You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tafi ya barni da tambarin kaunar
shi, bayan sunyi sallama dasu Umma, sai lokacin na koma d'akina. Ina murmushin jin
dadi. Duk da banga fara'a akan fuskar shi ba, amma nasan har abada ba zan kuma rasa
shi ba, dan shi RABO NA NE....

*** Tafiyar da zasu yi a kwana ɗaya da Wuni daya, shi yasa suka yi tafiyar
kwana ɗaya rak, domin basu isa garin Damagaran ba sai karfe biyar na safe, bayan
sunyi sallah asuba, ya shiga cikin gidan shi. Da A'isha ya fara cikin karo. Karb'an
jakar shi tayi, yace mata.
"Babu nauyi ne?"
D'aga jakar tayi tace.
"Kai haba wani nauyi kuma? Wallahi babu wani nauyi"

Wani irin murmushi yayi tace wato mata dai a Barsu a yadda suke, yarinya da
lalaci irin na Abin sai ALLAH zai iya mata, dan haka suka shiga taimaka mishi tayi
ya cire kayan jikin shi, kamshin turaren Anum da yake manne a jikin kayan. Tace
mishi..
"A ina kasami turaren mata?"
Kallonta yayi sannan yace.
"Ai turaren Anumullah ce!"

Daga haka ya shige ban dakin shi, yana shiga tayi wurgi da rigar, tana
hararar shi.
Zuge jakar shi tayi, tare da fara cire kayan cikin su, kawai ta ciro pant din
Anum, aikuwa ta shiga bala'i har ya fito faɗa take tare da nuna mishi kayan,
murmushi yayi sannan yace mata.
"Wandon Anumullah ce, tunda kika same shi a cikin kayana."

"Wato dan jaraba sai da kayi amfani da ita?" Zare towel ɗin k'ugun shi yayi, yace
mata.
"Mata ta ce, dan haka duk abinda ya kama zan yi da ita, ku da kuke da kayan ku kuyi
ta rikewa don Allah bani guri na dauki kayana."

Daukar pant din Anum yayi tare da kaiwa cikin wardrob din shi ya ajiye, sannan
ya saka yar karamar riga da wando ya gyara kayan da ta wargaza.

"Ya Asad meye nufinka? Zaka dawo mana da ita ne?" Sauya layin shi yayi sannan
ya kira Isma'il yace mishi.
"Bawa Umminka!"

Tunda suka jone a waya, yace mata.
"Sannu kin kwashe min kayana, sanan kina saka min pant din ki, bashi nake so ba,
abinda ake rufewa da shi nake so!"
Cikin Fushi A'isha tabar Dakin, tare da haduwa da Sharifa. Itama tana zuwa ta same
shi yana waya wanda kusan duk zancen manyan mutane ne, domin yana gaya mata yadda
yaji ne shekaranjiya.

Dariya tayi me daukar hankalin, sannan ta shiga zuba mishi sakarci da shirme,
wanda yake cike da yaranta, da zallar kuruciyar ta, murmushi yake kawai.

Itama Sharifa haka ta fita da haushin sa, suka kai ƙarar shi.
----Yau ban kai two in one, labarin yayi min sugar...sai Mun hadu Insha Allah....
#Mai_Dambu....
[2/19, 9:02 AM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SITTIN DA DAYA.

Wannan shafin Sadaukarwa ce ga Masoyan A-K....

Murmushi yayi sannan ya cigaba da shirya kayan, yana mamakin yadda take iya fadar
mugun fata akan tafiyar shi. Karshe sai da ya kare ya zuba mata ido sannan yace
mata.
"Ranki shi dad'e! Idan naje ban ce miki dawowa zanyi da mace ba! Amma naji
zantuntukarki, baki daya babu sauki ko ban dawo da ANUMULLAH ba, tabbas Asadullah
aure zai kara, dan haka a kiyaye furta kalmomi masu gwafa, dan ba zata rataye ni
ba, amma zata iya rataye zuciyar mutum."

Cikin borin kunya tace.
"Allah ya sawwaka, Ni zanyi kishi da matar da ban.santa ba? Ai ba zan fara shirmen
ba, kawai naga yadda kake nunawa kamar tafi mune!"
Ta fada tana me tsare shi da yan madaidaitan idanunta, murmushi yayi sannan yace.
"Ai nima nasan Indona bata kishi, amma dole idan kika ga Anumullah ki kuma jin babu
abinda zai saka kiyi kishi da ita. Sabida bata kai ki ba, nifa idan ban yi karya
ba, kina da zuciyar zinari ce shi yasa baki kishina."

Wani farr tayi da idanunta, duk da ta girma, dan kuwa da ta haihu tabbas zata iya
haihuwar Anum, babba ce haka ma Sharifah babba ce, Anum ce yarinya karama a cikin
su. Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah,bawai dan bata da kyau bane a'a asalin
kyakyawa ce kuma fara kamar tsada.

Matsalar da aka samu tana da jiki ne sosai, musamman bom-bom ɗinta, manya ne..
har sun rinjaye kafarta.

Murmushi yayi a ranshi, sannan ya gama kimtsa kayan shi, bai san dadin
mace ta haɗawa namiji kaya ba, sai dai shi ya hada abinshi,

Yana gamawa ya cire agogon shi ya shiga ban daki, koda ya fito ya same ta,
ta kwanta, takowa sake jikinta zata fara kwasan barci ya mari cinyarta, bude ido
tayi sannan tace mishi.
"Ya Asad baka da kirki, meye nayi na duka."

"Toh raguwa! Daga make ki zaki fara mita, jikinki yana da kyau da bukatar namiji
irina, yanzun ina farawa zaki ce hmm! Ita kuma wancan bata da aiki sai na shan
kayan mata." Daga haka ya fice daga d'akin, yana me musu fatan shirya.

* Washi gari tare da ila da rakiyar wasu manyan motocin sojin kasar, suka nufi
kasar Nigeria a mota dan yace yarinyar shi tana son kallon garuruwan kasar da na
Nigeria.

Tafiya ce tare da lafiyayyun ababen hawa, koda suka dauki dogon lokaci suna
tafiya suna isa garin Maradi suka kwana, washi gari suka kuma ɗaukar hanya.

**
Ban san me ya faru ba, amma tabbas naga Umma ta fita da sassafe, har na shirya zuwa
makaranta, ban dawo ba sai karfe biyar na yamma dan karfe sha biyu nake tafiya, ina
shigowa na samu Maman Aminu tana kuka, kallon Isma'il nayi naga ya zuba hannu
bibbiyu a kumatai.
"Kai bana son iyayi, uwar me aka maka?"

Kamar wani Babba dan ya iya manyance yace min.
"Wai su Umma Hafsat ce suka yi hatsari a hanyar tula."
Sake jakar hannu na, nayi tare da zuba mishi ido. Zama nayi tare da fashewa da
kuka, zunzurutun tausayin Hafsat.
" A wani hali take?"
"Hmm! Allah ya kyauta, ban san meye Hafsa take nima ba, ban san meye kika tare mata
ba, Umman ku ta dawo tace."

"Allah ya kyauta ya kuma bata lafiya yasa Zakkar jikine." Daga hakan na shige
d'akina, bana son damuwa tunda nayi mata addu'o'in shi kenan.

--; A can asibitin kuwa Hafsat tana fama da buguwar da tayi akanta sai surutu
take kamar me, babu wanda ya kulata.. a hankali ta fara surutun abinda ta aikata.

"Yanzun haka zan cigaba da kallon Anum tana tattara kome, itace soyayyar malam,
Umma Sonta take, itama Maman Aminu da nake nuna mata Anum bata jin maganarta ta
tsine mata haka zan cigaba da kallon su, a'a dole naje tura na fidda Ruwaidah.
Wallahi ba zan yarda ba, dole naga bayan su. Anum da Ruwaidah. Nice nayi mata
sharrin maita, na kuma je har gidan Hamisu na ce karsu yarda ta zauna, itama
Ruwaidah ai sawa naii a rufe mata bakin mahaifar ta, yadda ba zata TAB'A Haihuwa
ba, shi..."

Cikin mugun takaici Mijinta ya juya ya kalli Aminu da Usman, Sai Abdul Hakim.
"Kun dai ji da kunnen ku? Ba karya aka mata ba, Ni dai zance Allah ya bata lafiya,
amma na yafe zama da ita, taje can da jika bakin halinta ta sha." Wucewa yayi gurin
da Nurse suke ya amshi takarda ya saketa,

Sannan ya ajiye musu yayi tafiyar shi,

Yadda take magana da yadda tayi ta haɗa Anum da yan uwan, sai da ta fadi
kome, karshe alluran barci suka mata. Tana fara barci zata tsalla ihu, tace.
"Gashi nan yazo zai dauke ni, wayyo Allah na, karka tafi dani."

Dakyar tayi barci.
**
Kwana biyu ina jin suna ta zirga-zirga tsakanin Asibiti da gida, Maman Aminu taje
ta dawo da kuka, ga ciwon Isma'il da ya tashi gadan gadan, kamar nayi hauka.

Kudin salary na, duk ya kare a hanyar asibiti, tun da na kai shi suka duba
kodar, suka ce zasu wanke mishi. Ana bukatar dubu dari biyu, nazo na hada gwal
dina da wasu abubuwan hannuna, kudin Balance din na hada, sannan na, cewa Umma.
"Bari na leka makaranta nayi musu bayani, zan kai Isma'il asibitin."

"Toh shi kenan, nima ina son zuwa na duba Hafsat, Insha Allah amma sai kun
dawo na tafi sabida kar mu bar Maman Aminu a gidan."

"Toh bari naje!"
Na fita da sauri, haka kawai nake jin bakon yanayi a raina, dan haka na nufi
makarantar, ina shiga sai dariya ake min, ban damu ba, na nufi Office din mu, nayi
abinda zan yi na nufi Office din wancan watsatsen na shiga.

Ma same shi da wata yarinya yar aji shida, yana ta matse ta, kasa hakuri nayi na
fincikota na wanka mata mari.

"Dake baki da hankali, zaki bari ana niman..." Kwace hannunta tayi tare da cewa.
"Kema fa ansan kina zuwa gurin shi, kuma ance saboda kina da kanjamau yasa yake
korank..."

Marin ta na kuma, tare da turo ta waje, na shiga gayawa headmaster magana, tare da
cin mutuncin shi, fada sosai muka yi dashi dan na manta aure ne dani, muna cikin
haka ashe an sami wanda ya kira Rulwanu, haka yazo yaja hannuna bai damu ba.

Ina kuka ina masifa, dan ma Allah ya takaita akwai nikkab a fuskana, haka na
bar gurin faɗa nake ina kuka.

Ganin dandazon matasan Unguwar mu, ya sani juyawa na kalli Rulwanu, murmushi
yayi sannan yace.
"Kiyi hakuri, za a ci Uban koma waye, ki daina kuka, Madam."
"Nabi Madam da gudu ba takalmi, wallahi zan maka rashin mutunci."
"Ai ni dake dan jima ne da dan Jummai maza yi min."

.. Kirjina ne yayi min nauyi, sakamakon kamshin turaren shi da nake kuma jin
yana kutso ni, raba idanuna nayi ina niman ta inda yaƙe, amma ina wasu kartin maza
naga sun lullube wani Zaune, had'iye yawu nayi sannan na sunkuyar da kaina kasa,
jikina yana rawa,

Tabbas ina jin kaifin idanun shi cikin jikina, wayyo Allah na, ina...
"Dadda!" Na tsinkayo Muryan yar wata baby doll a gabana, kura mata ido nayi,
zunzurutun tayi min kyau, ga gashin kanta har gadon baya, cusa hannu na nayi a keya
na naji wutsiyar gashina.

Kallona take tana leka fuskana, nima haka nake ta mata. Hannuna na kai zan
kad'e mata kuran da ya haura mata saman gashin goshin ta, ya daka min tsawar da na
zabura.

Da sauri na juya jikina ya dauki rawa, da sauri na d'aga nikkab din, na kura
mishi ido.
"Karki kuma tab'a min Yarinya ta, uwar masu ya'yan Arziki, bar min Y'ata algunguma.
Kuma ki bar kallona, domin nafi karfin ki yanzun."

Da sauri na juya zan shiga cikin gidan, yarinyar ta rike hannuna, kuka ne
yazo min domin ina jin lokacin da ya zare hannun ta a cikin nawa ya ce mata.
"Karki yarda da ita."
Shiga cikin gidan nayi na samu anata muhawara tsakanin Yan uwana maza. Wasu na
cewa naje ayi min test wasu na cewa a'a bani dashi,har shima Zakin Fama ya shigo
gidan. Fita yayi tare da bawa Yaran shi damar su shiga cikin makarantar suci mishi
Uban headmaster. Sannan ya koma cikin gidan.

"Khadijah bata da wani ciwo, domin ni ne wanda nayi mu'amala da ita na
karshe, sannan kuma nayi imani ba zata tab'a wasa da igiyar aurena akan ta ba, dan
haka zan yi tafiya gobe Insha Allah, da Isma'il. Sati biyu zamu yi idan na dawo zan
kai ta Afrika ta Kudu,zata ga likitan fata."

Duk wannan maganar da suke iya tsakanin su ne, dan ban ji me suke cewa ba, dan
tun da na shiga d'akin, na sami Isma'il a zaune yana game a tap din da nake da
yakinin na wancan katon mutumin ne, kamshin turaren shi ya cika min daki, ina
kallon yaron. Yadda yake ta murna yace min.
"Ummina, nawa ne fa Abbana ya kawo min, shi da Princess hoor, Hoor!" Ya kwala mata
kira.
"Assalamun Alaikum! Na shigo."

Wani irin kwalla ne ya shiga saukowa daga idanuna, wato yarana rayuwar su,
nagartacce ne domin kowanne su cike yake da kamala,
"Shigo!" Tana shigowa ya gyara zaman shi yace mata.
"Ga Ummin mu!" Ya nuna mata ni,
"Kullum tana kukan Allah ya dawo mata da ku, ina jin kullum idan tayi sallah tana
addu'a, tare da niman Allah ya yafe mata, karki yi fushi da Ummin mu tana son mu"

A hankali ta tako har gabana, tare da saka hannun ta a baki, tana kallona
idanunta cike da kwalla, sannan ya cigaba da bata labarin su Hishmah ya gaya mata
ita ta rasu, amma Hisham yana nan. Fadawa tayi jikina.
"Zan iya manta kome, amma ban da maraicin da na gani a kwayar idanun yarinyar da ta
faɗa da'irar zanen ƙaddara ta, sake min Y'ata;"

"Don Allah kayi hakuri, wallahi nayi kuskure masu yawa, na zalince ku, amma na
rantse da Allah, na tuba, karka kuma raba ni da ita. Don Allah Aliyu!"
Na fada ina kuka tare da zuba gwiwata a kasa, saka hannu yayi ya zare yar shi.
"Abbana!"
Kallon yaron yayi, itama kuma Yarinyar tace..
"Dadda!"
Duk suka kafe shi da idanun su.
"Ni Dadda Ummina nake so!"
A hankali Isma'il shima ta tako gaban shi, tace mishi.
"Kayi hakuri! Bata da lafiya, kaga maganin da take sha, Umma tace wai zuciyarta ne
ke mata ciwo. Dadda, nima sabida ciwonta nake boye mata nawa ciwon don Allah ka
daina barin Ummin mu tana kuka."

Ajiye min yar yayi, sannan ta dawo jikina tana dariya, riko hannun
Isma'il yayi tare da ɗaukar jakar shi suka fita.

Ba zan iya gaya muku farin cikin da nake ciki ba, dan haka da kaina na fito
zanyi girki aka kawo cefane aikuwa na fata aiki babu kama hannun yaro, ba shirya
tuwon shinkafa miyar danyen kub'wa aka fita dashi a babban kula, saboda sojojin
shi, ita kuma nayi mata wanka, na shirya ta cikin kayanta masu kyau da tsada, haka
na fito na wanke kayan, sannan na zauna na sakata a gaba ina kallonta, a ranar Ya
Abubakar ya dauke ta suka nufi gidan shi. Bayan yasha masifar Umma.

Ban damu ba sabida suma suna kaunar Yarinyar kuma, dake tasake ranta, tana
son kowa. A can suka kwana, washi gari ya dawo da ita, Ya Usman ya dauka. Haka duk
ta zaga yan uwana.

Domin duk inda ta tafi sai ta kwana, su goma sha din nan sai da ta kwana
hannun su, banda Hafsah da take asibiti. Sai ranar na ke tambayar Umma.
"Wai ni Umma ina wancan BANIJARE ya kai min yaro ba lafiya!"
Abinda ya sani maganin tun ranar da ya bar gidan Umma ta sani a gaba da wasu
abubuwan, da kanta take sarrafa su, haka kawai ta sani jin kasala babu gaira babu
dalili, haka take haɗa Hulba da wasu abubuwan tana bani ina sakawa a boons dina,
ina matse su da bra me kyau, haka ta haɗa min sabulun wankan, da na tsarki. Ga baki
daya ta sauya min halitta ta, wai duk sabida wancan BANIJARE, lalle kuwa haka nake
kunsawa kullum ko tsakar gida da hijab nake yawo, wallahi ni kaina nasan na sauya
oba, dan haka nake tambayarta inda ya kai min Yarona.

Make kaina Maman Aminu tayi tare da cewa.
"Baki da hankali har yanzun, Uban Yaranki kike kira haka, dubi yadda ya dauki yaron
nan ya maida shi nasa karfi da yaji, sai kin ga na mutu da bakin cikin ki zaki huta
da wulaknta bawan Allah nan. Wato zai sayar miki da d'a shi da yabar lu'lu'un
shifa"

Tura baki nayi, domin Maman Aminu har yanzun ba wani lafiya ya ishe ta ba, a haka
take rayuwa, dan bata sati jininta bai haura ba .
"Allah Mama karki ce min haka, dauke shi yayi ko gaya min bai yi ba, ina laifin
yace min."

"Toh ai gwara ki kafe, yar masu taurin kan tsiya, Maman Sadeeq. Wallahi Anum da a
zamanin fir'auna tazo za a wahala da ita kafin ya yarda da Annabi Musa, yar banza
me taurin kan tsiya."

Ta kuma min keya, Ita kuwa Hoor dariya muka bata, tana cewa.
"Ummi! Dadda ya kai Yaya Isma'il asibiti ne,kuma shi yace kar a gaya miki Dan zaki
damu, wai ke kina kuka kamar baby."

Kallon yarinyar nayi idanuna kwalkwal, ai kuwa ta fashe da dariya.
"Ummi tana kuka!"
Tace.
"Wallahi kin sha kunya, Anum yaushe zaki girma."
.tura baki nayi, tare da cewa.
"Ina ruwana da girma."
"Allah ya kintsa min ke"

Haka muka yi ta hira, yarinyar ta a gefe mun tana nata, wasan dan Maman Aminu ta
koma kusa da ita, ina kallon ta daura kanta a kirjin Maman Aminu, suna hira.

"Kin san duk abinda yarinyar nan take duk kuruciyarki ce!"
"Kai Umma ban halin tayi abu sai kuce Ni"

**
Washi gari.
Bakuwar Number na gani.
*Ummi muna hanya da Dadda*
Tabe baki nayi tare da gyara kwanciya ta, ba Dadda ba daddo.

Ina sane suna hanya. Nayi biris dasu, sai da Rulwanu ya shigo da cefane yake
gaya min wai suna hanya.
"Kai bana son munafunci, na lura tunda wannan me kama da samudawan yazo kake wani
rawan kai, da kanin Ubanka ya dawo daga balagoron da yayi ko?"

"Don Allah idan kina ji da masifa idan yazo ki mishi bani ba."
"Umma!"
"Ke tafi can, kuma kiyi musu girki."
Abinda na Fahimta yazo ya kuma kwace min yar soyayyar da nake riritawa, aikuwa naji
haushin sa.

Karfe hudu suka iso, tunda ya iso ya sauka a dakin Rulwanu da yake zaure kin zuwa
nayi na bawa yaran kayan abinci zasu kai mishi, ai kuwa Maman Aminu ta balbale ni
da faɗa,haka nayi ta kwasan kayan abincin ina kaiwa dakin. Ina gamawa hankalin shi
na kan wayar da yake da alama da matar shi yake, dan sai wani narkewa yake, tsaki
naja, zan fita ban san ya kayi ya make ni da kafar shi ba, na tafi zan fadi.

Kallon shi nayi tare da zabga mishi harara. sannan na fito. Na kai mishi kome a
amma sai gashi ya kuma fitowa yana kiran Isma'il, kome ya gaya mishi oho. Yaron ya
shigo tare da b'ata rai yace min.
"Kawai kije bai da lafiya, dama tun a gidan su Hisham yace kan shi ma ciwo."

Shiru nayi tare da mik'ewa na bar d'akin, nufar dakin shi nayi na same shi garau.
"Wannan wani irin abu ne."
" Ke ban Nime ki ba karki d'aga min murya"

Ya fada tare da tsare ni da ido, a sanyayye na fara saka mishi abincinsa,na
ajiye sannan na hada mishi har da ruwa, zan fita yace min.
"Kinsan Allah! Karki yarda ki fita min a nan, inda ba guba kika sa min naci na mutu
ki dauke yarinyar ba."
Da sauri na zauna, sai da ya cinye sannan ya shiga gaya min bakaken Magana.nima
kuma ban da hakuri na biye mishi muka yi fada karshe ya matse min bakina.
"Matukar kika ce zaki cigaba da tanka min, Wallahi ina da masu gyara miki zama."
Buge hannun shi nayi tare da cewa.
"Ban yafe ba."
"Karki yafe mana, mara kunya kwadayayya me shegen son abin duniya."
"Kai karka so abin duniya, kuma Ni ba." Had'iye sauran maganar nayi sakamakon jin
hannun shi cikin rigana,kasa kallon shi nayi. Ya shiga duba jikina kai Maude bai da
imani, haka ya raba ni da kayana ya duba jikina, duk da ina tare kirjina, tsaki
yayi sannan ya watsa min kayana.
Ina mik'ewa zan saka ya kuwa riko hannun, tare da haukata ni da salon shi da nayi
kewar shi.

Kuka nake son yi, amma na had'iye. Dan Umma tace min.
"Kina da damar da zaki rike mijinki har abada, duk fushin da zai yi dake na lokaci
ƙalilan ne, idan ya Huce karki bar ya subuce miki baki ajiye mishi tambarin ki a
ran shi ba"

A hankali yake nuna min yadda yake bukatar kasancewa dani, a wannan
yanayin da nake bin shi har shagon shi, ya shiga biyar dani.

Kasa hakuri yayi, ya haɗa bayana da bangon dakin, hmmmmm
--
A hankali ya sauke ni, tare da sumbatar goshina, kifa kaina nayi a kirjin shi, ina
shashekar kuka, shafa bayana yake.
"Ban san tafiya malam ya rasu ba, nayi kuskuren tafiya, dan malam Ubane a gare ni,
Anum na dawo dake rayuwa ta ne bawai dan ina da ra'ayinki ba, a'a sabida dangina da
Yarinyar da kullum sai naga maraici a idanun ta, dan haka gobe zamu wuce ni da
yarana ita kuma na barta idan Allah ya kai mu zamu yi magana."
"Aliyu Asadullah!" Sake matse ni yayi tare da kai bakin shi kunne na, yana sauke
min wani irin numfashin da ya kashe min jiki, rungumo shi nayi domin jikina ya
mutu.
"Meke damun ki?"
"Ka yafe min!"
"Bani kikawa laifi ba Hoor zaki roka."
Ya faɗa tare da janye jikin shi, dukda fushi yake har zuwa lokacin, bai hanani
fahimtar yaji dadin yadda ba sake mishi ba.

Bayan na hada mana ruwa, tare muka yi wanka, sannan na fito na koma cikin
gidan, har dare ina jin nutsuwa a raina, ina kwance naga sako da wancan Number.
*Kizo ki min tausa*

Saka hijab nayi, bayan na shafa humra masu sanyin dad'i, dan Rulwanu da Sojojin sun
koma gidan shi da ake haya,. Tunda na shiga dakin Baga babu wani haske sai na
laptop. A hankali na haura katifar, ba janye mayafin da ya rufu, sannan na shiga
mishi tausa, a hankali yake lumshe idanun shi, har na gama, sannan ya juya tare da
janyo ni jikin shi, muka kwanta, zare hijab ɗin yayi.

Ashe na yamma wasa ne, sai da yanzun na gurju a hannun shi, kuka nayi har
na gaji, sannan ya shafa kaina, musamman yadda nake mishi kuka da zafi. Wani irin
mingira kai yake, zaka rantse da Allah baya jina, nan kuwa shegen Dadi yaji, yana
son mace me raki.

Dan haka Mutumin fa yayi ta zungura da raruka, sai da ya gaji dan kanshi, ya
kyale ni, bayan yayi wanka. Yace min.
"Allah yasa a wannan daren ba zuba jari na masu kyau."
Jan mayafin nayi tare da saka mishi kuka, tab'e baki yayi.

Tare da gaya min maganar mara daɗi wanda yaja min dole na bar dakin shi babu
shiri.
Washi gari da nakai mishi abin karyawa ya gama shiryawa, dan haka yana gani
na, ya amsa yaci da sauri dan tun biyar ya turo min sakon zasu bar garin bakwai
sojojin an hada musu nasu a shagon shi.

Ina zaune har ya gama shiryawa da taimakona, na barshi ya karya na hada mishi
kayan shi da suke Dakin, sannan na dauke turaren shi, da agogon shi na b'oye ban
san me zan saka mishi da zai tuna dani ba. Kawai ina mikawa na zare pant din jikina
na cusa a cikin kayan shi dake ya juya min bayane.

Ina gama shirya kayan na kalle shi nace.
"Maude!" Banza yayi min,
"Ay Asad!"
"Baki iya girmama uban Yaranki bane"
"Wani girma bayan nagama ganin girman tun daga jiya da yamma har daren jiya, koda
yake manta kawai, Ni na gama shirya maka kayanka akwatin yayi min nauyi."
Juyawa yayi tare da kallon mu, yar karamar akwatin yaji wai yayi min nauyi,
"Nauyi da?"
B'ata rai nayi, sannan nace mishi.
"Bama zan iya d'agawa ba, domin kirjina budewa zai yi ina dalili!"
Na fada a tsiwace, gyda kai yayi sannan yace min.
"Raguwar kawai,"
"Eh na yarda!"
Haka ya gama karyawa sannan ya dauki akwatin ya fita ina bin shi a baya, yana isa
bakin kofa yace min.
"Ko dan irin good bye babu!"
"Ok ina zuwa don Allah tsaya min!" Na kasa da gudu na shiga cikin gidan, na ajiye
kayan satan da nayi, sannan na dawo yana waje, ihu na saka da karfi nasan zai
Shigo ai, nayi wuf na shige dakin Rulwanu, yana zuwa na daka wawan tsalle na
rungume shi, tare da haɗe goshin mu. Hannun shi dukka biyu yana bom-bom dina, nawa
yana bisa kafad'ar shi, rike kanshi nayi ina dariya, hawaye na zuba daga idanuna.
"I luv you, da duk zuciyata, Nayi laifi amma don Allah kayi min koda murmushi ne.
Sannan na gode da bani aron Yarka da kayi, Asadullah ina haukar sonka."

Baki ba zai iya fadar yadda yake ji ba, amma zuciyar shi da gangan jikin shi,
sun isa

Please Login or Register in order to submit comment