You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk ta damu."

Tashi nayi na zauna, tare da kallon su, kafin na sunkuyar da kaina, na fara
matsa yatsuna suna kara, sannan na kalle su daya bayan daya nace musu.
"Duk wanda kuka ga tana ihun Ba'a mata adalci ba ku fara duba meye asalin
rayuwarta?

Me ta rasa a rayuwarta? Shin aure ibada ce? Ko rayuwar yanci ce? A iya sanina ni
dai nasan ibada ce, amma ban sani ba ki Badi'a tana da wani abinda yake bukata a
rayuwar auren!"

Girgiza min kai suka yi. A hankali na lashe bushashen lips dina,.sannan na zuba
musu ido. Kafin na fara cewa.
"Ban sani ba ko zaku dauki darasi a cikin Zanen qaddara ta ba, amma bari na duba
kadan daga cikin rayuwar da nayi a baya,"

---
Rayuwar Anum.
Zaune take a kofar gidan, ta saka kwanon tuwon shinkafa fara yar dass, miyar taushe
wanda yaji kabewa da yakuwa, gashi yasha manjan asali na kasar Idda, sai wani
daukar ido yake, yarinya ce yar shekara goma cif a kofar gidan, ta zauna tana
shashekar kuka, .zaka rantse da Allah zaneta aka yi, a'a kawai tsabar kiyayyar ta
da tuwo ne, sake shure kwanon tayi abincin ya koma gefe ta kuma tsalla ihu, kamar
an yanka namar zuciyarta, ta fashe da kuka.

Had'a shayi yake, amma gabaki daya jikin shi rawa yake, shi mutum ne da
bai kaunar jikin kukan yara, dan haka ta window kofar shagon, ya leko yana kallonta
sanye da riga da skirt na kanti, kanta ya sha kitson zare. Idan ta d'ago ta kalli
mulmulen tuwon shinkafar gabanta sai kuka ya kuma kwace mata.

Kallonta yayi cikin nutsuwa, har tsigar jikin shi yana mik'ewa, a hankali ya
fito, daga cikin shagon ya kalleta murmushi ne ya kwace mishi yadda ta zuba tagumi,
zuwa yayi ya tsuguna yadda zai kare mata kallo yace mata.
"Yarinya me kuka! Meye sunanki?"
D'ago kai tayi tare da saukewa kasa tace.
"Anum!"
"Me yasa ki kuka?"
"Wai naje na gama shan wahalar makaranta sannan a ce naci tuwo Wallahi bazan ci
tuwo ba!"
"Toh me zaki ci?"
"Taliyar Maman Dija"
"Ta nawa zata ishe ki?"
"Nera talatin!"
"Shikenan nan"
"Eh shi kenan!"
Ciro hamsin yayi ya mika mata, da sauri ta mike, zuwa cikin gidan ta dauko kwano
tare da fita da gudu, tana murna, girgiza kai yayi cikin nutsuwa.
Haka ya koma shagon shi ya cigaba da aikin sayar da shayin shi,. Har ta sayo ta
dawo tana isowa ta mika mishi ashirin din tace mishi.
"Me shayi kaga ban maka godiya ba, Nagode fa yau sai dai Mama taci tuwonta."

Murmushi yayi tare da girgiza kai, yana kallonta ta wuce da sauri, Anum kenan.

Haka ta cinye taliyar ba tare da ta tuna da kowa ba, sanan ta shige dakin
Umma ta kwanta, Domin kar Mama tace tayi Sallah, domin ta ki jinin sallah, tana yi
ne dan ya zama mata dole tayi, amma da dan ita ce ba zata yi ba, kuma Mama ba
kyaleta zata yi ba..
#Mai_Dambu
[1/31, 11:27 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai...

😂Feel Free.... Free book ne😂 🤣
Maude.
BABI NA SHIDA.

Mike kafa tayi ta tare da sake baki ta fara sharar bacci, tun karfe É—aya na
rana, take barci har biyu, asalima yadda ta konta ba zaka dauka cewa akwai mutum a
dakin ba. Haka ta wuni.

** "Ila ban tab'a ganin wannan yarinyar ba, sai yau."
Ya tambayi abokin shi da suka haÉ—u kwanan shi yayi mishi sanadin samun shagon kofar
gidan su Anum.
"Khadijah! Itace karamar yarinya a gidan nan, Kanwar su Alhaji Abubakar ce, taGna
gidan shi ne ko nace bata cika zama a unguwar nan ba sai a gidan yayunta."

"Ai shi yasa ban cika ganinta ba, amma akwai rikici naga za ayi rigimammiya ta
karshe!" Ya faÉ—a yana hada shayi ga wani matashi. Suna wannan maganar ne cikin
harshen buzanci.

... Karfe hudu na yamma, ta fito tana tsalla ihu, zaka rantse yagar namar
jikinta ake, amma ina kawai ance taje makaranta ne, wato islamiyya, take wannan
ihun. Girgiza kai yayi sannan ya kalleta tana tsaye da yar jakar buhun siminti.
"Toh Sarkin kuka,zo ki gaya min me aka miki!"
"Ni bazanje islamiyya bane!"
"Akan me?"
"Mama taki bani kudin tara, Umma kuma ta dake ni wai banyi sallah ba, kuma da safe
nayi sallah dukkan na yau."
"Yau naga abin duniya, Ni Maude.. ai ba a yin sallah haka"
Sake baki tayi tana kallon shi kafin ta sunkuyar da kai tana jan kukan da zatayi.
"Toh nawa ne kudin tarar?"
"Zan sayi calbin malam! Hanjin ligidi! Tsami gaye, aya da gyad'a. Dan malele!"

"Duk a cikin ki zaki zuba Dijamah?" D'ago manyan idanunta tayi kafin ta fara
jin wani sabon kwalla na zuwa mata ta, ta fashe da kuka.
"Toh... Toh....toh... Ya isa haka ai ban ce ba zan baki ba, zan baki nace meye na
tara mana jama'a."

Sai ka rantse da Allah, dukar ta yayi, haka ya ciro Naira hamsin ya bata tare da
rakata har islamiyya rariya da yake bakin kura, tana shiga get din makarantar ya
juyo abin shi.

..... Tunda suka shiga aji Beauty take kallonta.
"Yau kin zo da kudin tara ne?"
Tura baki tayi sannan tace.
"Mama da Umma sunki bani kuma sai na gayawa Malam"

Kallon rashin wayo XOXO tayi min, kafin tace min.
"Yau wallahi karki gayawa Malam kizo zan kai ki gurin Baba lado, idan kina son
kudin tara zai na baki yana saka miki hannu anan d'inki".
Wani shegen yawun tsoro ta had'iye, tare da zare ido waje, ta koma can gaban ajin
ta zauna.
"Anum!"
"Babu ruwanki dani! Idan ya Abubakar yaji wannan abun yanka Ni zai yi kamar yadda
ake yanka kaza, kuma yace a wutar jahannama ake wurga masu aikata haka. Ni babu
ruwana."

Ta fadi haka tare da canza gurin zaman ta.
(Kira ga iyaye! Mu kula da yaran mu,musan da suwaye suke mu'amala. Kuma mu gaya
musu illar zina da masifar shi.)

Duk yadda suka so shiryawa da Anum taki kula su, asalima tsoron su take
dan gani take kamar suna aikatawa ne shi yasa suka mata tayin itama tayi joining
dinsu.

Koda aka yi tara, fita tayi wajen makarantar tayi sayayyar abinda zata ci,
sannan ta juya ta koma cikin ajin. Akan kansu sun san halin Anum da shegen taurin
kai da kafiya, duk da XOXO shekaranta zai kai sha uku, haka Beauty zata kai shekara
goma sha daya. Anum ce me shekara goma.

----
Malam Muhammad Bello.
Asalin dan garin Badara ne a can karamar hukumar kirfi na jahar Bauchi, matar shi
Umma Mariyah itace ya aura tun saurayi da budurwa. Sai Mama Hauwa'u. Ita a bazawara
ya dauke ta, kasancewar ita yar kabilar Igala na jahar kogi.

Umma tana da yara bakwai Aunty Binta, Abubakar, Aunty Aminatu, Aunty Rabi', sai
Aunty Maryam sai dan autan tan ta Rulwanu,

Dakin mu kuwa cike yake da zaratan maza, Aminu shine Babba sai Usman, BASHIR,
Yusuf, Hafsah, Safiya, Sai Ahmad, Musa. Abdul Hakim yana can Imo yana aiki, sai
Muttaka sai Ni ce auta Anum KHADIJAH MUH'D BELLO....

Lokacin da aka haife ni yayi duk Yaran gidan mu sun girma dan sun kusan kammala
karatun su, aka haife ne. Domin lokacin Ya Binta yaranta shida, Aunty Amina tana
goyon Takwarab malam, Aunty Maryam kuma ta yaye Fatimah.

Nice karama sosai dan nazo akan girma ne, dan haka kowa ya tattara soyayyar
duniyar nan ya aza min a kaina.

Kasancewar itace auta duk wani tab'ara da sangarta ya kare a cikin ta, ba abin
damuwa bane Anum tayi ta zuba ihu, tare da rikicin gangan. Ko kuma tayi ta nimo
rigiman yara.

Bata cika zama a cikin gidan su ba, tafi zuwa gidan yayunta ta zauna, idan ka ganta
a can sai ka rantse sune suka haife ta.

Tun tasowarta Abubakar yana yawan musu nasiha akan babu kyau wasa da maza, hakan
yayi tasiri akanta da kuma yanayinta na karamar Kanwar su.

---
XOXO.
Wacce sunanta Abidah mahaifiyarta tana aiki ne a gidan Alhaji Ghali me sugar,
Mahaifinta yana sayar da buhu da tsofin kaya ne a kasuwar muda kasan bauchi, asalin
su yan Bauchi ne.mazaunan garin yalwan shaandam fadar da aka yi shekarun baya ya
dawo dasu gida.
XOXO kyakyawa ce fara doguwa, kasancewar mahaifiyar ta, bata
zama dasu da ita yasa yarinyar ta dauko hanyar lalacewa, dukda haka sai da aka sami
wani mara imani yana bata naira talatin yana wasa da jikinta, haka ya haifar mata
da girma so fast kana ganinta kasan tana hulÉ—a da maza.

Yarinyar tana mugun rawan kai, da iyayi yarinya karama ce
amma zaka rantse uwar mata ce, ga iya manyance. Gidan da suke haya irin babban
gidan nan ne, kuma akwai matan aure da zawarawa a cikin gidan, akwai yan matan
amare, akwai gwauraye matasa marasa aure har da yan cirani anan duka a gidan.

Sannan wani abun takaici gidan a gwamutse yake, idan nace a gwamutse
babu Yaren da babu Hausawa, Inyamurai, yarbawa, fulani, da wasu Yaren garin bauchi.

Dogon gida, basu iya fada ba ga munafunci da gulma, an iya ririta magana,
duk yadda kaso kaji gulma idan ya wuce dogon gida ba zaka tab'a jin shi ba kuwa, ga
rashin tarbiyya yaro karami idan ya lallaiyayo maka ashari'a sai ka zata a zamanin
maguzawa ne, ita kanta Adama Maman Abida, ta iya munafunci da gulma, ga sata
kamar jinin b'era, sannan ba abun damuwa bane ta zauna tayi gulmar mutum, idan ta
ganshi ta nuna nan duniya babu irin shi.

Matasan da suke zaune a gidan, duk tayi gulmar su karshe yaron
cikinta yake fitowa yana auna mata ashari'a.

A haka da take zagin yaran wasu da dibe musu albarka gani take baya
sauka a kan nata, ga dai XOXO yarinya ce amma Idanunta ya buÉ—e da wasan banza, idan
kaga yadda maza suke yi da ita sai ya baka tsoro, sannan ita kanta ta iya niman
maza da iyayi da kwainani, idan tana magana zaka rantse da Allah babbar mace ce.

Sannan daga kofar gidan maza yan cirani suke zaune, abin
takaici da tausayi idan suka dawo daga sayar da raken su, haka zasu kirata suyita
jagulata, har sai sun kauce hanya sannan suke kyale ta,

Beauty wacce sunanta Halima, irin gatsen nan ne, domin ko kama sunan Beauty
bata yi ba,. Kawai ana gaya mata ne saboda yanayin ta.
Mahaifinta malamin makarantar primary rariya ne, mahaifiyarta tana sayar da kayan
miya a cikin gidan su dake bayan rariya primary school.

Da yamma kuma tana fitar da danyen awara, tana soyawa da dare a bakin titin
bayan gari.

Wato idan kana niman maha'inciyar mace kasamu Maman Halima, toh an rufe
an shafa fatiha. Matar tana da mugun kwaÉ—ayi ga masifar bala'i, ga cin bashin tsiya
kuma idan kaci nata ta hanaka barci.

Ga karya da kazamta, amma kuma a haka bata zagin y'ay'an mutane, ita dai
burinta kar ayi babu yarta, tun beauty nada shekara tara ta fara saya mata man
bleach cewar ta yarta bata da kyau dole ta haÉ—a da wanka. Wani abun da ta manta
dashi, shine Allah yayiwa beauty Baiwar gashi har gadon bayanta.

Dake rumada ne irin bayin fulanin nan, amma wallahi idan tayi tsifa
sai ka rantse da Allah gashin doki ta saka, gashi baƙi sidik, gashi bata samun
kulawar da ta dace, amma idan kaga gashin sai ya burgeka.

Ko Anum da mahaifiyarta ta kasance yar ƙabilar Igala, gashin ta ja ne saman shi
kasar shi baƙi.
Beauty da XOXO tasu tazo kusan daya domin kuwa halayyar iyayen su ya
jefa su kazamin rayuwa..
......
Maude.

Maude dan kasar nijar ne, buzu ne kyakyawa ne, babu laifi idan kasan ajey mijin
kajol toh haka maude yaƙe, karfafa ne. Yana da kiran jaruman maza, wanda kana
kallon su zaka Fahimci mazaje ne a tsaye a gaban ka, mutum ne da matukar yana
tafiya zaka iya hango nutsuwa, kamala, dattako, domin a yanzun yana niman shekaru
arba'in a duniya, bai cika walwala ba. Amma yana da kyawawa halayya, yana da hakuri
da kawaici..
Wani abun da mutane suke kara girmama shi, mutum ne wanda yake da addini, idan
yana karanto Alqur'ani sai ka rantse da Allah, bakon Balarabe ne.

Idan kuwa aka tab'a shi, toh ka girmama abinda zai sanya yayi
magana, shi yasa yake zaune lafiya da kowa, kuma shagon shi cike yake da matasa,
ana hira. Musamman ya sayi tv ya saka sabida masu zuwa shan shayin shi suna kallon
kwallon.

Yan iskan bakin kura shakka shi suke badan kome ba, sai
dan sun fahimci bai da dad'i, domin kuwa sun tab'a zuwa bayan gari suka yi fada yan
kwanar kwaila, da yan bakin kura suna zaune kawai sai ga matasan bakin kuran sun
tawo zasu tafi fada da yan kwaila, kawai me zai faru!

Sai suka tsaya a bakin shagon shayin shi, zasu mishi diban albarka, yace musu.
"A'a jijiya kuyi tafiyar ku kawai, nan gurin sana'a tace."

"Toh idan munki fa, kasan Allah zamu kaddamar maka." Inji jijiya.
"Da dai zaku tafi zai fi alfanu."
"Kai ku watsar da kayan shayin shi yayi abinda zai yi."

Masu shan shayin duk sun watse, murmushi yayi sannan ya cigaba da
abinda yake, yana jin wani irin yanayi, wanda rabon shi da fuskarta haka shekaru
biyar baya.
Yana jin Dan sara sukan ya shigo shagon da niyyar watsar mishi da kaya, wato da
maude ya rike hannun Yaron ya murÉ—a baya, ya tima mishi dun-du a bayan shi sai da
ya kwara amai, a gurin ya suma.
Kallon su yayi fararren idnun shi,.suna kuma rinewa izuwa jajjur, tunda ya zuba
musu ido.

Da gudu suka bar shagon har rana me kaman ta yau basu kuna dawowa ba, kuma bai
fasa abinda yake yi ba, sai ma karshe dawowa da yaran suka yi zasu zama yaran
shagon shi.

Zama dasu yayi cikin nutsuwa da sanin ya kamata yace musu.
"Bangan siyasa ba naku bane, ki kashe junan ku, Ni bako ne ina da rayuwa na, ina da
kane irinku. Amma dayawan su, suna makaranta da aikin kamfani ko aikin gwamnati.

Dan haka kuyi kokarin daina shan kayan maye ku kama sana'a yafi kashe
juna da kuke yi.

Bana jin dadin ganin kun lalata tarbiyyar ku da rayuwarku, ba zaku gane rayuwa
tana da muhimmanci ba, sai lokacin da kuka wayi gari kana raye amma baka da ikon
sanin halin da wani naka yake ciki nan ne zaku gane muhimmancin rayuwar da kuke
wulakantawa."

Yayi musu nasiha sannan ya kuma kara da tambayar su me suke son yi. Kuma suka gaya
mishi abinda suke bukata yace su bashi lokaci yayi nazari....
Wannan kenan...
----
Tafe take rike da calbin malam, dayan hannunta madaran kuka ne.. ta kalli wani
yaron irin yaran nan ne masu katon kai, da gudu ta watsa mishi madarar kuka, tace
mishi.
"Rabe me kai uku daya doya daya dankali daya Allah ne ya bashi."

Aikuwa yaron ya biyota da mugun gudu, ta falla a guje sai shagon Maude, tana
shiga bata tsaya ba,.sai a bayan shi, jan wani majina tayi sannan tace mishi.
"Maude Abokina boye Ni kace bana nan"
Ba musu yayi hakan, tare da leka yaron. Sai zare ido yake tare da goge madarar
kukan da ta watsa mishi.
"Toh zo nan ayi shara'a, dan zan iya zaneka idan ka tab'a min Kawata."
Cikin kuka yace.
"Ce min tayi me kai uku!"
"Dijamah haka ne!"
Rike rigar shi tayi ta baya.
"Toh tayi laifi bari na baka bread da bota ko"
Aikuwa Anum ta daka tsalle tace ba za a bashi ba.
"Wallahi ka bashi na rantse sai na kwashe kafarshi,.kuma na daina abota da kai."

Lallabata yayi ta shige gidan su, ya sallami yaron.
"Alazi wahidin!!!! Iya Dan Malam na sallama!"
"Anum idan nazo gurin sai na fasa miki baki da shegen murya kamar na babanin
akuya."
"Ruwanu ruwanu ruwanu, baka iya aiki ba sai cin tuwon umma da Malam ruwanu me katon
kai,.da katon baki."

Haka ta cigaba da tsokanar Æ´aÆ´anta Rulwanu, bai kulata ba dake Umma na gurin, sai
Mama ce ta fito daga dakin Malam ta rike mata kunne, aikuwa ta callara kara zaka
rantse da dukarta aka yi nan kuwa zunzurutun makirci ne da ta fara koya a gurin su
beauty da XOXO. Amma Mamah bata mata kome ba...
#Truelifestory
#Mai_Dambu
[1/31, 11:27 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..

BABI NA BAKWAI.
Kuruci dangin hauka....

Cikin jin haushin sharrin da take shirin mishi ya mike tare da falla mata mari,
aikuwa ta kuma callara kara, tare da watsar da kayan makarantar islamiyya da ta
fito.

Rige rige ake tsakanin Umma da Maman Aminu, ganinta suka yi tana ihu da
birgima zaka rantse da Allah, shegen duka aka mata.
"Wayyo Allah na, wayyo Allah na. Wayyo ya kashe ni, na mutu na lalace, wayyo
fuskana, Allah ya isa min mugu kawai Azzalumi me shan wiwi."
"Kambu ina wasa dake ne? Yaushe kika ga nasha wiwi, wallahi sai naji miki ciwo dan
kaniyarki."

Kafin ya rufe baki Umma ta dauko bakin wuta ta rufa mishi da gudu ya fice daga
gidan, yana huci. Tare da alqawarin sai yaci kaniyar Yarinyar nan idan ya kama ta,
yana fita ta kyalkyale da dariya, cikin takaici Umma ta Zungure goshinta, aikuwa
tayi kwalkwal da idanu cikin fada tace mata.
"Yaushe kika koyo makirci? Khadijah har kin san ki saka kuka ba tare da anyi miki
kome ba? Toh idan kika kuma sai.."

"Maman Sadeeq! Yarinya ce fa? Ban ga amfanin a dinga mata fada ba." Inji Malam
wanda ya shigo gidan yanzun, cike da mamaki Umma take kallon shi,
"Malam tun icce yana danye ake tankwara shi, idan ya girma ba zan mana dad'i ba,
Anum shekara goma ace ba za a mata fada ba?"

"Maman Sadeeq! Ni banga amfanin tasa Anum a gaba ana mata fada ba, idan
tayi hankali zata gyara." Ya fadi haka tare da cire takalmin shi ya shige dakin
shi, ita kuma Maman Aminu ta wuce kitchen tana iza wutar tuwun da ta daura, Anum ta
shige dakin Malam tana b'abbaka dariya, suka bar Umma A tsaye a gurin. Jikinta a
mace ta koma d'akinta.

Umma wacce sunanta Mariyah yar garin dewu ce, iyayenta manyan mutane ne
a garin dewu, asalima fulanin can ne, mace ce me dinbun hakuri da sanin ya kamata,
tana da halin girma da mutunci. Gashi abinta bai rufe mata idanu ba, Umma irin
mutanen nan ne, masu shegen zurfin cikin, sannan tana da hangen nesa. Allah yayi
mata baiwa da idan tace karka yi abu toh wallahi karka yi domin kuwa daga baya da
kanka zaka bata labarin abinda ya fara idan ya kwab'e maka.

Saba'in Maman Aminu da Allah ya daura mata jarabar son abun duniya, yaranta
da ta aurar gani take mazajen su basu dace da su ba, kawai malam yafi karfin tane,
shi yasa ta dauki burin duniyar nan ta daura akan KHADIJAH,ta kuma hada da gaya
mata ita kyakyawa ce kamar fure, Kullum Mama idan ta zauna da Anum ce mata take.

"Ke lu'ulu'a ce,.kin fi sauran yan uwanki, kin fisu farin jini, dan
haka ka mata yayi ki auri mutum me daraja, wanda zai d'aga darajar ki sama da ta
kowa, duk wanda yayi fushi sake tabbas baya kaunarki ne, Ni da Malam muna sonki dan
haka ki nutsu ke kane jari na ce ke"

Wadannan zantuntukar take gaya mata, dake yarinya ce Anum sam hankalinta bai
cika daukar shi ba, asalima yarinyar tana da mugun wasa, Maman Aminu tana da Babbar
yarta Mawedo tana aure a can kogi a garin dakina.

Rabon su Aminu ya kai Malam aikin can ya ganta ya aurota, kuma zaman su
masha Allah, domin Allah ya azurta su sa yara.

.... "Malam ni bana son Oga Chide !" Ta fada kamar zata fashe da kuka, a hankali ya
zuba mata ido, wani irin abu tayi da idanunta. Take ta bashi tausayi yaji a ran shi
ba zai barta ta koma Oga Chide ba.
"Wani makaranta kike so?"
Dake Oga Chide wani makaranta inyaramuri ne, a nan Ibro quarts, dan haka ya jefa
mata tambayar da yake ran shi.
"Malam Ni dolphin nake so."
Ta faÉ—a tare da zubda kwalla, har da shasheka.
"Shi kenan, Uwata."
Ya ce mata,
Da ihunta ta fice daga d'akin, tana daka tsalle.

Bayan fitar ta ya d'aga wayar shi na tafi da gidanka ya kira Abubakar ya gaya
mishi yadda suka yi da Anum, sosai ran Abubakar ya b'aci yayi ta faÉ—a, dake Malam
ya san me yake yi nuna mishi yayi, a'a shi ne yake son sauya mata, makarantar bawai
dan ita ba.

Wanda kuma ba haka bane, kawai KHADIJAH bata niman Alfarmar Malam ya haÉ—a da na
kowa ne, shi.

A yanzun da take da shekara goma, rigimar da take yi sai ka rantse da Allah,
yar shekara biyar ce, ga rashin jin Bala'i.

Ita kanta Maman ta bata san maude yana bawa Anum kudi ba, har aka maida ta
Dolphin. Zoku ga dauki da murna rawan kai da rashin kunya ya dadu, bata cika shiga
harkan kowa a cikin unguwar ba sai Maude, wanda shi yake dafa mata Indomic da safe
da tea,.ya bawa Rulwanu ko wani daga cikin yaran shi su kawo mata, ya kai cikin
gidan.

Wa anum, taci ta gatse su a tunanin su malam ne yake sawa ana bata, sai
da abun ya ishe Umma ta zubawa malam ido tana dama kunun tsamiya da safe, shi kuma
yana dokin kofar kitchen É—in, dake Malam simple Man ne kuma bai zafaffawa rayuwa
ba, idan matan shi basu gama girki ba, yakan zauna ya jira su, suna hira dashi aka
shigowa Anum da kofin shayin tare da soyayen kwai da burodi.

Amsa tayi ta gyara zama zata fara ci, Umma ta kalle shi tace mishi.
"Malam wallahi wata rana zaka yi kuka da Anum fa? Taya ga abin karyawan nan a cikin
gidan zaka na amso mata shayi daga waje?"

Juyawa yayi tare da kallon Anum, dan dama da Umma ta titsiyeta cewa tayi Malam ne
yace kullum tana amsar shayin.

Kallonta yayi cikin nutsuwa, sannan ya zubawa Maman Aminu ido wacce ta b'ata
rai akan abinda Umma ta faÉ—a.
"Ni nasaka malam Maude yana bata shayi, dan naga bata son tuwo da kunun da ake
damawa!"

Zuba mishi ido Anum tayi cikin mamaki yadda ya kare ta, murmushin jin dadi tayi
tare da yankan wainar kwai da Maude yayi mata shi kamar bai san zafin nima ba,
tana gama karyawa ta koma d'akinta, tare da kallon basket din ta.

"Mama viju kawai na gani da karamin panke?" Ta faÉ—a tare da b'ata rai,
"Toh me kike so?"
"Ni wallahi ba zan tafi makaranta da wannan abincin ba, naje yara su rena ni!"

Kallonta Maman ta tayi tare da cewa.
"Toh me za ayi miki yanzun?"
"Nifa ba zanci wannan panke

Please Login or Register in order to submit comment