You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa taki zuwa asibitin tana taya Uwarta jin
haushi.

Kowa ya cire rai da farkawan, dan haka suka zubawa Sarautar Allah ido,
suna jiran su ga yadda zai yi dasu. Idan kaga Malam sun samu sosai, kasa zama yayi
kuma yaki ya dawo gida, haka ya cigaba da kallon Anum, tausayin jaririn da yake can
gurin kula da lafiyar shi, rike hannunta Umma tayi, tana kallon yadda tayi wani
irin, duk sai ta diririce. Tana tsoron kar ace mutuwa za tayi.

Haka likitocin suka kore kowa, suka tsaya akanta, har Allah ya basu nasarar
dai-daita numfashin ta, sannan suka fito, aka kaita d'akinta dan Malam yace a kaita
wani shashin inda babu hayaniyar mutane.

Turata aminity aka yi, Yaron kuma Umma take kula dashi, sai da aka kwana aka
wuni, sannan Anum ta farka. Shafa cikinta tayi taji shi a dinke, a hankali ta kuma
buɗe idanunta. Umma da yayunta, ta gani suna mata Sannun.

Lumshe idanun ta kuma yi, sannan ta sake buɗe shi akan Maude da yake rike
da Jaririn, murmushin ban mamaki ne ya kwace mata, tana me kara ware idanunta akan
shi, shima murmushi yaƙe, dan ji yaƙe kamar yace yau a daura musu aure, yaje yayi
jinyarta tare da kyautar da Allah ya bata, wani irin farin ciki yake zunzurutun
kaunar Uwar da Ɗan.

Ta kowa yayi har kusa da ita, ya d'an sunkuyar mata da Yaron, yana
murmushi. D'aga mata gira, itama ta mai da mishi tare da nuna mishi su Umma da
idanunta. Tab'e baki yayi sannan ya d'aga kafad'a alamar shi bai gansu ba.

Tari ne ya zo mata, tayi maza zata rike cikin ta, Umma ta rike hannun.
"Ku nimo mana likita, ai dinkin zai warware."
"Zai bari haka yake ai." Inji wata nurse da tazo kansu,

"Taya zaki ce haka? Bayan kina ganin halin da take ciki!" Ya faɗa kamar zai mata
duka.
Duk ita a tunaninta matar shi ce, dan haka tace mishi.
"Kayi hakuri dinkin matar ka bazai warware ba, wannan tarin yana cikin aikin yayi
kyau ne, kuma ai idan ka lura tab'a cikinta aka yi fa, dan haka karka damu zai
bari. Idan zata yi tarin tayi tayi a hankali."

Ce mishi da tayi matar shi, jin yayi kamar zai sume, zunzurutun
farin ciki. Washe fararren hakoran shi yayi.
"Abban Baby! Kwantar da hankalin ka, Ummin Baby zata samu lafiya."

Juyawa yayi ya kalli Anum, b'ata rai tayi tare da dauke kanta, Allah sarki kamar
sauna haka ya shiga hankalin shi, yana kallonta. Duk sai ya basu tausayi.

Haka suka shiga kulawa da ita, ranar da ta cika kwana uku. Maman Aminu
tazo, ta samu Umma tana kokarin a bawa Babyn nono.
"Kin gayawa Mudi? Naga yau kwanan ku uku?"

Bata kula ta ba, mai da hankali tayi gurin bawa nonon tana narkewa Umma.
"Umma na!"
Ta kira sunan tana kallon Maman Aminu,
"Sunan Yarona Isma'il, idan Malam yazo yai mishi huduba da haka,"
Make goshinta tayi, tana fadin.
"Allah ya shirya min ke! Maman Aminu, ki gaya mishi babu wanda yake da number shi."

Daga haka suka ci-gaba da hidimar su, shigowar Maude da laida, sai kayan tea
duk da Malam ya sayo mata, amma bai hana shi kawo babban gwangwanin madara da
Ovaltine ba, sugar me iyali. Sai nutella, ya ajiye.
"Abban Isma'il, wallahi ka bar asibitin nan, kafin na mike naci Uban wata mace."
Fita Umma tayi tare da cewa.
"Idan kika warware dinkin naki, sai ki nemi me zama dake."

Tura baki tayi, tana hararar shi. Tsaki Maman Aminu tayi sannan ya fita.
Tasowa yayi ya zauna a kujera, tagumi yayi sannan yace mata.
"Ranki shi dad'e, kayi hakuri. Wallahi babu abinda ya haɗa ni da wata mace. A amshi
tubana."

Dauke kai tayi kamar ba zata yi magana ba. Ganin yadda take kokarin cire nonon
a bakin yaron shi kuma yana faffutikar ganin ya rike nonon, ya sashi cewa.
"Don Allah bar shi ya sha!"
"Babu ruwanka dani"
"Idan akwai abinda ya fi ruwan dani acikin kuma zan shanye shi tass"
Ya faɗa yana kashe mata ido, rufe bakinta tayi tana cewa.
"Ka shiga uku, kai kan fita ka bani guri. Zan gyara rigana!"
"Oho dai! Yarinya duk boye boyenki wata rana, muna manne da juna sai naga kwal uwar
daka!"

"Abban Isma'il, tsoro kake bani Wallahi, don Allah fita umma ta samu ta shigo
min," ta faɗa tana ware idanunta.

Tab'e baki yayi sannan yace mata.
"Ba mamaki, ina cikin dangin dodanni, shi yasa zan cinye ki. Yarinyar ni ba haka
nake ba, ko mace aka ajiye min gayarta kamar sabon tuwo dauke kaina zanyi.

Ni halittar mace baya birkita min lissafi, ko lokacin da naje yak.."
Shiru yayi sakamakon subul da bakan da yake son yi.
Dariya ya bata, tana yi yana kallon shi.
"Wato lokacin da kaje me?"
"Eh toh gaskiya lokacin da naje Laberiya cirani."
"Hala kaga mata zuka zuka!"
"Ai ba hala bane, domin na tab'a zuwa Somalia, matan su larabawa ne, kyakyawa
irinki."

Dauke kanta tayi tana murmushi jin dad'i, shigowar Nurse yasa ta tsuke fuskar
ta.
"Kije idan ya tafi sai ki dawo!"
Ta faɗa tare da tsare gida, zai magana ta d'aga mishi hannu, dole nurse din nan ta
fita, dan tana lura da Anum ba mutunci bane ya wadacce ta.
"Allah da kayi magana da kaga rigima."
Daukar yaron yayi tare da sumbatar goshinsa, sanan ya kuma sumbatar kumatun shi,
yace.
"D'aya naka, daya na Umminka!"

"Ai na tsani sumbatar nan, shi yasa wancan tsohon banzan ban.tab'a yarda ya
sumba..."
"Mhh-hmm! Wannan tsakanin ku ne, babu ruwan me shayi!"
Daukar ledar ruwa tayi wanda Umma yasha ta rage ya watsa mishi.
Ajiye yaron yayi yana cizon lebban shi na kasa, tare da sake murmushin jin dadi, ya
shafa yalwataccen sumar kanshi, wanda yake kwance, asalin ta buzayen ce. Maude
kamar mace yake yana son gyara gashin kanshi.

"Wata rana zamu kasance abu ɗaya! Zamu zama inuwa d'aya, anan ne
zamu tabbatar da Abu daya muke so, ba kome bane sai kanmu, a ranar zan watsa miki
ruwa cikin so da kauna, zaki kuma kare fuskarki cikin farin ciki da shagala, a
lokacin ne kaunar mu zata tabbatar gaskiya ce."
D'aga kai tayi tana hango yadda suke wasan agwagi da ruwa, tare da dariya da farin
ciki, tana kare fuskar ta, yana watsa mata ruwan. Sai kokarin take ta boye
fuskarta.
"Malama don Allah dawo daga duniyar mafarki, Allah ya nufe ki da shirya."

Jan matashin kanta tai tare da buga mishi tana dariya.
"Wallahi ka cuce ni, duk bayanin da kayi min, duk na ganshi a zahiri."
"Toh ai kuwa kina da aiki, domin mafarkan mu,.ba zasu kare ba Anum sai ranar da
muka tabbata a tare! Daga nan duk bayan shekara daya sai."

Shiru yayi, lokaci guda ya sauya fuskar shi, bai yi niyyar tafiya ba, haka ya
sallame ta.

Tunda yayiwa Umma sallama, tare da Maman Aminu, yake zancen zuci.
*IDAN NA FAHIMTA NINE BANA HAIHUWA! TUNDA GASHI NAN YA AURI HAJJO BATA TAB'A KO
B'ATAR WATA BA! INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJIOUN UBANGIJI NAGODE MAKA DA JARABTA
NA DA KAKE YA ALLAH KA BANI IKON CINYEWA*
Da wannan tunanin ya isa shagon shi, cikin damuwa ya kalli Ila.
Anya ila bani ne bana haihuwa ba kuwa?"
"Kai haba, nafi dauka a kan lokaci ne bai yi ba, sai kaga idan yazo kamar habo."

"Amma baka ga har yanzu Hajjo babu labari ba?" Shiru ila yayi, sannan ya sauke
kanshi kasa, kafin yace.
"Nafi zargin cewa lokacin ne da saura, karka yiwa Ubangiji butulci, kasan dalilin
da ya baka aron numfashi a karo na biyu bayan an saka duk wanda ya ganka ya harbeka
ka? Yana da dalilin shi na sake baka damar ka cimma wata rayuwar shi yasa har kake
raye sai kace mishi Alhamdulillahi."

Kuma sai jikin shi yayi masifar sanyi, domin Ila bai barshi haka ba,
Cigaba yayi da mishi nasiha ta hanyar nuna mishi yadda rayuwa ta juya mishi baya,
lokaci guda ya koma me shayi, dan haka kar ya ce zai d'aga hankalin shi akan
haihuwa.

Jikin shi yayi mugun sanyi, fiye da baya, dan haka yayi ta astigifari, yana niman
yafiyar Ubangiji.

**Kwanan su Anum shida aka sallame ta, tare da dan ta, da lafiyar shi lau,
sai da aka sallame su sannan Alhaji Mudi ya samu labarin haihuwar ta bakin XOXO
wacce suka dinke kamar da baya can.

Ya kwaso kayan shirmen shi ya kawo amma Anum taki amsa, yaron ma Sai da aka
mishi Addu'a sannan aka kai mishi zaure, gashi yaron ya dauko kalar fatar uwar shi,
jajjur dashi har gashin gaban goshin Anum, haka yaron ya dauka. Haka ya gama santin
yaron, sannan ya bada aka mai da mata D'anta da bera dubu goma, tsigai ta fito zata
bala'i. Maman Aminu ta tare ta da nata bala'in dole ta koma, tayi ta kuka, ita kar
Alhaji ya cinye mata yaro tunda duk cikin sa take samu shine sanadin su.

Daukar yaron Umma tayi ta mishi Addu'a, sannan ta mai da mata D'anta.
Ai dan ráshin yarda sai da ta saka Rulwanu a gaba da tijara, ya kaiwa Maude dan ya
duba mata shi.
"Kan Uba! Ni sa'anki ne? Wato na baki jini na kuma ba zama boyi boyinki, ga katon
dan iska."

"Babba ma kuwa da kahonka." Cikin masifa ya fara bala'i.
"Idan na yarda Dan iska nake, yarinya dawo min da jini na, na fasa kyautar, wallahi
zaki dawo min da jini na, ai na gaya musu da zaran kika min rashin mutunci zaki
biya ni jini na."
Itama cikin jin haushin yaki kai mata yaron ta shiga mishi tijara,
"Dalla matsa wani banzan jininka mara kyau, da nasan jininka za a saka min na
rantse da nace su bar ni da cikina yar yau, dube shi zololo dashi kamar bishiyar
rimi."

"Umma kina jin ta ko?"
"Ai ta jima da jina bata da lokacin ka malam ficce mana a dakin mu ko na maka ihun
Barawo."

Aikuwa ya bude murya yana masifa kamar zai daki Anum, Umma kuwa taki magana,
domin daga Rulwanu har Anum sun gama bata haushi, matukar tayi magana toh ba
makawa, zata iya binsu da Muciyar tuwo.

!Dariya suke tare da cewa.
"Yanzun Aunty Anum, har yanzun kuma kuna irin wannan abun?" Dariya nayi tare da
dauke kaina. Nace musu.
"Ai sabida na dauke mishi Ummar shi ce yasa yake kishi dani, so muna kaunar junan
mu, amma fadar mu tafi wanzuwa cikin jama'a har umma tasan muna kaunar juna,
Rulwanu yayi min halicci ainun, Rulwanu ya min abubuwan da bazan tab'a matan dashi
ba, dan haka bana jin zai iya daukar fadar mu a matsayin k'iyayya ce da kishi, a'a
kaunar muce haka."

"Aunty Anum!"
"Na'am Badi'ah!"
"Kin koma gidan Abban Isma'il?"

Murmushi nayi sannan na matsa yatsun hannuna,.kafin na cigaba da basu labarin.

------
Aikuwa haka ya fita yana hayagaga. Sai bayan fitar shi Umma ta shigo itama, dariya
suka bata, tare da cewa.
"Keda Rulwanu zaku mannawa mutane hauka, gashi can Maman Aminu tana dariya har da
zama sai dariya take tana kumawa"

Itama Anum sai lokacin ta fahimci fadar nasu, kai abin dariya.

Satin su daya aka yi suna, kasancewar sunan Bauchi da yamma ake shiga basu yi wani
gayya ba, Ranar sunan Alhaji ya kawo raggo, Maude ma ya saya nashi. Aikuwa Anum
tace sai dai a yanka mata Ragon Maude shi take bukata.

Haka kuwa akayi malam ya sayar da Na Alhaji aka sayo wani Ragon dashi, ita dai
Anum abin hannun Alhaji ne ba zata amsa ba.

Bayan suna,Umma ta cigaba da kula da mai jego da D'anta, sunyi kyau kamar basu
ba. A yanzun hidimar da Maude yake tasa yan gidan suna jin idan Anum bata aure shi
ba, su zasu mata dole ta zauna dashi sabida yadda yake hidima dasu ita da D'anta.

A hankali rayuwa take tafiya, cikin hukuncin Allah. Tare da buwayar, domin
shine Buwayi gagara misali.
**Bayan wata goma sha bakwai.
Mafi yawancin mutane suna daukar abinda suke so ko suke bukata shi zai tabbata,
a'a shi Ubangiji ikon shi yake wanzarwa,. ita zanen ƙaddara a rubuce take tamkar
yadda zanen tafin hannun yaƙe, babu wanda zai iya isa inda kaddarar shi bai kai shi
ba, haka zalika wani lokacin hakuri da sadaukarwa takan cikawa Muminin kwarai
mizanin shi.
*Alhaji Hamisu Natsira me shagon gwala-gwalai....*
#Mai_Dambu...
[2/12, 10:20 AM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN DA BIYAR
*_Wannan shafin na yan Groups ne musamman grps ɗin da nake cikin su. Fitilar
hikayata! Sansanin Mai_Dambu! Zanen Qaddara ta Fans grp, Zanen qaddara ta Novel
Group! Zanen Qaddara ta Grp 3! Muamalata Novel Group! Matan Quarts Novel Group!
Furucina Grp B, Duniyar Littafin Hausa!Zainab Bawa Novel Group! GOBE NA Comments
section!Aisha Muh'd NOVEL GROUP, Aunty Halisso Fans grp Tare da Inda ban ambata ba,
Kuna Raina😂🤣 Don Allah karku manta da hayewa katanga 🤨😂 🙏🏼 Thank You Heart You
all...._*

Hamisu Natsira...

Wato alamarin Ubangiji, cike yake da mabanbanta ƙaddara, domin sai ka shirya naka
tsarin Ubangiji sai ya kawo nashi tsarin, kina da tsari.wancan yana da tsari amma
duk tsarin Ubangiji yana sama da na kowa.

!kallon su nayi naga jikin su yayi sanyi, sannan na sunkuyar da kaina na
cigaba da cewa.!
Al'amarin aure tankar habo ne, duk yadda ka so tsayar da jinin da ya hudo daga
ƙwaƙwalwar ka ba zai tsayu ba. I zuwa yanzun na fahimci dalilin da Ubangiji ya
nisanta mu, ya kuma tabbatar da ikon shi bayan faffutikar ganin mun zama tsintsiya
madauri ka daya.

A iya yau gare ni, gobe ga wani na ne, karka sake damar moran lokacin
ka ta wuce maka baka ribanci abinda ya dace ba, iya yau kawai zaka riskar.
(Wayyo Allah na! Wallahi hannuna ya fara ciwo fa🤗☺️bari mu gani ko zan kai labari)

Nayi rashin Abubawan da yawa, kuma nai laifi da kaina,.wanda na sani
har abada ba zai yafe min ba, amma ita ƙaddara idan tazo maka babu makawa sai an
isar dashi gare ka."
....
Wanke take sabida kayan Isma'il da take tarawa, d'azun suka gama raba hali da
Rulwanu, ba kome ya janyo haka ba, sai dan ta yayye Isma'il, yaron yana ta kuka har
da ajiyar zuciya, shine ya kawo mata shi.
"Dan Iskanci kin san ba zaki iya kula dshi har ya girma ba, kika yaye shi. Toh
wallahi ki bashi abincin shi ko muyi rigima dake."

"Ina ga kamar akwai nono a kirjinka? Tunda a kwai sai ka bashi ka huta da jin
haushin abinda na mishi" ta faɗa tana dariya.
"Maman Aminu, kina jin abinda yake gaya min ko?" Ya Fada kamar zai saka kuka,

"Ke Anum bana son rashin hankali, ki dauki yaron nan ki bashi abincin shi." Ta faɗa
mata a hasale,

"Ba zata bashi wani nono ba, kawai ya hada mishi kunun shi ta zuba a fidar shi
ta bashi ya sha, wannan me kama da zabiyar. Kwana yake yana tsotson nono"
Inji Umma, garin ta mike kawai wata zare ta rike mata zoben gwal ɗinta. Aikuwa ya
karye.

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Umma zobena ya karye." Ta faɗa da ƙarfi,
Cire zoben tayi kamar zata fashe da kuka.
"Toh ai sai ki shirya ki kai central yanzun."

Umma ta rike tare da juya.
"Ina da kudi kawai na sayar musu na sayo wani."
Dan gwara mata goshi Rulwanu yayi tare da cewa.
"Ba zaki gyara ba?"
"Ai ba naka bane, balle kace sai na gyara maka, Umma kice ya fita harkata."

"Wai Rulwanu, hanjin juna kuke gani ne kai da Anum?" Inji Malam yana shigowa,

"Wallahi kuwa malam sai kace wuta da auduga." Inji Umma,
"Amma ai Anum bata da gaskiya." Inji Maman Aminu,

Anum bata kuma bin takan su ba, ta shiga wanke kayan da sauri ta dauraye,
sannan ta shiga ban daki tayi wanka, tana fitowa ta shafa mai me gurguwa, sannan ta
shirya cikin riga da zani na atamfar bakar mace.

Tayi kyau sosai musamman da ta daura farin hijab da Nikkab akai, sanan
ta dauki Isma'il, ta rungume shi zasu fita.
"Ummana Maman Aminu, Malam dina, bari na shiga Central market yanzun zan dawo." Ta
ce musu.
"Toh Ubangiji ya dawo dake lafiya,ya kuma tsare hanya."
Juyawa tayi tana murmushi, sannan ta fita daga gidan.

Tana fita, ta tsaya a gaban shagon Maude, wanda yake ta lissafin shi.
"Takuttuta tiya!" Da sauri ya d'ago kanshi yana dariya, sannan yace mishi.
"Haba da gaske!" Aikuwa Yaron ya kuma lallaiyayo mishi wata gwarancin ya makawa
maude. Shi kuma da taya bera barna yace.
"Don Allah? Umminka naji labarin mugun aikin da tayi maka."
"Ke shige zaure, ki gaya min waye ya baki shawaran yaye min yaro daga jikin dadin
da yaƙe?"

Dariya tayi sannan ta ajiye mishi yaron, tace mishi.
"Zan je Central market na dawo, idan na dawo sai na baka amsa dai dai da tambayar
ka."

"Lallai kin ci Amanar yarda da muka baki,sai kin dawo amma ki tafi da yaron kar
wani ya ganki ya dauka budurwa ce." Ya faɗa alamar babu wasa a maganar shi.
Kuma ta fahimci abinda yake nufi, dan haka ta amsa, fitowa yayi tare da
tsayawa a gabanta.
"Karki damu, idan aka ganki babu wanda zai dauka budurwa ce, Ina Kaunar ki ne. Shi
yasa bana iya sarrafa kishina"

Gyada mishi kai tayi sannan tace mishi.
"Toh bari naje na dawo."
Shi ya tsare mata keke napep, suka shiga ya kuma biya kudin kai su.

Jikin shi yayi sanyi, musamman yadda yake ganin wannan karon ya Sami
Anum Insha Allah, ya sashi kuma samun kwarin gwiwa..ya nufi gurin aikin shi. Mutane
na mishi tsiya, murmushi yayi sannan yace musu.
"Anum ta sauya fa, ba wacce kuka sani bace."

---- Lokacin da ta isa kasuwar, shagon mijin Aunty Binta ta fara zuwa ta
ajiye Yaron kasancewar akwai yaran Anunty Binta Babaji da kuma Bababa, sai
Muddamsir. Da Muh'd Takwaran Malam, Shukrah itace babban su. Sai yar autar su me
suna Farha.

Yana ganin su ya kama d'aga musu hannu, aikuwa ta zauna tana cewa.
"Angona! Ya naga sai hada kumatai kake? Gaskiya Aunty Binta ta iya riko"
Dariya ya saka mata, suka gaisa sannan yace mata.
"Karki damu, sai ayi musaya dan naga zaki fi dacewa dani!"

"Tabdijam! Yasin bana wannan wasan da kai." Tun tana yarinya yake cewa, a sauya ta
Aunty Binta.

Dariya yayi ta mata sannan ya tambaye ta, me ya kawo ta kasuwa, anan
ta ciro zoben gwal ɗinta ta nuna mishi. Kallon Babaji yayi sannan yace mishi.
"Zoka kai ta Shagon Hamisu Natsira!"
"Toh Abba"
Babu musu ya shiga gaba zata tafi da Isma'il yaki dole ta barshi a shagon, tabi
bayan babaji.

Basu yi wani tafiya me nisa ba, suka isa shagon, nan babaji ya nuna mata
shagon wanda yake dankare da gwala-gwalai, ga cctv yana juya ko ina, abinda ya kawo
tayi, yana can kuryan shagon, yana bin duk wani shiga da fitar mutane ta tv, d'aga
nikkab din tayi, tare da cewa.
"Barka dai, na kawo zobe na ne, ina son naji nawa gyaran shi, idan ba zai gyaru ba
nawa za a sake min wani,"

Yadda take maganar da yadda idanunta suke kiftawa, ya sanya mishi wani irin
yanayi, wanda rabon shi da yaji tun shekarun bayan, haduwar shi da matar shi.uwar
yaran shi.

Kura mata ido yayi, ta tafi da Zuciyar shi, dan haka da kanshi ya taso. Ya tsaya
suka fara ciniki, karshe ya duba zoben yace mata.
"Ranki shi dad'e,me zai hana a baki wani irin shi amma wannan ai ta karye ta wuya
tane, kuma ai ba girmanki bane amsar joni joni,"
Sam bata kawo akan da wata manufa yake maganar ba, dan haka tayi murmushi tace
mishi.
"Babu damuwa, muga wasun!"
Haka ya ciro mata wasu masu kyau.

Ta zab'i wani me kyau sannan tace mishi.
"Nawa zaku sayi wannan ɗin?"
Murmushi yayi sannan ya zuba mata ido, kafin yace.
"Kamar yadda me shi take da tsada!"
Ware idanu tayi akan shi, sanan tace mishi.
"Toh don Allah kayi magana ina sauri ne na bar Yarona a shagon Alhaji Ahmed
Bababa!"
"Ai ke yar uwan matar shi ce ko? Sai yanzu naga kamar ku da Maman su Bababa, toh ba
damuwa, dan haka zan saya."

Nan suka tsayar da cinikin itama ta biya wanda ta dauka.
"Baki ce min kome ba?"
"Eh toh ni matar aure ce"
Ta bashi amsa, zata juya.
"Sam maganarki ba haka bane,baki yi kama da matar aure ba, zan yarda idan kika ce
min ke bazawara ce, amma hankalina ba zai dauka ba da kice min me matar aure ce."

Shiru tayi sannan ta juya ta fita abinta, dan tasan zai iya biyota.
Tana isa shagon ta samu sun sayawa Isma'il doya da kwai, an saka mishi a gaba
da namar kaza.
"Ni tafiya zan dan ba zan jira ka ba!"
"Toh guguwa! Ko nace ruwa ba, ki nad'e mishi a cikin laida sai ku tafi." Yadda take
sauri sauri yasa shi cewa.
"Khadijah!"
A firgice ta juya tana kallon shi.
"Wani abu ne?"
"A'a yallabai, guduna take. Ashe sunan ta Khadijah. Taki ta gaya min sunanta"

"Anum baki gaya mishi sunan ki ba!" Inji Mijin Aunty Binta,
"Sai anjimar ku!"
Ta dauki danta suka bar kasuwar kirjinta yana bugawa da sauri da sauri.
"Alhaji! Kanwar matar ce?"
"Eh autar su Binta ce."

"Don Allah kayi min jagora mana zuwa ga sirikinka" Inji Alhaji Hamisu Natsira,

"Gaskiya ba zan boye maka ba, Kwai wanda aka hada ta dashi mijinta na farko, kuma
yanzun ina ganin zata koma gurin shine." Ya faɗa.
"Amma an yanke rana ne?" Ya tambaya.
"A'a ba a yanke ba, amma kuma."
"Don Allah ka taimaka min mu jaraba, sai an gwada akan san na kwarai."

Haka yayi ta rokon mijin Aunty Binta, har ya shawo kanshi. Suka ajiye maganar
tunda gobe Juma'a sai su je su gwada sa'ar su.

---
"Alhamdulillahi!" Ta furta lokacin da ta iso gida, murmushi suka sakewa juna,
sannan ta tsaya a window shagon ta nuna mishi zoben, nan suka tab'a hira, sannan ta
shige cikin gidan.

Hafsat ta samu, gaisawa suka yi sama sama,har zata wuce tace mata.
"Har yanzun baki sami abin wuyana bane, ko mutuwa nayi ina da wanda zai ci min
gado, gaskiya a nimo min abuna, ko na kai karanki gurin Malam"

"Karki min rashin kunya, akan wasu kayan banzan ki can,kuma ba zan biya ba." Ta
faɗa a gadarance.
"Wallahi zaki biya, tunda babu guminki a cikin shi. Sai kin biya ni kayana."

"Ba zan biya ba, ƙaruwar banza ƙaruwar wofi, wacce tayi cikin shege." Ta
faɗa tare da dariya tana kallon Anum wacce jikinta yayi mugun sanyi.
Kowa a gidan sai da yayi bakin ciki da abinda ta faɗa.
"Naji Ni karuwa ce, amma a biya karuwa kayanta, idan ba haka ba , wallahi na rantse
da wanda rayuwata da mutuwata take hanun shi, sai na nuna miki karuwanci a garin
nan, ba Ni kika kira karuwa ba? Zaki ga.."

"Ya isa! Bani Bin wuyarta, dan shine a jikinki?"
Shiru tayi tana kallon Anum, sannan ta mike ta cire kome, sannan ta mika mata.
"Insha Allah, yadda kika amshi she kin amshi bakin ciki har karshen rayuwarki, mu
zuba ni dake."

Shigewa daki Anum tayi, Umma

Please Login or Register in order to submit comment