You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta juya ga Hafsat.
"Kika ce zata ga bakin ciki har karshen rayuwar ta? Toh shi kenan, ke ki zauna
kiga farin cikin da zai hanaki Fahimtar bakin ciki. Hafsat ba dai ANUM ta tsone
miki idanu bane? Hafsat ba dai ANUM ta tare miki soyayyar da kika rasa bane, Hafsah
Allah ya baki sa'a , Ni kuma zan tsaya tsayin daka, na cigaba da nima mata kariyar
Ubangiji. Allah ya baki sa'a!"

"Wannan ai shirmen su ne, kuma nasan Hafsat ba zata cutar da yar uwarta ba,
dan haka ki kwantar da hankalinki Umman Anum." Inji Maman Aminu, sannan ta juya
tayi ta fadawa Hafsat, tana nuna mata illar furucin da tayi, idan wani abu ya sami
Anum kar tayi tunanin dan ita ta haife su,ba kyaleta za ayi ba.

Shigar Anum daki,saka yaron tayi a gaba tana kuka.
"Kaga abinda kwaɗayi na yaja min ko? Kaga abinda Baban ka ya ja min ko? Gashi nan
ya b'ata min suna ya kuma lalata min rayuwa ta, Allah sai ya bi min hakkina."

Ta faɗa tana kuka, shima Yaron matsowa yayi jikinta tare da sake ajiyar
zuciya, dan kuka yake son taya Maman shi..

Fushi Hafsat tayi tare da barin gidan, tana me rantsuwa sai ta yi abinda ta saka
kanta. Bayan tafiyar ta Maman Aminu ta shiga dakin Umma domin yiwa Anum fada, ta
same ta tana kuka.
Dan haka ta fita daga dakin.

Tana jin ciwon abinda ya kuma faru, dan haka ta hakura da yiwa Anum faɗa, tunda
ko tayi ma, ai na rashin gaskiya ne, tunda akan...
*Ana barin halal dan kunya....
Yasin 46 na kasa, kuyi comments na sake muku shi bayan sallar juma'a ✊🏽🧗
#Mai_Dambu
[2/12, 2:53 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA SHIDA

*_🤔 Toh ba zance kome ba! Zan cigaba da zama a saman katanga 🤨_

FATAN ALKHAIRI AUNTY SA'AH tare da YAR UWATA RABI'AH 💝💞🤩

Gaskiyar tane, dan haka ta kyale Anum ɗin. Umma ce da ta shiga dakin tayi ta mata
nasiha, har tayi shiru.

Washi gari Jumma'a.
Ina zaune aka kawo min kayan Isma'il, sunyi min kyau musamman yadin da Maude ya
saka yau, wanda irin shi ya umarci Rulwanu da ya ce mata ta sakawa yaron. Da
karamin hular shi daidai kan shi.

Haka ta shirya yaron suka tafi masalaci har da Malam. Bayan sun idar da sallah
ne, suka dauko hanyar dawowa malam yana gaba Maude yana baya.

Dan haka koda suka iso kofar gidan, sun sami Mijin Aunty Binta da Alhaji
Hamisu tare da wasu dattawa har su uku, na cikin kasuwar Central market.. Nan suka
gaisa harda maude shi kuma ya wuce da yaron shi shago.

Bayan sun shiga cikin zauren gidan ya dauko musu taburma, nan suka zauna aka
kuma gaisawa, sannan suka gabatar da abinda ya kawo su. Tare da nunawa malam sabida
mutuncin da kimar gidan..yadda suka nuna girmamawa tare da mutuntawa,.yasa jikin
Maude yayi masifar sanyi, dan haka yaji a ranshi indai mijin Aunty Binta, yazo
sabida darajar malam da Binta tare da girmama surukinsa.
Bai ga amfanin ya so kan shi da yawa ba, ai ko babu kome. Malam ya zame mishi uba.
Amma da ya tuna yadda Anum take son shi, take ya share batun ya ji a ranshi Anum
tashi ce.

....
"Eh toh gaskiya nagode da mutuntawa, amma na tsayar mata da miji, wannan me shagon
shayin, Insha Allah nan da sati shida zan bashi ita." Ya faɗa cikin tsayawa akan
ra'ayin shi.

Nan suka yi shiru, tabbas malam ya burge dattawan nan, musamman yadda ya
gaya musu, ai ya badda yar shi ga bakon haure. Dan haka suka yi godiya ya basu
hakuri ba a kawo musu ruwa ba, suka ce.
"Babu kome wallahi."

Koda suka fito, kallon shagon Maude suka yi, dake yasan mijin Aunty Binta,
fitowa yayi suka gaisa cikin mutunta juna.
"A gaida min Hajiyar mu"
"Taji!"
Cikin mugun kishi Alhaji Hamisu, yace mishi.
"Anya zaka iya rike Khadijah da shagon shayin nan kuwa?"
"Me zai hana! Ai ki dako nayi na rike dijangala tame gari! Ba auren talaka
ba,.talaka noma da sassabe."

"Ka tsaya iya matsayin ka, ita matar Manyan mutane ce, ba talaka irin
ka ba, wanda fatara da talauci ya sashi niman inda , zai tsira da yan hanjin shi."
Inji Hamisu.
Murmushi yayi sannan ya juya zai tafi,ya kuma gayawa. Maude.
"Sana'ar shayi takai maka tunda har ka iya saka turaren dubu dari uku."

Bai kula shi ba, dan ya fahimci shine yazo niman Auren Anum, ya rasa shine zai
mishi rashin mutunci. Dariya yayiwa Hamisu, ai kuwa ya fusata ainun. yayi ta zage
zage.

Haka suka bar wajen sauran mutanen na bashi hakuri, Mijin Aunty Binta shima
ranshi ya b'aci tare da nuna mishi illar abinda ya aikata..
** Lokacin da malam ya shiga cikin gidan, yake labartawa Umma labarin. Zani a
hannun har tana tuntube zata zube tacewa Malam.
"Yanzun sabida rashin adalci, miji na gari yazo ka kore shi ka hadata da alfakara'u
alala lalurati, wallahi ba zai sabu ba! Indai ince na haifi Anum ba zan tab'a
lamunta ba!"

Haka tayi ta maganar ta, daga Malam har Umma zuba mata ido suka yi har ta
gama, sannan ta koma dakin ta, ai tunda taji labarin hankalin ta ya tashi dakyar
take haɗa kominta.

"Malam Ni kam da ka daura auren ne, domin akwai yan bakin ciki da basu son ganin
Allah yayi kome, dan haka Ni yau Jumma'a a daura auren dan kar na rasa Maude.".

Rulwanu da ya shigo yana shan zobo, yaji rashin kunyar da Anum take, sai da ya
kware. Yana zare idanu zobo har ta hanci ya kalli Malam da Umma yace.
"Na shiga uku na lalace, don Allah Malam ku daura mata auren kafin mu wayi gari
muji labarin ta tare a gidan Oga Maude. Ke kam inda kunya yabi kunyi hannun riga da
shegen idanu kamar na budurwan tsaka."

"Umma kinga irin su ko? Ai kome girman munafuki Allah sai yayi yadda yaso."
Inji Anum.
"Umma ki gaya mata ta bar kirana munafiki!"
"Sunan da ya dace da kai kenan." Inji Umma,

Haka akayi ta raha Maman Aminu tana can tana tufka da warwara.

Wayyo Allah na, tunda Malam ya shaidawa Maude maganar shi da Anum, ya shiga
hidima ai kuwa suka kama rikici da Hajjo, sosai suka rikice shi yace auren Anum
babu fashi, ita kuma ta nace ta kafe ba zai auri Anum ba.

Bai bi takanta ba, dan yana ganin ita ba kishi take ba, shirme take yi.

A hankali lokacin yake kuma zuwa, tare da shirya kome, kayan
aurenta na gidan Alhaji sayar dasu tayi, ta kuma cika kudi ta sayi sabo a bakin
kura dan akwai masu kayan furnitures, sai kayan kitchen da ta kuma kara wasu.

A wannan lokacin Maman Aminu tayi kokarinta amma Abine bata kamu ba, dan
ta dage da Addu'a da Ibada, sai Allah ya kare mata imaninta. Kuma babu wani abinda
ya tab'a lafiyar ta.

Dan haka ta bude mata wuta, itama kuma Anum ta birkice mata. Inda take
cewa.
"Wallahi aka hana Ni abinda nake so, idan ba sai na yanke jijjiyar hannuna ba, ko
kuma na shiga duniya yawon karuwanci dama ai ana goranta min, kuma na kwaso abin
kunya da cutar zamani na mutu a dakin mutum.

Haka kuma zai yi jinya ta, shima kuma ya dauka nace Umma da Malam su gudu
dan ba zan saka musu ba."

😂 domin babu wasa a cikin al'amarin
Yadda tayi maganar zaka matukar sha mamaki,()
Allah ya takaita malam baya gida, Umma ma ta fita islamiyya. Aikuwa ta rufe kofar
gidan, zata daki Anum ta dauki D'anta ta rike. Tana kallon Mamanta.
"Me yasa kika daura buri a kaina? Me yasa ba zaki gane abinda Zuciyata ke so ba?
Don Ki barni na auri Maude, shi kawai nake bukata a rayuwata, don Allah ki barni na
zauna da shi duk sauran Yaranki suna farin ciki me yasa Ni ba zanyi ba?"

Ajiye itaccen tayi sannan tace mata.
"Ba hanaki farin ciki nake ba, Anum Allah yayi miki nasibi, don Allah karki sake
damarki!"

"Wani dama wani dama kike ganin ba zan sake shi ba? Maude shine dama ta! Wallahi ba
zan iya rayuwa da wani namiji idan ba shi ba, don Allah ki barni na rayu dashi!"

Duk ta inda ta bullo Anum zata toshe.karshr dai haka Maman Aminu tayi tsirara
a gaban Anum, gwiwar dukka biyu a kasa, juya mata baya Anum tayi tare da fashewa da
kuka.
"Idan har haka na haife ki, ki janye aurenki da Maude ga Hamisu nan, idan kuma son
ranki kike so, Insha Allah sai kin wulakanta sama da yadda na wulakanta kaina a
gabanki!"

Girgiza kai tayi sannan tace.
"Har abada ba zan kuma miki Biyayyar da zan rayu cikin kunci da bakin ciki ba,
Maude nake so? Shine muradina, shine farin cikina. Ruwanki ne ki so shi ruwanki ne
ki kishi. Amma Tabbas saura kwanaki ƙalilan mu kasance a duniya daya!"
Wani irin kuka Maman Aminu take yi, haka Itama kanta Anum kukan take yi, bata
jin zata iya kyale Maman Aminu ta Cigaba da wulakanta mata farin cikin ta, dan
haka, ta shiga tuno yadda Alhaji yake saduwa da ita, cikin kazamta, tare da mata
sanadin rashin yaranta har biyu.

Kuma duk sanadin dogon buri, haka bawan Allah nan yaso haukata mata rayuwa, duk
mahaifiyarta bata gani ba. Kuka take tun daga tsaye har ta durkusa kasa, rungume da
Yaronta.
"Me yasa kika zab'i son ranki sama dani? Sauran Yaranki ba haka kika lalata musu
nasu rayuwar ba, amma ni kin mai dani hajarki, Ni ba zan auri abinda kike bukata
ba, koda kuwa shi kuɗi ne da kanshi.Allah ya bani miji na gari ban san meye
Matsalarki da kika tsani maude, Ni ya dace ki tsana na har abada, don Allah ki cire
ni daga cikin Yaranki, ki barni da Umma. Idan kuma ba ke ce kika haife ni ba ki
gaya min, na nono uwar da ta haife ni!"

Wannan maganar yayiwa Maman Aminu zafi, dan haka ta fincike Yaron hannun Anum ta
wurgar dashi, ta rufeta da duka da wani itaccen marke, sam dukar bawai bai shigeta
bane, D'anta kawai da ya kwalo da kofar dakin Umma yasata rarrafawa ta dauki yaron
tana kuka.
"Ina zaki san darajar shi? Ina zaki zafin shi, Uwar da ta amsa sunan Uwa kare
D'anta take daga jin ƙishirwa, dan haka Dake ni Maman Aminu, ki dake ni ki cire
haushin ki, bakin cikinki ne zaki fanshe domin ba zan miki yadda kike so ba, dan
haka dake ni ki cire damuwarki" tana kuka tana gaya mata duk abinda ya fito
bakinta, tare da kafewa da gaya mata.
"Auren maude babu fashi ko kina so ki baki so! Zaki ganni dauke da gidan jinin me
shayi."

Haka ta wurga da itaccen ta fincike Yaron a karo na biyu ta rike dan ta, goshinta
yana zubda jini.
"Ki sake min Yarona, lokacin da Ubanshi yasa a kashe ni dashi baki kawo min dauki
ba, lokacin da yake zubda min cikina baki kare ni ba, kin saka kwaɗayi da son
zuciya akai na, toh wallahi kinji sai dai gidan MAUDE."

Ta faɗa tana kallon Maman Aminu, wanda idanunta yake zubda kwalla.
"Ni kike gayawa magana Khadijah? Insha Allah kare sai yafiki daraja, wallahi sai
kinyi yawo tsirara, sai kinyi hauka tuburan Insha Allah sai Kinga mugun karshe. Ni
kika zabi wulakantawa saboda namiji"

Daukar yaron ta tayi ta shige daki dashi, tana kuka.
"Kamar yadda kika gaya min magana, Insha Allah dan da kika haifa sai ya dake ki,
sai yaja ki kamar kare zuwa kofar gida yana tozarta ki. Wannan yaron hannun sai ya
miki abinda kika min sama dashi. Kai Khadijah Allah ya isa tsakanina da ke, ban
yafe miki Haihuwar ki nayi ba!"

(Addah Ramlat! Ki isar da labarina duniya ta Fahimci halin da iyaye suke cilla
yaran su cikin shi! Addah Bakin Uwa masifa ce! Addah Ramlat baki ce kome ba, kuma
kina kallon sakona! Please said somethings!)

(Tun da nake rubutun labarin hausa ban tab'a ganin labarin da ya tsaya min a rai
ba, dan kusan shekara biyu zuwa uku nake son rubuta zanen ƙaddara ta, samun labarin
Anum ya kuma zaburar dani wannan labarin ya tab'a zuciyata)

Haka Maman Aminu ta cigaba da kwashe mata albarka, tare da mugayen alkaba'i,
tunda ta shiga dakin Umma take kukan har ta kwanta..tana rungume da Yaronta. Wanda
take ji ba zata iya barin shi a hannun Ubanshi ba ita tafi dacewa da rikon danta,
dan ba zata rab'a yarda ya tashi a wulakance kamar yadda take gani a gidan Ubanshi.

Koda Umma ta dawo ta tambayeta me ya faru, amma Anum taki magana, sai ma
kukan da take yi.
"Toh Allah ya kyauta, ya sa mu dace duniya da lahira."

Haka Maman Aminu ta cigaba da gayawa Yan uwan Anum ta zare hannu akanta,
kuma ta tsame albarkan da yake kan Anum, wannan abun yayiwa Hafsat dadi, dan haka
take mata dariya da nuna mata ai ita kan ta kad'e har buzunta.

Bata d'aga ido ta kalle su, hidimar bikinta ne a gabanta, wanda ya rage saura
kwanaki huɗu.

Kuma kullum suna tare da Maude, ko fasa mata goshin da Maman Aminu tayi sai da
ya rikice mata.kuka ne ya zo mata, amma haka ta had'iye. Rike hannun shi tayi
sannan tace.
"Don Allah ko na aureka karka juya min baya, Ni kuma zan tsaya na kare aurenka da
kimarka.

Ba zan taba barin wani ya tozarta min kai ba, Maude kai ne kawai nake
bukata, bayan haka duk inda ka ga ya dace ka kai ni zan zauna da kai."

Rike yatsun hannunta yayi suka yace mata.
"Insha Allah ba zan tozarta kimarki ba, kuma zan zauna dake kar karshen rayuwata
Amma....

*Hmmm... Inji me ciwon hakori*

#Mai_Dambu...
[2/13, 9:44 AM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI.

Hawayen da take kokarin dannewa ne ya fara saukowa, bakinta na rawa tace mishi.
"Amma me? Abban Isma'il. Don Allah karka sanya min shinge a zuciyata, na gama yarda
*KAI RABO NA NE*, karka sani jin cewa bani da Sa'a mana, idan ma laifi na maka don
Allah ka min hakuri karka sara min baki."

Kalmar KAI RABO NA NE, ya cigaba da yawo a cikin kanshi da kunnen shi, sake
hannunta yayi yana kallon yadda take zubda kwalla, cikin wani irin yanayi me dauke
da ban tausayi, hannun shi dukka biyu ya saka a fuskarta yana cewa.
"Nima nasan *KE RABO NA NE!* Shi yasa nake faffutikar ganin na same miki a rayuwa
ta, amma kuma idan zanen ƙaddarar mu bata so haka ba, zan cigaba da miji fatan
Alkhairi, Anum nasan inda rai da rabo wata rana ba zamu yi kuka haka ba."

Daga haka ya juya tare da barin zauren, tsayawa tayi tana kuka me matukar ciwo. Da
tashin hankali. Da yau bata bi ta mutane ba da basu kaita sun barota ba.
Duk kukan da take da musayan kalaman da take da maude duk akan kunnen Maman Aminu.
Murmushi tayi tana faɗin.
"Yarinya haka zaki yi hakuri tunda Allah ya kawo ki a cikina, ya kuma yanka min ke
da araha dole ki auri miji ready made."

Haka ta koma gida, tana tsakar gida, tare da yar wake waken su na Igala,
tana yi tana gyada kanta, Ismail ne ya fito yana kallon hanyar waje tare da kiran
Maman shi. Amma Maman Aminu bata juya ta kalle shi ba.

"Ummi!"yayi wani gwarancin shi tare da cewa "tiyaaa!"

Amma Maman Aminu bata d'ago kai ba, can ta mike tare da shiga kitchen ɗinta, ta
dauki ruwan zafi a butar karfe, ita kanta bata yi haka da wata manufa ba, sai dai
kaddara. Tana zuwa ta juye ruwan a bokitin ta koma kitchen. Ganin an.juye ruwan ya
taso yana cewa.
"Af.. af.....af!"
Yana kai hannun shi jikin bokitin, sai ya saka dariya ta kuma saka hannun shi ya
tab'a bokitin, ko ya aka yi ya kayi kawai yaron nan ya fada da fuskar shi cikin
ruwan zafin nan.

Wani irin ihu yayi, tare da hantsilawa, ita Maman Aminu bata Fahimci abinda ya
saka yaron ihu ba, amma Anum da ta shigo gidan tana share kwallar ta, ta ga danta
yana birgima. Wani irin kuka ne ya kuma zuwa mata ta fara kwalawa Umma kira, tana
gyaran murya. Alamar tana sallah.

Da sauri ta isa bakin randa ta saka hannu, tare da d'aga shi yana wani irin
nishi..jikin shi yayi jajjur, wurga shi cikin randa tayi. Tare da saka hannunta
tana juya shi cikin uwa, sai lokacin Maman Aminu ta fito. Ta samu Anum ta ciro
yaron, tana girgiza shi.
"Umma don Allah fito zai mutu!"
Ta faɗa cikin wani irin fitar kuka, da sauri Umma ta fito Maman Aminu tana kallon
su, Umma ta yaga rigar haka ta zare da fatar jikin yaron,komawa gefe Anum tayi,
tana kallon D'anta. Daukar shi Umma tayi ta ajiye shi sannan ta koma d'akinta ta
dauko kudi da wayarta ta fita dashi.

"Ya Allah!"
Ta iya furta kalmar, tana zaune har Rulwanu yazo ya taimaka mata suka bi bayan
umma, Maman Aminu bata ce mata Allah ya sawwaka ba.

Haka suka nufi asibitin, bayan sun isa suka nufi inda aka kwantar dashi, a
lokacin kowa sai da ya zagi Anum bata iya magana na, sai yake tana murmushi hawaye
na zuba mata.

Bayan ta gama abinda zata iya Umma ta bar asibitin, ta dawo gida. Haka yaron
nan yake kuka, can itama ta fara kuka. Yan uwanta ne suka zo. Ana ta sami sauki
amma dukkan su bata laifi suka yi kamar yadda Maman Aminu tace ta, fita gurin Maude
ta bar yaron ya faɗa ruwan zafi.

Karshe haka suka barta a gurin, tana rike da hannun shi Me lafiya, tana
share kwalla. Wajen karfe shida taga Umma bata dawo ba, ta kirata. Amma yadda Umma
ta bata amsa ya saka Anum rudewa tana tambayarta lafiya.
"A'a babu kome, kawai bana son damuwa ne, ki zauna a jikin yaron Rulwanu zai kawo
miki kome."

Da tasamu yayi barci, haka ta fita wajen asibitin, ta zauna tayi kuka iya
kukan da bata jin zata kuma yi a rayuwar ta, haka kawai take ji a yanzun babu
abinda zai iya sakata zubda kwalla matukar ba me hujja bane. Mahaifiyarta da kowa
nata ya wulankata ta, sabida bata da Arziki bata auren me Arziki, bata jin ko
duniya aka ajiye mata zata zab'a.

"Ke! Kece Maman Isma'il?" Da sauri ta mike,.garin amsawa nice ta tauna
harshenta. Bakinta yayi nauyi, dan haka ta ce mishi.
"Hmm!"
"Toh sai ki barshi kuma? Gashi can ya lalata alluran hannun shi"

Da gudu ta kwasa tare da nufar hanyar ward ɗin, tunda ta shiga Nurse
suke balbale ta, duk sai ta rasa ya zata yi, ta fashe musu da kuka..tare da zuwa
jikin yaron tana shafa kanshi.

Bayan sun maida mishi alluran suka barta tana kuka, mika mata hanky aka yi
ta amsa. Da sauri ta juya, wani katon abu ne ya tsaya mata a wuya, da sauri ta faɗa
jikin shi. Tana sauke ajiyar zuciya. Cak ya tsaya kamar Status, ya kasa kome.
Zuciyar shi tana wani irin bugawa, hannun shi ya kai kanta, tare da cewa.
"Kiyi hakuri!"

Kukan ne ya tsaya ta d'aga kai tana kallon shi. Kafin ta janye jikinta daga
gare shi, tana kuka.
"Sun juya min baya!"
"Allah bai juya miki ba"
"Sunce nice nayi silar fadawan shi ruwan zafi"
"Allah yana tare da masu hakuri."
Duk yadda take son kawo mishi maganar yaki bata damar haka, har zuwa karfe goma.
Kallonta yayi sannan yace mata.
"Kin ci Abinci?"
"Sai kana da gata zaka samu!"
"Inji waye yace baki da gata?" Malam ya tambaye ta, sunkuyar da kai tayi tare da
mik'ewa ta nufi malam, a hankali ta kai kanta kafadar shi, tana cewa.
"Umma ta guje ni!"
"Ina tare dake!"

Kukan da take yi ne yake tab'a shi, dan haka ya shiga ya fita aka mai dasu daki
na musamman, daga nan suka zauna su uku, a jikin yaron, Malam da Maude, ita kuma
shiga cikin abincin da malam ya kawo mata, tusawa take amma bata jin dadin shi.

Tana gamawa tayi alola da sallah, sannan ta koma zata takura malam yace ta
kwanta a kusa da Yaron, da Malam da Maude suka kwana akan yaron, da zaran ya fara
rikici zasu lallaba shi, suna ƙoƙarin tayi barci.

Abinda ya faru kuwa, Maman Aminu. Hada gurmi tayi wanda ya janyo aka yi fada
tsakanin Yaran Umma da Yaran ta, karshe ta fidda abinda Umma take mata, yadda ta
makale Anum, a jikinta. Tare da kundumawa maude Sharrin da Yaranta suka ce ya bar
musu kofar gida, Yaran Umma suka ce basu san da haka ba fada har kofar gida.

Gagarumin rikici aka yi, shine Umma ta ware yaranta da kuma cire Anum a
jikinta. Tare da rokawa Anum din mafita A gurin Ubangiji.

--- Asuban Fari suka bar asibitin, bayan sun tashi Anum daga barci. Ya
rage saura kwana ɗaya auren su. Dole Maman Aminu tazo asibitin tana murna, kota
kanta Anum bata bi ba, ta ficce.

...tana isa gida, ta kwanta ta huta a falon Umma. Sai da Rulwanu yake gaya mata
abinda ya faru, tare janye auren ta da MAUDE yayi.

Ihu ta saka tare da fita da gudu tana zuwa tayi wurgi da kayan shayin shi.
"Meye nayi maka? Ka tsaya ka bani amsa meye nayi maka da zaka fasa aurena, sadaukar
dani kayi?"

Ta kafe shi da manyan Idanun ta. Bai mata magana ba, ya shiga tattara kayan
shi da ta fasa, cikin masifa da zafin rai ta tsallaka gaban shi.
"Ka gaya min meye laifina? Meye nayi maka da zaka cutar dani? Duk dimbun kaunar da
mukewa juna da wannan zaka saka min?

Na zata zaka iya rayuwa dani ashe kai naka tunanin."

"Kinga nan gurin sana'a ce, ki shiga cikin gidan zamu yi magana da..."

"Fuck and hell You! Maganar banza" ta faɗa da karfi.
"Wallahi ban tab'a kawowa zaka karya min zuciya ba, Amma Insha ALLAH. Maude na
Barka har karshen rayuwata, ba zan maka kuka ba, amma kai sai kayi min kuka, Allah
ya bamu rai da lafiya me amfani."
Ta juya tare da barin gurin, tana shiga cikin gida, ta fashe da wani irin kuka,
wanda har kofar gida ana jin muryanta. Kuka take tare da zuba gwiwar ta a tsakiyar
tsakar gidan, duk da Maman Aminu tana Asibiti. Umma tana jinta haka bai saka ta
fito ba, sai da tayi ta koshi sannan ta tattara abinda tazo dauka.

Ta fita, zunzurutun zuciyarta ta karkashe, tun daga bakin kura har babban
Asibitin da kafa ta taka, lokacin da ta isa, kallon Maman Aminu tayi cikin wani
irin murya me matukar ban tausayi tace mata.
"Tashi ki koma gidan mijinki!"

Kallonta Maman Aminu tayi zata yi magana ta dakatar da ita, sannan tace.
"Bana son na dauki bakin mutane ne, don Allah bar asibitin nan kafin raina da naki
ya b'aci."

Tasan Anum kuma tasan zata iya aikata kome, dan haka ta mike tare da ajiye mata
10k.
"Zoki dauki kuɗin ki"
"Baby!" A fusace Anum ta zuba mata jajjayen Idanun ta,
"Karki kuma, kar ki yarda ki kirani baby! Dauki kudinki."

Babu musu ta dauka, sannan ta fita, tana zane a dakin Rulwanu yazo. Dauke kai
tayi tana kallon yaronta da yake barci, ajiye mata abinci yayi tare da

Please Login or Register in order to submit comment