You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana da addinin musulunci, ya kuma isar da sakon shi,
sannan yabaku amanar matayenku, ku zauna dasu da amana, karka yarda Manzon Allah ya
kamaka da hujjar shiga hakkin aure.! Da wannan nake kawo karshen yar ƙaramar
nasihar da na kawo muku da fatan zaku karu dashi"
[1/31, 11:27 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA...!!
_Rayuwar Aure a Arewacin Najeriya_

Mai_Dambu

Kowa ya tuna bara..
BABI NA HUDU
Wani banzan shewa Ya Hafsah ta saka, cike da izgilanci sannan ta taki gabana, zata
ci zarafina.
"Akaramakiya, Hamshaqiya, Sayyida, Ustaziya Khadijah, Eyye Ashe Anum ta iya wa'azin
zaman aure bamu sani ba?

Matar da ta gaza zama a d'akinta, yarinyar da tunda kuruciyarta take
dauko magana, karewa har cikin..."

"Ke wacce irin sakarya ce? Ke wacce irin mahaukaciya ce? Yo Allah na tuba, me zaki
gaya min? Me zaki fada a gaban jama'a? Wai naka ke yake shirin tozarta ka a gaban
mutane, gaya musu wacece Khadijah! Tayu ba zasu sake gani na ba, ke kuma ga
kishiyar ki nan ta sami abin goranta miki gara ni, wallahi duk inda na shiga bana
boranta Ni mowar miji ne, tun daga cikin gidan mu ya kamata ki fahimci Ni autar
Ƴaƴa ce , bana tab'a zama bora ko a gida ko a dawa. Idan kece da wuta da aljanna
don Allah Hafsah idan nazo ki rufe aljanna ki wurgani cikin wuta. Jahila kawai."

Daga haka na mike tare da ɗaukar jakata, na fara ƙoƙarin barin gidan sunan, ban ma
kira wanda ya kawo ni ba, zunzurutun raina ya b'aci, kuma a yanzun bana son tuna
bayana ne. Idan na tuna yadda na b'ata tambarin gidan mu sai naji na gaji da kome
na rayuwa. Tunda na fita na sami napep na shiga, goge kwallar da take fuskana
nayi, tare da kallon gefen hanya.

Beauty na gani, sanye da wata swiss gefenta Alhaji Dan Azumi ne, dauke kaina
nayi tare da cewa a raina.
"Allah nagode da ka cire ni a wannan kazamar rayuwar, Allah Nagode da ka barni da
Imani na, Allah ko makiyi na, karka wurga shi cikin wannan yanayin shi yasa Bala'i
tayi mana Yawwa."

A hankali napep din ya sauke ni a kofar shagon Oga Maude, haka
kawai yau nake matukar jin kewar shi, yana cikin raina wanda ban san lokacin da
haka ya min diran mikiya ba. A hankali na sauka tare da saka hannu a jakata zan
ciro kuɗi.
"Jeka malam."

D'ago kai nayi naga Rulwani ne, dauke kai nayi, tare da nufar cikin gidan.
"Shegen rashin mutunci, ai kyace kin gode ko?"

Tab'e baki nayi tare da cewa,
"Daka biya na saka ne? Ko kuma nace maka ba zan iya biya bane? Kai kaji gurin!"
Daga haka nayi wuccewa ta cikin gidan mu, ina jin shi yana bolokoko, ina ruwan
ayagi me fada ko daga zaune a tab'a.

... Ina shiga na sami fadar Mama,.kamar zata cinye ni wai na ci mutuncin
Hafsah a cikin jama'a me yasa ba zanyi hakuri ba, dan tayi min fada har ina mata
gori, shiru nayi tare da wuccewa d'akina, ina jinta tana kuka.
"Bayan b'ata min suna da kika yi haka ma bai ishe ki ba, sai kin tozarta yar uwanki
a cikin gidan suna a gaban jama'a kika zage ta."

"Mama, wallahi ba haka bane, kawai ta gaya miki son ranta ne, amma wallahi ban
zage ta ba."

"Ki min shiru! Karki kuma gaya min maganar banza, taya zaki ci mutuncin yar
uwarki a gaban jama'a? Daga gaya miki gaskiya, ke wacece da ba a gaya miki gaskiya
ba. Ni zaki kawowa karya!

Wallahi zan saka Bashir yayi miki mugun duka, sakarya kawai mara hankali ba
gwara ita ba, tana zaune a dakin mijinta, kuma tana min duk wani abinda ya dace ke
ince rashin rabonki ne ya hanaki Fahimtar Arzikin da Allah yayiwa mijinki."

Kallon ta nayi baki sake, hawaye na zuba daga idanuna, lekowa Umma da Goggo
Hamah, tare da kallon Mama ta sani a gaba zata dake ni.

"Toh ai sai ki kyaleta, lokacin da ta kika lalata abinki ai babu wanda ya sani,
yanzun da kuma duniya tayi muku juyin masa shine bari ki goranta mata, ai duk
abinda Khadija tayi bata da laifin ki ne, kwaɗayin duniya ya kai ku ya baro ku.
Yanzun kin wani zo zaki dame mu da Hausar ki da bata ishe ki ba, don Allah ki kyale
jama'a su huta haba don Allah."

Juyawa tayi tare da fita, Mama ta zuba min ido, cikin tsannanin b'acin
rai, yau akai na ake gaya mata magana, kafin na ankara sai ganinta nayi tana zubda
kwalla. Jikina ne ya dauki rawa tare da girgiza mata kai nima ina kuka.

"Don Allah!"
"Ya isa haka! Kije na cire hannuna daka kanki, kije duniya ta ishe ki riga da
wando, Anum Ni ake gayawa magana sabida ke? Idan dan soyayyar da na nuna miki ne
kije na barki da duniyar." Tana kaiwa aya ta ficce, ina tsaye a inda ta barni wani
irin kuka ne yazo min tare da nadama mara amfani, zama nayi cikin mutuwar jiki. Duk
da kiran sallah da ake bai sanya na tsayar da kuka ba.

Na kai minti goma sha biyar, har aka fito masalaci ina kuka,
kafin na mike na bar gurin, fitowa nayi na yi alola na koma cikin dakin, tunda na
zauna nake kuka, ina taryo abubuwan da suka gabata na rayuwata, da ace a lokacin ta
bata fahimci kallon tausayin da Baba Malam yake mata ba, me yasa bata fahimci
kallon tausayin da Maude yake mata ba.

Idan ta tuna lokacin da yake Maude yake cewa.
"Khadijah! Wannan rayuwar da kika dauka karya ce, Khadijah ni me kaunarki ne, kuma
ina kaunar farin cikin ki ne, KHADIJAH zan iya samun matar da suka fiki, Khadijah
ina da su, amma zuciyata bata kansu, sai ke don Allah ki taimake ni ki haifa min
cikin jikin ki lafiya Wallahi zan baki mamaki a rayuwarki!"

Dariya ta saka tare da gyara kwanciyarta bayan ta matsa daga inda yake, ta juya
mishi baya tace.
"Cikin ƙaddara ko? Toh zan haifa maka shi meye a ciki daga duniya sai Abuja, zan
haifa maka abinka amma wallahi ka sani babu rabon sharyawa a jikina, na gaya maka.
Duk abinda zaka yi kayi daga yanzun amma ba zan shayar maka da abinda zan haifa ba.
Me kake dashi? A cikin su Hishmah Dubai aka kai ni sayayya kayan haihu,a can na
haihu kai me ka tara? Me kake bukatar nayi da Kaddararren auren ka, banda cin Amana
taya zamu shirya abu da kai ka dawo kace baka san zance ba.

Sake ka daura aniyar sai ka tozartani shine ka dawo da cewa ba zaka sake ni ba,
wallahi zaka rabu dani domin tun fil azale bana kaunarka, kuma bana sonka ka gane
mana..."

Jikin shi na rawa ya matso kusa da ita, tare da janyo ta jikin shi.
"Karki ce haka! Naga soyayyar gaskiya a idanunki don Allah karki ce baki kaunata,
ni ana sonki zan cigaba da sonki, KHADIJAH Dubai fa, haba sai dai England kayan
haihuwar abin cikinki, wallahi na shirya baku farin ciki, zan d'aga ki daga cikin
gidan na mai dake gidan da kike bukatar rayuwa, Khadijah zan baki motar da tafi
wanda na amsa, don Allah ki amince dani. Mu rayu lokacin da na gayawa Dattijo kina
da ciki, cewa yayi na kai ki nijar ki haihu, amma nasan ba zaki tab'a amincewa ba,
don Allah ki taimake ni, ki kula da lafiyar abin cikin ki da kuma ni. Kaddarar ki
ce ta kawo ni, da kuma kaddarar cikin jikinki ya kawo ni tsawon shekaru a garin
bauchi.

Ina da rayuwa da dangina, don Allah karki juya min baya, ina sonki zan baki
kome kece matar da nafi so da kaunarta, don Allah karki ce zaki juya.."

"Maude! Wallahi kaji na rantse maka billahil azim, ba zan shayar da wannan
wulakantattacen cikin jikina ba, ai kaci iya kudinka, kuma ka sami abinda kake
bukata, ba dai jikina bane damuwarka ai samu.

Kuma nasan har abada ba zaka kuma sami mace irina ba, dan haka matsa min
na sauka daga hanya na sauka zan kwanta a kasa ka rike katifar, tunda dashi kazo
yawon cira ko? Toh indai zai kara maka jarin shayi da burodi ka dauka kara, dan na
san fatara da talauci ya kawo ka najeriya ko? Gashi daga zuwa ka auri Sumayyah,
gashi nan kazo ka kara dani."

Lumshe manyan idanun shi yayi cikin damuwa lashe bakin shi yayi, tare da zuba
mata ido, zata sauka ya dawo da ita, hannu d'aya ya saka ya zare rigar jikinta,
bai barta ba sai da ya sami dukkan nutsuwar da yake bukata, sannan ya janye daga
gareta ya sauka zuwa ban daki ya barta tana shashekar kuka, cike da bakin ciki.

..... "Anum!!!" Kiran da Umma tayi mata ya katse mata tunanin da take yi ta
mike a hankali ta fita, tare da mik'ewa tsaye ta fito waje.
"Kina ina Mamarku ta fadi innalillahi wa'inna ilaihi rajioun." Ji tayi kamar
zuciyarta zata fado daga kirjinta maza tayi ta rike kirjin ta, jikinta na rawa,
numfashinta yana sama da kasa.
"Ke kan kiyi asara rayuwa! Uwarki ma ba zaki barta ta rayu cikin salama ba, sai kin
kashe ta kamar yadda kika kashe mun d'an uwa, wannan wani irin masifa ce.

Anya babu hannun a jikinki, yarinya sai kace yar Allah bani."

Had'iye yawu tayi tare da kai hannu zata tab'a Maman su, aka buge
hannunta, aka yi tare da nuna ta da yatsa.
"Ke kan! Wallahi bamu san wani irin zunubi muka yi aka bamu ke ba, kin kashe mana
mahaifi yanzun ma mahaifiyar mu baki barta ba Anya Anum kina niman lahira kuwa? Toh
kar na kusku..."

"Bashir! Anya kuna yiwa kanku adalci kuwa? Meye laifin Anum, ai tayi kyan
kai."

"Zainabu ki barshi yayi magana! Me aka yi da yarinyar da ta kashe Ubanta da
bakin cikin! Wallahi ka mata shegen duka, me zayi da ita." Inji Goggo Hamah,
"Dakata Hamah,ke baki kashe wutar rikicin gidan kiba, ba zaki zo kice zaki kashe
na wasu ba, dan haka ki ja bakin ki, babu ruwan ki a wannan karon, domin ba zaki
tadda husuma ki tafi ki bar mu cikin Jalala ba. Sai mai kuna meye tayi muku?
Wannan yarinyar bata muku kome ba kuke tsana da tsangwama? Meye laifinta? Anan
Hafsat Da Safiya jikin su na rawa suka kira uwarku, suna gaya mata abinda ya faru!
Kai Jama'a? Anum ce baku son gani a raye ko Uwarku? Tunda nake da Anum aurenta
biyar bata tab'a zuwa gidan nan da sunan kawo kara ba. Kai kana ihun ka karta tab'a
ta akan me? Uwarta ce yarinyar nan tunda mutumin nan ya tafi da tarehi bata kuma
barci ba wai kasheta kuke so zaku yi ne? Toh idan Anum bakin cikinku bai kasheta ba
toh uwarku zaku kashe tunda ba zaku tab'a dauka maganar matsalar ku da Anum kuna
gaya mata ba, wallahi ita bata kashe ta ba, toh ku hankalin ku ya kwanta."

Daga haka ta koma d'akinta ta dauko hijab ɗinta, ta saka, tare da cewa.
"Ka riketa mu kaita bakas!"

Jikin shi ne yayi masifar sanyi, duk masifar da yake ji zai yiwa Anum sai
gashi Umma ta dakatar dashi tare da gaya mishi gaskiya, nima na basu zuwa
asibitin,muna zuwa aka karb'eta, cikin lokaci ƙalilan suna fara bata kulawa na
musamman, ina kallon kome kamar kiftawa da bismillah, kome ya lalace.

Dakyar na dawo gida, na kwanta, can cikin dare. Garin yayi sanyi kasancewar
muna cikin lokacin damina ne, dan muna dawowa daga asibiti aka fara ruwan sama,
wani irin feelings naji kamar me, tun bayan tafiyar Maude ban kuma jin wani abu a
kan shi ba, sai yau. Dan haka ina kwance har barci yayi nasarar tafiya dani.

Wani irin mafarki nayi da Maude kafin kace me, har naji Ni cikin wani
duniya na daban, tsawar da aka buga wanda yayi sanadiyar farkawa na daga mafarki
mafarkin da nake, tashi nayi zaune, sannan naji gaba daya bana cikin nutsuwa, tashi
nayi na tab'a flask dina na ji da ruwan zafi, dan haka na juye a babban butana. Na
fito tsakar gida, a hankali na nufi ban daki nayi wankan tsarki, sannan na fito a
hankali ina rawan sanyi, walkiyar da aka yi ya sani ja da baya, sakamakon kicibis
da nayi da...🤨[2/2, 9:41 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA ASHIRIN DA HUDU

*Godiya da fatan Alkhairi! Masoyan Zanen Qaddara ta 💞🤔 Me akayi da maza karuwa taga
mace da ciki🤭 Ku biyo Ni dan ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare! MOM SAYEED
how market naga kinyi shiru Eyyeeeee 😜 My Hafsat mom Khairat*
______________________________

"Alaji baka auri yar mutane domin ka kashe musu ita ba, asalima an baka ne sabida
ganin ka cancanci haka! Idan kace zaka biyewa halin mace wata rana sai ka fita layi
kana sumbatu, ita mace duk girmanta duk shekarun ta, yanzun dan sha tara zai iya
tsarata kuma ta tsaru!

Karka yi tunanin dan ka rabata da gidan su akan sadakin dubu hamsin kace
zaka maida da baiwa, ita ba baiwa bace Y'a ce. Karka ga dan tsaya ta nace sai kai
kayi tunanin bata da wasu masoyan ne! Idan da maza zasu yi tunanin cewa ina da
Uwar da ta haife ni mace ce! Ina da kane mata, kuma ba zan iya d'aga hannu na dake
su ba, tabbas da babu wanda zai wulakanta mace.

Amma kai ne baka da aiki ke Jummai, ina butata Jummai takalmi na, jummai tazoje
na. Haba bawan Allah, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Gidan shi har dashi
ake girki. Matan na aiki shima yana aiki, gidan Manzon Allah zunzurutun soyayya
idan yayi alola zai tafi masallaci duk macen da ya gamu da ita sai ya sumbace ta.

Me yasa mu ba zamu iya wa wannan tausayin ba, a'a tun daga lokacin da aka
aura mishi ita dan karta rena shi sai ya tsiro da wani halin banzan na fushi. Ka
dauko yar mutane ka ajiyeta a gida shin ita ba mutum bace, da zaka na b'ata rai dan
karta rena ka, sai dare yayi kace Laraba bude min zani, anya kayi adalci. Idan ka
dauki mace ta wannan sigar har abada zata na jin haushin ka, tayi ta addu'ar Allah
ya raba ku tunda bata da amfani a gurin ka sai na jima'i. Maza kuji tsoron Allah,
maza ku mu'amalanci matar ku da adalci.

Karka yarda matar ka ta maka kallon mara adalci, ka rike matar ka kamar yadda
Manzon Allah yace.

Wallahi karka yarda Allah ya kamaka da laifin ka zalince ta, mace ba a mikar da
ita da karfin tsiya, da hikima zaka mikar da ita, a duniya kowa yasan babu shu'uma
sama da mace, amma kuma kowa yasan babu halitta mafi raunin zuciya irin mace, matar
da kawai da layin baiti daya ka sace zuciyarta, ka gwada mai da gidan ka wani
yanayi na daban sai zaman gidan ya isheka. Dan haka nake baku shawara da mu rike
abokan zaman mu da amana,. musamman matan mu haka suma matan su rike mazan su da
amana wani tsabar rashin tsoron Allah, shi gashi nan dan dukununu. Amma matar shi
kullum burin shi ya ganta fess bayan shi bai gyara ta gani ba, idan ayi magana yace
feee. Kai kana son gyara amma ba zaka gyara ba, sai kaje waje ka dawo kana zare
ido. Wallahi sai ka ga sani namijin ya sami mace kamar jaka, bayan yana da kanwar
shi da Yar shi idan kaga anyiwa kanwarka ko Uwarka zaka ji dadi wannan abun fa
Simple And easy ne kana tab'awa ko kaho ne a kanka sai an rama,mafi alkhairi karka
cutar da yar wasu kai ma Allah sai ya tsare naka,karka yarda ka tab'a domin za a
rama mata, kai ko zina ce sai ka biya shi, balle cin zali me sauki ne a rama mata."

Yayi nasiha sosai ga ma'aurata, sannan aka tashi taron Anum tayi laushi kamar ba
ita ba, burinta ta isa gidan ta gaji, da wannan tsayuwar.

----
"XOXO baki ga kayanta bane yayi kaya da" tsuka tayi, sannan tace.
"Ba kayan bane matsala ta, auren ne bana son tayi, asali ma Ni bana son Anum ta
sami cigaba da nutsuwa a rayuwarta, gani nake zata wuce ni. Duk inda nake tsammani
samun damar nasara sai na ga Wancan tinkiyar ta wuce Ni.

. Waye ya tab'a kawowa Wancan me shayin zai yi abinda yayi mata,walimar nan da
abinda za a raba shi ya dauki nauyin shi.

Gaskiya iyayen ta, ba karamin shige shige sai da suka sa shi mata
b'arnan kudi, ya kika ga idan na lalata kome auren ya dawo kaina?"

Cikin tsoro da ruwan ciki, tace.
"Eh mana haka yayi, aure me shayin."
"Ke na aure me shayin zaki ce, ba mu aure ba, ki gane, tarawa da ragewa indai ba so
kike nace anyi asarar tara ba."

...... Ana gurin Walima su Aunty Binta da matan kanenta suka nufi gidan
da Anum zata zauna, matan abokan maude suka bude musu, mamaki ne ya kashe su,
sakamakon ganin yadda ka tsara cikin gidan kamar a g.r.a ko wani unguwar bauchi.

A hankali suka shiga cikin gidan suka yi, cikin uku daya na gefen shi
wanda aka raba da kofar glass, har kana iya hango falon wanda aka zuba mishi kayan
alatu, domin wata babban cinema tv ne a falon. Sai wasu irin kujerun alfarma wanda
ya watsa su a falon tare da labulen da zaka gani kasan cewa ma mallakin kayan gurin
yasan meke damun shi.

"Toh kenan ai da ya gaya mana falo biyu ne da..."
"A'a kin ya shigo gari cirani dole ya nunawa duniya shi din yana son auren yar
kasa." Inji matar Musa, wato Zeenatu.

Kallon ta Aunty Binta tayi sannan tace mata.
"Bana son rashin hankali!"
Sannan suka nufi kitchen, inda shima aka mishi tsarin shi irin na yan gayu, kai
gidan ya tafi da Zuciyar Aunty Binta har take gaya musu idan.

A hankali suka shiga gyara gidan, dama an kawo kayan tun shekaranjiya, dan haka
aka shiga kimtsa ko ina, tare da shirya kayan, masu saka labule suka zo aka saka
dasu.

Sosai suka kintsa ko ina, kitchen biyu yayi mata, akwai wani a tsakar gidan
wanda ya kasance ma daidaici ne.

Sai bayan gidan tsakar gida yadda ba za a dame su a cikin gidan ba, akwai daki
ma a tsakar gidan, cikin kuma dakuna uku ne daya na shi daya nata, daya kuma an
zuba kayan da ba zasu yi amfani akan lokaci ne, dan haka bayan sun gama wajen karfe
bakwai suka rufe gidan, sun kashe kudi na fitar hankali domin gas ɗinta babba ne,
har zata iya gasa Cake.

Sannan suka fito zuwa gida, suna shiga suka same Baba Hama tazo, tana
ta faɗa.
"Wato Bello dan bani da kudi shine ba zaka gaya min zaka aurar da yar ka ba, sai
dai naji labarin a wata uwa duniya."

Nan tayi ta fad'a, Malam da Baba Hama, y'ay'an maza ne, dan dakin su malam shi daya
aka haifa, amma yana da yan uwan kuma suma sun zo wanda suke Uba daya. Dake mutum
ne me zumunci take gidan ya cika da yan uwan da abokan arziki.

Anum tana kwance akan cinye shi, ta daura kanta akan cinyar shi. Sai kuka take,
tab'e baki Baba Haka tayi sannan tace mishi.
"Toh Bello idan bata sabon auren sai ta zauna kujika ta kamar kanwa."

Shafa kanta yake, cikin murmushi.
"Anumullah! Kukan ba zai kare bane? Idan kina kukan sai naga kamar akwai abinda na
tauye miki! Kiyi shiru kinji, kije Allah ya tsare gabanki da Bayanki, Insha Allah
babu namijin da zai wulakanta min ke da Izinin Ubangiji.
Ki zauna dashi da zuciya d'aya Allah zai albarkaci zaman ku. Bana son
kawo ƙara, bana son rashin kunya, ba sa'anki bane ki girmama shi kamar yadda
Ummanki take girmama al'amarina." Yadda yake mata nasihar sai jikinka ya mutu.
Bayan ya gama aka kaita dakin Umma, da take ciki uwar daki.

Kallonta Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, musamman da ta fahimci halin da
yarinyar ake ciki, shafa kanta tayi sannan tace mata.
"Zauna ku kuma, ku bani guri."
Fita suka yi, umma ta kawo mata, ruwan addu'o'in sannan ta d'iga zuma, ta bata
tasha kafin ta kuma dauko wani ruwan rubutu, ta bata tashanye. Sannan a lokacin ta
dauko kunun tsamiya ta mika mata, tana sha tana kuka.
"Kina son kullum ana kawo miki kunun tsamiya da na gyada ne?"
"Eh Umma na,"
"Dumame fa?"
"Duk abinda zai fito hannunki ina son shi!"
Shafa kanta tayi sannan tace.
"Malam ya shirya miki bazata, amma kuma yace sai kin zauna lafiya a gidan mijinki,
idan kuma kika ki zama toh ni dai ban san me zance ba, amma zaman da zaki yi a
dakin mijinki shi zai baki damar samun wannan abun.

Karki yarda kiyi abinda zai fasa miki kyautar, babban kyauta ce kuma, Allah
yana kallonki idan kika zalinci mijinki, ba zai barki." Umma tayi mata nasiha me
matukar shiga jiki, kuma dama malam aikin hajji ya biya mata, shine abinda yayi
mata na aure domin kome yayunta sun mata, babu abinda zai mata sai dinkunan ne da
ya sayo atamfofi ya zuba mata su..yasa Rulwanu ya kai gurin telanta basu sani ba.

A yanzun ma lace din jikinta na shine wanda yayi mata a cikin kayan, bayan ta
fito dakin Umma, hannunta dauke da wani zoben gwal din Umma.
"Anum me kike so a dakin?".ta tambaye ta, tare da danne kukarta. Dan itama tun Anum
bata tafi ba ta fara kewarta.
"Umma na, babu"
"Duba dai ba zaki rasa ba"
Haka ta tashi ta duba nan ta duba can bata sami kome ba, sai sauka da idanunta yayi
akan zoben gwal din, a hankali ta kalle ta tana zubda kwalla tace.
"Ba zaki bani ba, umma Na!".
"Me kike so?"
"Zoben hannun.."
Zare shi tayi tare da saka mata, dama Aunty Rabi ce ta saya mata, dan dukkan su,
sun saya mata, haka ta saka mata, wai ita Umma a nata tunanin idan tayi haka
yarinyar hankalinta zai kwanta da gidan mijinta, kuma haka take fatan samu.

Bayan sun gama, aka mikata dakin Maman Aminu.
"Ni bani da Abinda zan gaya mata, kome ba, tasan abinda na umarceta idan ta kiyayye
ni da ita zamu zauna lafiya, idan bata kiyaye ba. Toh ai tasan sharadi na."

Daga haka ta koma d'akinta, kallon bayanta Anum tayi, tare da sauke kanta kasa,
da idanunta da suka yi jajjur. Allah ya bata Umma ne domin ta tayata kuka, haka
kuma ya bata Maman ta domin tasata kuka, ta zab'i muradun zuci sama da ita kanta,
ta nuna mata ba lallai bane dai.kayi abinda zai faranta ran kowa, matukar zaka
faranta ran ka.

A zuwa yanzun ta Fahimci wacece Umma Mariyah, wacce Mama Hauwa, jin hannun
Abubakar a kafad'arta ya sata sake kuka. Haka yayunta mazan wannan ya rike ta,
wannan ya kamo hannunta, koda aka fita kis ta, basu wuce da ita gidan ta ba.
. Sai da suka zaga da ita ta tashan babaye tare da zagayowa ta titin baba sidi
primary school, suka fito ta kofan ran sannan suka

Please Login or Register in order to submit comment