You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar a gaban shagon shi, kowa sai jin haushin wannan banzan
soyayyar da yake mata yake ji, amma shi ko a jikin shi, ya kance musu "mun san
darajar na gaba damu, dan haka babu iya kallon a ci zarafin al'umma mu kyale
mutum."
Kwanakin malam biyar a gida, sannan ya koma gurin aikin shi, malam a tsaye
yake jinya amma yana ƙoƙarin boye damuwar shi babban matsalar shi Anum bata kosa
bane, amma ta kosa da baɗala.

Tun daga ranar aka kara tsayin katangar gidan, sannan aka zuba
mata ido, ga Umma yanzun ta dauke mata wuta, sosai take mata bana wasa ba.
**
Mika mata foam yayi ta kalla da wasu takardun.
"Akwai me napep din da zai na kai ki yana kawo ki, sabida kiyi kokarin daukar
abinda kika rasa na shekara daya."
.kallon shi tayi a wulakance..
"Toh banda rashin zuciya meye na biya min waec, Ni bana son shishigi da gulma, idan
an saka sai kayi kana wani nuna kai na Allah ne, nan kuwa babu abinda yake ranka
sai jikina daga ranar da ka samu ko kallo bai isheka ba."
.tana fadar haka ta juya tare da barin Maude a tsaye rike da takardan da ya kawo
mata ji yaƙe kamar zuciyarshi zata buga, yana kallon yadda take mishi rashin kunya
bai iya katabus. Dan haka bai kuma bin takanka ta ba,

Karshe ya bawa Malam takardun sai duk kunya ta kama shi, bayan kwanaki ta
fara zuwa makarantar, toh makaranta ne na yaran manyan, dan haka akwai masu zuwa
da wayoyin su.

Ranar da ta dawo tazo ta tsaya mishi.
"Kasan makarantar yaran manyan ne zai turani bani da waya?"
Murmushi yayi sannan ya ciro wata bakar leda ya mika mata, a wulakance ta amsa,
sanan ta juya cikin gidan su, ko nagode bai samu ba, tana shiga ta bude wayar LG.

Wani irin ihu ta saka tare da fitowa daga ita sai rigar makarantar da yar
skirt, ta bar hular ta a cikin gidan, wadatattun gashin kanta da aka mata kitson
cuku, ya sauka har wuyar ta, ga wani gurun wuya da ake dashi wanda ya kara mata
kyau, murmushi tayi yan manyan jorarrun hakoranta, ya bayyana.
Juya ido yayi tare da girgiza mata kai, da sauri ta juya inda yake ta
saka hannunta a bayan shi ta rungume shi kanta a bisa kafadar shi, tana dariya,
domin yana zaune ne a kujeran shayin shi.
"Mutane na kallon mu!"
"Nagode sosai! Ka fitar dani kunya ka nunawa duniya cewa Ni din mowa ce, a duk inda
nake!"

Murmushi yayi sannan yace.
"Toh kanki ba hula balle dan kwali, gashi kayan makarantar me haske ne, a taimake
ki a koma haka na gode."

Dariya tayi ta fita, da gudu tana murna, girgiza kai yayi tare da cewa a
ranshi..
*Khadijah indai kyauta ce muradinki kin samu har karshen rayuwata*

Ai da ta nunawa malam wayar yayi murna yazo har shagon yayi mishi godiya, Maman
Aminu kuwa ganin haka sai da ta mata fada karta sake ta fara son shi domin kuwa ba
zata iya daukar kasadar abin kunya ba, ace yarta dukiyarta takare da auren me
shayi, wannan ai faduwar darajar tace.. ga fura da nono amma babu ludayin damu.....
#Mai_Dambu
[1/31, 11:28 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
Na shiga ban dauka ba...!!
BABI NA SHA BIYAR.

"Kai Mamah kudin shi zan tatsa fa, zanci rabo nake kafin Allah ya kawo min
wanda ya fishi,ina zan kai wannan damuwar, ya nace sai kace talauci." Tana fadar
haka tana juya wayar hannunta, wani irin murmushi take fiddawa me daukar hankalin.

Haka Mama ta gama fadarta Anum bata damu ba, dan itama yar nima ta iya
shariya, washi gari suna zaune tana cin shinkafa da miyar hange aka yiwa malam,
umma tana wanke sawunta. Wani yaro yayi sallama rike da kofin tea da tiren kwai da
indomie.

"Dahiru! Sannu kacewa Maude nagode!" Har zai fita yaron ya mika mata wata
karamar farar takarda a wanda ya fidda shi daga aljuhun shi yace.
"Inji Oga Maude!"
Dariya tayi, dan ta saba amsar takardun shi sun kai amma bata tab'a buɗewa ba,
dariya tayi ta buɗe.
`Amincin Allah ya tabbata a gare ki, kyakyawan fuska ma'abocin murmushi da Ƙawa! Ki
duba sakona a wayarki!" Sai yanzun ta tuna wayar fa har da layin etisalat.

Tana buɗewa sakon soyayya ce,dariya tayi ta mishi har tana tintsarawa, tana
mishi kallon Gara koda yake tasan bashi zai rubutawa ba, zai bada a rubuta mishi
ne, dan haka ta share zancen bata kuma bin takai ba.

Bayan kwana biyu, Safiya ta haihu. Tattarawa Anum tayi ta koma gidan,Nan
yayunta aka yita zunzutatta, tare da wani kambama ta zaka rantse wata me ilimin ce
kome kamila, nan kuwa kyan fuskarta kawai yake rudar su. Kawayen Safiya da Hafsat
idan suka zo Barka sai shige mata suke, musamman ganin yadda take sanye da dan
kunnen gold da zoben shi. Anan wata take tambayar Safiya.

"Badai Anum ce ta girma haka ba? Kai masha Allah, ta gama secondry school ne?" Ta
kafe Safiya.
"A'a tana kai ne, ma. Insha Allah Soon zata gama." Gyara zama tayi kuwa ta
fara neman hanyoyin da zata nemi su hada kan Anum da Baban Yaron mijinta da yake
zaune a kasar waje.

Rimi Rimi aka ayi magana, bata gurin. Sannan yayunta suka ganin yadda Matar take.
Aikuwa take aka amince, har aka ɗauki maganar za a kai gurin malam.

**Ana jibi suna Anum tazo gida,dan dama sunyi waya da Maude zata zo, yana ganinta
ya barwa Ila hidimar shayin, yazo gurinta.

"Yan matan Maude! Kwana biyu baki je makaranta ba, me yasa?" Cak ta tsaya dama
tana waya ne kallon shi tayi daga sama har kasa, sannan ta tab'e baki,shekar
kamshin turaren shi tayi tare da bude idanun ta.

"Amma ai na gaya maka yayata ta haihu? Wai tsaya Bokon nan lahira zani dashi?" Ta
tambaye shi tana kallon fuskar shi.

Yadda yaƙe zaneta da idanun shi ne yasata yin kasa da kanta cikin sauri, dan kaifin
idanun shi yayi tasiri a jikinta.
"Ko koyi girmama nagaba dake, ko ba dan Ni ba, sannan ko a can zaki iya zuwa
makarantar ki,zama babu karatun ba zai amfane ki da kome ba.

Amma Arziki ne ace kana da ilimin addinin da na zamani, sannan, akwai aikanki
ki anjima za a kawo miki daga gurin tela na fitar sunan."

Daga haka ya juya abin shi, yasan koda zai bata kyautar da zai fi haka sai ta
gadama tace ta gode.

Bayan ta shiga cikin gidan, yana jin wani irin yanayi a ranta, amma haka
ta yakince shi ta watsa a gefe, ta shiga kitchen ta kwashi abinci ta koma gefe ta
fara ci, karo tayi da dutse, ta tsame hannunta tana kallon Umma da take dariya.
Yau sai dai kiyi hakuri, dan Shukrah ce tayi abincin kuma ta koma gidan su.
Raurau tayi da idanunta, ta mike tare da ɗaukar gyale ta fita, tana zuwa daidai
window da yake shagon ta buga mishi. Wato a duniya idan kana niman mara kunya ka
sami Anum kawai ka godewa Allah. Yana bude window ta sake mishi kuka.

Kura mata ido yayi, kafin yace mata.
"Me yasa?"
"Yinwa!" Ta faɗa a sakalce,
"Me zaki ci?"
"Soyayyen kwai, da namar tukunya, sai seven ko!"
"Dahiru zai kawo miki."
Juyawa tayi ba tare da tace mishi ta gobe ba, Bayan minti goma sai ga yaron ya
kawo mata, har zai fita tace mishi.
"Kacewa Oga Maude ina son cin kilishi."
"Toh Auntyn mu!"
Share shi tayi ta zauna, ta fara cin abincin kallonta Umma tayi Allah ya gani bata
da kwadayin ire-iren waɗannan abun.

Dan haka koda Mamn Aminu ta fito ta samu abinci kaca-kaca a gaban Anum, zama
tayi ta saka hannu suka fara ci, kawo mata kayan da aka yi ne yasata amsa.

Diamond ne guda daya sai Classic, tare da Phonixs hitaget me
fanti ruwan ash, riga da zani anyi mata ɗinkin pieces. Sai takalmin da haka, sai
wani karamin kayan kwalliya, da chocolat bata tab'a ganin irin shi ba, kiran Xoxo
tayi awaya tazo ta gani. Umma kallon su take kawa, Mama kayan bai burgeta ba,.domin
ita bukatar ta Anum ta haɗu da wanda yafi Maude haduwa.

Da Xoxo tazo Unguwar daukar kayan tayi ta kai mata, murmushi
tayi amma har ga Allah kayan gani take kamar ita ya dace tasamu kayan ba Anum ba.
Dan haka tab'e baki tayi sannan tace mata.
"Zan tafi, naga kaya sunyi kyau."

Tana fadar haka tayi tafiyar ta, ta rasa gane wani irin kashin Arziki ne da
ita, duk yadda yaso ganin Anum sai taga kamar kara bunkasa take,

...... Ranar suna da wuri Anum ta koma, bayan maude ya bata nashi gudummawar, har
take ce mishi.
"Maude wai wani irin turare ne Kake amfani dashi wallahi ko kudi ka bani zaka samu
yana kamshi turaren"

Murmushi yayi sannan ya mika mata leda sannan yayi mata fatan Alkhairi, rau rai tai
da idanunta. Tare da matsawa jikin shi sosai. Kafin ya ankara ta d'an jingina da
jikin shi, a rikice ya kalleta. D'ago kai tayi tana kallon shi. Tare da shakar
kamshin turaren shi.
"Baka gaya min sunan shi ba!"
Allah sarki a binka da mutum me cikakken lafiya, duk sai yayi gaba daya kome ya
kunce mishi.

Da dabara ya janyeta a jikin shi, yana kallon yadda take tura
mishi baki, shafa bakin yayi cikin wani irin romantic, yana jin he was miss more
moment, a hankali shaiɗan ya shiga kawata mishi dan bakinta, ba zai iya cewa yayi
losing control din shi ba, amma qaddarar shi da Anum wata aba ce ta musamman da
take yawo a jinin shi, a hankali ya kai bakin shi kan nata. Zato idanu tayi cikin
sauri dan ta tsani kiss. Ture shi tayi cikin b'ata rai tace mishi.
"Kai Ni bana son Iskanci, na tsani wannan kazamtar, wani a hada baki kai naka jin
kyamar abine ne."

Dauke fire yayi cikin damuwa, ya janye tare da barin ta a zauren , har ya isa
bakin kofar yace mata.
"Idan kin shirya na turo mutane na gurin Malam!"

"Ta..." Kome ta tuna sai kuma tace mishi.
"Karka damu!" Ta juya da sauri ta bar gurin shi, cikin gida ta kai kayan tare da
nuna musu, sannan ta shirya zuwa gidan sunan, ta kaiwa yayarta Safiya nata sakon da
ya bata. Hmm Umma da Malam zuba masu ido yayi domin dab sunan Hafsat tazo mishi da
maganar kawar su, bai ce mata kome ba.

...Toh ranar sunan ne aka kuma gaya mata wanda ake son hada su, kan uba zo kuga
Anum tana wani Blushing, zata auri wanda. Za a kaita kasar waje. Kanta yayi wani
tankwalelen ji take kaf unguwar bakin kura babu big beby. Dan haka tun da aka gama
suna take rayawa a ranta ta tafi Chicago.

..... Bayan suna da kwana biyu, ta dawo, shigowar Xoxo idan ta gaida Umma tana
hada dambun shinkafa, ta gaida ita. Kamar zata mata magana sai kuma ta bawa kanta
hakuri ta juya ta cigaba da aikinta, can suka fito.
Umma bari na raka Abidah waje"
"Kin san ALLAH! Kika wuce minti talatin sai na fasa jikin ki." Umma ta
gaya mata kai tsaye. Kallon juna suka yi da XOXO, dake Allah ya daura mata tsoron
Allah da tsoron dukar Umma, tace.
"A'a Abidah jeki kawai."
Tana zare idanu,

"Kai Maman Sadiq, tsananin ba shi yake gyara yaro ba, kawai addu'a shine ma..."
"Hmm! A gaban su kike gaya min magana Maman Aminu? A kan idnun su.".tayi maganar
tana wani irin murmushi me ciwo,
"Kuje karki dad'e."

Umma bata ce kome ba, amma da Anum tazo fita daga gidan tace mata.
"Zaki yi kuka wallahi."
Bata iya fita ba, ta juya tana kallon Umma dan tunda ta fadi haka ita a tunanin ta
umma dukarta tayi, sai da Maman ta tace taje karta jima.

Ta fita da sauri, tun Umma tana hada dambun, suka fita har ta daura,. Ta kuma
dake karago ta tankade da rariyar biski. Tana yi tana kallon Maman Aminu da take ta
leka soro, murmushin takaici tayi ta Cigaba da abinda take yi.

Karfe uku sai ga zugar yan mata,.kana ganin su kaga yan bariki ( Allah ka
shirya mana haularmu 🙏🏼) sun saka Anum a gaba lallai sai ta fito musu da kudin su.
Yadda suka shigo gidan tana kuka, tare da rantse rantse bata dauki kudin ba, yasa
Umma dauke kanta.
Mamarta kuwa ta shiga hayagaga, anyiwa Anum sharri. Kukan da Anum take
ya takura Umma sosai, ita kan bata san wani irin kauna takewa Anum ba, kallon su
tai sannan tace musu.
"Me ya faru?"
"Kinga Baba, mun ajo ne aka tara kudin ajon kawai, zuwan wannan me shegen kyau ta
sunkuce mana." Inji wata yarinya bata wuce sa'ar Anum ba.
"Kuma kun duba baku gani ba!"
"Hmm!" Ta kalli Umma, dan da farko da tayi maganar Umma tana daura tuwon dare ne,
ido biyu da tayi da Umma sai tayi mata kwarjini da kamala.
"Kika ce kun duba?"
"Eh!"
"Nana Khadijah! Kin dauki kuɗin su?" Umma ta wurga mata tambayar,
"Wallahi na rantse da Allah, Umma ki duba ni ma!" Ta faɗa cikin kuka. Kallon su
Umma tayi tsaf da XOXO wacce take bayan mutane, tacewa Yan matan su shiga dakinta
su zauna su bar Xoxo da Anum,
Babu musu suka shiga ita kuma ta tura Xoxo da Anum dakin Anum, suka shiga tacewa
Anum.
"Maza cire min kayanki!"
Babu musu ta cire kayanta tass, daga ita sai pant da bra,
"Saka ki je dakin Malam ki jirani!"
Bayan tasaka tafita, Umma ta kalli XOXO da tsoron Umma ya kamata.
"Nasan kice kika dauki kudin nan! Bani ko ki gaya min inda yake aje a dauko zan
rufa miki asiri nace musu ba biya sune!"

Cikin wani irin rawan jiki ta ciro pieces na kudin yadda ta kasa shi a jikinta,
cikin wani irin bakin ciki take kallon yarinyar.

Tana mika mata,.tace mata.
"Abidah, ni nasan alaƙar ku cutarwa ce,.kina zaluntar zuciyar da babu sharri a
cikin ta, amma ki sani Allah zai bi mata hakkinta, wallahi hakkin Anum ya tashi
kamaki, sai kinyi da gaske. Allah baya barin wani da hakkin wani, kina cutar
Khadijah ainun, amma ba kome kece jarabwarta, shi yasa take jin maganarki.

. Hmm Allah zai saka mata fa, wallahi na kuma ganinki da ita ko kika kuma
kiranta, na rantse da Allah sai na kama Mahaifiyarki da Mahaifinki sai na saka an
daure su.. kinsan Muttaka ai? Kin san yana aiki da yan sanda ne? Toh wallahi na
rantse da Ubangiji sai na saka an rufe min su. Na kuma ganinki da Anum zan saka
Rulwanu yayi miki dukar kawo wuka, kuma naga wanda ya isa ya hana shi."

Nuna mata hanyar fita daga dakin tayi, yarinya karama da bata wuce shekara goma sha
takwas ba, nonuwar ta kamar wacce ta shayar.

Koranta umma tayi ta kuma sami yaran tayi musu wankin babban bargo, ta kuma
tabbatar musu suka kuma niman Anum sai ta saka an rufe su.

Kamar munafukai suka bar gidan, tare da mamakin a inda aka aka sami kudin.
Mugu dan masara sai ga XOXO.
#Mai_Dambu
[1/31, 11:28 AM] +234 813 026 9641: ZANEN QADDARA TA..!!

Mai_Dambu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai..
Mare ni kad'an....!!
BABI NA SHA SHIDA.

_Idan na sauko a canza min suna 🤨🤔_

XOXO da taga asirinta bai tonu ba, ta shiga bin Kawayen su tana gaya musu Anum ce
Barauniyar su.

Tun bayan da abun ya faru, Anum ta shiga hankalinta na kwana biyu. Ga saurayin
da aka ce za a hada su ke suna Hamid yazo yana Abuja, gefe daya ta fake Maude, ta
daina kula shi idan dai ba yatsar shi zata yi ba.

Yadda yayi kwalliya tare da karya hular shi, ya tsaya a gabanta. Saka shi
tayi a gaba tana dariya, shima murmushi yaƙe. "Don Allah Maude wani irin turare ne
haka kasan ranar sai da Ya Usman yayi maganar turaren ka, da yaji kamshin a jikin
ledar kayan da ka turo min."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Turarena yar duri ce, kuma daga, Saudiya da Oman ake samun shi, yana da kyau da
tsada hmm kudin shi."

"Tsaya Maude, wallahi kana da abin dariya yo ko tabirin shayinka ka sayar ai
bazaka samu kudin zuwa umra ba, balle aikin hajji."

"Zaki umran ne?" Ya tambaye ta cikin sigar gaskiya da gaskiya.
Kallon shi tayi tana dariya,.tare da nuna shi.
"Yanzun don Allah banda kanzon kurege ta ina zaka iya biya min kudin Umra, kaga
maude ka bar yaudaran kanka, domin kalaman ka dariya suke bani." A takaice dai Anum
karya tashi take son yi. Dake tana jikin kofar gidan ne, shi kuma yana bakin Kofar
gidan.

Takawa yayi har gabanta, ya tsaya . Hannun shi shi ya kai kan k'ugunta, a
zabure ta kalle shi. Me data cikin soron yayi yana kallon fuskarta, kokarin ture
shi ta fara.

"Kaga Maude!"
"Zaki Umran ne?"
"Wannan sai a mafarkina zai tabbata, don Allah cire hannunka a k'uguna bana son
haka."

Kara matseta yayi da jikin bangon tana jin yadda zuciyar shi take wani irin buguwa.
"Baki ji yadda zuciyata take bugawa bane? Baki ji yadda take cike da kaunarki ba?
Ambaton ki take ba dare ba ran!" Yana mata maganar ne bakin shi dai dai kunnenta.
"Dalla Malam kyale ni bana son Iskanci"
"Waye dan iska!"
"Ni ban zageka ba"
"Koma meye idan Allah ya nufa zamu zauna inuwa d'aya, zaki tantance haka, Anum ki
bani daman mu gina rayuwar mu cikin kaunar juna! Ki amince min mu raya duniyar mu.
Insha Allah zan gina miki farin ciki, zan bakin abinda baki nima ba da izinin
Ubangiji."

Dariya ta saka mishi tare da ture shi..
"Da teburin shayinka? Nawa zai kai balle a saya min abinda nake so? Maude ni fa,
nafi kaunar rayuwa sama da soyayya, ka Fahimta mana"

"Na fahimci irin rayuwar da kike bukata, ba shine kuke kira Luxury life
ba?" Ya tambaye ta.
"Better!"
"For You!"
"Kace kai ma ka fara jin Broking English gaskiya kaci a tafa maka! Tun ku yan Nijar
official language dinku Faransanci ne!"
"Eh gaskiya kan zama da yar Najeriya ya sani koyan Harshen turancin dole dan na
fahimci autar malam baturiya ce."

Ya fadi haka yana matsawa daga jikinta..
"Maude akwai ashoben da zamu yi kudin shi dubu goma, kudin dinki dubu bakwai."
.cike da mamaki yake kallonta yana faɗin.
"Anum ke daya kinci dubu sha bakwai, gaskiya a rage min babu kudi ba."

Cikin tsiwa ta zuba mishi ido, amma dake tana niman abu ne, kallon shi tayi
kamar zata saka mishi kuka tace mishi.
"Ai shikenan! Zanje na nemi wanda zai bani kudin kasan da haka ka matsa min lallai
kana sona yanzun kasani na kori samarukana sannan kana kuma nuna min renin
hankali."

Yadda Anum take nuna ya hanata rawan gaban hantsi abun ya dame shi, bai ce mata
kome ba ya bar zauren gidan.

..... Washi gari ta shirya ta tafi makaranta, domin ta Fahimci idan tana
son abu ta fara zuwa makaranta, wato yaudarar maude ya bata.

Aikuwa sati biyu ajere ta tafi makarantar, ranar juma'a ya bawa Rulwanu dubu sha
bakwai ya kai mata da wani kwalbar turare da yadin shadda light blue.
Mika mata yayi tare da cewa..
"Gashi inji Atm card dinki wallahi Anum zamu yi uwar watse dake, kowa yasan halin
da kike jefa bawan Allah nan, idan kina son abu ko bai dashi sai ya nima anya da
imani a kirjin ki."

"Kan Uba! Ni na roke shi? Da zaka sani a gaba kamar Ubana kana min fada bari
kaga Iskanci." Tattara kayan tayi fuuuuu tayi waje, Maman Aminu tace.
"Haka nake son mutum, ai bashi bane autar maza,.maida mishi kayan shi."

Wani irin takaitaccen kallo Umma tayiwa Rulwanu, tare da cewa..
"Sai ka zuba ruwa kasha ka hada husuma!"
Zai mata bayani ta d'aga mishi hannu, dole yayi shiru.

--- "Maude wato bawa Rulwanu kayan kayi yazo yaci mutuncina?"
Numfashi ya sauke sannan yace mata.
"Koma window cikin gidan muyi magana"

Koda suka dawo cikin gidan, rarrashinta ya shiga yi har su Yaya Abubakar da
Bashir da Abdul Hakim suka zo daru take mishi, suma basu ji dadin rashin kunyar ba,
dan haka cikin lalluma suka jata cikin gidan suka shiga rarrashinta, kallon yadin
shaddar Bashir yayi cikin nutsuwa yacewa Abdul Hakim.
"Kasan wannan yadin kwananan na ga tallar shi a wani bincike da nake a google!
Kasan nawa kudin yafi dayan shi a kudin najeriya?"

Tura baki tayi sannan tace.
"A'a dari biyar ba, dake ya mai dani sakarya shine zai kawo min yafi me zubin sky,
wato ga yar kauyen kayau, ai wallahi ba dan kun dawo dani ba, da yaga yadda ake
rikici da rai ina kallon shi wato ya maidani jidali."
Takaici yasa Rulwanu juyawa yanar gidan yana ji da Allah zai bashi dama daya da
yaci Uban Anum daidaigwargwado ()😂amma Umma itace matsalar shi yanzun ta fara
Mishi fada da Niman make shi..kwafa yayi.

Ita kuwa ya zauna a tsakanin su, tayi ta zuba tab'ara sai da Umma ta daka mata
tsawa ta tashi tana tura baki zata yi kuka,
"Ayya Umma! Har..".
"Haka kake kallon su Bello suyi abinda suke so? Tambayar ka nake Abubakar,.nace
haka kake kallon su Ha'uwa suyi abinda ransu ke so? Toh indai ba zaku taya ni akan
Anum ba karku kuma shiga maganar ta"

Sai dai basu ga wani abun da yasa Ummu take d'aga hankalinta ba, kawai dai ta
cika uzurawa ne, amma ai Anum bata da matsalar kome, umma ce kawai me wannan
matsalar tare da takurawa Anum.

D'aga yadin Abubakar yayi, sanan yacewa Bashir.
"Wannan yadin nera hamsin ake sayarda yadi ukun nan fa? Lallai shayi tana kai
mishi!"

"Hahaha! Baka tab'a jin kamshin turaren shi bane, Yawwa ga kwalbar. Na tab'a jin
kamshin sa sau daya lokacin da mukayi tafiya da tawagar me girma gwamna zuwa
abuja,. Jikin mataimakin shugaban kasa naji kamshi domin na zauna kusa dashi
sosai."Inji Abdul Hakim,
"Kai Hakim! Karya dai ba dabi'ar ka bace?" Inji BASHIR,
"Wallahi ba da wasa nake maka ba, ni da hancina na tab'a jin shi kalar turaren bana
mata bane, Anum!!" Ya kwala mata kira,
Fitowa tayi tare da kallon shi.
"Wannan turaren kece kika ce kike bukatar shi?"
Cikin sakarci tace..
"Tab me zanyi da turaren karamin kwalba? Kawai zan ajiye ne ina sakawa a man
shafawa na."
"Saya yake ko?" Tab'e baki tayi zata bashi amsa Umma tace musu.
"Haramun ne shiga abinda babu ruwanka." Tsit suka yi,

Ita kuwa ta koma d'akinta,.tattara kayan suka yi tare da ajiye kowa ya shiga fita
kamar munafuki. Dama bikin yar mijin Hafsat ne ta nemi kudin a gurin Maude.

Haka ranar taki zuwa makaranta, ta shirya zuwa, Bakaro inda Hafsat take
aure, ta kai mata kudin, bata dawo ba sai dare, tana isowa ta kalli shagon shi babu
mutane, shiga tayi ta zauna a kujeran bai sani ba.
"Maudeeeee!" Ta kira sunan shi da karamin murya, har tsakiyar kan shi yaji
muryanta, jikin shi babu laka ya juya dan ji yaƙe kamar bai mallaki gangan jikin
shi ba. Zuba mata rikitattun idnun shi yayi yana binta da wani irin sansassanyan
kallo.

"Hmm!" Yace mata yaki magana, ya cigaba da abinda yake.
"Maudeeeee!" Kin kulata yayi sai

Please Login or Register in order to submit comment