You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita ta amso tare da kifin gwangwani ya zauna yayi wani irin hadi na musamman
sannan ya juye a plat.

Ya fito abun shi, a bakin kofar shiga ya ganta, bai ce mata ta tafasa ba
balle ta kone, kamshin girkin shine ya hanata zama dake kwaɗayi yayi mata katutu.

Cikin rashin kunya ya nufi falon shi, yana zaune ya hada tea, daukar
kofin tayi ta fara kurb'a, sannan ta kai hannunta kan abincin ya fara ci. Kallon
shi tayi cike da mamaki.
"Waye ya koya maka girki haka?"
"Kauyen mu na koya!"
"Hmm! Amma kuma ka iya yi yayi dadi hakan? Hmm! Yayi kyau."

"Ke baki iya girki bane? Ki girka baki mana ki bar min bawa!" Dariya tayi
sannan tace mishi.
"Wani kazamin abincinka mara daɗi, dan na taimaka ina cin abincin ka zaka min
wulakancin banza."

Bai ce kome ba, dan ya fahimci duk masufarta ba bazata iya bar mishi abincin shi
ba, haka suka cinye tare sannan ya mike yabarta a gurin, ta fara kallo kafin barci
yayi gaba da ita. Gudun karta zarge shi yasa shi ya barta a gurin, ya koma d'akinta
ya sami kayan da Umma ta kawo mata a wargaje.

Daukan shi ya bude kwallayen ya jerasu akan show glass, sannan ya nufi sauran
tarkacen ya kai kitchen ya jera su, sannan ya dawo gurinta ya durkusa kadan sannan
ya sumbaci goshin ta, tare da daukarta cak zuwa d'akinta ya ajiyeta sannan ya fita
abinshi bayan ya rufe kofar ta.

......
Duk yadda yaso su zauna lafiya Abun yaci tura, Umma tana bakin kokarinta
ita da Malm Maman Aminu da Hafsat suna kara haukata Anum, a hankali rashin
mutuncin da take yi ya fara fita yawo, idan tana mishi har waje Ana jin su, wani
lokacin fita yake ya bar gidan sai tayi barci yake dawowa gashi ta hana shi hakkin
shi.

Haka yake hakuri da ita,.har aka fara shirin azumi, a lokacin watan su biyu da
aure amma babu canji, domin Mama na zugata Hafsat ma haka, ga XOXO a gefe.

.. a cikin wannan yanayin malam yazo ganinta, da kanshi domin ta kai mutanen da
suke haya a gidan sun fara gulmar anum din, gefe daya mazan suka sami Malam da
maganar shiru yayi sannan yayi musu godiya shine yayi zuwan bazata yaji yadda take
sheka mishi rashin mutunci. Bai ce kome ba ya juya dan dama bai shiga gidan ba iya
karshe tsakar gida. Har sun gaisa da mutanen gidan ya juya ya fita.

Anan Maman Tasnim take buga mata kofa zata yi magana sai ga sallamar Umma.
"Kizo muje."

Hijab ta dauka tabi Umma...
#Mai_Dambu..
[2/2, 5:35 PM] +234 806 041 0931: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA ASHIRIN DA BAKWA.

Cikin rashin hankalin taja hijab tabi Umma, tunda suka fita taga wajen yayi mata
fadi da girma, suna shiga Malam ya rufeta da duka, irin wanda bai tab'a yiwa wani
daga cikin yaran shi ba, duka ne irin na cire haushin da kika bani.

"Wallahi ba zaka kashe min yarinya ba, haka kawai zaka samun yarinya a gaba
bayan auren da aka mata na dole, toh wallahi ba zan yarda."

Ko kulata bai yi ba, ya cigaba da dukar Anum, ran malam ya b'aci dan haka
dakyar Umma ta dakatar da shi, tana gaya mishi.
"Malam karka yi abun kunya idan akwai lalura a jikinta idan ya tabo me zaka gaya
mishi don Allah barta haka bata da laifi."

Wurga da bulalar yayi tare da juyawa ya shiga dakin shi, ita Kuma Maman Aminu ta
shige da ita d'akinta.
"Ai karki damu, haka zai gama jarabar shi ya kyalki. Nagode yar albarka, ki cigaba
da abinda kike yi babu wanda ya isa miki dole shi kuma wancan munafikin zan same
shi har gidan."

. Cire kai tayi tana kallon su Badi'ah, kwalla na zubo mata, ta gyara zaman sannan
tace musu.
"Ban san yadda zan gaya muku ba, amma tabbas zanen kaddarata tayi mugun
shatamin abubuwa da dama, wanda akan maude ya sauka, da ace ban dauki shawaran
mutane ba, da har yanzu ƙaddarar tana nan tare da juna, dan haka ku cigaba da
sauraren yadda na fatattaki masoyi na, na kama masoyan bogi"
Sannan ta cigaba da basu labarin kamar haka.
Haka Maman Aminu ta cigaba da nunawa Anum hanyar da ba zai bulle da ita ba, sannan
ta haɗa mata ruwan zafi ta shiga wanka, tana fitowa ta sami Umma a bakin rijiya
tana diban ruwan aiki.
Sake bokitin tayi tare da matsawa kusa da Umman, zata mata magana.
"Nana KHADIJAH! Jeki don Allah bana son damuwa"

Sake matsawa tayi zata kama gugar ta maza ta sake a rijiya, ya faɗa gaba daya
har da igiyar da sauri ta d'ago kanta tana kallon Umma. Zata mata magana.
"Karki damu, Rulwanu zai cire min..kawai ina Son ki cire Ni a cikin rayuwarki ne
kamar yadda gugan nan ya fada da igiyar shi!

Bana son na kuma jin kin kira Ni da Ummanki, Nana KHADIJAH kije kiyi rayuwar
ki yadda yayi miki, matukar Ubangiji yana sane da abinda kike Allah sai ya fidda
kowa hakkin shi, idan na rike ki da Amana sai Allah ya fidda ni idan kuwa kece kika
zalince tarbiyyar da na miki Anum nasan baki na ba zai kama ki ba, Amma gamu ga
duniya da abinda yake cikin ta."

"Ikon Allah! Maman Sadeeq baki kike sarawa yarinya na, toh Insha Allah ya sauka
akan ku keda Yaranki." Tazo ta ja hannun Anum suka kamo dakin su.

Ranar da dare Maude yazo ya dauke ta, bai ji dadin dukar da malam yayi
mata ba, asalima rarrashinta yake, tsabar damuwa yayi mata yawa, nan take gaya
mishi abinda Umma ta gaya mata, tana kuka.
"Maude ni ba wai bana son ka bane, kawai as my husban ne ban karb'e ka ba, kana da
abubuwan da duk macen da ta gani zata bukata, amma bana son haka, kawai ka barni na
tafi nayiwa Mahaifiyata biyayya."

Kallonta yake kawai ya rasa me zai mata, har suka kwanta kowa da abinda yake
damun shi, Umma ranar kwana tayi idanunta biyu, tana mamakin yadda Maman Aminu take
son kashe auren yar karama yarinyan irin Anum,

Bata kuma tsinkewa ba, sai da taji tana waya akan akaawo
mata abinda zata rufe bakin mutane akan Anum, nan ne ta yarda da duk wanda Allah ya
fitar daga ragamar shi karka ji mamaki.

Bayan kwana biyu, Umma ta zama yar kallo, domin tunda taji labarin
abinda zata yi ta daina cin abincin duk ranar girkin Maman Aminu, asalima tsiro da
azumi tayi, haka ya taimaka mata ainun. Wasa wasa malam ya zama hoto akan sha'anin
Anum.

Dan tun bayan komawar ta, suka fito da wani mugun abu, shine daukar Anum zuwa
unguwa, ko taje gidan yayunta tayi kwana biyu, musamman wanda suke uwa daya Uba
daya,

Maude bai hana su ba,.dan da farko yayi yunkurin dakatar dasu. Amma Maman Aminu
tayi mishi iyaka bayan ta hada shi da shugaban yan Nijar na garin bauchi. Tunda
suka fara magana bai d'aga kan shi ya kalleta ba. Sai ma zubawa kasa ido da yayi,
goldrn eyes din shi sunyi jajjur, har wani oily. D'ago kai yayi lokacin da shugaban
su ya kira sunan shi.
"Kaji abinda surukarka tace."

"Naji babu damuwa."
Yana fadar haka ya mike zai fita.
"Da sake min Y'ata yayi hankalina zai kwanta."
"Ba zan sake Khadijah ba, idan kun matsu ku kai maganar da mahaifinta idan yayi
magana zan san abinyi."
Daga haka ya bar musu gurin, ya koma shagon shi. Tun lokacin ya zuba musu
ido.
-
"Anum ki bani set din aurenki Insha Allah zan baki daga baya baban Annur ne kasuwa
ta juya mishi baya, Insha Allah idan kome ya mishi kyau zan dawo miki dashi." Da
sauri ta mike tana cewa.
"Ayya babu kome, wallahi."
Ta dauko tare da bata, tun daga ranar da ta fita suka shiga, mutunci a nutse ana
cin zarafin Maude..
Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon su, hawaye na zuba mata tace musu.
"Mun zalince maude fiye da yadda baku tsammanin, mun cutar da shi."

Sai da ta kai hatta ruwan shan gidan shi ya fi karfin shi zunzurutun tashin
hankali da rashin zaman lafiya, gashi a cikin gidan gulmar suke.

Umma da kanta ta kira shi suka yi magana, tare da bashi hakuri. Sannan ta
sami Malam yace shi babu abinda zai iya yi akan sha'anin Anum, su je suyi kome ma
yayi musu.

Musa da Bashir suka fara nasu rashin mutuncin, ta hanyar bawa maude notes ya
tashi musu a kofar gidan su, shi kuma basu suka bashi damar zama a kofar gidan ba,
Abubakar ne dan haka ya same shi da maganar, shima ya sami Malam da abinda yake
faruwa.

Malam bai ce kome ba, sannan ya tara su a kofar dakin shi.
"Kun ce maude ya tashi akan wani dalili? Kawai dalilin nake bukata idan kuka fada
nima zan baku goyan bayan ya tashi!".

Shiru suka yi tare da sunkuyar da kan su..
"Idan dan mahaifiyar ku ce, toh idan na yanke sauran igiyar da ya rage zaku sami me
saka ku kare shi? Toh zan kore maude a bisa sharadin zan sake mahaifiyar ku har
abada."

"A'a malam haka duk bai taso ba, Allah ya huci zuciyar ka. Ya sha zaman shi."
Aikuwa ya kafe sai ya kore maude, suka shiga bashi hakuri. Duk yadda
suke tsammanin abu ya ci tura sun nemi Umma tace babu ruwanta suyi duk abinda ya
dace..ta kuma umarci Abubakar ya fita cikin maganar su idan ba haka ba, zata saba'a
mishi.

Umma da yaran ta sun zubawa Mman Aminu da yaranta ido idan ka cire Usman da
Aminu, da suka zare hannun su akan sha'anin Anum da Maman su.
A irin wannan yawon banzan suka tafi wani gidan suna aka saci gwal din me
jego aka wurga a jakar Anum, da aka zo dubawa aka samu, karshe sai da aka dangana
da police Station na , hankalin Hafsah yayi mugun tashi dan haka ta nufi gidan ta
gayawa Maman ta.

Dake bata da hankali sai gashi tana ihu, tare da fadar Abinda ya faru,
Umma tana jin su bata ko tofa ba, har suka tafi..bayan awa daya, suka kuma dawowa
wai an tura su kotu.

Da Malam yaji haka, koran Maman Aminu yayi tabar mishi gidan shi, wasa wasa ana
ta boye abin dan kar Maude yaji,.a hankali maganar ta kai dare wajen karfe tara na
dare malam ta gaya mishi abinda ya faru. Bai ce kome ba, ya koma gida ya kwanta,
sannan ya tashi ya buga mashin din shi sai police Station. Nan ya shiga ya samu
wasu yan sanda biyu, maza a bakin table din sukayi magana.
"Wayyo Allah na, don Allah ku kyale ni wallahi Ni ba yar iska bace, kuma ban dauki
abin wuyarta ba."
Cakume wuyar yan sanda yayi cikin fusata ya daka musu tsawa.
"Waye a tare da mata ta?"
"Yallabai, d.p.o ne kayi hakuri." Wular dasu yayi tare da nufar cikin da gudu. Ya
samu jibgegen ya mata rumfa zai hake mata, ai kuwa ya shiga mishi lugude, sannan ya
d'ago matar shi suka fito. Ganin yadda suka kasa tabuka kome har maude ya bar
Office din, yana fitowa ya haura babur din shi ta dafa kafad'arshi. Dauke kai yayi
dan ji yaƙe kamar yayi ta dukarta, bai san ya zai yi da Anum ba.

Lokacin da suka tawo gida, ya wuce dakin shi, a ranar da dare ya shigar da
karar cin zarafin matar da akayi tare da tura dokokin kasa da ƙasa, karewa har da
dokar yan sanda da na sojojin kasar, a take aka dakatar da yan sanda, dama bawai za
a tura su kotu bane, tunda d.p.o yaga Anum yaji abin ya zo mishi.

Toh bai sami Anum ba,an dakatar dashi..
--- kwana biyu da faruwar haka ya fita zai shiga kitchen, ya same ta tana
kallon fim a falon ta, dan tunda abin ya faru ta rage yawo, kallon gefen fuskarta
yayi wanda yake kwance da jini. Sannan ya dauke kan shi.

Ya shiga tare da hada abubuwan da zai tafita ta kalle shi.
"Wai da gaske Malam bai da lafiya?"
"Eh yana can rimee Clinic!" Ya bata amsa a takaice,
"Toh don Allah meke damun shi?"
"Wai sunce hawan jini"
"Toh, yaushe zan je!"
"Keda kike auren kanki ai zaki iya zuwa ko ina."
"Ban gane ba!"
"Ok wancan lokacin da dan sandan ya kwanta dake babu abinda ya dame ki ba?"

Shiru tayi tare da sunkuyar da kanta, tana wasa da hannunta.

"Amma maude wannan bawani abu bane da zaka saka ranka akan shi" ta faɗa
mishi tare da tsare shi da idanunta..
"Eh ba wani abu bane a gurinki, Ni kuma igiyar aurena fa? Me zaki ce min idan aka
tab'a min kimar shi! Koda yake aikin ce zaki shiga bariki idan na tab'a fatar da
kike ajiyewa me kudi ko?"

Daga haka ya barta tsaye tana bin bayan shi da ido, kitchen ta shiga ta fara niman
abinda zata saka a cikin ta, domin bata san yadda zata iya sarrafa wani abincin
bayan taliya ba, kai ta dauka ta shiga soyawa, tana gamawa ta haɗa tea sannan ta
fito falon, tun zuwanta gashi an kusan shiga azumi bata tab'a girki dan ta ciyar da
maude ba, amma idan yayunta mata zasu zo.
Tare da Nafisa suke aikin abincin, Nafisa yar makotar su ce a cikin gidan take
zaune ta iya girki dake tayi aiki a Abuja...

Haka ta gama karyawa ta zauna tana jiran ko zai ce ta shirya bai fito ba, sai
da ya gama abinda yake zai tafi shago tace mishi.
"Maude jiranka nake fa!"
" Toh maza ina jikin ki, sauri nake!"
"Zuwa asibitin!"
"Baki na da iko da kanki ba, ko ke baki san cewa kina da damar yin yadda kike so
bane?"
Daga haka ya juya yi fitar shi.

--- yana fita, ya gamu da wata mata tana jan yaron ta zuwa makarantar rariya
primary school, sai ihu yake yana tirjewa..
"A'a barshi zan tafi a hankali."
.cike da b'acin rai ta juya, kamar zata yi kuka.
"Idan na sake shi guduwa zai yi!"
"Toh ina baban shi."
"Allah yayi mishi rasuwa shekara daya kenan."
Shiru yayi yana ganin zata cigaba da jan yaron yace mata..
"Bar shi zan kai shi."
Riko hannun Yaron yayi tare da nufar makarantar da shi, ya saya mishi sweet da
cheese,.ya saka akwandon makaranta yaron.

"Idan ka taso zan zo daukar ka, kuma zan saya maka kayan daɗi amma sai kayi
karatu fa"
"Zanyi!"yaron ya faɗa a sanyayye, sannan ya sauke shi....
#Mai_Dambu
[2/3, 8:57 PM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA ASHIRIN DA TARA

_Tun farko na gaya muku labarin nan True life story ne! Dan haka a cigaba da
bibiyar Labarin ✊🏽🤨🧗_


Bai damu da yadda zai tarar da hajjo ba, haka ya dauke ta suka fita rungume da ita,
zai kaita dakin shi tace mishi.
"A'a barni na koma d'akina."

Shigar da ita d'akinta yayi, tare da ajiyeta.
Har zuwa lokacin idanunta rufe tana kuka.
Dakyar ya samu ya tayi shiru, sannan ya fita, bata kuma ganin shi ba, sai jin
muryan shi yana hira da Hajjo, shima a bangaren shi duk yadda yaso zuwa ya dubata
abin ya ci tura.

Dan haka ya ajiye batunta ya shiga kula da Amaryan shi. Wajen karfe biyu na
rana tayi wanka ta shirya tsaf, sannan ta fito dan ta kasa jefa wani abu a cikin
ta, tana fitowa ta samu an mata kaca-kaca da falo, bata damu ba, ta dauki tsintsiya
da parka ta share falon tass, domin akwai wani abu da yake karawa Maude son Anum
tana da tsafta,

Duk da bata iya girki ba, saidai tana da tsafta me ban sha'awa,domin ko shigowa
kai d'akinta ka fita zata bika da sharan ka.

Hango su Hajjo a falon shi yasa ta sauke kanta, dan baya nan. Ita da mutanen
gidan, da gayya suke d'aga murya suna cewa.
"Wasu matan ai gantalallu ne, sun gama raba kansu a waje."

"Maman mansurah Kinga yadda ya hauka ce jiya, kai namijin da ya iya da mace
karshe ne"

Shiru tayi tare da dauke kanta, tana abinda yake gabanta.
"Ai wasu iyayen su, jahilai ne. Ko a tarihi ban tab'a ganin uwar da zata raba yarta
da mijin da take aure ba, koda yake an ci kudin shi gudun kar a zargi tsohon da son
kai," inji Hajjo.

"Tsohon banza ba!"
Wani irin duhu ne ya lullube mata idanu. Da gudu ta koma d'akinta tare da zuɓewa a
kasa tana kuka.

..... Da farkon Auren Anum ta fara watsar da al'amarin Mamanta, domin kwanakin
da ta gama al'adarta zata koma gare shi su fahimci juna, sai dai me?

A cikin abinda bai fi awa daya ba, zuwan HAFSAT da fadar da suka yi da matar
Maude, har ya kai Maude da kanshi ya hana Hafsat zuwa gidan shi dan tace.

"Ke masifa ce a rayuwar Khadijah, babu Alkhairi a tare da zuwaki gare ta, kar na
kuma ganinki domin zan dauki mataki akan haka!"
"Maude yaya ta ce fa, kake gayawa magana son ranka?"
"Anum ba zaki gane wacece ita ba, cutarki take, kuma wallahi daga ranar da ta ga
baki da amfani zata gudu ta barki."

"Haka muka fita da Hafsat duk da ya hanani fita, akan kar na bita, amma
haka na saka kai na bita" kallon su tayi ganin yadda suke kuka wiwi, kamar wanda
aka gaya musu anyi mutuwa.
"Aunty Anum, me yasa?"
"It's about Destiny, it's my Destination, babu abinda zan iya fahimta ina shekaru
sha shida hauka da rashin hankali yayi min yawa, i luv my husban fiye da kome amma
na kasa fahimtar kome akan shi, yayi kokarin shi iya kokarin shi amma ban fahimta
ba, kunga Ni na gaji gobe zamu daura."

"Don Allah kiyi hakuri karfe sha biyu ne na dare ko zuwa biyu zamu tafi!"

Suka fada kamar zasu yi kuka.
"Toh naji amma kunsan me? Shin duk abinda yake faruwa laifin waye?"
" Da farko akwai laifin Malam! Na biyu Laifin Maman Aminu! Na uku Laifin Yayunki!
Na hudu toh gaskiya ban gama hango laifinki ba."

Dauke kai nayi hawaye na zuba, daga idanuna,
"Tabbas sun taka rawan gani a rayuwa ta, amma ku biyo Ni kuji abinda na aikata."

--- tunda ga ranar da tabi Hafsat bai kuma magana ba, asalima ya zuba musu
ido ne dan saura kwana ki ƙalilan a fara azumi.

Wasa wasa, har aka fara azumi Anum bata dawo ba, sai ranar da Malam ya turo
da kaji da danyen nama kayan tea da garin gero, da gyadar kunu tsamiya, yaji na
musamman Umma ta haɗa mata, ga miya na garari da Aunty Rabi ta aiko mata, wai tana
sahoor dashi, sai kayan tea na Aunty Binta, dan tunda ta taso a hannun mahaifiyar
su basu banbanta da su, asalima kamar sunfi yan uwnta ciki daya kula da ita, sai an
Aunty Aminatu, da ta mata kamu aka kulla a laida da surfeffen wake an wanke shi an
gyara tass ya bushe. , a kawo mata Allah yasa yana gida Rulwanu ya zo,
Bayan sun gaisa ya saka almajirai su shiga da kayan.

"Gashi inji Malam da Umma sai su Aunty Binta, nasu kenan wannan tarkacen
Allah Maude yan uwana suna da son kai, dubi shara na Arziki da suka mata"

"Toh ai renon Umma ce!" Inji Maude,
"Ina gaya maka akwai mangyada rabin galan, da manja tare da kudi inji Ya Abubakar,
Ni kuma ko oho." (😜😂 Shifa Rulwanu gani yake Anum ta kwace mishi nashi fadar ne,)

Nan maude ya gaya mishi gaskiyar abinda ya faru, tare da nuna mishi kar ya
gayawa Umma da Malam, yayi alƙawarin haka.

Sannan yana fita ya kira Ya Usman ya gaya mishi tare da Ya Aminu, daga nan ya
zuba ido ya ga wani irin Action zasu dauka.

Bayan awa daya, Aminu da Usman, suka dira gidan Hafsat sun same su, su huɗu har
da Maman su, wacce tasan da cewa Anum bata gidanta. Babu fada babu zagi suka riko
hannunta, zuwa gidan Usman.

"Kina da ciki?"
"A'a bani da kome?"
"Ok zaki ci Ubanki yau din nan ba an jima ba, domin ba zaki kashe mana mahaifi ba."
Birkin mota Aminu ta rufe ta dashi, dake Usman mutum ne me rauni bai iya zama
a gidan ba, Matar Aminu ce ta kira Umma tana gaya mata Baban Amir zai kashe Anum
tazo,

Duk inda za a sami mace bayan Umma ce, dan haka wallahi babu nutsuwa dan ko
takalmin kafarta daban daban ta saka, ta saka Rulwanu ya kawo ta. Tana shiga gidan
ta nuna mata dakin shi, tana zuwa ta buga.
"Bude min kafin na sab'a maka."
Wurga da bulalar yayi tare da budewa Umma ta zuba mishi ido, kafin ta wuce tare da
d'aga Anum da take yashe a sume.

"Bani ruwa Maman me gida!" Umma ta ce mata, da sauri ta kawo
ruwan, ta shafa mata, a gajiye da wahala ta bude idanunta.
"Umma na! Wayyo Allah na wayyo cikina? Zan yi amai!"
Ai kuwa ta fara sheka amai, "idan kuma ka tab'a cikin me zaka gaya masa?"
"Wannan munafukar bata da kome Umma wai ashe Maman mu tasan ta gidan ta, yau kwana
goma kenan? Ba dan an kira Ni an gaya min ba."

"Duka ba zai gyara kome ba, Mahaifiyarku da su Hafsat sune suke lalata min
tarbiyyar Anum, wallahi tana son mijinta, don Allah mu bar wannan batun tsakanin
mu, dan yace matukar yaji wani abu ya biyo baya, ba zai bata kujeran hajjin ba."

Lumshe idanu tai, Umma tasa Maman Amer ta haɗa mata ruwan zafi tana
tambayarta ko tana da ciki ne? Tace a'a.

Bayan tayi wanka Maman Amir ta bata wata doguwar riga, wanda Aminu ya bata sabo, a
cikin kayan da zasu bata na sallah. Ta saka sannan Umma tasa Aminu ya dauke su, a
motar shi ya dawo dasu gidan ta.

Har suka shiga, kuka take kasa kasa, tana gayawa Umma Hajji gori take
mata tare da zagin iyayen ta, dan haka da ta dawo da ita, dama ya gansu yana tawowa
Aminu ya tare shi suka yi magana na Fahimtar juna, sannan yace saka ido akan gidan
shi, bayan na da ya shigo ya sami Umma a dakin Anum, kallon falon Anum da kujerun
ta da aka saka reza aka yaga rigar su. Sai kitchen ɗinta da aka mata barna na fitan
hankalin.

Shima sai yanzun ya fahimci haka, kallon ko ina yayi yaji ran shi ya b'aci,
"Maude ga Anum! Amma kasan ban tab'a maka magana akan Anum ba ko?"'

Ya gyad'a kai, mik'ewa tayi zata fita tace mu yi magana a waje.
Tunda suka fita ta kalle shi kansa a ƙasa ya rasa yadda zai yi.

Allah ya gani kofa biyu ne a gidan bai cika bin ta kofar Anum ba, sai ta kofar
falon shi za zai fitar da kai waje, kofar Anum yasan ya rufe, sai dai yana bawa
Hajjo key tana share mishi falon shi da. Dakin shi, akan me zata lalata mata kayan
ta?

"Ban san me zance ba! A matsayina na Uwar Anum! Idan nayi magana zaka dauka ina
tayata kishi ne!"
Da sauri

Please Login or Register in order to submit comment