You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon ta.
Kanwar shi wacce suka raba kuruciyar su tare, kullum cikin fada da tsokanar juna
suke, ta kowa yayi a hankali, ya rike hannun ta, janye hannunta yayi. A hankali
hawaye ya zubo mata.

Zama yayi tare da cewa.
"Maude bai da niyyar rabuwa dake"
Watsa mishi kallon banza tayi, sannan tace mishi.
"Dauki abinda ka kawo ka bar asibitin nan!"

"Anumullah!"
"Rulwanu!"
Ta kira sunan shi da karfi,
"Amma ki Fahimci Maude bai da nufin."
"Idan kanin Ubanka ne sai kaje can ka kare shi!"

Yasan yadda take cikin fushin nan ba lallai bane ta fahimce shi, dan haka suka
zauna a dakin yana kallon yadda yake share kwalla, har ya gama zai tafi.

Fuskarta kawai zaka kalla ka fahimci abinda yake ranta, dan haka bayan
tafiyar shi ta shiga ban daki tayi kuka har ta godewa Allah, sannan ta fito ta sami
Maude a tsaye. Abin sallah ta shimfid'a ta fara gabatar da sallah, zunzurutun bata
kulla gaskiya a sallah ba. Tayi raka'a kusan sha biyar. Daga karshe ya zo gabanta
ya zauna tare da saka kafar a kasa, yana zaune a gaban sallah, hannun shi yana kan
gwiwar shi.

Shafa kan shi yayi sannan yace mata.
"Sallah tayi yawa."
Cikin fushi ta juya zata bar kan abin sallah ya riko hannunta, tare da fincikota ta
faɗa kan shi, kirjin ta yana wani irin bugawa, rabonta da ta kusanci inda namiji
yake wata goma sha bakwai ana niman na sha takwas .
Zare hijab ɗinta yayi tare da janyota jikin shi, ai kuwa ta fara kiciniyar kwace
kanta.
"Ki nutsu!"
Amma haka ta mike tare da ture shi, mik'ewa yayi tare da isa gabanta.
"Ka fita min a daki kafin nayi maka ihu."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalle ta, tare da hada ta da bango. Aikuwa ta
shiga kai mishi duka da yakushi, ture shi take amma yana nan a manne da ita, bai
kuma ji ya hanata ba, a hankali ya kai bakin shi kunnenta.
"Zan cigaba da jiranki, ba zan tab'a sarewa da aurenki ba, Ba kome nake bukata a
jikinki ba, kece nake so mu karasa rayuwar mu a tare, ANUMULLAH ba zan iya gaya
miki irin kaunar da Ni Aliyu nake miki ba, ANUM KHADIJAH, Sabida ke na kasa komawa
daga inda nafito.

Khadijah Mahaifiyarki bata kaunar mu a tare, kuma ta wani gurin banga
laifinta ba.

*Mahaifina bai da lafiya! So idan na farka da asuba kafin na tafi asibitin zan na
muku typing ɗin, idan kuma baku gani ba! Ku rike a ranku bana gida ne! Domin dole
zan zauna a can don Allah na fadi Uzurina, dan wani lokaci mutane bamu da Uzuri*
#Mai_Dambu
[2/13, 11:38 AM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.

"Duk da na bata dukiyar da take bukata,sai dai ta gaya min gaskiya, kuma na gamsu."
Ture shi nayi tare da matsawa,
"Anum!"
Bude mishi kofa nayi, tare da nuna mishi hanya. Ban kalle shi ba.
"Ki bar hawayenki ya zuba mana! Yana rage zafin zuciya!"
Shanye hawayen tayi tare da kallon shi tsaf.
"Zaka iya fita!"
Wannan fushin baya kaunar shi, dan yana jin kamar tabo ce da yayiwa Zuciyarta,
dan haka ya rufe kofar, tare da fincikota ya matsata da kofar, tare da kai bakin
shi kan nata, kiciniyar kwace kanta take ya kai hannun shi dukka biyu, ya matsa
hannunta da kofar, ture kanshi tayi tare da juyar da kanta..tana wani irin huci.

"Bana son kazamta! Bana son ka b'ata min jikina da najasa, bana son ka karya
min tsarkin da yake jikina da zuciyata, karka ajiye min abinda ba zan iya cire shi
ga kowa ba, karka manta ni uwa ce, karka rabani da sauran abinda na tanadawa rayuwa
ta, don Allah karka sare min gwiwata.."
Hade goshin su yayi tare da sake hannunta.
A hankali ya maida kanta kirjinshi, tana jin yadda zuciyar shi take bugawa, shafa
bayanta yake tare da lallashinta, tana jin saukar ruwa me zafi a dokin wuyarta. Dan
haka ta d'ago kanta zata mishi magana ya kyale ta, ya sauke soft lips d'inshi akan
nata, wanda ake wani irin wet. Sakamakon yadda take bit d'inshi idan ta tuna abinda
aka mata.

Cikin idanun juna suke kallo, she can think how long time. Da ta tab'a
kallon romantic film, da yadda suke kazamtar shan bakin juna, but yau a madadin
warin bakin da take tsammanin yana dashi kamar yadda take jin bakin Alhaji Mudi
yana buga doyi, sai taji wani kamshin minti fresh, ya daki hancinta har zuwa
makoshinta.

Tunda take haduwa da maza bata tab'a haduwar da namijin da take hango madarar
kaunarta cikin eyes d'inshi kamar Maude ba, tana son yin breaking kiss din, amma ta
kasa sakamakon wani irin kewar shi da yake zuwa mata unexpt, a hankali ta janye
bakinta tare da sauke kanta kasa.
"Nagode da kasanya ni na samu nutsuwar kwalkwal, tunda baka jin rokon da nayi maka,
karka sani na rasa."

D'ago kanta yayi sannan ya bata wani light peck a goshi, sannan ya kai bakin shi
kunnenta yace.
"Daga gobe ba zaki kuma gani na ba, Insha Allah." Yadda yayi maganar numfashin sa
yana sauka a dodon kunnen ta, yasata zuɓewa jiki ba kwari by now ta kasa kuka.

Sai zafin zuciya, haka ya zauna a gabanta sannan ya ciro zoben azurfan dake makale
a sarkan da take yawan gani a wuyar shi ya b'alla igiyar ya saka mata a cikin
yatsunta. Tana zaune quiet bata iya ko d'aga kai ta kalle shi ba, zuciyarta ne yake
bugawa sosai.

Kallonta yake ta masifar bashi tausayi, shima zama yayi a gurin yadda bata
tashi ba haka shima bai tashi ba, yana yawan hango murmushinta tun daga yaranta har
zuwa girman ta, har zuwa karfe biyu na dare tana zaune bata d'ago kai ba, shi kuma
bai ji a ranshi ya tafi ya barta cikin damuwa ba, kiran sallah farko yasata mik'ewa
tana sauke ajiyar zuciya.. sannan ta nufi ban daki, sai lokacin ya lura da inda ta
tashi ya b'aci. Tashi yayi tare da zare key din kofar ya rufeta, koda ta fito duba
jakar kayan su tayi taga bata zo da pant din ta ba, kuma babu pad. Wayarta ta duba.

Ta shiga duba kayan kwanciyar Yaron, ta sami wata tsohuwar tsumma, ta ninke sannan
ta nufi ban daki. Ta saka sannan ta wanke pant din ta, ta koma fito ta goge inda ta
b'ata, sai lokacin ya shigo. Kallon juna suka yi ya ajiye mata laida, b'ata kalle
shi ba, bata kuma damu dashi ba.

Haka yazo ya tsaya a bayanta,ya kai hannun shi kafad'arta.
"Ki bani damar na kare kain.."
Shiru kake ji, yayi maganar duniyar nan Anum bata d'ago kanta ba, bata Kuma ji a
ranta zata amsa mishi ba, haka yayi ta surutu har ya kusan rasa sallar asuba, daga
nan ya fita tare da mata fatan alkhairi.

Lumshe idanun ta tayi tana kuma shaƙar kamshin turaren shi a jikinta, kwalla ne
suka shiga mata wasan tsare akan fuskarta, kuka take kamar ranta zai fita, dan haka
tayi maza ta dauki ledar da ya kawo mata ta rungume a kirjinta, tana kallon kamar
yau ta farka daga cutar mkanta.

Kmshin turaren shi yana tafiya da rayuwar ta, dan haka ta bude ledar, always
da pant ne, sai kuma madara da maltina shi yasa ledar yayi nauyi, zama tayi ta ci
kuka sannan ta shiga ban dakin ta saka pant din. Tayi mamakin yadda aka yi yasan
irin wanda take sakawa.

Sai dai fushin da zuciyarta ta dauka dashi bata jin zata kuma yafe mishi.
Har abada.

Tana fitowa ta samu wani mutum a tsaye dan lokacin gari ya waye. Ajiye mata
kayan kwali yayi, abun mamaki daga kayan ci har zuwa na sha, sai 50k.

_Zan cigaba da jiranki har karshen rayuwata_

A.A.H.T
Maude.....

Kai takardan nayi saman hancina, kokarin cusa k'iyayyar shi nake zuciya ta,
amma yaki shiga.
"Mugu ka zalince Ni zaka turo min kudi ka mayyar kuɗi ko!"

Ta faɗa haka a fusace, tana kuka.

Zama tayi tasha kukanta, abinda ya kawo mata a kwalin ta fara dubawa, manyan
gwangwanin madara da Ovaltine, sai suga. Tarkacen yara dangin chocolat.

Sai pampas, da man shafawa. Sai always. Da kuma wasu maganin yaron, dauke kai
tayi tare da share kwallar ta.
Zuwa karfe takwas, Aunty Binta da Aunty Rabi suka zo. Dake Aunty Binta da
unifoam yasa Aunty rabi bata wani samu matsala ba, har dakin da Anum suke tana kuka
rike da takardan maude, wanda bata damu da son sanin waye shi ba, duk da tasan
sunan shi na gaskiya Aliyu ne. Wannan ba damuwarta bane.

Matsalar ta dashi akan me zai tafi ya barta cikin damuwa, bayan dashi ya dace su
raba matsalolin rayuwar su. Tunda su Aunty Binta suka shigo. Sau daya ta kalle su,
bata kuma kallon inda suke ba.

Daukar takardun yaron Aunty Binta tayi, cikin sauri ta rike hannun ta, tunda
suke da Anum bata tab'a musu wani abu na reni ko rashin kunya ba, asalin ta irin
yaran nan ne masu matukar kiyayyewa da girmama na gaba dasu.

Wani abu dan gane da Anum tana da wasa da dariya, amma tana da mugun taurin
kai da kafiya, sai dai tana iya jure kowani irin abu, duk abinda zaka ga tayi
magana akai, toh tabbas babban al'amari ne, shi yasa Aunty Binta ta d'aga hannunta
kan takardun. Nuna musu hanya tayi, suka kalle ta zasu yi magana ta saka hannunta
ta toshe kunnenta.

"Tunda Umma ta juya min baya bana bukatar kowa a tare dani!" Ta
faɗa da karfi tare da nuna musu hanyar fita.

Babu musu suka fita, Aunty Rabi ta kira Umma ta gaya mata, abinda Anum tayi,
kuma babu karya sun nuna mata cewa ai tuntuni ya dace ta zare hannunta akan Anum
bata zare ba, sai yanzun da Anum take buƙatar ta zata juya mata baya, sai da kome
ya jagule mata mata zata bi na Maman Aminu.

A'a tayi kuskuren, dan haka ta dawo ga Anum dan tafi bukatar ta a halin yanzun.

Jikin Umma tayi matukar sanyi, dan haka suka tawo da Rulwanu, wanda
shi kawai Anum ta iya amsawa gaisuwar shi, sau daya ta kalli Umma, tace mata.
"Ina kwana!"
"Lafiya lau Anum, ya me jiki!"
Bata amsa mata ba, sai jan Rulwanu da tayi gefe ta rufe shi da masifa, tare da
ɗaukar kudin tace.
"Ka mai da mishi tsiyar shi, Ni ba mayyar kuɗi bane, kuma Nagode da ya sayar min da
kaunar da nake mishi."

"Anum!"
"Kaga Malam idan ba zaka kai mishi ba ka gaya min! Kowa ma gudu na yake, Malam bai
kuma zuwa min ba, itama wacce nake kallonta a madadin farin cikina, ta juya min
baya kawai ka kai mishi kace mishi nagode."

"But;"
"Karta yarda raina ya b'aci."

Cikin fushi ya wanketa da mari, cak taji kome ya dauke mata, sannan ya rungume ta,
yana fadin.
"Haka yaji lokacin da aka kai karan shi ga Ofishin immigration. Haka Suka tozarta
mana mahaifiya, haka suka yi ta gaya mata magana marasa dad'i ita da shi, kinsan
halin da Malam yake ciki? Duk saboda aurenki, ki buɗe ido da kyau, ki buɗe
zuciyarki da kyau, Domin Ya Gaya musu cewa, Idan *KE RABON SHI NE* duk duniya babu
wanda ya isa raba ku, sannan ya ajiyewa mutumin takardan shaidan zama ɗan ƙasar
Najeriya tare da na lasisin zama ɗan bauchi, Anum me Umma tayi a rikon da tayi
miki?

Wallahi har abada ba zan tab'a wulakanta Maman Aminu ba, amma ta tozarta mana
mahaifiya, ta sanya malam yankan jiki ya fadi. Ban mare ki dan ina jin haushin
Abinda akawa Umma ba, jiya yazo da bakin cikin ki saurare shi amma haka kika ki
kallon shi" jan iskar bakin shi yayi sannan ya fesar.

Ya cigaba da cewa.
"Ya hakura ne dan babu yadda ya iya, kuma idan ya tirje zasu cigaba da d'agawa
Malam hankali. Don Allah ki dube matsalar da idon basira, Maman ki tana son ki auri
Hamisu. So ki aure shi kawai."

Daga haka ya cireta a jikin shi, kallon idanunta yayi da suka
juye zunzurutun tashin hankali da dimuwa. But ba zata iya cewa kome ba, kowa ma
haushinsa take ji, ta kasa magana, dan haka ta koma gefe ta jingina da bango.

Wasa wasa sai da ta shafe awa daya da rabi, kafin ta bar gurin sabida kukan da
Yaron ta yake yi, taje ta rungume shi da ciwon shi tana kuka. Daga Rulwanu har Umma
tayata kokawa suke.

Haka ta cigaba da jinyar Yaronta, Umma tana zuwa ta wuni a jikin Yaron,
Maman Aminu kuwa idan tazo kamar zata goya Anum, murmushi take idan ta nuna yadda
take kwashe mata albarka, yau kuma tana fadar wasu kalmomin yabo da saka albarka a
tare da ita.

Ranar wata Jumma'a, Alhaji Hamisu tazo musu, daga yadda yake barin kudi
ta Fahimci matakin da ta ajiye mutumin, gashi nan dai bai da aibu, bafulatanin
Bauchi ne, kyakyawa baki dashi, yazo yayi ta mata zuba tana kallon shi, yana gamawa
yayi mata sallama, sannan ya bar Asibitin.

Nan Maman Aminu tayi ta gaya mata irin yayyafin nera, haka suka sami
sati biyu aka sallame su, tunda ta shigo Unguwar, idanun jama'a yake kanta, ta
tsime kamar ba ita, ba, tana isowa kofar shagon shi, tana jin kaifin dara darar
idanun shi a jikinta yana mata wani irin sauka a jikinta, a hankali ta d'ago
kanta,ta zuba mishi ido.

Murmushin takaici tayi mishi sannan ta dauke kanta, tayi imani da ita
ce, ba zata tab'a barin shi ba, ko Office din yan sanda aka kaita, zata tsaya akan
shi.

Amma shi fa, yayi wani wurgi da ita, kamar wani abu mara daraja, tana sab'e da
D'anta a kafad'arta, ta shiga cikin gidan su.

Da matukar ban tausayi yadda take kallon Maman ta tana wani rawan
kai zata amshi D'anta, ta wuce dakin Malam da shi, ta zauna a kasa, tana kallon
malam din da aka sanya mishi roban ruwa, dan sun jima da sallamo shi.
"Malam!"
Murmushi yayi mata, sannan tace mata.
"Allah yayi miki albarka! Insha Allah sai kin zama musu Inuwar gajimare, ke daya ce
tal zaki zamewa kowa bango. Insha Allah kukanki zai zame miki dariya, Khadijah,
nasan albarka zata zagaye rayuwarki, Insha Allah mijinki sai ya mai dake sarauniya
a cikin duniyar shi."

*Allah Ka bawa mahaifina Lafiya🙏🏼*
#Mai_Dambu
[2/18, 8:45 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SITTIN
😹 Alqur'an koda gudu da tsalle tsalle zanyi wuf da Labarin nan😜
My Emterh da sauran barkanku....

A fusace ya juya zai bar falon ta rike hannun rigarshi, hawaye na zuba da mugun
gudu akan fusakarta. Girgiza kai tayi sannan ta rike shi, tana shesheka.

"Barrak da Annur sunce min yar bola ce ni, shi yasa bani da Mama, Dadda Mama na
ta mutu ne? Wai duk wanda bai da Mama ko an dauko shi a gidan Marayu ko kuma an
yarda shi a bola, Dadda ka kai ni naganta."

Murza hannunta yake yana huci, tare da rintsa idanun shi, jijjiyar kan shi yana
mik'ewa sosai.
"Yaushe zaku yi hutu?"
"Ban sani ba!"
Ta faɗa a sanyayye.
"Hoor, ina da tafiya aiki. ne, Insha Allah idan na dawo da kaina zan kai ki,
gurinta sai dai Mamanki bata sona!"

Hannunta takai fuskar shi, tana dariya tace.
"Zunnoon yace min wai tenta din Class din mu tace wai ai kai hadadden mutum ne kace
Mama bata sonka,.Dadda kayi mata laifi ne amma nasan Mama tana sonka."

Yadda take dariya sai yake hango Anum a lokacin da take shekara goma, hatta
gashin sajenta wanda suka haɗu da na goshinta, hatta gashin giranta a hade suke
kamar na Uwarta, murmushin takaici yayi, tare da ɗaukar ta, suka fita yana saukowa,
ya kalli Sharifa da take faman da yaran Zulkhalainie, Yaran kanwata ce.

Kallon zaki gamu dani yayi mata, sannan ya fice da yar shi. Bai gaya
kowa ba, ya zuba mata ido zai yi ya ga gudun ruwanta.

--- Part din Innar shi ya shiga da ita, zama yayi da ita, ta
kalli Yayar Maude Rufaidah wacce tazo gida yanzun nan duba Innar mu da take fama da
ciwon kafarta.

Mika mata hannu tayi, Rufaidah tayi, da sauri ta sauka a jikin Uban
nata, ta nufi gurin Rufaidah, tana zuwa ta faɗa kirjin ta, tana sauke ajiyar zuciya
tare da zubda kwalla. Hannunta a bakinta.
"Asadullah! Ba dai kana nufin ba zaka kai ta taga uwarta ba?" Ta tambaye shi, tana
kallon, hade ranshi yayi tare da hararar Nusaibah da sauri Rafi'a suka bar d'akin.
B'ata rai yayi ainun.

"Addah!"
"Asadullah! Ni ban hanaka laifin matar ka ba, amma kasani Uwar Yarka ce, tana
bukatar mahaifiyarta ka duba kwayar idanun ta. Cike yake da maraici ta rasa
soyayyar Uwarta, don Allah."
"Addah karki roke ni, zan kai ta idan na dawo daga aikin da zanje."

Murmushin jin dadi tayi sannan tace mishi.
"Yarinyar nan zata yi hakuri, gata da sakewa."
"Haka Mahaifiyar ta take, sai dai yanayin kaddara ya sauya ta."

Ya faɗa a sanyayye, ciro wayar shi yayi, sannan ya mika mata hoton Anum, gata nan
lokacin tana yarinya. Akwai na lokacin auren mu.

A hankali take bin hoton, shigowar Nusaibah da ta leka wayar tace.
"Kamar nasanta, amma na manta inda na tab'a ganin ta."

Rafi'a ma ta leka, tace.
"Kai nasan wannan matar"
"Kusan me? Kafin na kareraya kafaffunku, ku bar nan."
Simi simi suka wuce, dakin Maman su, suka same ta zaune Hoor ta kwanta a
cinyarta suna karatu, Hoor ta dage sai gyara mata take.
"Innarmu! Kuna hira ne da Hoor?"

Kallon su tayi sannan ta maida kan Hoor din, tana kaunar yarinyar kwatankwacin
yadda take kaunar Y'aya'nta, duk da bata san Uwar Yar ba, amma taji a ranta tana
kaunarta har cikin jinin jikin ta, shi yasa ta kira Rufaidah ta gaya mata abinda
yake damunta, tunda tun shekara biyu da suka wuce suke tattaunawa akan lallai ya
dawo da Uwar yarinyar, amma yaki magana haka ta saka Muh'd Aasim yayi mishi magana
yace karsu dame shi akan Anum.

Duk sai da ta tara yaran mata da maza, amma duk suka ce wallahi tsoron
shi suke ji. kuma tasan Rahama da Hajara basu gari tunda Ita Rufaidah a tahwa take
aure, ita kuma Hajara a maradi, amma duk ta saka Rufaidah tayi musu magana.

Toh Allah ya taimaka sanadin abinda yarinyar ta faɗa yaji tsoron kar tsautsayi
ya fadawa rayuwar shi ko ta Yarinyar bata gana da Mahaifiyar ta ba.

Bayan ya bar yarinyar a gurin Innarmu, ya nufi gidan shi. Yana shiga ana
kiran magarib, dan haka yana shiga yayi alola ya wuce masalaci, bai koma ba. Sai da
akayi isha, yana sane yau girkin Sharifa ne, dan haka ya wuce dakin shi ya sauya
kaya tare da nufar cikin gidan su, ya shiga dakin Hajiya Hakamah, ya amshi tuwon
alkama miyar kuka, da manshanu. Har ya fara cin abincin sai ga wata Yar uwarshi ce,
itama kakarta Kanwar Dijimah ce, dan haka suka gaisa dake bazawara ce, bata jima da
mutuwar Auren ta ba, tasan halin shi idan zai ci abinci Kowa barin gurin yake ita
kuma tazo ta zauna ta saka shi a gaba tana mishi kallon kurilla.

Fitowar Hakamah tayi mata magana tare da cewa.
"Zuwairiyya! Ya zaki saka mutum a gaba haka, dalla tashi bana son shirme, ko kanen
shi basa mishi wannan haukar"

Mik'ewa tayi ta barshi a gurin.
"Asad kayi hakuri!"
"Hmm!" Yace mata, yana gamawa ya mike tare da nufar shashin Gajeh suka gaisa,
kallon shi tayi tare da cewa.
"Yau banga Amaryan Alhaji ba"
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Yau a gidan Innarmu take!"

Gyda kai tayi sannan tace mishi.
"Ayya yarinyar tana girma tana wayo, jiya ina jin su sa Amir yana ce mata wai
Mamanta ta mutu shi yasa bata da mama,.ai kuwa yar nima tana tashi tayi ta marin
shi nace yau naga zafin rai a jikin Yar nan duk girman shi sai gashi da kuka.
Dakyar na kashe fadar ma."

Murmushi yayi sannan ya mike tare da mata sallama, ya nufi gidan kakan shi,
ya zauna suka tab'a hira Dijimah ta kawo mishi fura kadan yasha sannan ya musu sai
da safe,.bai wuce gidan shi ba, ya nufi shashin Mahaifin su, ya zauna a inda yake
hutawa suka gaisa. Sannan ya gyara zama ya fara labarta mishi yadda suka yi akan
zai kai Hoor ganin Mahaifiyarta.

"Asadullah! Ni a nawa nazarin me zai hana ka dawo da ita, ba mamaki kaga Allah
ya kuma kara maka wani Haihuwar." Shiru yayi yana kallon yadda me shayi yayi.
"Nasan da zafi yanayin da kashiga, duk da ban san meye ya hadaku ba,. amma indai
horo ne na tsawon shekaru uku zuwa huɗu ta horu, kuma ka duba kodan Albarkacin
yarinyar nan ai tayi kome."

D'ago kai yayi tare da kallon Abban shi, sannan yace.
"Shi kenan Abba!"
"Allah yayi maka albarka. Ya kuma baka Zuri'ar dayyiba, ya Albarkaci rayuwar su."

"Amin Ya Allah Nagode sosai Abba!"

Sannan yayi mishi sai da safe ya bar d'akin, tunda ya fito ya nufi gidan shi,
ko ta kansu bai bi ba, amma tabbas dole ya rama abinda Anum tayi mishi, da wannan
ya rage kayan jikin shi, sannan ya kwanta. Har ya fara aiki a laptop din shi, ya
tashi ya kulle d'akin, yana rufewa kuwa yaji Alamar Sharifa. Tayi bugun duniyar nan
yaki buɗewa.

Karshe ya kashe wayoyin shi, tare da kwanciya, nazarin abinda kowa yake cewa
akan ya dawo da Anum yake, toh idan sun kai auren shi kotu fa aka raba? Kai ba zai
yiwu ba. Haka yayi ta tufka yana warware, har barci yayi gaba dashi.

Da asuba bayan sun fito masalaci, suna zama suyi karatun safe da Sheikh a
masalaci, nan ya shiga kawo mishi karar shi da Sharifah tayi. Kallon liman yayi
sannan yace mishi.
"Zan sako maka ita sai ka nima mata wani mijin!"
Ya faɗa yana shan mur, karshe kamar zasu haura sama, su rikito. Kafin suka dawo
suka shirya zunzurutun yaji haushi yana tashi daga masalacin ya shirya kayan shi ko
sallama bai yi ba, yayi tafiyar shi bayan ya kira Ahmadou (ila) sai bayan tafiyar
shi ne ya bada sako a kaiwa matan shi yayi tafiya, aiko sunji haushin abinda yayi
musu.

Suka ce zasu jira suga ya dawo da Matar shin da yake musu Iskanci akan ta.

**
Bauchi.
"Ke da za a taimakawa, shine kike wani gadara da bude hanci, wani irin Iskanci ne
baki buga ba a cikin Unguwar nan, har labarin cikin da kuka zubda naji, dan haka mu
taru mu rufawa juna asiri, mu more rayuwar babu shegen da zai san muna irin wannan
shagalin, gaki mace daga sama har kasa, bayan ne ko gaban masha Allah, kiyi tunani
me kyau, akan."

"HM! Wallahi baka da imani ko tausayin rayuwarka baka ji, nice zanyi zina da
aurena? Kai kasan ni ba sa'ar ka bace, amma kasan me Insha Allah, Ubangiji zai kawo
min wanda zai bi min hakkina, idan nayi magana ma cewa zaka yi sharri nayi maka.
Allah ya ganar da kai"

Ta fadi haka tare da barin Office din, tun daga lokacin ya takura min, kullum sai
na samu ya rigani saka hannu ko yace naje Office

Please Login or Register in order to submit comment