You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan aka yiwa Yarka haka zaka
ji dadi? Zaka yi farin ciki? A'a kawai dai ka auro mace kayi ta gana mata azaba,
daga karshe kace kai ba zaka zauna da ita ba, sai ta biyaka kudin da ka kashe, anya
kana tuna bayanka kuwa? Toh idan barci kake ka farka, tuni. Domin kuwa idan ka sake
Allah ya kamaka da hakkin wulakanta aure, sai kayi DANASANI mara amfani.!

Karku manta da wasiyyar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, idan yace
yafita hakkin mu, ya zo mana da addinin musulunci, ya kuma isar da sakon shi,
sannan yabaku amanar matayenku, ku zauna dasu da amana, karka yarda Manzon Allah ya
kamaka da hujjar shiga hakkin aure.! Da wannan nake kawo karshen yar ƙaramar
nasihar da na kawo muku da fatan zaku karu dashi"
[1/31, 11:27 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA...!!
_Rayuwar Aure a Arewacin Najeriya_
Mai_Dambu

Kowa ya tuna bara..
BABI NA HUDU
Wani banzan shewa Ya Hafsah ta saka, cike da izgilanci sannan ta taki gabana, zata
ci zarafina.
"Akaramakiya, Hamshaqiya, Sayyida, Ustaziya Khadijah, Eyye Ashe Anum ta iya wa'azin
zaman aure bamu sani ba?

Matar da ta gaza zama a d'akinta, yarinyar da tunda kuruciyarta take
dauko magana, karewa har cikin..."

"Ke wacce irin sakarya ce? Ke wacce irin mahaukaciya ce? Yo Allah na tuba, me zaki
gaya min? Me zaki fada a gaban jama'a? Wai naka ke yake shirin tozarta ka a gaban
mutane, gaya musu wacece Khadijah! Tayu ba zasu sake gani na ba, ke kuma ga
kishiyar ki nan ta sami abin goranta miki gara ni, wallahi duk inda na shiga bana
boranta Ni mowar miji ne, tun daga cikin gidan mu ya kamata ki fahimci Ni autar
Ƴaƴa ce , bana tab'a zama bora ko a gida ko a dawa. Idan kece da wuta da aljanna
don Allah Hafsah idan nazo ki rufe aljanna ki wurgani cikin wuta. Jahila kawai."

Daga haka na mike tare da ɗaukar jakata, na fara ƙoƙarin barin gidan sunan, ban ma
kira wanda ya kawo ni ba, zunzurutun raina ya b'aci, kuma a yanzun bana son tuna
bayana ne. Idan na tuna yadda na b'ata tambarin gidan mu sai naji na gaji da kome
na rayuwa. Tunda na fita na sami napep na shiga, goge kwallar da take fuskana
nayi, tare da kallon gefen hanya.

Beauty na gani, sanye da wata swiss gefenta Alhaji Dan Azumi ne, dauke kaina
nayi tare da cewa a raina.
"Allah nagode da ka cire ni a wannan kazamar rayuwar, Allah Nagode da ka barni da
Imani na, Allah ko makiyi na, karka wurga shi cikin wannan yanayin shi yasa Bala'i
tayi mana Yawwa."

A hankali napep din ya sauke ni a kofar shagon Oga Maude, haka
kawai yau nake matukar jin kewar shi, yana cikin raina wanda ban san lokacin da
haka ya min diran mikiya ba. A hankali na sauka tare da saka hannu a jakata zan
ciro kuɗi.
"Jeka malam."

D'ago kai nayi naga Rulwani ne, dauke kai nayi, tare da nufar cikin gidan.
"Shegen rashin mutunci, ai kyace kin gode ko?"

Tab'e baki nayi tare da cewa,
"Daka biya na saka ne? Ko kuma nace maka ba zan iya biya bane? Kai kaji gurin!"
Daga haka nayi wuccewa ta cikin gidan mu, ina jin shi yana bolokoko, ina ruwan
ayagi me fada ko daga zaune a tab'a.

... Ina shiga na sami fadar Mama,.kamar zata cinye ni wai na ci mutuncin
Hafsah a cikin jama'a me yasa ba zanyi hakuri ba, dan tayi min fada har ina mata
gori, shiru nayi tare da wuccewa d'akina, ina jinta tana kuka.
"Bayan b'ata min suna da kika yi haka ma bai ishe ki ba, sai kin tozarta yar uwanki
a cikin gidan suna a gaban jama'a kika zage ta."

"Mama, wallahi ba haka bane, kawai ta gaya miki son ranta ne, amma wallahi ban
zage ta ba."

"Ki min shiru! Karki kuma gaya min maganar banza, taya zaki ci mutuncin yar
uwarki a gaban jama'a? Daga gaya miki gaskiya, ke wacece da ba a gaya miki gaskiya
ba. Ni zaki kawowa karya!
Wallahi zan saka Bashir yayi miki mugun duka, sakarya kawai mara hankali ba
gwara ita ba, tana zaune a dakin mijinta, kuma tana min duk wani abinda ya dace ke
ince rashin rabonki ne ya hanaki Fahimtar Arzikin da Allah yayiwa mijinki."

Kallon ta nayi baki sake, hawaye na zuba daga idanuna, lekowa Umma da Goggo
Hamah, tare da kallon Mama ta sani a gaba zata dake ni.

"Toh ai sai ki kyaleta, lokacin da ta kika lalata abinki ai babu wanda ya sani,
yanzun da kuma duniya tayi muku juyin masa shine bari ki goranta mata, ai duk
abinda Khadija tayi bata da laifin ki ne, kwaɗayin duniya ya kai ku ya baro ku.
Yanzun kin wani zo zaki dame mu da Hausar ki da bata ishe ki ba, don Allah ki kyale
jama'a su huta haba don Allah."

Juyawa tayi tare da fita, Mama ta zuba min ido, cikin tsannanin b'acin
rai, yau akai na ake gaya mata magana, kafin na ankara sai ganinta nayi tana zubda
kwalla. Jikina ne ya dauki rawa tare da girgiza mata kai nima ina kuka.

"Don Allah!"
"Ya isa haka! Kije na cire hannuna daka kanki, kije duniya ta ishe ki riga da
wando, Anum Ni ake gayawa magana sabida ke? Idan dan soyayyar da na nuna miki ne
kije na barki da duniyar." Tana kaiwa aya ta ficce, ina tsaye a inda ta barni wani
irin kuka ne yazo min tare da nadama mara amfani, zama nayi cikin mutuwar jiki. Duk
da kiran sallah da ake bai sanya na tsayar da kuka ba.

Na kai minti goma sha biyar, har aka fito masalaci ina kuka,
kafin na mike na bar gurin, fitowa nayi na yi alola na koma cikin dakin, tunda na
zauna nake kuka, ina taryo abubuwan da suka gabata na rayuwata, da ace a lokacin ta
bata fahimci kallon tausayin da Baba Malam yake mata ba, me yasa bata fahimci
kallon tausayin da Maude yake mata ba.

Idan ta tuna lokacin da yake Maude yake cewa.
"Khadijah! Wannan rayuwar da kika dauka karya ce, Khadijah ni me kaunarki ne, kuma
ina kaunar farin cikin ki ne, KHADIJAH zan iya samun matar da suka fiki, Khadijah
ina da su, amma zuciyata bata kansu, sai ke don Allah ki taimake ni ki haifa min
cikin jikin ki lafiya Wallahi zan baki mamaki a rayuwarki!"

Dariya ta saka tare da gyara kwanciyarta bayan ta matsa daga inda yake, ta juya
mishi baya tace.
"Cikin ƙaddara ko? Toh zan haifa maka shi meye a ciki daga duniya sai Abuja, zan
haifa maka abinka amma wallahi ka sani babu rabon sharyawa a jikina, na gaya maka.
Duk abinda zaka yi kayi daga yanzun amma ba zan shayar maka da abinda zan haifa ba.
Me kake dashi? A cikin su Hishmah Dubai aka kai ni sayayya kayan haihu,a can na
haihu kai me ka tara? Me kake bukatar nayi da Kaddararren auren ka, banda cin Amana
taya zamu shirya abu da kai ka dawo kace baka san zance ba.

Sake ka daura aniyar sai ka tozartani shine ka dawo da cewa ba zaka sake ni ba,
wallahi zaka rabu dani domin tun fil azale bana kaunarka, kuma bana sonka ka gane
mana..."

Jikin shi na rawa ya matso kusa da ita, tare da janyo ta jikin shi.
"Karki ce haka! Naga soyayyar gaskiya a idanunki don Allah karki ce baki kaunata,
ni ana sonki zan cigaba da sonki, KHADIJAH Dubai fa, haba sai dai England kayan
haihuwar abin cikinki, wallahi na shirya baku farin ciki, zan d'aga ki daga cikin
gidan na mai dake gidan da kike bukatar rayuwa, Khadijah zan baki motar da tafi
wanda na amsa, don Allah ki amince dani. Mu rayu lokacin da na gayawa Dattijo kina
da ciki, cewa yayi na kai ki nijar ki haihu, amma nasan ba zaki tab'a amincewa ba,
don Allah ki taimake ni, ki kula da lafiyar abin cikin ki da kuma ni. Kaddarar ki
ce ta kawo ni, da kuma kaddarar cikin jikinki ya kawo ni tsawon shekaru a garin
bauchi.
Ina da rayuwa da dangina, don Allah karki juya min baya, ina sonki zan baki
kome kece matar da nafi so da kaunarta, don Allah karki ce zaki juya.."

"Maude! Wallahi kaji na rantse maka billahil azim, ba zan shayar da wannan
wulakantattacen cikin jikina ba, ai kaci iya kudinka, kuma ka sami abinda kake
bukata, ba dai jikina bane damuwarka ai samu.

Kuma nasan har abada ba zaka kuma sami mace irina ba, dan haka matsa min
na sauka daga hanya na sauka zan kwanta a kasa ka rike katifar, tunda dashi kazo
yawon cira ko? Toh indai zai kara maka jarin shayi da burodi ka dauka kara, dan na
san fatara da talauci ya kawo ka najeriya ko? Gashi daga zuwa ka auri Sumayyah,
gashi nan kazo ka kara dani."

Lumshe manyan idanun shi yayi cikin damuwa lashe bakin shi yayi, tare da zuba
mata ido, zata sauka ya dawo da ita, hannu d'aya ya saka ya zare rigar jikinta,
bai barta ba sai da ya sami dukkan nutsuwar da yake bukata, sannan ya janye daga
gareta ya sauka zuwa ban daki ya barta tana shashekar kuka, cike da bakin ciki.

..... "Anum!!!" Kiran da Umma tayi mata ya katse mata tunanin da take yi ta
mike a hankali ta fita, tare da mik'ewa tsaye ta fito waje.
"Kina ina Mamarku ta fadi innalillahi wa'inna ilaihi rajioun." Ji tayi kamar
zuciyarta zata fado daga kirjinta maza tayi ta rike kirjin ta, jikinta na rawa,
numfashinta yana sama da kasa.
"Ke kan kiyi asara rayuwa! Uwarki ma ba zaki barta ta rayu cikin salama ba, sai kin
kashe ta kamar yadda kika kashe mun d'an uwa, wannan wani irin masifa ce.

Anya babu hannun a jikinki, yarinya sai kace yar Allah bani."

Had'iye yawu tayi tare da kai hannu zata tab'a Maman su, aka buge
hannunta, aka yi tare da nuna ta da yatsa.
"Ke kan! Wallahi bamu san wani irin zunubi muka yi aka bamu ke ba, kin kashe mana
mahaifi yanzun ma mahaifiyar mu baki barta ba Anya Anum kina niman lahira kuwa? Toh
kar na kusku..."

"Bashir! Anya kuna yiwa kanku adalci kuwa? Meye laifin Anum, ai tayi kyan
kai."

"Zainabu ki barshi yayi magana! Me aka yi da yarinyar da ta kashe Ubanta da
bakin cikin! Wallahi ka mata shegen duka, me zayi da ita." Inji Goggo Hamah,
"Dakata Hamah,ke baki kashe wutar rikicin gidan kiba, ba zaki zo kice zaki kashe
na wasu ba, dan haka ki ja bakin ki, babu ruwan ki a wannan karon, domin ba zaki
tadda husuma ki tafi ki bar mu cikin Jalala ba. Sai mai kuna meye tayi muku?
Wannan yarinyar bata muku kome ba kuke tsana da tsangwama? Meye laifinta? Anan
Hafsat Da Safiya jikin su na rawa suka kira uwarku, suna gaya mata abinda ya faru!
Kai Jama'a? Anum ce baku son gani a raye ko Uwarku? Tunda nake da Anum aurenta
biyar bata tab'a zuwa gidan nan da sunan kawo kara ba. Kai kana ihun ka karta tab'a
ta akan me? Uwarta ce yarinyar nan tunda mutumin nan ya tafi da tarehi bata kuma
barci ba wai kasheta kuke so zaku yi ne? Toh idan Anum bakin cikinku bai kasheta ba
toh uwarku zaku kashe tunda ba zaku tab'a dauka maganar matsalar ku da Anum kuna
gaya mata ba, wallahi ita bata kashe ta ba, toh ku hankalin ku ya kwanta."

Daga haka ta koma d'akinta ta dauko hijab ɗinta, ta saka, tare da cewa.
"Ka riketa mu kaita bakas!"

Jikin shi ne yayi masifar sanyi, duk masifar da yake ji zai yiwa Anum sai
gashi Umma ta dakatar dashi tare da gaya mishi gaskiya, nima na basu zuwa
asibitin,muna zuwa aka karb'eta, cikin lokaci ƙalilan suna fara bata kulawa na
musamman, ina kallon kome kamar kiftawa da bismillah, kome ya lalace.
Dakyar na dawo gida, na kwanta, can cikin dare. Garin yayi sanyi kasancewar
muna cikin lokacin damina ne, dan muna dawowa daga asibiti aka fara ruwan sama,
wani irin feelings naji kamar me, tun bayan tafiyar Maude ban kuma jin wani abu a
kan shi ba, sai yau. Dan haka ina kwance har barci yayi nasarar tafiya dani.

Wani irin mafarki nayi da Maude kafin kace me, har naji Ni cikin wani
duniya na daban, tsawar da aka buga wanda yayi sanadiyar farkawa na daga mafarki
mafarkin da nake, tashi nayi zaune, sannan naji gaba daya bana cikin nutsuwa, tashi
nayi na tab'a flask dina na ji da ruwan zafi, dan haka na juye a babban butana. Na
fito tsakar gida, a hankali na nufi ban daki nayi wankan tsarki, sannan na fito a
hankali ina rawan sanyi, walkiyar da aka yi ya sani ja da baya, sakamakon kicibis
da nayi da...🤨
#Mai_Dambu...
[1/31, 11:27 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..

Kuskuren Baya...
BABI NA BIYAR
Cikin wani irin faduwar gaba, ta tsaya tana kallon Goggo Hamah, sannan ta wuce
d'akin ta, ta rufe kofar ta kirjinta na bugawa, Allah yasa tayi wanka da alola ne.

Sallar nafilla tayi, sannan ta kwanta cike da tunanin makomar rayuwarta, a
hankali barci ya dauke ta.
---
Kiran sallar farko, ya tashe ta. A hankali ta mike tare da nufar waje ta kama ruwa
da alola, sannan ta nufi d'akinta ta fara sallah, kasancewar babu Umma da Mama yasa
tana idarwa ta fito daga d'akinta ya shiga hada musu abin karyawan tana idarwa ta
tattara ta kai d'akinta, sannan tayi wanka ta shirya cikin atamfa riga da skirt,
ta daura babban hijab dark pink, karamin heart face dinta ne ya fito sosai.

A hankali ta dauki basket din zata fita, taga yayunta uku har da
Rulwan, rike da manyan bulalai. Cire nikkab din fusakarta tayi tare da kafe su da
ido.
"A gidan uban wa kika kwana juya?" Kallon Bashir da Musa tayi, tare da
cewa.
"Ni kuma? Ban je ko ina b..." Rufe ta da duka Bashir yayi irin dukar nan da akewa
maza, tare da kwallo da ita, wani irin taurin zuciya take dashi, domin mik'ewa tayi
tana kallon shi, tare da rike bulalar.
"Kai ba ubana ne! Kai ciki daya muka fita, Karka kuma duka na domin wallahi zan iya
sakawa a maka abinda zai dame ka."

Cikin jin haushi Musa ya shiga dukarta, kamar sun sami baiwa, sosai suke dukarta,
Rulwan ne ma yake musu magana, idan kaga yadda suke abin da suke ba zaka dauka Da
Babba a cikin gidan ba. Amma Baaba Hamah tana kwance abinta.

Allah cikin ikon shi sai ga Ya Binta da Yaya Sadeeq, sun shigo.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Bashir, Musa! Meye tayi muku?"
"Bin maza take! Jiya ma bata kwana a gidan nan ba"inji Baaba Hamah daga bakin kofar
shiga d'akin.

Kallon Juna Ya Binta suka yi da Sadeeq, murmushi suka yi sannan Tace.
"Meye shaidar ki? Baaba meye shaidarki katangar gidan nan dai ba karami bane? Kuma
tun Anum tana budurwa aka karasa shi, yayi tsayi, maza fa? Baaba shaidar Zina nada
girma kin ganta da wani namijin ne?"
"Hajiya Binta! Kuma toh gaskiya ban ganta ba, kawai dai na ganta ta fito wanka
ne talatimin dare? Kuma naga ita ba miji ba, taya zata."
"Idan ya kasance al'adar tace ta dauke fa zata yi sallar dare?" Ya Sadeeq ya
jefa mata tambayar haka, take jikin Baaba Hamah yayi sanyi, su kansu Musa da
Bashir, jikin su ne yayi mugun sanyi.
"Shine kika kira su, kika gaya musu kin kamata ta dawo daga yawon dare."

"Ko auren Alhaji Mudi wuntin dada rabo ne ya kaita gidan shi, amma Anum ba
matar da zata sake rayuwar ta a waje ba, ƙaddara da shaidanun kawaye suka kaita ga
sake jikinta ga wani namijin. Anan kina jin abinda Alhaji Mudi Wuntin dada, banda
ƙaddara da rabo me zata yi a gidan shi, wallahi kuji tsoron Allah, dukarda kuka
mata Allah sai ya bi mata hakkinta."

Daga haka ta juya zuwa dakin da Anum take, cikin murmushin takaici, tace mata.
"Tsalle daya ake a fada rijiya, sai kayi duba baka fita ba, dan haka tattara
kayanki ki koma gidana. Tunda sunce zaki kashe mamarku."

Haka ta kwashe kayan ta, tass sannan ta tattara ta kai motar Aunty Binta, ta dawo.
A hankali ta kalli kofar dakin Malam hawaye na zuba mata, sai gani take kamar gashi
yana mata murmushi,. Kuka ne ya kwace mata, tana yi Jikinta yana rawa, ta juya tare
da barin gidan baki daya, taje cikin motar Aunty Binta a zauna tana kuka.

Tunda Aunty Binta ta shiga, bata ce mata kome, ita kanta tausayin Anum
take, tana tausayin rayuwar yarinyar, tayi kuskure a baya, amma tun daga lokacin da
taji labarin rasuwar Baba Malam, dauke wutar da tayi har akayi addu'ar bakwai bata
magana da kowa. Kamar mahaukaciya haka ta koma lokacin.

Sai da suka hada da rokon Allah, amma ga baki daya rayuwarta ya koma abin
tausayi.
Haka tayi ta rayuwa, ga tsangwamar mutanen gidan su, ga na yan Unguwar,
karshe ma cewa akayi ta shiga kungiyar asiri ne ta biya bashi da mahaifinta,ai duk
wanda ya haɗa shirgi da ita sai taga bayan shi.

Dalilin da ya hanata zaman aure kenan. Wannan abun yana cikin dalilan da suka
addabi rayuwar Anum, ta takura kanta da rayuwarta.

---
Tunda ta koma gidan, Aunty Binta, bata cika fita daga daki ba, duk da gidan cike
yake da yan mata, amma haka bai sakata sake jiki da kowa ba, sai Aunty Binta,
yanayin da take ciki ya kuma dawo mata da ciwonta, musamman idan taga yadda yan
uwanta suke nuna tsanarta karara akan fuskar su.

... Yau ma taje asibitin, ta samu ciwon Mama ya. Haka ya faru ne
sakamakon rashin hankalin da Baaba Hamah tayi, inda take gayawa su Hafsah abinda ya
faru da Anum, wai tana fita yawon dare, shine ɗan Bashir da Musa sun mata fada
Binta da Abubakar suka shiga mata tare da hada kayan ta,ta koma gidan Binta, nan
suka shiga zagin su Aunty Binta da Abubakar.

Abinda ya d'aga hankalin Maman su kenan basu sani ba, tana sauka a gado
zata ban daki ta yanki jiki ta fadi. Shine daga zuwanta suka mata tozarcin da ta
kasa koda kuka, sai ajiyar zuciya. Tsabar tashin hankali, haka ta dawo gidan Aunty
Binta, kamar ba zata kwana ba. Itama dole aka kaita asibitin.

Rayuwar da Anum ke gani ba zaka tab'a dauka, sun sota da kamar ya ba,
sabida yadda suka nuna mata kaunar. Asalima kaunar da suke mata irin soyayyar nan
da ake cewa uwa ba kwab'a, Uba babu tsanani.

Soyayyar da aka nuna, mata wanda duk abinda take so, shi ake so,
soyayya irinta yaran da babu abinda suka sani sai sangarta da sakalci, wani irin
tashi Anum tayi wanda bata san kwab'a ba, ko hantara ba. Anum ta tashi bata san
kome ba sai zunzurutun rashin kunya, da fitsara.
Dan haka kwananta biyu, aka sallame ta, sannan ta dawo gidan Aunty Binta, tana
zaune. Da yamma dan tayi alkawarin ba zata kuma zuwa ba, sai an sallame Mama, ita
kanta Maman ta,.tana mugun kewarta.

Amma yadda yan uwanta suka gina zuciyar Mahaifiyar su, da kin abinda Anum tayi
yasa take boye kewar Anum din.
***
Tana daga daki taji Yar kishiyar tsakar gidan Aunty Binta tazo gidan, alamun tayi
yaji. Tunda tazo take sake surutun abinda mijinta yake mata.
"Wallahi, Maman Shukrah. Ba halin nayi abu zai hauro min, wai dan yana niman aure,
ba halin ya shigo gidan, yayi ta masifa kenan, wai kaya a watse."

D'ago labule nayi ina kallon ta, nayi ita kanta a hargitse take, domin bra ɗinta
har saman kafad'arta, daga nesa na fahimci irin matan nan ne masu kyau, amma duk ta
dishe, ga mace har mace, amma idan kaga zanin jikinta Super vlisco ne fa, amma yayi
mugun fita hayacinta.

Sake labulen nayi tare da kwanciya ta, ina jin Mahaifiyar ta ta ta biyo ta, da
yaron ta karami yana kuka shi kanshi idan ka ganshi zaka dauka ba danta bane,toh
ban yi mamaki ba, domin tunda naga kayan jikin shi na fahimci kalar uwar shi, domin
wandon jikin shi ta shadda ce Gezani, amma wallahi ya fita hayacin sa,rigar yar
kanti ce a jikin shi a kala ana sayar da rigar 3k.
Jinjina kai, nayi tare da sake d'ago labule naga kitson kanta, tana dariya
tabar gidan, shigowa Shukrah tayi, tana tsaki.
"Aunty Anum! Kiga sakarci kowa yasan halin Badi'a da kazamta, amma kiga don Allah
wai yaji tayi sabida mijin yace ta gyara."

"Toh ai tayiwa kanta, tana da masu share mata kuka ne, kyaleta."
Daga haka ban kuma magana ba, na gyara kwanciya ta, sabida
yarinyar bata da wani hankali, da dare Aunty Binta ta tafi asibiti aikinta, naji
anata shari'a da mijin Badi'a, anan yake gaya musu abinda take ga mugun kazamta, ga
shegen rowa, tare da son jiki.
Sam gidan shi babu inda zaka zauna kaci abinci, sannan idan ya kawo madaran
karyawa, wallahi tana buɗewa anan zata ajiye mishi tayi gaba abinta, yace tana da
masu aiki amma ba zai hana kaga ko ina a kazamce ba, yayi juyin duniya ta gyara
taki, ga shi, har hakkin auren shi bata bashi sai yayi mata bori, shi bawai baya
sonta bane a'a yadda ta maida kanta wata mara adalci. Yadda yake bayanin bata
musanta ba, shiru tayi tana zare idanu. Nan Baban Shukrah ya bata hakuri, sannan ya
juya ya bar gidan. Ita kuma aka mata fada, sai lokacin ne Mahaifiyar tane ta kawo
ta dakin da muke, ta kalle ni, tace.
"Anum don Allah ga Badi'a, wallahi dakin mijinta shine rufin asirinta, bawai tonawa
kai asiri ba, ai Kinga yadda Alhaji yake dauke da dawainiyar mu, ga na iyalin shi
yau aka ce baya nan asirin mu ya tonu, amma idan ta zauna a d'akinta yaron nan yana
da kirki. Ga ta nan ai."
Mamar tana fita, na kalle ta tare da sake murmushin takaici.
"Badi'ah kina sha'aninki."

Shiru tayi sannan nace mata.
"Tsakanin ki da Allah mijinki yana cutar ki?"
Cizon lips dinta tayi sannan ta girgiza kanta.
"Kema kin yarda baya cutar ki?"
"Eh Aunty Anum!"
"Toh me yasa kika rena shi?"
Idanunta ne suka kawo kwalla,
"Ko baya gamsar dake ne, a shimfidin ku?"
"A'a wallahi;"
"Toh meye ya kawo reni a tsakanin ku?"
"Wallahi babu kome Aunty!"
"Jin dadi ko?"
"A wannan lokacin mata suna bin maza domin su kwanta dasu, babu ko sisi, shine ke
zaki wulakanta naki? Baki rasa ci ba, baki rasa sha ba. Shine zaki tozarta auren
ki? Kin san iya adadin sab'awa Ubangiji da kika yi? Kawai rayuwar yanci ko?"

Girgiza kai tayi, can kanenta suka shigo har da Yayarta da suke Uba daya ta shigo
itama bazawara ce, kallon su nayi, tare da kallon agogon bangon dakin, kafin nace
musu.
"Kun zo kun baza kunne da baki da hanci kuna kallona, bayan koda nayi muku fadar ba
dauka zaku yi ba, dan haka tattara shirmen ku, ku bar min d'akina."

"Don Allah Aunty ki mana fada wallahi zamu dauka Hajiya Yaya

Please Login or Register in order to submit comment