You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng https://www.wattpad.com/996128765?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_pu
blish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=UxWDh15pyw%2FzRRiTXr
%2BIGdYXtvNNAH6ZFKV6HA11n8RLhG2lGrhzaYWwZ4KrRM2BZeNoAey
%2FEDIl5f5Y6edjvlTZlXnZZC6B0X96Y0nOs6TSR5eAJMGnH%2BCaFpLflqF5

ZANEN QADDARA TA..!!
_Labarin Aure a Arewacin Najeriya_



Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..

_Ban sani ba ko zaku amfana da darasin cikin labarin, shi yasa na zab'i mu gudu
tare mu tsira tare sadaukarwa ga Masoyana musamman mutanen da suka sayi Ruwa biyu
And😂 zaku yi hakuri dani domin wallahi akwai doguwar tafiya 😂 masu sauri kuma ku
jira na gama amma littafin kyauta ce ga Masoyan ruwa biyu. Suma nasan zasu yi
hakuri da sabiha mai buzu buzu 😂_
Tsalle daya ake...
Babi na D'aya.

Shiru nayi ina sauraron sauraron Nasihar da malamin Tafsiri yake mana, akan
rayuwar aure a lokacin, musamman lokacin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama,
da yadda mata suka mu'amalanci mazajen su.

Kuka nake sosai, musamman da naji yadda Matar da Manzon Allah yace
Julabibi yaje ya nemi aurenta, iyayen ta suka dan so jan jiki akan auren. Hawaye ne
ya zubo min musamman yadda Mahaifina ya rasu da bakin ciki na, ba kome ya janyo
min haka ba, sai yadda Matar da Manzon Allah yace abawa Julabibi, tacewa Iyayen ta.

"Abba na! Manzon Allah ne fa yace Julabibi yazo niman aurena, kuma kuce
ko ba nan ya turo ba, Abba Manzon Allah ne fa ya nima Mishi aure na, me yafi haka
gata, Na Amince zan aure shi."

Wani irin kuka ne ya kwace min lokacin da Malam yake fadar haka, har muryana
na tashi a cikin ajin kowa sai juyawa yake yana kallona, sabida yadda na daura
kaina akan kujeran ina kuka.
"Anum Muhammad Bello! Lafiya kuke kuka?" Malam ya tambaye ni, tashi nayi nace.
"Afuwa malam! Zan iya tafiya gida!"
Murmushi yayi sannan yace.
"Zaki iya tafiya"
Daukar jakata nayi, na fito a hankali ina shashekar kuka, kafin nayi kuka, nayi
hutu na kai sau bakwai. Kafin na isa gidan mu dake bayan makarantar Rariya dake
unguwar bakin kura na cikin garin Bauchi.

Tun daga bakin shagon Maude naga matasan da suke sayar da shayi kofar
gidan mu, suka taso tare da amsar jakata.
"Aunty Anum! Meke damunki ko jikin ne?"

"Babu kome! Kawai hakkin shi da na mahaifina ke bibiyana, na kasa samun
sukuni, Yaushe Maude zai dawo gare ni? Ni ba wai na koma rayuwar shi ba yafiyar shi
da yar shi nake nima!"
"Hmm, sai hakuri dama abinda ake jiyewa kenan, kai zaka kirkiro matslar ka,
sai ka ga kamar Allah ne ya kirkira maka."
Ya fada mata haka tare da rakata cikin gidan.

Sannan ya fita ya hado mata shayi me kauri tare da soyayen kwai. Da bread ya
bawa yara suka kawo mata, kallon abincin tayi kuka na kuma zuwa mata, kyakyawa ce
fara irin jajjanyen nan ce. Gaban goshin ta, kwance yake da gargasa.
Manyan idanunta wanda suka waddaci fuskarta, sai hanci dogo me shegen
kyau, gashin ta da ya kasance ja, saboda yanayin ta zai tabbatar maka da cewa.
Ita din ba cikakkiyar Bahaushiyah bace. Koda tana hade da Hausawar ita ruwa biyu
ce.
D'ago labule aka yi cikin harshen Yaren Igala, tace mata.
"Anum! Meye kike nufi? Zaki zauna ne ina miki aiki baki da abin yi sai zama a daki
ana kawo miki abinda ranki yake so."

"Mama wallahi bani da lafiya, daurewa nake kawai." Cikin jimami irinta
mahaifiyar da take da kaso saba'in cikin dari na laifin da yar autarta ta aikata,
yasata kauda kai tare da cewa..
"Allah ya sawwaka, kuma ko fito daga dakin, domin zama da kike a daki yasa yanzun
duk inda na shiga ake nuna ni da sunan uwar me kanjamau"

A wani irin sauri na d'ago kai me cike da ban tsoro. Jikina yana rawa bakina yana
rawa nace mata.
"Mama! Nice nake da Kanjamau? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, na shiga uku na
lalace. Wayyo Allah na, shi kenan mutuwa zanyi.". Ba fada cikin wani irin
kuka,.jikina yana rawa shi yasa mana duk yan ajin suke gudu na ashe suna min kallon
mutuwa ce.

Wayyo Allah na, na kuma daura hannu akaina, tare da sake kuka ina ihu. Jikina
yana rawa, fitowa Umma tayi ta shigo dakin, ganin yadda nake kuka, tare da matse
kaina cikin matsanancin kuka.
"Anum! Albarkar Ubangiji, me ya faru?" Rike hannunta nayi tare
da rawan jiki nace mata.
"Umma ashe kallon me kanjamau ake min? Umma kowa guduna yake! Umma don Allah ya
zanyi, Umma na cuci kaina, Umma ya zanyi da hakkin Baba Malam, Umma, mutuwa zanyi
wallahi mutuwa zanyi, Umma zuciyata zata buga. Umma!!"
Cak numfashin ta ya tsaya, a rikice Umma ta fito daga dakin tana faÉ—in.
"Maman Aminu! Zoki taimaka min, yarinyar nan ta suma fa!"

Tab'e baki tayi sannan taja tsaki, sannan ta wanke hannunta kasancewar ta
tankaden gari, a hankali suka shirya ta, sannan suka dauke ta tare da kiran Babban
Yaron gidan, Hafiz. Sannan suka leko waje aka kira napep aka dauke Anum. Aka sakata
a napep.
.....
TH-BAUCHI
Emergency aka wuce da ita, zuwa Suka yi aka biya kudin sayan Kati, tare da kudin
ganin likita, bayan sun gama dakyar aka turo wata nurse aka duba ta tare da saka
mata ruwa, sannan aka basu gado.

Maman Anum tana gajiya da zama ta dawo gida tana tsaki, tare da mai da
hankali gurin girkinta. Tare da kananun magana ita ba tsanar Anum bane. Asalima
bata da yar da take so sama da Anum, yaranta bakwai a cikin gidan, Malam Bello.
Amma dukkan su babu wanda yayi mata laifin da Anum mata.

Kwalla ne ya zuba daga cikin idanun ta, tare da Cigaba da aikinta,
hankalinta a rabe yake haka ta gama aikin amma, kuma dan ta bawa masu amfani da
laifin anum akanta haushi yasata had'iye zuwa gareta tana gamawa ta kira Aminu
yazo, ya dauki abincin ya kai musu asibiti,
Ya shigo da yaran shi Na'im da Na'ima, suka shiga mata kiriniya.

"Mama, don Allah ko zaki je ki duba ta, wallahi Anum zuciyarta ya
kumbura sosai," ya faÉ—a a sanyayye,
"Allah ya bata lafiya!"
Ta faÉ—a mishi tare da bashi abincin da zai kai asibiti.
"Mama!"
"Aminu kenan, lokacin da Anum take matsalar aurenta, me kuka ce min? Nice nake
sakata take kashe auren ta, hmm. Nice na saka Anum taki amsar Yarinyar ta,
Ni...Ni ...Ni...Ni...Ni."

Jikin shi ne yayi masifar sanyi, wich mean tana rike da abinda aka mata.
"Mama ki yafe mata mana." Ya faÉ—a muryan shi na rawa,
"Don Allah!"
Ya faÉ—a a sanyayye.
"Ni dama ai na yafe mata."
"Mama muje ki ganta mana"
Mikewa tayi tana fada mishi, cewa.
"Ina son zuwa, Lakwaja fa domin na samu labarin Mawedo ta haihu."

Kallonta yayi tare da sunkuyar da kai,
"Allah ya kai mu."
Ya faÉ—a a raunane, sannan ya dauki kayan abincin ya fitar dashi ya saka a motar,
sannan yazo ya kama yaran shi suka fita tare,

Sai bayan fitar shi, ta zauna tayi kuka, ta kuma tai kuka. Sannan tayi alola
tai sallah isha, bayan ta idar ne, ta daura da shafa'i da wutiri, tana zaune har
lokacin da matar Alhaji suka shigo suna bayan gidan su ne, da yake gidan Babban
gida ne a unguwar. Kuma gashi dama can baya anyi koyarwa na almajirai baya rabuwa
da almajirai.

×××
A asibiti kuwa jikin da sauki domin tayi barci har ta farka, aka kawo mata abinci.

Komawa gefe nayi, ina kallon yan uwana, dukkansu maza biyar, mata bakwai dani
takwas.

"Anum ciki abinci mana, Haba Hauwa'u na, kici ko kadan ne!"
Inji Ya Hafiz, kofin tea na amsa tare da kafa kaina, ina sha ina kallon wata
rayuwar da na sake ya kwace min, cirewa nayi tare da kallonsu.
"Ba zaka ce ya dawo min da yarinya na ba? Ni wall Yarinya na zaku amso min!"
Ina fadar haka tare da kuka, ina ture kome, sai da ka min alluran barci, kallon su
nayi sakamakon barcin da ya lullube ni.

"Wai da gaske ina da kanjamau?"
Daga haka barci ya kwashe ni.

Shiru dakin yayi tare da sunkuyar da kansu, kafin Aunty Hadiza ta d'ago kai
tace.
"Don Allah ina Anum taji wannan labarin? Ina ƙoƙarin kar ya isa kunnen ta amma sai
da ya faÉ—a."

"Hmm! Karku ga laifinta, Maman ku ce ta gaya mata. Tunda taji haka ta gigice baki
daya, amma wallahi babu wanda ya tasa zancen"
Kallon Umma suka yi, tare da cewa.
"Yanzun Mama ce tayi haka da saninta."
Girgiza kai tayi, sannan tace musu.
"Karku ga laifinta, kune kuka aikata haka, kunne kuka tunzura tsakanin su, Anum ba
laifin laifinta Maman ku tare da Malam suka b'ata Anum, shi malam yayi haka ne
kasancewar ta karama da tazo cikin manyan irin ku.

Anum yanzun ta cika shekaru ashirin da hudu, daga shekaru sha bakwai kome ya
tabarbare mata, a ce a karancin shekaru iri ne na Anum, tayi aure biyar ga na shida
akanta.

Ya tafi bai dawo ba, wallahi ban tab'a ganin Zanen kaddarar da yake shate da
ban mamaki, ban tab'a jin ko ganin kaddarorrin masu girma irinta Anum ba, tana
karamar ta tasan damuwa masu yawa. Wallahi na tausaya mata Sosai."

"Amma Umma ki bar tausaya mata, domin abinda Anum tayi yayi yawa, yarinyar da
ta haihu ta juyawa yarta baya, kowacce uwa tana sadaukar da rayuwarta domin yarta,
amma Abun juyawa Yarinyar baya tayi, ki duba girma irin na Maude karfi da jarumta,
bawan Allah nan sai da ya zuba gwiwar shi biyu a kasa yana rokonta, yana kuma rokon
ta amshi yarinyar nan.

Nan limamin masalacin izala yazo har kofar gida yasa aka kira Anum yayi mata
nasiha ya bata yarinyar, tace wallahi ba zata amsa ba. Ya kuma hada ta da limamin
masalacin Sheikh Aminu bakin kura, ya roki Yarinyar nan amma fir taki birninta ta
koma gidan wancan mutumin da bai san darajarta ba."

Haka Ya Abubakar, yayi ta faÉ—a kamar zai dake su,kuma duk haushin Anum ne kawai
da yake cikin shi a rai, yarinya dai shegen taurin kai.
Bata farka ba sai dare, a hankali take bin ko ina da ido, kasancewar tana
jiyo sautin muryan mutane ya sata kuma ware idanunta. Tana jin wasu suna gaisawa
tare da tambayar ya me jikin. Kokarin tashi tayi aka ce mata.
"Koma ki kwanta, sannun Allah ya baki lafiya."
"A'a Umma jikina ciwo yake min na gaji da kwanciyar haka."

"Toh bari na saka miki matashi a bayanki" gyad'a mata kai tayi tare da mik'ewa
dakyar, sannan ta jingina da matashin, ruwa ta kawo mata a cikin buta da yar baho
tayi alola, tare da bata hijab É—inta, dan tasan ko da zata ce taci abinci ba ci
zata yi ba, sai ta gabatar da salollin da yake kanta. Tunda ta fara take zubda
kwalla. Tare da kai kukanta gurin Ubangiji, duk da sallah a zaune take amma sai da
ta sauke tun daga azhar har isha, sannan ta cigaba da addu'a, tana share kwalla.

Shigowar wasu tawagar maza kusan su shida tare da jami'an tsaron yasata tadda
sallah dole, murmushi daya daga cikin su yayi, tare da gaida Umma, tare da
tambayarta ya jikin Anum? Tace mishi.
"Jiki da Sauki Alhaji Ibrahim, matsalar dai da sauki kawai rashin sukunin zuciya ke
damunta"

Shiru yayi sannan yace mata.
"Kuma ya dace yanzun ta fara daukar hakuri da wannan tunanin ba, dan babu wanda ya
isa ya kaucewa kaddarar shi. Hmm idan zata iya tayi min magana sai na tuntube
Abokina Kwamishina Shari'a, zai iya kai al'amarin ta zuwa ga babba Alkalin jaha,
kuma zai raba auren ba tare da wani matsala ba "
Wani irin duka kirjin ta yayi bata san lokacin da ta d'ago kanta tana
kallon shi ba, a yau ta kuma tabbatar babu adalin mutum kamar Maude, mutum ne da
yasan darajar kanshi da kuma mutanen da suke rayuwa da shi.

Sallama tayi tare da kankance Idanunta, sannan tace.
"Nagode da concerns, amma ka sani ko shekara duba zai yi ina anan ina jiran shi
please stay away daga inda nake bana son damuwa kuma bana son ganinka, haka yana
tuna min da bayana don Allah na roke ka, karka kuma zuwa."

Ta yaya ma zata kuma aikata kuskuren baya, a cikin hankalin ta, ai ko na baya
ma, tayi haka ne sabida muradin zuci, tare da rashin sanin darajar kai, amma a
yanzun da tasan ciwon kanta, Maude ya tafi ya barta da ciwon zuciya wallahi bata
jin zata iya daukar kasadar da ta dauka, wannan ma ya ishe ta, wannan ma ya wadatar
da ita, tana niman yafiyar Ubangiji akan wanda tayi Allah ya yafe mata ba zata kuma
kai kanta izuwa ga hallaka ba, tana ji tana gani ta zama abin kyama lokaci guda ana
shirin laka mata sharrin da take niman kashe mata rayuwa, innalillahi wa'inna
ilaihi rajioun.

Anya tayiwa rayuwar ta, adalci kuwa? Anya tayiwa iyayenta adalci kuwa? Yaushe
hakkin mahaifinta zai daina bibiyar ta? Yaushe kukan da yan uwanta suka yi akanta
zai daina bibiyar ta? Ta lalata sunan gidan su. Ta b'ata tarbiyyar gidan su, ta
kuma yiwa yaranta tambarin da har abada ba za a daina kallon su da shi ba, karfi da
yaji ta lalata goben ta. Zaka iya zana abu da pencil ka goge! Amma da zaran ka zana
da biro ba zai tab'a gogewa ba haka Zanen kaddara yake.

Babu wanda ya isa ya goge maka dan kar wani abu ya same ka, Ubangiji da ya
tashi halittar ka sai da ya cika maka kome baka, Arzikinka talaucin ka, kaddarar
ka! Sannan ya diba maka wa'adin ka, yadda matukar ya cika babu sauran jira ko karin
lokaci.

Da ace tun farko ta hango wannan yanayin a lokacin da take ganiyar
kuruciyarta, toh ba makawa da ta sake lalle, da ace yanzun ne abubuwan da ta aikata
zasu faru, da wallahi ba zata kuskura ya bar shi ya faru ba, dukda akwai ratar
ƙaddara!

Ana iya samun damar gyara kusakurai amma ba kowa Allah yake bawa wannan damar
ba, sai wanda yaso kuma wanda yayi niyya!

Me yasa wannan tunanin bai zo mata ba? Me yasa wannan nazarin bai tab'a kawowa
a ranta ba? Me yasa ta biyewa makircin kawaye da da na wasu? Me yasa Mahaifiyarta
ta gaza fahimtar da ita kusakuran da take aikatawa? A yau tayi dana sanin
kasancewar ta kyakyawa me kyau da haiba! A yau tayi danasanin rashin mai da hankali
ta ribanci lokacin ta, tun kafin lokacin ya kure mata? Yau tana ji tana gani amma
duniyar da ta zaba ta juya mata baya!

Mutumin da bata dauka a kome ba, shine yau take niman dacewa ko zata ganshi, me
yasa a lokacin da yazo mata da alkhairi bata fahimci haka ba? Taya aka yi bata
fahimci Alkhairin shi ba, sai yanzun da yayi mata nisan nisa! Yayi tafiyar bazata a
rayuwarta, lokaci guda yayi mata baya ba zani, yan bata aikata abinda zai kaita ya
baro bata ba?

A cikin shekara guda kome ya juye mata, ta rasa mahaifinta me mugun kaunarta.
Share kwallar da suka zubo mata tayi sannan tace mishi.
"Don Allah ka barni da ciwon da yake damuna"



The line of Destiny
#Truelifestory
#ZanenQaddarata
#Mai_Dambuhttps://www.wattpad.com/999953572?
utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_pu
blish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=tEKwF
%2FnkkbMYNxlXlMxQ4wdwG9YtjbXz5x4fnK1eop0i5ygnT%2FlJ0cFATDw61uNJl
%2FJFwi6Ul6b1Sd4Xfda0O2QRVKfR7zXzG%2F7qQ7LgZXo5nS%2FNWhaoiH3VRvMxwLeI
ZANEN QADDARA TA..!!
_Labarin Aure a Arewacin Najeriya_



Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..

Da ciwo a rayuwata!
Babi na Biyu
"Don Allah ka rabu dani, kaje kawai bana son ganinka, nasan da ciwo a rayuwata, ta
yadda duk wanda ya rab'e ni sai na goga mishi me yasa ba zaka fahimce Ni ba?
Me yasa ba zaka tafi ba? Me yasa har yau ake da burin sai ka mallake ni?
Anya ban sadaukar maka, wasu abubuwan masu yawan gaske ba? Indai haka ne toh na
cancanci ka rabu dani, kaje kayi rayuwarka ka barni na ji da ciwon da zuciya take,
don Allah ka tafi kayi nesa dani.

Karka kuma tuna ni,idan da hali kamanta dani, kaje kayi rayuwarka da XOXO tare
da masu kaunarka, ka barni na jira tsammanin zuwan shi. Nasan nayi laifi masu yawa,
amma don Allah ka tafi kabar na cigaba da niman yafiya. Meye amfanin bad'i ba rai.

Me yasa ba zaka gane abinda nake nufi ba, don Allah kaje bana son kara ganinka a
rayuwata, iya haka ma ya ishe ni."

Ta rushe da kuka, sosai wanda duk yadda kake da rashin imani sai zuciyarka ta
girgiza. Duk yadda taso tsayar da kukan yaki Asalima sake samun damar fitowa yake,
zata iya cewa tun rasuwar Malam rabonta. Dan har sai da aka mata alluran barci,
tana barci tana jan shasheka.

Shigowar yan uwanta manyan maza yasa Kwamishina mik'ewa tare da mikawa
Yayunta maza hannu, suka gaisa a mutunci kamar yadda suka saba idan suka haÉ—u.
Kallon juna suka yi tare da cewa.
"Umma ya jikin nata, naji tana shashekar kuka."
"Wallahi zuwa na ya sata kuka, Insha Allah ba zan kuma zuwa ba, amma zan turo
iyalina tare dasu Hishmah da Hisham."

"Allah ya kai mu da rai da lafiya," inji Umma, juyawa yayi ya fita har ya kai
bakin kofar ya juya yana kallon Anum, cikin sanyin jiki, ya girgiza kai ya fita.
Masu kula da lafiyar shi, suna take mishi baya.
"Umma waye ya gaya mishi bata da lafiya?" Inji daya daga cikin yayunta.
"Bashir ban sani ba, kawai ya ganshi yazo ne." Ta bashi amsa a takaice, tsaki yayi
sannan yace mata.
" Sam bana kaunar Bawan Allah nan, amma rabo ya haÉ—a mu dashi, kuma ban kuma jin
haushin dan banza ba, sai da naji ya auri XOXO."
"Allah ya kyauta, bana son daurawa kai damuwa ban da damuwa ina ruwanka da shi,
sirikinka ne tunda ya auri kanwarka sai ka kame kanka indai ba niman karanta kake
ba.

Kaga yadda suke da Aminu haka yayi hakuri da abinda yayi mata, balle kai da
rashin jituwarku da Anum yayi."

Shiru yayi murmushi daya daga cikin su yayi sannan yace mata.
"Umma! Nifa abinda Anum tayi banga laifin ta ba, sabida ita kanta Maman mu taki
zuwa dubata, sannan tana jin zafin Anum ne sabida rashin shayar da Yarinyar nan,
kuma abinda na sani da ace Anum ta amshi yarinyar toh ba makawa ba zata nutsu ta
fahimci girman Soyayyar da Malam yayi mata ba.

Ko jiya ta turo min sako tana kuka tare da cewa, ita tana sane da itace ajalin
Malam, ba kamar yadda ake fada bane, hatsari yayi ba! Wallahi duk sai naji ta bani
tausayi, duk da fushin da nake da ita, sai naga babu amfanin na cigaba da wofantar
da ita. Domin Allah ya gani ba ita bace sanadin malam hatsari ne yayi kuma ya zo
dai-dai da ya fita da b'acin ranta, shi yasa take ganin kamar itace tayi sanadin
shi."
"Eh mganarka haka yake, Usman amma kuma ai laifinta kafewa da tayi akan ba zata
shayarda yarinyar shi ya fusata kowa, sannan Ni da kaina naji ba wani bane ya gaya
min tana faÉ—in wallahi babu rabon shayar da yar matsiyaci a jikinta, dan haka duk
abinda zai yi yayi.

Kuma da na karanci al'amarin sai na fahimci, tana fama da kansa Allah yayi
mata ne, tana tutiya da abinda Allah ya bata ne, da ace Allah bai bata kyau da
tsarin halitta ba, da babu abinda zai saka ta rena Maude."

"Yusuf kenan! Kana wasa da ƙaddara, matukar Allah ya zana maka haka a cikin
ƙaddarar ka babu yadda zaka goce mishi, shi yasa ake fatan kyakyawan kaddarar."
Inji Nura.
Su hudu ne, mazan tunda suka fara su uku na hudun wanda yafi su Shekaru bai ce kome
ba, asalima mik'ewa yayi tare da kallon agogon hannun shi. Ya mike tare da cewa.
"Allah ya kyauta, Ni da wannan mutumin zai ji da ya hakura da zuwa gurinta, sabida
yanayin da take ciki bata bukatar damuwa."
"Yawwa Ya Sadiq nima abinda nake nufi kenan, a barta ta samu nutsuwar zuciya."

Inji Bashir. Haka suka yi tattaunawa har kusan tara na dare, kafin
suka fita daga asibitin dake suna emergency ne, kallon Umman Sadiq yayi sannan yace
mata.
"Zan turo Rulwani da bargon yanzun nan yau ban ga Aminu ba,!"
"Eh shi yayi ta dawainiyya da mu, ya kawo abincin amma bai kuma dawowa
ba, ina ganin halin da Yarinyar take ciki ne yaki dawo dashi."

"Toh ba damuwa, Sai da safe." Yace mata, ta amsa da.
"Allah ya tashe mu lafiya"

A hankali ya fito, daga cikin yaba kallon yan uwan shi da suke jiran shi, yana
zuwa ya bude motar ya shiga, dukkansu suka shiga ababen yawan su, suka bar asibitin
koyarwa na jami'ar Abubakar tafawa balewa.

Bayan minti goma sha biyar, can sai ga wani matashin Amma ba yaro bane
domin ya kai irin talatin da daya ko da biyu. Cikin b'ata rai ya gaida Umma sannan
ya kalli inda Anum take kwance yacewa Umma.
" Ba dai abinda nake ji a gari bane yake damun ta?"
Wani banzan kallo Umma tayi mishi sannan ta cigaba da abinda take.
"Umma ina magana kin ki kula ni?"
"Wallahi ka fita idanu na, kafin na fitar da kai da karfin tsiya, mara kunya kawai,
idan shi yake damunta kai sai ka shirya zama da masu lafiyar, Rulwani bana son
abinda ake fa? Bana son damuwa fa"

"Toh Umma Allah ya huci zuciyar ki!" Daga haka ya ajiye barguna biyun ya koma gefe,
yana kallonta, mik'ewa tayi ta dauki daya ta lullubeta da shi, sannan ta koma gefen
tana cigaba da cin abincin ta.
"Umma!"
"Ina jinka"
"Umma!"
"Kunne ke ji!"
"Hmm! Dama nace zaku jima ne a asibitin?"
"Anan zamu tabbata!"
"Kai Umma kome nayi sai ki zafaffa, kawai tambaya nayi fa!"
"Idan banji duka ba, ba zan daina zafaffawa ba!"
Shiru yayi tare da cewa.
"Toh shi kenan, tunda Anum ba zata yi laifi ba,.kowa kaiwa Anum magana, sai a
shiga jin haushika."
"Tashi ka tafi tunda baka da hankali."
Ba musu ya bar asibitin tare da mata sallama, dan matuƙar akan Anum ne Umma sai ta
iya kaiwa mutun duka babu gaira Babu dalili.
...
Haka suka kwana a cikin asibitin, Umma kan ita sallah ma take, dan tasan karfe huÉ—u
na asuba zasu farka ace kowa ya fito waje za ayi shara, da goge goge.
Haka ce ta faru kuwa, asubar farko aka tashe su, Ita mara lafiya na gado,
ku kuma masu jinyar su, za a koraku waje.

--- Da sassafe Maman Aminu tazo, dauke da abin karyawa tare da kayan Anum kala
biyu, sai na Umma.
"Sannu Maman Abubakar, ya kwanar sauro?"
Dake tasan Mama bata da wani hausa sosai, dan haka tace mata.
"Alhamdulillahi! Ya kema kika kwana?"

"Lafiya lau, ya me jikin?" Ta tambaye tare da kallon kofar Emergency,
"Da sauki kenan zamu ce ba, tunda kirjin yayi mata sauki!"

Tab'e bakinta tayi sannan ta tura mata abincin gabanta, tana faÉ—in.
"Ga abin karyawan ku!"
"Mungode!"
Nan suka yi shiru, kafin can Aminu yazo, nan suka tab'a hira dan bai tsammani zuwan
Maman su ba, kawai ya dai ganta ne har da abin karyawa, dan haka cikin lalluma da
rarrashi ya shiga bata baki tare da nuna mata, idan laifin da Anum tayi ne yaci ace
ta yafe mata, amma mata magana akan lafiyarta, tashin hankali ne. Ba laifi nasihar
ta shige ta, tare da yi mishi alƙawarin zata k'iyayye gaba.

---
A iyakan rayuwata na aikata laifukan masu mugun yawa, na b'ata sunana da sunan
gidan mu, na yiwa kaina tambari da munannan aiyuka,.sam ban saurari soyayyar da
iyayena ke min ba, nayi ta aikata kusakurai masu girma, har yau ina tsanar kaina da
kaina, nayi rashin jin maganar iyayena wanda shi kawai ya ishe ni ganin bakin

Please Login or Register in order to submit comment