lab'ab'e, tana bin bayansu, har ta shigo basu san tana"

bayansu.

"Suna zuwa basu tsaya, 'bata lokaci ba. Suka da'bama 'Dan ladi wuk'a ga ciki."

"Jini ya kama zuba, yana shure -shuren mutuwa."

"Inna Hajjo na ganin haka tayi kuwah, wani daga cikinsu ya ganta. Ya jawota da k'arfi ya kashe ta da mari,"

mai rai da lafiya.

"Zata yi musu kuwa kuma, su ka rufe mata baki. Su ka kwantar da ita da k'arfi da yaji, suka yi mata yankan"

rago.

"Suka kwashi gawarwakinsu Inna Hajjo, suka je can bayan gari cikin daji. Suka yar suwa gawarwakinsu."

(Ina Inalillahi wa ina ilaihirraji'un!!! Allah ya rabamu da rashin imani da zalunci da rashin tausayi)

"Bayan an wuce da gawarwakinsu, tasa wani ragga (Inna Harira). Tana goge jinin da ya xuba."

"Ta wanke raggan jinin, ta gina rami ta zuba ruwan jinin cikin ramin (mai Zurfi ) .Ta maida k'asan da ramin"

"ta rufe, kamar ba'a yi ba."

"Ta shige d'akinta, ta kwantawarta. Kamar ba'a yi komai ba."

"Bawan Allah, Malam Isiyaku ya na nan.Yana kwana har da minshari."

Bai san abinda ke faruwa ba..............

*Muje Zuwa*&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_*Ku sani kuna cikin zuciyar Mugirat, har abadan da'iman. Ina sonku da gaskiya.*_ "

_Nasiba Muhammad Umar_

_Hussaina Abubakar_

_Maryam Abubakar_

_Hamida Bala_

_Sumayya Surajo_

_Zainab kamba_

_Rumaisa'u Ahmad da sauran su._

*PAGE* 46-50

*WASHE GARI*

"Agarin Shiko, Malam Isiyaku ya tashi da asuba k'arfe 5:20am zuwa Masallaci. Yayi sallar asuba."

"Bayan ya dawo daga Masallacin, ya shiga d'akin Inna Hajjo domin ya gaishe ta da kwana. Ya kuma yaji ya"

jikinta ya kasance.

"Ya shiga cikin d'akin, yana dube -dubensa. Baiga kowa ba."

"Yashiga har cikin makewayi, da k'asan gado baiga alamar Inna Hajjo ba."

"Yafito daga d'akin, yana dubawa lungu da sa'ko na ko'ina a cikin gidan. Bai ga Innarsa ba."

"Yaji zuciyarsa ta buga da k'arfi!!! Kuma gaban sa na fad'uwa, yana jin shakku a cikin zuciyar sa."

"Sai kawai yaji hawaye na kwaranya daga idanunsa, yana addu'a a cikin zuciyar sa(Allah yasa ba wani"

"mugun abin, Harira ta yi ma Innarsa ba. Yasan ba k'aramin Aikinta ba ne )."

Yafito yanufin d'akin Inna Harira zaune suna fira. Cike da jin d'adi .

"Yayi musu sallama, ba wanda ya kula sa. Balle su amsa mashi."

"Yace ""Harira ina son magana da ke, ya kamata su Laure su ba mu waje ko?""."

"Inna Harira tayi masa wulak 'antaccen kallo na rainin wayo ta ce ""Kai Isiyaku ba zan je ko'ina ba, komi"

"zaka ka fad'a a gaban yarana, babu wani sirri da zamuyi da kai. Ka fad'a ina saurarenka ""."

"Malam Isiyaku ya nisa cikin jimami da tashin hnkali ya ce ""ba tashin hnkali ya kawo ni ba, dama Inna ce"

"ban gani ba. Shiyasa na ce bari in tambaye ki, ko kinga fitar ta wani guri ko d'azu da safe ne? ""."

"Inna Harira ta kallesa, kallon sama da 'kasa.Ta ce ""Ayyah Malam, wallahi banga fitar ta ba. Da naji shiru"

"na d'auka tare ku ka fita, ka kaita asibiti domin ak'ara duba lafiyar jikinta "",ta fad'a cike da makirci da munafurcinta."

"Malam Isiyaku yace mata ""yanzu nan na dawo daga Masallaci sallah na shiga d'akinta ban gan ta ba. Shi"

"ne na ce bari nazo na duba in gani ko tana nan ""."

"Inna Harira ta ce ""bata zonan ba, amma kam gaskiya nayi mamaki. To ina taje ne? ""cike da kissa take"

"maganar, kamar abin har cikin zuciyarta, da gaske bata ji dad'i ba."

"""To bari inje na duba cikin gari inbada sanarwa ko"".Cewar Isiyaku."

"Inna Harira ta ce ""Allah ya sa muji alkhairi, yasa aganta lafiya ""."

"Yace ""Amin""ya kama hanyar zuwa cikin gari."

"Bayan wucewarsa, Inna Harira da Laure suna ta dariyar mugunta da mayarda Mlam Isiyaku da Inna"

Harira ta yi shashasha kuma wawan 'k'warai.

"Inna Harira har da cewa ""Malam Isiyaku ya ma raina mata wayo, in banda wawanci da dolancinsa. Ya"

"d'auka shi tana k'aunar sa ne, balantana wata shegiyar tsohuwarsa mai yakutattar fuska da rub'ebb'en baki na cin goro ""."

Laure da Saude suka sake fashewa da dariyar 'keta.

"Saude ta kalli Innartasu, ta ce ""Amma Inna bakida dama wallahi, kin iya salon munafurci da makirci ""."

"Inna Harira ta ce ""kad'an ma ya gani, in dai ni ce.Ya za'a yi na bari ya fahimci mune sanadin mutuwarta""."

"Laure ta ce ""haka ne kam maganarki dutsi ce Inna, amma fa dan Allah abar mgnar kada wani ya jiyo mu."

"Bamu sani ""."

"""Ai andaina maganar ma ko Innarmu?"".Cewar Saude."

"Inna Harira ta dube su ta yi dariya,sannan ta ce ""An daina maganar d'iyanah na kaina. Kuma"

"matsoratahhhhh""."

"""Mun ji ya dai, ai tsoro gsky ne Inna ""Cewar su Laure da Saude."

"Inna ta fashe da dariya, suma suka kama mata dariyar suma su Laure."

"Acan gidansu 'D'an Ladi, shima 'yan uwansa sunyi nemansa lungu -lungu da sa'ko -sa'ko basu gan sa ba."

"Hankalinsu ba 'k'aramin tashi yayi ba, suna nemansa ruwa a jallo. Basu gansa ba. Idan hankalinsu yayi"

dubu ya tashi. 'Yan uwa da abokan arziki sun bazama cikin gari da dazuzzukkan dake cikin garin Shiko.

Suna neman 'D'an Ladi ko'ina kuma cike da tashin hnkali da rashin kwanciyar hnkali. Suna nemansa.

"Malam Isiyaku kuwa, yana fitowa cikin gari ya samu wannan mummunan tashin hankalin."

"Ya samu mutane suna neman 'Dan Ladi, ya tambaye su mi ke faruwa ne wai?. Suka fad'a masa abinda ya"

faru.

"Yace musu ""Allah ya sauwak'a,"" cikin jimami da tashin hnkali. Shi ma ya fad'a musu cewa baiga Innarsa"

ba.

"Mutane suka yanke shawarar za'a neme su tare, tareda cewa Allah ya sa ba sace su aka yi ba."

"Mata da yara kuka kawai suke yi, ko'ina garin Shiko kowa hankalinsa ya tashi. Da jimamin b'acewar"

wad'annan bayin Allah.

"Malam Isiyaku ya shiga cikin su, cike da tausayin Innarsa."

Suka kama hanyar zuwa cikin dazuzzukkan da ke garin.

"Su Inna Harira kuwa, suna cikin gidan su hankalinsu kwance. Cike da natsuwa da sha'aninsu."

"Mutane suka kutsa cikin dazuzzuka, suna nemansu."

"Bayan sun wuce daji mai yawa, sai suka kawo inda aka yarda gawarwakinsu Inna Hajjo."

"Suna isowa wurin, su ka iske gawar sa. Inna Hajjo kanta ya rabu da gangar jikinta."

Ayayinda shi kuma 'Dan Ladi an farke masa cikinsa.

Harda wasu daga cikin kayan cikinsa ana gani.

"Mutanen garin shiko, sunga tashin hnkali wanda basu tab'a gani ba, alokacin da Malam Isiyaku ya ci karo"

da wannan mummunar tashin hankali nan ya zube 'k'asa ya sume.Su ma 'yan uwan 'Dan Ladi wasu daga cikin su mutum ukku duk sun sume.

"Mutane suna ta kuwa da jimami, ayayinda wasu daga cikin mutanen masu sanyi zuciya suna ta kuka ,da"

bak'in cikin wannan mummunan al'amari.

Haka dai aka kwashi gawarwakinsu da su Malam Isiyaku wad'anda suka some zuwa gida.

**************

"Bayan sun isa cikin garin shiko, kowa aka kai gawarsa gidansu cikin 'yan uwansa."

"Wad'anda suka some kuma yayyafa musu ruwa aka yi, duk suka farfad'o daga suman."

"Arana nan garin shiko sunga tashin hnkali da kukan mutane da dama na bak'in cikin, da wannan alhinin"

da ya same su.

"Malam Isiyaku suman sa yakai hud'u, ana yayyafa masa ruwa. Yana farfa'dowa."

"Kusan lokaci guda, aka kai su Makwancinsu. (Allahu Akbar, duniya ba matabbata ce, shiyasa ake son"

"mutum yayi aikin k'warai a rayuwar sa. Ya kasance ya zauna da kowa lafiya, saboda ba mu san ranar mutuwarmu ba ko lokaci. Amma da yawa daga cikinmu basa tunanin zasu bar duniya, komai daren"

dad'ewa. Allah ya kyauta k'arshenmu. Ameen)

"Bayan anyi musu salla, aka binnesu gidan su na gaskiya."

"Mutane da yawa sunyi kuka har sun gaji, musamman mata da 'yan uwan mamatan."

"Malam Isiyaku sai da yayi rashin lafiya sosai, da dogowar jinya (rashin uwa babban rashi ne, a"

rayuwarmu. Hak'ik'a ya bani matuk'ar tausayi ni Mugirat).

"Bayan anyi gaishe -gaishe, da sadakar bakwai. Kowa mutane ya kama gabansa, suka koma bakin aikinsu"

"(to ya zasu yi wanda ya fisu k'aunarsu, ya karb'i ran abinsa )."

"Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, Malam Isiyaku ya koma shiru -shiru, babu magana irin da. Bayan"

"rasuwar Innarsa, Mariya da d'iyanta sunxo yi mata gaisuwa."

Kuma ya fad'a mata wasiyyar da Inna Hajjo ta bashi na neman gafarta.

Alokacin taji wannan magana tasa har da hawayenta. Kuma na nuna masa ta yafe ai ita bata rik'i kowa a

cikin zuciyar ta ba.

"Ya dube ta cike da tsohuwar 'kaunarta da d'iyanta. Da son k'ara kasancewa da ita a karo na biyu, ina"

"babu halin yin haka saboda Harira tafi k'arfinsa (kuma kusan aikin sihiri, har yanzu yana nan. Bai bar jikinsa ba)."

"Inna Mariya taja yaranta, suka wuce gidansu."

"Suka bar Malam Isiyaku cike da k'unci da damuwa, ya fad'a duniyar tunanin rayuwarsa ta baya. Wadda"

"yayi ci ke da farinciki da walwala, alokacin ga Innarsa Hajjo ga masoyiyar matar sa ta hak'ik'a wato Mariya."

*BAYAN WATANNI BIYAR*

"Laure ta tashi da ciwon nak'uda a ranar laraba, da safe k'arfe 9:30am na ranar."

Ta haifi santalelen 'danta mai kamada da ita sak. Babu abinda ya baro ta ga kamanni.

"Inna Harira ta yi mata wankan jego, mai rai da lafiya.Duk wani gata da mai jego zata samu, to Laure ta"

same su kamar d'an sunnah.

"Ranar suna, Rago biyu aka yanke masa, yaro yaci suna Abubakar."

"Anyi taron suna, an watse lafiya, kowa ya kama gabansa."

"Ayayinda su kuma 'yan uwan 'Dan Ladi, sunsa polisawa suna musu binkice a b'oye domin suna zargin duk"

"mutum d'aya ne. Ya kashe 'D'an ladi da Inna Hajjo. Shiyasa ko Malam Isiyaku basu sanar ma ba,"

Saboda sun fahimci baya cikin hayyacinsa.

"Bayan haihuwar Abu da wasu shekaru, yanada shekara takwas ya zama tantirin yaro. Wanda baya iya"

"zama ga kansa, ya buge wannan, ya jefi wannan."

"Ba irin kashin da baya ba, 'diyan mutane a cikin garin Shiko. Amma babu mai iya masa magana saboda"

tsananin tsoron Inna Harira da su Laure.

"A haka yana yaro, yasan ya tare d'iyan mutane mata yana shafar jikinsu. Su kuma yaran saboda tsoransa"

"suke kamar ciwon ajali, babu mai magana ko mai hana sa."

"Ko uwayen yaran, idan suka ji abinda ya ke ma d'iyansu."

"Wasu su hanama d'iyan su, fita ko'ina, wasu kuma basu hanama d'iyan su fita musamman wad'anda"

d'iya matan gare su.

"Abu tun yana wannan shekarun, ya hana d'iyan mutane shak'atawa cikin gari."

"Baya ganin Mutunci kowa, da girma mutane."

"Ga shegen tsokana, da jan magana da zagin mutane."

"Komai tsufanka, Abu yana iya zaginka tas. Ya ci maka mutunci. Ko kuma idan yana jin haushika."

"'Diyarka zai tare ga hanya ya shafe ta, sannan ya bata mugun bala'in kashin tsiya."

"Haka ya k'ara zamo musu, mugun annoba cikin garin, kunsan an ce ""Barewa bata tuma, d'an ta shi koyi"

rairahe. Ko shi ya taho tuma shi kai.

"Mugun hali da zalunci a cikin jinin su Laure ya ke, kuma gado sukayi. Ba daga sama suke zalicinsu ba."

"A haka Abu ya cigaba da matsama, 'd'iyan mutane da su kansu jama'ar garin........"

"_Yanzu labarin ya fara, ku kasance da ni a cikin wannan 'kayataccen labari .._"

*Muje Zuwa*&&&&&&

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

"_Kin kasance wani bangare a cikin jinin jikina, bazan manta da ke ba a rayuwata. Amina Umar Fana"

(AUFANA). Marubuciyar Jawad._

*PAGE* 51-55

Abu ya zama musu muguwar annoba a cikin garin Shiko.

"Inna Harira ko su Laure, babu mai iya kwab'arsa ko nuna masa abinda ya ke yi ba dai-dai ba ne. Sai ma"

'kara jin d'adi da suke Abu ya biyo mugun halinsu.

"Na bak'in zalunci da cin amana, har da kirari suke masa ""wai k'yawon d'a ya gaJi uwarsa, har ya zarceta"

"akan mugun hali da mugunta ""."

"Da yaga babu mai masa fad'a ,sai iskancinsa ya k'ara k'aruwa."

"Su Inna Harira da d'iyanta Laure da Saude, har yanzu basu bar iskanci ba. Sai ma abinda ya k'aru akan da,"

na rashin kunyarsu da iskancinsu.

"Bin bokaye da 'yan bori ya zama cikin jinin jikinsu, saboda yama k'aru fiye da tunanin mai karatu."

"Malam Isiyaku ya na cikin gidan, yana kallon ikon Allah. Kodayake bai faye zama cikin ba, saboda yana"

"yawan tunanin Inna Hajjo da mafarkinta cikin barci Tana cemasa ""yak'ara yawan addu'a da tashi sallar dare da yawan yin azzakar ""."

"Shi kuma idan ya tuna ta, yana kasancewa cikin sanyni jiki da matsananciyar damuwa."

Sai ya fita wurin sana'ar sa ta saida robobi ya kan ji dama- dama idan yana ganin mutane suna fira da

dariya. Yashiga cikin su ayi fira da shi.

"Lokuta da dama, Inna Mariya na turo su Abdullah da Atikah wurin sa a kasuwa saboda su d'ebe masa"

kewa da tunani.

Idan suka zo wurin sa ya kama tarairayarsu kenan da komai ya siya musu a kasuwa. Idan yaga abinda ya

kamata ya siya musu ne.

Idan ya gansu wata irin zazzafar k'aunar su ke taso masa a cikin zuciyar sa.

"Ya zai yi ne? Hak'ik'a yayi nadamar auren Inna Harira a rayuwar sa, shi kan shi yana mamakin yadda duk"

"suke masa abubuwa cikin gidan. Bai iya magana ko ya hana su, sai yaji wani irin bala'in shakkun Inna Harira da masifar tsoron ta."

"Sau da dama, ya zauna shi kad'ai a d'akin sa. Yana hawaye da addu'ar Allah ya kawo masa k'arshen"

zaluncin su Inna Harira da Saude.

"Ya iya? Allah ya riga da k'addaro masa Auren makirar mace kuma hatsabibiya, shed'aniyar mace. Wacce"

"babu abinda ta sama gaba in ba duniya ba, da abinda cikinta."

"Idan har zasu samu kud'i, to su Inna Harira da d'iyanta Kowacce hanya ce suna iya binta domin cikar"

burinsu a rayuwa.

"Babu tunani ko la'akari da zasu bar duniya suje daga su sai halin su. Basa tunanin ba'a xuwa da kud'i,"

"mulki, kyawo, nasaba, talauci, ba'a zuwa da su acikin kabari, da sauran abubuwan duniya wad'anda ke shagaltar da mutane su sab'ama Allah mad'aukakin sarki."

**********************

"Abu ya cigaba da tsagerancinsa, da iskancinsa su Inna Harira na k'ara d'aure masa gindi. Yana abinda ya"

"gadama ko yake son yi, babu wanda ya isa ya yi masa ko kallon banza a cikin kaf garin Shiko."

*BAYAN SHEKARU SHIDDA*

"Alokacin Abu yana shekara goma sha hud'u da haihuwarsa, Saude nada shekara goma sha ta shara da"

haihuwa. Ita kuma Laure tanada ashirin da biyar.

"Alokacin ne, Abu ya fara shiga gidan matan mutane. 'Kwartanci yana taushe matan mutane ko d'iyansu"

yana kauda musu budurcunsu idan budurwa ne.

"Idan kukaga Abu alokacin, ba zaku ce d'an shekara goma sha hud'u ba ne saboda tsawon k'afa, da"

girman jikinsa.

Mutanen garin sun k'ara matuk'ar tsorata da al'amarin Abubakar. Saboda bakada halin aiken 'yarka wani

wuri ba tare da Abu ya tare taba. Yayi mata fyad'e yayi wucewarsa ya barta kwance rai a hannun Allah.

Sai idan wasu mutane hanya ta biyo da su wajen a kawo maka d'iyar kah jina -jina har gida. Abin akwai

takaici da ban haushi da tausayi.

"Shiyasa da yawa daga cikin mutanen garin, suke kai d'iyansu mata garin mak'wabta a jiya irinsu Rijiyar"

"mai kabi, tungar tivi, 'kyangakwai da sauran garuruwan da ke kusa da su."

"Wasu sai dai suyi kuka su share hawayensu, suna cewa Allah ya isar musu akan su Inna Harira da d'iyanta."

"Alokacin ne Sauce tanuna wa Innar su cewa"" ita aure take son yi bata iya zama haka babu aure, saboda"

"ita mace mai ra 'ayin auren """

"Inna Harira ta kalleta tace ""to kinada wani wanda kike so?. Sai mu kaishi wurin boka a asirce shi, ya zama"

"bai son kowa sai ke?""."

"Laure tace ""ki fad'a mana tunda auren kike so, ko wane ne akai wurin boka Siddaru ""."

"""Ban gane aure nake so ba, to yaya Laure na gaji da kowane shegen yana murzata kamar danbu, Ke da"

"bak'ya ra'ayi kiyi zaman gidan "".Cewar Saude cikeda masifa."

"Laure ta hasala tace ""karfa kiyi min rashin kunya Saude, mi nace miki ne? Na ce kada kiyi auren ne da"

"zaki tasomin. Kina son cimin mutunci? """

"""Ba wani cin mutunci, sai gas. cewar Saude."

"Ai Inna Harira, bata bari Saude ta gama ba."

"Ta buga mata tsawah tace ""ke!!! Saude

Please Login or Register in order to submit comment