You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kashe
min Uwa ce." Aka suka fita da Beauty da ta kasa magana, a hankali ta koma kan
Adama, ta kalle ta, tare da kallon likitan.
"Da fatan bata mutu ba?" Ta tambaya cikin kuka,
"Tana raye bata mutu ba, amma kuma zai yi wuya ta tashi domin gefenta ya shanye."

Wani ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sake kuka, tana kallon uwar, a
ranta tana fadin..
*Na gama da ku, saura wancan yar iskar na saka a lalata min fuskarta*

***
Tunda suka koma gida bata iya fahimtar kome ba, asalima d'akin ta koma ta zauna
shiru. Cikin tsananin zafin abinda Hafsat tayi mata.
"Shin ko tana kallona a matsayin mazinaciya ne? Tunda ban taba tambayar wani ya
bani wani abu ba? Kai haba dai! Toh kallon me take min? Da zata min Sharri, toh
meye nayi mata?" Ga baki daya ta gama takura kanta da tunani har lokacin tafiyar
Aunty Binta aiki yayi.

Wajen karfe shida na yamma, su Badi'ah da fa'iza, gabaki daya sun gama
kaguwa suji yadda zata kaya tsakanin me shayi da Anum, malam da Maman Aminu. Ana
sallar isha. Sai gasu duuuu. Kallon su tayi duk da bata cikin nutsuwa gyara zama
tayi sanan tace musu.
"Yau kunzo da wuri, bari muga ko zan iya baku labarin kafin nan da sha biyu, dan
gaskiya zuciyata babu dad'i."

-----
-Back to story-
"Wallahi ba zata auri Me shayi ba, mara asali da dangi sannan me yaci me ya bata
taci,"
"Hauwa! Don Allah ki bari ya tafi sai muyi maganar Arziki!"

"Eh lallai kan maganar Arziki, Mariyah na jima ina kallonki, na jima da fahimtar
baki kaunar Anum, duk yarana a wulakance aka aurar dasu, baki wato sun huta nawa
kuma su kare a galgalance,, ga sakarya sauna sha-sha-sha me kayan ashsha, toh
wallahi baki isa ba, baku isa ba, yarinya da nake burin ta auri maitamakin gwamna
ko d'an Gwamna sai a ta kare da wani me shayi, dan cira."

"Malam Maude! Tashi ka tafi zan sami shugaban ku nan, zan"
"Baka isa ba!" Inji Maman Aminu, duk yadda malam yaso dauke kanshi sai da ta
tinzira shi ya mare ta, a gaban Maude sosai abin ya d'aga hankalin Umma, take ta
sallami Maude, sannan ta kalli Malam.
" A gaban mijin da zai auri Yarka kuke abin kunya?"
"Anamimiya munafuka,, Insha Allah sai Kinga abinda kika mana akan jikokinki"
Murmushi Umma tayi sannan ta dauke kanta, tare da d'aga Anum da take zare idanu.
"Sake min Y'ata, algunguma. Allah ya isa tsakanina da ke, kuma in Allah ya yarda ba
zaki tab'a ganin dai dai ba."

Idan kuka ga yadda umma take murmushi, sai ka rantse da Allah maganar Maman
Aminu baya mata ciwo.
Mik'ewa malam yayi zai shiga dakin shi yace.
"Mariyah na saki Hauwa'u! Ta koma garin su ta bar min Y'ata nayi iko da ita."

"Hhhhh! Burinki ya cika abinda kike muradi ya tabbata, kin jima kina niman hanyar
da malam zai sake ni bai sake ni ba, dake nafi karfin ki, shine kika zauna kika
raba min hankalin mijina, toh sauki kwanta ki mikar da kafarki"

Ina irin ka mannawa mutum hauka, haka Umma ta sata keyar Anum dakin ta, ta
rufe dan malam hana Anum bin Mamanta d'akinta ko ta koma d'akinta. A hankali Anum
ta fashe da kuka.

Duk yadda aka so barci cikin salama, Maman Aminu taki barin su. Karshe a
daren Malam ya kira Aminu ya fitar mishi da ita.
Dakyar da shudin goshi Anum ta iya barci, Umma kan kasa barci tayi tana
sallah, tare da gayawa Allah kukanta akan abinda Maman Aminu tayi mata, wajen karfe
biyu na dare ta fashe da kuka, zunzurutun zagin da Maman Aminu tayi mata sai
lokacin yake dukarta, sai da ta dauki Alqur'ani domin umma tana da ilimin addini da
na boko ba laifi, kuma wani abin burgewa tasan darajar kalaman bakinta. Shi yasa
bata tofa kome ba da Maman Aminu ta gaya mata.
** Banda zuciyarta me kyau ne da safe haka ta tashi Anum tayi musu aiki amma
yarinyan nan taki ko d'aga tsintsiya, da Umma tayi mata magana ta saka mata kuka.
Murmushi tayi ta kama aikin gidanta, har ta gama na karyawa ta daura na rana, tana
kallon Anum ta shirya ta fita daga gidan.

Bakin shagon Maude ta isa, ta shiga mishi b'arnan kunsan ta'asa, toh haka tayi
mishi mutumin nan bai d'aga ido ya kalleta ba, yana zaune yayi Crossing leg din
shi. Har ta gama fasa kwai tass ta ture table din na kayan tea din..
"How Are You da zaka ce zaka aure ni, matsiyaci da kai, wallahi idan baka rabu da
ni ba, sai na saka ka kayi asarar kome naka, ban da rashin hankali irin..."

Wani irin wawan duka aka kaiwa keyarta sai da takifa. Dukarta yake tare da kwallo
da ita, ran shi ya kai makura gurin.
"Kyaleta Rulwanu! Yaranta ke damunta, wata rana ba zata yi ba, aure kuwa tunda
malam ya bani bar dukar min Mata na."

Ai kuwa ta fasa ihu, tana faɗin.
"Rulwanu kaci abu kazan Ubanka shege Azzalumin mutum, Kai kuma bakin algungumi sai
na wulakanta aurenka wallahi sai na lalata maka farin cikin ka."

Asalin rashin mutunci da rashin kunya Anum take musu, sai da Maude yazo ya
dauketa cak dan ya gaji da abin kunyar da take janyowa kanta.... Aure Babu fashi
yar gatar gatan uwa! Wani zai gurji kwaila, Yarinya zaki tafi millions cloudy 😜
*(A gaskiya zan shiga dunkule hannun tunda Na sauko daga sama!😜Karku manta ina
tallar book dina me sunan Daula biyu 200₦ ta bank ko katin mtn)*
#Mai_Dambuje😂
[1/30, 1:46 PM] +227 98 70 95 87: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA ASHIRIN DA D'AYA.

_TEAM Maude kuke 🤨🧗 zan makale fa_

Cikin gidan ya nufa da ita bai direta a ko ina ba sai a tsakar gidan.
"Anum har yanzun ina kaunarki, shi yasa ba zan miki kome ba da b'arnan da kika min.
Allah ya bamu yara kyawawa masu.."

Cak yayi shiru kamar wanda aka hana karasa abinda zai ce, ya kura mata ido.
Zuciyarshi tana tuna mishi wani abu akan karan kanshi.
*_Karka manta waye kai? Sannan shekaru sha shida matan ka basu tab'a koda b'atar
wata ba, adalci ne ka auri yarinya karama ka amfana da kuruciyarta? Kasan baka
Haihuwa, sannan kuma ka nace zaka auri yarinya karama wacce nan gaba zata so
haihuwa itama._*

Tsintar kanshi yayi da juya tare da barin gidan, jikin shi yayi matukar sanyi,
lokacin da ya koma shagon shi ya samu ila da jijjiya suna kwashe kayan sai fada
suke, Rulwanu yana basu hakuri, murmushi yayi sannan ya tasawa Ila abinda yake
damun shi kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Amma ai ba hujja bane kace ba zaka aure ta ba, dan kana da matsala ta rayuwa,
sannan kuma wannan haukar da take babu abinda zai bada sai sakamakon aurenta,
wallahi Yallabai sai ka auri Yarinyar nan, ka nuna mata iya ikonka da karfin ka."
"Toh Allah yasa mu dace." Ya faɗa a sanyayye, yana kallon ta'asar da Anum tayi
mishi.
-- A can gidan Aminu kuwa Mama ta zagi Umma ta tsinewa Umma,.tayi fadar tayi
masifar karshe ta fashe da kuka, Yaran ta baki daya sun taru, suka yi ta bata
hakuri amma bai hanata kuka ba.

Da ciwo ace aurenku a shekaru kusan arba'in da wani abu ka wayi gari ace mijin
da kuka zauna dashi ya sake ka.

... Hafsat da Safiya suka fara zuwa bakin kura, suka sami Anum tana kuka,
Umma ta sakata a gaba tana mata nasiha.
"Rayuwar duniya da kike gani hmm sauki ne da ita, idan ka nemi sauki amma idan kace
zaka ci da zuci ba zaka kai labari ba.

Khadijah duk abinda kika ga ya sami bawa mukaddari ne, duk abinda ya
tsara miki me kyau ne, Ni nasan kina son Maude, amma wasu dalilai naki yasa kina
ganin baki dace da me karamin sana'a.

Anum masu manyan gidaje da manyan motocin nan, basu kai masu kananun
karfi tattalin mace ba, shi me katon gida da katon mota yana ganin su kika biyo,
dan haka yayi miki Alfarmar ki zauna da shi, kuma duk abinda yayi miki haka zaki
hakura dashi ba tare da kin fadawa duniya ba.

Sannan baki da ikon nuna damuwarki akan shi, tunda rana tsaka kika aure shi da
yatsunsa biyar kika same shi, shi kuma wancan shi zai zauna dake ne sabida kinyi
mishi alfarman haka, kuma koda yaushe yana cikin niman hanyar da zai kyautatta
miki,

Zai yi wuya ya cusguna miki da gayya, kullum kokari yake ya saya miki farin
ciki kida kuwa iya abinda yake gare shi kenan.

Idan zaki shekara dari dashi kullum cikin ririta ki yake, sannan kullum
tunanin shi taya zai inganta duniyar ku. Anum mijin mareniya kika samu, yayi wasa
da samun shi akanki, kaf unguwar nan zuba ido aka yi ana jiran malam ya baki wani
mijin ayi mishi dariya saboda an gaya mishi cewa ke ba matar talaka bace.

Kin san saunawa ana tare malam ana ce mishi kar ya nuna halin butulci ga wanda
ya bautawa yar shi? Kin san yawan lokutan da aka bi ana gayawa Aminu magana akan
ki.
"Kanwarku ta zama babban yarinya shi yasa take wulakanta me shayin kofar gidan ku,
koda yake shima yayi karambani, waye ya aike shi auren matar da Sanata zai aura ko
minista." Ire-iren waɗannan kalaman da ake gaya miki, Anum Ni a nawa gani na,
alkhairi ne ya kawo Maude rayuwarki, da babu Alkhairi ba zai nace ya aure ki ba.
Ban san iya abinda zan gaya miki ba. Karki bijirewa mahaifinki, wallahi matukar
kika yi biyayya Allah kaf yan uwa kin sai kin fisu daraja da farin ciki. Kiyi
hakuri ki mishi biyayya. Allah zai baki abinda kika rasa, Anum maude nagartaccen
Mutum ne. Yana da addini, kuma Manzon Allah yace idan mutumin kirki yazo niman
auren dayan ku, kuka hana shi bayan kunsan mutumin kirki ne.

Allah sai ya jarabce ku da damuwa da tashin hankali, kina son jefa Mahaifinki
cikin tashin hankali ne."
"Umma kifa bana son shi ne! Don Allah ki cewa Malam ya hakura da auren
mutuwa zanyi."

Dariya Umma tayi lokacin da su Hafsah suka shigo a ranta so take tayiwa
Umma rashin kunya dan wai ita ta saka malam ya saki uwar su, kallo daya umma tayi
mata take ta shiga hankalinta, kyale su Umma tayi bata kuma mata magana ba, har
suka gama kananun rashin kunyar su, a daki.
Lokacin da suka tafi Anum kasa fitowa tayi dan sun zugata, tayiwa Rashin
kunya, amma ta kasa, ba zata iya ba. Sai tayi ta kuka a dakin. Sosai yadda take
kukan har Umma tana jiyota. A cikin kananun maganar da Hafsat tayi akwai wanda ya
tab'a ran Umma.

"Ko yau malam ya fadi ya mutu kowa yasan uwar mu ce da gidan
nan, dan haka juya mishi hankali da aka yi Allah sai ya saka mata." Wani irin
murmushi take, tare da kallon Anum bayan ta d'aga labulen dakin tana zaune ta cusa
kanta tsakanin cinyoyin ta. Hannunta ta zagaye kafarta dashi. Zama tayi sannan ta
janyota jikinta.
"Kiyi hakuri Umma! Ni ba zan iya miki rashin kirki ba."

Hawayen da take kokarin binne shine ya zuba akan dokin wuyar Anum, innalillahi
wa'inna ilaihi rajioun, zo kuga yadda ta birkice tana kuka tare da rike hannun
Umma.
"Don Allah Karki zubda min hawaye, Umma ki rufa min asiri wallahi zan auri Maude,
UMMA na ki bar kuka. Ba zan kuma ba, don Allah ko daina kuka, Umma daga yau ba zan
kuma kuka ba. Na shiga uku na lalace Umma tana kuka aka ina."

Rungume ta tayi a jikinta, tana shafa bayanta.
"Kince zaki auri Maude ba dole aka miki ba?" Cikin kuka tace.
"Naji zan aure shi ba dole aka min ba."
"Anum idan kika san baki san shi yau Insha Allah zanyiwa malam magana."

"Umma Ni mallakar ki ce, ba zan tsallake bukatar ki ba" shafa kanta tayi,
sannan tace mata.
"Daga yau kar na yarda na kuma jin wani ya zugaki akan Maude!"
Cikin wani irin shashekar kuka tayi ta gyada mata kai tana kukan.
"Wannan kukan yana fada min kamar dole aka miki?"
"A'a Umma!"
Haka ta kuma kara mata da nasiha.
"Duk wanda yayi wa iyayen shi biyayya da ɗa'a Allah ba zai tab'a wulakanta shi ba,
Allah yana girmama al'amarin shi..duk wanda ya sab'awa iyayen shi. Allah yana fushi
da fushin da iyayen shi, kuma sai ya wulankata shi a duniya, ya kuma je lahira.
Anum kin sami mijin da yake kaunarki.

Tunda ya iya baki kyautar shaddar dubu hamsin, meye ba zaki baki ba, Anum maude
ba zai tab'a wulakanta ki ba, wallahi zai girmama al'amarin ki. Anum ki nunawa
duniya cewa, ba lallai me kudi bane yake samun kyakyawar mace ba, talaka irin maude
yayi deserved dinki, sannan ki tuna rayuwar ki da kika yi waye zai iya jure zama
dake ba tare da anyi uwar watsi dake ba. Wata rana zaki nazarci abinda nake son ki
fahimta kuma bana son lokacin kome ya kure miki."

Duk yadda Umma take kokarin mamaye zuciyar Anum tayiwa Mahaifinta
biyayya sai da su Hafsah suka hanata, Yaran Umma kan iyaka tayi musu, tare da
gargad'in kar taji labarin wani ya Kuskura ya ce wani abu akan Anum da Mahaifin su
indai ba zasu bata shawara tayi biyayya ba.

A bangaren Maude yan uwan su yan Nijar da kuma shugaban su, sun zo
sun nima mishi auren Anum, malam ya karb'e su hannu bibbiyu, tare da mutumtaka,
inda suka kawo har da sadakinta, nera dubu saba'in da takwas. Malam kan talatin ya
dauka ya maida musu arba'in da takwas,.yace musu.
"Kowa yasa halin yar da zan baka, idan na amshi wannan kudin haka yana nufin na
rufe ka ne, dan haka idan ta cancanci kari zaka iya bata."

Haka suka dawo da sauran kudin. Bayan an saka ranar nan da wata uku,
sakamakon zai yi yan gyare-gyaren wuraren da zasu zauna.
***
"Anum me kike nufi? Ni zaki tozarta? Ki amince da auren matsiyaci nan sabida
Mariyah!" Kashe wayar tayi tare da fashewa da kuka.

Umma da take bakin kofar, rike da abinci ta shigo dakin a hankali ta fara
bata tana ci, tana kuka.
"Umma wai na gudu zamu tafi Edda!" Ta faɗa tana amsar abincin dan ita kanta ta
manta rabon taci abinci da hannunta, wanka kawai da alola da saka kaya take,, sai
maganin sanyin da Umma take ta bata.

Dan tace ita ba zata bata maganin mata ba, zata dai gyara mata jikinta yadda
zai zauna cikin dumi.

Tana gama bata abinci, ta dauko zunguro, ta saka lalle a cikin shi ta saka
mata.
"Duk wanda zai baki shawaran ki gudu, zai b'ata miki martabar ki ne, kuma zai
lalata miki alaƙar ki da Mahaifinki ne, Malam bai zab'a miki maude dan ya cutar
dake ba, yaga yafi dacewa dake ne."

.tana gama kunsa mata lallen ta fita, wato irin kulawar gargajiya da ake yi
zamanin da Umma takewa Anum, bayan awa biyu. Ta cire mata lallen sannan ta mika
mata dafaffen madara, dama tayuwa malam magana yana kawo mata d'anyen madaran
saniya daga gidan gona, karamin galan din manja. Shi take sakawa a randan kasa,
idan ta diba ta faɗa, sauran kuma tana zuba kayan kamshi kanumfari, tazargaje,
kurku lalle, ta kaiwa Anum ban daki tayi wanka dashi. Idan tafito kuma akwai asalin
dafaffen siga da madaran turare, tana goge mata jikinta,. Tana gamawa zata kwab'a
kwai da nesfe, ta zuba garin kurku a cikin shi, sannan ta goge mata jikin ta dashi,
tas.

Takan so Anum tayi kuka, amma dake tana da taurin kai, sai dai kaga
tana ajiyar zuciya, idan umma taga haka takan ce mata.
"Autar Malam!" Wannan sunan sakata kuka yake tuni zata sake kuka.

Ire-iren waɗannan abubuwan yana matukar damun Umma, dan haka ta sami Malam
ya dawo da Maman Aminu.
"Ki fita ki bani guri bana son damuwa"

"Babu inda zani sai ka gaya min meye nufinka akan Maman Aminu? Kasa duniya
tana zargina akan na rabata da uban Yaran ta, Malam ka rufa min asiri ka dawo da
Maman Aminu, domin wallahi nima ina dab da barin gidan nan!" Ganin yadda take fada
har da kuka yasa shi juya mata baya.

Idan ya cire munannan halayyar maman Aminu mace ce, me matukar biyayya da
sanin darajar aurenta kawai Abu daya yake damunta son kanta da rashin adalci yasa
shi sake ta daya. Kuma yasan idan ya dawo da ita ba zata bar Anum tayi mishi
biyayya ba, zata cigaba da zugata ne. Don haka yayi mirsisi ya dauke kanshi daga
batun komen Maman Aminu.

Ita kuma Umma sai da ya kai karar ta, gurin Usman da Aminu, tare da Aunty
Binta. Saka umma suka yi a gaba suka kallonta kowa dariya yake an rasa wanda zai
mata, magana. Dakyar Usman yace.
"Umma! Idan kika tafi kika bar malam waye zai tsaya mishi? Duk halin da yake ciki
yasan kina tare dashi ne? Don Allah Umma ki duba Alamarin shi karki ce kema zaki
juya mishi baya!"

"Umma! Idan muka yi yaji ke me zaki ce mana, Umma a halin yanzun ina niman shekaru
arba'in, ban tab'a yaji ba sabida Ni din tarbiyyar ki ce, toh yau wacce ta bani
tarbiyya tayi yaji Ni me zanyi gaba, ina budurwa sa'ar Anum, yau gashi kakar ta
zata yi yaji." Inji Aunty Binta,
"Umma kiyi hakuri! Don Allah Ni dai ban san me ya faru ba, amma tabbas nasan ana
b'ata miki rai. Don Allah kiyi hakuri! Insha kome zai"
*_Ba zaku sami na dare ba, Yau weekend ne lokacin iyalina ne da nawa kaina dan haka
karku saka rai zaku sami na dare!_*
#Mai_Dambuje
[1/31, 10:55 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA ASHIRIN DA BIYU

*_Salon d'an magori nake yawan amfani dashi a labaruna shi yasa da yawan mutane
suke ganin kamar ba Nice nake rubutawa ba!😜Ku dunkule hannun✊🏽 toh a haura katanga
😂idan ta rushe daku babu ruwana_*

"Babu kome Al Amin, ya wuce wallahi kawai ya dawo da matar shi, shine gaskiyar
magana..idan kuma bai dawo da ita ba, zan bar mishi gidan shi. Na rantse da Allah
ba zanyi kaffara ba." Daga haka ta wuce dakin ta, ta bar su a falon.

Allah sarki, idan ka ga yadda suke zauna sai sun baka tausayi, domin kuwa
yanayin su ya nuna a tsorace suke da matakin da zata dauka basu san me zasu cewa
Malam ba,dan haka suka nufi unguwar mahaukata akwai yayan Umma a can, a bayan
dutsen unguwar, suka dame shi da maganar, shiru yayi sannan yace musu.
"Akwai abinda ake mata ne? Indai babu toh tabbas zata iya abinda tace, amma kuce
mata inji ni Yahya nace ta zauna a d'akinta idan kuma bata mutuntani ba Allah ya
bata sa'a."

Lokacin da suka dawo aka rasa wanda zai mata magana, sai zare ido suke tare
da kallon juna, kafin Usman yayi kundum balar mata magana.
"Wato kun kai karana? Naji kun kyauta min Allah yayi muku albarka."
Daga haka ta juya ta koma cikin Kitchen tana hada tuwon dare.
"Anum!"
"Me zata muku? Bana son tana shan iska mara dalili ne, kuma nasan zata iya fitowa
kamar gayan borodi ne."

Tashi Aunty Binta tayi tare da shiga dakin ta d'aga labulen dakin.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Jama'a Ku
taimake ni Ya Allah." A rud'e suka shigo dakin tare da sake salati.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel
La'ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minazzalimin" jin Umma, kallon Anum tayi
ta ke kwance dafara yana fitowa daga bakinta. Tace,
"Usman dauko min mangyada a d'akina"
Da sauri ya juya, sai gashi da mangyadan "bude bakinta Binta, juye mata shi!

"Aminu ka nufi waje yanzun ka amso min madaran ruwa!" Kamar zai kifa haka ya
fita, can sai gashi da tin din milk yana zuwa aka juye mata, aikuwa ta fara amai.
"Goge mata jikinta, ku nufi asibiti da ita," da sauri suka nufi da ita waje, kallon
su Maude yayi tare da tambayar su.
"Lafiya?"
"Faduwa tayi ta buge kanta!" Inji Anunty Binta, haka suka sata a motar Usman aka
nufi babban asibiti da ita.

Tunda aka shiga da ita, kasancewar sun san Aunty Binta basu sha wahala ba,
aka fara kokarin mata karin ruwa, tare da tambayar abinda ya faru, wa likitan kawai
suka wa bayani, suka yi shiru.

Duk yadda suka so Anum ta farka ranar, abin yaci tura domin maganin kwarin
da taci yana ƙoƙarin tab'a kayan cikin ta, dan ma umma ta bada taimakon gaggawa.
Haka suka gama kokarin su akanta. Har dare bata farka ba.

---
A gida kuwa, maude ne ya shiga cikin gidan, ya gaida Umma cikin nutsuwa. Sannan
yace mata.
"Ban gamsu da abinda Hajiya Binta tace ba, ko dai akan auren ne?"
"A'a! Ba kai bane! Kawai faduwa tayi kuma."
"Umma, a uwa na dauke ki. Meye akayi da madara? Kenan Khadijah ta zab'i kashe kanta
ne sabida aurena?" Ya faɗa a cikin sanyin murya.
"Kayi hakuri! Da abinda zan gaya maka, ka janye niman auren..."

"Wallahi ko mutuwa Anum take ta dawo, ba zan sauya tsarina ba. Ba zan fasa abinda
na saka kaina ba, Mariyah kisaka a ranki auren anan dan da sati Uku, da yardan
Ubangiji idan anyi ta kashe kanta, ba tasha piya piya sabida auren bane, toh
wallahi idan Anum taki auren nan sai dai na zare ta a cikin yarana!"

Duk yadda aka so taushe shi amma fir malam yaki,asalima kara tunzura shi suke,
dan haka ya hana Umma itama zuwa asibitin, yace zata dawo ta same shi.

Sannan ya umarci Maude da ya fara shiri babu kama hannun yaro,. Bayan fitar Maude
ya dauke kanshi daga Umma da take kallon shi, tana bude bakin ta yace.
"Duk wanda yaga zai iya tsayawa KHADIJAH na yafe mishi ita."

Dan haka ta ja bakinta tayi shiru.
Tunda ta Fahimci ranshi babu dad'i ta kasa sakewa ta koma dakin shi, ta
zauna a d'akinta.
Washi gari.
Da safe sai ga yaran d'akin Maman Aminu, suka saka malam a gaba, da cewa.
"Tunda tace bata son shi! Dole sai shine gashi zamu rasata a karon iska, gaskiya
Baba Malam ka duba Al'amarin Yarinyar nan fa, karta shiga duniya bamu sani ba!"
"Allah ya bada sa'a, wanda bai zo ba ma duniya tana jiran shi balle wanda yazo ya
same ta a cikin idan zata tafi kuyi min magana zan bata guzirin da zata rike a
hannunta."

Shiru suka yi tare da jinjina al'amarin malam, duk borin da suka shirya banza
yayi dasu, ya gama karyawa ya barsu a gidan bai saurare su ba. Bayan tafiyar shi,
Safiya da Hafsat suka yi tawa Umma rashin kunya. Kasa hakuri tayi sannan tace musu.
"Duk wacce ta zage ni sai nasaka Abubakar ya mata shegen duka, kuma naga allon
rashin kunyar ku, wallahi kubi duniya a sannu."

Simi simi suka bar gidan, ransu a b'ace, sam sun manta Alkhairin Umma, gani
suke kamar itace take kuma rura wutan rikicin su, dan haka suka fito da niyyar
warware Maude, kallo daya yayi musu, kawai sai ganin shi suka yi ya cika musu ido,
babu hanyar da zasu mishi diban albarka.



Please Login or Register in order to submit comment