You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya daina zuwa wurinta,,, sannan ya daina kiranta. Hakanan ta cigaba da b'oye abin acikin ranta,,, da ta ga abin bana k'arewa ba ne dole ta kira Asma'u ta nuna mata. Tana son ganinta yanzu yanzun nan a gidansu,,, Asma'u tace mata ga nan tafe"

yanzun nan. Suka kashe waya a tare....

"Bayan mintuna kad'an saiga Asma'u,, ta shigo har cikin d'aki tare da sallama. Aisha ta amsa mata tare da"

"yi mata sannu da zuwa,, Asma'u ta zauna kusa ga Aisha saman gadon Umman Aisha..."

"Ta dubi Aisha cike da kulawa,, tace ""Aisha lafiya dai kin kayi min wannan kiran gaggawa haka,,,mi yake"

"faruwa ne kuma mi yake damunki? Naga duk jikinki yayi sanyi ""....."

"Aisha ta marairaice kaman zatayi kuka,, tace ""Asma'u kenan Yaya Abbas ne,,,yanzu kwata kwata ya daina"

"zuwa wurina. Sannan ya daina kirana kuma idan na kira shi ko na tura mishi text messages. Baya d'auka kuma baya reply,,, shi ne na kiraki domin in tambaye ki ko lafiya yake sannan ki tanbayeshi dalilin da"

"yasa ya fita batuna. Saboda ni bansan laifin da nayi mishi ba ""..."

"Asma'u ta yi huci mai zafi,, tace ""kiyi hak'uri k'awata kuma lafiyar shi k'alau,, abubuwa ne sukayi masa"

"yawa shiyasa kika ji shiru har yanzu. Amma insha Allah zan yi masa ince kina neman shi kinji ko ""...."

"Aisha tayi ajiyar zuciya mai nuna ta d'an samu natsuwa. Sannan tace ""hak'ik'a naji dad'in kalamanki"

"Asma'u,, wallahi har hankalina yayi mugun tashi amma yanzu ta d'an samu natsuwa. Amma dan Allah kice masa ya kira ni domin in tabbatar da yana lafiya ""..."

"""Wato baki yarda da magana ta ba,,, har sai kin kira shi ko.. Hmm wani abu sai soyayya da k'auna,,, Allah"

"ya bamu namu mu rama "".Cewar Asma'u cike da zolayar Aisha..."

"Aisha ta yi murmushinta mai k'ayartar da fuskarta. Tace ""ba haka ne wallahi na yarda da ke Asma'u,,, na"

"dai matsu ne naji muryarsa mai dad'i a cikin kunnena. Domin mun rabuda waya kwana biyu kin fahimce ni ""..."

"Asma'u ta dubeta cike da tsananin tausayi,,, tace a cikin zuciyar tah sai dai kiyi hak'uri Aisha saboda Inna"

"Saude ta riga ta shiga a tsakanin ku da Yaya Abbas,, hak'ik'a kin ga jarabawar rayuwa Aisha Allah ubangiji ya musanya miki da wanda,,, zai rik'e ki amana ya share miki kukanki. Kada kiyi maraicin rashin uwa Allah ya baki mafi alkhairi miji wanda yafi Yaya Abbas komi da komi. Ina tausaya miki a ranar da zakiji Yaya"

"Abbas ya rabuda ke bazai aure ki ba,,, wata zai aura a ranar nasan sai kinyi abinda yafi kuka ciwo...."

"Aisha ita kuma da taga Asma'u tayi shiru,, bata ce mata komai ba can dai da taga ta dad'e ta tab'eta."

"Sannan tace ""Asma'u lafiya dai,, tunanin mi kike yi kuma? Tun d'azu ina jiranki ki k'yale ni ""..."

"Firgigittt Asma'u ta yi cike da tsananin damuwa. Tace ""Ba komai tunanin nake yi wata rana kin zama"

"Amarya,,, Yaya Abbas ya zama Angonki "".Tace mata cike da zolayar Aisha da wasa...."

"Aisha ta yi murmushi tace ""na kuwa gode da wannan tunani na ki ""..."

"""ko "".Asma'u tace haka suka cigaba da firarsu,,, cike da tsananin shak'uwa da k'aunar juna. Sun dad'e"

"suna fira sannan daga baya Asma'u tace zata gida,, Aisha ta yi mata rakiya har waje tare da ce mata tana gaida su Mama. Asma'u ta wuce zuwa gida ita kuma ta koma gidansu....."

"Tana komawa ta d'auki wayarta,, ta tura mishi tex message kamar haka :Masoyina ina fatar kana cikin"

"k'oshin lafiya,, kwana biyu naji ka shiru ashe ayyuka ne suka yi maka yawa. Allah ubangiji ya baka nasara akan dukkan abinda ka sama gaba,,, ka sani nayi missing d'inka tare da rashin jin zazzak'ar muryarka. Ina"

"kana cikin zuciyata har abada domin kaine farin cikina,,, kuma muradin zuciyata ."

Daga mai k'aunarka. Aisha.

"Ta tura sak'on tare da tunanin aAbbas,,cikin shauk'in so da k'auna. Hak'ik'a so masifa ne kuma guba ne"

"ga wanda Allah ya jarabce shi fad'awa tarkon so,, muddin ya shiga mutum baida natsuwa balle sukuni"

"har sai mutum ya mallaki,,, muradin zuciyarsa. Ya zamuyi haka rayuwar ta ke tafiya cike da abubuwan,,"

al'ajabi da ban mamaki.....

********************

"Bayan Asma'u ta koma gidansu,, ta samu Mamanta ta gaya abinda ke faruwa...."

"Mama tace ""hak'uri kawai zasu yi da juna,, domin Saude mace ce wadda bata da imani da tausayi ko"

"kad'an. Kuma ba zata tab'a barin Abbas ya auri Aisha ba,,, saboda yawan shige -shigenta da neman magani. Ni dai fatana Allah ubangiji ya musanya mata miji nagari mai tausayi "".... ."

"Asma'u tace ""ni ma nasan ita ce ta raba su,, ta yadda na fahimta akan maganarta. Amma ta bani tausayi"

"Mama Allah ya kareta daga shairin Inna Saude,, kada tayi mata irin yadda tayi ma uwarta "".."

"Mama tace ""Amin amin nima shi ne fatana agareta,,domin yarinyar tana bani matuk'ar tausayi wlh. Ai"

"idan tayi dacen mijin k'warai ta dace batada matsala ""....."

"Asma'u tace ""Hakane kam gaskiya Mama,, Allah ya sa mu dace baki d'ayanmu""...."

"""Amin "".Cewar Mama. Ita kam Mama ta shige cikin d'akinta domin ta kwanta,, ta bar Asma'u zaune tana"

tunani da nazari.....

"Can ta jima da zama,, saiga sallamar Abbas ya shigo cikin gidan. Ta amsa mashi tare da yi masa sannu da"

"zuwa,,, ta kawo abincinsa da ruwa masu sanyi ta aje masa. Ya zauna ya ci abinci tare da shan ruwan sanyi,, bayan ya gama ne ya shiga wanka domin yaji dad'in jikinsa. Yana fitowa ya sanya jallabiya bak'a mai k'yau,, ya dawo wurin Asma'u da ta ke zaune tun d'azu,, ya zauna nesa kad'an da ita.."

"Sannan yace ""lafiya dai 'yar k'anwatah? Naga kamar bakinki da magana ""."

"Asma'u tace ""lafiya k'alau ba lafiya ba "".."

"""Gayamin mike faruwa ?"".Cewar Abbas..."

"Asma'u tace ""akan maganar Aisha ne Yaya,, tana cikin tsananin damuwa akan rashin ganinka da rashin"

"d'aukar wayarta. Bansan abinda ke faruwa ba ni kaina na kasa sanar mata cewa ka jaye,,, ba zaka aureta ba ""..."

"""Wato Asma'u maganar gaskiya,, ni kaina bansan abinda ke damuna ba.Kwata kwata naji kamar an ba ni"

"ba an ciremin sonta a cikin zuciya ta,, an sanyamin mugun tsanarta a cikin zuciya ta. To ya zanyi ya zama dole in rabu da ita domin kada inci amanar marainiyar Allah,,, ko in zaluncenta saboda kada Allah ya"

"kamani a gobe k'iyama "".Cewar Abbas cike da sanyin jiki...."

"Asma'u tace ""to ya zakuyi in banda hak'uri,, hak'ik'a wannan duk yana cikin kundin k'addararku. Kuma da"

"sharri da k'ulle-k'ullen Inna Saude ne ko shakka bana yi ""....."

"Yace ""Ta je tayi ta yi indai duniya ce,, dama ta sha gayamin bazan tab'a auren Aisha ba. Saboda bata son"

"taganta cikin farin ciki da walwala. Allah ya bata wanda ya fi ni "".Cewar Abbas.."

"Asma'u tace ""Amin Yaya Abbas hak'ik'a maganar haka ta ke,, duk Inna Saude ce silar komai "".."

"Abbas yace ""Ai duniya ce ta ishi kowa riga da wando ""..."

"Haka suka cigaba da firarsu,,, cike da tsananin zullumi da tausayin rayuwar Aisha....."

"Inna Saude ta kira Aisha daga cikin d'aki,,, bayan ta fito waje ta kama yi mata masifa da bala'i..."

"Alokacin ne Inna Saude,, tace ""'Yar kamaryar buro uba,, mi kike yi acikin d'aki don kutumar ubanki,,,"

"shegiyar yarinya ai ni an barmin annoba cikin duniya ""...."

"Asiya tace ""Ai Inna Aisha ba k'aramar 'yan iska ce ba,,, kullum batada aiki zama cikin maza tare da yin"

"wasa da su "".."

"Inna Saude tace ""Ni ina ruwana duk wanda zata ba jikinta,,, taje ta basuwa babu abinda ya shafeni. Allah"

"ubangiji yasa tayi cikin shege ai ubanta zaiyi kuka da bak'in ciki ba ni ba,,, mu dai iyakarmu dariya da murna ""."

"Asiya ta yi dariyar mugunta,, tace ""wallahi kam ni na matsu ta kwaso cikin shege ""..."

"Aisha tace ""wallahi Inna ban aikata duk abinda Asiya ta ke fad'a ba,,, k'arya da k'azafi ta ke yi min "".."

"Asiya tace ""Dan ubanki ina marinki!! Uban wa yake yi miki k'arya shegiya karuwar mai hankad'ama kowa"

"buje ""..."

"Inna Saude tace ""bar shegiya Asiya ce zata miki k'arya,,, tsinannar la'ananna mai bakin uwa.Mai mugun"

"hali dallah tashi!! Kije ga wanki can kiyi mana ""...."

"Tace ""to "".Tare da mik'ewa tana hawayen k'unci da bak'in cikin rayuwa,,, ta nufi wurin tulin wanki wanda"

"idan mutum ya gansa sai yayi mamaki. Saboda tsananin yawansa ga kuma shegen wari da d'oyi da ke fita daga cikin kayan,, haka Aisha ta d'ebo ruwa ta ciccika randuna. Da bokitaiya sannan ta fara wanki cikin damuwa da k'uncin rayuwa..."

"Haka ta cigaba da wanki,, Inna Saude da Asiya banda zaginta da ci mata mutunci,,, babu abinda suke yi"

"sai cin mutunci da tozarci tare da zagin mahaifiyarta Amina da danginta uwarta,,, cike da tsananin rashin tausayi da imani...."

"Ita dai babu abinda ta ke ce musu,,, cigaba da wankinta kawai take yi... ."

_*Allah ubangiji ya rabamu da 'yan tashin hankali da masu kishin jahilci da hauka. *_&&&&&&

KISHIN JAHILCI

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 191-192-193

"Aisha tacigaba da yin wankinta,,, har ta kammala ta shanya su ga igiyar wanki. Bayan ta shanya ta shige"

d'akinta domin tayi wanka.....

********************

"Washe gari da safe misalin k'arfe 10:30am na safe,,, bayan Aisha ta kamalla ayyukanta na safe ya kama"

"ranar asabar ne yau. Tana zaune tana k'walliya sai ga yaron mak'wabta ya shigo,,, yayi sallama Aisha amsa masa tayi masa umurni da ya shigo cikin d'aki,,, ya shigo yace mata ana sallama da ita waje tace masa to. Yaron ya juya yayi wucewarsa zuwa gida,,, bayan Aisha ta kamalla shiryawa cikin atamfarta light blue and white,,, haka ma takalminta fari ne da hijabinta. Tasa turare mara k'amshi sosai,,, ta kama hanyar fita waje domin ganin wanda ya ke kiranta,,tana zuwa waje suka yi ido biyu da Abbas d'inta,, har cikin zuciyar Aisha tayi farin ciki sosai da murnar ganinshi. Suka gaisa da juna tare da yi ma juna ya kwana biyu?,,, bayan sun gama gaisawa ne. Abbas ya dubi Aisha kallo mai cike da tausayi da tsananin"

k'aunar ta da ya ke yi.

"Yace mata ""Aisha ""..."

"Sai da gabanta ya fad'i saboda bai fiye kiran sunanta ba,,, idan ba magana mai matuk'ar muhimmanci"

"zaiyi da ita ba,,, ta dube shi kallo mai cike da tarin soyayyarsa..."

"Tace ""Na'am Yaya Abbas ""..."

"Abbas yace mata cike da tsananin tausayinta da tsantsar soyayyarta ""Ina son ki yafemin da abinda zan"

"gaya miki,, ki fahimceni fahimta ta natsuwa. Kada ki d'auka tun farko banyi niyar aurenki ba,, a'a wallahi har gobe Aisha ina sonki da kuma k'aunar ki banga abin so ba sama da ke k'anwatah. Amma ina son ki sani komai ya faru da bawa muk'addari ne daga Allah kuma tun ranar gini ran zane,,, haka Allah ya k'addara bawa bai isa ya guje ma k'addarar shi ba,, sannan kuma matar mutum kabarinsa,,, ina matuk'ar son kasancewa da ke amma bazan so cutar da zuciyar da yarda da ni ba,,, tare da nuna mini so mai"

"tsabta kuma ""............"

"Aisha ta chafke maganar,, tana hawaye tace ""dakata Yaya Abbas ban fahimci maganarka ba,,, kana son"

"kace mini ba zaka aureni ba yanzu. Dama nasan haka abin zai zama da ban fad'a cikin tarkon sonka ba,,, wayyo Allah! Ni Aisha sai yaushe ne zanji dad'i a rayuwata,, sai yaushe ne zanyi farin ciki kamar kowa kuma na samu 'yancin kaina? Hak'ik'a nasan ba zata tab'a barina inyi farin ciki a rayuwata ba "".Tace tare"

da sake fashewa da kukan bak'in ciki da maraici...

"Yace ""Dan Allah Aisha ki daina kuka,, ba laifina ba ne nima bansan abinda yake damuna ba. Kuma bazan"

"so in aurenki ba in sanya ki cikin bak'in ciki ba,,,,dan Allah kada ki d'aukeni maci amana "".."

"Aisha ta d'ago jajjayen idanunta,, tace ""Wallahi na fahimceka nasan babu cuta balle cutarwa a tsakanin"

"mu,, na yafe maka har abada domin nasan ba laifinka ba ne,, nasan wannan yana daga cikin *kundin k'addararmu*.Kuma nasan ba'a son ranka ba ne,,, Na yarda da wannan abu *k'addara ce* ban isa in"

"gujema *k'addarata* ba. Allah ya zab'a mana mafi alkhairi a rayuwarmu ""..Tace cike da tausayin kansu...."

"Abbas yace ""Nagode sosai Aisha da kika zamo mai fahimtata,, ki sani har abada bazan tab'a mantawa da"

"halaccinki gareni ba. Kuma ina jinki har acikin zuciyata ""....."

"Tace ""karka damu Yaya Abbas bakada laifin komai a wurina,,, ka soni alokacin da kowa ya gujeni kayi min"

"halacci a cikin rayuwata. Kuma bazan tab'a mantuwa da kai ba har abada da'iman,,, nagode sosai da kulawarka da soyayyar ka acan baya gareni "".."

"Yace""karki damu ko babu soyayya ke k'anwatah ce,, kuma duk abinda ya tashi na bikinki zanyi miki"

"abinda Yaya zai iya yima k'anwarshi insha Allah. Karki damu muna tare har abada ba za mu daina zumunci ba ""...."

"Aisha ta yi murmushi kad'an,, tace ""Babu komai Allah ya bamu abokanin zama na gari ""....."

"""Amin amin to ni zan wuce gida "".Cewar Abbas.."

"Aisha tace ""Allah ya kiyaye hanya "".Ya yi wucewarsa da matarshi,,, ita kuma Aisha ta juya zuwa cikin"

"gidansu.. Tana shiga ta iske Inna Saude tana wak'e -wak'enta,, na jin dad'i saboda kuwa d'azu tayi musu lab'e duk abinda suke fad'a tana ji. Tana jin sunyi sallama da juna da sauri ta jiyo cikin gida ta zauna akan kujera k'arama. Aisha tana zuwa kusa ga Inna Saude ta tsaida ita,, ta dubeta cikin tsananin farin ciki da"

murna..

"Tace ""ke miya sami idanunki naga kinyi kuka? Ko wani abu ne ya fad'a miki cikin idanu kinzo kina mana"

"kukan munafurci,,, da azuzanci shegiyar karuwa mai bin maza "".."

"Aisha tace ""babu abinda ke damuna,,, Inna kawai idanuna ne kemin ciwo "".."

"Inna Saude tace ""Hmmm k'arya kike munafukar Allah,,, duk abinda kuke fad'i inaji babu k'aryar da zaki"

"min. Abbas ya rabuda ke saboda ya riga ya sanki 'ya mace,,, ya ma za'a yi ya aureki bayan ya sanki 'ya mace tun a waje. Karyar mata dama abinda kikeyi kenan ko to Allah ya tona asirinki wawuya doluwa,,, yanzu kika fara kuka tunda kin saida mutunci a waje. Ba ke babu farin ciki a rayuwar ki ""..."

"Aisha hawaye kawai ke fita,, daga idanunta tace ""wallahi Allah Inna ban aikata abinda,,, kike zargina da"

"shi ba "". ."

"""Zanci ubanki Allah kika sani bak'ar munafuka,,, ke ada kinji dad'i zaki auri mai kud'i kije ki huta,,, kina cin"

"abinci mai k'yau da gurayen kaji ko. To babu ke babu auren mai kud'i muddin muna tare,,, kinji abinda na gaya maki mai shan miyar kuka da tuwon k'ullu. Shi yafi dacewa da ke ba jar miya "".Cewar Inna Saude..."

"Aisha tace ""Inna ba haka ba n......"

"Kafin ta gama magana,, saiga sallamar Asiya ta fito daga yawon tambad'arta da karuwanci. Tana zuwa ta"

"dubi Inna da Aisha tace ""Inna mi ya faru naga wannan karuwar mata,,, tana kuka har idanunta sun yi ja "".."

"Inna Saude ta bushe da dariya,, tace ""ke Abbas ya rabuda ita bayan ya gama da ita. Shi ne zata zo tana"

"min kuka na munafurci da azuzanci,,, sai kace ni nace ta bashi jikinta har ya yaudareta ""..."

"""Allah nagode maka,,, dama k'arshen alewa k'asa. Ada har kuri takeyi zata auri mai kud'i,,,tasha jar miya"

"shegiya. Dama ga irinta nan Allah ya tona muku asiri,, ashe ya gama da ke shiyasa ya fara aurenki "".Cewar Asiya..."

"Inna Saude tace ""Ya riga ya gama da ita,, saura ciki ya bayyana gare ta. Bayan kin haihu sai mu had'a ki"

"aure da Lado abokin Abu,, ya taimaka ya rufa miki asiri ya aureki.Kuma ko ubanki bai isa ya k'etare umurnina ba ""."

"Asiya ta yi kuwah tace ""sun ko dace da juna Inna,,, wallahi kin iya zab'en miji na gari. In yaso idan sukayi"

"aure ya maidata Shiko can. Taje tana fyad'i da sussukar hatsi saboda haka shi yafi dacewa da ita ""."

"Inna Saude ta yi muguwar dariya tace ""Haka za'a yi idan ta aure shi ko aiki yana iya halakata,,,zansa Abu"

"ya kira shi domin afara maganar aure. Tana gama makaranta sai musha biki lafiya "".."

"Asiya tace ""Hakan ma yayi keeee!!! Dan ubanki tashi kin tsaya kina kallon mutane da shegunan"

"idanunki,,, mazinaciya karuwar gida kawai "".."

"Aisha ta tashi ta yi wucewarta zuwa cikin d'aki,,,, babu abinda tace musu illah hawayen da ke fita daga"

"idanunta,,, cike da k'unci da rad'ad'in rabuwa da Abbas.Rabuwa ta har abada tasan duk abinda ya faru bayada laifi ko kad'an,,,saboda ko farin cikin da Inna Saude da Asiya sukayi yanzu ya nuna mata,,, da sa hannunta a ciki amma ta dangana ta barma Allah komai. Tasan shi zai yaye mata abinda duk yake damunta,,, sannan ya musanya mata da mafi alkhairi. Haka dai tayi wanka domin ta ji sanyi a jikinta,,,"

tana fitowa ta sanya doguwar riga mara nauyi tayi kwanciyarta.....

"Suma su Inna Saude suka kaita firarsu,,, cike da tsananin jin d'adi da murna. Bayan sun gaji da yin fira"

"suka shige cikin d'aki,,, suna cin kayayyakin dad'i da lemuka kala kala wanda samarin Asiya. Suke kawo mata da sauran abubuwan buk'ata na yau da kullum..."

******************

"Acan cikin kasuwa rumfar su Aliyu,,, Adamu ne zaune yake cemasa."

"Adamu yace ""Aliyu ""."

"""Na'am Adamu "".Cewar Aliyu.."

"Adamu yace ""Mi zai hana kayi ma Aisha aure,, idan sun kammala makaranta. Kaga zata rage zafin"

"maraici da musgunawar rayuwar da Saude ke mata,,, saboda na lura kwata kwata Saude bata son tayi farin ciki ko kad'an "".."

"Aliyu yace ""dama ina sonyi maka magana tuntuni,,, amma wani hanzari ba gudu ba mi zai hana idan"

"akwai wanda ya ke sonta tsakani da Allah. Ya fito ayi auren yanzu tana kammala makaranta sai ta tare,,, saboda nasan nayi abubuwa da dama a rayuwata na cin amanar marainiyar Allah "".."

"Adamu yace ""babu matsala hakan ma yayi,,, dama akwai wani Alhalin birni da ya nunamin yana ganinta"

"akodayaushe tana zuwa islamiya. Yace min ko na santa na nuna mishi 'yata ce,,, yace idan babu damuwa yana son nema ma d'anshi aurenta. Na nuna mishi zanyi magana da kai,,, kaga kuwa abin yazo dai-dai "".."

"""To babu damuwa ka gaya mishi azo da sadaki kawai a d'aura aure,,, amma miyasa tun farko baka gaya"

"min ba?"".Cewar Aliyu.."

"Adamu yace ""Na zata ba zaka yarda ba ne,,, kuma Insha Allah zan sanar da shi Alhajin yazo da 'yan"

"uwansa "".."

"Aliyu yace ""hmm to babu damuwa,, Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama alkhairi "".."

"""Amin amin abokina "".Cewar Adamu .."

"Aliyu da Adamu suka kama tattaunawa,,, ta yadda zasu aurar da Aisha bata re da sanin Inna Saude ba,,,"

balle ta k'ulla wani abu..

******************

"Acan d'akinsu Tanko da su Lado,,, sune suke fira cike da shed'anci da rashin kunyarsu..."

"Abu yace musu ""Wallahi ina cikin jin dad'i kullum ina hawa saman network,,, kuma Asiya yanzu ba zata"

"iya rabuwa da ni ba "".."

"Tanko yace ""haba dai abokina kace kana shan gararka,, bakada matsala "".."

"Lado yace ""ina ko yaga matsala kullum yana shan d'adi,,, Allah ya sa k'wallonka ya shiga cikin raga ""."

"Abu ya bushe da dariya,,yace musu ""Amin wlh abokaina ai saina cika burina ko ta halin k'ak'a,, ai zata"

"samu ciki karku damu ai ni nan da kuke gani na banida wasa,,, aiki yanzu cikawa yanzu ""....."

"Tanko yace"" abokina kada ka damu muna bayanka d'ari bisa d'ari ,,,wannan abu ba matsala ba ne ""."

"""Ina yaga matsala ina ta ganshi,, yabi gabas ta bi yamma. Kada ka ragama duk wadda ya shiga gonarka"

""".Cewar Lado...."

"Abu yace ""ai ba k'aramin sona Asiya ta keyi ba,,, saboda yadda nake kashe mata kud'i da kud'in sata zata"

"ci ubanta ai. Saboda ko mijin k'warai mai ya gagareta aure bar makwad'aiciyar shegiya ""..."

"Lado yace ""zata gane duniya budurwar wawa ce "".."

"Tanko yace ""wasu matan basa ganewa,, sai alokacin da ruwa ya k'arema d'an kada. Sannan azo ana"

"nadamar da batada amfani ""..."

"Abu yace ""ai bana son su gane da wuri,,, so nake susan ko gaba da gabanta Aljani ya taka wuta ""..."

"Tanko yace ""takkwallai ne basu da wayo daga uwar har d'iyar,,,ina mamakin wasu sun iya sama d'iyan"

"wasu ido. Amma basu iya sama nasu idanu saboda sunfi zama abin k'warai ""..."

"Abu yace ""har dai Saude ga kuma shegen kwad'ayi kamar karya,,, matar nan wallahi batada imani da"

"mutunci ko kad'an. Ga shige shigen bokaye da yin zinace zinace kamar jaka,,, kullum bata gajiya ni wlh Malam Aliyu har tausayi yake bani. Allah ya had'a shi da aladanyar mata "".."

"Lado yace ""to ya zanyi da jarabawar rayuwa,,, k'addara ce taja masa aurenta da kuma asiri da tsafi. Idan"

"ba haka ba mi zaiyi da ita a matsayin mata"".."

"Tanko yace ""haka ne kam gaskiya,, Saude babu mutunci ko kad'an balantana tausayi "".."

"Abu yace ""zata je tayi tayi ai zata gane shayi ma ruwa ne,,,duniyar nan idan ta juya mata baya ko fak'iri"

"sai ya fita k'yawon gani "".."

"Lado da Tanko suka ce ""haka ne kam gsky "".Tare da fashewa da muguwar dariya shed'anci da"

shek'iyanci...

"Haka suka cigaba da firarsu,, cike da tsananin shak'uwa da shed'ancinsu..."

********************

"Acan garin Shiko kuwa Laure da Ilu mai saida hoda,,, suke soyayya tare tun lokacin da Saude ta yi aure."

"Suka k'ulla alak'ar iskanci da rashin kunyarsu,,, kullum kullum suna tare kamar mata da mijinta. Babu abinda yake rabasu idan ba ciwo ba,, ana nan wata rana Inna Harira ta dubi Laure.."

"Tace ""Wai Laure ke ba zakiyi aure ba,,, kin fison xama haka har k'arshen rayuwarki ba igiyar auren wani"

""".."

"Laure tace ""Haba Inna idan kin gaji da ganina ne,, sai ki gayamin na tattara kayana in shiga duniya ""...."

"""Allah ya baki hak'uri Laure,, dama ai magana ce d'auka bai zama dole ba,,, kuma ai bana son duk ku"

"watse ku barni ni kad'ai na, ,,,saboda kinga Isiyaku ba k'aunarmu ya ke ba ""Cewar Inna Harira.."

"Laure ta bugama Inna Harira tsaki,,, tace ""Kinsan da haka kike neman takura min,,, to ina barinki da shi"

"idan asiri ya warware ya fara ta kanki "".."

"Inna Harira tace ""kiyi hak'uri Laure ban sakewa kinji "".Tace cike da tsoron maganar Laure...."

"""Na hak'ura amma ki sani bana son yawan damuwa,,, da shegen surutun ki na banza da yofi "".Cewar"

Laure..

"Inna Harira tace ""bazanma k'ara ba "".."

"Laure tace ""da dai yafi miki iya gani iya k'yalewa ""...."

"Inna Harira tace ""to"".."

"Sun fara fira ne saiga Ilu mai saida hoda,, ya shigo gidansu babu ko sallama. Ya shigo ya gaida Inna Harira"

"ta amsa mishi,,, ba domin ranta ya so ba,,, Laure ta jashi suka shige har cikin d'aki. Suka bar Inna Harira zaune waje tana mamakinsu....."

"Laure tace ""Iluna sannu da zuwa,, ko kana jin yunwa ne yanzu? ""..."

"""Yauwa masoyiyata, ina jin yunwa amma yunwarki na ke ji "".Cewar Ilu cike da shed'anci."

"Laure tace ""karka damu yanzu kuwa zan kawar maka da yunwarka,,, ka sani farin cikin ka shi ne nawa ""..."

"Ilu yace ""to to masoyiyata Laurena "".Yana dariyar jin d'adi...."

"Laure ta rungume shi,, tare da fara cire mishi kaya itama ta cire nata.. Suna ta abinda suka saba babu ji"

babu gani..

"Inna Harira tana zaune tana zullumi da fargabar da maganar da Laure ta gaya mata,,, yanzu idan Malam"

"Isiyaku ya dawo cikin hayyacinsa dole ya saketa. Kuma yayi mata mugun walak'anci,,,suma mutanen garin Shiko idan sihirin da ke jikinsu ya warware tasan sai sun kusa kasheta da ranta. Inna Harira duk hankalita yayi matuk'ar tashi sosai tace ""k'arya ne bazan tab'a barin asirina ya tonu ba,,, muddin ina raye ko da zanyi yawo tsirara wallahi. Bazan tab'a bari Malam Isiyaku ya dawo cikin hayyacinsa ba balantana suma mutanen garin Shiko,,, nasu sihirin ya warware su tsane ni. Saboda haka ya zama dole in sake komawa wurin boka SIDDARU. Na gaya masa buk'atata domin shi ne mai share hawayena,,, ni Harira"

"Galma! Bansan bak'in ciki ba da rashi ba .Saboda haka bazan tab'a saninsu ba har abada ""...."

"Inna Harira ta kama sambatu da maganganu,,, cike da tsananin tashin hankali......"

"_*Rayuwa kenan duk abinda zakayi,, ka shuka Alkhairi...*_"

*Mugirat ce*&&&&&&

*KISHIN JAHILCI*

&&&&&&

_*Story and written by Mugirat Musa*_

_Editing By~Sis Nerja'art_

*PAGE* 194-195

"Inna Harira ta yanke shawara har acikin zuciyarta,,, zata je wurin boka SIDDARU domin magance"

matsalarta.....

"Haka dai suke gudanar da abubuwan su,, Malam Isiyaku yana gefe babu abinda ya dameshi dasu. Kunsan"

"yanzu shi baida matsalar rayuwa yanzu,,, saboda Abdullah babu ne kawai bai bashi. Kullum yakan je can wurinsa kasuwa ya bashi kud'i masu yawa sosai,,, albarka kawai Malam Isiyaku yake saka mishi da shi da Atika k'anwarshi. Inna Mariya da Inna Ladidi da kuma yayanta Sani,,, basuda wata matsala domin abinci da kud'i kodayaushe ake kawo musu available. Wannan baya k'arewa an kawo wani kuma duk abinda suke so shi suke ci,, babu ne kawai basa ci haka suke tafiyar da rayuwar gidansu cike da tsananin k'aunar"

juna da jin d'adi......

*******************

"Malam Adamu kuwa suna gama magana da Aliyu,,, yana komawa gida ya sanar da mai d'akinshi abinda"

"yake faruwa. Itama tayi murna da farin cikin jin wannan labari ta kuma bashi goyan baya,,, domin ataimaki marainiyar Allah Aisha. Bayan Malam Adamu yayi wanka da cin abinci ya samu natsuwa,,, yasa wayarshi ya kira Alhajin birni ya kawo bayanin komi ya gaya mishi,,, na amincewar uban d'iya .Alhajin birni ya nuna tsananin farin cikinsa,,, tare da yin

Please Login or Register in order to submit comment