You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su isar da sakon zuciyar shi, yasan ita Rabon shi ce, shi yasa ya jure duk
tsanani da wahala, dan haka yau yafi koda yaushe farin cikin, gashi da Anumullah a
hannun shi,
Hade bakin mu, yayi mun jima a haka, kafin ya sauke ni. Kallon kayan jikina yayi
yar gajeren wando jeans ne da wata haf vest, hannun shi ya zura cikin vest din yana
kallon idanuna, yadda nake zubda kwalla. Sake hade bakin mu yayi, mun jima a gurin
me shirin barin garin bauchi bakwai so gashi garin tsinke fure har tara saura,
dakyar muka rabu ina kuka.
Duk kamshin turaren mu ya haɗu da juna, haka ya tafi ya barni da tambarin kaunar
shi, bayan sunyi sallama dasu Umma, sai lokacin na koma d'akina. Ina murmushin jin
dadi. Duk da banga fara'a akan fuskar shi ba, amma nasan har abada ba zan kuma rasa
shi ba, dan shi RABO NA NE....

*** Tafiyar da zasu yi a kwana ɗaya da Wuni daya, shi yasa suka yi tafiyar
kwana ɗaya rak, domin basu isa garin Damagaran ba sai karfe biyar na safe, bayan
sunyi sallah asuba, ya shiga cikin gidan shi. Da A'isha ya fara cikin karo. Karb'an
jakar shi tayi, yace mata.
"Babu nauyi ne?"
D'aga jakar tayi tace.
"Kai haba wani nauyi kuma? Wallahi babu wani nauyi"

Wani irin murmushi yayi tace wato mata dai a Barsu a yadda suke, yarinya da
lalaci irin na Abin sai ALLAH zai iya mata, dan haka suka shiga taimaka mishi tayi
ya cire kayan jikin shi, kamshin turaren Anum da yake manne a jikin kayan. Tace
mishi..
"A ina kasami turaren mata?"
Kallonta yayi sannan yace.
"Ai turaren Anumullah ce!"

Daga haka ya shige ban dakin shi, yana shiga tayi wurgi da rigar, tana
hararar shi.
Zuge jakar shi tayi, tare da fara cire kayan cikin su, kawai ta ciro pant din
Anum, aikuwa ta shiga bala'i har ya fito faɗa take tare da nuna mishi kayan,
murmushi yayi sannan yace mata.
"Wandon Anumullah ce, tunda kika same shi a cikin kayana."

"Wato dan jaraba sai da kayi amfani da ita?" Zare towel ɗin k'ugun shi yayi, yace
mata.
"Mata ta ce, dan haka duk abinda ya kama zan yi da ita, ku da kuke da kayan ku kuyi
ta rikewa don Allah bani guri na dauki kayana."

Daukar pant din Anum yayi tare da kaiwa cikin wardrob din shi ya ajiye, sannan
ya saka yar karamar riga da wando ya gyara kayan da ta wargaza.

"Ya Asad meye nufinka? Zaka dawo mana da ita ne?" Sauya layin shi yayi sannan
ya kira Isma'il yace mishi.
"Bawa Umminka!"

Tunda suka jone a waya, yace mata.
"Sannu kin kwashe min kayana, sanan kina saka min pant din ki, bashi nake so ba,
abinda ake rufewa da shi nake so!"
Cikin Fushi A'isha tabar Dakin, tare da haduwa da Sharifa. Itama tana zuwa ta same
shi yana waya wanda kusan duk zancen manyan mutane ne, domin yana gaya mata yadda
yaji ne shekaranjiya.

Dariya tayi me daukar hankalin, sannan ta shiga zuba mishi sakarci da shirme,
wanda yake cike da yaranta, da zallar kuruciyar ta, murmushi yake kawai.

Itama Sharifa haka ta fita da haushin sa, suka kai ƙarar shi.

----Yau ban kai two in one, labarin yayi min sugar...sai Mun hadu Insha Allah....
#Mai_Dambu....
[2/19, 8:06 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SITTIN DA BIYU.

REAl AUTAR KN ga shafin nan keda yan Group din ku 💝💞🤩
....................................................

Katse kiran yayi sakamakon ganin Number Liman ya shigo mishi, a gajiye ya kalli
agogon wayar tare da kallon sabon kiran Liman dana Anum wanda suke karo da juna,
katse kiran Liman yayi tare da ɗaukar na Anum.
"Na gaji!"
"Da ina kusa da kai, tausa zan maka. Har kayi barci."
"Me yasa baki yi tunanin haka ba?"
"Lokacin duniya ta aure ni ne, a yanzun da ta sake ni bana jin zan kuma saken da
kanayi a baya"

"Anumullah!"
"Mhh! Zakin Allah!" Murmushi yayi sannan yace mata.
"Kina nufin haka zaki kirani kema?"

"My Lion!"
"Hmm!"
"Ok my sugar pie!"
"Hmm!"
"My Rockstar!"
"Haka ma yayi, zan kira ki anjima!" Katse kiran yayi sannan, ya shiga falon Liman
da sallama, lura mishi ido Liman yayi cikin nutsuwa, yana hango walwala shi a fili
ko ba a fada mishi ba, sun sasanta da matar shi, zama yayi tare da kallon matan
shi.

"Barka dai Dattijon arziki, na same mu lafiya."
"Alhamdulillahi, ya ka baro su?"
"Masha Allah, suna lafiya"
Sun jima suna gaisawa tare da cewa, akwai tsarabar shi, amma sai anjima zai kawo
mishi yanzun ta gaji,
Shigowar Dijamah ce yasa yace mata.
"Yar tsuhuwata, zan sami kunun daka nan?"
"Akwai, wadanan matan baku da sarar Arziki, marasa kunya. Ko kunya babu a ranku,
kun kwaso jiki kun kawo karar shi, wallahi kuka sake ya dawo da matar shi, kuke
wannan haukar, kun kade har Buzun ku."

"Don Allah! Ban kira ki ba, ki Barsu su fadi abinda aka musu," juyawa tayi, tana
fada tare da sababi.
Kallon su Liman yayi sannan yace.
"Aliyu! Sun kawo karan ka ne"
"Toh ina jin su!"
Cikin rashin hankali, A'isha ta faɗa abinda ya gani, yazo mata da turaren matar
shi, tare da dan kamfenta, itama Sharifa ta fadi nata.
Kasan shi a sunkuye, har suka gama.
"Anyi haka ko ba ayi ba?"
"Amma meye ya kaita min bincike? Dattijo nifa ba yaro bane, kuma Ni na zan zauna
suna garani son ransu ba, na gaji da kawo kara, idan ba zasu iya zama da ni ba kofa
a bude take, kamar yadda kuka bani su, sai na dawo maka da kayanka. dan haka su
kwantar da hankulan su, nan da karshen wata zan dawo da Anumullah."

Yadda ya kira sunan sai da ya sanya manyan mata d'agowa da sauri.
"Liman kaji ko? Wai Anumullah wato mu kuma watsatsu, ita kyautar Allah mu kuma
kyautar mutane, tun da dole aka mishi ya zauna da mu"

"Wallahi na gaji da fitinarku, meye asalin sunanta?" Cikin ban haushi da niman
magana yace.
"Khadijah Anumullahhhhh,! Zaku iya kiranta ANUM KHADIJAH!"

Kallon juna suka yi, tare da girgiza kanshi, "liman ka gani da idanunka, kaga yadda
yake juya sunan wato dan sunan Innarsu."
"Keeee! Sharifah," ya daka mata tsawa, idanun shi jajjur. Mik'ewa yayi zai fita,
murmushi tayi sannan tace mishi.
"Wallahi kace zaka nuna mana fifiko tabbas zan cigaba da.."

Cikin zafin rai, ya shiga tattara hannun rigar shi, dan dukar ta zai yi. Sai da
Malam ya daka mishi tsawa, cikin fushi yace.
"Wallahi kar na ganki a cikin gidan, ki koma gidan Baffa Lawan."
Ya saka kai ya fice daga gidan, fada Liman yayi musu, sannan ya ce ta koma
d'akinta, tana shiga ta sami Aliyu,.yace ba gidan shi ba, dan duk Iskancin da zaka
mishi karka tab'a mishi iyayen shi, tsakanin shi da Allah ya koreta.

Duk yadda aka so ya dawo da ita, fir yaƙi dan yace taje sai ta san darajar
uwarenta.

Sai da aka yi babban zama kafin ya amince ya kuma kawo musu maganar dawowa da
Anum, kowa yayi mishi fatan Alkhairi, tare da cewa.
"Amma kuma kasan bare ce, zata iya zama da mu?"

"Eh zata iya tunda tana son zama dani!"
Shiru suka yi, sannan suka mishi mishi fada tare da nuna mishi illar abinda yake
yi.
"Bamu hana ka kawo ta cikin mu ba, amma maganar gaskiya, kayi ƙoƙarin boye
Kaunarta, sabida yadda kake nuna alamarinta yasa suke yawan fusata."

Shiru yayi, domin ya fahimci shigowa Da Anum cikin Zuri'ar shi zai an kai ruwa
rana da wasu mutanen. Har ka watse ana yana jinjina al'amarin, sai yayi kokarin
b'oye yanayin akan fuskar shi, Domin kuwa, yaji kananun magana suna yawo a cikin
gidan shi.

**
Wasa wasa wankin hula yake shirin kaiwa ga dare, domin yan uwan Maman shi, dangin
su na cikin masarautan ransu ya b'aci taya ga mata zai fita ya kawo musu bare, kuma
sun san cewa tunda ya kafe babu me hana shi, har gurin sarki aka kai shi. Yace shi
fa babu wanda zai dakatar dashi, Dukkansu matan shi ne, sannan su ya aure sune
sabida Biyayya ita kuma zab'in shi ce.

Wannan abin ya fusata Sharifah, domin kuwa tace wallahi ko ita ko Anum.
***
Bauchi.
Fito da kayan da yawo mana Umma tayi dan sai da ya tafi aka fara sauke kayan,. Duk
kusan na Isma'il ne, babu nawa sai na malam wanda aka bawa Yayuna suka raba. Kamar
zanyi kuka yadda naga kayan da ya sayawa Umma da Maman Aminu,

Duk sai jikina yayi sanyi, sako na tura mishi da cewa.
```First love is important
but
last love is very important.
B'coz,
first love changes the nature
and
last love changes the life...```

Murmushi na sake lokacin da sakon ya tafi, na cigaba da aikina.
A gefe guda kuwa, Umma bata barni haka ba, gyara take min ciki da waje na,
akwai hadin da tayi na normal maganin mata, inda ta haɗa dabino, y'ay'an zogale,
kanumfari, mazarkwaila, zuma, ta dafa min sosai sai hakin daka.

.. akwai wata kawarta yar garin Gombe, ta kawo mata goron tula, da kuma
zumar shi, haka ta haɗa a cikin tsumin, na cigaba da sha, sosai ban san ya akayi
ba,na ga dai suna ta fita kasuwa. Suna sayayya,
"Umma! Kina nufin Anum Nijar zaku kaita?"
"Ji min mugu, na zauna kayi ta kallona dan bakin ciki, toh ba zan iya rayuwar
tunzuranci irin naka ba."

"Umma kin ganta ko?"
Dafe goshinta tayi, sannan tace.
"Amma baka da kirki! Toh Anum zan ci kaniyarki!"

"Umma dan ƙin kai na zauna nai ta irin rayuwar shi." Na fada ina gwalo.
Washi gari na shirya zan tafi Saloon na riko hannun hoor.
Har bakin kofar Isma'il ya rako mu, kallon titin muka yi ana jan wata mata.
"Wacece haka Rulwanu?" Tab'e baki yayi, sannan yace.
"Kawarki mana XOXO, ta kashe uwarta, ta daurawa Abida, bayan mutuwar Yarki aka sami
labarin tana can bayan gari tana zaune, an kai mata sumammen ta gudu.
Kuma dan bakin hali ashe tace wai Beauty ce, itama bata da lafiya daga gidan yarin
aka dawo da ita, da aka san gaskiya ne"

"Allah kasa muyi kyakyawan karshe." Na tsari Napep muka bar unguwar ana dambe
da ita.

Ko jiya yadda naji suke maganar jikin Hafsat na tausaya mata, domin hauka take
sosai, domin kuwa nice taso nayi wannan haukar Allah ya maida mata, lokacin da aka
mata ruki'a suka ce, ai ita ta tab'a turo su, kuna dama sunce zasu dawo.

.... Tunda muka isa gurin Saloon din, sai ga wata mata ta shigo Bayan mun zauna ana
min gyaran gashi, kallon Hoor tayi domin nace a wanke mata kanta.

"Don Allah wannan Yarinyar Yar waye?"

Bakina dauke da Addu'ar niman tsari daga sharrin kambun baka, na tofa mata.
Sannan nace.
"Yar Yaya na ne?"
"Kai Masha Allah! Tayi min kyau kamar ki bani"
"Tabarkallah, bamu bada kyauta d'a wannan sha'ani ne na Ubangiji."
Na gaya mata, sannan na janyo yarinya na jikina, ina mata. Dauko chocolat tayi zata
bata.
"Mun gode, Baban ta ya hanata amsar kome a hannun mutane."

Kamar dole sai cusa mana take, Yarinyar ma ta makale tace bata so.
Haka ta kare ta barmu har aka gama min muka barta a gurin, ina dalili,

---
NIGER.
Rigimar da ake a family house din su Maude ya girmama, sun so.ya hakura da dawo da
Anum shima kuma yace bai iya ji ba, dan haka kawai ya tsaya akan ra'ayin shi, dan
dole suka kafa mishi sharadi, dole ya kuma kara aure.. inda Hakamah tayi ruwa tayi
tsaki aka bashi auren Zuwairiyya. Yace idan Anum ta shigo zai yi da ita. Na hudu.

Da wannan sharadin ya amince, suma suka amince.
....
"Na gaya maka ka daina bayyana kaunar da kakewa yarinyar nan da zata sami matsala
da mutane,"
Kallon Mahaifiyar shi yayi, tare da sunkuyar da kanshi, sannan yace mata.
"Zan rage, "
Ya faɗa a sanyayye,
"Wannan abun ba zai kare ka, da kome ba sai b'acin rai, domin zasu ga kafifita
ta,akan su duk abinda zaka yi gani zasu yi kana nuna wariya da rashin adalci, amma
idan ka boye haka a ranka zai saka kowa yayi tunanin ki baka yinta ne."

"Naji Innarmu".haka ta gama mishi fada sannan ya mike ya bar gidan,
***
An dauki Hajara da Rahama, Sai Kanwar Baban su, Umma Rukayya da Maimuna, sai Hajiya
Hakamah da Mama Sa'adatu, kawar Innarmu ce, sai Shafa'atu Kanwar Innar ce, aka nufi
Najeriya dauko Anum.

***
Bauchi.
Gidan shi na nan unguwar mu, aka gyara ta sosai, aka share.

Dan ana saka ran isowar su zuwa dare ne, tunda na tura mishi sako yau sati daya
kenan, na kasa gane mishi, idan na kira shi ba shi zai hana shi ya rufe ni da faɗa
ba kamar zai dake ni, kashe wayar nake na tura mishi Allah ya baka hakuri.

..... Abu kamar wasa sai da ya daina kirana, sai dai suyi waya da Isma'il, su
sha hirar su sa Yara. Shi Ni kuma ko oho, haka na gayawa Umma, itama fada ta min
tace min .
"Ke baki da Uzuri ne? Kika sani ko yana cikin damuwa da uzuri ne, yana da iyali
bayan ke dan haka bana son korafi, karki yarda na kuma jin kinyiwa wani cikin yan
uwanki maganar shi, shi yasa auren yanzun bai da wani karko kamar da! Domin babu
me wannan shirmen, ke daga yayi miki abu zaki fara kawo karan shi, bana son rashin
hakuri, ki zuba mishi ido."

Nutsuwa nayi sannan tace min.
"Yana da mata! Idan kika je ki zama wawuya, yadda zaki Fahimci waye su din, haka
akewa kishiyoyi, karki yarda ki sake ki nuna musu kin san rayuwa, ki zauna dasu da
amana, idan kika ga suna da wata dab'iar ki yi kokari ki Fahimci shin wani irin
cigaba dabi'ar take karawa zaman takewar su dashi.

Karki yarda ki zama datti bola rumfar kasuwa, ki zama mace me aji, wacce
murmushin ta ya ishe kowa kokwanto, ba mamaki ya fito daga babban zuri'a ce, ki
zama kowa naki, banda dan banza, idan yace miki Anum wannan nawa ne, amshe shi da
hannun bibiyu, idan yazo yana magana ki bashi hakuri, karki yarda ki zama
ballagaza da zata sake mijinta yana ihu tana ihu.

Dole zaki yi hakuri da shi da kuma cikin inda zai kai ki, karki yarda ki
nunawa Zuri'ar shi baki san ciwon kanki ba, sau dari idan yayi miki, dauki
alkur'ani ki karanta zaki ji sauki, karki yarda ki rike abin hannunki, akwai
Mahaifiyarshi da Mahaifin shi, ki nuna musu ke yar su ce, karki sake ki fara girki
baki kaiwa Mahaifiyar shi da mahaifinsa ba,koda sauran suna yi ke ma kiyi.

Anum dole ki dauke Kanki daga duk abinda zai yiwa matan shi wallahi kika
zama me dauke kai, na miki imani da Allah, da kanshi sai ya tambaye ki akwai abinda
ake miki wanda ranki bai so ba? Kiyi ƙoƙarin koyan sana'a a cikin gidan, karki
dogara da abin hannun shi, haka zai saka shi ya kuma girmama ki, Anum karki yarda
Aliyu ya kirani da sunan kuka. Faɗa ko wani abu.

Yin haka zai sani naji a raina kamar ba riko na bace ke, kanen shi yayun shi, da
sauran dangin shi, kina da yadda zaki janyo hankalin su gareki......
#Mai_Dambu... Body no be firewood 😔
[2/20, 9:58 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SITTIN DA UKU.

Antyn dáma
Gimbiya afrat
Ummiemie
Faidah
Maman noor
bloodynah
Ummee
Khadeee dodo SARAUNIYAR N N Z NOVELS
Maman Fátima.
Ga sakon ku nan 💝💞🤩🙏🏼

_Bawai zan bawa Anumullah damar ta wulakanta Matan Asadullah bane! Amma tun
farkon labarin na gaya muku su din zabin Iyayen shine da dangin sa! Ita kuma Matar
Da zuciyar shi ke so ce🙄 So ayi hakuri_

🏌️
SORRY DA LATECOMA 🧗
2in1

Karki dauka zaki je zaman soyayya ne, a'a zaman ibada zaki je. Duk yadda kike
tsammani kinyi rayuwar aure a baya a'a rayuwar jin dad'i kika je yi, a'a rayuwar
aure kika je, bayan shi babu wani abun da zaki yi,.ki rabauta sai ibada.duk wani
abinda zan gaya miki akan rayuwarki da aurenki ba zaki Fahimta nan kusa ba.

Amma zan miki fatan kiyi nisan kwana yadda zaki Fahimci ni'imar da Allah yayi
miki, karki yarda ki mu'amalanci abokan zamanki da sunan kishi, ki zauna dasu yadda
su zasu kasa tunkarar ki da rigima.

Kawaici da Yakana, yana matukar kawo kwarjini a cikin al'umma, kai ba kowa ba
amma sai ka rayu kowa na takatsantsar da al'amarin ka, bawai kuma kiyi girman kai
ba, dan gaki miji yana sonki, sai ki shiga tsula mishi tsiya kala kala.

Abokan zamanki, zasu iya finki sanin waye shi, ke kuma kiyi kokarin sanin meye
yake bukata, idan kika kalle shi, ki Fahimci me yake nufi, idan yayi shiru ki
nazarci meke damun shi, idan yayi gyaran murya ki halkanta da abin da yake son
fada, idan kika yi haka, ko akan idanun shi kika yi abu ba zai tab'a yarda ba, kuma
ba zai tab'a barin wani ya tozartaki.

Hadizah! Ba mamaki bai tab'a haihuwa ba sai akanki, idan har haka ce ta faru,
karki tab'a yarda abinda zasu miki ya dame ki! Kin san dan me? Na farko zasu jira
su ga ko zaki kuma haihuwar! Na biyu zasu iya tsangwamarki, na uku dangin shi zasu
iya karkatowa gare ki, abinda zaki yi sai ki shimfid'a taburma na karb'an kowa,
akwai masu kaunarki domin Allah, akwai munafukai zasu kawo miki domin tadda husuma,
akwai mutanen da zasu kare ki koda baki gurin.

Idan haka ya faru, karki tab'a yarda ki ce wani abu, (😂Wallahi bazan iya ba🤨😂 )
idan zasu dawo domin tadda abinda ya wuce, kalmar da zata fito bakinki, karta wuce.
Laa wallahi na manta, ko ban sani ba. Iya wannan kika yi toh kin gama da duk wani
abinda wani zai ce ko zasu, karki yarda wata tayi amfani da fushin ki akan mijinki.
Idan ya fara magana ki bashi hakuri, kiyi kokarin ganin kin kiyayye abinda zai
sanya shi fushi dake, Anum ki ajiye mana taurin kan nan, ki ajiye kafiyan nan don
Allah"

Yadda Umma take rokona na ajiye kafiya da taurin kai, ya sani dariya kawai, domin
dai nasan ibada zan.tafi gidan MAUDE.
***
Karfe goma saura suka iso tare da Ahmad (ila) da kuma Baban A'isha Baffa Saminu, da
wani Kawun Maude me suna Bukar, gidan shi suka sauka, aka gyara sannan Umma tayi
abinci masu kyau da ɗaukar hankalin aka kai musu,

Ba zai yiwu Su Umma su shiga ba, dole aka bari sai gobe da safe, tun
karfe hudu na asuba Umma ta fara suyar masa, tun daren jiya suka yi miyar da za a
ci Masar wanda yayi kajin turawa. Sai kunun gyada me kyau na shinkafa. Kome anyi
shi kafin karfe takwas na safe an gama, har an daura abincin rana.

Iyayen shi, da suka zo sun shigo har cikin gidan mu, kuma aka yi magana, tare
da mika musu amanata, Maman Aminu babu ruwanta dan yau baki daya ciwonta ya tashi
sosai, dan haka yayuna maza sune suka tsaya min tare da Baba Kasimu daga Badara.

Sune suka tsaya min, wunin ranar hidima ake tayi dasu. Tun daren jiya
motar da zata kwashi kayana, ta iso. Dan har da tambarin sojojin ƙasar nijar, a
cikin shi aka kwashe min kayana, wanda yan uwana suka min sabo dall, kamar na
budurwa. Har da gas da kome na amfani na, sai da suka sabunta min.

Ga kayan furnitures dina da aka min manyan kujerana. Haka suka fara tafiya,
domin su isa da wuri. Dariya Ila yayi tawa Rulwanu, dan yace sai ya bi motar kaya,
har da ɗaukar jakar shi, kuwa hakan yabi su. Yana cewa.
"Ku gayawa Anum, na rigadata isa d'akin ta."
"Zaka sha tafiya!"
"Babu damuwa,"

Haka ya suka bar garin Bauchi, sai da naji kewar shi.
...... Washi gari muma bar garin bauchi, dakyar suka rabani da jikin su Umma da
Maman Aminu, aka fitar dani. Tunda na shiga motar da ta kawo su, da zata kai mu
kano.

Tunda na kifa kaina, akan gwiwata nake kuma nazarin abinda Umma ta faɗa min,
tare da auna shi, a matsayin mizani.

Karfe sha biyu muka isa Kano, daga nan muka nufi airport.
***
Nijar.
Ya koma gurin aikin shi, sakamakon niman shi da a kayi, duk abinda yake yana yine
amma bawai yana fahimtar wasu abubuwan ba, ya shiryawa Anum abubuwan, murmushi yayi
tare da cigaba da aikin da yake gaban shi, yana waya da Hajara da take can
Damagaran akai akai.

***
Mun riga su Rulwanu isa, duk da mun isa karfe biyar na yamma sabida mun bi jirgi
ne, dan haka muna sauka motar aikin shi na soja suka zo daukar mu, aka wuce damu
gidan su. Tunda muka isa gidan, yan mata da yara Tare Da yan uwan shi na family
suka shiga zuwa kallon Anumullah.

Kaina nad'e yake da alkyaba, me kyau. A hankali na sauko daga cikin motar, a
hankali Ummul Salma ta riko hannuna, tare da riko hannun Hoor, tana murmushi, kowa
sai bin mu suke da ido, tunda muka isa shashin Liman, duk jikokin shi suna zagaye
shi.

Tunda muka shiga yake addu'a a kwanon sha, yana gamawa ya mika min, na amsa
tare da cewa.
"Nagode!"
"Toh kunga yadda ake mutuntawa, kunga na bata tace ta gode."

"Kai wannan tsohon da rikici kake, idan ka gama mu tafi da ita," juya harshe yayi
cikin Yaren buzanci yace su bashi guri.

Haka suka fita daga d'akin, har su Aunty Binta. Suna da fita,
Ya kalle ni, tare da yace. "Anumullah"
"Na'am!"
"Kudi ya baki ne dan ki so shi ko kuma ya nuna miki bakin bindiga ne?" Gyara
zama nayi sannan na kuma sunkuyar da kaina, nace mishi.
"Nagartaccen Mutum ne shi, mutum ne me hakuri da juriya, mutum ne da yasan darajar
kanshi da mutanen da suke tare dashi, Abban Isma'il, yana da hakuri da sanin ya
kamata. Iya wannan kawaicin da yayi min ya sani amincewa na bashi rayuwa ta,!"

Kafe ni yayi da ido, sannan yace.
"Indai haka ne, hausawa sunce idan kana da kyau ka kara da wanka, ki rike
Mahaifiyarshi da Amana, ki kambama ki nunawa duniya cewa ke Matan Asadullah ce, ki
nuna musu bambancin daga inda kika fito."

Bayan nan ya kira Ummul Salma, ta fitar dani, cike da mamaki.. haka yayun shi mata,
suka yi ta nuna min ni matar da yake so ce dan haka ga mahaifiyar su, itace suke
fatan na rike musu ita hannu bibbiyu.

Haka ranar muka kasance sau zuwa suke suna kallona, duk da dai ina
kunshe a cikin d'akinda aka bamu. Na sashin matar baban shi,an kawo mana abinci.
Tunda Hoor ta ga danginta, bata kuma zuwa mana ba, har dare sannan su Rulwanu suka
iso anan suAunty Safiya suka nufi inda aka nuna musu shashina.

Suka shiga jere, duk da gidan Babba ne, amma kuma part uku.
Biyu a kasa daya a sama, da manyan falo biyu, duk nashi ne. Sai da zai dawo da Ni,
ne ya ce zan zauna a sama. Suka tadda rigima, nan ma shima ya ɓalle musu, domin ya
rantse da Allah zai ajiye aikin shi, ya dauke ni da yar shi mu bar kasar baki daya
ba zasu kuma jin labarin shi ba.

Sanin zai aikata yasa suka shafa mishi lafiya, a saman aka min jera min kayana
tsaf, sannan suka fito, lokacin tara na dare yayi.

..... Koda suka dawo nasiha suka min, sosai dan sun ce zasu koma babu zaman da
zasu yi,. Washi gari da karfe tara gidan suka yi karamar walima, bayan an tashi
suka dauke ni zuwa shsshin Liman, suka ajiye mishi ni, sannan Aunty Binta tace
mishi.
"Baba gamu nan mun kawo maka Anumullah! Gata nan dai itace yar autar mu, kuma bana
tunanin ta haɗa shekaru ashirin da biyar, Baba idan Anum tayi laifi idan ka
hukuntatta ka rage mana aikin da sai mun niko gari munzo mata fada.

Idan tayi kuskuren kayi mata

Please Login or Register in order to submit comment