You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

glass na dauki turaren wuta na nufi
dakin shi da shi.
Ina gama sakawa na fito.
Da Sharifah muka hadu, bata min magana ba, nima ban bi ta kanta ba.
D'akina na dawo yana cin abinci har zuwa lokacin, zama nayi nima na dauki
cokalin ina taya shi ci.
"Me yasa zaki cinye min nawa?"
"Me maganar ma idan ya sake ba kama shi, fyade zan miki;"
Na fada ina tsare gida kamar yadda yake min.
Dariya na bashi, haka muka gama cin abincin na kwashe kayan na fito dashi, ina
sauka na gan su, kowacce tana cin abincin ta.
Bayan na gama wanke kayan na ajiye sauran abincin a firij na juya zan fito.
Suka tare ni.
"Jikinki yana rawa zaki kwana da mijin mu ko?"
Dariya suka bani, sannan nace musu.
"A'a me zan cire a jikin shi? Kawai dai zanji yadda kuke ji ne."
"Ke mu kike wa rashin kunya?"
Rabawa nayi zan wuce suka kuma matse hanyar, tare da kai min duka fa, ihu na saka,
ko kafin ya fito, tulatulan mata masu manyan dantsuwa sun make ni, duka sosai suka
min.
Lokacin da yazo ina kwance a kasa, bakina ya fashe haka ma hancina.

Ranshi ya b'aci dan haka ya juya zai fita.
"Ka kyale su! Ai kai ka basu damar su min haka, dan haka babu amfanin kullum kayi
min fada ni me nake yi.da bazan yi fadar kai na ba,"

Haka na hana shi musu magana, ya taimaka min na haura sama, da kanshi ya kula
da ciwon da suka ji min, bayan nan haka yayi ta kallona, karshe kwanciya nayi
abuna,ina son nayi kuka amma ban son hankalin shi ya tashi.

Duk yadda naso na tare su, ba zai yiwu ba, dole sai ya daina fushin nan dani, idan
ya kasance haka toh zan iya haukata su. Haka yayi kwana dayan shi, kowanne mu a
dakin shi ya kwana, washi gari na shuga kitchen nayi mana abin karyawa na kai sama,
na kuma zuba na su Hajja Dijamah da Mamn shi, na kai musu da kaina na gidan liman
na fara kaiwa.

Sannan na nufi cikin gidan su, na gaida Matan baban shi, sannan na shige shsshin
mahaifiyar shi, ban tab'a shigowa ba sai yau.
A hankali na shiga cikin dakin, da sauri Sharifa ta amshi basket din hannuna,
"Barka da safiya, da kanki kika kawo?"
"Babu kome!"
Zama nayi a kasa, kasancewar mahaifiyar su tana saman kujeran falon, a hankali na
d'ago kai tare da cewa.
"Ina kwana Umma?"
Kallon juna muka yi,
"Ikon Allah! Khadijah"
Sai lokacin na tuna itace matar da ta bani shawara akan aurena da shi wancan
lokacin, kunyarta da girman ta, ya cika min ido. Nan muka kuma gaisawa.

"NUSAIBAH, zoki saka mata abinci." Ta kira wata Kanwar shi. Yarinyar bata da
sakin fuska, dan haka tana zuwa ta zuba min tare da dangwarawa a gaba, tana ja min
karamin tsaki.
"Nagode!"
"Munafuka;"
Kallonta nai sannan na sauke kaina ƙasa, a hankali na fara cin abincin, kadan naci.
Na bar sauran sai kunun tsamiya ce fa nasha sosai, anan muke hira da ita jifa jifa,
jiran duk nasiha ce da godiyar da tayi na...
#Mai_Dambu

ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Ka

BABI NA SITTIN SHIDA.

Na yadda na mai da ta mutum, ba tare da kallon yanayin ta na saniyar ware ba.
Murmushi nayi sannan na nuna mata ita Uwar mutumin kirki ce, kuma wanda ya bawa
rayuwata gudummawa. Babu abinda zata nima na gaza mata.

A nan muka yi ta hiran mu, har ya Shigo, zama yayi tare da harara na.
"Me yasa baki gaya min kina nan ba!"
"Babu inda zanje bayan gidan Liman da nan!"
"Asadullah! Kana takura mata fa"
"Innarmu kawo miki kara na tayi?" Ya tambaye ta yana kallonta.
"Na gaya maka kowacce mace sakarya ce da zata mai da kai kara wani abu me
muhimmanci a rayuwar auren ta? Ko daya karka kuma zarginta domin bata yi kama da
ballagaza ba."

Murmushi yayi Ni kan, ban ce mishi kome ba, bayan amsar da na bashi, idan
ya fara kananun magana zata dakatar dashi, ta hanyar buzanci dole ya hakura, sai
karfe ɗaya saura na bar gidan na nufi kitchen gidan ban ga kowa ba, dan haka na
gama girkina da sauri dan bana son tashin hankali.

Ina gamawa yana shigowa, ban san ya shigo ban dan ina wanke hannuna, jin hannun
shi nayi a bayana, a firgice na juya da wuka.
"Anum!" Sake wukar nayi, tare da fashewa da kuka.
"Me aka miki?"
"Na zata sune suka kuma dawowa"
Jinjina kai yayi sannan yace.
"Daga yau karki kuma daukar mataki domin kare kanki, ba dai ina nan ba."

Wuce shi nayi na haura sama da gudu, karasa sauran aikin yayi ya biyo ni,yaji
kofana a rufe. Na sha kuka sosai. Sannan ba share idanuna.

Ban fito ba sai ƙarfe biyar, na sauko kasa, yana zaune a falon.
"Meye nufinki?"
Banza nayi dashi, tasowa yayi tare da juyar dani!
"Ina magana kin mai dani dan Iska!"

"Toh kayi hakuri;" nace mishi tare da barin gurin shi. Abincin da na saka
mishi naga bai ci ba, juyawa nayi na kalle shi.
"Baka ci abincin ka ba?"
"Ba zanci ba!"
Hawaye ne na ya fara sauka min,
"Yanzun Dadda!"
"Idan da kina son naci ba zaki barni a waje ba, me nayi miki kike azabtar dani?"
Kura mishi ido nayi, sannan nace mishi.
"Kayi hakuri!"
"Wai Anum me yasa mike bani hakuri? Babu wani abun da zaki min nayi magana baki ce
min nayi hakuri ba."
"Toh Afuwa!"
Na gaya mishi, karshe haka ya zauna na zuba mishi abincin yaci yana mita, wai zamu
haukata shi. Ban ce mishi kome ba. Kallon shi kawai nake yi.

Haka ya gama kwanakin shi ya koma, sai lokacin naga matan shi sun dawo,
ashe koran su yayi. Bayan ya bayan yabi su da belt yayi musu duka suma, bayan
fitana zuwa gidan Innarmu.

Aikuwa suna dawowa suka taso ni gaba, ba halin na fito girki suce zasu dake
ni, dan haka na daina fita suna nan, abin karyawa da na rana nake yi, na dare kuma
na nufi gidan kakan su.

Zunzurutun bana son ya Mani da laifin na saka shi tashin hankali. Amma matan
nan basu Fahimci haka ba, sai suka d'aga min hankali. Ranar ina wanka suka biyo ni
zasu dake ni, Allah yasa na rufe kofar d'akin, dan haka ina fitowa na kira shi, na
gaya mishi.

Shine ya turo Zurkhalaini ya fita dani, daga nan ya kai ni gurin Liman, ai kuwa
ya gayawa Liman ya same su da bulala zasu dake ni.

Babu shiri aka hada family meeting, abin da ya matukar girgiza ilaihirin Zuri'ar
su kenan. Har shima sai da aka nimo shi ya dawo.

Tunda muka hadu, Liman yace.
"Zurkhalaini kace ya kasame su?"

Gyara zama tayi sannan ya ce.
"Wallahi na same su da Bulala zasu dake ta, suna buga mata kofar d'akinta."

Shiru iyayen su, suka yi.
Wannan ba shi bane karo na farko da suke dukar ta ba, sun tab'a haduwa suka mata
duka, wanda yaji shima ya rama mata, har kuke cewa na fufita shi akan su. Yau ma
banda Allah yaso haka zasu taru du dake ta, sabida ba yar dangi bace. Dan haka Ni
na maka izini ka dauki matar ka, ku tafi, idan ka sami lokaci zaka na zuwa kamar
yadda na ce maka."

"Amma Baffa baka ganin ya shiga hakkin su?"
Kallon Hajiya Gaje yayi sannan yace mata.
"Dani dake waye ya san ya kamata? Ko mijinki bai da ikon tsallake abinda nace, ka
dauki Khadijah ka tafi da ita!" Daga nan ya yiwa kowa tass, sannan yayi mana
addu'a.

A ranar muka bar garin, bayan ya taimaka min na hada kayana, ina kallon shi,
yana b'ata rai, a raina nace.
*Gulmamme kawai*
Haka muka bar garin, wanda sanadin haka na sami Yanci.

Koda muka isa babban gida ne me kyau sosai, haka ya nuna min d'akina. Tunda
muka samu damar Ni shi. Ya kuma tsiro min wulakancin, baya shiga min, ko nayi
abinci zai dawo yace ya koshi yaci a waje..

Kuɗi kuwa wallahi har na rasa inda zan saka shi, Ni kuma ina jin kunyar nayi mishi
magana akan hakkina, sai na zuba mishi ido.

Lokacin da muke waya da Aunty Safiya nake tambayar ta ya jikin Hafsat da Isma'il,
nan take gaya min ai ya jima a Saudiyya, ya tafi karatu. Amma Dadda bai gaya min
ba, nayi kukan farin ciki sabida ya cika alkawarin da ya dauka min, da ya dawo na
mishi abinda na saba yace ba zai ci ba.

"Akan me ake wulakanta ni?"
"Saboda zuciya ta tana gurin yarinyar da nake so! Dan haka kiyi hakuri."
"Aure zaka yi?"
"Ai zaki hana ni ne?"
"Allah ya sanya Alkhairi!" Na fada ina kuka, kiran Aunty Binta nayi ina gaya mata,
dariya tayi min.
"Anum! Kina da diri me kyau, kika sake kina kuka, idan kika kuma kira a irin wannan
yanayin, sai na baki mamaki, kiyi fada domin mijinki, sai kace baki zauna da su
Xoxo ba, kin manta baya ne? Kiyi kokarin daidaita rikicin ku, sauran kuma zan miki
bayani."

Kashe wayar nayi kafin na fito, ina kallon shi, komawa dakin nayi na sha wanka,
tare da tsefe gashina, jika shi nayi tare da tsantsame shi, sannan na saka wasu
shegun kayan barci, na dawo da gashina zuwa kirjina, kitchen na wuce, Ban ko kalli
inda yake ba.

Haka na tsiro mishi Iskanci nima, ai ba dutse bane shi balle yace
ya fi karfin sha'awa.
Kullum ina update Iskanci kala kala, tun yana share ni. Har ta kai idan ya
ganni sai ya make min mazauni na,

Cizon bakina nake, tare da kallon shi na wuce. Tsakanin mata da miji sai Allah, sai
gashi da yar murya yana cewa.
"Ni bana son damuwa, wani irin Iskanci ne Zakina yawo tsirara? A cikin gidana."
"Ai haka ne? Toh bari nayi fuck dinka yadda bakin ka ba zai kuma cewa ina yawo
tsirara ba."

Aikuwa na shiga aika manyan makaman yakina, tare da nuna mishi yau ko ni ko
shi, hmm.
Hmmmm! Gulmamme, sai gashi ya ma fini zakewa, fushin da ba kwanaki da gajiyar shi
ya sauke.

Yo mijina dai jarumi ne, mutum ne nagartaccen me sanin ya kamata,.yana da kyau
da sanyin hali, yana da kokarin isar da mace bukatar ta, sai da ya jiyar dani,
kome sannan ya kwantar da ni yana shafa bayana, ajiyar zuciya ya sauke yana
kallona.

---- Tun daga ranar muka bude kofar SOYAYYA, irin na bugawa a jarida, sosai
muke bawa juna hakkin mu, ina ƙoƙarin bashi hakkin shi, shima yana ƙoƙarin sauke
nauyina.

Wata na biyu, muka tawo Damagaran, matan shi kamar zasu cinye shi da korafi,
musamman da yayi wata haske da haiba, nutsuwa ta same ruhin shi.
Shi kanshi yana jin cewa, kamar ya samu duk abinda yake so, dan haka ina
dawowa na gyara gurin mu, tare da niman abinda zanci.

Duk da ina ƙoƙarin kiyayye musu, sai na lura da kishinsu Jahilin kishi ne,
sai na fara aiki na yadda ya dace,

A ban kowa ina iya barke mishi tare da kirkiro rigima, haka yake sake kome
yana tambayana lafiya.

Tunda na fahimci yana tare dani, na fara shiririta da shirme, saka kayan da
yayi min, ko kuma nazo nayi mishi oyoyo,

Haka yana matukar bata musu rai, dan haka. Aikuwa sai ga A'isha ta fara mishi
oyoyo, gata ba kadan ba. B'ata rai yayi sannan yace mata.
"Ke ina zaki? Tsaya anan ke ko kunya baki ji ba? Abinda yara suke yi zaki yi? Koda
kika ga ina daukar Anum ai dan yarinya ce qarama, dan haka don Allah ki daina
wannan haukar dan bata miki kyau ba."

Yana gama fadar haka ya wuce abun shi, nan dai suka ji haushina, dake naga Hoor
bata tare da mu, dan haka shigar kananun kaya nake, sosai ina murza iskancina, dan
Allah ya taimake ni yana juyin karshen shekara.

Aikuwa ganin yadda nake saka English wear,sai ga Sharifah. Gata ba kadan
ba, ga teb'a. Yadda take tafiya da cikin riga da wando sai da ya sani boye kaina
nayi dariya sosai. Sannan na wuce ta niman abinda zanci.

Dake baya nan, yana shigowa ya ganta,
"Sharifa! Meye haka? Dube ki don Allah cire kayan nan, aiko Anum bata."
."ai mune kayan baya mana kyau amma ita dake matar So ce yana mata kyau ko?"
"Toh Allah ya baku hakuri."

Ina jin su, na kama dariya sosai sabida abin dariya yake, aikuwa nasake
taku, na shine sai na saka shi a daki ranar girkina ba zai fito ba sai sallah yana
Sallah zai koma, karku ce wani abu meke, a'a kawai shirme da bashi labarin abinda
ya faru, ko kuma na bashi labarin film, sosai nake shige mishi duk da nasan kafin
ya manta abinda nayi mishi zai jima, amma na kuma samun kusanci dashi, sosai.

Kamar yadda bana tsammanin, haka na shige mishi. Ga mahaifiyar shi da nake bata
kulawa, ana haka watan azumi ya kama, muka tafi Umra dashi da sauran matan, bamu
dawo ba sai da aka yi Azumi da sati biyu, muna dawowa muka cigaba da faffatawa
domin duk kusan addu'o'in akan shi da yarana suka kare, dan haka da zan dawo na
dawo da kwarin gwiwar akan shi.

Bana wasa da addu'a da Ibada, shi yasa yake makale min, na mikawa Allah
Al'amarin mu, kuma yana bani nasara akan duk abinda nake so.

Yana masifar kaunar mahaifiyar shi, sai na nuna mishi ni nafi shi sonta, domin
kuwa kome ina mata, hatta wankinta nakan shiga nayi mata, kitso da gyaran farce,
wani irin ɗaukar hankalin mutane nayi, duk da yana da yayu mata, amma shine namiji
babba, dan haka na nuna musu shi din mijina ne, Mahaifiyar shi kuwa uwa ce min.

Koda aka yi sallah, kayan da yayi mata sai da na kara mishi bai sani ba, dan Ni ya
dauka muka je sayayyar ta, kome sai na dauka mata, na kanen shi kuwa kamar bazai
musu ba, nice na saya musu da wannan kudin da yake ajiye min, na kai musu, amma
Nusaibah ta ki dauka karshe ta min rashin mutunci, Innar ma ta mata tass.

Sabida suna mutunci da Sharifah kuma ana maganar yayan Sharifa shi zai aureta,
shine take tsoron karta tsaya min dangin mijin su mata caa, idan anyi auren.
Aunty Rahama da Rufaidah, aka ya aika musu da nasu, Hajara da Ummul Salma, suma
haka.

Sai matan Baban shi da Baban shi din,. Da baya musu sai da nice na tuna
mishi, aikuwa suka fara girmama al'amarina.


Da basu tab'a tunanin zasu samu ba, sai gashi ya basu daga aurena.

Duk da nasu yake aure, tuni suka ce nayi musu asiri ne, na rufe idnun su,

Bayan sallah hutun shi ya ƙare, anan ma suka dauki kananun magana, anya nice
na haifi Hoor, tunda gashi nan har yanzu Ban kuma haihuwa ba. Ina jin su nayi banza
dasu..

Sai ranar da muka koma, ne shima ya damu, dan haka ya dauke ni zuwa asibitin
aka gwada ni, suka ce lafiya lau lokacin ne da saura.

----
Sai da muka shafe wata shida, duk karshen wata yana zuwa duba gida, sannan Allah ya
dube mu da idanun rahama ya bani ciki. Babu laulayi babu kome. Da farko ban yarda
ba, sai da nake asibitin barrack din aka tabbatar cikin ne dani, dashi yana cewa
zamu tafi Damagaran.

Kamar ba zani ba, haka na shirya muka nufi garin, tunda muka isa ba fara
zazzaɓi sama sama, tare da yawan kwanciya dukda ina yin kome, amma sai da suka
fahimci bani da lafiya, dan haka Sharifa take gayawa Nusaibah, suka zo duba ni.
"Amma ciki ne sake?"
"Me kika gani!"
Na tambaye ta, fuskana babu wasa. Ganin zasu rena min hankali, na Barsu gurin.

Ranar wata Alhamis na amshi girki, dan haka nayi abincin rana da na har da zobo,
bai ci da wuri ba, sai dai ma kanen shi maza suka ci ya dauki zoben na kai mishi
firj, da dare da yaci tuwon dare yasha zobon muna hira, naga yanayin shi yana sauya
wa na zata ko yar kullum ce, dan haka na biye mishi muka koma dakin.
Tun ina jure abinda yake min, har na fara girgiza shi, ina gaya mishi marana ya
ciwo..

Bai saurareni ba, har sai da yaji numfashina yana daukewa sabida yadda nake jin
kamar ana hura min wuta, yana zare jikin shi jini ba biyo shi. Jijjigani yayi
yaga bana ko motsi, a tsorace ya saka min jallabiyar shi, ya nufi asibiti da Ni.

Duk yadda aka so tare al'amarin cikin sai da ya tab'u, kiran Liman yayi ya
gaya mishi ai ga halin da nake ciki, akan lokaci yayi addu'a aka kawo min, toh ina
sume, ana kawo min, yace a tabbatar ruwan ya shiga bakina, haka kuwa aka yi suka
dura min har na had'iye, jikin su a sanyayye....
*Allah sarki Murna ya koma ciki, Ba rabo ba dan fari ya koma*
#Mai_Dambu
[2/21, 8:36 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA SITTIN DA BAKWAI

*Ya ilahi 🙈 AUNTY Sa'a da MAMAN ABUNA ga Pagen kun nan 💞🤩💝*

Dafe goshinsa yayi tare da shiru. Sun kai awa daya a waje kafin Nurse ta fito da
sauri.
"Wani hali take ciki?"
"Alhamdulillahi, cikin ya tsaya amma ita din ce har yanzu numfashin ta bai zauna
dai dai ba."

Haka suka zauna har bayan minti arba'in kafin ya suka fito da likitan, kallon
shi yayi sannan tace mishi.
"Muje office."
Babu musu ya bi bayan likitan, sun zauna likitan ya kalle shi sannan yace mishi.
"Naga kamar kana damuwa, cikin ya tsaya amma don Allah a d'aga mata kafa, daga
wannan yanayin domin dan cikin ya tasa"

"Ko tasha wani abu ne?" Ya tambaya a dame,
"A'a sai dai kai ne dai nake tunanin ko ka sha wani maganin kuzari ne, tunda kana
tare da ita jinin ya ɓalle."

Shiru yayi sannan ya dauke kanshi yana faɗin.
"Ta bani zobo nasha bayan nan kuma ba zan iya cewa kome ba, dan daga haka muka
fara."

"Toh gaskiya akwai matsala tunda, kawai kayi bincike." Mika mishi hannu yayi suka
yi musabaha, sannan ya fita inda ya sami yan uwan shi duk sun tawo.
"Ya Anum da jikin?"
"Alhamdulillahi cikin ya tsaya!"
"Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!"
Inji Liman, suna tsaye. Aka fito da ita tayi Fayau gwanin ban sha'awa, aka wuce
da ita. Juyawa yayi ya nufi gidan, abun da ya fara bincike zobon ya dauka sannan ya
wuce dakin Anum. Garin bincike ya hango parket din maganin kuzari.

Juyawa yayi yaga yadda tayi amfani da har kwaya biyu, cikin masifar tashin
hankali yayi wanka tare da shiryawa ya dawo asibitin,

Tabbas ya yarda Anum bata shirya zama dashi ba, abu daya zuwa biyu ya dawo da ita
rayuwar shi, Yarta da kuma abin hannun shi da tasan yana dashi. Shi yasa tayi
yunkurin zubda gudan jinin shi. Dan haka ya zauna har kusan asuba sannan ya dawo
gida.

Gabaki daya ya juye Aliyun shi, dan abinda bai kai ka fada ba, kowa sai yasha
faɗa, kanen shi kuwa sai da ya mari Nusaiba, sabida tasaka Hoor a gaba tana zaginta
tare da kiranta yar me ido kamar na mujiya,

Ya tsare ta sai ta gaya mishi meye na mujiya a idanunta. Dakyar ya kyaleta,
daga nan ya nufi asibitin, lokacin na fito wanka a hankali nake tafiya, kallo daya
yayi min, sannan ya juya kan Kanwar Maman shi da take tare dani.
"Sannu Innai! Kin kwana lafiya?"
Kallon shi nayi, zuciyata tana bugawa sabida yadda ya daure fuskar shi.
"Abban Isma'il!"
A fusace ya juyo tare da kafe ni da ido.
Sunkuyar da kai nayi, tare da zama a bakin gadon, ina haki.
"Sannun kinji!" Karamin murmushi nayi ina wasa da yatsun hannuna,

"Zan tafi! Innai ki saka ido sosai akan cikin domin akwai wasu da samuwar su
duniya ce a gaban su basu damu da mutanen da suke faffutikar rayuwa domin su amfani
ba."

Dake bata fahimci abinda yake nufi ba. Kallon shi nayi naga ya hade rai kamar
yadda ya shigo. Babu shakka akwai matsala.

Bai iya hakuri ba, sai da ya gayawa Liman abinda nayi mishi,
Tsam yayi yana kallon shi kafin yace mishi.
"Ni kuwa nake ganin ba zata tab'a wasa da cikin jikin ta ba, sabida tana kiyaye
zaman ku.

Sannan kasan zata fika kaunar cikin sama da yadda kake tsammani, akwai abinda
baka sani bane amma Allah zai magance kome!"
"Liman kalli maganin da na samu a dakinta wato dan ina sonta bari ta wulakanta ni
ko?"
"Kai dai kana ci da zuci!"
Karshe fushi yayi tare da ɗaukar jakar shi ya bar magana garin.

Duk yan uwansu da dangin nesa sun zo gidan, Amma babu wanda yasan da cikin
yana nan, kowa a tunanin shi ya zube.

Lokacin da Hajja Dijimah ta sako matan shi a gaba suka zo min. Yadda na ga kishi
a idon su na Fahimci sune suka tab'a min lafiyar cikina, dan haka dakyar na amsa
musu gaisuwar su. Daga nan na dauke kaina akan su.

Kwana na biyar aka sallame ni,. A gurin mahaifiyar shi na cigaba da zama, dan
Mahaifin shi yace na zauna a gurin mahaifin shi har cikin ya zauna a jikina. Haka
na zauna. Ina kula da lafiyar cikina da kuma kai na.

A hankali na Fahimci irin tsanar da aka min a cikin gidan baki daya, hatta matan
yan uwan shi, sun tsane ni irin tsana me mugun cin rai, sabida yadda Mahaifiyar shi
ta nuna min kauna ba ita kadai ba, hatta Liman da kan shi yake kawo min Addu'a, har
cikin ya shiga wata biyar.
Ranar da ya cika biyar sai ga Ahmad (ila) ya dauke ni muka tafi
inda yake aiki. Tunda muka isa naga ya wuce sani asibiti. Hankalina ya tashi, ina
zuwa na same shi babu yadda yaƙe, ga gefen kirjin shi ta dama an mishi daurin, kan
shi ya ma haka,
Zama nayi ina ambaton Allah, rike hannun shi nayi ya bude idanun shi.
"Me yasa kika zab'i zubda min cikina? Da abin nake kwana nake tashi Anum kin san
yadda nake kaunarki?"

"Kayi hakuri!"
Lumshe idanun shi yayi tare da cigaba da barci,

"Ila meye ya same shi?" Na tambaye shi,
"Wallahi tun da ya dawo daga Damagaran, yake fama da yawan damuwa, wallahi duk
lokacin da ya zauna haya iya kome, toh jiya ya fita, ne yayi hatsari. Shine yace
koda ya mutu don Allah na tambaya mishi ke me yasa kika yi kokarin zubda mishi
cikin jikinki? Anum wallahi ban tab'a ganin wanda so bai wa Adalci irin Yallabai
ba.

Yana miki kaunar da bayawa matan shi, amma kin kasa ganewa yana girmama
al'amarin ki amma baki ganewa. meye laifin shi da zaki zubda cikin?"

Ban ce mishi kome ba, kawai hawaye ke zuba min daga idanuna, tare da kallon Abban
Isma'il. Gabaki daya sun kasa yarda dani akan ba zan zubda cikin ba, gani suke da
gayya na zubda.

Haka ya tafi ya barni a gurin shi dake babban soja ne, tunda nazo nake
dawainiyya da shi, tun bai farka ba, har ya dawo nutsuwar shi, suka sallame mu..na
cigaba da jiyar shi a gidan. A can kuwa

Please Login or Register in order to submit comment