You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai da yazo da wani lauya akan a gabana kina fada mishi kinyi
cikin, abinda na sani Allah yana tare da masu hakuri."

Rikici ta saka musu, ita ba zata auri Mudi ba, idan yazo ta yi mishi
rashin mutunci da rashin kunya, haka bai hana shi kuma dawowa ba, karshe Haka
mutumin nan ya ci mutuncin Malam.

Babu shiri aka ranar juma'a aka daura auren Alhaji Mudi da Anum, haka Umma tayi ta
gyarata, tare da kulawa domin ansaka tarewan sabon wata.

Duk wanda ya kalli Anum sai ya tausaya mata, domin ta fita hayacinta,
burinta ta kashe auren, tun da Maman Aminu ta fahimci haka, wani tudu wani ganganre
aka wani Anum tana son aurenta, kamar tayi hauka. A wannan tsakanin mijin yayi ta
koda musu kudi, yana fita da ita.

Duk tafiyar da zai yi da ita yake tafiya, kafin ta tare ta zama side chick
din Alhaji. Kuma kome dare tace mishi ga abinda take so zai kawo mata. Hmmm.

---
"Hajiya Hafsat Kanwar ki nan wata rana ba zata cigaba da biye muku ba, kin rufe
mata baki bayan kin san cewa tafiki gaskiya. Sannan maganar gaskiya idan kika
cigaba da haka wata rana zata bijire muku, wanda ku kanku ba zaku tab'a jin dadinta
ba, ku daina tankwarata dole tayi abu."

Jikinta ne yaso yin sanyi, amma ta kudira a ranta sai ta hanata sakat yadda
babu wanda zai fahimci meye a kasa, domin ba zata iya maida mata gwal ɗinta ba.

---
Yadda yake kawowa malam Uzuri, yasa shi tsayawa sosai suka fahimci juna.
"Alhaji idan ba zaka zauna da ita ba, toh kawai asan abin yi, na gaji da ganinta da
aurenka tana yawo." Inji Mlm,
"Toh babu damuwa wata sati sai ta tare ba, ai ba wani abu bane."
Ya fadi haka, amma a kasan ran shi bai so haka ba, dan haka ya koma gida ya shiga
gyaran shashin da Anum zata zauna. Umma ta cigaba da gyarata, duk da sai tayi
zuciya amma ta Cigaba. Dan gani take kamar itace tafi dacewa da amsa sunan
mahaifiyar Anum, amma sakamakon Maman Aminu ce ta haifeta bai hanata kaunar ta
kamar yadda take kaunar Yaranta, sama da Yaranta ma.

Ita kanta tasan tana son yarinyar da rayuwarta ya inganta, amma bata
jin uwar ta nan zata barta ta zama abin zata yi kyau gobenta.
---
"MAUDE!"
Ta kira sunan shi a hankali, tana kallon yadda yake aikin shi.
"Kayi hakuri!"
Bai tanka mata ba, asalima abinda yake gaban shi yake, irin wannan kuma matsalar
kice,
"Don Allah!"
"Khadijah! Ke matar aure ce, kuma matar wani, me zai hana ki daina min magana,
saboda kar mu saba'awa Ubangiji."

"Amma san kai mutumin kirki ne, baka tab'a min maganar Asha ba. Maude bana barci,
idan dare yayi sai nayi ta juyi, Bana jin dadin rayuwata, Mutumin nan ina matuƙar
tsanar shi, amma kasan me? Haka kawai sai naji ina son zama dashi, amma a raina
bana son shi."

"Anum kina wasa da ibada, shi yasa kowani kare da doki yake iya cutar dake,
shawarar da zan baki ki hana idanun ki barci kina kiyamul laili, yana taimakawa
gurin maidawa masu sharri sharrin su. Kina yawan karatun Alkur'ani, magani ne na
kowani irin lallura.

Anum rayuwar duniya idan babu addini ba zai yiwu ba, ki rike Allah. Duk inda
kika shiga Allah yana tare dake,kasan me? Idan wancan tsohon banzan yayi miki
Iskanci. Ki Kur'ani wallahi sai na gyara mishi gurin zama!"

Murmushi tayi tare da dauke kanta, tana dariya.
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Koma kafin ace ina magana da matar aure!"
A hankali ta juya, duk sai take jin babu dadi, ta cutar dashi dayawa, kuma yana
ƙoƙarin sataka farin ciki. Juyowa tayi tana kallon har ya rufe window, a hankali ta
juya tare da shigewa cikin gidan.

Maganarta ne yake yawo a kunnen shi.
"Ila! Yarinyar nan tana cikin damuwa da?"
"Ai ba Kanwar gyatumata bace da zan hana kaina sakat akanta, ba damuwa ba, tashin
duniya take ciki."

Rike baki yayi yana kallon Ila da ya matse fuskar shi, alamar yana cike da
maude, kuma kiris yake jira Mauden ya tinzira shi ya kwashewa Anum albarka
daidaigwargwado.

"Ila maganar gaskiya nake gaya maka fa?"
"Lallai kuwa, maude kana nufin duk Iskancin da akan ta, wai Ni kam yarinyar nan
tafi sauran mata ne? Meye take dashi da ka damu da ita? Gaskiya karka dame ni akan
ta, Allah yasa ta mutu kowa ya huta."
."amma da ka saurare ni, kaji abinda zance maka, kawai ka hau fada kamar wanda na
gaya maka wani abu na daban."

"Eh kai, ai abu na daban ka gaya min, me aka yi da halin Yarinyar da bata da
kamun kai,kafi kowa sanin halin gidan ku, wallahi faduwar daraja ce ka nime wannan
Yarinyar da bata mai da kanta Mutum me kima ba, a duk lokacin da ka girmama kanka
Allah sai ya kawo maka masu girmama ka, Yallabai gidan ku manyan malamai ne, manyan
mutanen ne da suka san ma'anar daraja, taya zaka dauko musu kara da kiyashi daukar
mara sani?

Yallabai ka rabu da yarinyar nan. Karka manta Nana Aicha mahaifinta shine
sarki a maradi, kuma mahaifiyarta Kanwar mahaifiyarka ce, me yasa ba zaka gane
mugun irin da zaka kai muku cikin zuri'a ku!"

Shiru yayi sannan, ya dauki ruwa ya sha, tare fita yayi daga shagon ya
nufi gidan shi. Ya sami gidan cike da matar gidan da suke haya, ana gulmar da aka
saba.. suna jin sallamar shi suka shiga, mik'ewa kowacce bata gama gulmarta ba,
zata fita amma babu karya sun ji haushin dawowar shi.

Yana shiga ya sami, Hajjo tana kallon wani Hausa Film, tashi tayi tare cewa.
"Barka da dawowa, kayi hakuri sun zo kallo ne!"

"Karki damu," ya gaya mata tare da niman guri ya zauna, a dame yake, amma
baya jin damuwar shi ta kai wanda Anum take ciki, tabbas yana jajjantawa halin da
Anum take ciki, ji yaƙe kamar ya cireta a cikin matsalar ya wurga kanshi, yasan
Allah zai fidda shi da Insha Allah, ita kuma fa?

Yadda ya lura da Maman Aminu, bata da cikakken hankali, yasan bai zama dole
tasaka ta a cikin addu'o'in ta ba, yasan dai in akwai addu'ar da zata mata, bai
wuce na niman kudi ba. Kai matar nan bai tab'a ganin mutum me shegen masifar son
abun duniya irin Maman aminu ba.

Tsakanin da Allah idanunta yafi raja'a akan kuɗi, idanunta idanun nera, har
tausayin ta yake ji, irin su ne ake saka musu abu a cikin kudi.

Murmushi yayi, tare da shafa kanshi. Yadda take son kudin nan, ka
tula mata miliyan goma nata na kanta, zunzurutun tashin hankalin da zata shiga sai
takwana bata rintsa ba, dariya ya sake yana girgiza kan shi.

---
Yana jin a ran shi, tabbas dole ya taimakawa Anum domin.. wani tunani ne yazo mishi
yace.
"Toh ita da zata yi aurenta, ina ruwana?"

Haka yayi ta magana shi daya yana kuma ganin rashin dacewar, saka mata baki akan
rayuwar da zata yi gidan mijinta...

--- Rana bata karya.
Ranar juma'a da dare aka kai a gidan mijinta, wanda yake wuntin dada, a can baraya
Quarts. Babu laifi inda aka sakata, plat ne me kyau.

Inda Safiya suka mata jere kome nata, A daren kuwa Alhaji Mudi ya gurji
amarcin shi son ranshi, babu wani katabus, sai tsabar jaraba. Bayan minti goma zai
sauka. Kuma ba zai fasa matseta ba, har asuba idan yayi barci ya tashi zai tab'ata.

Karfe biyar tayi wanka, maranta na mata mugun ciwo, har bayan ta. So gari na
wayewa. Aka shiga kawo mata abin karyawa,.kafin karfe goma gidan ya cika da baki
yan uwan ta, da matan yayunta.

Tayi kyau cikin buba na lace, an mata dauri me kyau. yaran Alhaji
Mudi suka shigo. Sun kai rai goma, kana ganin su kamar yaran dan wake, kuma kowani
yaro kamar shi daban, gashi kamar wanda aka kwato su daga fari. Gasu da katon ciki
da katon kai.

Sai zare idanu suke, lokacin da aka kawo abinci daga bakin kura. Kamar
zata yi kuka tace musu.
"Daga ina kuke? Kun shigo kuna kare mana kallo"

Kallon abincin da suke ci har da namar kaza, Hafsat na ajiye filet din suna
saka super! A guje Anum ta koma saman kujera a tsorace.
"Na shiga uku!"
Shigowar daya daga cikin matan Alhaji yasa su d'ago kansu.
"Kuyi hakuri! Kai kuzo muje, sha'anin yaro bai saba ganin haka ba, shi yasa suke
muku halin su. Gaki da kyau me yasa kika zab'i kare rayuwarki a cikin gidan nan?
Amma ba zaki gane ba, sai nan gaba."

"Malama dakata mana, ki fita ki bamu guri." Inji Hafsat,
Murmushi matar tayi sannan ta kalli Anum, kafin ta kori yaran waje.

Kallon juna suka yi, sannan wasu suka fara cewa, kishi ne da rashin
godiyar Ubangiji, amma kamar Alhaji ai ba zai wulakanta su ba.
Dan haka suka shiga zuga Anum ana gaya mata kar ta sake su rena ta, dan yanzun miji
yana hannunta....
🤔🤫 Kuma dai!
#Mai_Dambu
[2/10, 9:50 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
😘
*Dubun gaisuwa gareki Mrs J Moon! Ga shafin ki nan*

```Ga masu bukatar littattafan Marubuciyar da aka kammala zasu iya tuntubar
Marubuciyar +2348132166848 an kammala Dr Laylah```

BABI NA TALATIN DA TARA.

Kallon su Anum tayi tare da sunkuyar da kanta, tana jin wani abu ya tokare mata,
kirjinta bata kuma d'ago kanta ba, sai da tayi kusan minti talatin a haka, sannan
ta d'ago kanta, tana kallon matan makotan su, suna shigowa.

Haka suka gama gulmar su, suka fita,Yayunta mata suka shiga mata ingiza me
kantu ruwa, har yamma suka watse dan daga unguwar zuwa bakin titin akwai tafia,
bayan tafiyar su. Ta shiga kimtsa cikin gidan, tana gamawa ta nufi cikin dakinta,
domin sun rage mata aiki sun tafi da kayan da suka zo dashi, sauran abincin sun bar
mata a cikin kitchen ɗin ta.

Wanka ta kuma tare da sheka kwalliya, sannan ta fito falo, sai lokacin ta sauke
sallah da yake kanta, tana kan Abin sallah ta tsinkayo Muryan mace tana ihu, lekawa
tayi ta window. Da sauri ta mai da labulen ta rufe kirjinta na dukar tara tara,
zunzurutun tsoron yaran Alhaji Mudi.

Sake d'aga labulen tayi taga sun zuba mata ido, kamar wasu zombia,
zunzurutun yunwa da suke ji, dage kanta tayi taga Alhaji da kanshi yake zane matar
nan da ta musu magana, murmushi tayi sannan ta isa bakin kofar ta, ta bude kofar
juyowa yayi tare da sake mata murmushi. Itama murmushin tayi Mishi, taja kofar ta
ta rufe. Dan lokacin karfe shida da minti hamsin ne, ana kiran sallah a ko ina.

"Baby, ya isa haka kazo muje kayi alola ka tafi masalaci, zan baka labari."
Sake belt din injin din yayi, tare da juyawa suna murmushi. Sanan suka bar gurin,
tunda daga ranar Alhaji yake riga Anum, abin karyawan su special. Haka abincin
ranar su ma, na dare kuwa fita suke su tafi saya a waje, idan tafiya ta kama shi
zai dauke ta su tafi tare, idan zasu dawo haka zata yi sayayyan kayan abinci domin
yana masifar jin dadi mu'amala da ita.
Wato bari kuji yadda gidan Mudi yake, babban gidane me dauke da mata uku
da kananun yara kusan rai goma sha biyu, banda cikin da sauran mata biyu suke
dashi, aka'idar gidan.

Abinci sau daya ake girkawa, idan aka saka ƙatuwar lamva talatin na tuwo,(🙄🤨🤣)
ƙatuwar lamba sha biyar na miya, asalin tuwon za ayi talgen shi(mu nan muna kiran
shi da Ruɗe) ne da tsakin garin tuwon, sai a dauren wancan talgen da garin tuwo,
miyar kuwa TOH yaddiko tana iya nata ƙoƙarin.

Dukda bata da d'a a cikin gidan, amma wallahi duk wani wahala itace take
Mishi, ya aureta a bazawara ce, lokacin mijinta ya rasu, tana da manyan yara a wani
gurin, da taimakon su take iya daukar dawainiyar gidan Alhaji, domin tana sana'o'in
hausawa, kukar miya, garin kubaiwa, kayan miya Daddawa da kanta take yi domin yawan
gidan su tasa take hada daddwan waken soya, dashi ake miyar gidan.

Dan haka idan za'ayi miyar,akan zuba yaji daddawa, da kuma ajina
moto, yadda miyar zata yi zaƙin Bala'i.

Idan aka gama tuwon, akwai wani kular da Yadiko ta sayo, a gurin tani
dilalliya, shi ake kwashe abincin dukkan a juya shi, sai miyar wanda zunzurutun
rashin manja.

Zaka dauka barin garin kuka aka yi a cikin miyar haka suke ci,har suna kashe
hannu.

Matan shi da yake aurowa daga ƙauyukan bauchi, a yanzun wanda suke gidan Akwai.

Barirah, daga kayarda sai Mairo, daga Nasaru, sai Karime daga can maina maji, anan
ya auro su. Dake yan kauye ne kuma yara ne suna bin Yadiko sosai, kafin shigowar
Anum akwai wata yar bununu me suna Sakina, dake ita tana da ciki shine aka sake ta,
tare da hankadata can garin su da yake geendi.

Duk yaran da suke cikin gidan Mudi babu wanda suke su biyu, sai Hassan da
Hussaini, sune UWARSU daya. Domin amma kaf yaran uwaren su daban, kuma suna shirin
dosar talatin, domin itama Barirah ana kyautata zaton cikin ne da ita.

Yadiko dai itace turmin tsakar gida, sha daka, wani banzan halin Alhaji shi ba
zai ci abincin gidan shi ba, sai dai ya sayo daga waje, nama, tukunya, balangu ko
tsire, doya da kai ko kuma taje Banilla yasayo abinda zai ci, yana da kayan abinci
a cikin dakin shi.

Idan kaga an girka shinkafa a gidan,(😂😹😂 Marori)
Toh sallah ce, ko sadaka. Dake mutum ne me mugun bin malamai, haka zaka ga yaran
shi suna buga sowa, (wallahi abin da mugun ban tausayi, maza kuji tsoron Allah,
wallahi Allah ba zai barku ba, nasan maza dayawa da suke karanta book dina, kuma
nasan zaku gani)

Sannan yadda ya rena Yadiko zaka sha mamaki, dukarta yake a gaban uban kowa,
dayawa matan da ya aura bawai sun aure shi dan kasu bane, a'a yana sake kudi idan
yarinya zata mishi gardama ya saka malamin shi ya rufewa iyayenta baki yadda zai
aureta ya kuma kawo ta yaci Uban ta.
Sannan akidar shi idan mace tayi ciki, zai fara cin Ubanta, ko ta fita da
kafarta ko kuma ya wulankata ta, da kanshi, baya son haihuwa yace hayaniyaar yaran
ta ishe shi, na farko dai basu zuwa boko balle islamiyya, na biyu basu da tarbiyya,
balle su sami nutsuwa. Na uku basu koshi ba, balle su zama masu cikakken lafiya da
kuzari babu wannan abun a tare dasu..idan gansu zaka rantse irin yaran nan ne da
aka yi yaki da baƙin talauci ya cinye su. Ga rashin sutura wanda ya taka rawan gani
domin wallahi yaran almajirai sunfi su gata, tunda suna fita bara, su kuma wannan
basu fita ko ina, ga sata idan ka ajiye abunka kafin ya dawo sun dauke kuma a rasa
waye ya dauka a cikin su.

Idan suka fara fada da junar su, wallahi sai Yadiko ta dauki Muciyar suke
rabuwa dan yi suke kamar zasu kashe junan su, idan kuma aka zuba musu abinci, sai
kayi kuka da idanunka, domin baya wadatar su, karshe wanda yafi wani ƙarfi shine
zai dauko tiren abincin, wannan yanayin sam Yadiko bata fatan wata ta auri Alhaji,
domin mara mutunci kamar wanda yake da ciki a hannu yana d'aga bujen mace, toh
magana ya kare, shi yasa da taga Anum taji ciwon auran Alhaji da tayi har ta mata
magana, karshe bayan an watse suka fara sa'in'sa da Alhaji take gaya mishi magana.
"Kaje ka auro yarinya karama, me dauke da danyen kuruciya bayan wanda ka tara a
gida, idan ta sami ciki ka sake ta ka sauko wata, wallahi Baka kyauta min, meye na
rage dashi, ina laifin ka barta tayi rayuwarta amma ka aurota, sannan ka ajiye ta
nan da wani lokaci, ka sake ta bayan ka gama gina mata wulakancin, sannan ka na
sane kake barinta take abinda ta dagama, wallahi Allah sai yabi mana hakkin mu,"
shine ya kamata da duka fa,

Abubuwan fada akan Mudi dayawa suke, idan zaka fada sai ranka ya b'aci a
banza.

Ko lokacin da ya gayawa Malamin shi batun Anum, sai da yace mishi akwai aure a
tsakanin su, amma kuma ba me nisan kwana ba, shi yasa lokacin da akayi auren yaso
su rabu, dan malamin ya gaya mishi matsalar da zai iya samu da kasuwancin sa, sanan
yake gaya mishi abubuwa biyu ya bashi damar auren Anum, uwarta da yar uwarta basu
barta ba, dan tana da kashin Arziki, shi yasa suke gudun ta auri mutumin da bai da
wani arziki, sai kuma cikin jikinta da shi kadai zai yake ta ta aure shi.

Amma kar ya kuskureta, domin yin haka dai dai yake da lalacewar wasu abubuwan
shi, sannan ya kara mishi da cewa, tana da kwaɗayi da hangen dala,

Ya gaya mishi abubuwa dayawa akanta, sannan kafin auren ya kuma ce yayi bincike
akan me ya rabata da mijinta, koda ya gaya mishi abin da ya faru, da wannan abun da
abinda Maman Aminu suka mata, suka daure tunaninta guri guda.

Shine lokacin da take gayawa Maude cewa, ai bata jin dadin rayuwarta, bata iya
barci. A duk lokacin da ake nufarka da sharri matukar baka tsaya da ibada ba, toh
haka zaka ji, ka kwana kana jin damuwa da faduwar gaba, ciwon kai da na jiki, barci
ya kaurace maka, sannan zaka naji kamar ana kiranka, ki wani abu na daban, toh idan
kana yawan sallar dare, abun yakan komawa masu aiken.

----
Abincin da ya rage shi aka ta hada musu, sannan ta jera musu. Bayan ya dawo
masalaci, dan ba wai sallar yake ba, ya fita ya zauna a gurin motar shi ne, sai da
aka fito masalaci ya koma cikin gidan, inda ya samu ta Baje musu abinci suka ci
😳 yana hawa ko minti biyar mekyau bai rufa
tare da hira, daga gurin aka fara, ()
ba, mutumin ku ya sauka.

Haka yayi ta janta da wannan shirmen, dakyar ta dakatar dashi tai
wanka, marar ta yana ciwo.

... Haka suke ta amarcin su, yayinda ta budewa mutanen gidan rashin
mutunci, shima kuma Alhajin bai fasa ba, haka sukewa mutanen gidan tijara. Idan ka
ga yadda take tsiyar ba zaka tab'a dauka zai zo karshe ba.

*** Maman Aminu, baki har kunne yarta ta auri me kudi, sai hura hanci take,
babu abinda ya dame ta, gashi tana dai samu a jikin sauran yaran amma dake Allah ya
cire albarkan a cikin rayuwar sai taga abin baya jimawa.

Haka malam yake haɗa duk wani abun da samu zai bawa Umma ta ajiye a Anum, hidima
sosai suke mata ana ajiye mata, ko bata zo ba za a kai mata. A cikin irin wannan
lokacin kayan miya yayi araha, Umma tasa Malam ya saya musu kwando da aka markade,
ta daure wasu a laida, ta saka a cikin freeza. Sauran kuma ta juye a langa tsirara.

Sannan ta ajiywa Anum, duk wani tattalin duniyar nan daga malam har Umma wa
Anum ce, dan babu karya yaji labarin waye Alhaji Mudi, amma dan Anum ta janyo
mishi rikicin da ba zai iya tarewa ba, ya amince ya bada aurenta.

"Malam yau sati biyu da auren Anum baka tab'a mana mijinta ba, dan ita Bama
samunta" inji Maman Aminu,
"Tana lafiya, tafiya suka yi!"
Daga haka bai kuma cewa kome ba, sabida Allah ya gani ta ficce mishi a kai, kawai
sabida Albarkacin Yaranta yake zaune da ita, bacin haka da ya hakura da ita baki
daya .

---
"Beauty! Kinga tunda Alhaji ya auri Anum ya daina hulda da mu? Sai ma sakamu da
yayi a blacklist." Inji XOXO,
Shiru Beauty tayi tana wasa za wayarta, kafin tace mata.
"Toh ni dai ban san me zance ba, amma kuma ki hakura da dashi mana"
"Wallahi ba zan iya ba, shine yake kashe min kudin da sauran basu bani, shi yasa na
hanaki mu'amala dashi wata banziya daga mu'amala sau saya ta kwace min shi, Allah
sai na dawo da da shi."

Ta faɗa tare da ihu, tana kuka. Kallon ta Beauty take, sabida bata san me
zata iya cewa ba.
Kuma tasan halin Xoxo ba mutunci ne da ita ba, yanzun tace da ita aka kulla mata
wulakancin duniya, shi yasa take Binta duk yadda ya dace.
"Toh kiyi hakuri, ai babu wani abu da zaki d'aga hankalinki, Alhaji na mune! Kuma
Insha Allah zai dawo gare mu, muyi yadda muke so dashi, kinji My Bestie!"

Da wannan maganar ta gyada kai kawai, domin tasan Beauty zata...
*Kuyi hakuri, idan na sami lokaci zan kara muku*
#Mai_Dambu...
[2/10, 9:50 PM] MRS USMAN😘: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.
BABI NA ARBA'IN.


Bayan Amarci....

Kwanaki suna tafiya, amarci nan dai gurjanta ake, sanabe da iyayin Anum kara yawa
yake, kokarin ta na ganin ta sami damar juyar da kan Alhaji ya faskara, a hankali
suka shiga jikin juna. Inda Anum ta fara fuskartan Allah Alh baya son ibada, sannan
mugu ne na fitar hankali.

Idan zai samu nutsuwa a jikinta, baya damuwa da ita. Abinda ya fara damunta,
ba kome bane, ana cikin haka gas din ta ya kare. Dan haka ta nufi dakin shi ta same
shi yana barci.

"Baby bamu da gas din da zamu yi abin karyawa"

Budar bakin shi yace mata,
"Amma naga a gidan uban ki uwarki itace take amfani dashi bana son jakanci, ki fita
ki hura wutar itacce."
Kallon shi tayi tare da sake baki hawaye na zuba mata.
"Ni dai ba Ubana da Uwata ba."
Ta faɗa cikin kuka, aikuwa tsalle yayi ya dirko daga gadon, ya rufeta da duka. Tare
da kwallo da ita, dukar kawo wuka yayi mata, tare da mata wulakancin, aikuwa yaran
gidan kowa ya shiga cikin nutsuwar shi. Yana gama dukarta ya fito.
"Idan kuka ganta zata fita kuyi mata haushi kamar kare, karku barta tafita ko kofar
gida."

Bayan tafiyar shi, kuwa ta sab'i hijab zata buga yaji, tana isowa tsakar
gidan, yaran suka fara mata gurnani kamar wasu karnuka, tare da mata caa zasu mata
diban albarka, da gudu ta koma d'akinta. Ta rufe kofar ta.

Kuka take tare da niman wayarta, ta manta inda yake ma, tayi niman duniyar nan
bata gani ba.
Haka ta wuni ranar bata saka kome a cikin bakinta ba, sai dare da aka gama
kirb'a tuwon datsa, aka kawo mata. Shi taci dakyar ya wuce wuyarta. Ranar tayi kuka
har ta godewa Allah.

Tun daga ranar kuma,

Please Login or Register in order to submit comment