You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga da gudu . Tana ture shi,
fadawa kirjin shi tayi tana kuka tare da dukar shi. Tana tambayar shi.
"Meye nayi maka? Me yasa zaka min haka! Na baka hakuri jiya na gaya maka zan zauna
da kai me yasa ba zaka gane haka ba, me yasa ba zaka gane abinda nake fada ba.
Maude kayi yadda kake so dani ba zan hana ka ba, amma karka kace ka sake ni, don
Allah ka rufa min asiri."

Jingina yayi da bango, yana kuma jin wani tashin hankali a ran shi. "Maude
kace ka fasa!" Ta faɗa cikin kuka.
"Kiyi hakuri! Kije gurin Mahaifiyar ki!"

Yana gama fadar haka ya cireta a jikin shi tare da fidda ita waje, ihu take
tana kiran shi. Ai kuwa ran Maman Aminu ya b'aci ta rufeta da duka, tana janta har
waje.
"Wayyo Maude kazo kace ka fasa, Maude kazo ka ɗauke ni, don Allah kace ka fasa sake
ni, don Allah Maude."

Haka Maman Aminu taja ta har gida, suna shiga ta wuce dakin Umma da gudu ta
faɗa jikinta, tana kuka da ihu.
"UMMA na maude ya sake ni"
"Toh Anum amma naga abinda kuke bukata ya baku meye na kuka a ciki? Ba sakin kuke
nima ba tsawon wata biyar? Alhamdulillahi ya huta kema kin huta, amma ki sani idan
kece kika zalince shi Allah ba zai barki ba, idan kuma shi ya zalince ki Allah ba
zai bar shi ba."
Daga haka ta nuna mata hanyar waje, tunda ta fita ta zauna a bakin kofar a hankali
ta shiga dakin Malam, ta same shi kwance yayi rigingine, zama tayi tare da rike
hannun shi.. yadda ta kifa kanta a jikin gadon shi tana kuka, yayi duk sai yaji
babu dad'i.
"Karki damu! Ba shi ya zabi rabuwa dake ba, tilasta mishi aka yi, dan haka kiyi
hakuri. Ai nasan Uwata zata iya daukar haka a matsayin ƙaddarar ta ko?"

"Malam! Amma kuma yana da kirki, kuma ya zauna da ni bai taba min dole ba, malam."
"Ya Isa Anumullah."
.dan baya son jin yabo ko gwarzanta maude daga bakinta, duk wanda ya tozarta maude
bayanta ne, duk wanda ya wulakanta maude bayanta ne,
Itace ta bawa Mahaifiyar su damar ayi hakan. Suna cikin wannan yanayin Aunty Binta
bata iso, suka gama duba malam sanan dan ita da abokiyar aikinta ce.

Kallon Anum tayi, bayan ta dawo daga raka kasarta,
"Anum, me ya faru?"
"Mmmm! Wancan dan ciranin ya sake ta mana, dama ai ba zai iya ba malam ya saka
bashi ita toh ga sakamakon nan!"

Kuka Anum take tare da cewa.
"Saka shi aka yi ya sake ni, shi ba zai sake ni akan kan shi ba, Allah sai ya saka
min, an raba Ni da mutumin kirki."

Haushi ya kama Maman Aminu, ta dauko mucen tuwo. Ta shiga kwala mata. Tare da
gaya mata wasu kalaman da dole idan mutum ya nutsu zai fahimci inda Maman Aminu ta
dosa, daga cikin su kuwa har da cewa an asirce mata yarta da tsafin buza ne, magana
wasu marasa dad'i,

Daga Umma har Binta babu wanda ya ce mata ta tafasa balle ta kone, har Binta ta bar
gidan, bayan umma ta gargade ta, akan karta ji ta gayawa yan uwanta mutuwar Auren
Anum.

Wannan karon Umma zuba musu ido tayi, domin da dare Anum tafiya take gurin
Maude, ta saka shi a gaba tana kuka, inda take baya duba har ya tashi ta shigo
gida, nan ma da Maman Aminu ta Fahimci ta kashe maciji ne bata sare kai ba, sai ta
kuma saka Anum a gaba suka bar Bauchi..

*Wannan shi ne mafarin fadawa ta hanyar da ban bulle ba*
Na kalle su, naga suna kuka. Kallon agogon dakin nayi sannan na cigaba da basu
labarin kamar haka.
.... Tunda muka isa, ba a ce min kome ba, sai dai daga kulawar da ake bani ya sani
fara jin kamar ana danne min kewar maude, a hankali naso Mantawa da wasu maude,
watan mu uku. Na manta da rayuwar shi, sannan muka dawo da Mama.

Lokacin da napep din mu ya tsaya a kofar gidan mu, sauka nayi tare da fidda
jakar mu, kudin napep din zan mika, naga an bawa me napep ɗin kudi juyawa nayi muka
kalli juna. Dauke kai nayi sabida kamar ana watsa min ruwan zafi, yana mikawa ya
wuce abin shi.

Dauke kai Anum tayi tare da kallon Mamanta zata yi magana ta nuna mata
kofar gidan, da gudu ta juya tana dariya umma ce tsaye tana murmushi, rungume juna
suka yi dan tayi kewar yar nata.

"Autana sannu da dawowa! Yawwa Umma na, na same ku lafiya"
"Alhamdulillahi, mu shiga cikin gidan." Haka Almajirai suka shigo mana da kayan mu,
tare da Mama. Tunda na shiga cikin gidan,nake raba idanu ga Baba Hama tazo gidan,
dakin da nake da shi aka bata.

"Toh yar gwal har an dawo daga ga lakwajan ne?"
"Eh Baba mun same ku lafiya?"
"Hmm! Lau,"
"Umma na ina Malam dina nayi kewar shi."
"Yana nan d'azun yazo dubawa ko kin dawo,"
Wai irin murmushi take tare da gyada mata kai, haka suka shiga dakin Maman Aminu
suka gyara ita da Maman ta, bayan tasha katon kashedi, tare da rike mata kunne.

Da karta ji karta gani wani dogon sabo ya shiga tsakanin su da Umma.. gyada mata
kai tayi, ita Maman Aminu tana tsoron kar Umma ta dan karya mata abinda tayiwa Anum
na Mantawa da Maude, shi yasa take gargad'in ta. Sai dai kuma tsakanin su babu
wanda ya isa ya shiga.

--- bayan dawowarnsu yan uwan ta, da malam sun ji dadin ganinta, gefe
guda Xoxo da Beauty har gida suka zo mata jajjen mutuwar aurenta, kallon su take
tana son tunowa ita ta taɓa aure ne, karshe dai haka ta amsa musu.

Tun daga lokacin suka kuma dinkewa kamar da can baya, sake kulla alaƙar su ya
sanya Anum ta kuma sanin wasu abubuwan akan rashin kunya, fitsara wanda yaci Uban
nada, kiriniya kan ba a cewa kome.

Ga shegen yawon tafiya bikin ko yar uban waye, tsakanin ta da Maude harara da
hantara, ta tsane shi sama da kome a duniya, bata kaunar ta kalle shi. Asalima idan
aka ce mata ta zabi mutuwar shi zata zab'a.

Haka ta zama wata karamar Side chicks, wannan na sauke ta wannan zai
dauke ta, Anum ko kasuwa ta shiga sai ta fito da zawarawa.. wannan gaga din da take
yasa ta kuma fallewa..su kansu zawarawan kashe mata kudi suke na bala'i, Anum ta
zama wata big beby, ga Maman Aminu har maganin gyaran jiki take saya mata, Umma da
Malam nasu ido. Uwar kwaɗayi Baba Hama, ana bata tana gulma dan ma Umma bata daukar
iskanci, tsefeta take tare da nuna mata illar haka.

Dan ita Umma da zuciya daya take tare da Maman Aminu.

Zaune take tana waya, Rulwanu ya shigo, kallonta yayi sabida ta canza daga
yadda ya santa abaya, tana shafa man bleaching. Ta kuma fari sama da nada, yadda
take wayar zaka rantse da Allah, bakinta ciwo yake saboda baka jin me take cewa.
Bayan ta gama yace mata.
"Akwai wani yana miki magana a waje."

Hijab ta saka tare da cewa.
"Toh kace mishi ganin nan zuwa."
Tsaki yayi sannan ya zauna abin shi, dariya tayi sannan ta fita,

Sauke glass din motar shi yayi yana murmushi.
Dafe goshinta tayi sannan ta shiga kusa da shi.
"Sorry alhaji, na rashin maka kwantancen gidan mu!"

"Toh Anumullah! Baki gaya min sunanki ba, sabida kina ganin na tsofa ko? Toh ga
Alhaji Mudi wuntin dada nan yazo baran soyayyar ki ya sani zuwa gare ki ta hanyar
Aminiyarki XOXO."

Dauke kai tayi tana kallon waje, ita duk rashin hankalin ta, bata iya sake jiki
na miji ya more ta ba.
Hannun shi taji a saman gwiwarta, ba wani sabon abu bane a gurinta, duk da tasan
shi abu zasu nima ba, iya su sanyi shafe shafe da dai soyayyar shan mintin nan da
ake tana sakewa ayi da ita, amma bayan shi bata jin zata iya sakewa wani namijin ya
lalata mata rayuwa.

"Alhaji Ni ban ki maka ba, kawai irin soyayyar da kuke dasu Xoxo baya tsarina."
Daga haka ta juya zata fita yace mata.
"Toh meye Matsalar ki?"
"Ba ma zai yiwu bane kana tare dani kuma kana tare da kawaye na, sannan kuma ka
zago gurina taya haka zai yiwu?"
Ta kafe shi da idanu, murmushi irinta yan duniya yayi mata sannan yace mata.
"Karki damu sai na rabu dasu.".
Girgiza kai tayi sannan ta fita daga cikin motar.

Bata ko mishi magana ba, tana zuwa dab shagon Maude suka zubawa juna ido na
wasu dakikai, kafin ta dauke kanta daga gare shi ta nufi cikin gidan, gabanta yana
faduwa.

---
Kallon shi Xoxo tayi ai tasan za ayi haka, ita da take burin ya aureta shine zai zo
mata da maganar banza. Mik'ewa tayi sannan tace mishi.
"Ka cigaba da nace mata, sai dai fa bazawara ce, kuma kaga zata fi sanin wasu
abubuwan wanda da ace budurwa ce zata baka wahala. Dan haka kayi ƙoƙarin nace mata.
Tana son kyauta da kuma son rayuwar hutu, idan ka shiga mata haka zata iya baka
hadin kai.

Dauke kai tayi sannan ta sake kayanta tana kuma jin tsanar Anum a ranta,
idan ta fahimci wani abu Anum ta zame mata karfen kafa, sannan a duk lokacin da ta
taso domin gyara GOBEN TA, wargaza mata take.

---
"Ai ina miki addu'a Allah ya kawo miki miji nagari, wanda zaki huta na huta, ina
dalilin kasayar da akuyarka ta dawo tana ci maka katanga." Inji Maman Aminu,
"Kwarai! Ai Anum yarinyar nan ba karamin farin jini ne da ita ba, Ni ina ganin a
manemanta har da attajiran aljanu, kiga idan ta fita sai ta shigo mana da kayan
Arziki."(😂 Chaiii if you no die you go neva see wandaful pipul shaa 🤔 naji ance
wani abu)

Wani irin murmusa mata Maman Aminu tayi, tare da wurga mata robon vanilla ice
cream, tana lasa.
"Ai yarinyar tasan darajar kanta, gashi kaf unguwar nan da gidan nan babu wanda
yayi farin jininta, Yar Arziki irin albarka yar da aka haifa tsiya na barci."

Murmushi Umma tayi tana lazumi, domin duk abinda Anum take ƙawowa bata taɓa
amsar shi ba. Wani lokaci a dakin Umma Anum take boye abubuwan da taxo dashi, domin
Maman Aminu da Baba Hama idanun su idanun abinda tazo dashi.

Haka wani lokaci Baba Hama zata na yadawa Umma magana, basu isheta ba balle tayi
kokarin biye masu..

***
"Khadijah!" Ya kira sunan ta dai dai zata shiga cikin gidan "Malam me shayi! Da
wani abu ne?"
Ta tambaye shi, murmushi yayi sannan yace mata.
"Kawai rayuwar da kike ne sam babu wani Cigaba a cikin shi, babu dad'i yau ace kina
hawa wanan motar kina sauka a wancan motar"

"Toh kace kai ma ka fara sana'ar banza sa'ido sana'ar banza, wato kana jin haushin
dan ban kula ka ba shine bari ka fake da guzuma ka harbi karsana. Idan ka cika d'an
halak karka kuma min magana, banza dan kauye kawai."
Kura mata ido yayi sannan ya dauke kanshi, tare da cigaba da jinjina kalmar banza
dan kauye da tace mishi. Komawa shagon shi yayi yana kuma rokon Allah ya bashi dama
ko wacce iri ce ya nuna mata shi dan banzan dan kauye ne.
#Mai_Dambu
[2/6, 9:18 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
BABI NA TALATIN DA HUƊU.

*_Fatan Alkhairi Sadnaf 💞💝🤩😘😍 Nagode sosai_*


😹 gaya muku bani da salo da😹
_Na amma akwai Chakwakiyya zalla🤣 irin sa zuciya tsalle🧗
✊🏽_


Shiga tayi cikin gida tana kananun rashin kunyar ta, sabida ta tsani renin hankali,
ji fa sai kace Ubanta yana wani irin magana sai ka ya ajiye ta, irin ga yar shi.

Nan Mama da Baba Hama suma suka shiga maganar suna gaya mata idan ya kuma
mata magana karta raga mishi tayi mishi tijara taya za ayi dan cirani da kazamin
rayuwar shi zai sakawa yarinya me tsada idanu.

Tun daga nan, bai kuma mata magana ba, amma ya zuba mata idanu.
--- Tare da Alhaji Mudi wuntin dada, suka fito daga hawala hotel. Daga nesa Rulwanu
ya hangota. Cikin b'acin rai ya sauka akan mashin din da yake tafiya ya nufi inda
take, bai yi wata wata ba, ya finciko hannunta yana janta. Duk da ta razana amma
yarinyar nan cewa take.
"Malam lafiya? Waye kai da zaka rike hannuna Jama'a ku taimake ni wallahi ban san
shi ba, dan iska ne"

Lokaci guda yaji kamar an daure shi da jijjiyar shi, a hankali ya juya
ga mutane da suka Mishi kawanya, ji yayi zuciyar shi zata kwace daga kirjin shi.
Bakin shi na rawa, ya juya zai mata magana. Aka rufe Rulwanu da duka, sosai da
sauri ta nufi gurin Alhaji suka bar gurin.
Khadijah amma yayanki ne fa? Idan suka kashe shi fa?"
Tab'e baki tayi tare da dauke kanta tana kallon waje.

"Ni Wallahi ban tab'a cin abinci me dad'i irin na hawalan nan ba, kome nasu yayi
babu laifi"
"Haba gobe ma ai zamu iya dawowa idan kin yarda"

Dariya tayi tana kallon shi, bude asusun motar shi yayi ya ciro mata wata kwali,
sabuwar waya ce dall, juya wayar take cikin wani irin yanayi me cike da jin dadi da
mamaki.

"Ya hajj, duk Ni daya?"
"Haba Baby ai kinfi haka ma," wani fashewa kanta yayi tana murmushi har suka isa
unguwar su. Murmushi yayi tare da riko hannun ta ya sumbata,

"Mun iso gida, me zan kawo miki da daddre?"
"Alhaji ka kawo min Habib yorgot da duk wani abin makulashe."
"Baki da case!"
Suka yi sallama zata fita yace mata.
"Baki ji ba" tsayawa tayi tana kallon shi, ganin yadda yan shagon Maude suka zuba
mata ido.
"Gashi nayi typing so jiya na dawo, na manta ga tsarabarki" mika mata jaka
yayi ta amsa bayan wayar da ya saya mata har da wani kayan, k'arara ta fidda
halinta nason abin duniya, tana murmushi ta amsa tare da mishi godiya, dake tsohon
banza ne, muna mata yayi. Ta sumbaci kumatun shi.

Babu b'ata lokaci ta kai bakinta, tare da sumbatar shi, sannan ta fita tana
mishi godiya.

Tun da ta fito, sau daya ta kalli Maude, sannan ta dauke kanta gabanta
yana faduwa. Tana tsaye Alhaji yabar kofar gidan su..ya tafi sanan ta nufi hanyar
cikin gidan.
"Kasan yanzun zawarawa sun zama ƙaruwai! Basu maida bin maza a bakin kome ba"

Cak ta tsaya tana kallon su, murmushi tayi sannan tace mishi.
"Dayyabu! Da tsohonka muke karuwanci, shi yake biyana kudin karuwanci. Kai ma
munafukin da kake ajiye su sai na zagi danginka mara zuciya, wanda tsiya da talauci
ya hana shi zaman kasar shi ya shigo cin Arziki."

Magana marasa dad'i da muni take gayawa Maude..
"Ke dan Uwarki!"
"Ka gayawa Babar Asabe"

"Jijjiya!"
"Wallahi wannan yarinyar, shikenan Oga."
Ya faɗa cikin jagaliyanci, tare da cin magani, bata fasa zagin maude ba,.har da
cewa.

"Idan kayi zuciya kabar min kofar gidan Ubana, tunda anan aka makale ake zagina
Annamimai munafukai."

Wallahi zaku sha mamaki, babu wanda ya kuma kulata manna mata hauka suka yi
abinsu.
Da wannan bakin cikin ta shiga gida, ko zama bata yi ana aka yi
sallama da Umma, lekowa tayi tare da cewa.
"Anum leka ki gani wake sallama"

Zuba kayan tayi sanan ta koma kofar gidan, Ila ta gani..kallon rashin imani
yayi mata sannan ya dauke kai yana faɗin.
"Ki min sallama da mahaifiyar Rulwanu"
"Mtsew banzan dan ƙauye!"
Aikuwa ya bita zai mare ta, tace.
"Mare ni ka gani, wallahi zaman Bauchi cirani sai yafi karfinka."

Sake sallama yayi bai kulata ba, fitowa Umma tai dan tana jin rashin mutuncin da
Anum take mishi, kallon ta tai tare da girgiza kai tai sannan tace mishi.
"Lafiya malam Iliya?"
"Toh Rulwanu ne ya gamu da hatsari. Yana asibitin badan Allah ya kawo ni ba, toh da
sai dai kuyi hakuri"

Shiru tayi sannan tace mishi.
"Wani Asibitin?"
"Nan bakas!"
"Toh bari na kira yayun shi. Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi."

Sannan ta koma cikin gidan, ta kira Sadeeq ta gaya mishi, ko awa daya ba ayi ba sai
ga yaran Umma dukkansu suka nufi asibitin da Rulwanu yake.

"Me ya faru haka?"
Murmushi me ciwo yayi, maganar Maude yana dake yawo a kanshi.

_Khadijah yar Uwarka ce! Idan ka gayawa Umma har abada ba zata daina ganinta da
tabon ba, kayi ƙoƙarin shiru ka mata addu'ar shiriya, sannan idan ka yi magana ma
zai iya zama rikicin cikin gida, don Allah ka kyaleta muyi ta mata addu'o'in
shiriya_

Idanun shi ne ya cika da kwalla, badan Allah ya kawo ila akan lokaci ba, da shi
kan yasan ya tashi aiki. Share kwalla yayi.

Bayan tafiyar Anum da Alhaji mudi, aka rufe Shi da mugun duka, har suka cewa zasu
saka mishi taya, kokarin ya gaya musu Kanwar shi ce amma suka ki, sauraron shi. Shi
kuma ila ya fito amso kwai ne yaga taron mutane har zai wuce ya tsaya tare da
tambayar me ya faru, nan ake gaya mishi ai wani ne yazo sace wata budurwa, ta yi
ihu shine aka rufe shi da duka.

Gyada kai yayi zai wuce, sai suka d'aga shi sama, shine ya hango rigar kamar na
Rulwanu dan har yana mishi tsiya da cewa yayi zuciya ya canza yar gado, ajiye kwan
yayi tare da tsallakawa.

Ya ciro wayar shi ya kira MAUDE, ya gaya mishi don Allah yazo akan lokaci. Shi
kuma taje ya leka yaga Rulwanu ne.
"Subhanallahi! Malam Rulwanu,"

Dakyar ya bude idanun shi da suka kumbura.
"Kunga d'an uwan shi abokin satar mutane!"
Juyawa suka yi tare da nufar Ila, suka mishi caaa.
"Kasan shi ne? Wato tare kuke sana'ar sace mutane? Toh zamu kona ku."

"Kuna da hujjar da sace ta yazo yi?" Maude ya tambaye su, lokacin da yake karasowa
gurin, ya cika musu ido sosai, kwarjinin da yayi musu yasa suka kasa bashi amsa.
"Rulwanu me ya faru?" Ga baki daya ya fita hayacinshi ya fara mishi bayani,
"Yarinyar da kuka dake shi akanta kanwar shi ce. Ko baku ga kama bane?"

Riko shi suka yi tare da saka shi a napep, suka nufi Asibiti da shi..anan yake
rokwanshi ya rufa mata asiri.
"Mara kirkin mutum! Kaje ka lakato rigima sun maka rotsi, toh bani zaman jinyarka."

Umma ta shiga mishi fada, kwallar bakin ciki, da tsanar Anum yasa shi kuka(😂😹
shegiyar yarinya kowa sai yayi kuka da ita) yana yi yana kwashe mata albarka, tare
da jan Allah ya isa yafi kwando dubu.(😂😹)
.... Lokacin da Umma ta dawo gida tana faɗa abinda ya faru, dariya Anum tayi
tare da gayawa Maman Aminu abinda ya faru, tace.
"Allah ya kara duk wanda ya nufe mu da mugun nufi sai yaga karshen abun shi."

Suka ci-gaba da hidimar su, dakyar Anum tayiwa Umma jajje.

..... Da dare, zata fita dake babu wuta sai a shagon Maude, zauren gidan da
akwai duhu Sosai. Tun a bakin kofar cikin gida ta hango mutum a tsaye, saka kanta
da tayi zauren kamshin turaren shi ya daki hancinta.. sassanyar ajiyar zuciya ta
sauke, yana tsaye tana zuwa zata gitta ta gefen shi ya fincikota. Tsoron shi ne ya
cika zucuyarta. Ta kasa magana.
"Akan wancan dan iskan kika wulakanta yaron da uwar shi da yayun shi suke miki
hidima? Anum wacce irin lalacewa kika yi ne? Maza sun bude miki idanu baki ganin
kowa da gashi. Kyamar ki nake ji! Tunda kin zama abinda kika zama, wawuya jahila
wacce gata bai mata rana ba."

Daga haka ya ture ta, ta fadi shiru tayi domin tsoron kar yayi mata wani abu,
haka ya fita ya barta kafin ta sami damar mik'ewa ta fita, a gurguje suka gaisa da
Alhaji ya bata kyautar shi da ita. Sannan ya bar kofar gidan su.

---
"Alhajin Allah, ai ko uwar Khadijah kasani na dauko maka zan dauko maka ita balle
ita kanta, yanzun ka cigaba da jan ra'ayinta da kyaututtuka wanda zai saka ta bika
ko ina!"

'"Yawwa Xoxo, haka yayi min.kuma zan baki kyauta na musamman. Amma yaushe ne zaki
kawo min ita?"

Shiru tayi sannan tace.
"Ka bari nan da sati Uku."
"Kai ina wallahi a matse nake da ita, kuma idan ban yi yadda nake so ba, kai har
sati Uku!"

"Toh shi kenan kayi yadda kake so?" Ta faɗa tare da bude motar zata fita.
"A'a bai kai haka ba, na amince."
"Akwai bikin yar Shehu, zamu yi anko ka bata kudin zan kai mata ankon ta gani sai
ka saya mata. Idan yaso sai ka kaita gidan ka na bayan airport ba."

"Nawa ne zan baki?" Kallon shi tayi sannan tace.
"Yadda idanunta ya bude da me shayi bani hamsin, da ace a budurwan ta ce zan iya
amsar dari ma,"

Dariya yayi tare da shafa fuskar ta, ya ciro kudin sannan ya ce mata.
"Karki ji kome idan tayi min zan kara miki sama da haka"
Tab'e baki tayi sanan tace mishi.
"Karka damu ai wani ya tsotsa abinda zaka samu dan haka wani abu da zaka samu!"

Haka dai suka yi ta jayayya har ta gaji tare da fita daga cikin motar.

..... Bayan kwana biyu, aka sallami Rulwanu, tsakanin shi da Anum ido, domin
Allah ya gani tsoron sharrinta yaƙe, yarinya karama ta zama bom, dan haka baya mata
magana. Sau dari idan zai shigo gidan ya same ta ita daya baya tab'a kallon inda
take, zunzurutun sharrin ta. Ita kuma tsabar niman tsokana idan ta ganshi dariya
take mishi, bai tab'a damuwa ba.

... Matar Aminu da ta haihu, kullum zata fita zuwa gidan nan kuwa yawo
take fita da Alhajin Allah, wanda yanzun take mishi lakabi da suna baby, idan yace
mishi baby.(soko 😂 Chaiii)
Abin haushin haka zai ta yawo da ita, ana gobe suna ya dauke ta zuwa
Zaranda hotel,. Anan suka yi kicibis da Ya Abubakar, ranshi ya kai kololuwar ɓaci.
Har inda take ya nufa sannan ya nuna mata motar shi, babu musu ta juya, ba tare da
ta cewa Alhaji Mudi wani abu ba.
"Alhaji mudi, kai babban mutum ne. Kuma kana da wasu abubuwan na girmamawa. Don
Allah ka rabu da kanwata."
"Toh amma ai ni sonta nake"
"Ba soyayya bace, Muradin rai da zuci ne don Allah ka bar mana ita!"

Bai kuma magana ba, yana kallon su, suka bar hotel din. Tunda ya saka ido akanta
sai da yayi abinda yake so da ita zai kyaleta.

.... Bai mata magana ba, suna isa gida, ta fita, bai iya hakuri ba dan ya
zuciya sosai..dan an sha kawo mishi karar ta, da abinda take aikatawa. Yana shiga
kawai cikin gidan ya shiga rufeta da duka. Aikuwa Hafsat da Safiyya suka fito.

Tare da tambayar me ya faru, ranshi ya b'aci.
"Zaka kashe ta ne? Wannan rashin imanin na me?" Inji Hafsat.

Bai fasa dukarta ba, sai da Umma tace mishi.
"Ban sanka da wannan halin ba, ka kyaleta idan ka kuma d'aga bulalan a jikinta
lallai furucin da zai fito bakina zai tab'a har bayan bayanka!" Wurga da bulalar
yayi, cikin bakin ciki ya kalli Umma da jajjayen idanun shi,
"A hotel na same ta ita da wani mutum wanda kowa yasan mutumin dan iska ne da
tsofar shi yake bin Kananun Yara."

"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun,

Please Login or Register in order to submit comment