You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Anum ban daki tayi wanka, tana fitowa suka
bata wani kaya.

Niman Alhajin suka yi, akan zasu kai Anum Asibiti, yaki zuwa. Dole suka kira
Binta. Tazo har gidan ta saka mata ruwa, suka duba akwai sauran kayan abincin da
aka dawo da ita. Yana nan.

Girki Umma tayi mata faten wake, da ta tura Rulwanu ya sayo mata ganyen
alayahu a kasuwar Wuntin dada, suna cikin haka Aunty Binta tazo ta saka mata ruwa
da allurai, da Magani,
"Maman Sadeeq, gaskiya auren Anum da wannan mutumin akwai matsala, gaskiya ba zan
iya ba."
"Ni kam a bar min aurena, ina son zama da shi. Lokacin da nace bana son shi ai cewa
kika yi zaki tsine min yanzun kuma kice zaki raba bar min aurena ina son shi haka.
Duk wani rayuwar aure juriya da hakuri yake tafiyar dashi, Ibada da niman dacewar
Ubangiji yake zaunar dashi lafiya, ba za a kuma kashe min aure ba."

Ta faɗa a sanyayye, tare da lumshe idanunta, aikuwa ran Maman Aminu ya b'aci,
wallahi sai ta kashe auren ko da kuwa zata rasa nata auren ne. Haka suka zauna har
ruwan ya kare, sai da zasu tafi Alhaji yazo, kallon juna suka yi da Umma, kwarjinin
da tayi mishi yasa shi sunkuyar da kai.

"Sannun ku! Ayya wallahi ina ta sauri naje ganawa da Me girma gwamna n.."
cikin jin haushi Maman Aminu ta kalle shi zata yi magana, Umma ta rike mata hannu.
"Toh Alhaji, Ga Anum can mun gama abinda zamu yi, idan Allah ya kai mu ko zuwa dare
zamu zo mu duba lafiyar ta, da abin cikin ta."
"Ciki ne da ita?" Ya tambaye su a rikice.
"Eh Muna fatan haka!" Inji Aunty Binta,
Shiru yayi sannan yayi fatan Alkhairi, ya raka su har suka fita, dawowa yayi wani
irin bakin ciki yake ji.
Yana shigowa ya same ta akan abin sallah, tana addu'a. Dauke kai yayi tare da cewa.
"Ashe ciki ne dake?"
"Nima haka naji!"
"TOH gaskiya a zubda!"
"Ba zan iya wannan kasadar ba"
"Lokacin da kika zubda wancan me yasa baki gane kasada ce"
"Saboda ban ji a raina na haifi dan gaba da fatiha ba,"
" Ni kikewa rashin mutunci?" Shiru tayi bata kuma kula shi ba, haka ya fice, tun
daga ranar ya tsiro da rigima, tayi magana yace zai hadata da yaran shi, bata kula
shi.

Sai dai wani barazanar da take fuskanta da yaran shi haka kawa zasu shigo mata
suyi ta mata wani abu kamar marasa hankali, duk abinda suka gani naci saukewa suke
su fita dashi su cinye, Nan ma bata kyale su ba. Ta cigaba da addu'a, tana saka
turaren ta,
Idan ta saka da gudu suke fita, kawai sai taji tana shakku akan haka, dan hakan ta
fita gurin yadiko yaran suna ganinta suka taso mata, cikin wani irin tsoro take
kallon su, kamar ta zura d'akinta. Daka musu tsawa Yadiko tayi tare da kallon ta,
ta dauke kanta.
"Nace ba"
D'aga mata hannu tayi, sannan tace mata.
"Ba zaki samu abun da kike son sani ba, ku matan waje kuna rayuwa ce ta wata irin
hanya mara bullewa, kuna ganin mazan da suke shiga manyan mota kamar sune yan Gatan
Allah, idan da zaka bincika dukiyar su bata halal bace, amma burinku ku aure shi ko
ba haka ba?

Idan ya sauke wasu matan daga kauye, ke fa a cikin gari ya ganki ya auroki.
Toh gashi an wayi gari iyayenki suke ciyar dake, meye amfanin bad'i ba rai? Ka
sayar da Akuyarka ta dawo tana ci maka danga, abinda naso sanar dake kenan ranar,
baki dace da nan gidan ba, Allah yana sonki da rahama ne yasanya iyayen ki sukar
tsaye akanki, bai kai da ya miki kome ba."

Daga haka ta juya abin ta, shiru nayi ina kallon bayanta, ina jin tashin
hankali a kasan raina, ina na kawo kaina? A hankali ya juya tare da komawa dakina,
idan na fahimci yanayin gidan nan, akwai wani abun da Alhaji yake aikatawa. Amma
Allah ya fishi. Tunda na shiga naji sabon zazzabi ya rufe ni.

Karfe tara na dare, muna zaune a falo, tsautsayi ya sani kunna BATV, na samu
sun saka labarai. Ina zaune ina kallo har suka gama, wani horror fim suka saka. Wai
The rings.

Tashi nayi na shiga ban daki nayi alola, sanan na gabatar da sallar
isha tare da shafa'i da witiri. Ina fitowa falo na sami Alhaji yana zaune. Zama ina
nayi ina kallon fim din.

A hankali aka fara yadda yaron yake ganin fatalwar, Film din baki
dayan shi abin tsoro ne, dan haka da naga zan razana zuciyata, na tashi tare da
mishi sai da safe, ina shiga dakina. Nayi sabon alola. Sannan ta kwanta.

Ko minti biyar banyi ba barci ya dauke ni, ba zan iya cewa ido biyu nake
ko mafarki nake, karar tvn naji hakan yasa na mike domin kashewa ina mamakin me
yasa Alhaji bai kashe tvn ba.
Ina fita falon, naji Ni cikin ruwa, dubawa nayi naga ashe daga tvn jini yake zuba,
daga wani rijiyar jini, ga wannan yar fatalwar cikin jini tana mika min hannu.
A firgice ta fara karanto ayatul kursiyu, kafin na farka. Addu'ar
wanda yayi mugun mafarki.
Wanda Ya yi Mafarki mara kyau.
‫َأ‬
‫ ُعوُذ ِباللِه ِمَن الَّشْيَطاِن الَّرِجيِم َثَالٍث َمَّراٍت‬.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem (3)
Wanda ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi wadannan abubuwan:-
-Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.
-Ya nemi tsarin Allah daga shaidan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.
-Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.
-Ya juya daga kwibin da ya kasance yana kwance a kansa.
Sannan na kara da addu'ar farkawa da nayi a firgice.

Addu'ar wanda ya Razana a cikin barci, Da wanda Ya Kasa Barci.

‫ َوَشِّر ِعَباِدِه َوِمْن َهَمَزاِت الَّشَياِطيِن َوَأْن َيْحُضُروَن‬،‫َأُعوُذ ِبَكِلَماِت الَّلِه الَّتاَّماِت ِمْن َغَضِبِه َوِعَقاِبِه‬.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin
hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin
bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin al'amurana).
Kullewa mara na, yayi na tashi zuwa ban daki nayi tsarki da Alola, nazo na fara
nafilla, ina cikin sallar naji abu na sauka daga tsakanin kafana, sallame sallar
nayi na nufi ban daki, na tsuguna a kasa, hawaye na zuba daga idanuna.

Ina jin yadda gudan jini ta, yake zuba. Kuka take kamar wacce ta rasa
uwarta da Ubanta. Tun karfe sha biyu na dare, take wannan yanayin, bata samu sauƙin
al'amarin cikin ba, sai karfe hudu na asuba, sannan taji saukar shi, sannan ta
shiga rarrafa zuwa d'akinta, ta haɗa ruwan zafi, a hankali take sauke ajiyar
zuciya, jin kanta take kamar ana mata ihu akai. Dan haka ta shiga karanto addu'o'in
niman tsari.


‫َأ‬
‫ اْلَعِزيُز اْلَغَّفاُر‬،‫ َرُّب الَّسَمَواِت َوْال ْرِض َوَما َبْيَنُهَما‬،‫َال ِإَلَه ِإَّال اللُه الَواِحُد الَقَّهاُر‬.
La ilaha illal-lahul-wahidul-qahhar, rabbus-samawati wama baynahuma, al'azeezul-
ghaffar".

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, makadaici, marinjaye, ubangijin sammai da
kasa da abin da ke tsakaninsu, mabuwayi, mai yawan gafara.

Da sauki ta samu, sakamakon kuwwar da kaita yake. A hankali ta janyo ruwan
zafin ta shiga da shi ban dakin, tayi wanka da shi. Ta wanke gidan jininta, ta nade
shi da tsuma, sannan ta wanken jinin d'akinta, tare da abin sallah.

Tunda ta samun ta gyara jikinta ta fito, rub da ciki tayi ta kwanta.

A hankali barci yayi gaba da ita, me cike da mugayen mafarkai. Sakamakon
ganin Alhaji yana Binta da wuka, wannan karon ma macijin nan sai da ya fado kanta
ya makale, akan cikinta, kanshi a kirjin ta. Haka ta farka daga barci.

Ganin Alhaji tai a kanta, addu'a tayi tare da, wanda ya ji tsoron wasu
mutane zai fada:

‫َالَّلُهَّم اْكِفِنيِهْم ِبَما ِشْئَت‬.
Allahummak finihim bima shi'ita.
Ya Allah! Ka isar mini su da abin da Ka so.

Birkicewa yayi, tare da kallon ta. Yana ƙoƙarin boye abinda yake hannun shi.
"Meke damun ki?".
Dakyar ya bude baki tace mishi,
"Bari nayi!"
"A garin sakarcin ki, kika zubda shi? Don Allah yanzun me zan gayawa iyayenki, ko
kina son ki koma gurin mijinki nan ne kika zubda min cikina?"

Kwanciya ta gyara,tayi sannan ta cigaba da addu'a, har barcin ya dauke ta,
murmushi yayi sannan ya fice daga d'akin.

A hankali ta farka daga barcin tayi addu'o'in farkawa daga barci, sannan ta
lallabatawa tayi cikin nutsawa ta kwashi abin miya, da soyayyen nama, taje tayi dan
farfesun wanda yaji attarubu, tana zaune a gurin jiri na diban shi.

** Koda ta gama miyar, taliya ta dafa, tare da juye abincin zuwa
d'akinta, tayi wanka tare da gyara Jikinta, sannan ta ci abinci, ta shiga Niman
maganin ta na wancan barin.
Shi tasha, sannan ta kuma kwanciya. Karfe biyar na yamma Umma suka kuma
zuwa, anan take gaya musu cikin ya ficce.

Shiru Umma tayi sanan tace Mata.
"Babu kome, Allah ya baki wani me amfani."

Ta mata nasiha sosai, sannan suka bar gidan, washi gari sai ga
Rulwanu da katon bokitin anyi miyar kafar saniya, da bindin shi aka kawo mata, sai
kamu da kayan yaji, Dakyar Maman Aminu ta bada dubu uku aka kawo mata, malam kuma
ya sake hada mata kayan gara.

Sannan Suka zo da Maman Aminu, ta kawo mata har da Ganyen auduga aka
tafasa mata, ta sha madara, kafin wani lokaci ta daina jin jiri. Sun mata hira
kafin suka bar gidan.


Tukun nan....Inji me mugun labari🤔
#Mai_Dambu
[2/11, 9:05 AM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA UKU

Bata sake zani ba, dan zaman ba wani dadi bane, take ji daga kan wannan b'arin bata
kuma samun ciki ba, sai bayan wata biyu cif ya samu ciki.

Dan haka tayi ta b'oyewa, duk da ya fahimci tana da ciki, sai ya zuba mata ido yaga
iya gudun ruwan ta, abu kamar wasa cikin yana zaune kyam.

Wani rikici suka yi, ta gudu gida Malam ya dawo da ita da kan shi, suka yi
magana sosai. Bayan Nan Muttaka da Abdul Hakim, suka je har gurin aikin shi suka
mishi rashin mutunci, kamar zasu sake shi, Muttaka kam ma sai da ya mari Alhaji.

....Abinda ya fusata shi shi kenan ya dawo gida, tare da saka yaran shi, suka rufe
Anum da duka, Suna cikin wannan yanayin Allah ya wurgo safiya da Hafsat, sune suka
kira yan uwan su, suka gaya musu. Ko minti talatin basu yi ba, suka iso aka kaita
asibitin.

Dakyar aka tsayar da cikin jikinta, shi kuma Alhaji aka kama shi, domin Yadiko ta
gayawa yan sanda abinda ya faru.
Koda aka kai shi Office din yan sanda, nuna musu yayi yana da kuɗi aka juya
case din tare da tuhumar Anum, tana kawo mishi maza gida, kuma ba kowa bane sai
MAUDE.

Lokacin da aka zo kama maude bai d'aga hankalin shi ba, bin su
yayi.tunda ya shiga office din D.P.O, wani tudu wani ganganre aka juya case da
cewa. Alhaji yana tsafi da cikin Anum, abubuwan da yake aikatawa da wulakancin da
yake mata, karshe dama yana koran matan shi da ciki ne, sai gashi ita kuma bokan
shi ya ce ya barta ta samu cikin yana bukatar shi domin Arzikin shi yana jikin
cikin ne, shi yasa tana samun cikin yake sanin yadda yake zubda shi.

Sannan idan tayi b'arin baya barinta ta samu hutu yake koma mata, wanda haka
cin zarafi ne, gashi baya ciyar da ita,abubuwan da ake yi ta lissafowa basu fadi.

Dan haka suka tura su kotu. Tun daga nan maude bai kuma bin case din ba, sai
ranar da za a zauna ne, aka nuna musu iyakar su,kuma ace babu saki sai ma ta bada
miliyan daya da rabi, kudin wanke muni.

Maude da kanshi ya kuma niman Alkalin a sirrince, bayan sun gama magana, aka
kuma d'aga kara.

Ranar da za a kuma komawa, cikin shirin shi na buzaye ya isa kotun, inda ka
gabatar da wani case kafin nasu Anum, cikin takaici da bakin ciki, Alhaji yayi ta
ihu yana zagin maude da Anum sannan alkali ya raba auren. Tare da zaman gidan kaso
ko zab'in biyan tara miliyan uku da wani abu, sakamakon yayi yunkurin kashe mace da
ciki.

Wannan shine dalilin da ya kashe auren Anum da wancan jahiliin.

A can asibitin kuwa, Anum sauki ya samu sosai domin ba zaka ce tayi jinya ba, ta
mai da jikinta kamar ba ita ba, sabida kulawar da take samu a gurin Umma.
Idan ta Maman Aminu ce, bata ki a zubda cikin ba, amma Malam ya hana kowa, dan haka
da aka sallame ta, suka dawo gida, nan suka shiga lallabata tare da ririta cikin
jikinta, ana bata kulawa.

Cikin da kamar jira yake, a san da zaman shi, Alhaji ya kawo kudin baki daya,
Maude ya bawa Malam shawara ya sayawa Anum fili wata rana zata amfana dashi.

*** A gurin kwashe kayan ta, ne suka shiga tsoro wasu mugayen abubuwan da
aka saka a cikin dakin, basu tab'a ba,suka tattara aka kawo wa malam, shi kuma ya
duba ya kona tass, sannan ya bada addu'o'in aka kawo mata tana sha tare da yin
sallah dare.

A hankali rayuwa take juya musu, tare da abubuwan ban mamaki, a yanzun Anum
ta shiga nutsuwarta babu ita babu su Xoxo, gashi Malam yana ƙoƙarin inganta mata
lafiyarta, da abinda zata ci, Maude ma kullum yana bashi ƙoƙarin, koda zata fara
awo. A kofar ram tayi awonta.

Rulwanu yake kawo ta a mashin din Maude, bayan ya ajiye ta, tana gama abinda zata
yi zata kira shi.

Wani irin jituwa da mutunta juna, ya kuma samun mazauni a zuciyar su. Idan ka
gansu da juna zaka fahimci cikin jikinta shi yayi musu iyaka da juna, dan haka take
ala ala ta haihu, domin su koma rayuwar su ta baya.

**
Bayan wata uku.

Indomie da kwai ta cinye tare da sake katon gatsa, sannan ta jingina da bango,
tana lumshe.
"Umma na nagaji wallahi ko ina na na jikina ciwo yake!"

"Toh ai sai ki kwanta kiyi barci tunda barci kike ji, umma bata rufe baki ba,
ta dungura a gurin, tayi barci ya har da munshari,

Tunda ta dawo bata wasa da ibada, kuma bata tab'a barin sallah ya wuce ta, ga
shi Umma ta bata addu'o'in sosai tana yawan karantawa tana sha, musamman ba kambun
baka da idanu, haka take kullum, malam yana mara Rubutu, ga wanda ake kawowa daga
shagon Maude,

Cikinta yana shiga wata bakwai, kawai maude idan ya fita yaga kayan yara wanda mace
da namiji zasu iya sakawa yake kwasowa. Duk wanda ya gani sai yayi maganar kayan.

Dan haka ya tattara soyayyar duniyar manya daurawa cikin Anum,matar shi kuwa
fada suke har da yaji akan zai dawo da anum murmusa mata yake kawai tare da manna
mata Hauka, Kuma ta zata da da gaske yake shi yasa take birninta, bai tab'a damuwa
ba.

--idan ka kalli Anum sai ta baka dariya cikin ya sata tayi muni, tare da
zama rushsshiya hancinta yayi wani katon, cikin ya buda ta sosai kamar ba ita, ba,.
Shi yasa wani zuwan da Malam yayi Badara, yayi mata sayayya kayan kamshi da Umma
ta bashi aikan,
Aikuwa ya tawo mata da uban lodin kaya,kamar wanda bai san ciwon kudin ba, tun
haka bai damun Hafsat da take zuwa lokaci zuwa lokaci har ya fara samunta.
Haka maude da daurawa kai dawainiyya,ya shiga mata sayayya kayan baby, duk
lokacin da ya shiga kasuwa sayan kayan shagon shi yana ganin abinda yayi mishi zai
sayo mata,

Tun Umma bata magana har ta kare tayi mishi magana,sai dai abin da ya gaya
mata ya kashe mata jiki ainun kasa magana tayi tare da cewa.
"Toh mun gode, Allah yasa ka da alkhairi!"

Haka ta koma cikin gidan tana jinjina qarfin hakurin shi tare da yarda da
ƙaddara. Abinda yace mata ya tsaya mata a rai. Da tace mishi.
"Malam Maude, kana hidima da yawa, don Allah ko zaka hakura da wani abun ne?"

Murmushi yayi sannan yace mata.
" Ba Anum nakewa hidima ba, abinda zata haifa nakewa hidima, rabon su ya hanani
zama da ita, ashe kuwa idan na yarda da ƙaddara toh yaran da zata haifa tankar nawa
ne, ni ki dauke ni a matsayin d'an ku, karku duke Ni a matsayin surikinku, kuma da
ace ban rabu da ita ba,. ƙarshe mutuwa zan yi sabida rabo, kuma yarda da ƙaddara
wajibi ne ga musulmin kwarai."

Wannan maganar ya tsaya mata a rai, sosai. har take gayawa Malam yadda suka yi
dashi. Murmushi yayi sannan yace mata.
"Dan babban gida ne, ya fito daga gidan da aka san darajar mutane da kan shi ne!"

---
Bayan rabuwar Alhaji da Anum a kotu, kamar zai yi hauka. Dan Yadiko ma ta bar
gidan, yaran ta sun zo sun dauketa. Barirah ma ta gudu garin su. Sai gidan ya zama
wani irin gida, yana shiga yaran shi zasu nime kamar zasu kashe shi. Karshe guduwa
yayi ya bar gidan, ya koma gidan gonar shi ya zauna.

** A gidan Maude ma, Hajjo masifar take kamar zata cinye kanta,
sakamakon yadda Maude yake b'arnan kudin shi akan Anum, idan tayi mishi korafi yace
bata da hakuri, ko ta cika kishi.

Anum da take da ciki me zanyi mata ko me zata mishi. Wannan dalilin yasa take
hakuri, dan ráshin kunya har gida tazo tayiwa Anum kashedi ta rabu mata da miji,
murmushi Anum tayi sannan tace mata.
"Idan ina son na kasance da shi, wallahi sai kin rabu dashi, ko yayi pushing dinki
out, dan haka karki sake na haihu, domin me guri yazo, mai taburma ya nad'e."

Ta gaya mata haka, sannan ta cigaba da abinda take yi, wai ita tazo gaida Anum ne
take gaya mata magana, kuma Alhamdulillahi taji amsa daidai da wanda bata zata ba.

---
"Umma! Don Allah kice Rulwanu ya bar kallona." Ta faɗa da karfi, tare da tura baƙi.

"Rulwanu tashi a gabanta" inji Malam.
Tsaki Maman Aminu tayi, babu wanda yabi ta kan tsakinta.

"Wallahi Umma yarinyar nan ta koma kamar matan sayawa!" Ya faɗa yana
Dariya.
"Umma kinji shi ko, wai kice basaya"
"Shi kuma sai mu kirashi da bahangashe. Ko shi da kare mutu kara ba!" Inji Umma.
"Malam kana jin Umma ko? Wai ni ne hangas!"
"Toh Rulwanu, kai kace mata Basaya, kai kuma bahangashe" inji Malam,
Hiransu gwanin ban sha'awa, har malam ya fita aiki. ya rage daga Umma sai Anum da
Rulwanu, wanda yake mata tsiya.
"Umma nikam!"
"Ya dai Anum? Ke kam me?"
"Wallahi abin nan ne yake tsaya min a cikin Kinga yadda yayi ranga ranga!"
Ta kuwa bude cikin, tana kallon Umma.
"Yaushe ya fara miki haka?"
Shiru tayi na wani mintinan tana son tuno lokacin da ta fara jin haka.
"Umma ba zance miki ga lokacin ba, amma bana jin dadin yadda yake min, sai naji na
gaji. Sanan nayi ta hakki"
Kura mata ido Umma tayi, sannan ta kira Maman Aminu,
"Toh Ni da aka kira ni wata uwar zan mata?"
"Babu abinda zaki min, kije abinki, kudi yana iya fin d'a! Miji! Da wasu abubuwan,
Amma soyayyar gaskiya bata tab'a karewa, ban san me yasa Ubangiji ya sani fitowa ta
jikinki ba."

Aikuwa ta rufe ta da duka, sai da Umma ta shiga tsakanin su.
"Wannan wani irin shirme ne? Zaki daki yarinya da ciki. Meye Matsalarki da rayuwa
Anum, ai gaskiya ta faɗa, ince nan kike kuna baki son ta, da abin cikin ta. Har
kina cewa ta zubda cikin. Tsakani da Allah, kike nunawa yan uwanta sun fita daraja
a gurin ki, Maman Aminu kowa rai ya amfani yafi ga me shi. Anum Yarki ce, amma
yadda kika juya mata baya bata cancanci haka daga gare ki ba."

Juyawa Umma tayi ga Anum da take kuka wiwi,
"Ke kin san darajar Uwa? Toh karki yarda ki sab'a mata, karki yarda ki rabuwa da
ita cikin bakin ciki da damuwa, Uwa ba abar wasa bace!"

Cikin kuka tace.
"Umma me take so na mata wanda ban yi ba, Umma nayi mata biyayya, ta rabani da
mutumin kirki, ta amshi kudi a hannun Alhaji Mudi, duk lokacin da muka sami saba'ni
sai ya gaya min, cewa Uwata makwadaiciya ce. Me take so? Na zubda cikin na kuma
fadawa zawarci me hatsari? Sakacinta ya sani na fada sharrin kawaye da Alhji mudi,
wallahi Maman Mu, ki tanaji amsar da zaki bawa Ubangiji, domin ni dake zamu tsaya a
gaban shi yayi mana shara'a. Kuma daga yau mijin da yayi min zan aura, inda kika ga
Ban Auri Maude ba, wallahi tsananin rabo ne ya kuma shiga tsakanina dashi."

Daga haka ya yinkura da karfi, zata mike Aikuwa bayanta ya amsa, komawa tayi ta
zauna, kwalla na zuba mata, kallon Umma tayi sannan tace mata.
"Umma bayana kamar zai b'alle!"
Umma kan kasa magana tayi, domin abin ya fara damunta. Dan haka ta taimakawa
Anum zuwa d'akinta, Maman Aminu kuwa bakin ciki kamar ya kasheta, domin tana ganin
Anum tana shirin fin karfinta.

Duk da cikin bai cika watan Haihuwar shi ba, amma Umma ta Fahimci irin
silent labour take yi, dan haka basu B'ata lokaci ba aka wuce da ita asibitin. Suna
zuwa kofar ram aka tura su Babban Asibitin.

Suna zuwa, aka ce musu aiki ne. Dan haka Umma ta kira Abubakar, shi kuma ya
gayawa Yan uwan shi, jinin da za a saka mata, aka rasa wanda yayi dai-dai da nata,
dole aka shiga nima. Na malam kuma yana fama da rashin sinadarin glucose. Dan haka
suka ce a'a. Na Rulwanu aka diba shine yayi daidai da nata, yayi ta fushi tare da
cewa..ai idan aka gama mata tayi mishi tijara sai ta biya shi jinin shi.
#Mai_Dambu
[2/11, 8:16 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA HUƊU.

_Wannan Shafin na kune! Usainah B Abubakar, Mrs Abubakar da Maman Shahid_

Cikin ikon Allah da kudirar shi, aka cire mata katon yaron ta namiji dashi, amma
sun kai shi shsshin kula da jarirai. Haka Yan uwanta suka rufa akanta, babu wanda
ya damu da jaririn, Umma ma Mantawa tayi dashi.

Domin numfashin ta, yana sarkewa, da zaran tayi kamar zata farka sai ya kuma
sarkewa, hankalin yan uwanta yayi mugun tashi, ban da Hafsat wacce Maman Aminu ta
gaya mata, abinda Anum tayi mata, ai

Please Login or Register in order to submit comment