You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bude mata wulakancin da cin mutuncin, ga cin
fuskar Bala'i. Ya kira Maman Aminu mayyar kuɗi. Malam kuma ɗan maula.

Ita kuma karuwa, gashi kamar ya dauke hankali kowa a kanta, wani salon cikin
Ubanta yake yadda ta kasa motsi.

Ana cikin wannan yanayin, sai ga ciki. Babu imani ya saka aka mata allura cikin ya
fita, domin da ddare ya shigo da Nurse din, tayi mata alluran, kafin karfe hudu na
asuba cikin ya fita, dukka dukka satinta biyar da kome ya lalace, da gari ya waye..
farkawa tayi cikin jini.

Dakyar ta mike ta kuma zuɓewa cikin jinin tayi tare da lumshe idanunta, kafin
ta kuma yunkurawa.

Dakyar ta tashi ta rarrafa zuwa d'akinta, katon butar da take
cikawa ta ajiye shi idan aka kawo wuta ta tafasa ruwan zafi, ta nufa tare da kunawa
butar, Allah ya taimaka akwai wuta, kwanciya tayi a gurin, tana fidda numfashi.
Ruwan na fara tafasa, ta ja dakyar ta kashe, sannan ta ja butar ta kashe wutar.

Tunda ta shiga ban dakin ta sirka ruwan zafin, ta fara wanka da shi, sai da
ta gasa jikinta sosai. Sannan ta koma ta saka wani ruwan tana ganin jiri haka ta
fito ta gyara falonta domin anan aka mata alluran tayi ta birgima har cikin ya
zube.

Mopping ta goge falon, tana kwashe jinin tana kuka, tare da zuba gwiwar ta, a
kasa sai da ta gama wanke gurin ta goge ta saka turarukan wuta, ta rum frsh. Ta
koma dakin ta tana haki.

Bai shigo ba sai karfe biyu na rana, ya kawo mata bread naira hamsin da wata
ruwan bunu, ya ajiye mata, gashi ta zubda jini. Tana bukatar kulawa amma babu.

A daddafe ta ci bread din da ruwan tea din, tana gamawa wani irin zufa ya karyo
mata, kwanciya tayi a gurin, dungurawa tayi a gurin, tana jin Alhaji ya raba
tsakanin cinyoyin ta, ya kwanta da ita, sanan ya fita yabar a cikin mugun yanayi.

.... Kallon su nayi naga duk sun rud'e, tare da lumshe idanuna nayi tare da
sauke wasu irin kwalla masu zafi, murmushi nayi, sannan na ce musu.
"Kunsan hakki masifa ce, karki yarda wani yabarku da Allah, na zalinci Aliyu, ya
kuma gaya min Ubangiji yana madakata. Har yau ina ganin sakayyar Allah. Mu Cigaba"
...
Kwana biyu, Anum ta warware. Kamar ba ita ba, kuma a cikin wannan jinin da
tai na kwana goma, sai da Alhaji yayi ta tarayya da ita, ga azabtar da yunwa, ga
hantara da masifa. Idan kuma ya zage ta ta rama, ya mata shegen duka..tare da
rashin mutunci.

A cikin wannan yanayin wata rana ta samu ta kwace daga gidan, bata tsaya niman
kudin abin hawa ba, ta nufi hanyar gida. Kamar wata kuncen hauka. Haka ya sauka a
mashin tare da zare idanu, Allah ya takaita Muttaka da Abdul Hakim, suna kofar
gidan, sune suka biya mata kudin mashin din, tunda ta shiga cikin gidan.
Da gudu ta nufi dakin Malam, yana kwance dake da daddare ne ta fita.

Ganinta yayi ta shigo mishi tana zare idanu, kamar dai irin ta firgita, rike
hannunta yayi tare da zauna da ita, yana kallon yadda tayi zuru zuru, kamar wacce
ta tashi cutar hauka.

Kiran Umma yayi, tana shigowa tare da sallama, kallon Anum tayi cikin
mamaki da al'ajabi.
"Alhamdulillahi, Ayya yau nake batunki a raina, ashe kina hanya ne? Tare kuk..."

Murmushi malam yayi sannan ya bude baki zai Magana Abdul Hakim yayi musu sallama,
tare da tambayar.
"Malam lafiya me yasa mu Anum?"
"Abdul nima ban sani ba, gata nan dai kamar wacce aka korota, Mariya duba cikin
d'akina zaki ga ruwan zam-zam da zuma!"

"Toh malam." Inji Umma, tana daukowa ya janyo allon karfen shi ya fara mata
Rubutu yana murmushi, zama yayi tare da mata mata rubutu, sannan ya bawa Umma
Addu'a, yana kallon yadda Anum take zare idanu. Bayan ya gama ne aka wanke mata,
tare da bata dabino, taci da bismillah.

Umartan Umma yayi ta haɗa mata tea me kauri, tana bata ko tsayawa bata yi ba,
ta shanye tass. Sannan ya mika mata kular tuwon shinkafa miyar taushe wanda yaji
tantakwashi.

Ga manshanu, ba karamin dad'i taji ba, hannu baka hannu karya ta cinye abinci
tana zare idanu, mik'ewa Umma tayi ta kuma hada mata tea, tare da kiran Rulwanu ya
karbo mata soyayen kwai, a shagon Maude.

Aka tura mata da bread, kamar mahaukaciya, ta nad'e shi. Tana gamawa Umma ta
mika mata ruwa, tana sha tayi gatsa. Me shegen ƙarfi. Sannan ta fashe da kuka,
zunzurutun tashin hankali. Tana son gaya musu halin da take ciki, amma bakinta yayi
nauyi. Haka ta gama kukanta sannan ta tattara tare da nufar dakin Umma, ko dakin
Mamanta bata nufa ba.

" Oga Maude! Kasan Anum tazo kamar mahaukaciya, wallahi tana dakin Malam sai
kuka take, ina jin Malam yana cewa kamar bata da lafiya an tambaye ta meke damunta
tace babu kome." Inji Rulwanu.

Cikin tashin hankali, yake kallon Rulwanu, kafin ya tashi daga shagon,
gidan shi ya nufa. Abincin da Hajjo ta ajiye mishi bai duba ba, ya nufi dakin shi.
Haka ya jima yana zaune kafin yayi alola tare da gabatar da sallar. Goran faro ya
dauka tare da karanto ayatul shifa, sannan ya ajiye, tare da gabatar da wani
sallah. Kafin ya dauki goran ya fita dashi wajen karfe goma saura, ya isa shagon ya
mikawa Rulwanu yace.
"Ka bawa Umma ta bata tasha. Insha ALLAH zata yi magana."

Kamar da wasa, ya amsa..tare da mishi sai da safe. Cikin jin haushi ila yayi ta
surutu, da ya gaji barin shagon yayi, tare da nufar gida.

Har su Umma sun kwanta Rulwanu ya buga mata kofa, amsa tayi tare da cewa.
"Toh amma!"
"Ki bata!"
Tana shiga dakin ta same ta, a zaune ta takura kanta, kuka take yi babu
kakkautawa, sai da tayi ta isheta, sannan Umma ta mika mata ruwan tasha da
bismillah. Sannan suka kwanta.

Wasu irin mafarkai take Alhaji yana Binta da wuka zai soka mata, bata san me ya
tare ta ba, ta fadi sai dai mik'ewar da zata yi wani maciji ya fado kanta, tayi
tayi ya wurgar dashi ta kasa, ihu take a cikin mafarkin wanda ya sanya ta farka da
ihun, sai da Umma ta rike ta. Tana tofa mata addu'o'in. Wanda yazo bakinta, kuka
take tare da gayawa Umma halin da take ciki, da yadda yake dukarta kamar jaka, ga
wulakanci kamar me.

Ga yunwa, duk wannan maganar da take bata ce zata rabu dashi ba, dukda kuwa
zuciyarta tana jin me yasa ba zata rabu dashi ba, amma akan harshen ta, ta kasa
fadar haka. Alola suka yi da Umma tare da gabatar da sallah nafilla. Har karfe
biyar suna gurin sai da suka gama azkar, sanan umma tace ta koma ta kwanta. Kallon
yadda ta rame, yasa Umma tace mata.
"Amma kina da ciki ne ko?"
"A'a bari nayi."
"Shine kika lalace haka."
Yake tayi, kawai sannan ta lumshe idanunta.
"Ina kayan garanki bai ci ace ya kare ba."

Gabatan ne ya fara dukar tara tara.
"Umma Ni ban gansu ba, wallahi ban san inda suke ba,"
Ta faɗa cikin kuka, sannan ta sunkuyar da kanta.
"Toh Allah ya kyauta"
Tunda ta fadi haka ta fita, tana jiyo muryan Maman Aminu, da malam suna musayar
kalamai masu zafi, akan lallai za a kashewa Anum aure ne, shi yasa malam yaki kiran
mijinta, shima kuma yace bai ga shegen da ya isa ya maida mishi Anum gidan
Azzalumin mutum ba..

Abun yayi tsamari wanda har ya sanya Anum din fitowa daga cikin dakin Umma,
kallonta Mamanta tayi tare da sake baki. Ita a tunanin ta yarta ta kai ƙatuwar ban
mamaki, sai ga Anum kamar a hureta ta fad'i.
"Ciwo kika yi Khadijah?"
Yake tayi tare da shafa fuskar ta, tace.
"Ban yi ciwo ba, kawai halin rayuwa ce."
"kamar ya?"
Shiru tayi, tare da komawa dakin Umma, haka maganar ta mutu. Tace lallai sai dai
Khadijah ta dawo d'akinta, ita kuwa kamar wacce ka gaya mata wani abu, tace bafa
zata koma d'akinta ba.

Wasa wasa sai da Anum ta kwashi kwana goma sha biyar, sannan Alhaji ya dibo
jiki yazo, kallon juna suka yi, da Maude ajiye yanke bread din da yake hannun shi
yayi sannan ya nufi inda yake.

Shiga motar shi yayi, shima alhajin ya shiga motar, kallon juna suka yi.
Sannan Maude ya dauke kanshi yana faɗin.
"Kasan sai duk wani makirci da sanin darajar surkulle ba za'a gayawa Buzun mutum
ba, domin shi yana rayuwa ne sak da bafulatanin mutum, ba zan hanaka shiga da
sharrin da ka dibo dan su baka ita ba, sai dai wannan karon, wallahi zan baka
kyautar da ba zaka iya min godiya ba, ka tsayar da fajurcinka iya kanka, ka rabu da
ita, kai da kake nima a gurin wanin Allah, ina kuma ni da na tashi na rayu a yadda
za a karyawa mutum sharrin da aka tura mishi. Idan ka kuskura ka kuma tab'ata, kai
ma kasan abinda kake nima ba zaka samu ba, dan haka ka fita idanu na,.na rufe idan
na rufe da kai, wallahi sai kayi hauka tuburan. Ka kuma gayawa Jahilin da yake maka
shirka, Ni kuma zan ji daku da Yardan Ubangiji."
Daga haka ya ficce daga cikin su yabar Alhaji cikin motar alhaji, shakkar maude ne
ya shige shi, wani irin mugun tsoron shi yake ji, dan haka ya kasa yin abinda ya
kawo shi. Da sauri ya bar unguwar. Zuciyar shi kamar zata buga...
#Mai_Dambu....
[2/10, 9:50 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA ƊAYA.

GAISUWA TEAM MAUDE ANA MUGUN TARE🧗🧗✊🏽

Yana barin unguwar ya kira Maman Aminu ya gaya mata shi akwai mutumin da yake shiga
tsakanin shi da Anum, dan haka kawai zata kiran shi, waye ya mutu waye ya dawo, shi
wallahi badan yana ganin mutuncinta da ya rabu da Anum.

Nan tayi ta bashi hakuri, tare da mishi alkawarin yazo ya dauke ta bayan sun
gama waya ta fito tayi ta ruwan bala'i tare da sakata a gaba zata dake ta, wai ta
tana biyewa Maude zai kashe mata aure, kuka Anum tasaka tare da nuna mata ita fa,
babu wanda take kira sannan bata da waya dan bata san inda yake ba.

Mutumin nan haka ya kullawa Anum sharri, koda malam ya dawo,Maman Aminu tayi ta
barbad'anci tare da kananun magana. Ai Anum da Maude kaza kaza, bai ce mata kome
ba, sai bayan isha da Alhaji yazo Nan malam ya cire kome ya mishi magana akan
rashin Abinci. kuma yar shi ba baiwa bace,kar ya kuma dukarta domin wallahi zai
kai abin gaban Kwamishinan shara'a.

Sake maude ya mishi kashedi kafin ya shigo gidan haka dai yayi ta bada hakuri
da sannan malam yace ba zata koma yau ba, sai bayan ta huta dan yaga bata da
ishshen lafiya.babu yadda ya iya haka ya hakura tare da dauke kanshi, lokacin da ya
samu ganin Maman Aminu, ya ajiye mata kudi, take ta fara cara a bar Anum ta koma.
Dake munafiki ne yace ai ya barta ta huta tukun.

Sannan yayi sallama zai fita, ta kira Anum, bata son zuwa haka ta fita
har zauren gidan ta same shi. Ta kowa gaban ta yayi tare da zuba mata ido.
"Kin kawo karana ko? Kin gaya musu na miki abubuwa, me yasa Bazaki nemi saki ba?"

"Saboda ni nasan illar haka ne, aure rai ne dashi, dan haka Ni ba zan kashe abu me
rai ba!" Ta gaya mishi a hankali,
"Ok shi wannan banijaren fa? Shi yasa kayi mishi Sharri? Allah ya fika duk mugun
nufinka zai dawo kanka Insha Allah."

"Yaushe kika sami bakin magana?" Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Tun ranar da na raggon maza ya fara dukana."

Hannun shi da ya gama tab'e tab'e da wani layyar shi,a cikin aljuhun wandon shi ya
kai zai tab'a ta,tayi maza ta dakatar da shi..
"Nagode, Mr ten minute. Ba sai ka tab'a ni ba,"

Shiru yayi sannan yace mata.
"Ok! Zaki dawo."
"Insha Allah zan dawo da Alkhairi idan ba zama ba, gamawa."

Daga haka ta shige cikin gidan, ba tare da ta kalle shi ba. Aikuwa yaji
haushi. Yana barin gidan ya kira malamin shi ya gaya mishi. Bai boye mishi ba, ya
mishi ai da yabi sai yafi kowa moranta, amma fir yaki fahimtar haka dan haka yaje
yayi fama da matsalar shi.
--- Washi gari.
Tare da Malam suka karya shi ya bata kuɗi taje tayi lalle da kitso. Haka kuwa ta
tafi gidan lallen aka mata, bayan ta dawo Aunty Binta tazo ta kaita asibiti, aka
duba lafiyar ta, aka samu jini ne bata dashi da yinwa sosai, magungunan jini aka
bata, suna dawowa gida, suka fadawa Malam,

Haka yasa Ya Sadeeq ya kuma sayo mata magani, Umma ta mata miya, dan
Malam yazo da nama daga gidan gona, me shegen yawa, aka kuma soya mata wani. Yadda
ake ta shirya mata kayan kome zaka rantse da Allah wani garin zata koma, Umma ta
saka aka mata garin kunun tsamiya, wanda ake haɗawa da tsamiyar a nika, ga kullun
gyada wanda yasha kayan kamshi.

Sai dambun Naman, da garin tsari da kuma shinkafar tuwo da ta wara. Malam
ya kuma bata kuɗi yace ta rike saboda wani abu, hidimar da malam da Umma suka mata
babu iyaka, Ita Maman Aminu burinta ta koma gidan kamar wanda ake yakushinta.

Maude bai samu damar ganinta na, sai ana gobe zata koma, ta tsaya a shagon shi
suka gaisa, mika mata wani roban butter yayi sannan yace mata.
"Gashi ki bawa Malam, kice mishi yajin mu na buzaye ne, naga yana fama da Mura."

Dariya tayi sannan tace mishi.
"Allah yasa da dad'i nima ya samin domin ina mura,"

"Me kwaɗayi!"
"Nagode, Amma Maude ina cikin damuwa"
Kallonta yayi sannan yace mata.
"Allah ya kawo miki dauki, kuma ita rayuwa da kika ganta ba dukka mutane bane suka
san hakkinta, dan haka kiyi hakuri. Duk abinda aka miki ki bar mutum da Allah zai
bi miki hakkinki."

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace mishi.
"Maude har dukana yake! Sannan bai."
"Anum me yasa kike son zama daya daga cikin matan da bazasu iya boye sirrin su ba?
Kiyi hakuri ki boye wannan lamari, Allah yana tare dake, idan naji labarin abinda
yake damunki hakan zan ta kallon Alhajinki"
Ya faɗa yana mata dariya, sam bata ga abin dariya ba, murmushi tayi sannan tace
mishi.
"Aifa, Alhajina mmm!"

Yayi mata nasiha, sannan ya bude wani drowa a shagon ya dauko mata karamin
Alkur'ani me dauke da Yasin! Da wasu addu'o'in. Ya mika mata, insha Allah kika rike
Alkur'ani Allah zai tayaki yaki, amma kema fa baki da dad'i!"

Gyada kai tayi sannan tace mishi.
"Eh bani da shi, amma toh ba damuwa."

Ta faɗa, ya fahimci taji haushi yasa shi, ya sashi dafa mata indomie tare da kifin
gwangwani, suna tsaye tana mishi mita, yana jinta sannan ta mika mata.
"Jeki ci, nasan kinyi kewar shi."

Hawaye ne ya zubo mata daga idanunta, tana kallon shi. Dauke kai yayi tare da
rufe window, a hankali ta koma cikin gidan, ta zauna tana wani irin kuka. Ga
abincin amma ta kasa kai loma daya. Tana ji a ranta tayi rashi na har abada, me
yasa bata rike shi na lokacin da yake tare da ita, tana kuka ne da duk zuciyarta.

Kallonta Umma tayi,
"Toh ya isa haka kar malam yazo yaga kina kuka."
Bata daina kukan ba sai da Umma ta zauna a jikinta, ta fara ajiyar zuciya. Shafa
kanta tayi sannan tace mata.
"Ci!"
"Umma"
"Bana son magana!"
Haka ta kwantar da kanta, tana ajiyar zuciya, daga baya ta cinye indomie (😂😂😹😸)
tunda ta cinye ta kasa maida mishi plat da cup din, karewa sakawa tai cikin kayanta
ta boye.

Haka umma tayi ta bata maganin gyaran jiki, tasha a daren washi gari ma ta
wuni sha, kafin yamma. Aunty Binta da Yan uwanta suka rakata, har gidan ta, sun
sami Alhaji yana korawa Barirah Ashari'a, ganin su Anum ysa shi yin Fuska. Ya karbe
su hannu bibbiyu, ya kuma kai su part dinta, da ta samu a gare.

Sai lokacin maganar Malam ya dawo mata,.tare da turaren da ya bata, wanda
Maude ne ya hada yabawa Malam, sai wannan yajin, bai bata abun dan ya kashe mata
aure ba, asalima ya bada ne dan taci yakin duk surkullen da. Alhaji zai mata Insha
Allah ba zai kamata ba.

Sai wasu na karya sihiri ko tsafi,.wanda ya haɗa mata a cikin turaren wuta, ya
bawa Malam dan ya gaya mishi kome akanta, ya kuma ce mishi Insha Allah, ba zata
kuma fita hayacinta ba.

.... Tana shiga abinda ya fara yi, shine dauko burning, ta zuba turaren
tare da zama tana cewa.
Aunty B! Ina kewar Umma Na!"
"Ai baki isa ba, muma haka muke kewarta, kuma muka yi hakuri."
Inji Aunty Aminatu,
Tura baki tayi, tare da cewa.
"Sai na gayawa Umma abinda kuke min!"
"Ke Anum bamu ciki da gulma me muka miki"
Inji Aunty Rabi.
"Oho ina nasani, kawai dai naga kuna min dariya."
Dariyar suna saka sannan suka nufi kitchen ɗin ta,.suka saka mata kome a cikin
freeza musamman garin kunun tsamiya, da miyarta sai soyayyen nama,.kula shi aka yi
a laida.

Suka bata tare da cewa.
"Saura ki ajiye mishi."

Murmushi tayi, sannan tace.
"Toh"
Make keyarta Aunty Binta tayi tana dariya, haka suka taimaka mata ta shirya kome
cikin tausayin rayuwar da take, da zasu tafi haka Suka bata dubu biyar biyar su
Uku, dan Aunty Rabi bata zo ba, Ya Abubakar ne da Rulwanu, shima sabida gobe zai
kawo mata taliya yar murji ne, da su tafi har kofar gida ta bisu, tare da cewa
Rulwanu.
"Rulwanu don Allah kace Umma, barshi ungo ka saya min Masa a kawo min"

Ta faɗa idanunta na kawo ruwa,
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ni zan saya miki, Insha Allah zan kawo miki kinji ko!"

Hawaye ne ya sauko sharrrr, tsayawa suka yi suka rarrashe ta, sannan suka bar
gidan, tana shiga cikin part dinta, ta sami Alhaji yana zaro idanu.
"Wannan turaren babu dad'i."

Bata kula shi ba, ta wuce kitchen ta daura abinci a saman reshon da tazo dashi,
tare da katon galan din kananzir. Haka ta shiga abinci cikin sauri ta dafa shinkafa
da waye, sannan ta juye a wani kularta, ta kuma kai d'akinta miyarta ta zuba a kan
wanda taci, sannan ta dawo falo,.ta ajiye yayi sanyi dan bata son cin abincin da
sanyi d'akinta ta shiga tayi Alola, kamar ance ta d'aga labulen d'akinta bayan
tafito daga alolan hango Alhaji tayi yana saka wani irin halitta yana hura mata
abincin da zata ci, cikin tsoro ta sake labulen.

Shi yasa Maude yace barci ba nata bane, bata cancanci barci ba. Tana rayuwa
idanunta a rufe, had'iye kukan da yazo mata tayi, sannan ta gabatar da sallah, tana
idarwa ta fito. Yana gurin sai sashe baki yake, daukar plat din tayi tare da fitowa
waje, ta kira yaran shi kafin ya dakatar da ita, ai kuwa yaran sun fauce abincin
tare da daka sowa. Tuni suka cinye abincin.

"Wannan wani irin Iskanci ne da zaki basu abincin." Kallon shi tayi cikin mamaki
sannan tace.
"Ai Yaranka yarana ne, kuma banga laifin dan na basu abincin na ba, so idan ba wani
abu bane a ranka manta kawai."

Daga haka ta ajiye Plat din, ta shiga cikin d'akinta ta koma kitchen ta sake
zuba miyar asalima tsoron kar ya zuba mata abinda ta gani tasa a ranar ta maida
freezan ta d'akinta dake akwai sarari, shima firjie din ta mai da cikin ɗakin.

Ta bar kitchen ɗin domin girki, kayan abincin ta kuwa a cikin wardrob ta
zuba kayan sawanta ta maida cikin akwatinta.

Duk bai Fahimci abinda take ba, sai da da.ddare da ya shigo. Yaga
freeza a d'akinta ya tambaye ta hujja.
"Kawai naga zai fi min sauki ne na ajiye kome a d'akina, dan wancan lokacin ban san
ya akayi kayan ya watse ba. Shi yasa yanzun na tattaro kayana ka ajiye kusadani.
Ban sani ba ko nayi laifin da za a zagi iyayena da dukana ba."

"Haba Autar malam, babu wannan keda kike da masu tare miki fada ai ko tsohon
mijinki ba zai bar mutum."

"Don Allah, barci nake ji!"
Ta faɗa mishi a sanyayye, domin ta ji ya fara lallubar ta, duk yadda taso bijire
mishi, haka ta bar shi ya mori gajiyar Umma, iya hanata barci yayi tare da masifar
naci. Sai karfe biyu na dare ya mike ya fita, da sauri ta sauka tayi wanka, tare da
alola tazo ta fara sallah, tasan idan ya dawo zai kuma koma mata, dan haka ta shiga
sallar dare babu wasa.

Koda ya shigo ya same ta, tana sallah, ƙarara ya razana da wannan sabon lamarin
da tazo dashi. Dan haka ya zauna tun yana jiranta har ya kwanta. Haka ya bingire da
barci, tana idarwa ta dauko Alkur'anin da maude ya bata, ta iya karatu toh meye ya
shagaltar da ita, dan haka ta shiga karatu tare addu'a.

Karfe uku da rabi ta kwanta, dake akwai, masalatai a cikin Unguwar, tashi tai daga
abin sallah ta nufi ban daki, tayi tsarki da alola, sannan ta kuma gabatar da
sallar asuba. Tana zaune a gurin har rana ta fito, Alhaji yana barci, bata tashe
shi ba, dan tasan yanzun sai ta fara masifa. Tana idar da azkar, ta kwanta a
gurin....
Tsugunne Ba kare ba.....
#Mai_Dambu.
[2/10, 9:50 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA BIYU.
_Wannan Shafin na kune masoyan Zanen Qaddara ta! Nagode Nagode na kuma Cewa
Nagode sosai! Ga Anum a gidan Mudi wunti_


*** Washi Gari
Sai ga Rulwanu da katon kwalin taliya, da kular masa, na gidan Dahiru me sugar. Sai
farfesun kayan cikin rago, yayi kyau sai kanshi yake, ta zauna tana ci tana kuka.
"Rulwanu kayi hakuri!"
"Babu kome Little princess! Ci abincin ki, Insha Allah duk ranar Juma'a zan na zuwa
duba ki!"

Haka kwalla ya shiga zuba mata, shi kanshi Rulwanu tausayin Anum ya kama shi,
dan haka ya fita da sauri ya barta karta karya mishi zuciya....

Tunda ya lura da sabon salon da ta bijiro dashi, sai ya shiga mata rashin mutunci.

Idan tayi mishi abu zai kama masifa kamar zai dake ta, ita kuma bata
tab'a damuwa ba, dan tasan haka zai ganta ya barta.
Suna cikin wannan yanayin, ta kuma samun ciki, irin me shegen laulayin nan, bata
son wanka. Kai duk wani dabi'ar kazamta, duk da Rulwanu yana zuwa dubata.

Amma bayan jin dadin yadda take rayuwa, akwai lokacin da yazo ya samu ta tara
wanki, haka ya sakata ta hada kayan, ya tafi dashi gidan, Umma da kanta tayi mata
wanki. Aka mata goga, sannan da zai kawo suka zo tare da Umma da Maman Aminu.

Duk yadda take tsammanin zata ga gidan sai da ta karaya, dan haka babu yadda ta
iya, koda suka shiga part din Anum, suka ga tana kwance a kasa, ga dan roban
yawunta, sai da suka rasa yadda za suyi da ita, take Umma ta shiga gyara mata
gidan,
Jikin Maman Aminu yayi sanyi. Kamar me duk yadda take ganin Alhaji yana mata
b'arnan kudi, ashe cin Uban yarta.

Shiga dakin Anum tayi tare wanke ban dakin ta fidda sauran kayan da ta b'ata,
Sannan ta haɗa mata ruwan zafi, ta kai

Please Login or Register in order to submit comment